Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fatanmu allah yasa bai riga ya ba wai ba.rufe bakin mahmud ke nan,lsmail ya ce,amin...bai karasa ba,sai ga MIMI ta fito sanye da riga da wando damammu,sai dan mayafi da ta rataya shi kamar yadda take yi tana janye da dan akwatinta.da sauri ya nufo ta,ina za ki je?ta kalle shi sama da kasa,ta ja tsaki,ta tsallaka kwata.ya kalli gurin zaman yan majalisar kofar gidansu ba su fito ba rana.mahmud ya ce,bar ta mu bita a baya. haka kuwa tana tafe suna bin ta.sai ta tare dan acaba ta hau.su ma suka hau suna hangenta tana waya har zuwa garejin mota.tana tsayawa suka tsaya ta ciro kudi ta ba dan acaba,su ma haka.ta nufi wata mota.kafin su tsallaka su isa ga motar har sun tashe ta.lsmail ya shiga tashin hankali sosai.ya ce, mahmud barin ta za mu yi ta tafi?na yiwa mahaifiyarta alkawari. mahmud ya ce,zo mu dauki mai gulf din can ya bisu.sun nufi gurin sai suka ga hamisu direba ana sa masa fasinjan abuja.lsmail ya ce,aa me kuma ka tsaya yi?ya ce,lodin abuja zan yi,in dan kara na mai,ln samu na batarwa.lsmail ya ce,sauke sumu bi su MIMI,ta gudu ga su can sun dauki hanyar kaduna.
[01/10 10:35 pm] Abdul: (50)Nan da nan hamisu ya sauke su,lsmail ya shiga gaba,mahmud ya shiga baya.duk da halin da lsmail yake ciki bai hana shi ya yi wa hamisu direba nasiha ba.ya ce,hamisu tsakani da allah ban zaci kana cikin direbobi masu cin amanar iyayengidansu ba.sam bai dace ka yi lodi ba tare da izinin maigidanka ba.haramun ka ci.ai gara ka ce min in kara maka na mai.amma wannan cin amana ne.ya baka amana ne fa.ko ya san kana yi?hamisu ya ce,wai!ln alhaji ya ji ai na shiga uku. lsmail ya ce,ka gani ko?yana biyan ka hakkinka.hamisu ya ce, lnsha allah na daina.daga yanzun ba zan kara ba. Da yake hamisu gudu yake yi,sun hango su,har sun kusa zuwa daf da jun. MIMI ce ta gane motar gidansu.ta ce,ana bin mu. waccan motar gidanmu ce. nan suka kara gudu.gudun nasu yayi yawa.allah dai ya tsare...karan da suka ji shi ne ya tabbatar musu da cewa taya ce ta fashe ta su MIMI. daga inda suke suna hangen yadda motar take tuntsira gudi-gudi a kan titi.gaba dayansu suka hau salati.hamisu na cewa taya ta fashe shi. kuma ya taka burki.hankalin lsmail ya yi mugun tashi.suna isa gurin,motar tana tsayawa bayan ta tokari bishiya.suka fito suka nufi gurin.motoci suka tsaitsaya ana ta kokarin ciro su.duk jikin lsmail bari yake yi.wasu na cewa tun dana ga tukin da yaron nan yake yi na san zai yi wuya basu fadi ba. Nan zan dan huta.sai mun hadu a kashi na uku don jin shin su MIMI za su rayu?ln sun rayu,yaya zamansu zai kasance?wai na'ima ta ci nasara da ta hau saman abbas?mene ne labarin zainabu? Taku Halimarku K Mashi. sai na ji ku a 08081165107. lna jiran shawara ko korafi.
CANJIN RAYUWA 3
Halima K mashi
Littafi na Uku
Hausaebooks
Shuraih 99%
Daga:- http://keffiansonline.cf

Hankalin isma’il yayi mutukar tashi lokacin da aka
juyada motar domin gaba daya khalil yadagargaje
har kwanyarsa tanzuba juyawa yayi yana salati kmar
yadda sauran sukeyi bai iya sake kallon grinba har
aka faito da mimi sai da aka zuba su amota sannan
mahmud yazoya kama kafadun isma’il yana cewa
karka damu isma’il mutafi asibiti sun nufi motar
kenan mahmud ya hango wani daga cikin masu
kawo daukin ya kunkuci dan akwatin mimi dajakar
khalil ya gane akwatin mimi ne sbd a gabansa tafito
lkacin dazata tafi dasauri mahmud yanufishi yana
cewa kaiba ni kayan nan konakane?

Yace ammm dama inace za aje gurin yansadane
mahmud yace nanne hanyarguri yansandana,a gurin
sojoji zaaje ba yan sandaba irinku ne masu yin sada
in anyi hadariko? Mutumin ya miko akwatin tare da
cewa bani kadi bane yanuna wani gawanda yadauki
waya chan! mahmud ya kwada masa kira, kai zonan
bani wayar hannunka shi ma babu kunya yamiko ta
muhmud yace kuji tsoro allah batare da ya jira jin ta
bakinsu yajuya ya nufi motar hamisu ya zuba kayan
sannan ya shiga yana cewa “muje hamisu!” kuwwar
motar yansanda itace ta tsaidasu,suka iso.
Sannan suka nufi asibitin tare. Cikin sauri aka amshi
su aka yi emergency dasu, musamman dayake
angansu da yan sanda.isma’il yana tsaye cikin
matsanancin hali.addu’o’in da isma’il yake yine
sukasa jikinsa ya daina bari saidai kallo daya zakayi
masa ka san cewa yana cikintashin hankali.daya daga
cikin yansandan ya nufosu.ya kalli mahmud waiyaya
abin yafarune? Mahmud yakalli dan sandan gudu
yakeyi sosai,dan sandan yace naji lokacin da mukazo
gurin,wani yana cewa,koyasha wani abune? Sai wani
ne acikin motar yace,irin yaran masu kudin nan ne
suke dauko mota suzo sunamugun godu
atiti.mahmud yce, yarinyar da suke tare matar
wannance, yanuna isma’il.jiya aka daura musu aure
shne yazo ya dauketa zasu gudu, shine fawannan
hadarin yafaru.dan sandan yakalli isma’il batason
kane?
Lsma’il yace, babanta ne yahada nida ita ranka
yadade baxan iya saniba.kafin dan sandan
yasakecewa wani abu,sai ga likitan da sauri.ya ce,
kune yan uwan masu hadarin nanko? dasuri
mahmud ya taso,mune likita.likitan yace kun san
cewa namijin yarasu ko? duk da cewa dama suna
tunanin cewa ya mutu,saida suka dauki kabbara.
Sannan suka ce, allh yajikansa da gafara.isma’il
yakama hannun likitan yana fadin”doctoh itafa?
“yace,kar kadamu,munayin iyak kokarinmu.ta samu
karaya guda biyu a kafarta, da kuma guda daya a
hannu.sannan munaso ne ta farfado don mu sani ko
ta samu wata matsala awani guri daga cikin kanta,
saboda ta zubar da jini sosai.yaba shi wata takarda,
kaje gurin sai da magani,gashi can zasu baka
wadannan,yanxun kakawo mana.
Isma’il yace to,sannan ya kalli mahmud,gashi kudin
suna gida.mahmud yace,to muje kadauko mana.
Daga nan sai mutan gadan su san halinda ake
ciki.kafin su wuce saida suka dauko jakar khalil da
wayarsa suka ba wa yan sandan.don tasa aka gani ba
agata mimi ba. hamisu yajasu, kai tsaye gidan
suka koma, inda isma’il ya aje jakar mimi,sannan ya
dauko kudinsa duka na aikinsa da alhaji ya bashi.

Ya kulle dakin ,sannan yashiga cikin gdan yasanar da
su inna abin daya faru.bai tsaya amsa tambayoyin
dasu innar sukeyi masa akan wai yaya akayi haka,ko
unguwa suka fita?ya fita suka koma asibiti suka sai
magungunan. lokacin ne ma dansandan yake fada
musu cewa,yakira iyayan khalil.sunyi amfani da
wayar khalil din ne. yakuma sanar dasu cewa,dansu
yayi hatsari, kuma ya rasu.suzo su dauki
gawarsa.isma’il ya girgiza kai don jinjina yadda
mahaifan khalil zasuji wannan lamari.alhaji yakira
hamisu don yaji ko ya kosa kaduna.
Zai sa shiya amsar masa sako gurin wani abokinsa na
maganin diabetes ne na hausa da abokin nasa yace
xaiba shi,don shima yaji dadinsa. Hamisu
yace,matsala aka samu alhaji,ko katsina ban baroba
har yanxun.alhaji ya ce, meya faru kuma? Hamisu ya
sanar da shi komai. ran alhaji ya bace mutuka dajin
cewa mimi tasake yankurin guduwa.cikin bacin rai
yace ma hamisu,”kataho kawai!”yace,alhaji yarinyar
nan tana cikin mawuyacin hali sosai,don duk
akakkarye taka.alhaji yace,hamisu kabarsu kawar.
Babu abin da zan iya yi mata, kaima bbu abin daxaka
iyayi mata,don haka kayi abin da nace kawai.yace,
shikenan,alhaji zan taho yanxun.”yace,” to, kana kusa
dashi malam isma’il din ne? Yace, “eh ina kusa
dashi.yace,toka bashi!”ya mikama isma’il wayar.sun
gaisa,alhji yace,”ashe abinda yafaru kenan?”isma’il
yace kwarai kuwa alhji.yace Allh yakyauta.”cikin
tashin hankali isma’il y2e,alhji kayi mata duk abinda
takeso,zata iya rasa ranta,domin shi khalil din ya
rasuma.”duk da alhajin ya jinjina batun mutuwar
khalil a ransa,amma afili sai yace,”karka damu
malam isma’il,tunda yanxun ta karye ai bazata sake
yankurin guduwa ba.ka ba hamisu wayar.”isma’il
yace alhji kuzo ku taimaka mata.”alhji yace,isma’il
inayi maka jajen abin da yafaru da iyalinka,amma
kayi hakuri ba zan iya taimaka mata ba.kaba hamisu
wayar!”cikin rawar hannu,isma’il ya mika ma hamisu
wayar.
(Za mu ci gaba)….
(Tare da Halima K Mashi)
Canjin rayuwa
A sanyaye ya koma ya jingina da bango. Sai
lokacinne ma ya tuna ya kamata ya sanar da hajiya
sauda. Ya kalli mahmud, “ya kamata in sanar da
mahaifiyar yarinyarnan ko? ” Mahmud yace, “tabbas
ya kamata ka sanar da ita” kan benci ya zauna,
sannan ya soma kiran layinta. Bata jima ba ta daga. A
sanyaye ya gaishe ta. Ita kam yanayin muryarsa tasa
ta faduwar gaba. Tace, Ismail ta sake guduwa ne?
Yace Eh hajiya, amma sunyi hatsari akan hanyar su
ta guduwa. Yanxu haka muna asibiti. Tace, Inna lillahi

wa inna ilaihi raji’un! Da sauqi dai ko? Yayi ajiyar
zuciya, to da sauqin dai za’ace amma shi ya rasu… Ya
rasu?? Ta katse shi. Yace tabbas, ita dai sunce suna
jira ta farfado. In har ta farka a cikin hayyacinta, to
suna ganin karayar data samu ce guda biyu a kafarta
daya kuma a hannunta sune kawai matsalar, cikin
kuka hajiya tace, wane asibitin kuke? Yace babbab
asibiti, tace shikenan bari in Kira alhaji zanzo ynxu,.
Kafin ya amsa da cewa Alhaji ya kirashi, har ta kashe
wayar.
Hajiya ta soma kuka. Su hasana suka fito da sauri
suna tambayar ta lafiya? Tace musu mimi ce sukayi
hadari. Nan suma suka shiga damuwa. Tace bari in
kira Alhaji Muje mu ganta. Ta shiga kiran layin
Alhajin, tana soma ringing ya daga, Tace cikin kuka
Alhaji kaji abinda ya faru? Yace naji. Ko ba hadarin
su mimi ba? Tace ashe ka sani. To dama zamu tafi da
yara ne. Ga mamakin ta sai taji yace, ban amince ba,
yaci gaba da cewa, ki Fadama duk sauran ‘ya’yanki
banyi wa kowa izinin zuwa duba ta ba, matsawar na
isa. Mamaki ya cika hajiya sauda, tace sbd me Alhaji?
Yace cikin fushi, ban isa ince ga abinda nakeso ba
saina fadi dalilina kenan ko? Tace kayi haquri. Yace to
na saka Allah ya isa! Daga kanki har sauran da suke
qarqashi na matsawar kuka taka gurinta! Ya kashe
wayarsa.
Shi kansa Alhajin cikin damuwa yake, amma ya tsara
ma kansa cewa, dole ya haqura don wani dalili nasa,
sannan yasan cewa, abin Ya ta6a zuciyar hajiya
sauda, sbd hk ya yanke Shawarar sake kiranta. Ta
daga, har lokacin kuka take, a nata ganin bai dace
abar mimi cikin wannan halin ba. Yace amma hajiya
don Allah kiyi haquri, akwai dalilin da yasa dole sai
nayi hakan.
Zan yi miki bayani daga baya. Sannan ina mai
jaddada miki ban haquri na, ki taimaka kuyimin
wannan. Nasan zaki iya saka ‘ya’yanki su dangana da
zuwa gurin mimi. Kuma daga baya zaki daina jin zafi
na in kinji dalilina. Kin fahimceni ? Tayi ajiyar zuciya,
shikenan zanyi duk yadda kk so. Shima ya sauke tasa
ajiyar zuciyar. Na gode, Allah yayi miki albarka, ya
saka miki da aljannah. Sai nazo. Tace to Allah ya
kawo ka lfy.
Ta kalli su usaina tace, inaso kubar maganar nan
anan, ko su yayanku abba, bana son su sani. Hasana
tace sbd me hajiya? Tace sbd hk dadynku ya buqata.
Kuma banison ku damu da cewa sai kun san dalili.
Zamu dinga jinya lafiyarta daga bakin mijinta. Suka
kalli juna da ido, suka mamakin zancen mahaifiyar
su, sannan suka miqe suka shiga dakinsu. Ita kuma
sai ta daga waya ta kira layin Ismail. Cikin sauri tare
da yin sallama, ya amsa a sanyaye, yace kun iso ne?

Tace a’a ba zan samu zuwa ba, in dai ta tashi kace
ina gaisheta.
Yace hajiya kema baki samun damar zuwa kenan? Ta
soma shesshekar kuka, mahaifinta yayi mana iyaka
da zuwa gurin ta, cikin sauri yace sbd me? Don Allah
ku yafe mata, sbd tana cikin wani hali, wanda ba dole
bane ta tashi. Hajiya tace na yafe ma ta duk abinda
tayi min, wanda na sani da wanda ban sani ba. Kuma
nima bansan dalilin sa nayin hkn ba, amma idn ya
fadamun zan sanar dakai. Sannan kuma malam
Ismail zan sake baka amanar mimi, ka qadd ara
batada kowa, sai kai kadai mijinta. Lokaci zuwa
lokaci zan dinga jin yadda jiki nta yake, amma ta
waya daga bakinka. Ismail yace shikenan nayi miki
alkawarin zanyi iyakar iyawata, sai Anjima.
Ya kalli Mahmud, bayan ya kashe wayar, wannan
wace irin qaddara ce ta hau kaina? Alhaji ya hana su
zuwa ma. Mahmoud yace wanna n abin da Mamaki,
amma tunda kai iyalinka ce, nauyinta ya rataya ne a
wuyan ka. Kai ya cancanta kaci gaba da kula da lfyr
ta har zuwa lokaci n da zasu huce. Nawa zaton sunji
zafin guduwar data sake yi ne. Amma in sun huce
zasu zo. Ismail yace Allah ya sani, tunani na dama
banida qarfin dazan iya kula da lafiyarta. Mahmud
yace, kar ka damu Allah zai duba maka. A sanyaye
Ismail yace Allah ya duba mana, suka hada baki
gurin cewa Ameen! Saida lokacin sallah yayi sannan
suka miqe suka nufi masallaci. Daga masallaci ne
Mahmud ya nufi gd don sanar wa malam Aminu.
Ismail yace kabi ta gdn yaya Amina ka fada mata don
bata sani ba, Mahmud yace zanbi insha Allahu.
Kusan qarfe uku yaya Amina tazo tana kuka don
tausaya ma dan tilon qanin nata. Yace kar ki damu
yaya Amina, insha Allahu zata samu sauqi. Tace wai
yaya abin ya faru ne? Nan ya sanar mata da komai,
tace Allah mai iko, yanzun kaine zakayi jinyar ta, ko
yaya zakayi kenan alhalin bata qaunarka? Yace yaya
ai dole in kula da ita tunda nine mijinta. Kidai tayani
da Addu’a. Allah ya bani yadda zanyi. Tace to Allah ya
shige mana gaba. Yace Ameen.
Bayan la’asar su malam suka zo tare da wasu
malamai suka yi masa jaje, tare da addu’ar cewa,
Allah ya bata lfy, sannan suka tafi. Itama yaya Amina
sai alokacin ne tace bari ta tafi gd sbd batun abinci.
Ta ciro kudi daga aljihun Jakarta naira dubu uku da
dari takwas, tace gashi kadan kara. Ya kalle ta a’a
yaya ki barsu, inada kudi. Sannan kinsan akwai batun
abinci, kece zaki dinga kawo mana. Tace dukda
hakan, yace a’a ki riqesu a hannunki, sbd kema
kinada rauni. Tace to bari inje gida sbd inyo muku
abincin da wuri. Yace a’a kai ki yo abincinnan yau
tukunna, ki vari sai gobe, don bazan iya ci ba, bari

dai muga yadda jikin zaiyi, tace shikenan baka
buqatar komai? don bayan magriba zamu dawo da
abbansu saddam.yace sai dai dardumar sallah, sbd
basu riga sun bamu daki ba tukunna. Tace hk ne
shikenan sai zuwa Anjima din. Bayan fitar yaya
Amina, ya sake miqewa ya nufi qofar dakin da mimi
take kwance yana hangenta, zuciyar sa cike da
tausayinta, kamar da wasa, idanun sa suka nuna
masa tana motsi, da sauri ya nufi gurin nurse da
suke zaune, yace ina likita? Tana motsi. Nan take
suka tafi kitan likitan. Da gudu-gudu likitan ya iso
suka shiga s
Canjin rayuwa
Canjin rayuwa
sun kai kusan minti goma, sannan wata nurse ta
leqo, ta kalli Ismail, tace masa wanene khalil? Yace
mata shine wanda sukai hadari tare ya mutu. Ta juya
da sauri, Ismail dai yanata kai komo. Ya kai kusan
rabi sa’a sannan likitan ya fito, ya kalli Ismail yace
masa, zo muje! Ya bishi zuwa offishinsa, inda suka
zauna, ya kalli Ismail, kai wanene dinta? Ismail yadan
yi jim kadan don yana jinjina kalmar, duk lokacin da
zai furta ta. Tsakanin jiya zuwa yau, ya lumshe ido,
“ni mijinta ne” likitan yace ok to zamu kaita dakin
jinya, domin ynxun ta farka, amma yanxu munyi
mata allurar varci sakamakon tana ta kiran sunan
marigayin. Ya ajiye biron daya dauka, sannan ya kalli
Ismail yace, wazai zauna da ita? Ismail yace nine,
likitan ya girgiza kai, babu dama ka zauna da ita, sbd
kai namiji ne, kuma dakin akwai matan mutane, sai
dai in zaka biya daki na musamm an, sannan za’a
buqaci kudi sbd likitan da zai mata dorin zaizo ne da
ga kano, kuma gashi dorin har guri uku ne, Ismail
yace to likita kamar nawa ake nema? Yace kasan shi
likita ne mai zaman kansa, dauko shi akeyi, qila yakai
gurin dubu sittin, banda magani. Ismail yace insha
Allahu za’a san yadda za’ayi, Amma likita bata samu
matsalar da ake tunanin ta samu ba ko? Ya girgiza
kai, bana zaton ta samu wata matsala, Ismail yace
Allah yasa dai, zan biya kudin daki na musamman
din.
Likitan yayi masa kwatancen inda zai biy a kudin
dakin. Har ya miqe sai likitan ya sake kallon sa, ba
tada iyaye ne a garinnan? Eh, kawai yace, to ko cikin
dangin ka ba wanda zai iya zama da ita? Cikin qosawa
yace nima yayata ce guda daya, kuma tana da
qananan yara. Baya son doguwar magana, shiyasa ya
amsa a qagare, shikenan ka iya tfy, inji likitan, an
kaita daki na musamman akan kudi naira dubu
ashirin a sati biyu. Dakin akwai TV da dan fridge, sai
na’urar sanyaya daki. Ismail yana tsaye yana kallon
mimi, an manna mata bandeji a gurin da taji ciwo.

Addu’o’i kawai yake yi mata, har lokacin da yaje yayi
sallar magrib a bata farka ba.
Yana shigowa yaci karo dasu yaya Amina, suna
neman dakin da aka kaisu. Ya amshi kular hannunta
sannan suka nufi dakin, suka gaisa da abbab saddam,
yayi masa jaje. Basu jima ba suka ce zasu wuce. Yabi
su don yadan taka musu, anan ne take tambayarsa
ko ‘yan gdansu sunzo? Yace kinsan dai koda zuwan
ne, sai dai in mazan, amma matan ban sa rai ba,
mazan ma daqyar in sunji, tunda lokacin da naje gdn
basa nan, tace to ba komai Allah ya bata lfy, yace
Ameen, tace tuwo ne fa akular da muka zo da ita,
naga kana son tuwo, yace nifa yau ko karyawa banyi
ba, dama zan samu ruwan zafi, tace vari to inje in
dafa maka, sai abban su saddam ya kawo maka,
tunda ga mashi n ahannunsa. Ismail yace to na gode.
Suna fita, wayar Ismail ta soma ringing, ya daga ashe
Mahmud ne ya kawo innarsu zata duba ta, suna cikin
gaisawa da innar sai ga kiran hajiya sauda. Bayan sun
gaisa take tambayarsa jikin mimi, yace da sauqi,
amma tana varci, bata farka ba, tace to zata kira
zuwa gobe, sannan ya turo mata account number
dinsa, yace to insha Allahu, sannan yayi mata godiya.
Kusan qarfe goman dare, mimi ta farka, lokacin
Ismail yana zaune kan sallaya, ya idar da sallar shafa’i
da wutiri. Sai yaji tana cewa, “daddy na, daddy na!”
cikin wani irin sauti mai ban tausayi. Da sauri ya
miqe ya nufi gadon da take, ya kama hannunta yana
“khadija, sannu kinji. Kin tashi ne? Bari in kira likita”
ya miqe ya nufi qasa da sauri domin kiran likita.
Ta soma kuka, ni fa taimako nayi sbd kar aji kunya,
yace aikuwa zakiyi da kin sanin wannan taimakon.
Inaso kisan wani abu, ni mutum ne wanda in naga
abu inaso, to so ne na gske, kuma ba zanyi wasa da
son ba. Haka nan kuma qi, don bana yin qi da wasa,
mimi na gani nace inaso, tunda tace bata yi ai sai
abarni inji da ciwon rashin ta, ba wai akwaso min ke
ba, baqi qirin! Ni farar mace itace ra’ayina, kin gane?
Na’ima ta soma kuka wiwi, tana cewa, toni ynxun ka
fatamin matsayi na, ya miqe tare da nufar dakin
varcin sa. Gashi na fada miki kuwa, banda wannan
matsayin wanne kk son ji? Don Allah tashi ki fita a
daki na, Na’ima ta miqe jiki babu qwari, ta nufi
dakinta cikin kunya da kuka, ta kira momy nafisa a
waya, momy tace lfy da wannan daren? Na’ima cikin
kuka tace “momy Abbas baya so na, ya fadamun ”
momy tace sakarya! Baki dai iya kissa ba kawai zaki
ce. Har akawai namijin d zai raina mace? Bare ke da
kyanki da komai, amma dai ki vari zamuyi magana
dake zuwa da safe, na fada miki jikin dadynku ne ya
motsa, gashi ma anyi masa waya mimi tayi hadari.

Duk da ya nuna abin bai dameshi ba, amma jikin
nasa ya qara rikicewa, ynxun dai ya samu varci,
bayan likita ya gama dubashi. Na’ima cikin sauri tace
“sis mimi din ce tayi hadari momy? ” tace eh itace,
sake guduwa wai tayi, ita d wanda takeso din, sunyi
mummunan hatsari, shi wanda take so din ya mutu.
Na’ima tace innalillahi wa inna ilaihi raji’un! To
ynxun tana ina? Amma da sauqi ko? Momy tace,
dalla can, duk kin wani rude, ni ina zan sani? Dadyn
ku ya hana zuwa. Hamisu direban yara yace, tana jin
jiki. Na’ima tace Allah sarki sis mimi!
To shi daddy ya haqura mana, momy tace karma ya
haqura, su qarata can, kedai ki samu kija ra’ayin
mijinki, yadda zaki samu hanklin mahifinku ya dawo
kanki. Ni araina ma cewa nayi dama itace ta mutu,
Na’ima tace a’a momy kar ta mutu, tunda dai mun
samu ta barmin abbas din ba shikenan ba. Ki tayani
in shawo kansa, baki ga irin wulaqancin da yayi min
ba, tace shikenan zanzo da safe. Na’ima tace Yauwa
gara ma kizo kiyi masa magana, tace to shikenan sai
nazo din, sukayi saida safe.
Zainabu tana kwance akan gadonta, sai juyi takeyi,
cikinta banda hautsinawa babu abinda yake yi, amai
kawai take ji, amma ta kasa yi, ga zazza6i data kwana
dashi. Da qyar tayi sallah. Budo qofarta da akayi ne
yasa ta tashi a firgice, tasan Alhaji ne, kullum sai ya
shigo dakinta daidai wannan lokacin, yayi buqatarsa
da ita, kuma babu ruwansa ko da dakin wa yake
cikinsu, ya cire rigarsa ya rataye, tace don Allah kayi
haquri yau banida lfy, yace ruwa na da ciwonki?
Nima yau sauri nake yi, ba ddewa zanyi ba. Ya fado
kan gadon. Ji tayi aman da takeson yi tun jiya ya
taho. Nan kuwa tayi ta sheqo masa shi a jiki har kan
gadon, ji tayi turarensa dada hankado mata aman,
da sauri ya tashi ya wanka mata wani wawan mari.
Yana ta surfa mata ashariya. Ita dai amai take ta
wankawa, har saida ta amayar da duk abinda taci,
sannan ta kwanta tana maida numfashi. Shi kam da
zage-zage ya fita har xuwa dakinsa, ya wanke ya fito
ya nufi gurin wacce zainabu take bi mata don kai
buqatarsa can tace, sai yau kasan dani? Tunda kayi
amarya ka daina shigowa da safe, yace ai tsiyarki
kenan mita. Ita wancan har mace ce da har zaki
damu kanki? Yarinyar da kullum saina dake ta ko na
zage ta sannan zan samu buqatata. Wai ahakan ne ta
kama amaye amaye, in dai ciki ne zanci mutuncinta,
sbd ban mori kudina ba. To bata sonka kai kuma ka
nace, in bata sona ai tanason kudina ko? Ba sai a
faranta min na kudina ba, sisina bazai yi ciwo ba.in
ba zata zauna ta faranta min rai ba, to zasu bani ‘yan
kudina.
Uwar ta ga roqon tsiya, ko jiya saida ta aiko wai in

bata dubu goma. Kuma kabata? Ta katseshi. Yace
dan iska ne ni, dari biyar na bada aka kai mata. Wane
farin ciki nake samu gurin ‘yarta da har zan dinga
bata kudi? Tace inace ka bata ne,nima ince akai wa
uwata.
Yace ke har kinyi magana? Ko wata uku ba’ayi ba,
tsohonki ya dage saida na sai masa mashin, tace eh
amma kayimin gori yafi sau dari akan mashin
dinnan, kai matsalar ka kenan gori duk wanda kaba
abinka to ya tabbata zaisha gori, yace eh amma su
kuma iyayen naku rokonsu yayi yawa. Ni muje kinji,
sauri nake zan fita.
Alhaji lawal kenan, sam bai damu dayin al’amuransa
bisa tsarin addinnin musulunci ba bare bin doka.
Rayuwar gdansa yana tafiyar da ita bisa son zuciya,
shi ganinsa, kudi za suyi masa maganin komai, bai
qara bi takan zainabu ba ya fito. Shirun da uwar gd
maman bushira taji, yasa ta leqa dakin tana cewa,
amai kkyi haka? Kai ta daga, alamun eh, maman
bushira tace anxo gurin kenan. Ta kama ta, tashi in
taimaka miki, ban daki takai ta tace ta wanke jikinta.
Ita kuma ta koma tana kwashe kayan gadon, saida ta
gyara ta, sannan tasa aka kawo mata abin kari. Da
qyar ma tadan kur6i ruwan kunu.
Ta kalli uwar gdn, maman bushira me yasa kk ce
anzo gurin? Uwar gd tace alamu sun nuna cewa
kinada ciki ko? Zainabu ta zaro ido, nima ban sani ba.
Uwar gd tace gsky ina zaton ciki gareki. Yaushe
rabonki da al’ada? Zainabu ta sunkuyar da kai, fashin
sallah kuma? Eh, inji maman bushira. Tun ana saura
kwana biyar bikina. Maman bushira tace tabbas ciki
ne dake, abinda yasa nace haka, sbd Alhaji baya son
haihuwa. Zaki fuskanci wulaqanci sosai.
Zainabu tace, banda wannan wulaqancin, har akwai
wani kala da zai min? Maman bushira tace sosai ma
kuwa! Amma Shawarar dazan baki, in ya tambayeki
cewa kina da ciki ne? Kice masa a’a shawara ke
damunki, Zainabu tace sbd me to? Tacesbd zai baki
maganin zubar da ciki. Zainabu tace zaifi murna, in
har cikin ya zube, maman bushira tace ai ba wannan
ne matsalar ba. Matsalar zaije ya kawo miki magani,
kuma ba wai zai kaiki asibiti bane. Akwai wata
yarinya daya ta6a aure, haka akayi qarshe Yarinyar
rasuwa tayi, sbd jini ne ya 6alle mata.
Tace to in na 6oye masa, kuma yasa aka kaini asibiti
aka gano cewa inada ciki fa? Maman bushira tace
bazai gane ba. Don ba zai kaiki asibiti ba, don kuwa
baya daga cikin mazajen da suka damu da lafiyar
iyalinsu, don ko panadol sai dai ki saya. Zainabu ta
soma kuka tana fadin dole zai sani, tunda cikin zaiyi
girma, maman bushira tace kafin cikin naki yayi
girma, da ace zaki iya sakin jiki dashi kema ki sauko,

ki tarairaye shi, to da kin yagi na xuwa asibiti, dana
kayan jariri. Zainabu tace, nayi ta qoqarin in
kwatanta tun kwanaki da kk fadamun, amma na kasa
sakin jiki dashi, don inada wanda nake so, kuma yake
sona. Tace shikenan zako kiyi zaman wulaqanci, duk
ranar daya gano akwai wannan cikin, sabulun wanka
sai kin rasa. Zainabu tace zan kwatanta in gani ko zan
iya. Maman bushira tace da dai yafi miki. Ranar
Zainabu wuni tayi sheqa amai da kuka. Ta galabaita
sosai, da magriba ya shigo ya ganta kwance. Ya dube
ta a wulaqance, ke kuma kukan me kkyi? Tace
shawara ce, dama ko a gd inayi, yace oho’ to kina
shan wani magani ne in ya tashi? Tace eh, amma
banida kudi ban sayi na asibiti ba, sannan ina kuma
shan na hausa. Yace to ina kumazaki samu kudin na
siyen maganin, tunda ni dazan baki kin mai dani
kamar wani dodo?
Ta kalleshi, ai na bari, yace da gske? Ta sunkuyar da
kai, sannan tace eh. Yace kinyi alqawari? Ta daga

1 Comments On CANJIN RAYUWA
avatar
mariya-6-8

9 months ago

Reply

In HAUSA language

Please Login or Register in order to submit comment