Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nasani nima
nahana yakusance ki domin yana dauke da aids ke kuma
kina ganin kobaki maiba shiyasa bayasan kusantarki to
kirabu dashi
ga bikin nafi zan hadaki da wanda yafishi yanxu bazan
baki komi ba sai lokacin
ke kuma nafi wannan karin aljani dan kundalo jarirai
yakeso guda biyu domin aikin yanada wahala kinga
haryan xu yakasa shiga jikin haisham harya dauki hanyar
kaduna saukima ba ajirgi yatafi ba amotane
nafi bata damuba jin boka yabukace jinin yara awajan
domin dama tasaba duk sadda tazo saita bada jini
shiyasa ake mata aiki mai kyau abinda yasama
gabanta yafadi jin abinda boka yace mata wai har yanxu
dan kundalo baishiga jikin haisham ba
dariya boka yasa chan kuma ya daure fuskar tamkar
gunki karkiji komi kamin ya isa nasan saiya mantar dashi
wata uwar tsawa yadaka kutashi kufice man dagani da
sauri sukayo waje kayanda suka tube suka dauka sukasa
dominshi aqa idarshi ba ashigar mai fada koda da
dankwali ne
suna fitowa daga dajin sadi tasauke wata uwar ajiyar
zuciya wai qawata boka yatai makeni ke inba danshi ba
dayanxu nazama lbr
kedai bari sadi shiyasa nakejin maganar bokan nan
domin da bazarshi nake rawa ke inba danshi ba da tuni
bashir dinda nake taqama dashi yaguje ni nifa koda
cewa yayi nacigaba da bauta mashi to wallahi xanyi
wa ixubillah Allah kakaremu da zuciyoyin mu fadawa
halaka
motarta tatada suka qara gaba
haisham yana cikin mota dagashi sai PA dinshi sai drive
sauran motocin cike suke da sojoji sai jiniya suke saki
cikin motarshi kuma karatun alqur'anine ketashi kira
arar sudas domin yasaba duk sadda zaiyi tafiya indai
amotane to kira aceke tashi
to shiyasa aljani dan kundalo yakasa shiga wurin amma
dayake shi shedani ne saida yashiga duk yadda jikinshi
ke konewa amma yahaqura
haisham ne yatashi da sauri kai kukashe wannan karatun
akwai wani pilat nawa koki samanshi daga PA dinshi har
drive saida suka dago suka kalleshi
*Ansholly*
😭BAKAR IZAYA😭
42_43
*Aunty ta baxan gaji dayi maki godiya ba nagode sosai
Allah yabar zuminci*
su mlm iro sun galabaita iya galabaita amma hainan ko
ajikinta dariyarta kawai take
gashi koda mutum yasuma bawai zata qyaleshi bane
saisunji inama basu sumaba
haka taita dukansu Abu tun bakwai na safe har akai
kiran sallah magariba kana taqyalesu suduka basusan
inda kansu yakeba itama sulalewa tayi akasa sume
yayinda cikin rugar kowa yake mamakin ardo dan
bainuna wata damuwa ba nanfa yan gulma suka fara
kawo mashi gulmar cewa yaqori mlm iro daga cikin
rugar tunda har abin yaxo kanshi
taka masu birki yayi yace bazai koresuba shiya dauki
kaddara yasan kuma Allan daya bashi yusif shiya amshe
shi baxai xama daga cikin jahilan mutane ba
ya yinda mutane dayawa bahaka suka soba sunso aima
mlm iro korar kare tuntini
ammashi ardon yaqi to yanxu zasusa tunda abin
yatabashi zai dauwani mataki domin da suna ganin Dan
abin vaixo kanshi bane shiyasa yaqi daukar wani mataki
juyawa sukai kowa yakama gabanshi dan sunsan koda
zasu kwana awurin suna cemashi yakori iro bazai yiba
duk cikin yan uwan su lawai ba Wanda yaqara tunaninsu
saida akai kiran sallah kana matar lawai tatuna cewa
tundazu daya fita xuwa gidan mlm iro baidawo ba da
sauri tayi hanyar soro tana tunanin ya akaima bata tuna
dashiba sai yanxu
tana fita takira wan mijinta tafada mashi abinda yafaru
dawowa yayi yafa dama sauran mutanan dake wurin
abinda ke faruwa kowa sai yanzu yake tunanin ya akai
suka manta da lawai bayan shiya dace yarife danshi
wanine yafara magana dazufa naga audu yake ceman
gidan iro xaixo dan matarshi ta mutu shikuma bazai
yarda ba dole saiya dauki mataki
amma abun mamaki har yanxu ban qara ganinshi ba
kuma koda mukaje maqabarta rife matarshi banda shi
mukaje
wan lawai ne yayi magana yanxu dai mutashi mije miyi
sallah inmun gama saimu shiga gidan iron muga lafiya
ke kuma kikoma cikin gidan harmu dawo to kawai tace
mashi
su sukai hanyar masallaci itakuma takoma cikin gidan
tana shiga yan uwan lawai mata suka kama tambayarta
wai ina yake
nan tagaya masu komi yafaru shiru sukai ba Wanda
yaqara magana
koda aka gama sallah wan lawai tashi yayi yafa dama
mutane abinda yake faruwa nanfa kowa yafara cewa
shima baiga dan uwanshi
liman ne yace sutashi suje gidan iron sugani ba wanda
yayi musu haka suka fito suka kama hanya
suna isa qofar gidan suka iske mata cike da qofar ba
wanda yai masu magana cikinsu liman domin sunsan
matan wa inda ke cikin gidan mlm iro ne sai kuma yan
uwansu
shegewa sukai cikin gidan amma asoro sukaci karo da
gawar auwalu wanda yafito yabarsu mlm iro
ihu matarshi tasaka shikenan ankashe man miji aradun
Allah baxan yarda ba arado nima saina kasheta
ba wanda yatan kamata domin kowa zuciyarshi iya wuya
take dan suna tinanin dukta kashesu
suna shiga cikin gidan suka iskesu yashe kasa wanda
saika qura ido sosai kana kagane suna nunfashi
ya yinda hainan take chan gefe ayashe amma shigowar
mutane yasata tashi zaune cikin firgita
kamin ta tabbatar da wani yanayi take ciki matar auwalu
tashigo tamkar kububuwa tayi kan hainan amma kamin
taqarasa akai wani irin juyi da ita aka bugata kasa wani
irin ihu tayi wanda gadukkan alamu tasamu tija qafa da
hannu kowa yaji tausayinta yayinda hainan kanta yake
duqe tsakanun
cinyoyin tana jiran taji duka
amma mai makon haka saitaji ihu da sauri tadago kanta
wacce tagani ayashe kasace tayi mamaki ita data taho
dukanta to ya akai hakan yafaru
wurinsu lawai sukayi matarshi da sauri tayi kan mijinta
yadda taganshi yasa hankalinta tashi domin duk jikinshi
jini yake fitarwa
cikin sauri take mgn mlm waye yaimaka wannan aikin
aradun Allah kowa nene baxan barshi ba domin ita har
azuciyarta batai tunanin hainan xata iya yimasu haka ba
daqyal lawai yadago dan duk cikinsu ba wanda yakaishi
shan wahala
cikin jin jiki yafara mgn Abu ba ruwanki dakowa yayi
mana wannan dukan nidai kawai ko daukeni kokaini gida
tun daxo damiketa ihun neman tai mako bako taima
kamana ba sai yanxu
wani tari yataho mashi wanda yahanashi karasa mgnr
dayake
daukar kowa akai aka kaishi gidanshi yayinda aka bar
yalwa nan
gidan uwale
amma suduka saida akai masu gyaran tijar dasuka ji
mlm iro ne kawai yaji ahannu amma uwale da yalwa
duka aqafa sukaji indama uwale taji dadi cikinta bai
xubeba
*wannan nakune masoya bakar ixaya nagode da irin
kulawar dakuke bani kuma alhamdulillah naji sauqi
yanzu zakujini akan lokaci insha Allah*
Ansholly😘
😭BAKAR IZAYA😭
44_45
*hadixa nanette wannan pagen nakine tabbas ina yaba
maki akan qoqarin dakike*
😘ANSHOLLY😘
ba wanda yayi mashi musu acikinsu dan sunsan baya
san musu
amma abun yabasu mamaki sunsan ogan nasu bayaso
asa mashi waqa amota amma yau da kanshi yace asa
kidane yacika motar ba afi mnt5 haisham yace su juya
sukoma abuja ba wanda yai magana domin sunga
kwanan nan ogan nasu wani fada yakeji
aban garan aljani kundalo kowa duk jikinshi yaqone yaji
haushin abun amma yana tuna jinin daxa abashi yayi
wata irin dariya yabace bat dan yasan yagama aikinshi
nafi koda suka shiga cikin garin abuja kai tsaye asibitin
su Dr bashir suka wuce domin tasan bata dawata
matsala zai saman mata jarirran
office dinshi tashiga dan duk hospital din sun dauka ita
din kanwarshi ce kamar yadda yafada masu
xama tayi agudan sit din tafara bashi lbrn yadda sukai da
boka koda yaji ta ambaci jarirran da boka yace takawo
kodar baiji ba baccinma hannun daya bata suka tafa
dayake tabar sadi cikin mota
karkiji komi dan yau anzo asa a domin akwai kusan
mace samada goma adakin haihuwa kinga dan jarirrai
biyu sun mutu aiba wani abu bane
kamin nafi tace wani abu aljani dan kundalo yabai yana
amma fuskarshi amurtuk duk da asufar mutum yazo
amma saida sukaga wura ran daya qone
basu tsorata da ganinshi ba domin dama inhar xasu
bashi jini haka yake masu sunan wace zasu bashi kawai
zasu fadamai shikuma yaje ya ida aikinshi
da sauri Dr bashir yajawo list din sunayan matan dazasu
haihu dan damashi ake kawo mawa
sunan mata biyu yafada aljanin yabace yabat yayi dakin
haihuwar
watace keta ihu ga dukkan alamu haihuwar nagab da
zuwa ita Kuma ta gefinta sunan Allah kawai take kira
nurse dince taima wace ke ihun mgn domin nurse din
musilmace haba baiwar Allah kamar ba musilmaba sai
ihu kike dan zaki haihu
kiduba takusa dake kiga yadda taketa kiran sunan Allah
nasan wallahi koda wani abin cutarwa baxai cutar da
wannan baiwar Allah ba
domin tana anbatan Allah bakisan ba lokacin haihuwa
aljannu nazuwa kusa da mataba inkina wannan ihun
tsab zasu shafi yaranki saikiji anata cewa cuta takama
man da tunda na haifeshi kuma kece sila
kamin nurse takai karshen maganarta takuma fasa wani
ihun wanda yai dai dai dafa dowar kanda
kamin dan yayi kuka tuni aljani dankundalo yatsotse
mashi jini
yakoma wurin wace taketa ambatan Allah ganin dayai
xata ida konashi yasashi bar mata wurin
yaje wurin wata itama irin wace tahaihuce ihu kawai
takeyi itama tana haihuwa yana zoqe jinin babyn yabace
nanfa idanuwan sauran suka raina fata dansunga
gaskiyar nurse tafito gashi su biyu dasuketa ihu cikin
dakin duk sunyi asarar baby dinsu
nanfa sauran suka kama kiran Allah
nafi natashi xata tafi wayar Dr bashir takama ringing da
sauri yadauka tare dayima nafi alamar tatsaya
morning sir morning Dr ina ina fatan kana office yes
sir to nanda mnt30 kafito bakin get xaka rakani gidansu
yarinyar dakace ok sir
rungume juna shida nafi sukai kana tafita daga office din
da gudu domin taje tashirya kamin su iso
shima Dr bashir bakin get din yafito yatsaya
baifi mnt25 da tsayuwa ba saigasu sun iso
mota guda yabude yashiga wace ke gaba domin motar
haisham itace sukasa tsakiya kwatance yaitaima drivan
har suka iso da sauri yafito daga cikin motar tare
dacema haisham yafitosu shiga cikin gidan
saida yakusan daqiqa goma kana yafara mgn inbaka da
hankali bashir ni inada shi taya zakace nashiga cikin
gidan mutane batareda kanemi ixininsu ba
sry sir namanta banfada maba gidana ne yarinyar take
dan kanwar mata tace kuma tunda kace zakuzo nakira
waya nafada masu
saida yakwashe kusan mnt20 kana yafito cikin isa da izza
wanda kallo daya zakaimai kasan nairata zauna anan
haisham kenan ga kudi ga kyau shiyasa yammata da
yawa ke kawo mashi cafka shikuma baya tatasu
dakin baqi Dr bashir yabude mashi ya yinda sojoji suka
ciki qofar dan daga bakin get xaka san gidan akwai
babban mutum aciki wanda Nigeria take jidashi
nafi kuma anachan ana birsine jiki da abinda boka
yabata wata qatuwar hijabce ta dauko tasaka ya yinda
sadi tai shigar alfarma wace tafito tamkar matar auran
dan dama tagirmi nafi da shekara 2
shiyasa dr bashir yace kanwar matarshice dan inhar
yace kanwarshi ce to bada jimawa baza,a gano shi
shiga palon yayi nafi taso mutafi gashichan apalon baki
yana jiranmu
to yanxu yayana ya zanyi da kwallin da boka yabani kisa
yanxu sai sadi taimaki jagora har ashiga Palon dan
inkince saikinje chan xakisa to bazai sanyuba dan sojoji
suncika gidan gabaki daya
sawatayi saita maida kanta cikin hijabin tamkar amarya
sadi tariqe mata hannu har palon tunda suka doso palon
gaban haisham ke faduwa amma yadake
ganin dayai sunshigo cikin dakin yasashi dai daita
natsuwarshi kallansu kawai yake
ya yinda sadi taje taima nafi wurin zama itama tasamu
wuri tazauna nan suka fara gaisawa shida sadi duk
atunaninshi itace
ganin tatashi tace to bari nashiga daga ciki kamin akawo
maka abun motsa baki
taran nunfashinta yayi no am full wallahi nagode to
kawai tace tafice warta
shikuma yafada tunani yanxu dama Dr makauniyace
yasamo mashi amma bashir yagama dashi maganar
nafice tadawo dashi daga tunanin daya tafi
ina wuni yaji tace mashi domin 12 tayi
lfy kawai yace mata kana yaqura mata ido cikin hijab din
taga yana kallanta da sauri taja hijab din baya ido 2 sukai
jiyai kamar wani abu yadakar mai xuciya da sauri yadafe
wurin
*Ansholly*
😭BAKAR IZAYA😭
46_47
😘Ansholly😘
*wannan page nakine aunty mamie Allah yabar
xuminci*
*rugar jalo bayan shekara biyu*
abubuwa dayawa sunfaru ciki harda haihuwar uwale
tahaifi namijin data keso hainan har yanxu bautar
datake bata daina ba saida taji saukin wani abun dan
yanxu uwale tadaina dukanta haka yan rugar
domin suna tsoranta yanxu dukda ba ba adaina asarar
rayukanba duk shekarar daxatai amma bamai iya
dukanta saidai zagi ita kanta tanajin dadin hakan dukda
batasan miyasa suka daina dukanta dinba
ya yinda sarkin rugar ardo ko fuska baichan xamata ba
domin yadauki kaddara kuma cikin ikon Allah har
yazuwa yanzu bai qara wata asaraba
mlm iro kam yanxu qiyayya hainan ce lifke cikin
xuciyarshi dan tunda taimai wannan dukan qiyayyata
taqara habbaka saikuma gashi uwale tahaifa mai namiji
wanda yaci sunan baffanshi
so yake nuna mashi sosai saidai hainan tai tsaye tana
kallansu danji take inama itace sule wanda suke cema
mai kudi dan haka uwale tace adunga kiranshi domin
tace saiya zama mai kudin rugar kana shine namiji tasan
shinexai taimaka ma rugar ba hainan ba
yalwa da uwale anshirya amma saida uwale tasha fama
kamin yalwa tayarda sudawo da amintarsu shima saida
tasama uwale sharadin saidai tariqa zuwa gidanta amma
ita tagama zuwa gidan uwale
kaji yalwa da tsoro saikace
London girl lol
yaune bokanya takira su uwale akan maganar hainan
zaune suke gaban bokanya bayan sungama kirarata kana
suka dakata bushewa tayi da dariya kana tamaida fuskar
tahade tamkar bata tabayin dariya ba
kana tafara magana cikin aman murya bokanya natare
daku batattu nayi binkice hanya dayace xa,a iya kashe
hainan to amma tanada wahala amma inxaku iya bata
dawata wahala
cikin rawar jiki uwale tace wace hanya ce bokanya aradu
komine ne zanyi indai har wan tsinanniyar yarinyar xata
bar duniyar
dariya bokanya tasa kana tadaure fuska zaki kawo shanu
guda goma maza biyar mata biyar sai rakuma guda
hudu mata biyu maza biyu
uwale da sauri tadafe kirjinta dan tsabar firgice to itadai
tasanko kanta zata saida bazata kai kudin sayan wa innan
abubuwan ba ita wallahi ta haqura duk qiyayyar
datakema hainan gwara tahaqura
domin inhar tace to tasan zata shiga tsaka mai wuyane
gashi bokanya batada mutinci indai har tace abu
kumaka amsa to baka isa kadawo daga baya kace baka
samu abunba
amma kuma data tuno yadda tatsani hainan gashi
bokanya tace saita zamamma
rugartasu abin alfahari saitaji wani qwarin zuciya
yashigeta
da Sauri tamaida hankalinta wurin bokanyar zakice ina
zaki samu shanun da rakumman to mijin innarki
nafarko ya mutu kuma kinsan bashi da da kodaya gashi
yabar tarin dukiya
jibine za airaban gadanshi wanda yan uwanshine xasu
raba wani kullin magane ne tamiko mata kisamu rushin
wuta kisa wannan maganin kiturara kifara yau saiki gobe
da jibi kinga sau ukku kenan
to saiki tunkari rugarku tanda asuba yadda zaki isada
wuri dan da antaso masalci zasuyi raban kina zuwa
karkije ko ina inba gidan mijin innarkin ba kuma duk
wanda yaimaki magna karki amsa domin inkika amsa
aikinki yalalace
da kinshiga duk wanda kika iske kicemasu gadan
mahaifinki. kikazo amsa nantake zasu baki batare dasun
maki wani musuba kuma abinda nayanke maki dai dai
zasu baki basu kara maki koda daya ba
kutashi kutafi inkika dawo zan fada maku komiza ai
dasu
*kuyi haquri da wannan promise gobe insha Allah xan
maku mai yawa sadaukarwa ga Mira danfodia*
😘Ansholly😉
😭BAKAR IZAYA😭
50-51
😘Ansholly😘
*wannan page nakune ansholly fans2*
rugar jalo
bayan kwana biyu uwale tagama aikin da bokanya tasata
tun daddare tatambayi mlm iro cewa xataje rugarsu bai
hana taba
shiyasa tatashi tunda asuba tafara shiri goya mai kudi
tayi kan baya takama hanyar rugarsu
tana ganin tafita tatashi tayi hanyar madafi dan rabanta
da abincin yau sati biyu kenan dan har wani duhu take
gani acikin idanuwan ta
gashi duk wa inda uwale tace tarika yima aiki suma
kamar uwalan suke basuda tausayi
tuwa tazubo yanada yawa sosai gashi yayi wani irin sanyi
dan yanxu lokacin sanyi suke amma bata damu da
sanyin dayiba haka taketa turashi saida taji taqoshi kana
tatashi ruwa tasha kana tadauki buta tayi alwala tana
gama sallar daba tasan mitake cewaba
takama shara dan mlm iro yana masallaci
uwale nashiga rugarsu bata zarce ko inaba sai gidan
wanda aka kira mahaifinta
lokacin anfito daga masallaci duk yan uwanshi suna
zaune za araba gadan aba kowa hakkinshi kamar yadda
addini yatsara
ganin mutum sukai tsaye bako sallama kowa yadago
yana kallanta lfy mlm kikazo kikai mana tsaye aka kindai
san baki da gadan mamacin nan kowa kuma yasani dan
haka kama hanya kikoma inda kika fito
A,a illiya baza ai hakaba ke uwale miyaka woki nan uwale
datun dazo take tsaye tamkar damisi dan maganganin
illiya sunbata mata rai badan bokanya tace kartai wata
magana ba bayan taraban gado to aradu da maikwatar
illiya sai Allah
illiyan ne yakara magn waibake akema mgnb banxar
mata kawai inhar kinsan baki da abincewa ubanmi
kikazo yimana nan aradu koki wuce konazo natatta kaki
cikin isa uwale tai mgn gadona nazo amsa tsit kaji kowa
yayi illiya yanaso yayi mata mgn amma yakasa samun
wuritai tazauna sai wani cika take tana batsewa
haka sunaji suna gani sukaba uwale dukiyar gaba daya
dan ba abunda tarage masu inba raqumi daya ba kuma
kosuce mata basu yarda ba wanda duk sbd dukiyar suka
kashe yayan nasu amma gawata arana tsaka tazo tatafi
da ita
sunajin gidan nan kawai suka qaru dashi sai raqumi daya
kallan illiya tayi tashi muje karakani wajan da shanin
suke ba musu yatashi yabita yana gaba tana biye dashi
har sukaje wurin tsaye yayi yanama uwale kallan tsana
domin shima yaci buri akan wa innan shanun
to mlm sai akara gaba ko jinjina kanshi yayi kana yafice
daga wurin domin wani kuka yaji yataho mashi
tana dukawa xata fara kwancewa taji mgnr bokanya
wanda yasata zabura dan tsanin tsoro saura kadan tasaki
goyan dake kan bayanta
karkiji tsoro nice bokanya ina tare dake tun tahowarki
kibarsu anan zamu dauki abunmu ke kingama aikinki
to uwale tace cikin qermar jiki dan har fitsari tasaki
ficewa tayi daga wurin da sauri bata tsaya ko inaba
hanyar rugarsu tayi
gidan yalwa tashiga taci Sa,a tana nan sauke goyan mai
kudi tayi buta tadauka tayi bayi da gudu
chan saigata tafito yalwa yau naji tsoro aradu bantaba
jin tsoro hakaba sai ranar danaga Hainan cikin dakina
baccin nasan naya data rafi sai kuma yau
ya akaine uwale har kinje rugar taku kindawo ko biyoki
sukai yan rugar taku
ke yalwa duk wannan mai saukine to miyafaru
wai ina cikin kwance shanin dana samu kawai sainaji
mgnr bokanya nan dai tagaya mata yadda sukai da
bokanya
ke uwale ashe abin bokanya harya kai haka
kedai bari shiyasafa bana wasa da al amarinta yanxu dai
tashi mutafi wurinta muji mizatace
uwale da yalwa zube gaban bokanya bayan sungama
kirarata dan yau har kirarin dabasu taba yimataba sunyi
mata
kallansu tayi daya bayan daya kana tafara mgn
aljanin daxai maki aiki akan kisan hainan shine akaba
dukka shanun da raqumma
kubashi nanda wata bakwai xai baki mgnin da zaki zuba
mata abinci tanaci ko sharawa bazatai ba zata mutu
cikin firgici uwale tadago kanta bokanya wata bakwai
yayi yawa nida nakeso yanzu dana koma gidata mutu
tsawarda bokanya tayice yasa dan uwale firgita yasa
kuka
Ansholly😘
😭BAKAR IZAYA😭
48_49
😘Ansholly😘
*wannan pagen sadaukarwace ga dukkan masoya bakar
ixaya ngd d kaunard kuke nunama littafina*
*garin abuja*
hannu yasa yadafe zuciyarshi danjiyai tana wani irin
bugu amma yana ganin tamkar arba dayi da abinda yaji
nantake yanaso ne domin yana ganin tunda yake baitaba
san wataba sama dawannan baiwar Allah wace ko
sunanta baisani ba
nafi tasowa tayi daga wurin datake zaune dan tanasan
yaji kamshin turaran da boka yabata sosai taba
kafadarshi tayi firgigit yadawo daga tunanin daya tafi
ido takashe mai yadai my haisham kodai ban makaba ne
haisham da tunda yashaqi kamshin Nafi ya ida birkicewa
yafara magna cikin voice dinshi mai saka yan mata
surude irinsu halima Lol
tunda nake bantaba samun macen danaji tashiga
zuciyata irinki inajinma yanxu dana fita daga nan kd zani
dan inaso ayi auran nan cikin kankanin lokaci dan baxan
iya jure rashinkiba akusa dani
dadin danafi taji Allah kadai yasani dan jitai tamkar
tazuba ruwa akasa tasha amma tayi alkawari da haisham
yatafi zata hada wani qwarya qwaryar party
kallanta haisham yayi yaga tatafi tunani tabata yayi lfy
naganki cikin tunani
murmushi taimai kana tafara mgn ina tunanin Sa ar da
Allah yabani nasamun qwarxan namiji irinka haisham
ina sanka tunda naganka naji narasa sukuni harsai yau
daka firta man kallamar so
kallanta yayi cikin murmushin shi dama kintaba sanina
ne baby
sai yanxu tagane katobarar datasoyi girgixa kanta tayi a,a
kasan dai inso yana azabar da mutum baima san miyake
fitowa daga bakinshi ba
fira sukaci gaba dayi tamkar sunkai shekara yayinda
haisham ma yamanta yana dauke da wata cuta mai suna
aids yana ganin tamkar yanxu zaifara
aure kuma auran saurayi da budurwa
saida akayi sallah azahar kana yai shirin miqewa
baby nah baqo zaiyi halinsa zantafi badan nagaji dake ba
saida i haquri ne domin inda xani danna sameki ne
amma dazaki yarda kibini mutafi tare dana tafi dake
saidai nasan baxaki iyaba
cikin kisisina irintasu ta yan bariki tafara mgn nima haka
nakeji my haisham jinake tamkar karmu rabu amma
yaxanyi tunda tafiyar taka takasance wacce xamu xama
abu dayane saidai kawai naimaka addu,a
shafo fuskarta yayi baby kintafar man da xuciyata gabaki
dayanta inama ganan gaba
amma kinman laifi m kallanshitai alamar firgici afuskarta
laifin minai ma my haisham
murmushi yayi kwantar da hankalinki baby bawani laifi
kikaiman mai yawaba
sunanki ne baki fadaman kinaso naje gida dad dina
yatambaye ni nakasa fada dakuma garinku kifada man
komi
sunana nafisa mubiyu ne wajan iyayenmu nida yar
uwata sadi mahaifina Allah yaimashi rasuwa shekara
goma data gabata wani hawayan muna firci tashare daga
fuskarta
ayya sry Nafisa Allah yajikan baba
amin tace kana tafara mgn sunan qyauyan mu sulaja
mahaifina kamin yarasu yanada rifin asirin shi amma
tunda ya mutu yan uwanshi
suka kwace mana komi yazam mana abincin dazamuci
yana gagararmu to lokacin Dr bashir yaje qyauyanmu
domin duba asibitin cikin qyauyan ko wa inda aka turo
suna aiki yadda yakama to anan yaga yayata yace
yanasan ta
kamin takara mgn wayar haisham tadauki qara da sauri
yadauki wayar assalama alaikum chan dayan bangaran
akace
wa alaikumussalam dad ina wuni lfy dama cemaka xanyi
inbaka samo matarba toni nasamo ma yarinyar mutinci
diyar alhaji Ahmad aikasan irin tarbiyar dayake ba
yaranshi ko
murmushi yayi dad karka damu nasamu wata yarinya
mai tarbiya gani nanma wurinta tace nagaida ka duk
mgnr dayake idanshi nakan Nafi
shima alhaji hamxan fadada fara,arshi yayi to ina
amsawa yaushe xakazo gidan dan xaman dakake ba
mata yana damuna
dad yau ina nan tafe to saikazo kashe wayar yayi yakalli
Nafi to nidai xan tafi baby inajin sai gobe xandawo inna
dawo xaki idaban lbrn
dariya tayi tace saidai muhadu asilaja dan gobe muma
zamu tafi dan afada masu dawuri to xanm sameku
achan din kiran orderly dinshi yayi da waya kakawo man
2milyan yanxu ok sir
ai Nafi mutuwar tsaye tayi 2 milyan to itaxaiba koko
tsaye kawai take amma xuciyarta taruga wani wuri zata
iyacewa duk karuwancinta bata taba rike koda 1milyan
ba amma yau gata harda 2
ba afi 3mnt ba yashigo dauke da kudin ahannunshi
amsar jikar haisham yayi gashi baby kiyi manaiji kamin
nadawo inkuma bakisan wannan kinfisan kifiddo da
kanki to kifada man
girgixa Kai tashigayi uwa kadan garu murmushi yayi
mata kana yajuya yatafi dan yaga tamkar batasan inda
take ba
itakuma tayi shirune domin tasan inhar tabude baki to
ihu zata saki dan tsananin murna to bataso tabada
kantane
Ansholly
😭BAKAR IZAYA😭
53_54
😘Ansholly😘
*wannan page nakini Aisha*
kd
haisham ne xaune shida mahaifiyarshi kasha hanya dan
nan dayake baka safe take fadin sunanshi ba
murmushi yayi haba hajiya wace hanya ga mutuman da
yaxo ajirgi
duk da hakanan akwai gajiya yanzu katashi kaje kadan
watsa ruwa kana kaci abincin
to yace mata dan yanasan hajiyar tashi ganin yadda take
tattalinshi tamkar karamin yaro dayazo wurinta jiyake
duk wata damuwarshi takau
yana shiga bedroom din wani kamshi yadakeshi yasan
aikin hajiyarshi ne wani tausayinta yaji tabbas inba
uwaba bawanda zaima haka dan yasan ita tagyara dakin
dakanta tunda tasan bayasan na house girl
cire kayanshi yayi yafada bathroom
Nafi tanajin qarar fitar motarsu haisham tabuga wani
irin ihu nafarin ciki da gudu Dr bashir suka shigo palon
dama suna kusa da wurin dan tunda sukaji alamar
haisham yatafi suka fito daga cikin gidan
tana ganinsu tarungume Dr bashir yayana mafarkina ya
kusa zama gaske kaduba kaga irin kyautar da haisham
yayi man alokaci daya to inama ga abu yayi nisa
nandai sukaita murna Nafi ce tai mgn aiyau akwai party
dan dolene achashe
dole kudi suyi kuka sadi taba hannu suka tafa
shidai Dr bashir yana xaune yana kallansu yayana yanaga
kai shuru ina tunanin wani abune Nafi
bai kamata ataba kudin nanba gwara kitashi mubi
hanyar kauyanku yanxu dan mugaya gidanku yake
kinsan tunda bawani gidan kirki bane ko qyaure babu
ballantana yyanxu
wannan kudin chan yakamata suyi kuka banan ba kinsan
matsayin haisham kodashi baiga aibun gidanba tunda
yana sanki wasufa zasu gani yakamata muje mugaya
gidan yake kana
amma inkinga shawar batayiba shikenan
tashi tayi da sauri haba yayana wanama irin shawararka
batayiba tabbas kakawo shawara mai amfani kawai tashi
muje
bawani bata lokaci suka dauki hanya bayan tayi amfani
da mgnin da boka yabata
muntoci kadanne yakaisu cikin kauyan dan bawani nisa
daga cikin gari zuwa kauyan
yadda gidan yake haka yake saima kara lalacewar dayayi
shiga cikin gidan sukai itada sadi sai wani irin warinne
ketashi tamkar ba mutane aciki sadice takalli Nafi anya
nafi akwai mutane cikin gidan nan jibafa kiga gidan duk
kazanta aini wallahi ko yawo bana iya hadawa
Nafi tajuyo zatai mata mgn sbd tadanji haushin abinda
sadi tace kamin tace wani abu wata mata tafito daga
cikin wani daki wanda yake bara xanar xubewa koda
yaushe
kuyi haquri yarannan ina sallah ne shiyasa kukajini shiro
kushigo maraba banku
wani kallan tsana nafi takebin matar dashi wai yanxunan
wannan itace mahaifiyarta
ya yinda ita kuma taga yan burni sai washe baki take
wata yalolowar tabarma tadauko tashim fida masu ga
dukkan alamu bata gane kosuwaye ba
kallanta Nafi tayi cikin tsana dan tanaganin tabada ita
gaban qawarta yadda sadi take bata girma duk da ta
girmeta amma tasan yau girman yazube dan taga yadda
takema gidan kallan raini
wai Abu baki gane niba ne sai wata qerma kike dan haka
take kiranta tunda da sauri wadda aka kirada Abu tajuyo
danko da cikin bacci taji murya Nafisa dole taganeta
tasan yanxuma abinda yasa bata gane taba farin dataga
tayi mata
baccin tasan diyarta bakace Nafisa kece kika koma haka
tamkar baturiya zo kuzauna nabaku ruwa kusha
a'a Abu bazamu iya shan ruwa acikin wannan gidanba
kidauko hijabinki kizo mutafi gidan kawu kema bazaki
kara shigowa ba harsai angyara gidan
to kawai tace domin wata irin shakkar nafin taji tanaji
koda sukaje gidan kawunta ba wanda yachanxa mata
fuska ko yanuna abinda tai bata kyautaba murna ma
suke nantake cemasu mgnr auranta ne yataso kana take
gaya masu matsayin wanda zata aura
karkuso kuga yanda kawu habu kewashe baki shida
matansh
ita kanta tasan wannan nasarar tata tana daga cikin aikin
boka
shi kuma Dr bashir yakoma cikin gari dan dauko wa inda
xasu fara ginin gidan
*Ansholly*
😭BAKAR IZAYA😭
55_56
😘Ansholly😘
*page nakune duniyar hausa novels*
tsawarda bokanya tasace yasa dan uwale kuka wata
tsawar takuma dakawa kutashi kuban wuri konasa
ya'yan aljannu sutsotse ma yarannan jini da

Please Login or Register in order to submit comment