Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gefen gadon. Cikin qarfin hali irin
nasa, ya kai hannu, ya dauko qaramar ciki, wadda
itace ya tanada don iyalinsa kawai, mata da yara. Ya
shiga Numbers, sannan ya danna, kai tsaye yayi qasa,
ya latsa masoyiyata sauda. Sunan da duk cikin
matansa ba wadda bata nuna kishinta tsantsa
akanshi ba. Domin su ya rubuta musu matata wance
dukkansu.
Yayi guntun murmushi sbd tuna hakan, sannan ya
latsa kira. A ringing na uku, ta daga tare da yin
sallama. Yayi shiru na kamar qiftawar ido, sannan ya
amsa. Sakamakon duk lokacin da yaji muryarta, sai
yaji wata nutsuwa ta ratsashi. Yace “sauda.” tace
Na’am Alhaji. Mun tashi lfy, ya kuma jikinka? Yace da
sauqi sauda, amma fa ciwo yananan. Koda yaushe
likita ya gwadani sai yace sugar yana qara sama.
Kila ma ciwon bana tashi bane. Ji tayi wani abu ta
tokare mata qirji, sbd fargaba. Tace Alhaji bakaje
asibiti bane? Yace na gaji da zaman asibiti. Kinsan
bayan taron nan, na kai kaina asibiti an bani gado.
Tace ynxun a gd kk a kwance? Yace eh. Likita yana
zuwa dubani. Kar kijini shiru sauda, kina raina. Da
naji ‘yar dama zanzo in wanke kaina a gurinki
Zugum tayi tunda suka gama wayar da Alhaji.
Kalmarsa ta qila ciwon ba na tashi bane ta tsaya
mata arai. Ta san cewa, mutuwa dole ce, amma gsky
batason rabuwa da Alhajin ta. Bata san yaya zatayi
ba, in har hakan ta kasance. Kurum sai taji Hawaye
na zuba daga idanun ta. Hasina ce ta katse ta da
cewa, menene hajiya? Cikin sauri ta share hawayen,

tare da cewa, babu komai hasina. Ta zauna kusa da
ita, shine kk kuka? Ba kuka nakeyi ba Hasina, tunanin
rayuwa nakeyi mai cike da canje-canje. Yau fari,
gobe tsumma. Hasina bata fahimci hausar ba, don
haka sai tace, sis mimi ce? Eh, kawai hajiya tace, don
kawai Hasina ta rabu da ita. Miqewa tayi ta nufi gefen
masu aiki, sbd aiken da zatayi ayo mata niqan dan
waken da muktar ko Abba zai tafi dashi Abuja
Anjima.
Momy nafisa kuma, lokacin da taje dakinta ta saurari
koken Na’ima sai tace, ta jira, bari ta bawa dadyn su
magani. Bayan yace, ta fita ne ta koma dakinta ta
soma kiran Na’iman. Cikin sauri Na’ima ta daga har
lokacin kuka takeyi. Na’ima wai kkce Abbas ya
mareki? Tace eh momy marina yayi akan karuwar
daya kawo suka kwana tare. Gsky momy zan dawo
gida bazan jure ma wannan cin kashin ba Allah.
Momy tace, kai wannan abu ya isheni. Aure ko sati
daya baiyi ba, amma matsalarsa tafi ta shekara daya.
Amma ba komai, ki qara haquri. Zan turo Aminiyata
anjima, zatazo da mayukan da kuma qwayar da
zakiyi amfani da ita. Munyi waya tun jiya. Ni kinga
dadynku ba zai barni in fita ba sbd baijin dadi, amma
kome kenan ki fadawa hajiya nana din kinji? Na’ima
tace to.
Suna gama wayar, ta budo grp chat dinsu na wtsapp.
Qawayen ta suna ganinta tayi musu hello, shikenan
suka shiga shewa. Ga Amarya! Ina ango? Amarci ya
6oye ki. A turo mana sababbin hotunan da aka
dauka cikin amarci. Kowa da kalar tambayar da yake
mata. Kasa cewa uffan tayi a group din sbd hawayen
da suke zubo mata. A fili tace, da ace kun halin da
nake ciki, haqiqa da baku tambayi Amarci ba. Tana
kashe data dinta ta jiyo qwanqwasa qofa.
Tayi kamar ba taji ba, sbd tana zaton ko sune da suka
fita suka dawo. Kusan minti uku ana buga qofar,
sannan ta tashi ta nufi qofar da zummar taga ko
waye. Tana budewa, sukayi ido hudu da surikarta
Hajiya Bilkisu da qawayen ta. Ta hau raba ido tana
kallon su. Sannan tace musu, “sannunku da zuwa. Ku
yi haquri. Wlh bansan ku bane. Hajiya Bilkisu ta
harareta, cikin 6acin rai tace, “au dama in kinji a ta6a
qofar bazaki bude ba, sai kin san ko wanene? Hum
kuzo mu shiga hajiya ladi.
Suka shiga Na’ima ta zauna a gabansu tana cewa,
kuyi haquri momy. Sannan ta miqe ta nufi kicin don
kawo musu abin sha. Zuciyar ta cike da nadamar
rashin bude qofar akan kari. Hajiya ladi ta kalli hajiya
Bilkisu, Yarinyar nan tanada tarbiyya kuwa? Hajiya
zuwaira tace, banga alama ba. Hajiya Bilkisu tace, ai
kuwa ba zan dauki rashin tarbiyya ba. Kusan minti
uku muna buga qofa kina ciki kina yauqi, sai kace

gidanki.
Har Na’ima ta kawo musu abin sha da cincin, su
diblan, da alkaki, irin wanda amare ke ba ma
baqinsu, amma basu daina maganar ba. Kai kurum
Na’ima ta sunkuyar, suka yi mata tatass. Har kuka
saida tayi tana bashi haquri, amma basu daina ba.
Sunyi kusan minti talatin, sannan suka ce zasu tafi.
Har gurin mota ta rakasu, sannan ta dawo cikin
damuwa da takaici mara misaltuwa. Alamu sun nuna
sam ba zata ji dadin dangin mijinnan nata ba. Tun
kafin motarsu tabar harabar gdn, hajiya ladi tace,
hajiya Bilkisu gsky bakiyi sa’ar sarakuwa ba, alamu
sun nuna zatayi rowa. Kin tuna lokacin da muka raka
hajiya mairo gdn danta mansur?
Wace irin kyauta tayi mata harda mu? Hajiya Bilkisu
tayi tsaki. Abinda ke raina kenan ladi. Mu kanmu
surukar hajiya mairo ta bamu turaruka masu tsada,
ita kuwa lesuka ta bata da atamfa. Hajiya zuwaira
tace, ko qannensa da sukaje yini, sai da ta hado su da
kayan shafa. Gsky hajiya Bilkisu ki taka birki tunda
wuri. Domin in kk bari wannan rowar da rashin son
jama’ar nata yayi nisa, to kuwa nan gaba shi kansa
dan naki, kina ji kina gani, zai tsani danginsa, ya
kuma qanqame abin hannunsa.
Ran hajiya Bilkisu ya qara sosuwa, ta ce, ina zai yiwu!
Gobe zan turo su Aisha da samira, har Azima da
jamil, in gani suma rowar zatayi musu. Hajiya ladi ta
saka dariya, kinji hajiya Bilkisu, kema tayi miki rowa
ballantana wasu yaranki? Kawai danki zaki tasa a
gaba ki nuna masa cewa, yayi mata tarbiyyar kyuta
da son jama’a tunda an kasa yi mata gidansu. Hajiya
zuwaira tace, zancen kenan. Tafdijam! Wannan shine
gaba kura baya damisa. Na’imar da bata samu
kwanciyr hankali daga Abbas ba, ta yaya zata san
yadda zatayi abida ya kamata? Muje dai zuwa.
Haka kuwa washe gari sai Na’ima ta sake jin bugun
qofa, guraren qarfe dayan rana. Bata yi qasa a gwiwa
ba, ta tashi ta nufi budewa don kar ayi irin na jiya. Su
Aisha ne da samira da kuma Azima harda auta jamil.
Cikin ‘yar fara’a mai kama da yaqe tayi musu sannu
da zuwa. Suma suka amsa cikin isa, musamman
samira da Azima. Sun zauna, ita kuma ta nufi kicin
don kawo musu abin sha da dan na ta6awa sannan
ta sanar da masu aiki cewa, ga baqi a dora musu
abinci. Taje ta kawo musu hotunan biki.
Sannan ta zauna. Jin basu gaisheta ba tace musu, ina
yininku? Suka ce lfy. Aisha tace, ina bros Abbas fa?
Na’ima tace, ya fita tun safe, don tana daki taji
fitarsa. Samira tace, sis Aisha kin manta jiya bros
daya zo yace, zai koma aiki? Aisha tace, haka ne,
Na’ima tace, eh ya koma aiki yau. Ta fadi hakane
kurum, sbd kar su fahimci irin zaman da sukeyi. Sun

wuni cur, amma bataji dadinsu ba. Komai cikin isa
da nuna mata iyakar ta sukeyi. Sannan Abbas ya
shigo kusan shida na yamma.
Tana dag cikin daki tana jiyosu yana ce musu, kunci
kunsha duk abinda kk so, ko kuma anyi muku
rowar? Samira, wadda tafi kowa rashin kunya, tace,
an ma isa? Bros muzo gidanka ayi mana rowa? Za ma
mu jira kenan. Kowa abida take so, shi tasa masu aiki
suka dafa mata. Yace, kunyi daidai. Bari inyi wanka
inzo in kaiku gida. Aisha ce ta shigo tana ce mata.
Bros fa ya dawo. Tace to, sannan ta taso daga kan
gadon, ta nufi samanshi, cikin fargaba, sbd kar
qannensa su fahimci wani abu.
Ta tura qofar falon ta bude. Na’ima ta shiga cikin
fargaba. Yana zaune kan kujera yana ciro wasu
takardu daga cikin jakarsa. Tace sannu da zuwa. Baiji
shigowar ta ba, sai magana kawai yaji. Ya dago a
fusace, “lafiya? ” A tsorace kuma cikin faduwar gaba
tace, dama Aisha ce tace min ka dawo, kuma su baqi
ne dai, kada su gane cewa akwai wata matsala
Tsakanin mu. Ya watso mata harara. Don Allah fitan
min anan! An dade ba’a gane cewa, Tsakanin mu
akwai matsala ba. Waton ma jiya da Momyn mu
suka zo shine kkyi musu wulaqanci ko?
Na’ima ta riqe kanta sbd wani sarawa da yakeyi.
Tace, ai dai na basu haquri ban zaci sune suka zo ba.
Na zaci wannan matar ce data biyo ka. Yace, in itace
sai kiqi bude qofa tunda gidan babanki ne? To bari in
sanar dake, in baki sani ba, ta fiki matsayi. Ke har iko
ta fiki a gidannan. Sbd haka kibi a sannu. Sannan duk
lokacin da ‘yan uwana suka zo wani yayi kuka dake,
na rantse miki sai na zane ki. Fita! Wawiya kawai!
Na’ima ta dubeshi rai 6ace, kai bakasan darajar dan
adam ba. Ka sake ni kawai, don ba zan iya da wannan
wulaqancin ba. Yace, fita nace kiyi. Da kuka ta fito,
sbd 6acin rai har ta manta da baqin da suke gidan.
Gadonta ta fada tana kuka. Samira, suka kalli juna da
Aisha, lokacin da ta wuce su a falo. Har suka shiga
dakin, sallar magriba tana kwance tana kuka. Aisha
ce ta tambaye ta ko lafiya? Sam Na’ima bata tanka ba
har zuwa lokacin da suka gama shirinsu suka ce,
mun wuce, Na’ima bata daina kuka ba bare ta amsa.
Sun isa gida cike da dokin labarin kaiwa mahaifiyar
su. Aisha tana jinsu tana kallon su, samira Tana sanar
da mahaifiyar su cewa, Bros Abbas yasa Na’imar
kuka. Qila ma dukanta yayi. Azima kuma tace,
sannan munyi abinda muka ga dama a gdn. Aisha
tace, ku dai bakuda hankali, ina ruwan ku da kukan
ta?shiyajiya Bilkisu tace, yayi min daidai! Ai shiyasa
jiya daya zo na fada masa abinda tayi, sbd ya kwa6a
mata. Samira tace, mu ma da zamu taho ba tace

mana komai ba. Aisha tace, ku dai kuna da matsala
wlh, ba kuga tana ta kuka bane? Tayi tsaki, ta miqe ta
nufi dakinta. Ita dai ko a cikin ranta, bata so Bros
Abbas yaci zarafin matarsa ba. Domin ta ba ta
tausayi lokacin da take ta kukan. Na’ima kuwa kiran
layin momy nafisa tayi, amma bata daga ba. Don
haka sai ta tura mata saqon waya kan cewa, ita fa ba
zata iya wannan auren ba. Domin mimi ba qaramar
sa’a tayi ba, da bata kasance matar Abbas ba. Don
Allah ki ceci rayuwa ta. Sam ynxun na haqura da son
Abbas. Saqon yaje sama da minti goma sannan kiran
momy nafisa ya shigo. Na’ima ta tashi zaune, ta
tallafe kanta mai matuqar sarawa, sannan ta daga
wayar, momy tace, Na’ima yaya ne? Na’ima ta soma
kuka. Momy tace kashh! Ke kullum Sallamar ki kenan
kuka? Sake dukanki yayi? Na’ima ta sanar da momy
zuwan mahaifiyar sa da qannensa. Momy tace,
tirqashi! Abin harda danginsa? Na’ima tace, momy
kizo ki daukeni don Allah. Momy tace gobe zamuzo
da hajiya nana. Na’ima tace, don Allah mommy
kuzo. Tace karki damu zamuzo.
Kwanan Zainabu biyu a asibiti, amma babu labarin
alhaji. Innar ta kuwa taci bashi yafi na dubu goma.
Sawunta hudu a gidan Alhajin, amma bata samunsa.
Don haka sukayi shawara da aminiyarta yalwa cewa,
in an sallami Zainabu su wuce da ita gida kai tsaye, in
yazo ya biya kudin saita koma. Baban su Zainabu
kuwa yaje ya duba ta sau daya, bai kuma komawa
ba.
Zainabu kuwa kuka takeyi akan ba zata koma ba,
domin kwanakin nan da bata gidan, duk da cewa a
asibiti take yafi mata zaman gidansa. Hankalinta bai
sake tashi ba, saida ‘yan gidan su Ismail suka zo duba
ta, taji wannan fatu din tana cewa innar su wai sunzo
duba matar Ismail ne tayi hatsari. Innar su Zainabu
tace, ai yayi aure ne? Nan su fatu da sauran matan
gidan suka soma ba innar su Zainabu labari. Ai
maigidansa ne ya bashi ‘yarsa, ita kuma bataso, ta
gudu shine tayi hatsari. Daga nan Zainabu bata iya ci
gaba da saurarensu ba, ta shiga rera kuka. Daren
ranar bata runtsa ba, kenan Ismail yananan asibitin
yana jinyar matarsa.
Ita dai zata so ta sake ganinsa a rayuwar ta ko da
daga nesa ne. Ta san lallai ta rasa Ismail tunda har
yayi aure. Ta yi ta tuno kalaman da yake fada mata
na irin tsantsar son da yake mata. Washe gari da safe
innar ta taje famfo inda zata wanko ‘yan kayan
Zainabun, ita kuma zainabu ta sauko a hankali, ta
dauki zani guda daya daga cikin zannuwanta ta yafa
ta nufi fita. Matar kusa da gadonsu tace, ina zakije
Zainabu, ko bandaki zaki shiga? Tace a’a zan dann
tattaka ne, sbd jikina duk ciwo yake sbd zaman guri

daya.
Ta fito tana tunanin ina zata nufa. Tafe take sannu sannu tana ‘yan waige-waige. Daga baya ta yanke
shawarar tambayar dakin ‘yan hadari. Dan haka sai
ta tun kari wata nurse. Tayi mata sannu, ta amsa.
Sannan tace, don Allah inane dakin ‘yan hadari?
Nurse din tace, mata ko maza? Zainabun tace “mata.”
Nurse din ta nuna mata. Zainabu ta nufi gurin a cikin
zullumi kala-kala. Shin zata gashi ko ba zata ganshi
ba? Matar tashi ta fi ta ko bata kaita ba? Ta shiga,
dogon falo ne kamar nasu, kwakkwance da marasa
lfy gado-gado. Tabi tana yi musu sannu, tare da
tambayar matar Ismail, amma har ta gama dubawa
bata ganota ba.
Ta fito ta tafi tana waigen dakin. Yinin ranar cikin
damuwa tayi shi, don ko ‘yar shinkafa da waken da
innarta kan siyo mata taci, yau kam kasa ci tayi. Da
magriba, innarta ta nufi dan lungun da sukan
shinfida tabarma suyi sallah. Ita kuma zainabu ta fito
ta sake zuwa dakinnan na ‘yan hadari. Bata shiga ta
qofa ba, window qarshe ta nufa, ta dafa windon tana
leqen mara lafiyar dake kwance a gadon. Zuciyarta
ce ke zargin cewa, lallai wadda ke kwance a Gadon
nan ita ce matar masoyinta. Bisa dalilinta na ganin
cewa, kaf dakin itace yarinya qarama. Sannan da safe
da tazo babu mai jinyar ta a gurin gadon su, sannan
da tace mata kece matar malam Ismail?
Kai kurum ta girgiza alamun a’a. Ita kuma sai take
qara dogara da cewa, batason sa shiyasa shine dalilin
da yasa tace a’a. Fatanta ace Ismael yana gurin ta
samu ta dan ganshi ko zataji sanyi. Sai dai tana
leqawa taga wata gyatuma zaune kusa da Yarinyar.
Tayi ta leqe-leqe kusan minti biyar. Ko mai kama da
Ismail bata gani ba. Taja silifas dinta zata tafi dakin.
Daidai kwanar da zata kaita babban daki, inda suke
kwance, sai ta hango Mahmud shida rabi’a,
budurwarsa, don ta san ta, itama ‘yar islamiyyarsu
ce, sai dai ita, ‘yar babban aji ce, ajin da Ismail ke
koyarwa.
Da sauri ta shiga kwanarsu ta juya baya, sam su basu
ganta ba suka wuce. Ta fito ta bisu da kallo, yana riqe
d kula ita kuma da leda mai dauke da lemu da ayaba.
Wata zuciyar tace, ki bisu mana, kinsan dai babu
gurin wanda zasu, sai gurin masoyinki. Da sauri tabi
bayansu, sai taga sun nufi wata matattakala. Itama
sai ta bisu har suka hau saman. Wata qofa suka
shiga, dan tsayawa tayi kamar mai tsoron binsu don
batasan yaya cikin qofar da suka shiga take ba. Sai
kuma taga ashe dogon guri ne mai dauke da dakuna.
Can ta hango su sun kusa kai qarshen dakunan. Don
haka ta shiga itama cikin azama. A tsorace take tafiya
har takai gurin da Nurses masu kula da wannan

sashen suke zama. Yadda take tafe tana waige-waige
ne yasa wata nurse tace, ke ina zakije? Nan Zainabu
ta daburce, ta soma inda-inda, “am zan..zanje can
ne. Yin me? Nurse din ta katse ta. Duba mara lafiya
zanyi. “ya sunan wadda zaki duba? Zainabu ta sake
rudewa, ni ban..bansan sunanta ba. Nurse din tace,
daga ina kk? ynxun bama yarda da mutane, sbd
rashin gsky yayi yawa, don ko jiya an saci Jariri a
dakin ‘yan tiyata. Zainabu ta firgita. Nima nan nake,
can dakin ‘yan 6ari aka bani gado. Dan uwana ne
matarsa take nan tayi hadari. Shi sunansa Ismail.
Nurse tace, ok na gane shi, wani ustaz haka ko?
Zainabu tace eh, shine. Ta nuna mata, ga dakin can
na qarshe. Zainabu tace, nagode sannan ta sauke
ajiyar zuciya.
Cikin fargaba ta doshi dakin. Zuciyar ta tana
tambayar ta me zata ce, in ta shiga? Ta kalli jikinta,
dube ni sai kace wata tsohuwa. Gabanta yana
tsananin faduwa, don haka sai ta fasa shiga, ta
window taje ta leqa. Tana iya hango Mahmud da
Ismail suna zaune bakin wani gado. Rabi’a kuma ta
zauna kan kujera ta kare fuskar mara lafiyar. Sai dai
tana ita kallon qafafun mara lafiyar akan gado.
Zuciyar ta ta tsananta da bugu, sakamakon Ismail
data gani, hawaye suka soma sharara akan
kumatunta. Can kuma sai taga Ismail din ya bude
kular da ta gani ahannun Mahmud ya zuba acikin
plate. Bata dai san ko menene ba. Tana kallo, yazo ya
dagata ya jingina. Tana ta son taga fuskarta, amma
gashin kanta mai tsawo ya bazu ya tare. Rabi’a ta
tashi, shi kuma ya zauna yana bata a baki kan bencin
dake gurin.
Ta koma ta zauna kuka sosai takeyi. Daga bisani ta
miqe, ta tafi tana kuka. Bata damu da mutanen da
suke kallonta ba. Wasu a zatonsu ko mutuwa akayi
mata, sai suce, “Allah sarki! Allah ya jiqan rai. Tana
saukowa taci karo da innarta tana nemanta. Tace ke
ina kk shiga ne, inata nemanki? Zainabu bata kulata
ba, ta wuce. Tsakiyar gadon ta zauna tare da dora
kanta akan gwiwoyinta. Matar kusa dasu tace, wai
Zainabu lafiya kk wannan kukan? Yau tun safe kk
cikin damuwa. Innarsu ta qaraso. Wai Zainabu daga
ina kk da kuka? Cikin kukan take cewa, an cuce ni an
hadani da namijin da baisan darajata ba. Tunda nazo
asibiti ko sau daya bai leqo ba.
Innar taja tsaki, tare da ce mata, sai ki tona ma kanki
asiri kowa yaji. Ai duk laifinki ne tun farko da kk qi
nuna masa so. Zainabu tace, to ni bana sonshi, kuma
bazan koma gidansa ba. Inna tace, sai kiyi tayi. Ga
faten doya nan da mai
wancan gadon ta sammiki. Cikin takaici tace, bana ci.
Innar tace bari inci, dama ba qoshi nayi da tuwon da

wannan ta kusa damu din ta bani Zainabu ta zame ta
kwanta, idanunta na qara hasko mata Ismail dinta ke
baiwa matarsa abinci a baki. Ta tabbatar da irin son
da Ismail yake yi mata, da ace ita ce, qila ma sai ya
tauna a bakinsa zai bata. Tuno durowar da ake dora
abubuwan ci na dakin dasu Ismail din suke tayi
shaqe da abubuwan ci. Gashi a daki na
musamman. Su kuwa abincin da zasu ci ma sun rasa
mai kawo musu, sai dai maqotansu na kwanciya su
sam musu. Da wannan takaici Zainabu tayi varci mai
cike da mafarkan masoyinta Ismail. Mahmoud ya
kalli rabi’a kinyi qoqari domin mara lafiyar nan bata
ci komai ba tunda tazo asibitinnan sai yau da kika
kawo mata. Azaton Mahmud Ismail baijishi ba
yanayin jinjina ne ga masoyiyarsa. Sai kurum yaji
Ismail ya cafe da cewa, ni kaina na jinjina miki rabi’a
domin a tarihin mami abincinki ta fara ci. Sai dai
abinda basu sani ba mimi mayyar kifin ruwa ce,
kuma farfesunshi rabi’a tayo da alayyahu.
Haka nan ta dai yo ne don batasan me zata yi ta
kawo ba. Yayanta masunci ne, in yayo fatsa yana
saida ma masu suyar kifi. Shine tace ya dan sam
mata zata girkawa mara lafiya. Sai gashi ta kawo a
daidai. Mimi dai tana jinsu bata ce komai ba, sai data
qoshi sannan tace, ya bata ruwa. Tasha sannan tace
zata kwanta. Tun lokacin da likitan ya taimaka masa
suka shawo kanta bata qara yi masa gaddama ba sai
dai kuka. Sannan bata magana sai in tana da
buqata. Ko da suka tafi zariya shi da Mahmud ya
barta tare da yaya Amina da suka dawo ta fada masa
cewa, batayi kuka ba hakanan ta yini shan ruwa,
kuma sun saka mata pampers ita da wata nurse.
Harma mimin tace, su sake canza mata rigarta. Yaji
dadin sannan ya dawo da murna sun samu
admission islamic ya nema. Mahmud kuma sai suka
bashi English baiso ba amma hakanan ya haqura.
Mahmud sun kai kusan qarfe goma sannan suka fito,
Ismail ya rakosu, saida suka hau mashin din
Mahmud sannan ya dawo. Sannu yayi ma wadannan
Nurses din na gefensu da zai wuce, sai dayar take
tambayarsa dazun wata ‘yaruwarka ta gane gurin ku
ko?
Ismail yace, da yau she kenan? Tace dazun nan kuma
nice nayi mata kwatancen dakinku. Ismail yayi shiru
kodai rabi’a ta gani da Mahmud. Yace ita da Abokina
dinnan ko? Nurse tace, a’a ita daya ce tace, tana nan
asibitin ne dakin masu 6ari. Ismail ya girgiza kai.
Gsky babu wanda yazo. Dayar nurse din tace, naga
lokacin data dawo tana kuka, sai nayi zaton tana
tausaya ma wadda ba lfy dinne. Ismail ya sake
dawowa kusa dasu. Tace kuma mu take nema?
Nurses din Sukace, sunanka ma ta kira. Yace to gsky

bata zo ba. Suka ce. Shikenan. Mu dama munga har
kwatancenka anyi mata tace kaine.
Yace to bari inje qila bayan mun fita ne tazo. Shiru
sukayi masa don sun kasa fahimtarsa, kamar yadda
shima ya tafi ba tare da ya fahimcesu ba. Ya shiga
dakinsu ya isa gadon mimi, ya leqa fuskarta har
lokacin idonta biyu. Yace, mimi bayan fita ta anyi
wata baquwa? Tace A’a sai dai ina neman wata
alfarma guda daya. Ya zagayo saitin fuskarta.”ina
saauraronki” yadan rusuna sbd Mimi bayayin
magana da qarfi dama ita. Tace, banason ka sake
cemin mimi, sbd sunan yana tunamin da gidanmu.
Idanunta sukayi narai-narai. Ya girgiza kai, a hankali
yake magana tamkar rada wane suna kk fi son in
kiraki dashi? Tace, khadija kadai ya isheni. Yayi
murmushi. Nima zanfi so ince miki khadija. Sbd
suna ne mai dadi da ma’ana. Allah yasa halayenki su
rikide su koma irin nata. Ta kalleshi, idanunta sun
nuna alamun son qarin bayani. Yace matar manzon
Allah ta farko sunanta kenan, kuma itace mace ta
farko data soma kar6ar musulunci a tarihi.
Ta sadaukar da dukiyarta sbd addinin musulunci.
Sa’annan itace ta haifawa ma’aiki ‘ya’ya guda shida.
Kinga ko anan aka tsaya ta kai daraja. Mimi ta
lumshe ido, ta bude bata ce komai ba. Cikin zuciyar
ta taji dadin jin asalin sunanta a takaice. Shi kuma
ganin bata yaba ba, sai yace aransa, ashe wannan fa
bata san kan musulunci ba. Allah yasa ta san
wadanda nake magana a kansu. Ya dago ya dubeta.
Kin fahimci wadanda nake magana akansu? Ta
dubeshi da sauri, sai kace ba musulma ba? Duk
wanda aka haifa a cikin musulunci, kai ko ba
musulmi ba yasan mai tsira da Aminci.
Ismail yayi murmushi mai sauti, sbd shi in har za’a yi
hira akan addini yana Jindadi. Sannan yace, nasan
kinsan shi mana. Na zata dai baki fahimceni bane.
Kinsan tarihinsa ai? Tayi shiru don bata sani ba. Yace
inada wani littafi da wani malamn sunna Mutumin
kirki ya fassara shi zuwa hausa da turanci, zan kawo
miki in naje gida. In kin karanta aciki zakiji tarihin
Annabin Rahma, da iyalansa, da nasabarsa, zuwa
jarumtarsa har zuwa mutuwarsa. Har lokacin bata ce
masa qala ba.
Ya sake cewa, in kin gama dashi zan sake baki
wadansu littattafan ki karanta na Addini. Zasu
taimaka miki wajen fahimtar me musulunci ke nufi.
Tsaki taja, sannan tace, kana nufin can dama bansan
komai a musulunci ba? Yace ba haka nake nufi ba.
Tace shikenan, ni inason ka fadama doctor na gaji da
qafafuna a haka ni kam a sauke min qafafuna daga
wannan sagalewar na kasa varci. Yace, to zan fada
masa. Amma ynxun kiyi varcinki. Shiru tayi masa.

Bayan ya idar da sallar nafilolinsa cikin dare, sannan
ya nufi gadon mimi yayi mata addu’o’i ya shafa mata,
sbd yau ya manta bai mata ba har varcin farko ya
daukesh. Sannan ya koma kan gadonsa ya kwanta
yana tunanin rayuwa mai juyi da canji a kowane
lokaci. Tunanin wadda akace tazo nemansu ya fado
masa, to ko wacece? Ko kuma cikin ‘yan uwanta ne?
Haka yayi ta tambayar kansa amma babu amsa. Sai
kuma yaya Amina ta fada masa cewa, dasu inna suka
zo tare da matan yayyinsu sunce zasu je su duba
Zainabu. Sai yake cewa, lallai kuwa yaga innarta da
yalwa Aminiyarta anan asibitin, to me ya samu
Zainabun? Yaya Amina tace, oho. Kai ina ruwanka ma
da wata Zainabu tunda matar wani ce? Yace hakane.
Daganan abubuwa sukayi yawa, bai sake tuno da
batun ba sai yanxun. Sai dai duk da haka bai kawo ko
a ransa cewa, Zainabu ce tazo nemansu ba.
Yaya Amina ta shigo, lokacin likitan da yayi dori yazo,
kuma yace, komai yana tafiya daidai. Sannan yasa an
cire mata qafafun sai aka dora mata su kan filo.
Sannan yace, bayan sati biyu in ya dawo sai ayi
hoton qafar sbd a gani ko qashin ya hadu da kyau.
Mimi tace, yaya don Allah za’a iya yimin wanka? Yaya
Amina tace, ki qara haquri mim.. Ismail yace, “yaya
ta ce batason mimi dinnan, a kirata da khadija. Yaya
Amina tace, tanada gsky. To khadija kiyi haquri zuwa
dan kwana biyu, kada muje wanka wanka muyi fami.
Ba ga shi kullum inayi miki gugar jiki ba? A jikinki
babu datti. Takai hannu ta ta6a gashin kanta ta
sunsuna.
Allah yaya, sai inji kamar ina wari, har ta gashin
kaina. Yaya Amina tace, bakya warin komai khadija,
don dai kina da son wanka ne. Mimi ta lumshe ido
tana tuno gidansu da sasanta da dakinta. Ta tuno
gatan ta. Sai kurum taji Hawaye suna bin kumatunta.
Ismail ya dawo kusa ita yace, haba khadija. Menene
na kuka kuma a batun wanka? Wannan fa duk anayi
ne sbd lafiyar ki, garin wanka in aka turgude qafar ko
hannun, kinga sabon dori ya samu kenan ko? “Don
Allah malam ku barni inyi kukana, sbd in nayi ne
nakejin sauqin abubuwa. Ba wai inayi don na raina
qoqarinku bane, ina yi ne sbd ya zama dole inyi. Yaya
Amina tace, ki dinga sassauta wa zuciyar ki dai
domin wani ciwon zai shigar ki.
No related posts.
POST COMMENT
22
Let God take the burden off your shoulders.
Connect now.
GodLife OPEN
22

Ismail ya miqe “yaya ni dai bari in barki da ‘yar
rigimar nan taki inje gd inyi wanka. Sannan zanje
gurin malam Aminu. Su Mahmud dazun ya kira ni
wai lallai yana nema na. Tace to sai ka dawo. Amma
fa kar ka taushe hannu sbd yau waina nakeson yi,
zan koma gida da

1 Comments On CANJIN RAYUWA
avatar
mariya-6-8

9 months ago

Reply

In HAUSA language

Please Login or Register in order to submit comment