Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tana zaune tana jiranta. Momy kinji
abinda na sameshi yanayi? “me? ” inji momy. Na’ima
ta fada jikinta, tana kuka, na sameshi yana waya. Don
nayi masa magana, kai tsaye yace min waishi yana
neman mata. Kuma wai yana shan giya da wiwi.
Momy nafisa ta zaro idanu, cikin faduwar gaba tace,

da gske? Kai inajin wasa yakeyi, zalayarki kawai yake.
Kin ta6a ganin mai aikata irin wadannan qazaman
laifukan sannan ya fada ma matarsa kai tsaye? Dole
zaiji shakka. Ki barshi bari yazo.
Na’ima tace, ai yace, ba zaizo ba, shi yana aiki. Momy
ta yi shiru tana ta kallon Na’ima cikin matuqar
mamaki, sannan ta miqe. Muje gurin nasa, mara
mutunci kawai. Na’ima ta kalleta. Da kin barshi kawai
momy, tace muje kawai, bazan dauki raini ba, gara
in taka masa birki.
Ta tasa Na’ima suka nufi saman. Yana latse latsensa a
computer, yaji shugowarsu, amma sai ya dauke kai,
yayi kamar baiji shugowarsu ba. Saida momy tace,
bakaji Sallamar mu bane? Sannan ya waiwayo,
fuskarsa babu annuri, yace, naji. Ina jinku, aiki
nikeyi, ina kwana? Duk da baice su zauna ba saida
momy Nafisa ta zauna, sannan tace “lfy” shine wato
Abbas nace kazo, amma kacemin kana aiki ko? Ya
nuna computer da hannuwansa guda biyu, ba gashi
ba kina gani? Ya juya yaci gaba da aikinsa. Tace, to
zaka iya bani ‘yan mintuna muyi magana? Ya hada
tafukan hannuwansa wuri daya ya murza tamkar
mai jin sanyi, sannan yace, kamar minti nawa? Ta
zaro ido cikin mamaki. Abbas ni kk tambaya? Ashe
baka da mutunci har haka? Da sauri ya juyar da
kansa gefe yana kuma dannar zuciyarsa, don kar ya
nuna mata ainihin kalarsa. Taci gaba da cewa, to
zuwa nayi inji laifin da Na’ima tayi maka da har zaka
soma wulaqanta ta daga kawo ta.
Har na qaryata ta, sai kuma gashi nima ka gwadamin.
Ya kalli Na’ima, me nayi miki harda zaki kai qara ta?
Tace, ko Yanxun dana shigo ba na sameka kanayin
magana da wata bane? Ya daga murya cikin zafin rai
yace, me ya dameki don kin sameni ina waya da
wata? Meye naki a ciki? Ya kalli momi, tunda taxo
gidannan ban ta6a shiga harkarta ba sbd banason
matsala. Tayi harkarta inyi tawa.
Momy tace wannan kuwa ba zai yiwu ba kana
mijinta. Sannan kace, kowa yayi harkarsa? Ko kuwa
dama baka amince da auren bane? Ya miqe tsaye
yana kallon momy tare da cewa, “au dama baku sani
ba? Ya girgiza kai, ni gsky mimi na gani nace inaso.
Momy tayi shiru tana kallon sa, gabanta ke faduwa,
damuwa ta bayyana qarara akan fuskar ta. Ta sauke
ajiyar zuciya, ta rasa me zata ce, sai ta kalleshi tare
da aje fushinta, to ynxun me kace? ko ince me kk
nufi? Ya kalleta, ban gane ba.
Momy tace, matsayinta. Yayi murmushi, sannan ya
koma ya zauna kan kujerar computer tare da yin
juyi. Ban sani ba gsky. Momy ta miqe tsaye ta sake
daga murya, to me ya hana ka cewa iyayenku baka
sonta tun kafin a daura auren? Yace, momy karki kiji

haushi na. Ko na fada musu ba zasu fahimceni ba a
wannan lokacin tunda suna da burin kansu. Ya nuna
Na’ima, ke kuma ki bani lokaci, in burikan iyayen mu
sun cika, sai in sauwaqa miki. Da sauri momy ta
katse shi da cewa, ha Abbas, ai ko mutuwa tana
kunyar idon mahaifi, inji masu magana.
A gabana kk fadin bakason ‘yata? Yayi guntun
murmushi, momy kenan. Don dai ni ba danki bane,
saiki takura min? Ya kamata kusan cewa, shi so ba’a
masa dole. Ni mimi na gani nace inaso. A tsari na
farar mace nake so. Kinsan kowa da ra’ayinsa. Qila
da fara ce da nayi manage. Momy ta miqe, shikenan
na fahimce ka. Yace, Yauwa nagode da kk fahimceni,
kuma naji dadin haka, don ni mutum ne mara son
takura. Ta kalli Na’ima, tashi muje.
Na’ima wadda ke ta faman kukan takaici, ta miqe
tana cewa, nidai kawai momy ki tafi dani, bazan iya
zama ba. Yace, kin kawo shawara, ku tafi tare kawai
momy, ta dube shi a qufule.
Babu inda zanje da ita, zan kuma sanar da
mahaifiyar ka, daka-duka auren yau kwana biyu,
sannan ace tana gida? Yace, umm, yadda kuka za6a
haka zakuyi. Amma in da zakiji shawara ta, da sai
ince kar ki kai qara ta gurin momy na, sbd itama
irinki ce, tafi son ‘ya’yanta akan na kowa. Ni dai kunji
ra’ayina. Sannan don Allah a daina takura min, a
kuma guji shiga harkata. Basu sake cewa komai ba
suka fice. Shi kuma yaci gaba da aikinsa. Dakin
Na’ima suka koma sukayi jugum-jugum. Na’ima tana
ta faman kuka. Mommy ta kalleta cikin damuwa,
sannan tace, share Hawayenki. Badai farar mace
yakeso ba?
Na’ima tabi ta da kallo. zamu duba mayukan cikin
akwatinki, in babu wanda zaisa kiyi fari, saimu shiga
kanti. Kafin da wata guda, sai kin koma tamkar
baturiya. Daga nan sai ki dinga yin duk wani abu da
zaki ja ra’ayinsa. Na’ima ta dan ta6e baki tallafe kanta
sbd tsabar ciwon da yake yi, tace, hmm mu gwada
mu gani, haka suka sauke kafatanin kayan shafan
dake cikin lefen, amma basu fahimci komai ba,
ma’ana basu gane ko mayukan zasu iya yi mata
bilicin din ba.
Momy ta dafa Na’ima, cikin sigar lallashi, karki damu
Na’ima, zan nemi Shawarar Aminiyata hajiya nana,
domin na ta6a jin suna zancen qwayoyin da suke
saka fari. Na’ima tace, to kafin ta wuce saida ta
tabbatar hankalin ‘yar tata ya kwanta, ta nuna mata
cewa ta zauna tayi haquri, ta zauna kada ta sake
maganar tafiya. Ta kwantar da hankalinta, wata rana
sai abin da tace masa zaiyi.
Momy dai ta tafi cikin takaici, ta bar Na’ima cikin
damuwa. Ta jima sannan ta tashi ta shiga cikin kicin

dinsu masu aikinta ssuna ciki. Dattijuwar tana zaune
tana firar dankali. Yarinyar kuwa tana wanke-wanke.
Daqyar ta amsa gaisuwar da suke mata, wai ita dole
ga matar gida, ta kalli tsohuwar, me za’ayi da wannan
dankalin? ‘Yalla6ai ne yace ayi masa cips da shayi.
Na’ima tayi sororo, cikin muzanta, domin itace ya
dace tayi masa, ko kuma tazo tasa ayi masa, amma
sai ta wayance da cewa, dama har ynxun baku kai
masa ba? Dattijuwar tace, hajiya zuwansa kenan
yazo yai magana. Na’ima tace, ni bance sai kinyi min
lissafi ba. Inason ki gasa min bread da kifi, Na’ima
kenan. Wannan kuma ai cimar mimi ce. Yinin ranar,
Na’ima ta kasa sukuni.
Domin ita gsky tana matuqar son Abbas. Tana jin
lokacin da zai fita wuraren daya saura na rana, ta fita
taje gurin window tana leqensa har ya dau motarsa
ya fice. Qarfe goma da mintuna na dare, taji
tsayuwar motarsa. Cikin sauri ta fito falonta wanda
tasan nan ce kadai hanyar binsa don hawa samansa.
Ta dau gayu cikin riga da wando matsattsu, kanta
babu dan kwali, tayi wankan turaruka har maqaqi
suke mata a wuya.
Sai dai kash! Tayi dana sanin fitowa daga dakinta,
don burge angonta, domin kuwa da wata budurwa
ya shigo, bayan ya buga alarm ta bude, sororo tayi
cikin tsananin kishi, ba tada wata power da zata iya
ce musu wani abu. Kuka ta saka sannan ta juya ta
nufi dakinta. Abbas ya kalli Jenifer, kin gani ko? Har
ynxun babu kamarki, tayi murmushi suka nufi
samansa bayan ta saqalo hannuwanta a qugunsa.
Tana fadin, na yarda honey.
Cikin matsanancin kuka, Na’ima ta kira layin momy,
wadda shugowarsu kenan daga asibiti, ita da daddy.
Jikinsa da dan sauqi, shine ya matsawa likitan ya
sallamesu, don ya tsani zaman asibitin. Momy Nafisa
bata son daddy yaji wannan matsalar, don haka taqi
dagawa, saida ta shiga dakinta. Tana dagawa ta fara
da cewa, meyasa bakida haquri ne? Na’ima ba nace
zanyi shawara bane? Zan kiraki da kaina. Tsaya kiji
momy, da karuwa fa ya shigomin gida. Karuwa??
Momy ta tambayi Na’ima. Ta rantse, sannan ta ci
gaba da cewa, ni bansan yaya zanyi ba ynxun, Momy
tace, ki barshi zuwa gobe zanje gurin uwarsa. Na’ima
ta shiga daki, ta zauna bakin gado cike da nadamar
auren Abbas.
Kuka take sosai, amma babu mai lallashi. Qarfe shida
na yamma, innar su Zainabu ta shigo tare da
Aminiyata, inna yalwa, suka sake dawowa gidan
Zainabu, ta danji dama, tana zaune kofar dakinta. Jin
muryar innar tata yasa gabanta faduwa. Rai a dagule
ta kallesu, sannan ta shiga dakin, suka bi ta ciki,
Aminiyar inna ta kalli Zainabu, meye kika dagule rai?

Zainabu ta sunkuyar da kai. Ni wallahi da baku dawo
ba, za’a ce iyaye na suna ta sintiri. Da ma aikowa
kawai kuka yi.
Ni bana son abin gorin nan gidan. Inna tace a daura
miki goruba, mu dai in burinmu ya cika ina ruwan
mu dasu? Inna yalwa tace, anqi a turo wani din,
basha zakiyi ba. Ta daga hijabinta, ta ciro wata gora
mai dauke da maganin da suka hado. Tace, zauna
kisha shi maza-maza. Zainabu ta soma kuka tana
shan maganin. Tasha kusan rabi suka ce, ki ajiye
Anjima sai ki shaki shanye sauran. Karki sake baki
shashi ba. Tun fitarmu daga gidannan, muna can
muna qoqarin hadoshi. Don haka ki maida hankali ki
shanye.
Alhaji lawal ya dawo gurin su Maman bushira yanata
zage-zage, wai shi za’a kawo wa raini da rashin
mutunci? To, shifa ba zai bada jininsa ba bare kuma
kudinsa. Duka-Duka yaushe ne akayi auren ma? Ko
wata daya ba’a yi ba za’a ce har tanada wani ciki?
Uwar gidan tace, haba Alhaji yaya kake irin wannan
maganar? Sbd Allah, dubi yadda mutane suke
kallonka. In jiya kuka yi aure, ai ba abin Mamaki
bane ku wayi gari da ciki. Kai dai kayi fatan samun
sauqinta, ka kuma bada duk abinda ake nema. Ya
kalleta a fusace, sisi na bazai ciwon kai ba. Zanje in
fadawa uwarta, wadda ta kawo mata maganin zubar
da ciki. Sai su zo suyi jinyar ta, da kuma kudin sun,
tace haba Alhaji don Allah ka duba wannan
al’amarin. Cikin tsawa yace, in zakije gida, kizo muje!
In ba zakije ba, in tafi.
Tace, abarta da wa? Tsaki yaja, sannan ya wuce
abinsa. Nurse tazo ta kira maman bushira zuwa
dakin da aka ajiye Zainabu. Sannan taba ta wata
takarda, ta nuna mata wata qofa, ki shiga zakiga
wasu nurses, anan ne zaku biya kudin gadon, sannan
zasu rubuta muku takardar shaidar biya. Likita zai
shigo ya rubuta magungunan daya kamata tasha.
Maman bushira dai, to, kurum tace, tana tsaye da
takarda bayan tafiyar nurse. Gashi ba tada ko sisi
tunda fitar bana shiri bane.
Shi kam Alhaji lawal, kamar yadda ya fada, gidan su
Zainabun kuwa ya zarce. Kafin ya kai saida ya kira
direbansa, dan korensa. Bayan ya daga, sannan yace,
iroro kana ina ne ynxun?
Yace, Alhaji naje gidan, ance kunje asibiti da amarya
ba lfy. Alhaji yace, mu hadu gidan iyayenta ynxun
nan. Ka hau aca6a. Yana isowa qofar gidan, ya hangi
iroro har ya iso, suna tsaye da dan acha6an, iroro ya
nufo Alhaji yana cewa, sannu da qarasowa Alhaji.
Alhaji yace, har ka rigani, to me kuma dan acha6a ke
jira? Iroro yace, banida ko kwabo Alhaji, daman kai
nake jira in sallameshi. Tsaki Alhaji yaja, sannan ya

ciro naira dari biyu ya miqa masa, iroro ya amsa tare
da cewa, Yauwa. Ya biya dan acha6a, sannan ya zuba
sauran aljihunsa. Ya kalli. Alhaji, “lafiya dai kazo nan?
Alhaji yace, zuwa nayi in sanar da iyayen Yarinyar
nan Zainabu suje suyi hidimarta a asibiti.
Kaji ma wai har tanada ciki, Duka-Duka yaushe akayi
bikin? Iroro yace, tafdijam! Ba don ma baka mori
kudinka ba ai da sakinta kayi kawai, ka kawo wata.
To, jinyar cikin takeyi a asibitin? Alhaji yace, sun
dirka mata maganin zubar da ciki, jini ya 6alle mata.
Ai shiyasa nace, suzo suyi jigilar, iroro yace, kayi gsky
Alhaji. Kuma zan soma duba maka madadinta tun
daga ynxun.
Alhaji yace, shiyasa nake matuqar sonka iroro. Sau
da yawa in kayi magana, kamar ka shiga raina. Da
ace ta kwana biyu, zuwan nan da nayi, yadda take
asibitin nan, da takardar ta zanba iyayen ta. Amma
su gama jinyarsu, zan dawo da ita, ba zanyi asara ba,
kuma ba zamuyi dogon Zango da ita ba, don daga
gani ita irin masu jarabar haihuwarnan ce, sai kace
6era.
Cikin fada likitan ya shigo, ya kalli Ismail, “kai kanaso
ne sai zuciyar ta ta buga tukunna? Me zaisa ku fada
mata mutuwarsa? Don Allah ku fita waje, banason
ganin kowa anan sam. Bai saurari kowa ba, bare
yasan ba laifin Ismail bane. Gaba dayansu sukayi
waje,, Ismail yana cewa, kun gani ko? Nasan dama
laifina zai gani. Cikin kuka mai tsanani, mahaifiyar
khalil take cewa, kuyi haquri, nima ban sani bane,
Mahmud yace, karki damu hajiya, babu komai,
shidai Allah ya jiqansa. Tace Ameen, bari mu tafi,
Allah ya bata lfy.
Ameen ya rabbi, ina fata ‘yan sandan sun baku
jakarsa da wayarsa ko? Sai dai ban sani ba, tunda
tare da mahaifinsa muka zo, qila sun bashi, Mahmud
yace, ‘yan sandan sunzo lokacin da mukazo. Tace
bari zanyi musu magana in munje. Mahmoud yabi
su da kallo, suka tafi cikin damuwa. Ismail kam
tamkar zuciyar sa ta buga don damuwa. Ya qosa
likitan ya fito don yasan halin da ake ciki. Ya kusan
rabin sa’a tare da taimakon nurses, sannan ya fito, ya
kalli Ismail, fuskarsa a daure, ku biyoni office. Sun
sameshi a tsaye yana duba wani file. Suna shigowa
bai zauna ba, kuma bai musu izinin su zauna ba.
Sai ma fada da ya hau yi musu, tare da cewa, kasan
meye? Kaje ka samo wacce zatayi jinyar ta, domin
kaikam baza ka iya ba. Ismail yace, doctor ba laifina
bane, nan ya sanar dashi komai, likitan yace,
shikenan, daga yau zuwa gobe bamason ganin koea
gurin ta. Ina nufin ‘yan dubiya. Likitan ya sassauta
murya, ka nutsu sosai, ka lallasheta, sbd kasan dole
ne ta zamo ta farka cikin damuwa da tashin hankali.

“Ismail yace, Insha Allah. Na gode likita. Ynxun ta
farfado ne? Mun kuma yi mata allurar varci, bamu
fito ba saida varcin ya dauke ta. Don haka saiku kula
sosai. Tashi kuje, za’a zo a dabi jinin naka ynxun.
Ismail yace, to nagode likita.
Suna fitowa suka dawo gurin su Mahmud, yace vari
ya wuce, sai zuwa anjima. Ismail yace, Allah ya
kaimu. Bayan tafiyar su, Ismail, a hankali ya tura
dakin ya shiga. Ya jima tsaye a kanta, yana kallon ta
tana varci, ya juya ya koma kan kujera, zamansa
keda wuya, sai aka turo qofar dakin. Ya dago ya kalli
mai shigowar, Namiji ne da riga fara, irin wadda
likita ke sawa, sai wasu kayan aiki dake hannunsa.
Yace. Kaine Ismail bin Abdurrahaman? Ismael yace,
Na’am, Mutumin yace, nazo ne in debi jininka. Ismail
yace, to bismillah. Bayan an dauki jininsa ne, sai wata
nurse ta kawo masa wani dan tea a kofi da wasu ‘yan
qwayoyin magani, yasha ya dan kishingida, kafin
lokacin sallah.
Bayan la’sar, sai ga babban wan su Ismail yazo,
lokacin Ismail yana dawowa daga masallaci, suka
shiga ya duba ta. Har lokacin bata farka ba, bayan
sun fito yace masa, ance zata gudu ne tayi hadari.
Ismail Yace, eh, yayan yace, in bata sonka dolene? In
ta warke ka maida musu ‘yarsu, Ismail bayason
doguwar magana, don haka yace wa, to, sai ya sake
cewa, ka fadama iyayen ta? Yace eh, da haka suka kai
qofar asibitin, inda yayan ya hau mashin, shi kuma
ya koma ciki. Duk fargaban Ismail, in ta farka baisan
dame zata tashi ba, bai san wane qalubale zai
fuskanta ba.
Kuma shi gaba daya ma zaman asibitin ya gundure
shi, sam ya qosa ya barshi. kiran hajiya sauda yake
shigowa, sai lokacin ya tuna da zancen account
number da tace ya tura mata. Suka gaisa, bayan ya
daga, tace masa. Baka turo ba, gashi har yamma tayi.
Yace, kiyi haquri hajiya, kaina ne yadau zafi. Ban tuna
ba, kuma banida account nawa na kaina, sai namu
na makaranta. Insha Allahu dana sanar da malam
Aminu zan turo. Tace, zancen dorin fa? Yace, sai
gobe. Ynxun dai jini za’a qara mata. Tace, an samu
jinin ne? Yace, eh, nawa ne za’a sa mata. Tace, Allah
ya bata lfy, sai naga number, yace, insha Allahu.
Ismael ya shanyo kwanar da zata kaishi matakalar da
zai koma dakinsu, sai kurum ya hango innarsu
Zainabu, ita da aminiyarta hannunta riqe da wata
takarda. Ya jira har saida suka iso gurinsa, sai dai da
alamu innar bata lura dashi ba. Yaji tana cewa,
wannan maganin shi kadai dubu daya da dari
bakwai, su kuma sauran kudinsu ya zama nawa?
Qawar tace dama nice ke, tunda ta samu dan qwarin
jiki daukarta zanyi mu gudu, mu bar asibitin. Baiji

mai innar tace ba, sbd lokacin sun dan gota shi, ya
hau sama yana tunanin, to wa suka kawo asibiti? Sai
dai babu mai bashi amsa.
Ya samu har an sawa mimi jinin, har lokacin tana
varci. Likitan ya tambayeshi inda yaje? Yace ya raka
wansa ne. Ya tambayi likitan ko babu matsala a irin
wannan varcin da takeyi? Likitan yace, babu komai
karka damu. Fitar likitan da nurse dinnesai ya kira
malam Aminu suka gaisa. Malam ya tambayi mai
jikin, Ismail yace, da sauqi, sannan yace, dama
mahaifiyar tace take son in tura mata account
number na, nace mata banida shi, amma zan turo
mata na makaranta. Shine nake neman izini. Malam
Aminu yace, babu komai, ko baka fadamin ba zaka
iya amfani dashi. Ismael yace, nagode malam, Allah
ya saka da alkhairi. Malam yace, haba babu komai,
Allah dai ya bata lfy. Ismail yace, Ameen. Suka yi
sallama.
A take ba tare da 6ata lokaci ba, Ismail ya turawa
hajiya Account number din, bada jimawa ba ta
kirashi tace masa zaiga saqo zuwa gobe. Yayi mata
godia, sannan sukayi sallama. Lokacin da zai tafi
sallar magriba, yanason sai yayi isha’i zai dawo don
haka yaje ya fadama nurses din da suke kula da
dakin na musamman dake sama cewa, zaije sallah
koda za tayi motsi tunda suna daf da dakin ne sukace
to, amma yayi sauri don sun kusa tashi, masu
shifting din dare suke jira. Bayan an idar da sallar
isha’i sai yadan kishingida, dan varci yana da fizgarshi
don akwai bashin varcin akansa na tsawon lokaci.
Tun ranar da ya rasa Zainabu baya varcin kirki, har
zuwa shigowar wannan matsalar.
Can sai yaji vibration din wayarsa don ya sa ta a
silent, lokacin da ya shigo masallaci. Ya duba yaga
ashe Mahmud ne. Don haka, sai ya tashi ya fita daga
masallacin, sannan ya daga wayar. Mahmud yace,
nazo baka nan, ina kaje? Gashi ma ta farka. Cikin
sauri Ismail yace, ta farka? Cikin wane hali take?
Mahmud yace, kana inane kai? Ismail yace, ganinan
zuwa, sallah naje. Ya kai qarshen maganar tare da
kashe wayar, take yaji varcin ya sakeshi. Cikin
hanzari ya nufi saman. A bakin qofa ya samu
Mahmud, ya miqa masa hannu sukayi musabaha. A
maimakon gaisuwa, sai Ismail yace, ta farka fa
kacemin Mahmud?
Mahmud yace, eh ta farka sadda nazo. Ban ganka ba,
sai na tambayi nurse tace, kaje sallah. Shine na tsaya
jikin window. Can na leqa sai naga alamun tana
motsi, shine na kira nurse din. Da sauri Ismail ya
bude dakin ya shiga. Nurse daya ce a kanta tana
lallashinta. A tsakiyar dakin Ismail ya tsaya yana
tunanin ta inda zai fara lallashinta. Yana jinsu da

nurse din tana ce mata ya isa mana, ki daina wannan
kukan haka. Nurse dince ta waiwayo ta dubeshi.
Yauwa kazo ka lallasheta. Yace, ko zaki kiramin likita?
Tace, ya tafi, kuma mai shifting din dare baizo ba.
Ya isa bakin gadon ya daura hannunsa saman
goshinta, sannan ya rusuna saitin kunnenta. Mimi
kiyi haquri da wannan kukan. Ba magani bane, khalil
ynxu babu abinda yake buqata agareki sai Addu’a, ki
roqa masa yafiyar Allah, yafi miki wannan kukan.
Batayi magana ba, kuma bata daina kuka ba. Haka da
Mahmud yana tayi mata sannu, sam bata san ma
yanayi ba. Duk wani lallashi da ya kamata, Ismail yayi
mata, amma sam bata ma san yana yi ba. Don haka
ya miqe daga kusa da ita, ya nufi waje ya zauna akan
benci tare da riqe kansa mai sarawa. Mahmud ya
biyo shi ya dafa shi, sannan ya zauna kusa dashi.
Ismail Yace, Mahmud yadda kasan in fasa kuka haka
nakeji. Yarinya sai kace wata jaririya, bata jin lallashi.
Nifa in ta qure ni, sai in tafi in barta. Domin yadda
bata sona, nima bafa yimin tayi ba. Gashi sai wani
uban kuka takeyi, ban san yaya zanyi mata ba.
Mahmud ya dafa shi, kar ka damu Abokina, kayi
haquri. Ka jure, ka jajirce, in ka tafi to ka barta da
wa? Kada ka manta matarka ce, wadda take a
matsayin ba tada kowa, sai kai. Kayi iyakar yinka, ka
hada da Addu’a. Zamu taya ka, wata rana sai labari,
ka jure, karka sare, Ismail ya sauke ajiyar zuciya, tare
da cewa, abin ne ya fara isata. Mahmud yadan girgiza
kafadarsa kadan, alamun lallashi, kar ka damu akwai
Allah. Ya sake sauke ajiyar zuciya. Allah ya taimake
mu. Mahmud yace, Ameen, sannan ya miqe, bari in
tafi, gidansu rabi’a zanje.
Insha Allahu gobe zamu zo da ita. Ismail ya kalle shi
da dan murmushi, kace ina gaishe ta. Sai kunzo. Ya
miqe ya taka masa zuwa gurin matattakalar benen.
Har ya juya zai tafi, Mahmud yace, Ismail kaga na
manta ko? Ismail ya waiwayo. Yaya akayi? Mahmud
yace, na zo ne in fada maka anyi admission fa. Haba?
Inji Ismail. Mahmud yace, sosai ma kuwa. Ya kamata
muje mu duba. Ismail yace, bari mu gani ko zuwa
gobe ne, in wannan rigimammiyar ta dangana, sai
yaya Amina ta zauna da ita muje, Mahmud yace,
shikenan Allah ya kaimu goben.!
Yadda mimi taga rana haka taga dare, kuka kawai
take, babu qaqqautawa har mutyarta ta dishe. Tun
Ismail yana lallashin ta, har ya gaji ya fice yayi alwala
don yin shafa’i da wutirinsa tare da da addu’o’insa
daya saba. Haka suka kwana har asuba tayi ya tafi
sallah. Gurin qarfe taran safe aka shigo aka soma yi
mata shirin yin aiki, wato dori. Goma saura aka shiga
da ita. Lokacin ne malam Aminu ya kira Ismail yana
sanar dashi cewa, yaga alert. Ya duba yaga an turo

kudi naira dubu dari(100,000). Kuma yaga sunan
saudatu bashir.
Ismail yace, eh, saqon da mahaifiyar ta ta turo din
ne. Ynxun haka ma an shiga da ita gurin dori. Zan fito
Anjima sai in amshi katin ATM din in yana gurin
Mahmud. Dama kudin hannuna sun qare kaf. Yace,
kar ka damu, ko nine sai inje in ciro maka tunda
akwai mashin a gurina. Allah dai ya bata lfy. Ameen,
inji Ismail. Sannan sukayi sallama. Ismail ya saukar
da ajiyar zuciya, har ya danji dadi sbd samun
wannan kudin, domin hannunsa babu kudi. Tagumi
yayi yana tuna irin kukan da mimi tayi ta rerawa jiya.
Ko sallolinsa yayi ne dai kawai, amma gunjin kukanta
yana daukar hankalinsa. Cikin wannan tunanin ya
hango yaya Amina. Yaji dadin zuwanta sosai, domin
zamansa shiru ya isheshi.
Ya tare ta, tare da amsar kular hannunta da kuma
ledar ruwan pure water, suka shiga cikin dakin, tace
ina mara lafiyar? Yace, an shiga da ita dakin da za’a yi
mata dori. Ya bude kular, dame kk zo? Tace, alala ce
don nasan kanaso. Yayi dan murmushi, a fili yace,
naka sai naka. Yaya Amina nagode da hidima. Tace,
haba Ismail wa gareni banda kai? Kaima kuma
bakada wadda ta fini. In ban maka ba in ma wa?
Donma Allah yasa ni ba mai hali bace. Yayi dariya,
hakane yaya. Allah ya qara mana zumunci. Tace
Ameen, yaci alalar sosai, yana ci suna hira, har take
bashi labarin cewa, su inna dasu fatu sunce sunanan
zuwa anjima.
Yace, Allah ya kawosu qila ma ke zasu samu yaya.
Sbd jiya Mahmud yace min anyi admission, zamuje
mu gani ko Allah zaisa mu samu. Don kinsan
qasarmu sai Allah. Qiri-qiri zaka ci jamb amma saika
rasa admission. Sai ace baka ci post UTME ba. Mu dai
munce zamuje mu gani. Sannan mahaifiyar mimi ta
turo kudi a account din makaranta zanje in cire.
In kuma malam ya ciro shikenan, don yace koshi sai
yaje ya ciro tunda da mashin a gunsa. Sha daya
saura aka fito da mimi daga dakin da aka yi mata
dori, tamkar wadda akayi wa operation. Nurses suka
kwantar da ita akan gadonta tare da maqale
qafafunta da gadon. Bayan sun gama kintsa ta ne
likitan shima ya shigo, tare da ainihin doctor salis,
likitan dayake kula da ita. Sunyi ma Ismael bayanin
babu matsala, insha Allahu zata samu lfy, cikin zolaya
doctor salis yace ma Ismael, “yar amanarka zata
warware. ” Ismail yace, Allah yasa. Sannan suka
rubuta magunguna suka ce ya siyo kafin ta farka.
Yace musu zata iya cin abinci? Suka ce eh, zata ci
komai in ta farka. Wannan varcin ma da takeyi anyi
mata allura ne sbd ta wahala. Sai azahar Mahmud
yazo, don haka nan yabar yaya Amina suka tafi. Sai

dai iyakacinsu banki don bazai yiwu suje zariya yau
ba, sai gobe, Daga nan yaje ya sai magungunan da
likitan ya rubuta masa wadanda bai samu acikin
asibiti ba. Sannan ya koma gida yayi wanka, ya
shanza kayansa zuwa farar jallabiya qal da hula ‘yar
fakistan. Ya fesa turaruka, sannan ya fito. Ya rufe
qofar zai fita saiga su inna zasu shigo. Ya tsaya suka
gaisa, sannan yace, daga unguwa kuke ne? Suka ce,
daga asibiti muke. Ai mun samu Amina. Yace to mun
gode, Allah ya saka. Sukace Ameen.
Fatu tace, umm. Wannan abu yaban mamaki Inna.
Me ya janyo wannan hadarin? Inna ta kalleshi, “ina
zan san abin da ya janyo. Kai sama’ila yaya abin ya
faru ne? Yace, tsautsayi ne kurum. Fatu tayi
murmushi. Zancen dake yawo a gari haka ne kenan.
Guduwa zatayi sbd bata sonshi. Ta kalleshi, kaima
kayi wauta Ismail. Dubi wannan Yarinyar, kallo daya
zaka san ta saba da hutu, amma ka cusa kanka. Da
ido kawai Ismail yake binsu. Kuma bai shirya ce
musu komai ba. Yasa kai ya fita. Tsaki Inna taja
“Mtsss” sannan tace, aishi tsiyar sa kenan. Qarya ne
kaji cikinsa.
Shidai ya sani. Inji rashida, daya matar wan nasa.
Matar musa ce kurum bata ce, komai ba don bata
cika shiga shirginsu ba. Sai da ya fita titi, sannan ya
kira Mahmud yake fada masa cewa, gashi zai koma
asibiti. Mahmud yace, to sai sun shigo Anjima shi da
rabi’a. Ya tare dan acha6a zuwa asibiti. Suna cikin
tafiya ne yana kalle-kallen sa, idanun sa suka sauka
akan wani super market. Yace ma dan acha6an don
Allah dan dakata in duba nan. Dan acha6an yace,
amma ba dadewa zakayi ba ko?
Daidai lokacin da ya tsaya, A’a insha Allahu bazan
jima ba, Ismail ya bashi amsa bayan ya sauka daga
mashin din. Ya shiga tafkeken super market din
tunaninsa kawai ya sayi abinda mimi zata iya ci

1 Comments On CANJIN RAYUWA
avatar
mariya-6-8

9 months ago

Reply

In HAUSA language

Please Login or Register in order to submit comment