Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

haqqin Allah daga cikin dukiyarsu ba, Allah zaisa musu albarka, qila ma tafi ta da. Tace, rannan ma munji ka bada sadaka harda mu. Allah ya saka da alheri. Yace, Amin. Tare da miqewa. Ya koma dakin Mimi, "bani in kin rubuta. Ta miqa masa 'yar guntuwar takarda. Ya amsa, ya bude. Sai yaga ta rubuta cewa, duk abinda ya sauwaqa. Ya kalleta, zuciyarsa dajin dadin hakan da tayi. Yace nasan ba zan iya sai miki abinda kk so ba, amma zanyi iyakacin qoqarina. Ya juya ya fita. Kwana uku bayan nan, Ismail yazo Gidan da safe, misalin qarfe takwas, Mimi tana varcin safe. Ya gaisa da yaya sannan ya shiga dakinta. Bai mata dogon kallo ba, ya aje ledar hannunsa ya duba durowar gefen gadonta ya dauko takarda da biro ya rubuta cewa, ga kayan nan, in kin farka ya ke mai yin kyau a varci. Ya dora takardar a tafin hannunta. Sannan ya fice, yayi sallama da yaya ya wuce.
[25/09 9:28 am] Inna👬👫: Canjin rayuwa

6⃣5⃣Mimi kuwa tana farkawa taji da abu a hannunta, sai ta duba, taga abinda ya rubuta. Sai tayi murmushi tace, waton in idanuna biyu banida kyau, amma a varci inada kyau. Ta dauki ledar ta bude, wani tsadadden leshi ne mai kalar 6awon dorawa, sai Atamfa 'yar England sai takalma masu kyau da tsada. Ba anan tasha mamaki ba, saida taga irin man shafawarta da hodarta, sai kuma jan bakin da take shafawa. A fili tace, "ina Ismail yasan wadannan? Lallai zan tambaye shi inji. Ta ciro hijabai dogaye guda uku, sai niqabi guda daya. Tace, wai harda wannan yakeson in sa, ta6! Na dai saka hijabin in zanyi sallah. Ta kaima yaya ta gani. Suka tayata murna. Tace, in yazo anjima sai ince yakai dinki ko? Yaya tace, eh kam ya kai don inda na kai nasu Ummi macece, kuma ba wani qwarewa tayi ba. Dama su Ismail sun kafa kwamiti qarqashin jagorancin Mahmud inda za'a dauki sunayen marayun Unguwar, da na kusa dasu. Don haka sai suka sai kayan abinci dana sallah na yara, maza da mata. Sannan sukaje suka kai ziyara gidan yari, inda yayi musu wa'azi tare da basu taimako. Ana saura kwana biyu sallah, ya kawo masu Mimi cefane jibgi guda, da kuma kaji, sannan Washegari ranar jajibiri masu hali sukayi ta aiko masa da nama cikin manyan ledoji. Yaba Malam Aminu, harda Mahmud, sannan ya miqa cikin gidansu. Irin wadannan abubuwan suna burge Mimi.6⃣6⃣Hasana da usaina suna zaune suna kallon rufe tafsir din Ismail, Hasana tace, kai Malam yayi wlh! Na qosa daddy yayi mana izinin zuwa muga sis Mimi. Itama nasan ynxun ta hadu. Usaina tace, ai na dauki number din da ya bada wadda yace mutane suyi message kawai banda kira in sunada tambaya, so muyi masa text cewa, mune. Sainya fada mana gidansu, sai muje muga sis Mimi. Muryar Hajiya sauda ta katsesu da cewa, Allah yasa in samu labari. Wai ba ku nace ma tana lfy bane. Kuma fa na fada muku cewa, akwai matsala in munyi yunqurin zuwa gurinta zata sake guduwa. Karku damu tunda muna samun labarinta. Muyi ta Addu'a komai zai wuce. Hasana tace, Hajiya shi Malam a matsayinsa na Malami ba sai ya nemi lambarki ba kiji komai daga bakinsa? Usaina tace, ya fa san nan gidan meyasa ma ba zaizo ba? Hajiya sauda tace, Nice da laifi, don na tura masa saqo cewa, naji dalilan mahaifin Mimi, kuma na gamsu dashi. Don haka nima zaka jini shiru. Kaima kayi haquri karka sake nemana ko a waya. Ina mai sake baka amanarta. Lokaci yana zuwa da zamu nemeka da kanmu. Kunji tun daga lokacin ban sake nemanshi ba, shima bai sake ji daga gareni ba. Hasana tace, to sai zuwa yaushe ne sannan za'aje gurinta? Usaina tace, ke kam kamar bada hausa Hajiya tayi magana ba? Hajiya sauda tace, zaku soma musunku ko? To ni nayi nan! Ta nufi kicin. Ranar sallah, Ismail ya matsawa Mimi wai ta shirya suje masallaci. Da ma tun ranar jajibiri yake fada mata lokacin da yazo ya kawo mata dinkinta. Tace, ba zataje ba, qila 'yan gidansu zasuje. Yace, ba ga niqabinki ba, sai ki 6oye fuskarki, dama amfaninsa kenan. Zama haka ba ya yiwuwa Mimi, dole sai da dan fita ana dan motsa jiki. Balle sallar idi wadda daga shekara sai shekara. Ba tada za6i dole ta shirya cikin leshinta, yayi mata kyau matuqa, tayi alwalla, sannan ta shafa hodarta da jan baki, ta saka hijabin da niqabi. Suka fito tace, yiwa yaya sallama. Ummi ma da take ta rabon abinci gidajen maqota tayi kyau cikin kayan sallarta. Su kuwa su saddam dama sun tafi da abbansu a mashin.6⃣7⃣Ismail yayi kyau cikin wani tsadadden yadi, mai ruwan madara, malum-malum ce ta dauki aiki. Hularsa da takalminsa sun dace da kayansa. Yayi kyau matuqa. Ita kanta Mimi lokacin da ya shigo Gidan, sai da Zuciyarta ta buga. Daga lokacin da Ismail ya soma tafsir zuwa ranar sallah, yayi abokai kala-kala, kowa yanason ace suna hulda, masu da kuma talakawa. Daga cikinsu ne wani yazo har gida ya daukeshi, shine yace, su biyo ya dauki matarsa. Mutane sukanyi mamakin ganin Ismail a wani guri daban. Duk wanda ya tambayeshi yakan ce masa, shi ba lazauni bane. Matarsa kuma ba tada isasshiyar lfy, shiyasa ya barta gidan yayarsa. Bayan sun dawo sallah ne Ismail yaci abinci anan gidan, sannan ya miqe zai fita. Sai Mimi taji sam batason ya fita. Amma ba tada ikon hanashi, wani sonshi ne taji a cikin Zuciyarta. Tana kallonshi ya fice. Bayan sallah da kwana tara Ismail suka shirya nasu-yanasu sai makaranta. A ranar ne Mimi taji inama itace, Rabi'a. Ranar ce, tayi kuka sosai, wanda batasan ko na menene ba. Ismail yayi zaton ko tana yi ne don bai saketa ba. Sai yace, karki damu khadija, shekara kamar kwana ce, in na dawo komai zaizo qarshe, kinji? Bayan tafiyarsu tayi ta dana sanin qin yarda da tayi ya sai mata waya. Amma tace, bataso. A fili tace, kashh! Menene ma zai sa ince ban son waya? Tsaki taja, tare dayin tagumi. Ynxun kam ta gama fahimtar cewa, Zuciyarta tana matuqar son Ismail, sai dai tsoronta daya shine, shi baya sonta. In ba zata manta ba ya sha fadin cewa, shi mace mai kyau yakeso ya aura. Tuna hakan sai taji jikinta ya mutu. Ta kalli kudin daya bata kafin ya tafi. A fili tace, dole ne in nemi wanda zai siyomin waya ko don in hada hulda dashi. Tsaki taja, a ranta tace, ta yarda jama'a rahama ne, inda tana hulda dasu da ynxun ta samu mai siyo mata. Dakin yaya Amina taje, tace yaya inason a siyomin waya ne. Yaya Amina tasha mamaki, "ke kuwa meya hanaki yarda Ismail ya siya miki? Don nasan babba zai sai miki. Tace, lokacin banason wayarne, amma inasonta ko don inji Rediyo. Amma fa karki fadama kawun su Ummi. Tace, shikenan ki kawo sai qanin abban su saddam ya siyo miki. Ta dauko dubu bakwai, cikin dubu ashirin din da Ismail ya bata kafin ya tafi.
[25/09 9:30 am] Inna👬👫: Canjin rayuwa

6⃣8⃣Zainabu kuwa tunda taga Ismail a TV, hankalinta yayi matuqar tashi. A fili tace, Ismail yafi qarfi na ynxun. Ta saka kukan takaici, tayi har ta gode ma Allah. Innarta cikin tsantan nadama tace, zainabu kiyi haquri, qila zaku hadu ne ko anan gaba. Tunda yana sonki, na san ma zai dawo gareki. Zainabu dai bata tanka ba. Innar ce da kanta ta fita neman labarin Ismail, har gidan mahaifinsa gurin su fatu. Anan ne fatu take fada mata cewa, Ismail yana madina garin manzo, dama zuwa yayi don can yake karatu. Ta qara da cewa, Ismail fa ya wuce da tunaninki, mu kanmu mun dangana bare ke. Dole mu dangana ko don alherin da yakeyi mana. Azumin nan shine geron kununmu, shine waken qosanmu. Da sallah tazo kuwa, zo kiyi kallon hidimar, dinkunanmu da yara, ke har cefanen sallah. Innar zainabu tace nima ai nadamar ta kawoni, ban san yaya zanyi da zainabu ba, taqi sauraron kowa. Fatu tace, dama ta saurari kowa, sbd Ismail da ya yafe tunaninta. jiki babu qarfi ta koma Gida.6⃣9⃣Ya zuwa wannan lokacin, rikicin su Na'ima ya kai su ga zuwa kotu, inda shi Abbas ke qarar Na'ima, akan ta bashi dansa. Ita kuma Na'ima tace, ba zata bada shi ba. Duka 6angaren guda biyu sun dauki lauyoyi. Inda ake fafatawa tare da dage zaman sauraron shari'ar. Nadama kuwa, Momy Nafisa tayi akan auren nan yafi cikin buhu. Ita kuwa Na'ima nata ganin alhakin Mimi ne. Duk lokacin da tace haka, sai momy Nafisa tace, ki daina wannan maganar, ai komai muqaddari ne. Na'ima tace, qaddarar da mutum yake qadddara ma kansa ba. Da mun bar Mimi ta aure shi, na tabbata hakan ba zai faru ba. Haka Allah yake ikonsa, sau da yawa sai mutum yayi ha'inci, sai kuma kaga ya dawo yana nadama. Kukan Na'ima da yawa, ita ba a karatunba, ita ba ga auren ba. Ynxun ne take burin in ya saketa, ta koma makaranta. Shi kuma yace, tana bashi dansa zai sake ta. Lauyoyinta suna ta zuba hujjojinsu kan cewa, dole ne ya saketa tare kuma da bar mata danta don itace tafi dacewa ta kula dashi. Su ma nasa lauyoyin hujjojinsu suke bajewa akan cewa shine yafi dacewa ya riqe dansa a matsayin sa na uba. Nidai nace, ku kuka sani, mu dai 'yan kallo ne.
Lokacin da aka kawo wa Mimi wayarta, ta hada ta tasa aka sai mata layi ta saka aciki. Number Ismail kawai ta dauka a cikin wayar yaya Amina. Wtsapp Mimi ta bude, cikin sa'a kuwa da lambar yakeyi, hotonsa ne ma yasa a D.P dinsa,yana sanye da farar jallabiya. A saudiyya ya dauki hoton daga gani. Wannan lokacin ma yana online. Mimi tayi murmushi sannan tayi masa sallama. Sam bai kula sallamarta ba, duk da tayi ta kusan sau goma. Tace, nasan yaya zanyi. Ta sauka daga kan wtsapp din ta tura masa message, da cewa. Dama haka malaman suke basa son sauraron al'ummarsu, balle su basu fatawa akan matsalolinsu? To, ka sani bin Abdurrahaman, in har na mutu ban samu mafita a matsalar da nake ciki ba, to ka sani har da kai zunubin, domin na kira baka daga ba. Kuma nayi maka magana ta wtsapp baka kula ni ba. To ynxun ga message dina nan. Tana turawa tayi murmushi, sai ta kashe wayar ta aje.7⃣0⃣Bata sake kunnawa ba sai bayan kwana uku. Tana kunnawa saqonni guda uku suka shigo, data duba daya na MTN, biyu na Ismail dama da Malam tayi saving. Murmushi tayi, sannan ta bude saqon. Gajerrn saqo ne, kawai cewa yayi, ki fadi matsalarki. 'yar dariya tayi don ganin cewa zatayi wasa da hankalinsa. Ta hau wtsapp nan ma saqon iri daya ne. Ta soma tunanin me zata rubuta masa, wanda zaija hankalinsa, ya saurareta? Sai ta soma rubuta cewa, Malam Allah ya sani tunda nake ban ta6a ji ko ganin matsala irin tawa ba, ko da a film ko kuma labarin qirqira. Sai ta tura masa. Daga nan sai ta kashe wayar. Washegari data hau wtsapp sai taga yace, ki fadi matsalarki kai tsaye ba tare da kin gutsutsura batun ba. Ke nake sauraro. Dariya tayi, sosai sannan ta tura masa cewa, roqo na da kai, shine in kaji wannan matsalar tawa ka taimakamin, kuma ko da kisan kai ne ya kasance hukunci na to zan dauka. Ta tura masa. Haka tayi ta tura masa wadannan saqonni na wasa da hankali, tun yana nuna mata yanason jin ko wace matsala ce, ta daina jin tsoronsa ta fada masa, har ya gaji yayi banza da ita. Tare da haka, in ya kira yaya Amina yakance, a bashi Mimi su gaisa. Cikin ja masa ajin data saba yi take amsa su gaisa. Inya tambayi matsala, sai tace babu. Kwancitashi su Ismail sun kammala karatu na digiri, tare da sakamako mai kyau. Hukumar qasar ta tuntu6i daliban da aka yaye a wannan shekarar, ko akwai wanda yakeson yin aiki tare da su bisa ga albashi mai tsoka? Su Ismail kam cewa sukayi sunfi son suzo su amfanar da ilimin da suka samo ga al'ummar qasarsu. Sannan Ismail yanason samun nasa iyalin, ya gaji haka.
Mimi bata ta6a yin murnar dawowar Ismail ba kamar wannan karon. Domin gsky tayi kewarsa, tanason ganinsa, sosai matuqa. Wani abu da ya sake burge ta shine tasha gwada Ismail da sim kala-kala, don taga ko yana hulda da mata, amma sai ta sameshi a natsattse wanda bashi da lokacin shashanci. Sun iso gida cike da murna da doki. saidai Ismail ya baro madina cike da burin komawa don samun digirinsa na biyu, in komai ya tafi masa daidai. Dakinsa ya sauka, wannan karon zai kama masauki amma sai ya saita lamuransa.7⃣1⃣Shi mahmud bashi da wannan matsalar ta gurin zama, domin suna da mazauninsu, daya daga cikin gidajen mahaifinsa. Sunyi isowar dare ne wannan dawowar. Kusan qarfe biyun dare suka shigo katsina. Kai tsaye gidansu ya wuce, ya sauna da kayansa. Su kuma su Mahmud da Rabi'a da dansu mus'ab yayi wayo sosai, suka wuce nasu gidan. Ismail ya buga gidan. Yayyinsa maza guda biyu sukazo sun a tambayar ko wanene? Ismail yace nine Ismail. Da sukazo suka buds mass, suna yi masa sannu da zuwa. Sun yi sallama Sai da safe, suka nufi ciki. Shikam bai kwanta back Sai daya share dakin. Want Abu daya bawa Ismail mamaki, bayan yay sallar asubahi ya dawo, ya kwanta don ya huta, bai yi niyyar fita ba don yana tsammanin babu Wanda yasan ya dawo, gurin qarfe goma yaji sallama a qofarsa. Barcin nasa sama-sama ne. Don haka Sai ya tashi ya suka jallabiyarsa ya fito, ya baqon nasa, Sam bai sanshi ba, amma ya miqa masa hannu, suka gaisa. Mutumin ya Ciro wasu takardu ya miqa masa, game saqo daga wani bawan Allah, yace in Baka tun kusan wata uku da suka wuce. Ismail ya kalleshi cikin rashin fahimta, saqon menene? Yace mai gidana be, inayi masa aikin sama. Ni kafintan same ne. Duk wani aikin gidajensa ni keyi masa daya shafi Sana. To shine ya tambayeni ko ma sanka? Nace unguwarmu daya. Ta yiwu Baka sanni ba, ina can bayan mayo be, gidan malam kadi. Ismail ya kalleshi. Gidan su hashimu? Baqon yace, yauwa, to ni wansu hashimu be. Zakkar gida be, ko ince kyautar gida yace in Baka. Wadannan takardun gidan be. A can unguwar GRA be gidan take. in ka shirya Sai mine in Nina mama.
[25/09 3:10 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa

7⃣2⃣Cikin mamaki, Ismael yace a ina wannan mai gidan naka yake, kuma yaya sunansa? Baqo yace nidai sunana Nasiru amma shi mai gidana ya hana ni in fadi sunansa ko unguwarsa. Yace, shi yayi ne don Allah, kuma malam ya sakashi a cikin addu'ar Allah ya biya masa buqatunsa na alheri. Ismail yace jirani ina zuwa. Ya koma daki ya canza kaya, ya fito yace, zo muje gurin malam. Sun samu malam Aminu, inda dan aike yayi masa bayanin kimai. Bada 6ata lokaci ba, suka nufi gidan, harda mahmud, wanda ismail yayi masa waya, shima yazo ya samesu. Sun samu mai gadin gidan ya bude musu suka shiga. Mai gadi yazo ya gaishesu tare da tambayar su ko wanene mai gidan cikinsu? Mahmud yace, wa yasa ka gadin gidan? Yace 'yalla6ai ne. Yace min duk randa wanda yaba gidan yazo, shi aikinsa ya qare. Mahmud yace, to ya sunan shi 'yalla6ai din? Tsoho maigadi yace, ya hanani in fadi sunansa.
Sun zaga gidan qato ne sosai. Ginin na gefe hawa daya. Mai gadin ne yabasu makullan ciki tare da nuna musu ko ina na gidan. Shikam ismail filin gidan ne yafi burgeshi, domin har ya hango yadda zaiyi makaranta a gurin, harda masallaci. Take ya sanar da su malam Aminu sha'awarsa da gurin, suka ce tabbas bakan yayi. Sun yi bankwana da maigadi bayan ismail ya bashi dan abinda ke hannunsa tare da bashi baquri kan cewa bai fito da kudi ba. Suka fito suka kulle gidan suka tafi da makulli. Babu abinda gidan ke buqata saidai kayan da za'a zuba na amfani. Sun koma gida, inda Ismail ya kawo dubu biyar tare da sabbin jallabiyu a cikin kayansa yaba dan aike tare da bashi haquri, kan cewa dawowarsa kenan daga karatu bashida kudi. shi kuwa dan aike godia yayi, tare da cewa, ni ai babu abinda yafi faranta mun rai kamar sada ka da saqonka da nayi. Domin tun shekaran jiya yake cemin cikin satinnan zaku dawo. Ismail yace, wato harma ya san lokacin da zan dawo. Dan aike yace gsky ya sanin kenan. Sukayi bankwana, ismail ya rakashi tare da yi masa godiya mai yawa. Ko daya dawo daki, yayi iyakacin qoqarinsa don ya gane ko wanene. Amma hakan yaci tura. Sai kurum yayi masa addu'ar Allah ya cika masa burinsa, duniya da lahira.
7⃣3⃣Mimi suna da labarin dawowar ismail amma basu ganshi ba. Mimi bataji dadin hakan ba, domin sai taga kamar bai damu da ita ba. Sai washe gari bayan la'asar, yinin ranar Mimi tayishi ne cikin qunci da rashin walwala. Har yaya ta nemi dalili, amma sai Mimi tace, kanta keyi mata ciwo. Tana zaune a tsakar dakinta tana yanke qumba, kanta babu dankwali ta kama gashinta a tsakiya, kamar yadda ta saba tun tana 'yar gayunta, muryarsa ta jiyo yayi sallama, sai sowar yara ta jiyo suna yi masa sannu da zuwa. kamar ta tashi ta fita sai kuma ta fasa, ta kalli jikinta, riga da wando ne wadanda shine ya sai mata su. Taje madubi ta kalli fuskarta. Sai ta samu kanta da zazzaga hoda a tafin hannunta ta hure, sannan ta shafa ta hau tsakiyar gadonta ta zauna, ta kunna TV. Catoon sukeyi. Kusan minti ashirin da tara, sannan ya kalli dakinta, ita wannan bata nan ne? Yaya tace, tananan. Dazun dai tayi fama da ciwon kai, amma yayi sauqi. Da sallama ya shigo. Ta dago tamkar lokacin taji shigowarsa. Qwarjinin dake kan fuskarsa ya doketa, tayi saurin sunkuyar da kai, sannu da zuwa. Yace, sannunki, in zauna bakin gado? Ta dago ta dubeshi, yaune zaka nemi izinina? Yayi murmushi, ai na qara wayau ne ynxun. Da kinsan yaro ne. Tayi dariya, to ka zauna. Ya tsura mata ido, "kinci naman hawainiya ne? Yayi tambayar cikin tsokana. Ta zaro ido, meka gani? Duk lokacin da na tafi na dawo, sai inga kin canza kala. Gabanta ga fadi, tsoronta kar ya kusheta, ta kalleshi, duk nayi muni ko? Yayi dan murmushi, nidai ban fada ba. Tace to fadamin me nayi? Da ya fahimci tanason jin ta bakinsa game da yabon da yayi niyyar yi mata, sai ya canza da cewa, wai don Allah meyasa in na dawo baki doki na? Tayi masa kallon gefen ido, injiwa? Yace injini mana. In ana dokin mutum ai anayi masa tarba ta musamman da girke-girke. Ta ta6a baki, ai muma bakayi dokin ganinmu ba. Sai fa da kayi kwanaki, mutane suka gama ganinka, sannan kake zuwa mana nan. Yayi murmushi, amma zuwana na farko nan na fara sauka. Mimi tace, wannan ne kawai. Ta sake maido da wancan zancen. Baka fa bani a msa ba. Tame? Ya fada tare da kanne mata idonsa daya. Canzawar daka ce inayi. Shine nace muni na qara ko? Yayi 'yar dariya nidai bance ba. Ki kawomin ruwa mai sanyi insha, ya sake kauda zancen.
7⃣4⃣Ta sauka sannan ta dauki qaramin hijabi tasa. Yasan sbd kayan jikinta ne don sun kama fa tsam, duk motsin da tayi jikinta yana rawa. A zuciyarsa yace, lallai! Yau Mimi ce da rufe tsiraici? A fili yace Albmdlh. Ta kawo masa ruwa da kofi, ya kalli goran ruwan, lallai 'yan gayu, swan kuke sha? Tayi masa hararar wasa, wa zai bamu ruwan swan? Na fanfo ne muke sawa yayi sanyi. Ya tsiyaya ya sha. Cikin son jin me yayi niyyar cewa yaqi fada, tace ai kaima ka canza. Ya dubeta don ya riga ya dago ta. Yace, eh nima nasan na canza, na qara kyau sosai haka? Ta harareshi, ka cika son kanka da yawa. Yace inba gaky na fada ba sanar dani kawai. Tayi shiru. Yace shiru yana nufin eh ne. Ni nasan inada kyau. Ta 6ata rai, kai kyau ya dama. Ni ynxu nafison kyan hali. da ne nake kallon kyau wata tsiya. Yayi dariya shima inada shi, don naji mutane suna fada. Ranta ya sake 6aci. Da gske batasan shi zolayarta yake ba tace, ka cika wasa kanka. Kuma ance duk wanda yace shine, to ba shi bane. Yace nidai nine ismail bin Abdurrahaman. A ranta tace, karma yaga cewa na wani damu dashi ne ma, bari in masa zancen rabuwarmu. Tace gashi dai karatu ya qare, yaushe zamu warware maganarmu? Gabansa ya fadi. Nasa zaton ta dangana da wannan maganar. Maimakon yabata amsa, sai yace, ni na manta ma munyi gida fa. Ya miqe bari in sanar da yaya Amina. Itama ta miqe ta biyoshi. Nan ya labarta musu komai. Suka yi murna sosai. Yaya tace, kuma takardun da sunanka da komai? Yace cikakken sunana kuwa. Tace ko wanene wannan, Allah ya saka masa da alheri. Yace Ameen, gurina da akwai wasu kudi, zan gani ko zasu sai mana kayan gado dana girki. Ba sune dai akafi buqata ba? Yaya tace sune mana. In ma na gado ko katifa ce zatayi muku. Kayan kicin shine yafi zama dole. Yace hakane mu shirya gobe zanzo in kaiku gidan.
Haka kuwa washegari yazo ya kwashesu. Gidan ya burgesu sosai. Mimi ta shiga fargaba, tana tambayar kanta wa zaisa a gidan? Bata san lokacin da tace to kawunsu ummi yaushe zaka dawo nan gidan? Ya kalli cikin idonta, ya karanci wani abu. Don haka sai yace, bari mu koma gida, zaki bani shawara ko? Ta daga gira, alamun eh. Yayi murmushi.
[26/09 8:41 am] Inna👬👫: Canjin rayuwa

7⃣5⃣Ismail tunda ya dawo bai zauna ba, abubuwa zunyi masa yawa. Sun raba takardun neman aiki a jami'o'i kamar su A.B.U da B.U.K, har Abuja. Sannan qungiyarsu ta da'awa, suna ta gudanar da aikace-aikace, musamman na gidan marayun da suke ginawa. Sannan ga gayyata da yake samu gidajen rediyo, da talabijin da gabatar da filaye na addini irinsu tambayoyin addinin musulunci, Filin fatawa, da dai sauransu. Haka sauran jihohi irinsu kaduna, kano, sakoto, suna gayyatarsa don yin majalisi dashi. Hakan yasa ismail ya zama kullum yi nan, yi can. Ga shi har ynxun bai daina zama gaban malamai ba don neman qarin ilimi. Daukaka ta Allah, lokaci qanqani sunansa ya karade jihohin Arewa. Wannan yasa mahmud ya matsa masa. Wai ya tare a gidansa. Yaso su tare da mahmud din tunda sama ne da qasa, amma sai mahmud yace, in har ya sake ya tare a gidan ismail din, ba zai maida hankali a nasa ginin ba, wanda yayi nisa da farawa. Ranar wata lahadi misalin qarfe takwas da wani abu na dare, ismail ya shigo gurin su mimi, lokacin babu wutar NEPA ta kwanta a tsakar daki akan tabarma, tana dannan wayarta. Sallamarsa ta jiyo yasa ta kashe tocilar wayar, sannan ta kashe ta gaba daya, ta tura a qasan gado. Lokacin daya iso dakin da sallama, ta amsa. Yace farko dana shigo, sai naga kamar dakinnan da haske. Tace, idonka ne yaga haka. Ya ciro qaramar wayarsa daga aljihu, ya haska dakin. Kafin ya zauna yace, me kuke dashi na ci? Tace shinkafa mukayi da wake, sai mai da yaji. Jiya ne yaya tace, muyi alala, qila kozo, tunda ka kwana biyu baka zo ba. Amma sai kaqi zuwa.
Yace ba zaki gane bane khadija. In a lissafa maki lamurran dake gabana, zaki sha mamaki. Karku damu da yin abinci dani. In nazo kamar haka in na samu zanci. Ban cika son cin yaji ba, shirya ki rakani

1 Comments On CANJIN RAYUWA
avatar
mariya-6-8

9 months ago

Reply

In HAUSA language

Please Login or Register in order to submit comment