Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

windo,ta yaye labule tana kallon masallacin,wanda dama saitin windon nata yake.tabbas masallacin nan ne,to wane ne wannan da karfi hali?lta tunda ta ta so bata taba jin an kira sallah a masallacin nan ba.ta koma ta kwanta ta saki tsaki.za ta ga mai wannan kokarin na hana mutane barci.ta fara barci ta ji an sake kiran sallar,aka shiga masallaci aka yi sallah,ba ita ta samu barci ba sai da aka idar da sallah. don haka bata farka ba sai shabiyu,ta yi mika tare da hamma,ta silalo kafarta kasa kan lallausar kafet. tamkar sarauniya ta ke jan taku har zuwa bandakinta, wanda aka tsara shi da kalar pink,kalar da take bala'in so,bandakin da yafi na kowa tsaruwa a gidan, hatta mahaifinta.ta shiga bahonta,bayan ta cika shi da ruwan dumi,sama da awa daya ta dauka a wanka,ta fito.gurin shafarta daya ne da kayan sawanta, bata cika yin kyale-kyale a fuska ba, hoda kadai sai jambaki bayan mai,amma tsadarsu ta ishi talaka jari. ta saka wando baki irin mai kama jikin nan,da riga ja,ta ja dogon gashinta ta kama shi da bakin ribbon. ta soma wanka da turaruka.ta nufi gadonta ta dauki wayarta tana dubawa,miss call kusan goma dadin ta,da na dear khalil,dana hajiya guda biyu. bakin gadonta zaune tana kiran layin dadinta,ya daga tare da cewa uwata ya ya aka yi?cikin shagwaba da muryarta din nan wanda ke fid da sauti a hankali cikin salo ta ce, dad na ga miss call din ka ne fa?ya ce,uwata har na fita baki tashi ba,lafiyarki kalau ko?ta ce,eh dad,emm yawwa dad wane ne jiya cikin dare ya hana ni barci da kiran sallah?ya ce, malaminki ne,gabanta ya yi bala'in faduwa ta ce,dad shine da zuwansa zai canza mana tsarin gidanmu?mene ne nufinsa da haka?ya ce,babu komai MIMI,kin san malamai da son masallaci,yau ni mana samu yin sallar asuba a kan lokaci,sannan makwabtanmu sun shigo mun yi sallar tare da su.ta ce kash dad,yanzu gidanmu gurin tara mutane kenan? ya ce,kar ki damu musuluncin kenan,ina fata za ki sauko domin daukar karatu.
[01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (40)Gurin malamin na ki.kuyi amfani da falon baki, ko falo na ki ke so?ta ce,aa dad ya tsaya can falon baki,ba falon ka ba,da wannan bakauyiyar kafar tashi.ya ce,shikenan tunda naima tana gida ita mata soma karatun,in su ahmad sun dawo da yamma sai yayi masu,ta ce,shikenan dad,bari in kira hajiya naga ta kirani.ya ce,ok nima yanzu muka gama waya,ki ce ina gaida ta.cikin fargaba ta kira mahaifiyarta,hajiya ta daga cikin lallausar murya ta yi sallama,MIMI ta amsa tare da cewa,ina ki ka bar waya?ta ce,ina barci yanzu nayi wanka sai naga miss cal dinki.hajiya ta ce,na zaci kin fita gurin karatu ne?ta ce,hajiya ban san ma ya zo ba sai yanzu dad ke fada. ln na yi break zan yi yanzu,hajiya ta ce,ki maida hankali saboda ki san abinda zaki bauta ma ALLAH mahaliccin ki.suna yin sallama kiran kalil ya shigo sai da yayi daf da tsinkewa ta daga,wannan wani raayinta ne.ta ce, hello dear ya aka yi?ya ce,ba komai ina son in ji muryar ki ne?yanzu ki ka tashi?ta ce, fh,yaya hutu?ya ce,ga shi muna yi,don ALLAH ina son in zo gidanku wannan karon,ina jin tsoro kamar zan rasa ki,kar ka damu dear na fada maka don juna aka yi mu,ina jin haka a jiki na. ya ce, lovely har yanzu ban yi mafarkin haka ba ina ganin sai zancen ya je gurin manyanmu.ta yi 'yar dariya, ka san fa dad naka ba zai yarda ka yi aure yanzu ba, ni kuma in dad dina ya ganka guri na kila ya ce,zai min aure,ka ga sai matsala ta samu. ya ce,na fahimce ki,ba na son na sha wahala a aurenki kamar yadda na sha kafin na samu amincewar soyayarki na garu.ta yi 'yar dariya cikin salon maganarta ta ce,dear ka manta da haka,bari na karya,ya ce,to shikenan sai in mun hadu online ta ce,tam.cikin tafiyarta tamkar mai tausayin kasa take saukowa daga benenta,wanda ita kadai ce a sama ta ke mallakin kato falo da dakuna uku.daya dakin barcinta daya kayan karatun ta,tun daga computer zuwa kasa, dayan kuwa rufe yake duk da cewa shima da komai a cikinsa.
[01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (41)Momi nafisa tana zaune tana kallon fim a cikin tafkeken tv dake manne a bangon falon.ta waiwayo,kin fito MIMI?ta kalle ta,na fito momi an tashi lafiya?ta ce,lafiya lau, dadinku yayi ta kiran ki baki fitoba,ta yatsi na fuska,mai kiran sallar cikin dare nan ne ya hana ni barci.momi ta ce,ai malaminki ne,na ga dad dinki ya yaba da hakan.ta ce,na lura da haka a wayar da muka yi dazun. ta isa gurin karin ta hada shayi tana sha,ta dubi mahaifiyar tasu naima fa?ta ce,tana dakinta,ta dauki wayarta dake kusa da ita,ta soma kiran layin na'ima,tana dagawa MIMI ta ce,sis zo mana,naima ta fito cikin riga mai gajeran hannu da wandon jins damamme,kanta ita ma babu dankwali,ta kama gashinta da ribbo blue. ta ce,sis gani,MIMI ta daga fararen idanuwanta ta kalli na'ima cikin harshen turanci suka fi yin magana.ta ce,ki je gurin folina a kicin ki gani ko ta gasa kifin,ta ce,sis mu je snacks store mana mu ci, MIMI ta harare ta,ki yi abinda nasa ki mana,ta daga hannu,alamun ban hakuri ta rinka fadin sorry. folina ta zo,ta shirya wa MIMI gasashen kifi tare da gasashen biredi,tana gamawa ta kalli naima ina son a kira mini malamin da yazo jiya,amma ban san yaya zan yi ba,don ba za kije ba,amma ki duba in kin ga direban ku,ko wani dai ya kira shi,ta ce tam sis. lokacin da hamisu ya sanar da lsmail cewa ya je ciki ana neman sa,sai ya ce,sai mun yi sallah tukuna. don yanzu zan kira.bayan sun idar sannan ya ce,ma hamisu ya yi masa jagora zuwa cikin gidan. barandar kofar falon,nan suka danna 'yar wata danja,jim kadan aka bude. naima ce ta kalle su irin kallon da wasu 'ya'yan masu da shi suke yi wa masu yi masu hidima.ta ce, wane ne malamin?hamisu ya nuna lsmail wanda ke tsaye sanye cikin yadi mara nauyi,hularsa ta dace da yadin wandonsa a dage irin na ahalil sunna. ta kalle shi sama da kasa, ta ce,ina zuwa.kamar minti biyu ta dawo ta ce,sis ta ce,ka shigo,ya shiga dankareren falo wanda tsarin saya wuce duk tananin lsmail ga sanyi AC
[01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (42)AC ko ta ina.ta waiwayo ta ganshi tsaye, ka bi ni mana,ya ci gaba da binta cikin zuciyar shi yana addu'ar ALLAH ya tsare shi daga sharrin da ke cikin gidan,alherin dake ciki ALLAH ya sada shi da shi. wata kofa suka shigo inda suka iske wani falon madaidaici,shima ya tsaru ta ce,ka jira ta a nan. kusan minti biyar,sannan MIMI ta shigo falon ba tare da sallama ba,rashin sallama yana kona ran lsmail,don haka bai ko kalle ta ba.ta zauna tana kallon fuskar wayarta,ta fi minti biyar chatin ta ke yi da kalil dinta,labarin karfin halin malamin take ba kalil.ta ce, ni da zai ci a gurin ubana, amma ni yake jira in ji da shi,kalil ya ce,kin san talaka da girman kai.ta dago ido ta kalli lsmail wanda ya bude ALKUR'ANI yana karantawa a zuciyarsa.ta ce,hamm mai neman taimako baya girman kai. ya dago ya kalle ta,kafin in ce komai zan soma yi miki nasiha,da saka hijabi don suturta jikin ki. ki koyi sallama yayin da ki ka zo gurin mutane,abu na uku,ba neman taimako na zo ba,ke nazo in taimaka ma wa,don haka yanzu sai ki dauko littafi mu fara daga huruful ija'iyya.ta ce,ba ka isa ka ce za ka taimake ni ba,don baka da komai,kuma ba zanyi sallamar ba,ba zan rufe jikin ba.ln baka sani ba,barin in fada maka,na sa a kawo ka nan gidan ne saboda in tozarta ka,in nuna maka kai kaskantacce ne.ya ce,don na miki wane laifi?ta ce,kai ne mutum na farko dana taba yin sa-in-sa da shi.wanda ya taba kallon cikin ido na ya fada min magana,kuma ina son ka zama na karshe,wannan shine laifin ka.lsmail ya ce, yanzu dai za ki yi karatun ko a'a?ta ce,na ce ba zanyi ba,ya mike tare da kwashe takardunsa.ta ce,ban sallame ka ba,yayi tafiyarsa ya bar ta zaune. MIMI ta bi shi da kallo cikin mamaki,shi wannan dame yake takama,har da baya jin shakka ta,kamar yadda sauran jamaa suke ji?ya san wace ce ni kuwa?ya san wane ne ubana? Ba wani ba ne uban MIMI fa ce alhaji bashir,dan asalin masari ne,karamar hukumar kafur jihar katsina. mahaifiyarsa 'yar dabai ce,su shabiyu ta haifa,
[01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (43)Amma yanzu saura su biyar,bakwai sun rasu,mahaifiyarsu ta rasu lokacin ya kammala sakandire,yayyin shi. mata uku ne,sai namiji daya dake bin shi,rakiya da basira a malumfashi suke aure, saratu kuma tana cikin kafur,malam aliyu mahaifinsu ya sake yin aure. inda matar ta kasance mai son kanta game da son zuciyarta.wannan yasa ya bar masari,ya soma shiga cikin garin katsina don neman abin kanshi, maimakon noma da suke taya mahaifinsu,shi da shafi'u kaninsa. ya yi sana'o'i kala-kala, tun daga kan kwandastan mota har zuwa dako,daga bisani ya soma bin wasu abokansa guda biyu da suka kama shago daya su uku,da lsa mani da kabiru naalla suna harkan dabbobi. tun yana karba yana saidawa ya cire ribarsa,har ya zo ya samu jarin kansa. sannu a hankali suka yi zangonsu na dabbobi, lokaci bayan lokaci yana zuwa masari ziyartar danginsa da mahaifinsa kuma yana yi masu alheri. kaninsa shafiu har yayi aure matarsa ta haihu,don haka mahaifinsa da yayyansa kullun burinsu yayi aure.wani zuwa da yayi har mahaifinsa yana cewa,ga 'ya'yan 'yan'uwansa ya zo ya auri daya daga cikinsu,sai bishir din ya ce,yayi hakuri,shi ba ya shaawar auren zumunta,amma duk lokacin da ya ga wanda ta yi masa,to zai yi aure,amma a yanzu neman kudinsa ya sa a gaba. ranar wata jumaa lsa mani ya tare shi yana sauri za shi masallaci ya ce masa,bashir ga wadansu shanu can zaa saida su a rugar fulani nan mashi.bashir ya ce,har mashi?gaskiya da kyar zan je,lsa mani ya ce,za ka samu alheri mutumi na,don jiya na dawo tafiya,ka sani da na saye su,amma ka daure mu je in ka dawo masallaci.hardon gar ne ke son zuwa aikin hajji,shine zai cikon kudi.bashir ya ce,ni dai masallaci na nufa ga shi ina jinjina zuwa mashin nan,lsa ya ce,mu je dai masallacin nan tare ma kawai,da zanje na karfe biyu ne,in ya so daga can sai mu wuce.a masallaci suka hadu da kabiru na'allah,inda suka nufi mashi dukkan su.
[01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (44)Sun je rugar fulani,inda suka shiga garke shanu don duba shanu.ya nuna masu,aka shiga ciniki, an daidaita kuma bashir yayi alwashin kawo kudi gobe,saboda kudi suna banki.suna cikin sallama ne idon bashir suka kai kan wasu 'yan kwailoli guda biyu,sun dawo daga tallar nono,dayar ya kure da ido, 'yar similmila ta yi masa kyau,sai da ta bace ma idanunsa,ya bar kallonta.har lsa mani ya gane,bayan sun bar gurin ya ce,bashir kana ta kallon 'yar mutane saboda me?kar dai ka ce min son wata kake yi daga cikinsu?bashir ya ce laifi ne yin hakan?lsa ya ce,aa ban ce ba,sai dai ka bani dariya kawai,duk 'yan matan da ke cikin garin katsina? ka rasa wanda za ka zaba sai wadanan 'yan ruga mitsi-mitsi da su?kabiru na'allah ya ce,in dai fulanin nan nema,ba su son baiwa bare 'ya'yaansu.bashir ya ce,ku yi min addua in rabo na ce za su bani,don gaskiya na ga wacce nake so.suka sa mishi dariya. Abin ya wuce da tunanin bashir,domin ranar da tunanin 'yar fulani ya kwana,ya kosa ya je su kai kudin shanu,don haka tun tara ya shirya ya nufi banki ya ciro kudi,daga nan suka nufi mashi. ko da suka isa burinsa ya ga yarinyar da ta hana rayuwarsa sakat, har suka bayar da kudin shanun suna kokarin zuba su a mota,amma bai ga giccin wani da ba.ya kama mota zai hau sai ya hango ta tana kada nono cikin dan kuttunsu da suke cire mai,da sauri ya fasa shiga motar ya nufi gurinta. sallama yayi mata ta dago a firgice ta ji abin kamar daga sama,ganin mutum sai ta amsa cikin dariya. ya ce,'yan mata ya ya sunanki? ta kalle shi ta ce, suna na?ta kau da kai,ta ci gaba da abinda ta keyi.lsa ya kwada masa kira daga nesa,bashir ka zo mu tafi mana,bashir gani ya ke idan fa ya tafi ya bar damarsa,ya ma rasa ta kenan,shi damuwa.don haka da ya ga abinda zai dame shi,nan da nan zai yi maganin abin,in har zai iya, musamman in na kudi ne, tunda yanzu ba laifi yana samu. sake komawa yayi ya sa aka yi masa sallama da ardo,wanda ya tafi don ya adana kudinsa.kabir yazo gurinsa,
[01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (45)Zo mu je in ya so mu sake dawo wa,bashir ya ce,ba a haka da ni,ka san ni in ina son abu,zan yi duk abinda zan iya in kuna sauri kuyi gaba zan zo.kabiru ya gane fusata ta sa bashir fadin haka,sai yayi dariya,ya yafito lsa mani da hannu, suka zosu ukun suna jiran fitowar ardo. ya ce,da muna daki daya da ku,duk ku kayi aure ku ka barni,dole ku yi min dariya.duk yadda suka dauki lamarin da zafi gurin ardo,maana ba sauki sai suka ga akasin haka.ardo yana da ilimin addini,ya fahimce su,kuma yayi masu bayanin cewa lallai sun yi dace,domin har an bayar da ita,sai wanda aka baiwa din ALLAH yayi masa rasuwa wata biyu kenan. ya kara da cewa,in yana son ta ta amince ya nemi soyayyarta,in ta amince gurin shi babu wata matsala.kwana biyu tsakani bashir ya sake yi wa rugar fulanin tsinke,cikin ado aljihu dam da kudi.lsa mani yasa shi yin tsarabar sarka da 'yan kunne,wai mutanan ruga suna son abin ado mai kyalkyali.bai samu ardo a gida ba sai babban dansa jabiru.sun gaisa inda yayi masa bayanin cewa,ardo ya je cikin gari maganar tafiyarsa aikin hajji.sai dai yayi wa jabiru alheri,ya ce, masa yana son ganin bengel,kamar yadda ya ji ardo ya ambata rannan. sai jabiru ya ce,oh!sauda? ai saudatu sunanta,ardo kadai ke fada mata bengel, na gode bari in turo ta,domin yanzu zasu fita tallar nono.yana tsugune sauda ta isko shi,tana sanye da koriyar atamfa da kuma farin mayafi mai kyalli.duk da fuskarta babu walwala farin ciki gurin bashir ba ya misaltuwa.ta tsuguna can nesa da shi,ta gaishe shi,ba tare da wata kwana-kwana ba ya ce, saudatu kina so na?rufe fuska ta yi da gefen mayafinta ta ce,ardo ba za ya bada ni ga wanda ba bafulatani ba.ta yi magana cikin hausar da bata goge ba.ya ce,kar ki damu ardo ya san da zuwa na,ya amince in nemi soyayarki. saudatu yarinya ce ba za ta wuce sha uku-sha hudu ba,sai kyau tamkar balarabiya.ta ce,in na amince me zai faru?ya ce, aure ne zai faru,ya fada cikin kwaikwayon muryarta, ya lura akwai kuruciya,
[01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (46)Gurin yarinyar.ta ce,kamar ya ya?yanzu da na amince sai a kama aure? ya yi dariya,to me za a jira?zan turo iyaye na su gana da naki,zan bayar da sadaki da duk abinda kuke yi na al'ada,sai a daura mana aure.ta sake kallon shi,sai me daga nan?ya ce, a kai ki gida na,ta ce,ina?ya ce,cikin gari,ta ce daga nan sai me?kuma me zanyi a gidanka?ko kaima kana da shanun ne da zan dinga tatsar nono ina kaiwa kasuwarku.ya ce,aa abinci kawai za ki dafa min,sai in kin haifa min yara ki kula min da su.ta rufe fuska,zan tafi ya ce,haba da sauri haka muna hira mai dadi? ya ce,saada ce ke jira na za mu je talla.ya ce,wace ce saade?ta ce,'yar'uwa ta ce, kanmu daya,ya ce,tare zaayi maku aure?ta ce,ni kan zan tafi ta fada tare da rufe fuskarta.ya ce, ba na son tallar nan,ta ce,ni kan ina son zuwa talla,don naga kasuwa,kai kam,me ya sa baka so?ya ce,ina tsoron kar wani ya kwace min ke.ya ciro tsarabar sarka cikin gidanta ya ce,ga wannan,ta amsa da murna. tana godiya.ya sake fiddo da sabbin kudi 'yan naira goma-goma ta yi ta godiya ya ce,mata zai dawo jummaa ta ce,sai ka zo,cikin abinda bai fi wata daya ba ya mallaki zuciyar 'yar fullo.lyaye sun shiga, inda aka tsayar da rana,sai ardo ya dawo daga aikin hajji.su biyu aka hada bikinsu da saade,ita an kai ta wata rugar fulani da ke kusa da su.lta kuma saudatu can masari aka yi da ita,inda mahaifinsu ya ba su daki. satinsa guda ya koma katsina,a nan tudun wada ya nemi daki,ya koma ya dauko ta,ya saka ta lslamiyya saboda ya lura tana da karancin ilimin addini.ta kasa fahimtar cewa shi din fa mijinta ne,fa di take,yadikko,ta ce, ka da ta bari namiji ya taba ta,balle ma jikinta,ita kan ba 'yar iska ba ce. sai da ya lura ta saka hankalinta a karatu,kuma tana fahimta,sai ya samu malamin ya sanar da shi matsalarsu,nan malamin ya cire minti biyar kullum yana yin nasiha ga dukkan dalibansa don akwai me irin matsalar addini bai rufe komai ba,don haka bayani filla-filla ya dinga yi masu ya yin.
[01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (47)Nasihar.sauda ta fahimci komai,kuma ta mika wuya ga mijinta game da neman gafarar sa,lokacin watannin su goma da aure, shi kam yayi ta ji da ita tare da kara son ta tamkar ya ba ta kamshi. sunyi shekara uku,kafin ta samu cikin farko,ta sauka lafiya danta namiji, ya ce,sunan mahaifinsa aliyu,suna kiran sa abba, kullum kara son saude ya ke yi,saboda biyayyanta da ladabi.a wannan lokacin mahaifinta ardo ajalinsa ya sauka,sun shiga tashin hankali,domin damuwarta ta tayar da hankalinsu sosai.tana nan a rugarsu har ta yi sati biyu da kyar ya lallabe ta suka dawo. Bayan iyayensu sun fita takaba,sai aka yi masu rabon gado,sauda ta samu shanu tara da raguna, saboda su biyu ne a gurin ardo,bashir ya ce,ta ba shi aronsu ya saida,zai fadada kasuwancinsa,in komai ya daidaita zai maido mata da shannunta ko kuma kudinsu. amma ta je ta yi shawara da yadikkonta,yadikko ta ce,ki ba shi,in kin san zai ba ki.sauda ta ce zai ba ni,ta ce,to ki ba shi,sauda ta tattara komai da ta mallaka ta damka ma mijinta. ALLAH ya sama abin albarka,inda kasuwanci ya bunkasa ya fadada ta hanyar bude manyan shagunan kayan masarufi, kayan abinci,shaddoji da zannuwa,ba a fi shekara ba ya soma fita irin su kwatano,togo da dai sauransu.kafin shekara biyu ya fara shiga china da dubai.ln ya sayo kaya sai ya raba ma 'yan kasuwa. daidai lokacin ne ta sake haihuwar danta na biyu,inda aka rada masa muktar.bayan ta yaye,shine suka je aikin hajji,shine ya biya masu ita da shi,da wata shekara ta zagayo kuma ya biya wa mahaifinsa. shekara daya ya bude kamfanin kansa da ake sarrafa robobi da katifu. shekarar ne ta sake haihuwar danta na uku,aka sa ma shi suna abdulkarim. lokacine ya soma nuna mata maitarsa ta son 'ya mace.ya ce,sauda ban taba fada miki ba tun cikin abba na ke son 'ya mace.ln kina da ciki koyaushe ina cikin addua,ta ce,mu ci gaba da adduar ALLAH ya bamu 'ya mace amin.sai in sa mata suna khadija,suna mahaifiya ta ce,
[01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (48)ALLAH ya bamu masu albarka.abdulkarim ya shiga shekaru uku,amma ba ta samu wani ciki ba,lokacin ne alhaji bashir ya hadu da hajiya binta a saudiyya, bazawara ce,mijinta ya mutu,ya bar mata dukiya, amma bata taba haihuwa ba.a girme zata girme sauda,a boye suka yi ta soyayya,don ya rasa yadda zai yi ya fada ma sauda,sam baya son bacin ranta.wani dare bayan sun gama muamalarsu ta ma'aurata,sai ya rike hannunta yana me sake jaddada mata cewa sonta daban yake a cikin zuciyarsa.matuka take jin dadi a duk lokacin da ya yi irin wadannan kalaman,ta ce,ai tuni ta san haka,kuma ta yarda da wannan.ta kuma fada masa cewa,ba fa sama da shi a rayuwarta,amma in an cire yadikkota.ya yi murmushi sannan ya ce,kin san aure mukaddari ne ga kowane bawa ko?ba tare data fahimta ba ta ce hakane. ya ce,zan kara aure,da farko ta dauka wasa ne, amma jin yadda ya kuke yana ta zayyana mata inda suka hadu,da inda maganar ta tsaya a halin yanzu,sai ta mike cikin fushi ta nufi dakinta.kishi kenan,kumallon mata,rigima sosai suka yi har ta bukaci kudinta.ba da bata lokaci ba ya maido mata,sannan ta dauki matakin kaurace masa,ya yi ta lallabarta amma ta ki.ta kai kudinta gidansu,inda za a sai mata filaye da shanu.wannan ne karo na farko da ya taba kai karanta gurin kannin mahaifinta.har gida baffa ya zo yayi mata fada da nasiha,ta ci kukanta ta hakura doke. An yi biki inda aka kawo amarya sabon gida daya gina masu a sabuwar unguwa.katon gida mai tsari,sai da zama ya soma yin nisa,a nan saudatu ta gane lallai mijinta ya fi son ta.don haka ta saki ranta ta zauna da su zuciya daya. cikin wannan zaman ne ta samu cikin MIMI,haihuwar MIMI ta zo masa cikin nasarori,randa aka haife ta, rannan ya bude kamfaninsa na fulawa a kano.da ya dawo ya ga 'ya mace kyakyawa,mai kama da abar son shi wato mahaifiyarta,yayi murna tamkar ya hadiye 'yar. Yayi walima gagaruma, inda aka rinka sanarwa a jarida,gidan rediyo da talabijin,sabon abu,saudatu ta ga sabon abu kamar na fari.
[01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (49)Wani abinda ya fi bata al'ajabi,tuni ya amshi renon jaririyar tamkar ba zai fita ba.ya na burge ta har ta soma jin haushi, domin baya kula da ita yanzu kamar da koyaushe uwarsa MIMI,wai shi sam baya son jin kukanta,duk lokacin da yaji kukanta,ya dinga fada kenan,ita kuma ga shegen kuka.sannu-sannu MIMI ta soma girma, sai ta shiga yi ma kowa kuya sai dady,lokacin zama take yi.amma in dady yana gida ko hajiya sauda bata amincewa ta dauke ta.hakanan zai iya barin kowa da komai ya lallasheta,in har tana kukan rigima.haka ta taso cikin mugun gata da rigima ga shagwaba,abin da ta ce,shi zaayi,su abba har suka soma jin haushinta,

1 Comments On CANJIN RAYUWA
avatar
mariya-6-8

9 months ago

Reply

In HAUSA language

Please Login or Register in order to submit comment