Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sa ni banzo asibitin ba, amma ai momy tazo. Tace, Momyn taka me tazo tayi in ba wulaqanci ba? Don haka inason in fada maka babu inda Na'ima zataje. A Gidanka ma bataji dadi ba bare a gidan iyayenka? Usman yace, ayi haquri dai momy. Nan da can duk daya ne. Momy tace, ba zataje ba. Abbas yace, shikenan zan kira daddyn nan gidan. In ba zata koma ba, saidai mu rabu. Momy tayi shiru, ta kasa magana. Domin tasan Alhaji baisan komai ba a kan matsalar. Da qyar tace, ka fada masa mana! Zai matsa mata dole ne? Abbas ya miqe, ku tashi muje su usman! Zan bada mamaki Gidannan. Suna fita Na'ima ta fito tana kuka tace, Momy ni bazan koma Gidansa ba, bare Gidan iyayensa. Ni tsoron mamansa ma nakeji. Momy tace, qyaleshi yayi ta fadama daddynku din. Ynxun ne suka san ki koma can? Da suna so ki koma da basu kaiki asibiti ba? Na'ima dai sai kuka, ita kuma momy tana lallashi.
Shi kuwa Abbas ya gama tsara ribar da zaici gurin mahaifinsa da wannan cikin. Ynxun burinsa a samu namiji kamar yadda mahaifinsa ke matuqar so. Haka kuma shi da mahaifiyar sa suna ruwan ido akan abinda ya kamata su za6a a matsayin kyautar da kakan zai bawa jikansa. Shi dai yana sha'awar gidan saida motocin Alhajin nasu, yayin da Hajiya Bilkisu ke sha'awar wani kamfanin Alhajin. Ranar asabar, Alhaji Bashir yana zaune a bayan mota tare da 'yan samarin sa guda hudu, malumfashi suka nufa gurin Hajiya Binta. In sun kwana biyu su wuce masari don ganawa da dangi, wato su ziyarce su. Wayarsa ta buga, Ameen ya miqo masa, yana kallo yaga lambar Abbas. Bai ta6a kiransa ba. A fili yace dan nemabbaka ta6a kirana ba, sai yau da aka samu qaruwa. Ya daga suka gaisa, sannan yace, daddy dama inason in fada maka ne an sallami Na'ima daga asibiti, amma momy tace, ba zata dawo gida ba saidai ta zauna Gida gurinta. To kuma daddyn mu daya dawo yace ta koma can gidanmu gurin Hajiyarmu. Da naje don mu taho, sai kuma momy ta hana. Ran Alhaji Bashir ya 6aci matuqa, cikin zafin rai yace, karka damu zansa akawo ta har gurin Hajiyar taku. Abbas yace, nagode daddy. Alhaji yace, babu komai. Suna yin sallama ya kira layin momy Nafisa, tana dagawa, ko amsa Sallamar ta baiyi ba ya soma ruwan bala'i. Nafisa kina hauka ne zaki rabo yarinya da Gidanta? Sbd me? Ba zan amince ki zubarmin da mutunci ba, in har ke baki damu da naki mutuncin ba.1⃣4⃣Tace, tsaya kaji Alhaji! Ba zanji komai ba. Ya katse ta. Zan kira Hamisu ynxun nan yaje ya kai yarinyarnan Gidan minister, kamar yadda suka buqata. Sannan zan gargadeki, kar ki bari inji wata matsala ta fito da sunanki a ciki, ko wani tseguminku na mata. Aure zaki kashe mata ko me? Tace, kasan da Yarin..."ya sake katseta, ba nace kiyimin shiru ba ne? Kinsan Allah kikayi sanadin kashewa yarinyarnan aurenta, ko kuma kika zama silar matsala tsakanina da Abokina, wlh saina baki mamaki, zan yi miki abinda baki zata ba bare tsammani. Ke baki da hankali ne? Baki ganin halin da nake ciki na rashin Mimi da kuma ciwon dake damunap. Shiyasa har in koma ga Allah ba zan daina son Sauda ba da ganin qimarta da girmanta. Kizo katsina ki ganni, kiga yadda na samu lfy da kwanciyr hankali, sbd ina tare da mace ta gari mai tattali. To na fada miki, ki fita idona in rufe. Ya kai qarshen maganar tare da kashe wayarsa
Momy Nafisa, tayi shiru da waya a hannunta, bata ta6a ganin ranar da Alhaji yayi dogon sababi ba kamar na yau. Bata da wani za6i face, yin abin da yace, amma dukda haka saida ta kira layin Hajiya Nana, ta fada mata cewa, Alhaji yace, lallai sai Na'ima ta koma Gidan surukanta. Hajiya Nana tace, ki barta ta koma zamu san yadda zamuyi mu samu mafita. Tana aje wayar, Hamisu yana shigowa. Ya gaida momy, ta amsa rai 6ace. Yace, maigida yace... Ta katseshi, karka cikani da surutunka! Jeka naji, zata zo inta shirya. Ta shiga dakinta inda Na'imar take kwance kan gado, ta zauna a bakin gadon. Na'ima taso kiji! Tace, menene? Bayan ta taso, momy tace, ki tashi ki koma can gidan su Hajiya Bilkisun. Na'ima ta soma kuka, ni ba zanje ba momy. Gsky, na haqura da auren Abbas. Baya sona ko kadan. Momy Nafisa ta riqe kai, cikin damuwa tace, kai ni dai wannan abu ya isheni dai, wannan abu ya isheni. Duk nice na jawoshi. Inda nasan ma haka halin Abbas din yake, wlh da nabar Mimin ta auri Abbas din. Na'ima tace, inda itan ce na tabbata ba zai mata haka ba, don yana mugun sonta. Momy tace, yi mata zaiyi dan bariki, dan bariki ne. Da an gama soyayyar, za'a shiga tsiyar. Ke dai ynxun ki tashi muje can din mu gani. Na'ima tana kuka, tana komai ta kwashi nata ya nata aka nufi Gidan minister da ita.
[17/09 1:18 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa

1⃣5⃣Mimi tana zaune a tsakiyar katifar dakin Ismail na zaure, da idanu take ta bin dakin da kallo tamkar bata ta6a shiga cikinsa ba. Ismail dake qoqarin kunna mata 'yar tsohuwar fankarsa, ya kalleta, "me kk kallo a dakin? Shine dai, ba'a qara komai ba, kuma ba'a rage komai ba. Mimi batasan ma yayi ba, tunaninta yana can gurin sashinta na Abuja, amma dubi inda take ayau. Gsky bata ta6a tsammanin ko a cikin mafarkinta abinda ya faru dinnan zai faru da ita ba. Kuma kowane lokaci tayi dogon tunani don ta gano menene laifinta a cikin duk wadannan abubuwan da suka faru, amma bata gano ba. Kowane lokaci tunaninta yana tsayawa ne akan laifin na mahaifanta ne. Tafi dogara akan cewa, basa sonta ne, ko kuma tace, daddy ya daina sonta, don dama can Hajiya ba wai tana sonta bane. Da wannan ta dogara, takeson nesanta kanta dasu iyayen nata yadda ba zasu sake jin labarinta ba.
Ismail dai tsaye yayi yana kallon yadda hawaye ke kwaranya daga idanunta. Dukda cewa ya saba da ganin kukan mimi, amma daga ganin wannan na musamman ne. Da haka ya nufi gurinta, ya zauna a gefen katifar, cikin sanyin murya ya kira sunanta, "khadija! Kina jina khadija? Kina jina? A firgice ta kalleshi, yace me kk yima kuka? Cikin shasshekar kuka tace, babu komai. Yace, khadija, Kalle ni! Ta dago ta kalli cikin manyan idanunsa. "zuwa ynxun na fahimci halayenki a dan zaman da mukayi, fahimta ta sosai. Inda ni marubuci ne, tsaf zan rubuta halayenki. Duk kalar kukan da zakiyi, ina iya fahimtarsa. Nasan kukanki na shagwa6a, nasan kukan ki na rigima, sannan nasan na takaici da kuma na zallar baqin ciki. Wannan kukan naki na tsantsan baqin ciki ne, hade da takaici. Don Allah ki fadamin menene silar wannan kukan naki?" Ta sunkuyar da kai. Yace, karki manta kin dauki alqawari a asibiti cewa, zaki riqeni tamkar dan uwanki. To, in baki fadamin damuwarki ba, wa zaki fada mawa? Kuma nima ynxun dole ne in inada wata damuwa kece zaki fara sani, kafin kowa tunda kece muke daki daya. Ki kalli cikar Gidanmu, amma babu wanda zan iya kaima kukana cikinsu. Daga yaya Amina, sai Mahmud, sune abokan shawarata. Fadamin abin da yasa ki kuka.
1⃣6⃣Tace (cikin shessheka) Na tuna yadda mahaifana suka watsar dani. Dubi inda na dawo. Ni ko cikin novels din da nake karantawa na turanci, labarai irin na turawa masu yin wata irin rayuwa da tasha bambam ta tamu, amma ban ta6a cin karo da labarin masu hali irin na iyaye na ba. Ismail yace, khadija inkin duba tsaf, zakiga cewa, kema fa baki kyauta musu ba. Yadda na samu labarin gatan da mahaifinki yayi miki, bai dace ki watsa musu qasa a ido ba. Amma shikenan duk abinda zai faru ya riga da ya faru. Bari in miki wani alqawari, na sani cewa arziki na Allah ne, amma inya bani, zan miki duk abinda kkso. In ya kai arzikina kamar na mahaifinki, zanyi miki fiye da abinda mahaifinki yayi miki. Inason ki rubuta wannan ki ajiye ko don sheda. Amma ynxun inason ki daina kukan nan, ki kuma yi haquri da yadda kk sameni. Ta runtse idanunta. Ina matuqar da na sanin dawowa ta hutu daga Dubai, na rantse da na san cewa duk wadannan abubuwa zasu faru dani, da na zauna can nayi hutuna. Daddy ya matsamin wai in dawo, ya kuma sake matsamin inje katsina. Ashe yamin hakane sbd ya daina sona.
Ismail ya sake yin qasa da murya, "ki daina fadin haka khadija. Ki sani bawa baya iya gujema qaddararsa. Sannan bana zaton akwai iyayen da zasu daina son dansu. Kuma na tabbata inda iyayenki suke, ynxun suna tare da takaicin rabuwa dake. Hankalinsu yana kanki. Tace a'a ban yarda da batunka ba. Hankalinsu yana kaina ne zasu watsar dani bayan sun samu labarin halin da nake ciki? A dan qaramin tunani na kome nayi musu bai dace su banzatar dani ba acikin halin ciwo. Shiyasa nima nakeso ka nesantani dasu kamar yadda kayi min alqawari. Ta soma wani irin kuka mai shiga rai. Baisan lokacin da ya rungume taba ajikinsa. Kiyi shiru. Zanyi miki duk yadda kk so khadija. Saidai ina sake neman hadin kanki. Yadda kk sameni talaka, ki qara haquri. Kinji khadija? Kimin alqawarin zama na har abada. Ko na tafi makaranta ki zauna da yaya kinji. Haka dai Ismail yayi ta lallashin Mimi da kalamai. Kasancewarsa mai hikimar magana, har tayi shiru, ta kuma amince, tare da alqawarin ko baya nan kar ya damu babu inda zataje.
[17/09 1:18 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa

1⃣7⃣Ismail ne ya girka musu abinci, taliya ce yayi dafa duka, ya zabga kifi. Kuma Mimi taci sosai. Matsalarsa ban daki, amma tunda ga 'FO' din daya siyo mata, sai yace, tayi amfani dashi, zai dinga zubarwa. Cikin kwana ukun da sukayi, Mimi har nauyin Ismail takeji, domin ko cikin dare ta farka fitsari ko ba haya zaisa ta a 'FO' in ta gama, ta wanke sai yazo ya zubar, kuma ta lura yanada matuqar tsafta sosai sbd yadda yake gyaran dakin, ya wanke komai na girki, sannan yayi musu wanki. Wanka ne dai matsalarta ynxun, don acikin kwanaki ukun nan batayi wanka ba, sannan yana sata su danyi tattaki a cikin layin ya sagale ta a kafadarsa don tadan taka qafarsa. Sai dai damuwarta yana matsa mata sai ta saka hijabi, ita kuma bata saba da yawo dashi ba. Da ma shi ya sai mata sbd sallah. Yakan lallasheta da cewa, kinga duk kayanki matsattsu ne, khadija ki saka, in mun dawo daki, sai ki cire. A ranar ne Ismail ya daga katifa yayi share-share, har ya ciro ma Mimi Jakarta. Daya gama share-sharensa, sai ya taimakawa Mimi, ta koma kan katifar dama cikin zaure ya zaunar da ita. Sannan ya dauko Jakarta ya ajiye a gabanta. Har ta dauki littafin daya bata na tarihin Annabi Muhammad (SAW) ta bude tana cewa, ina page na ashirin da uku. Sai yace ga jakarki. Tace jefa ta can kan akwatunan can. "yace da kudinki a ciki fa." Ta dago ta dubeshi, sannan ta kalli jakar, "kudi?" yace duba mana. Ta ajiye littafin, sannan ta dauki jakar, ta zazzago kudin. Cikin mamaki ta kalleshi, "dama ba dasu ka biyamin kudin asibiti ba? Yace a'a. Tayi shiru tana kallonsa, ta sake cewa kodai bakasan dasu bane? Yace na gansu. Sai taga ya qara qima a idonta. Sai tace, nagode sosai, amma ka amshi wannan kudin kayi duk abinda kkso dasu, na baka. Yace, kudin da yawa khadija, ki riqe abinki. Tace babu abinda zanyi dasu. Amfanin dana debo kudin don inyi dasu basu min ba. Komai ya zama tarihi. In ma bakada buqatarsu, to zaka iya ba wasu masu buqata. Kuka ya kufce mata. Ismail yace, shikenan kiyi shiru, na amsa kuma nagode. Ya tattara kudin guri daya, yana tunanin me zaiyi dasu? Cikin baqar leda ya zuba su. A zuciyarsa yana Jindadi, domin ko babu komai, zai samu tarin buqatun dake gabansa.
1⃣8⃣Waje ya fita ya kira Mahmud cikin waya ya sanar dashi komai, Mahmud yace, Ismail ka gode ma Allah. Duk lokacin da wata matsala ta taso maka, sai kuma Allah ya kawo maka mafita. Kaga kana cikin matsalar abinda zaka bar musu in zamu tafi da wanda kai kanka zaka riqe don amfaninka, sai kuma ga wadannan kudin. Ismail yace, Allah shine abin godiya. Ni kaina nayi tunanin sassauci ne Allah ya turomin. Kuma fa kasan harda darajar aure ko? Inji Ismail. Mahmud yace, tabbas! Kasan aure daraja gareshi. Albarkacinsa sai kaga budi ko ta ina. Shiyasa ko yaushe nake baka haquri, ina tausarka a kanta. Kuma duk runtsi kar kace, zaka saketa. Ismail yace, insha Allahu zan kula. Amma fa karka manta ba sona takeyi ba, kuma nima harga Allah banajin sonta a zuciyata, tausayinta kurum nakeyi. Mahmud yace, "Allah yayi mana za6i mafi alkhairi. Ismail yace, Ameen. Sannan sukayi sallama. Ummin yaya Amina ce tazo ta kawoma Mimi faten wake hade da kifi. Sai Ismail yace, ummi zauna da aunty khadija inje gurin mamanki in dawo. Tace, to kawu. Amma ka fada mata inanan. Yace zan fada mata. Ya kalli Mimi, sai na dawo. Kai kurum ta daga masa.
Sun tattauna da yaya Amina, inda sukayi shawarar a gyara ma Mimi dakin kakarsu saddam. Babansu saddam da ma ya Amince ta dawo nan. Yace, ai Ismail dansu ne tunda ance babbar ya uwa. Yaya Amina tace, ka ba Salisu aikin,, qanin babansu saddam. An kira Salisu yaga dakin, kuma Ismail ya fada masa yanason asa masa tayals a qasa, sannan a saka silin na zamani na roba, kuma a yi masu fenti duka Gidan, ya canke kudin da Salisu ya fada ya bashi harda na aiki. Sannan ban dakinsu yasa shima a duba, aka duba, yace abin tsugunno na zamani asa tayals a qasa ayi fenti asa wuta. Dama tsakar gidansu mulmule yake da siminti. Sannan ya ware wasu kudi ya ba baban su saddam yace, su siyo kayan abinci sbd halin yau da gobe. Bayan fitarsa itama yaya Amina ya bata 'yan wasu kudin ahannunta, sbd yasan Mimi ba zata amshi kudi daga wannan kudinba. Yace ta riqe do zuwa asibiti ko wata buqatar. Bayan ya koma ya tarar Mimi tana varci, ummi kuma tana zaune a tsakiyar dakin tana wasa. Yace, a'a varci tayi antin taki? Ummi tace, eh tana cikin karanta littafi, sai naga tayi varci. Ya kalli littafin, sai yaga littafin tarihin nan ne daya bata. Ya dauka ya duba yayi mata alama a inda ta tsaya ta hanyar ldan linke gefen littafin sannan ya ajiye. Ya kalli Ummi, to tashi kije gida ko mamana. Tace, to kawu, sai Anjima. Ta tashi ta fita.
[17/09 1:18 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa

1⃣9⃣Daga tsaye yake yana kallon Mimi. Duk runtsi saidai yace, bayason Mimi, amma ba dai yace, ba tada kyau ba, don ma fatarta ta rage haske sakamakon canjin rayuwar data samu. Ga ta da gashi, abinda yake matuqar so ga mace. Ya koma gefen teburin daya dora littafin akai ya zauna yana kallon Mimi sosai. Yaga abubuwa da yawa a tare da ita wadanda suke sawa mace ta amsa sunanta mace. Harma ya jishi cikin wani irin yanayi daya tilasta masa lumshe ido. Muryar Mimi yake tunowa irinta matan da suka amsa sunansu na mata. Domin duk macen data amsa sunanta mace, bata yin magana da qarfi. Mimi ko masifa takeyi ba zakaji muryarta a sama ba. Hakanan in tana waya, qarya ne don kana kusa da ita kaji me take fadi, in dai ba ka saurara sosai ba. Haka zalika in tana magana da kai tamkar bata so. Wadannan dabi'un da kuma shagwa6arta tana matuqar burge Ismail, kuma yana sonta ga matar da zai aura. Qarar wayarsa ya dawo dashi tunaninsa. Ya daga, Mahmud ne yace, ka fito ina waje. Ismail yace, ganinan.
Yayi masa bayanin Yadda sukayi da yaya Amina. Mahmud yace, yayi hakan. Ismail ya ciro dubu biyar yaba Mahmud yace, kaima kadan qara. Mahmud yace, babu matsala ka barsu don Allah. Ismail yace, a'a ka amsa kudinfa sunada dan yawa, dukda ban qirga ba. Ni tunani ma in na cire abinda zanyi amfani dasu, sauran sai in buda account in zuba, ko don buqatar su khadija. Mahmud yace, wannan ma tunani ne mai kyau. Sun jima suna tattaunawa sannan sukayi sallama. Daren ranar, gurin misalin sha daya Mimi ta farka daga varci, sakamakon hasken wutar lantarki da aka kawo, dana rashin wankanta na kusan kwana hudu, ya sata sai juyi takeyi. Ta tashi zaune tana kallon Ismail, wanda babu riga, ta lura sam shi ba mutum bane Maison varci da tufafi. Amma yanason rufa sosai. Ynxun haka rabin jikinsa, ko ince daga qafa zuwa qirjinsa a rufe yake. Sannan fuskarsa tamkar yana murmushi. Ta dauke idanunta tare da lumshe su. Sannan ta sauke ajiyar zuciya. Wannan duk don idanunta sun kalli sumar dake kwance a tsakiyar qirjinsa ne. Hasken wuta ne yasa shi bude ido, yayi miqa tare da salati, yace NEPA sun kawo wuta kenan. Yana tashi zaune yaga Mimi a zaune. "kema hasken wutar ne ya farkar dake? Na manta ban kashe ba. 2⃣0⃣Ta 6ata fuska, cikin shagwa6a tace, jikina yana yimin qaiqayi. Yace khadija kinqi yin wanka dole kiji haka a jikinki. Tace yaya zanyi ynxun to? Yace, bari in kaiki ciki, ki daure kiyi mana. Tace amma zaka tsareni a waje? Yace eh. Riga ya saka, sannan ya nufi cikin Gidan. Saida ya wanke bayin, sannan ya kai mata ruwan wankan. Yace, babu dai na zafi, kuma kinga har ynxu da dan sauran sanyi. Tace, zanyi hakanan. Kujera yasa mata ta zauna sannan ya fita. Data gama saida tasa kayanta data dauko na varci masu dan kauri sannan tace, na gama. Yazo ya kamota suna tafe a hankali. Sunzo daidai qofar dakin fatu, sai ta turo qofa ta fito. Ta kallesu, "ikon Allah, don jaraba ba'a bari a warke ba? Su dai basu tanka ta ba. Sai da Mimi ta zauna akan katifa sannan tace, wai me matarnan take nufi da abinda ta fada? Ismail dukda ya fuskanci inda fatu ta dosa, sai yace, nima ban gane nufinta ba. Daya koma kwaso kayan wankanma, saida tace, ya dai kamata a bari a warke. Ismail yace, ai da ciwon ma ba haramun bane. Tace, eh lallai ka riqa. Shidai ya fice a zuciyarsa yana cewa, sa ido sana'ar banza!
Cikin kwanaki uku zuwa hudu an kammala gyara tsaf. Lallai komai yanason gyara, inji abban su saddam, lokacin daya gama kallon Gidan. Sannan ya juya ya kalli Ismail, qanina muna godia fa. Ismail yace, Ameen. Ismail shida Mahmud sukaje kasuwa, inda suka siyowa Mimi Gado waya goma na kwanciyar mutum daya, saitinsa harda sif. Sai fanka, dan TV dinta madaidaici. Mahmud yace, ga wata shawara, me zai hana kudin da kace kaba yaya Amina, ka amshe su ka cika ka sai musu firji ko dan qarami ne. Kaga ko da ruwan sanyi suke saidawa zasu samu dan na rufin asiri. Ismail yace, haka ne, amma bari mubar musu wancan kudin tunda ga wasu nan, sai mu sai musu dashi. Dogon fridge suka siya, sannan suka nemi shatar a kori-kura suka loda kayan, suka nufi Gidan yaya Amina. Maqota sai leqe sukeyi. Wasu suce 'yan haya suka sa a gida, wasu kuma suce kodai aure abbansu saddam ya sake yi. Suka shiga da kaya suka shirya komai tsaf, firjin kuma suka sashi a dakin yaya Amina. Su Ummi kam murna babu dama. Tana fita wata maqociyarsu, Bakaraba tana ta leqe, dama tanason taga giccin wani dan gidan ta kirashi. Tana hango Ummi, ta kwada mata kira. Ummi tazo, tace kunyi baqi ne a gdn naku, ko ko abbanku ne yayi aure? Ummi tace a'a kawunmu ne zai tafi madina, shine matarsa ta dawo Gidanmu. Tace ohoo, wadda ke asibiti? Ummi tace eh.
[17/09 1:18 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa

2⃣1⃣Daga nan fa duk wanda yazo jin meya faru, sai tace, qanin mamansu Ummi ne zaije karatu, ya dawo da matarsa Gida. Dama ita balaraba gun nan duniya ce. Ga duk maison jin wani tsegumi a Unguwar, gurinta yake zuwa don ta shahara. Tunda taga anayin fenti a gidan take shige da fice don jin dalili. Bata samu cikakken bayani ba, sai a bakin Ummi. Saida komai yayi tsaf, sannan suka tafi. Bayan sunyi sallama da Mahmud ya shiga gida, ya zauna. "khadija na barki ke daya ko? Don Allah kiyi haquri. Ta dube shi, sannan ta kwantar da kanta gefe, babu komai, karka damu dani na saba da zama ni kadai. Yace, an gama gyaran dakin naki, na gidan su yaya Amina, yaushe zaki koma? Cikin sauri ta tashi, "ynxun zan koma. Yayi murmushi, meyasa kk gaggawar rabuwa dani? Kin gaji da zama dani ko, bana kula dake yadda ya kamata. Cikin sauri tace, a'a Nayi kewar yaya Amina ne, kuma nan din ina takura maka sosai. Qasa fa kk kwana, amma kana kula dani sosai. Yace nikam inata kewar rabuwa dake, tsawon lokaci muna kwana daki daya, zamu rabu. Ta sunkuyar da kai, "ba zaka rinqa zuwa Gidan ba? Yace, zan dinga zuwa kullum kafin in tafi. Ya kamata in sai miki waya ko? Sai mu dinga gaisawa ko? Tace, ka barni kawai tunda banida wanda zan kira. Yace, ba gani ba? Tace, a'a ka saimin novels na dan dinga karatu. Yace, wadanne iri? Tace, na turanci. Yace zan hada miki dana addini, tarihin Annabawa, da kuma wadanda zasu koyar dake, kisan yadda zaki ibadarki. Suma akwai masu fassarar turanci, akwai na hausa. Tace, to ka saimin. Yace kuma sai gobe zako koma gidan yaya din, sbd yau da dare nida Mahmud mu kwashe kayankin nin, ya nuna akwatunanta da yatsansa. Tace, "to Allah ya kaimu.
Ya shiga cikin Gida ya sanar dasu inna cewa, matarsa zata koma gidansu yaya Amina, sbd zasu tafi makaranta. Tace, "sbd nan din ba za'a kula da ita ba? Yayi murmushi, don dama ya zaci zata fadi haka. Yace a'a saboda bata gama samun sauqi ba. Tace, Allah ya taimaka. Yace, Ameen. Haka kuma da dare ya samu 'yan uwansa mazan ya fada masu. Suma sai suka ce, hakan yanada kyau. A daren suka kwashe kayansa da Mahmud tsaf. Sannan washe gari ya kama ta Suka shiga cikin gidan tayi musu sallama, dukda dai ba kulata suke ba, sai wanda yayi biyya yake leqawa dakin yayi musu sannu. Tayi mamakin ganin dakin haka don gsky bata zaci dakin yayi kyau haka ba. Ta kalli Ismail, nagode da kulawa. Sannan tace ma yaya Amina taba ta Ummi su dinga kwana. Yaya tace gatanan.
[17/09 1:18 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa

2⃣2⃣Shi kuwa Ismail daya koma ya kwanta a dakinsa kan katifarsa, sai yakejin dakin yayi masa girma. Zuciyarsa ta cika da kewar Mimi. Itama a nata 6angaren haka ce ta kasance, juyi kurum takeyi tana kallon Ummi wadda keta sheqa varci. Gizo Ismail yakeyi mata, sai taga kamar gashi yana sallah. Koda ta tabbata ba wai tanason Ismail bane, amma yana da dabi'un da take matuqar so, suke kuma burge ta. Yanada tausayi, ga gsky da Amana. Shine mutum na farko wanda ya kasance mai addini kuma yake birgeta. A da in taga ustaz kamarsa, sai ta dinga yi musu kallon 'yan kauye wadanda basu waye ba. Haka kuma yana burgeta Kasancewarsa tsayayyen namiji, wanda baya daukar raini, gwarzo mai tsayawa da safafunsa. Don

1 Comments On CANJIN RAYUWA
avatar
mariya-6-8

9 months ago

Reply

In HAUSA language

Please Login or Register in order to submit comment