Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kai,
alamun eh. Cikin yace to shikenan vari inzo in nemo
miki magani. Ko ke fa? Ynxun zaki san kinyi aure.
Amma zan vari yau ki huta tunda baki jin dadi,
amma gobe da safe zanzo ko? Tace eh, yana fita ta
nufi ban daki ta dinga kakarin amai, don gsky shi
kansa wari kawai yake yi mata.
Washe gari yana shigowa, haka tayi qoqarin yi masa
duk abinda yake so, tare da maida masa martanin
duk abinda yayi mata. Tasha wahala matuqa, amma
haka ta jure ta nuna masa tana tare dashi, yaji dadi
matuq a. Dazai fita ya kawo dubu biyar ya bata. Ya ce
ki jirani da daddare, gabanta ya fadi, tace a ranta na
shiga uku, a fili tace ai yau ba’a dakina kk ba, yace ina
ruwana da wani inda nake, karki damu, abinda kawai
na sani dukkanku matana ne, kuma zan shiga gurin
duk wacce raina ya biyamin ko kina da ja?
Cikin sauri tace, A’a haka ya fita ya barta tana
mamaki, tare da tambayar kanta wai daman haka
auren yake, ayi ta abu sai kace cin tuwo, kuma ba
gajiya? Ita kam ta gaji wlh. Ta dinga juya kudin a
hannunta, sannan ta bude akwati nta ta saka, tana
yin wanka, sai kuma zazza6i ya rufe ta, ta qudundu
ne akan gado cikin bargo. Bata san tsawon lokacin
data dauka ba akan gadon nata. Can kamar daga
sama sai taji muryar su innarta suna salalla ma.
Da sauri ta tashi suka shigo, itace da aminiyarta inna
yelwa. Suka iso bakin gadon suka zauna. Inna tace
lafiya na ganki cikin bargo haka? Zainabu tace banida
lfy ne inna, tace me kuma ke damunki? Ta sunkuyar
dakai, tace wai uwar gdnsa ce tace ciki ne dani, shi
kuma gashi baya son haihuwa, inna tace to ynxun
daya ji kina da cikin me yace?

Zainabu tace, bai sani ba. Uwar gdn tace, kar in fada
masa, shine nace masa shawara ce ke damuna
kawai, kuma tun ina gd take damuna, shine ya siyo
min magani. Inna yalwa ta ce, anya kuwa gsky
wannan matar ta fada miki? Ance kar ki sake ki
saurari maganar kishiya. Har wata soyayya ce zaki
samu a gurin kishiya? Zainabu tace Allah kam tana
sona da gske.
Don tana fadamin gsky, kuma in tabani shawara in
nabi ina ganin daidanta. Jiya ma saida ta matsa kan
cewa in na saki jiki dashi zan samu kudi, wai anan ne
zan samu nayi siyayyar kayan Jariri. Shine nadan
daure na saki jiki dashi, shine ma har ya bani dubu
biyar. Kuma dama ko yaushe tana fadamin cewa inyi
hakan, don dai naqi yi ne.
Inna tace kedai akwai sakarya, dama qin sakin jiki
kkyi dashi don ubanki? Shiyasa ni kaina ya rage bani
abinda yake bani, don jiya na aiko ya bani dubu
goma, amma sai ga dari biyar, yadda kk san in yaga
ta don haushi, amma na fasa, to tashi ki dauko min
dubu biyar din, Zainabu ta turo baki, to zan tara ne
fa inna, don fa an fadamun har in ya gano cikinnan,
bazai bani komai ba, kuma kayan Jariri ma fa nice
zan nema.
Inna yalwa tace, jaririn banza, ke kk ta Jariri, waya ce
miki za’a barshi? Yanxun nan zamu je a hado
maganin da zaibi makwarara, ko yaya kk gani
Aminiyata?
Ta kai qarshen zancen da kallon innar Zainabu. Inna
tace tace, yadda kk ce dinnan haka za’ayi. Zainabu ta
soma kuka, don Allah inna kar ku bani maganin
zabar da ciki, ance fa wata matarsa ta rasu
sakamakon shan maganin zubar da ciki. Inna yalwa
tace to shikenan don ta mutu sai aka fada miki cewa
kema .mutuwar zakiyi ko? Inna taja tsaki, bar
sakarya! Duk abinki cikinnan baza’a barshi ba.
Inna yalwa tace, saurara kiji Zainabu. In an zabar da
cikin, sai kinfi jin dadin kar6ar kudin a gurinsa. Duk
lokacin daya zo gurinki, ki tarairaye shi. Zainabu tace
shifa ko wane lokaci, sai yace zai shigo dakina, koda
ba anan yake ba, inna yalwa tace saurare ni dakyau,
in kullum zaizo gurinki, karki sake kice masa NO, inji
ku ‘yan boko, kuma kar ki nuna kin gajiya. Sannan
zamuje a hado miki kayan da’a a gurin ‘yar jibiya sbd
aqara samun kansa.
Kinga ya qara sakin miki baki n aljihu. Inna tace
shikenan sai a shigar mata zubin adashi, ai kya san
abinda kk tara ko? Ta kalli inna yalwa. Tace qwarai
kuwa. Inna tace to yaya batun zuwa gdn
malaminnan yalwa? Inna yalwa tace, abar batun
zuwa gidan malamin nan, tunda shi ga inda yasa
gaba, sai mubishi tana gurin. Tayi ta dirkar maganin

da’a masu qarfi. Inna tace shikenan hakan yayi, inna
ta miqe, ynxun dai tashi muje yalwa, zamu dawo
zuwa Anjima. Zainabu ranta 6ace tace anjima kuma?
Nidai zaku fa sa ace iyaye na suna ta sintiri a
gidannan, ayi min gori. suka ce a daura miki goruba!
Anjiman nan zamu zo. Ai da zafi-zafi akan bugi qarfe.
Don haushi ko sallama bata yi musu ba, ta sake
qudundunewa akan gado tana ta kuka.
Ismail kusan kusan tare suka shigo da likitan, har
lokacin daddyn ta take kira cikin sarqarqiyar murya
wadda take a galabaice. Likitan ya isa gaban gadon ya
dafa goshinta, sannu khadija ? Bude idanun ki in
gani. Ta soma yunqurin budewa, dishi-dishi take
gani. Yace kin sanni? Ta sake lumshe idanu. Ya
waiwaya ya kalli Ismai l sannan ya yafito shi da
hannu, Ismail ya matso. Likitan yace yi mata
magana. Ismail yace bude idanunki ki ganni. Yakai
hannu ya dafa goshinta. A wahalce ta bude idon ta
numfashin ta sama sama, tace malam ina khalil di
na? Yace yana nan yana varci acan dakin maza. Bai
mutu ba? Yana samun sauqi, sannu kinji. Ta daga
idanunta a wahalce, ta kalleshi, malam ka kaini gurin
daddy na zan mutu ne kaji? Zan mutu.
Hankalin Ismail yayi mugun tashi. Ya kama hannun
likitan. Don Allah ka bata magani. Wlh Yarinyar nan
amana ce a gurina likita. Likitan ya kama hannun
Ismail zuwa bakin qofa, yace karka damu, tambaya
daya zan maka, Ismail yace to. Sunan data ambata
wanene? Ismail yace daddy mahaifinta ne, shi kuma
khalil .shine wanda yasu, ina nufin wanda sukayi
hadari tare. Likitan yace Alhmdlh.
Ynxun ina ganin matsalarmu wannan karayar ce. Sai
dai kafin zamu qara mata jini, don ta zubar da jini
sosai, daga nan sai mu dora ta. Ismail yace babu
matsalar jini, a gwada nawa, in zan iya bata, sai asa
mata. Likita yace babu matsala, da safe zamu gwada
jinin naka. In zaiyi sai mu ta ce asa mata. Sannan
maganar dori, nayi maka batun mai dori, ban nemi
shawararka ba, ko kuna son na gd, Ismail yace to ni
dai likita, wanne kaga yafi? Domin wannan Yarinyar
amana ce a gurina.
Likitan ya dafa kafadarsa, kar ka samu damuwa. Mu
dai a gurin mu wannan likitan, kamar yadda na fada
maka zaizo ne daga kano, kuma yana yin dori sosai
anan asibitin, kuma bamu ta6a ganin wata matsala
ba. Amma kayi shawara da ‘yan uwanka.
Yace to shikenan zuwa da safe duk yadda muka yi
zaka ji. Likitan yace, babu komai. Ni zan tafi dama
na jira ne sbd inga farkawarta. Ismail yace, to yanxu
ba zan iya bata wani abu ba ko da tea ne? Likitan
yace kai ka damu, zaka dai iya bata ruwa ne in ta
buqata. Nurse zasu zo su saka mata ruwa tare da yi

mata allurai, domin ta samu varci da kuma sauqin
radadin. Ismail yace, nagode likita, saida safe. Ya
girgiza kafadar Ismail, kar ka damu. Insha Allahu zata
samu sauqi, ‘yar amanarka. Akwai likitan dare ma,
wanda ina zaton ma yazo. Inda wata matsala sai ka
fadawa nurses, zasuje su kira likitan.
Ismail yace nagode sosai likita. Bayan fitar likitan ne
Ismael ya sake dawowa ya tsaya akan mimi. Yana
matu qar tausaya mata. Ji yake kamar ya kar6ar
mata ciwon. Nunfashin ta dai-dai yake fita. Yasoma
karanta addu’oi don nema mat a sauqi daga
mahaliccinta. Bada jimawa ba Nurses guda biyu suka
shigo suka sa mata ruwa tare da yi mata allurai. Suka
ce, ka lura ko da cikin dare, kar ka bari ya goce. Yace
musu, to suna fita ya zauna yana riqe da tattausan
hannunta, wanda shine mai lafiyar, yana ta kallon
fuskarta tare da tuno yadda abubuwan suke ta
faruwa tamkar cikin mafarki.
Alamun tayi varci yasa shi ajiye mata hannun a gurin
da ba zata gotar ba. Sannan ya tashi ya koma kan
dayan gadon ya kwanta yana fuskantar ta, har ynxun
yana ci gaba da kallon abubuwan kamar almara ko
kuma mafarki. Ina mabya farka ya ganshi a dakinsa
na zauren su, ace ma shi baisan wata mimi ba.
Amma da ya dan ciji yatsansa, sai ya tabbatar cewa
ba mafarki yake yi ba, domin yaji zafi. Amma ya
tattara komai ya barma Allah, da haka varci 6arawo
yake ta fisgarsa sama-sama.
Cikin dare ne yaji shigowar nurses din, sunzo ne su
sake duba ta, yayi musu sannunsu da aiki, suka amsa
suka tambaye shi ko kwai wata matsala? Yace musu
babu komai suka ce to. Suna fita ya shiga bandaki
yayo alwala yazo ya soma yin sallah, yana fada ma
Allah matsalolinsa.
Washe gari misalin qarfe bakwai na safe yana zaune
kan sallaya yana tilawar qur’ani, sai aka turo qofar
tare da yin sallama, Mahmud ne dauke da flask din
shayi a hannunsa. Bayan sun gaisa ya tambayi mai
jiki, Ismail yace, da sauqi, gata nan bata ma farka ba,
tun jiya data farka suka yi mata allura, Mahmud
yace, ta farka babu wata matsala ko? Ismail yace,
babu matsala, don ta gane ni, tana ta kuma kiran
daddyn ta da kuma khalil dinta. Ban san yaya zanyi
mata ba. Da nace mata yaron yana raye. Kasan ni na
tsani inyi qarya, amma hakanan na fada mata sbd
kar ta qara tada hankalinta, Mahmud yace, to yaya
za’ayi dama ka fada mata gsky? Gara dai in ta samu
sauqi, sai a fada mata. Ismail yace, tunani na kenan.
Sannan kuma likita ya tambaye ni wai anan za’ayi
mata dori, ko kuma a gida,wai inyi shawara, shine
nace bari dai kazo inji yadda za muyi. Mahmud yace

gara dai ayi mata anan asibitin, kasan dalili? Ismail
yace a’a, Mahmud yace, kasan masu kudinnan aje ayi
mata na gida, Allah ya kyauta ba’a fata, a samu
matsala suce an barta a gd babu kula. Ismail yace
hakane, duk nayi wannan tunanin.
Sannan ga matsalar gurin zama. Ina zan kaita in an
dora ta? Ni mai daki daya a zaure, Mahmud yace,
hakane koma dai yaya ne, mu roqi Allah yasa ayi a
sa’a. Baki suka hada gurin cewa Ameen. Ismail ya
kalli flask din yace, harda ruwan zafi kazo min? yace
eh, inna ce tace in taho maka dashi, ynxun ma zanje
in siyo maka bread, sbd lokacin dana fito duk masu
shagunan basu fito ba. Ismail yace, ka bari sai kamar
qarfe takwas, don ynxun zaiyi wuya ka same su.
Mahmud yace, to shikenan dama kai nake tunani,
qila ma jiya ba kaci komai ba. Ismail yace saida yaya
Amina suka zo, sannan da suka zo da abinci nace nafi
son, ruwan zafi, shine mijinta ya kawo min bayan
sun koma. Mahmud zai sake magana kenan, sai yaga
kamar mimi tana motsi. Da sauri yace Ismail kamar
tana motsi.
Cikin azama suka isa gaban gadon, Ismail yace mimi
kin tashi? Ta lumshe idanunta, sannan ta sake
budesu ta kallesu. Alamu sun nuna yau jikin da
sauqi, Numfashinta ya daidaita. Hawaye suka soma
zuba daga idanunta, Mahmud yace sannu ya jiki?
Bata amsa ba, sai dai hawayen ne ka bin gefen
kumatunta. Ismail ya dora hannunsa akan nata, cikin
damuwa yace sannu kinji? Zaki sha ruwa? Taja wani
numfashi, cikin muryar marasa lfy tace, ni daddy na
zaka kai ni, ban son wannan asibitin.
Mahmud ya daga ma Ismail kai alamun yace mata
eh, zai kai ta, Ismail yace eh zan kai ki, amma sai kin
samu sauqi, sbd kinsan ba za’a iya tafiya dake a haka
ba ko? Ta lumshe ido, ina.. Ina hajiya ta? Da momy
na? Yace duk zasu zo. Sunce inyi miki sannu. Tace
malam kace suzo su tafi damu, ni da khalil, kirasu
ynxun malam. Yace zan kira su, zaki sha ruwa? Ta
sake juyar da kai, dai dai lokacin ne wayar Ismail ta
soma ringing.
Ya ciro ta daga aljihunsa, sannan ya kalli fuskar
wayar, hajiya sauda ce, don haka sai ya fita waje, ya
daga tare da sallama, suka gaisa. Tace masa, Ismail
yaya mai jikin? Yace da sauqi, tace ta farka ne? Yace
eh ta farka kuma Alhmdlh jikin da sauqi sosai. Tace
to mungode ma Allah, kar ka manta ka turomin
account number dinka. Yace insha Allahu. Tace
nagode sosai.
Bayan ya kashe wayar, zai juya kenan sai ya hango
likitan ya nufo dakinsu don haka sai ya jira shi, likitan
ya qaraso. Sun gaisa ta hanyar yin musabaha, sannan
ya tambayi yadda ta kwana da jikin?

Ismail yace jikin da sauqi yau, don ta daina wannan
nishin. Likitan yayo ciki, Ismail ya biyo shi yana masa
qorafin har ynxun bata ci wani abu ba. Daidai sunje
kanta ne, likitan yake bashi amsa da cewa, kar ka
damu da wannan, sbd ruwan da muka sa mata jiya
da daddare yana dauke da sinadaran abinci, so, ko
bata ci ba, ba zai zama matsala ba.
Ynxun muje a debi jininka a gwada mu gani, in yayi
sai muyi qoqarin saka mata a yau. In mun tabbatar
da samun sauqin ta, sai mu saka ranar da za’a yi
mata aiki, ina nufin dori. Ismail yace, na zaci yau
za’ayi mata sbd kar qafar tayi tsami. Likitan yayi
murmushi, kar ka damu zata samu sauqi, ba tare da
wata matsala ba. Haka kuma babu abinda zai faru ko
da takai sati daya ba’a dora ta ba. Ismail yace,
shikenan Allah ya bata lfy.
Ameen, inji likitan, tare da dafa kafadar Ismail ya
jinjina. Sannan ya kalli mimi, sannu khadija. Ta dago,
ta kalli likitan, ya kama hannunta mai lafiyar, inane
yake yi miki ciwo ynxun? Tace duk jikina, amma
qafafu na sunfi yimin ciwo da hannuna. Likitan yace,
bayan nan fa? Ta soma kuka, nidai gidanmu nake son
a kaini, can zanje gurin daddy na. Likitan yace, za’a
kai ki da zaran kin samu sauqi, kinji ko? Tace ina
khalil?
Likitan yace, yana nan yana samun sauqi kinji? Cikin
sigar lallashi yayi maganar. Kar ki damu kisha tea
kinji ko? Tace ni banajin yunwa. Ina son in wanke
baki na. Likitan yace, karki damu k8nji ko? Ya kalli
Ismail, ka bini muje ko? Ismail ya dubi Mahmud, ina
zuwa ynxun. Mahmud ya koma bakin daya gadon ya
zauna tare da cewa to.
Ismail yabi bayan likitan, suna fitowa, sai gasu yaya
Amina, yace su shiga bari ya dawo Yanxun. Likita ne
ya nuna masa har sashen masu dibar jinin, sannan
ya kalleshi, in sun gama, ka sameni a office dina, kar
ka damu ko kaga mutane ga shigo kawai, Ismail yace
to nagode. Bayan an diba ne, sai suka ce ya tafi zasu
kaima likitan sakamakon in sun fitar.
Yace to, nan ya nufi office din likitan, kamar yadda
likitan ya fada masa haka yayi, ya shiga duk da
wadanda ya samu suna ganin likitan. Ya samu yana
ganin wani a ciki, har zai fita, sai likitan yace, dan jira
mu kadan, ynxun zan sallameshi, yana fita, ya nuna
ma Ismail kujera, zauna nan. Ya dora hannuwansa
saman babban teburin dake gabansa, sannan ya kalli
Ismail wace, shawara kuka yanke? Game da daurin
dorin matarka.
Ko baku riga kun yanke shawara ba? Ismail yace
mun yanke, kawai ayi mata anan. Likitan yace,
shikenan za’a kawo maka takardar biyan kudi, sai
kaje ka biya, sannan su baka takardar shedar biyan

kudi, Ismail yace to, na gode. Likita yace, amma shi
wanda ya mutu yaya suke da ita? Ismail yace, shi
take so, likitan ya aje biron dake hannunsa, ya tattara
hankalinsa a gurin Ismail, kamar yaya shi take so,
gaka mijinta?
Ismail saida ya danyi shiru, don ya tsani bada
labarin, sannan yaba likitan labarin aurensu a
taqaice. Likitan ya danyi jim, sannan yace, kayi
haquri, ka kuma riqeta, wata rana zakaji dadin
haqurinka. Ya miqe tare da cewa na gode likita, kar
ka damu zan taimaka iyakar iyawa ta, inji likitan,
Ismail ya sake cewa nagode, yace ba komai kaje, in
sun kawo sakamakon kazo.
Lokacin daya dawo, ya samu mimi tana ta kuka, yaya
Amina tana ta bata haquri, ya isa gurinsu, yaje cikin
damuwa, daidai kunnenta ya rusuna yana cewa, yi
haquri mimi, ki fadamin me kk so? Tace ni gurin
daddy zanje, ka bani wayata in kira daddy na.
Yasa dan yatsansa yana share mata Hawaye, wayarki
ta 6ace a gurin da kukayi hadari, amma ki bari zan
siya miki wata. In kinji sauqi, zan kaiki gurin daddyn
ki. Sabon kuka ta saka, tana fizge-fizge, ya miqe ya
koma kusa da Mahmud yace, nifa gsky zan kira mata
shi suyi magana, Mahmud yace ka kira shi kawai don
kada ta zarge ka. A handsfree ya saka wayarsa,
sannan ya kira layin daddyn nata, tayi ta katsewa
ba’a daga ba. Ya sake kira, gab da zata katse aka daga,
tare da cewa hello! Ta gane muryar daddy, don haka
cikin kuka tace, daddy kazo ka tafi dani. Zan mutu
anan. Daddyn cikin zafin rai, a fusace yace kar ki sake
kiran layina.
Ni ba mahaifinki bane, baki daga cikin ‘ya’ya na, da
farko nayi niyyar in huce sbd kinyi min biyayya a
karo na biyu, kinbi wanda na baki, ashe ke kina kan
bakanki, to inaso ki sani, ko mahaifiyarki na samu
labarin inda kk, sai na kada ta ta barmin gidana, bare
wata nafisa da kk kira tazo, kisa a ranki bakida kowa
sai wannan mijin naki. In kinga dama ki zauna. In
kuma sake tafiyar za kiyi, duk ba damuwa ta bace.
Nidai gargadina kar ki sake kirana, ko ke ko mijinki!
Yakai qarshen zancen tare da kashe wayar sa. Ihu
mimi ta saka, tare da fizge ruwan da aka sa mata a
hannunta mai lafiyar. Saboda tsananin kukan da
takeyi, ya hana Ismail lallashinta, don bai san ta ina
zai fara ba. Tayi kuka har muryarta ta dushe, babban
takaicin ta, ba zata iya tashi ba, don da tuni ta fita titi,
mota ta taka ta ta huta.
Ganin abin bana qarewa bane, yasa Ismail kiran
likitan. Yayi fada sosai, ganin halin da mimin ke ciki,
yace bai dace mara lfy irin haka a sata cikin damuwa
ba. Ya kalleta, khadija kiyi haquri dadyn ki zai huce

insha Allahu, kinji ko? Tace ya daina so na, tunda ya
iya hadani aure da talaka, nasan ya daina so na,
kuma da gske yake yi, abinda yz fadamin, ya cire ni
daga cikin ‘ya’yan sa. Likita ka taimake ni, kayi min
allurar guba in mutu, likita yaja kujera ya zauna, bai
kamata ki nemi mutuwa ba bayan Allah ya raya ki,
kun yi mugun hadari fa, da Allah ya ga dama, sai ya
dauki ranki a lokacin.
Ki natsu koda daddyn ki ya qi ki, ba ga mijinki ba?
Tace bana sonshi! Malami ne fa? Ismail ya lumshe
ido cikin takaici, kar ki damu, ki bari ki qara samun
sauqi, muga yadda za’ayi, kinji? Ta dago ido ta
dubeshi, zaka barni mu tafi tare da khalil? Ynxun
bani da kowa sai shi, yace zaku tafi, da qyar suka
lallashe ta tayi shiru
Kwadayi madudin wahala na’im da mom Nafisa
bakuga komaibama ai, Ismail yace, ga ruwan da ta
cire nan a maida mata. Likitan yace, babu damuwa,
tunda ta dawo hayyacinta, zata iya cin komai ba sai
an maida ba. Sannan jininka za’a iya ba kowa, don
haka za’a zo a diba ynxu. Ismail yace, zanje can ne?
A’a ba sai kaje can ba, inji likitan. Anan ma za’a zo a
diba.
Da qyar Mahmud ya matsa ma Ismael yasha ruwan
tea. Shi kansa duk ya rame sbd tashin hankali. Tara
da kusan rabi, Sai ga wata nurse ta shigo da wasu
mata guda biyu, lokacin yaya Amina tana cewa bari
ta tafi, shi kuma Ismail yana cewa Mahmud, ya
kamata kaima ka tafi. Shi kuma yana cewa, bari dai
in an dibi jininka din sai na wuce. Sallamar wasu
matan ne, yasa su yin shiru daga zancen da suke yi
don jin ko su waye.
Dai dai lokacin mimi ta dangana daga kukan da
takeyi har ma ta yanke hukuncin yadda zatayi. Nata
ganin, abin da zai fissheta, in sun samu sauqi ita da
khalil, zata bishi gidansut tunda shi hajiyarsa tana
sonsu tare, sai ta zauna a gidansu, in ya kammala
karatu sai ayi musu aure, Amma ta daukar ma kanta
alqawarin yadda daddy yace ya barta, ita ma har
abada ba zata sake nemansu ba.
Dama hajiya bata sonta, shikenan zata yi Rayuwar ta
da khalil, ta amince bata da kowa sai shi din.
Sallamar matan ne ta katse mata tunani. Ta daga ido
ta kalle su. Ko cikin mata dubu ba zata kasa sheda
fuskar mahaifiyar khalil ba. Ba wai don kamar da
sukayi dashi ba, domin tun kafin suje gidansu a
kwanan baya ita da khalil din, ta mallaki hotunan
mahaifiyar tasa masu dinbin yawan gske a wayar ta
wadanda khalil din ke turo mata. A ranta tace
shikenan ma tazo tafiya damu. Nasan khalil ya riga
ya fada mata komai. Sai taji wani farin ciki ya darsu
acikin zuciyar ta.

Kukan da mahaifiyar khalil din ta fashe dashi ne ya
katse tunaninta, tare da tattaro dukkan hankalinta
zuwa gurin ta. Ji tayi tana fadin. Alahu Akhbar!
Yarinyar nan babu rabon kuyi aure da khalil, ajalinsa
ya jawo miki wahala. Ni dama nayi tunanin wannan
zazzafar s soyayyar da khalil ya kamu da ita, da qyar
in zai rayu, yaron nan bai ta6a min sata ba tunda ya
taso, sai dalilin wannan soyayya. In da mahaifinsa ya
bada hadin kai, kila da ynxun khalil yana raye. Allah
ya baki lfy. Mimi ta zaro idanu tana kallonsu.
Qwaqwalwarta ta kasa saita zantukansu. Wai suna
nufin khalil ya mutu ne?
Ismail kuwa ya rikice, yana ta yi wa nurse din alama
da yatsansa a baki wai suyi shiru, amma sam basu
lura ba. Saima fadi da nurse din take yi, wai iyayen
wanda ya mutu dinne suka zo daukar gawarsa, shine
suka ce a rakosu su duba ta. Daya matar kuwa
wadda suka zo tare, fadi takeyi, kiyi haquri aunty
Amina, Addu’a kawai zaki yi masa, kinyi dauriya a
gida, baki masa kuka ba, sai anan? Cikin kuka mai
tsanani mahaifiyar take cewa, ban gaskata
mutuwarsa ba saida nazo naga gawar khalil. Ihun da
mimi keyi ne ya katse mahaifiyar khalil.
Wani yunquri da mimin tayi shine ya saka su nufar
gadonta. Sai dai Ismail ya rigasu isa. Duk da haka
kafin yakai ta riga ta kai qasa a sume. Ya dauke ta
yana fadin, inata alamta muku cewa kuyi shiru. Sbd
batasan komai game da mutuwarsa ba, amma sam
baku kula ba, gashi kunsa itama za’a rasa ta. Ya dora
ta akan gadon yana cewa, ku taimaka ku kiramin
likita! Mahaifiyar khalil fadi take, Inna lillahi wa inna
ilaihi raji’un! Ai ban san bata sani ba, nurse kuwa tuni
tayi qasa da gudu don kiran likita.
Qarfe sha daya da mintina momy Nafisa ta shiga
gidan ‘yarta Na’ima. Aljannar duniya. Ha ta furta
lokacin data iso cikin falon farko, Ta kalli ‘yar tata,
wadda tazo ta bude mata qofa. Na’ima kina cikin irin
wannan gdn kk daga hankalinki? Na’ima ta turo baki,
momy ni wannan gdn yayi mintg girma, abin haushi
kuma ni hadai ke yini a cikin sa. Momy tace, a’a ina
masu aikin da akace an kawo miki? Tace, suna
gefensu. To ai su ba abokan hirana bane momy. Suje
su raina ni? Momy tace, ba nufi na kenan ba, ba wai
kuyi hira ba, ina nufin a qalla kina jin motsin wasu a
cikin gdn. Na’ima ta turo baki, to momy shifa bashi
da lokaci na.
Momy tace, matsalarki dai mijinki ko? Na’ima tace
eh. Momy nafisa tace, kije kice masa inason ganinsa,
ko har ya fita? Na’ima tace, yananan banji fitar sa ba.
Ta miqe ta nufi sama cikin zumudi. Tana bude qofar
ta jiyo shi yana waya, yana zaune a kujerar
computer. Daidai abinda kunnenta ya jiyo yana

cewa, “tsaya mana kiji Jennifer. Kar kisa ma kanki
damuwa, na fada miki ba wadda nakeso din na aura
ba, ko da ita dince ma kinsan cewa ke ta musamman
ce, kina tsammanin rayuwa ta zata tafi sak ne in
babu ke? Cikin turanci yake magana. Yayi jim,
alamun yana sauraron abinda take fada. Sannan yayi
‘yar dariya, tare da cewa, na san dai zaki iya bada
sheda ta kan fadar gsky komai dacinta. Ya sake yin
jim, sannan yace, to zan tabbatar miki da cewa kinfi
wadda aka kawomin a matsayin mata. Zan tabbatar
miki yadda ke da kanki zaki gamsu da batun, ya sake
saurawa. Sannan yace, fadamin me zan miki ki yarda
tunda naga kina tantama, kamar kin manta ni waye.
Dariya taji ya saki, tare da fadin, ai wannan mai sauqi
ne, in dai kwana da nine, ina me yi miki albishir
cewa, ni da ke yau a gida na zamu kwana. In nayi
miki haka, zaki gamsu cewa ni dake mutu-ka-raba?
Maganar ta maqale, bai qarasa ba, sakamakon jin
muryar Na’ima da yayi cikin kuka tana cewa, dama
mata kk nema? Ya saki murmushi, sannan ya maida
wayarsa kunnensa. Baby zan kira ki zuwa Anjima. Ya
kashe wayarsa, sannan ya juyo da kujerarsa gaba
daya, don irin mai jujjuyawarnan ce, cikin fara’a
yace, baki sani ba dama? Ta tsaya tana Numfashi,
tare da mamaki, gami da zaro idanu. Yayi murmushi
mai sauti, kina nufin dama bakuyi bincike ba? Ya
girgiza kai ayya.
Ni qasurgumin manemin mata ne. Sannan ina shan
wiwi da giya kadan, akwai wata matsala ne? Ta rasa
me zata ce, sai kuka. Cikin kuka take cewa, ba zan iya
zama dakai ba. Mutumin da baya iya 6oye laifinsa.
Yace, oho, dama kinzo kin la6e min ne? Kada ki
zauna dani din mana, dama ni na kawoki? Ko na riqe
ki ne? To kazo momy na tana jiran ka a falo, ya ta6e
baki, wacece kuma momy? Tace, don wulaqanci,
mahaifiyata dince baka sani ba? Ya kalli danqareren
agogon bangon falon, me kuma tazo yi da wannan
safiyar?
Ya kalli computer dake gabansa. Ta jirani, aiki nakeyi,
in zata iya, in kuma ba tada lokaci, taje ta dawo wani
lokacin, in abinda tazo dashi ya dame ta. Na’ima
tace, wadda ta haifeni ce fa? Yayi mata wani kallon
banza, cike da izgili yace, don ta haifeki, ni ta haifa?
Kuka ta fasa, sannan ta juya ta tafi ranta a 6ace,
hankalinta kuma a tashe. Cikin kuka ta sami momy
nafisa
zaune a falo,

1 Comments On CANJIN RAYUWA
avatar
mariya-6-8

9 months ago

Reply

In HAUSA language

Please Login or Register in order to submit comment