Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

qa'idarsu ce, sai mu haqura mu bisu yadda sukeso. Mahmud yace, karka damu, zamu yi wannan tunanin in mun kusa hada karatunmu. Ismail yace, inason in gina makaranta, babbar makaranta, amma lamarin babu sauqi. Mahmud yace, inda anan qasar ne, zaka samu masu taimakawa, amma mu masu kudin qasarmu, gsky taimakonsu da sauqi. Masu taimakon basuda yawa, wasu ma in zasu taimaka sai sun debi 'yan jarida. Sukayi dariya, sannan suka tafa.
3⃣2⃣A batun kyau, Ismail yayi kyau. Sun yi kyau na ban mamaki, musamman Ismail, wanda ya kasance fari. Jajir yayi sbd AC, ga cima mai kyau. Yayi 'yar qiba, farinsa yayi tas-tas, gashin kansa da sajen sa zuwa gashin bakinsa, sunyi shar tamkar an shuka su. Idanunsa sunyi tas-tas le6unansa sunyi jajir. Kallo daya daka masa, zaka san ya canza. Kai ko shi da kansa ya kalli kansa yana gode ma Allah daya halitta shi. Ko Mahmud dayake baqi yayi kyau, yayi sumul. Kwanci tashi rayuwa tana tafiya, har azumi ya kawo kai. Su Ismail sukan dan yo aike daga dan abinda sukayi ta ragewa daga dan abinda suke samu na tallafi daga makaranta. Wani dan uwansu dalibi shine ya hadasu da wanda zasu dinga turawa saqon, sai Malam ya amsa sannan ya kira abbansu saddam yaje ya amsa. Farkon azumi sai yaya Amina ta samu ciki, ta kama laulayi, sai aikin gidan ya koma hannun Ummi da saddam. Rashin lafiya yaya Amina takeyi sosai. Hakan shi ya tilasta Mimi fitowa don kamawa su Ummi aiki. Tana taimaka mata da girki, shara da wanke-wanke. Sbd lokacin ta warke sarai, sai dan dingishin da takeyi wanda ba dolene a gane in ba kayi mata kyakkyawan sani ba. Shima dingishin da takeyi saida sukaje asibiti, Doctor salis ya fada musu lokacin da likitan da yai mata aikin zaizo. Ko da lokacin yayi sunje kuma sunyi masa bayani, yace karta damu zata koma rass dinta. Tsoro taji lokacin da zata soma tafiya. Amma tunda batajin ciwo agurin, babu wata matsala. Haka kuwa kafin sallah, tayi sumul a fannin lfy. Saidai fa ga wanda yasan Mimi zaiyi wahala in ya ganta ya ganeta. Hakanan tunda tazo gidan bata ta6a fita ba, ko kanta saidai a wanke a gida. In ya isheta, tasa yaya ta kama mata kalba, domin ko a da bata damu dayin kitso ba. Amma lokacin sallah a ranar idi ta saka Ummi ta rakata saloon ta wanko kanta. CANJI DAI NA RAYUWA gashi nan qarara a gurin Mimi.
[19/09 9:35 am] Inna👬👫: Canjin rayuwa

3⃣3⃣Alhaji bashir ya kalli Hajiya sauda, sannan ya 6alli karas din data wanke masa yakeci, sbd likitansa yace, lallai yana da kyau ya dinga cin karas sbd yana qarawa masu ciwon suga qarfin ido. Yace, "kina dai korata ko?" ba haka bane, ta yaya zan gaji dakai? Yace to kince in tafi Abuja. Tace kawai naga ka dade bakaje bane, kusan tunda ka sallamawa yaran nan kasuwancinka, sau daya kaje. Gashi har anyi azumi, an gama, yau kuma sallah. Yace, shikenan zance Nafisa ta tattaro yarannan gaba dayansu, suzo katsina suyi sallah anan katsina. Sam bana jin dadin yin sallah ko ina inba gida ba. Kinsan wannan. Tace, shikenan suzo nan din. Yace, banda Na'ima tanada tsohon ciki, da sun zo da ita nan itama cikin danginta. Sauda tace, zaiyi wuya minister yabarta, yadda naji kana fadin yanaji da jikansa. Yace, hakane kam. Sai kuma Mimi ta fado mata a rai. Ko ynxun ina Mimi take? Ko tana cikin wane hali? Anya kuwa ba zata bi shawarar Hajiya mardiyya bane? A wani zuwa da tayi ne, suna zancen Mimi, tace ynxun ke Hajiya sauda kin biyema zancen mazannan, kinbar 'yarki ba tare da kinsan halin da take ciki ba? Kiyi tunani fa, su maza ba kamar mu bane, zai iya jure rashin ta, kuma koda wane irin hali take ciki. Hajiya sauda tace, ni banason yace, banji maganarsa ba. Tace, a 6oye zakisa a bincika miki inda take, sai kije ki ganta. Sauda ta danyi shiru tana nazari, can tace, yayi min bayani kuma na gamsu, harma nayi masa alqawari. Hajiya mardiyya tace, shikenan tunda kince haka.
Alhajin ne ya katse mata tunani da cewa, kina tunanin Mimi ne ko? Ta kalleshi. Yace, sauda nima tana raina. Hawayen data jima tana tarawa suka zubo mata. Ya zaro idanu, cikin matuqar mamaki. "Sauda keda kk bani haquri, kuma yau kece da hawaye? Lallai haqurinki ya soma gazawa. Tace, Alhaji inason Mimi kamar yadda kowace uwa takeson danta. Kaga kuwa dole in damu da lamarinta. Da ace mutuwa tayi, na tabbata da ynxun na dangana. Amma tunda tana raye dole in zama cikin tunaninta. Kila ma ynxun ta rasu.
3⃣4⃣Ya matsa hannunta, ba ta mutu ba, ta samu sauqi tun watannin baya, an sallameta daga Asibiti, kuma tana zama gidan 'yar uwar mijinta wadda sukayi zaman jinyarta tare, ko da bata fita, ina zaton zuwa ynxu ta saba da irin rayuwarsu. Ta kalleshi da mamaki, "duk ina ka samu wannan labarin? Yayi murmushi, ke kinsan son da nake yiwa Mimi bazan iya yin da nake tayin iqirari ba. Sbd haka nayi bincike akanta. Tun daga kan likitan daya amshesu har zuwa can Unguwar tasu. Kuma an tabbatarmin yaron yana kula dasu sosai. Haka nan tunda ta shiga gidan 'yar uwar tasa bata ta6a fita ba. In ma ta fita, to mai bani labarin yace, shi bai ta6a ganinta ba. Hajiya sauda tace, lokaci yayi daya kamata mu nemeta, tunda ta horu. Yace, a'a lokaci baiyi ba. Ki sake yin haquri kadan, sbd ynxun haka batun da nake miki mijin nata bayanan, yana madina yana karatu. Sannan akwai wata yarjejeniya tsakanin Mimi da mijinta. Likitan ke bani bayani. Bai fadamin yarjejeniyar da sukayi ba, amma ya bani shawara akan kar mu nemeta da wuri, domin akwai yiwuwar ta sake guduwa. Ya tabbatar min cewa zai nememu da kansa in lokaci yayi, don ya kawo mana ita da kansa, a wata fira da sukayi. Don haka inason ki qara haquri.
Ta sauke ajiyar zuciya. Shikenan Allah yasa munada rabon ganawa, ya sada mu da alkhairi. Yace, insha Allahu zamu gana da ita. Tace, to Allah yasa. Mutuwa ce gatanan da take ci kamar rana. Ynxun kuna tare da mutum, Anjima ace maka ya mutu. Yace, hakane, Allah dai ya bamu cikawa da imani. Dubi maqocin nan namu mutuwarsa ta kada ni sosai. Tare fa mukayi sallar isha'i, lafiya mukayi sallama dashi. Amma sai muka wayi gari ya zama gawa. Sauda tace, ikon Allah kenan. Allah yasa mu cika da imani, in tamu tazo. Ameen, inji Alhaji. Sannan ya miqe yana fadin bari indan fita. Itama tashi tayi donyi masa rakiya. Bayan dawowarta ne ta nufi dakin su hasana don tabasu labarin data samu game da Mimi. Domin kullum suma cikin zancenta suke.
[19/09 6:54 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa

3⃣5⃣Kwanci tashi mai cinye kwanakin bawa. Yau gashi mun wayi gari su Na'ima anayin naquda. Da qyar ta kira wayar momy Nafisa ta fada lata, sbd azaba. Tace, Momy kizo marata tana yimin wani irin ciwo wanda ban ta6a ji ba, ina zaton ma dai mutuwa zanyi. Momy tace, ganinan haihuwa ce. Saida tabi ta gidan Hajiya Nana ta dauketa suka nufi asibiti. Hajiya Nana tace mata ki kira mara mutuncin ki fada masa mana. Ta kira Abbas har sau biyu bai dauka ba. Don haka sai ta kira uwarsa ta fada musu. Ba'ayi minti talatin ba sai gasu a asibitin. An gaisa sama-sama, sannan suma suka nemi wani mazaunin suka yada nasu zangon. Momy Nafisa tana fatan 'yarta ta sauka lfy, yayin da Hajiya Bilkisu ke fatan jikanta ya iso lfy. Kusan awa biyu a haka sannan wata Nurse ta fito tanayi musu albishir da haihuwar 'yarsu, kuma ta samu da namiji kamar yadda hoto ya nuna. Nan aka kaure da murna. Su Hajiya Bilkisu kam tasu murnar tayi yawa. Nan suka shiga kiraye-kirayen 'yan uwa suna fadawa dangi tare da daukan yaron hotuna kala-kala. Qa'idar asibitin, ko lafiyarki lau kk haihu, sai kinyi kwana biyu kafin a sallameki sbd su tabbatar da babu wata matsala. Hakan ta kasance ga Na'ima. Amma randa aka sallameta, rannan tsiya taso ta kaure a Tsakanin su. Domin Hajiya Bilkisu tace, gidanta za'a je, yayin da mai jego tace, itafa ba zataje can ba, Gidansu zataje. Momy Nafisa tace, tunda bataso abarta. Hajiya Bilkisu tace, sam. Nanma Abbas dinne ya kira Alhaji wanda ke umra, ya fada masa halin da ake ciki. Ransa ne yayi matuqar 6aci, ya kira Momy Nafisa yayi mata tatas. Yace kula ta bar masa mata yayi yadda yakeso da abarsa. Kuma yana mai sake sheda mata kar ta bari tayi sanadiyyar auren yarinyarnan. Ba tada yadda zatayi, cikin takaici ta bari suka tafi.
3⃣6⃣Ranar suna yaron yaci sunan mahaifin Abbas, wato Aqilu. Sam Na'ima bataso wannan sunan ba, domin itama taso ne tasa sunan nata mahaifin. Amma yace, ba tada ikon za6a ma dansa suna. Tace, kai kayimin naqudar yaron? Yace ai ba ruwa kk sha kk samu cikin ba. Haka dai take ganin qarfin hali iri-iri akan san da ta haifa. Sai kace wanine cikinsu yayi mata wahalar cikin. Hajiya sauda da Hajiya Binta, duk sun halarci sunan, amma Gidan Momy Nafisa suka yada Zango. Sai dai 'ya'yansu ne sukaje can gidan sunan, domin harda su usaina akaje. Sai yamma sannan su Hajiya sauda sukaje gidan mai jego. Sai dai Hajiya sauda tayi matuqar mamakin ganin yadda Na'ima take a kode, a rame, Na'ima mai garin jiki, amma harda qashin wuya. Hajiya sauda ta kasa dannewa tace, Na'ima kinyi ciwo ne kafin ki haihu? Kai ta sunkuyar, "nayi ciwo sosai Hajiya. Hajiya Binta kuwa baki ta ta6e, tare da cewa, Ai dama hangen dala ba shiga birni ba. Alhaji Bashir kuwa, ta Abuja ya sauka don yaga sabon jikan nasa tare da 'yar tasa. Duk da yana namiji, yayi matuqar mamakin ganin lalacewar Na'ima. Amma sai yayi shiru sbd ya san cewa haihuwa tayi, kuma baisan irin wuyar da tasha ba.
[19/09 6:54 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa
3⃣7⃣Ismail da Mahmud suna zaune a farfajiyar makarantarsu, inda sukan hadu da abokansu don qarama junansu sani, da qaruwa da basirar juna. Yau kam su biyu ne saura basu riga sunzo ba. Mahmud yake cewa, Ismail kasan me nake tunani? Ismail ya dago kansa daga littafin dake hannunsa, yana dubawa yace, sai ka fada. Mahmud yace, wannan hutun da zamu samu tunda na qarshen shekara ne, yanada tsawo, zamuje gida. Ina tunanin da matata zan taho. "wace matar?" Mahmud yace, Rabi'a mana. Aure zansa a daura mana. Dariya sosai Ismail yayi, sannan yace, ba kace ka fasa ba? Mahmud yace, kai malam haqurina ya qare. Kullum cikin mafarkai, gara kai gwanin azumi ne. Ismail yace, in kaga zaka takura kuwa yin hakan shine mafita. To amma ya batun aikin hajinmu? Don gsky koda hutuna zai qare banje gida ba, nayi wa kaina alqawarin aikin hajji. In na samu yadda nakeso la duk shekara sai nayi har in gama karatu. Mahmud yace, munada lokaci ma, tunda sai an yi fiye da sati biyu da gama aikin hajji za'a koma hutu. Ka ga kuwa har zamuje mu dawo. Ismail yace, Allah ya kaimu lokacin, ai hutun ma ya qarato. Su Ismail sun dan tara kudi sakamakon wani aiki da sukayi tare da amincewar hukumar makarantarsu. Wadanasu masu hannu da shuni ne suka nemi makarantar ta taimaka musu da dalibai wadanda zasuyi musu rabon abincin sabil, da yake can qasar kowa so yake yi yaga an cinye nasa. Shine makarantar ta nemi dakiban ta tuntu6e su ko akwai wanda keson yi. Ismail da Mahmud suka shiga cikin sahun wadanda suke son yi. To anan ne suka samu kudi. Kamar yadda suka tsara hakan ce ta kasance, domin sunyi aikin hajji lfy sun gama lfy. sannan suka koma makaranta sukayi shirye-shiryensu suka nufi gida Nigeria. Abuja aka sauke su. Zukatansu fal da farin ciki mara misaltuwa. Ismail yace, gsky Gida daban ne, duk da cewa Abuja ba katsina bace, sai naji wani irin dadi, duk da cewa qasar dana baro tafi tawa komai, amma farin cikin na daban ne. "Ai Gida yayi." inji Mahmud.
[20/09 12:59 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa

3⃣8⃣A kaduna sukayi azahar, sannan suka dauki hanyar katsina cikin qosawa. Mahmud yayi murmushi don Jindadi, don cewa zaiga iyaye da kuma Rabi'a. Ya kalli Ismail, na qosa matuqa mukai Gida. Ismail yayi dariya, "wai kai wa kk zumudin gani ne haka?" Mahmud yace, su inna dasu Malam, sai kuma rabi'a. Ismail yayi murmushi. "Gara dai ka fadi gsky. Mahmud yace, gskyr kenan, kai wa ka qosa ka gani? Ismail yace, yaya Amina mana da 'yan yaranta, tunda ni ba uwa gareni ba bare uba. Sai dai 'yan Gidanmu da yayuna, duk da cewa, su ba lallai bane suyi murna da ganina. Amma harga Allah nidai ina sonsu, kuma nayi kewarsu. Haka ina kewar Malam sosai. Mahmud yace, kayi tuya ka mance da albasa, matarka fa khadija? Ismail yayi murmushi, "kasan harga Allah na manta da ita." Mahmud yace, sbd me? Ismail yace, sbd ko waya na kira, ba ko yaushe take amsa ba. Ba ta damu dani ba, shiyasa. Amma duk sadda zan sayi Tsaraba bana mantawa da ita. Mahmud yace, kenan bakayi kewarta ba? Ismail yace, ba sosai ba. Don nasan itama bata damu da ganina ba. Mahmud yace, kamata yayi kawai ka taho da ita in zamu dawo. Ismail yace, banajin hakan a jikina, ni kwanakinnan ma mafarkin Zainabu ke damu na, da kuma yawan tunaninta. Mahmud cikin jin haushi yace, wacece kuma zainabu? Nayi tsammanin ma ka dade da shafe babinta? Gidan wani fa take. Ismail yace, na dade da shafe babinta Allah kuwa. Tunda tayi aure, ka ta6a jin nayi maganarta? Mahmud ya girgiza kai. Ismail yace, ni kaina bansan dalilin dayada ta dawo cikin rayuwata ynxun ba. Mahmud yace, sharrin shaidan da mugayen mafarkai.
3⃣9⃣La'asar sakaliya, guraren qarfe biyar suka sauka garin katsina. Shatar mota sukayi zuwa gida, za'a fara sauke Ismail gidansu yaya Amina, domin suna kan hanya, sannan a wuce da Mahmud. Ta kan layinsu Zainabu zasu wuce, sbd Gidansu yana bakin titi. Tun kafin su qaraso yaketa leqen gidan. Daf da zasu gota gidanne, kamar cikin mafarki, idanunsa suka qyallo masa Zainabu ta fito daga maqotansu dauke da bokiti a hannunta. Da alamu ruwa ta debo. Ismail cikin sauri yace, Kalli Zainabu, Mahmud. Mahmud ya waiwaya ya hangeta. Yace, tabbas itace. Qila tazo ganin gida ne. Ismail dai yana can yanata waiwayen Zainabu har ta shige gidansu. Ya lumshe ido gabansa yana wata irin faduwa. Gida Zainabu tazo kamar yadda Mahmud yace, ko kuwa aurenta ne ya mutu? Mahmud ya lura da yanayin da Ismael ya shiga. Don haka sai ya harareshi, cikin salon son kushe Zainabu yace, duk ma ta tsufa, qila ma ynxun ta haifi yara uku. Da sauri Ismail ya kalleshi, "haba dai Mahmud! Sai kace, akuya, duka yaushe akayi mata auren? Mahmud yayi dariya, tsufan ne naga yayi yawa. Ismail dai bai tanka ba illa dai yanason sanin labarinta. Sadam yana fitowa an aikeshi sai kurum yaga mota ta tsaya. Shima tsayawa yayi, domin ganin ko su kawun nasa ne. Sororo ya tsaya yana kallon kawun nasa tamkar wani sabo fil. Da gudu ya juya cikin gida yana fadin mamanmu! Kizo ga kawunmu nan ya iso! Mimi ta rasa dalilin dayasa taji gabanta yayi wata irin faduwa. Tana daga cikin dakinta, ta sake jiyo saddam yana fadin, kinga kawunmu sai kace wani balarabe. Da sauri su yaya Amina suka fita, ga tsohon ciki, Ummi kam da gudu ta isa ta qanqameshi. Cikin murna suka gaisa da Mahmud, sannan aka kwashe kayan Ismail zuwa cikin gidan, sannan ya rako Mahmud zuwa gurin motar, sukayi musabaha, yace, ka gaidamin Malam. Sai na shigo zuwa dare. Ya koma cikin Gida, ya samu su yaya sunata yi masa shirye-shiryen inda zaici abinci. Ya Kalli yaya, dama ciki ne dake? Shine muna waya baki ta6a fadamin ba, da nayi miki tsarabar kayan jarirai da kuma pampers. Suna arha acan. Ina gani gurin abokan karatunmu masu iyali. Tayi murmushi, cikin kunyar qanin nata. Tace kurum sai ince maka inada ciki? Kafin ya sake magana tace, mu shiga ciki mana ga abinci.
[20/09 12:59 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa

4⃣0⃣Ta kalli Ummi, "kira auntynku mana, ko tana varci ne, sarkin varci." Ya kalli dakin, "dama tana ciki ne? Yaya tace, eh, sai dai ynxun haka varci takeyi. Yaya ta soma gabatar masa da abinci dana sha mai sanyi harda kaza aka soya masa. Yace da baku wahalar da kanku ba gurin soya min kaza, ko acan na jima banci ba, sbd ta hau min kai. Yaya tace, ai kuwa gashinan ka zama tamkar balarabe. Ka ganka kuwa? Ismail yayi murmushi, bari inci Alalata dai yaya. Yana ci suna hira. Ummi ta shigo tace, mamanmu aunty khadija tana varci. Tace ki tasheta kawai. Yace a'a ki varta kawai. Bayan ya gama, suka fito, yace, su saddam su kwashe kayansu sukai masa dakin khadija. Tana kwance tamkar mai varci, amma idanunta biyu. Gabanta ke faduwa tanajin jin qamshinsa, lokacin daya shigo dakin, bata ta6a jin irin qamshin ba. Yana tsaye yana kallon ta. Yaya ta shigo tasa hannu ta girgiza ta, "khadija ki tashi mana, magriba tabkawo jiki, ke varci baya yi miki wahala." Miqa tayi sannan tace, yaya kk ce mene? Tace, ki tashi Malam Ismail sun iso dazu. Shikam yana jingine da bango ya harde hannuwansa. Mamakin ramarta yakeyi, ga shi tayi baqi, ga qurarraji a fuskarta. Da ma ita ba qiba ba, sai tyi tamkar wata baby. Mimi kasa dago ido tayi ta kalleshi. Kanta a qasa tace, sannu da zuwa kawun su Ummi. Sunan data kirashi dashi yasa shi murmushi. Yace, yauwa sannunki malama khadija. Muryarsa da taji ta canza ne yasata dago kai. Jin muryar tayi tamkar ta balaraben da ya koyi hausa, ko ko bafillatanin da hausa bata isheshi ba. Mamakin kyawun surarsa ta bayyana a fuskarta, ta kafa masa ido, batasan lokacin da bakinta ya furta cewa, kai! Amma kayi kyau da yawa. Qasar ta canza ka, ta amshe ka. Yayi murmushi, a zuciyarsa yace, ina girman kan? Ya dubeta, nayi kyau? Khadija dama can ni mai kyau ne. Tadan ta6e bakinta tare da yin dana sanin fadar hakan a ranta, ta lumshe ido. Maza sunada kyaune? Kawai dai ka samu hutu. Yayi dariya, ko ma dai yaya ne kin yaba, kuma nagode. Taso kidan taka in gani, tafiyarki ta koma daidai? Yaya dake zaune bakin gado tana jinsu, sai ta tashi, "bari in kira abbansu saddam in fada masa ka iso, ta fice.
[20/09 8:59 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa

4⃣1⃣Mimi tace, in kayi haquri, ai zaka gani, ba sai kasa ni yin wata tafiya ba. Yace, amma kin daina dingishin? Harynxu tana tare da jin haushin maganarsa ta dazun, tace, "Qila." ya matso ya zauna a bakin gadon, ya rage muryarsa, "kinyi baqi, kin rame. Amma muryarki dinnan mai sauti can qasa da miskilancinki suna nan." Ta zuro qafafunta ta dayan gefen ta sauka. Sannan tace, bai kamata kaji mamakin ganin na canza ba, domin kafi kowa sanin komai. Ina Mahmud? Shi ma ya miqe, yana gida. Anjima ki shirya muje mu gaida malam. Ta girgiza kai, "ban fita kayi haquri." yayi dan murmushi, hakane, tam bari na dan yi wanka kafin a kira magriba. Ta nufi gurin madubinta tana fadin yanada kyau. Ummi ce tasa ruwan wanka takai masa. Ya bude jakarsa ya dauki kayan wankansa cikin wata jaka ta leda, wadda aka yita don saka kayan wanka. Sannan ya ciro jallabiyarsa, wata mai shegen kyau ruwan hanta, tana da zif daga qirjinta har wuya, sai kuma tsintsiyar hannu da ma6alli. Sai hula mai kalar zaren da akayi dinkin. Mimi tana kallonsa da gefen ido, ya dora kayan saman gadonta, sannan ya fita. Da kallo tabi bayansa. Kyawunsa yana bata mamaki. Bayan ya fito, sai daya shirya tsaf, Mimi tana ta satar kallonsa. In ta ga alamun zaya waiwayo saita sauke kanta. Ya feshe jikinsa da turarukan larabawa, qamshinsa ya gauraye ko'ina, sannan ya kalleta, nayi kyau? Cikin zolaya yayi tambayar. Ta ta6a baki, tare da cewa, ina wani kyau anan? Yace son ranki kk fada. Bari inje gidanmu. Daga can in wuce in gaida malam. Tace ka gaida su. Ya dauki qaramar jaka daga cikin jakunkunan da yazo dasu. Tabi bayansa da kallo har ya saki labulan. Ta jingina da sif dinta tana mamakin yadda ya rikita ta har haka. Yaya tana zaune zatayi alwalla, ya ajiye jakar a gabanta, tsarabar 'yan gidanmu ce, su yaya jallabiyu, matan kuma dabino ne da zam-zam. Inna kuma harda darduma da wata doguwar riga. Yaya tace, yayi, Allah ya bada lada. Yace Ameen. Ya dauka ya fita.4⃣2⃣Duk wanda suka gaisa da Ismail, sai yace, Masha Allahu kayi kyau. Yana shiga gidansu ana kiran magriba, ya Kalli dakinsa yayi murmushi, sannan ya shiga cikin gidan, babu zato suka ganshi. Don haka suka shiga kallon kallo. Sai kuma aka shiga yi masa sannu da zuwa. Yayi musu qwarjini sosai, don haka da 6are-6aren jiki sukayi ta amsa gaisuwarshi. Ya shiga dakin inna sai yaga ta qara masa tsufa. Ya gaida ta sannan ya kawo tsarabarsu ya bata tare da yi mata bayani a gurguje ita kanta duk sai yaga tayi sanyi. Ya nufi masallaci. Bayan sun idar da sallah nan sukayi ta gaisawa da mutane suna tayi masa sannu da zuwa. Yana tare da jama'a har zuwa bayan isha'i, sannan ya nufi Unguwar su Mahmud. Ya shiga cikin gidan suka gaisa da mutan gidan, sannan ya fito ya zauna gaban Malam inda suka gaisa tare da ci gaba da hira. Malam yayi murna da zuwansu, sannan ya saka musu albarka. Sun jima suna hira suna ta bashi labarin makarantar. Daga bisani suka nufi gidansu Rabi'a, shida Mahmud. Yaro ya samu ya tura cewa, ana kiran Rabi'a. Bayan tafiyar yaron ne yace, bari mu gani tana fita da bananan. Ismail yace, kar kayi zargi. Rabi'a ba zata yi maka haka ba. Dan aiken ne ya katse su da cewa, wai ance tayi aure. "Aure?!" Mahmud ya tambaya cikin faduwar gaba. Ismail yace, ba kunyi waya ba? Mahmud cikin tashin hankali yace, ko jiya munyi waya, bazata kawai naso inyi mata, shiyasa bance mata muna hanya ba. Ismail yace kai yaro je kace inji Mahmud. Tare da dan aiken suka fito tayi murna sosai da ganin masoyinta. Tace ina zuwa. Duk da cewa dare ne, saida ta qara hoda a fuskarta sannan ta fesa turare mai madaidaicin qamshi, sannan ta dauki tabarma ta fito. Shikam Ismail, suna gaisawa daya lura masoyan suna dokin juna, sai yaga ya dace ya basu guri. Don haka sai yace, to ni zan tafi. Suka yi musabaha da juna. Ismail yana cewa, sai na shigo da safe. Zan shigo in kawo ma Malam tsarabarsa. Mahmud yace, shikenan Allah ya kaimu. Gidan yaya Amina zaka kwana? Ismail yace, a'a Gidanmu zanje in gyara dakina ynxunnan. sukayi bankwana ya wuce.

4⃣3⃣Gidansu ya koma, inda ya bude dakinsa, duk qura da yanar gizo-gizo. Ya kai qarfe goma sha biyu Tsakanin share-share da kuma goge-goge, sannan ya shiga gida yayi wanka. Sai daya kwanta sannan ya tuna cewa yayi masu yaya alqawarin cewa, zai koma. Ya kalli agogon wayarsa, a fili yace dare yayi. Washegari tunda ya dawo daga masallaci ya sake kwanciya bai farka ba sai qarfe takwas. Ya shiga cikin gida suka gaisa da mutan gidan. Sai dai yayi Mamakin ganin yadda suka sakar masa fuska. Amma sai ya tuna cewa fa yayin dawafin sa a dakin ka'aba, yayi ta roqon Allah cewa, Allah yasa shida 'yan uwansa da suke uba daya sun fahimci juna. A fili yace, Allah ya amshi addu'ar sa. Bayan yayo wanka ne, sannan ya ciro jakar kayansa tada, ya cire ma abbansu saddam kala biyu, sannan ya dauki sauran zuwa cikin gida yaba yayyinsa, sannan ya nufi gidan yaya Amina. Mimi ce amsa sallamarsa lokacin da ya isa gidan. Tana zaune akan qaramar kujera, tana wanke-wanke a bakin rijiya. CiKin Mamaki ya kalleta, tare da tausayi, yace, Mimi

1 Comments On CANJIN RAYUWA
avatar
mariya-6-8

9 months ago

Reply

In HAUSA language

Please Login or Register in order to submit comment