Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

haisham din yanema yayinda bugu daya
yadaga suka gaisa kana yafara gayamai abinda yafaru
ran alhaji hamxa shima yabace haquri yaba alhaji bishir
sosai
kana suka kashe wayar ya yinda alhaji hamza yaita fada
dama zaune yake shida matarshi suna dinner
kallanshi tai tace lfy wai alhaji tsaki yaja kana itama
yafada mata abinda mafi soyuwar danta yayi haisham
su biyu allah yabata amma har azuciyarta tafisan
haisham yau kuma ita kanta yabata haushi domin
tanasan matarshi hafsat batada matsala kwata kwata
ya yinda alhaji hamxa kwana yayi yana neman layikan
haisham amma akashe
sai 9:00 am yasa meshi aiko yana dagawa yarife shi
dafada naji abinda kayi ngd kuma yanzu nasan kayi
kudi kuma kazama babban kanka giyar mulki na ibarka
tunda aikamin kasamu milkin zaune kake da matarka lfy
kuma bakasan bata haihuwa va sai yanxu
to wallahi bari kaji nabaka nanda 2 weeks ka nemo
mataka aura kuma wace nanda 9 month zata haihu
danni ma namatsu naga jikana inba hakaba ranka saiya
bace
😘😘Ansholly😘
[3/8, 1:07 AM] +234 703 962 5239: 😭BAKAR IXAYA😭30
page nan nakine ke kadai Mira danfodio ina godiya da
kula warki gareni
😘ANSHOLLY😘
shidai haisham haquri kawai yakeba abban nashi domin
wata irin tsanar hafsa yakeji tana qara shigarshi
domin yana ganin baccin abinda taimai bai ishetaba har
saida taje tahada shi da mahaifine
mgnr alhaji hamxa ce tadawo dashi daga tunanin daya
lula
haqurin da zanyi haisham dayane kawai kayi abinda
nace maka kuma karka sake kazo man gida har sainan
da sati biyun dana baka
inkuma kaqi to wallahi wa innan samu dawan daka aje
abakin get zansa sufida mankai inkuma kana ganin wasa
to bismillah yana kawo wanan yadatse wayar
yana ganin abban nashi yakashe yanemo lambar hafsa
saidai yayi rashin sa'a wayar akashe take ita kuma tasan
dole zai kirata shiyasa tacere layin gaba 1
taba kanwarta mira sautin inta dawo daga makaranta
tatsaya tasayo mata saban sim card
yau kwanan haisham ukku ko qofar gida bai leqaba
danshi yana jiran mutuwar shine shiya sama ko mgnin
da dr yace yaje yariqa sha bai amso ba
amma abin mamaki komi bayaji ajikinshi shiyasa
yashirya yauxai fita office domin yasan aiki nachan
najiranshi
amma saiya biya wurin dr shi domin yacemai yasamo
mashi mata mai irin cutarshi ya aura danya ciki umarnin
abbanshi
inba hakaba shida aure har abada yana fitowa
bodyguard dinshi sukayo kanshi baiko tantama yasan
tunda yashiga cikin gida konan dachan basu jeba domin
dukba musilmi acikinsu
da sauri dukkansu suka kame tamkar gunkuna
kallansu yayi daya bayan daya kana ya umarcesu dasu
tafi gida dukkansu suhuta
yacema PA dinshi yakira mashi wa yansu domin chanji
suke inwa innan sunyi nasati saisoba wa yannan haka ko
akai ba ai 10mnt cikakke ba saiga wa insu sun iso kana
wa incen suka tafi
aka bude mashi mota yashiga wace tamkar yashiga palo
dan komi akwai aciki harta kitchen akwai
kallan PA dinshi yayi kana yabude baki cikin isata
zaratan maza yace hospital zamu dan inaso naga doctor
kallanshi PA yayi yace bai dace ace ranka yadade kullin
kaike zuwa ganin shiba wanda
dolan shine yazo inka kirashi komi yake dole yazo
kiranka kuma yabi yama buqa tunka
wata irin tsawa haisham yasama PA nashi abinda nakeso
za aiko abinda kace
sry sir kana yaima drive"n inda zasu
*rugar jalo*
Ansholly
[3/8, 1:07 AM] +234 703 962 5239: 😭BAKAR IZAYA😭31
page nan nakine nanette ina yaba maki akan qokarinki
😘Ansholly 😘
daqyal aka samu aka kai yalwa daki kana aka dawo wurin
uwale
ruwa aka dauko masu yawa aka watsa mata ihu tasaki
kana tatashi zaune
mutane take gani dishi dishi domin gani take tamkar
mutane tamkarba mutane ba wani irin ihu tasaki
gatanan zata cinyeni
dan Allah kutai makaman xata kasheni waiyo Allah gata
nan ihu take tamkar zata fasa gidan mlm iro ne yamatso
ya dauketa da mari domin tabashi haushi
wata qarar da tasaki saida yayi dana sanin marinta dan
Allah kiyi haquri aradu nadaina dukanki karki kuma
dukana nima natuba baxan qaraba aradu bazan kashe
kiba
nima kisakanman wuya hakanan
wuyanta takama tanata ihu mutane sai kallanta suke
gashidai sunga bakowa gurinta amma sai ihu take da
naiman tai mako
mlm iro mutane kawai yaima godiya domin yasan ihun
uwale ba yanxu xata barshi ba
barinta akai nan zaune kowa yakama gabanshi domin
anyi magrib
ya yinda hainan take gefe zaune tunda tatashi takoma
gefe taxauna tanata kallan ikon Allah
tana nan zaune taga mlm iro yayi alwalla ya wuce
masallaci itama da sauri tatashi tadau buta tayi alwallar
tazo takama dosa sallah wace bata san mita kecewaba
ya yinda har yanzu uwale bata bar rusa ihu ba ita kuma
yalwa ko motsi batayi
nandai tsakar gida uwale takwana itada hainan domin
mlm iro ba yarda baiyi da itaba takoma daki amma
daya dosota zata fasa uwar kara dole yaqyaleta
ga kuma hadari yataso daga gani xai saki ruwa sosai haka
yanaji yana gani yashige daki yaqyale uwale
wadda har cikin xuciyarshi tausayinta yake dan ruwa ake
kamarda bakin qwarya
ya mance yarshi duk ruwan daza ai tana cikinsu amma
ita vaiji tausayinta ba har yawuce yatafi masallaci taga
banta sai matarshi
mlm iro dai bai runtsaba ko kadan ana kiran asuba
yafito daga dakin lokacin andaina ruwan saidai wani irin
sanyi
wurin uwale yayi ko kallan inda hainan take xaune baiyi
ba domin yasan tabbas itace silar ciwan matarshi
yana zuwa kamin yatabata tamiqe tsaye tana kallanshi
amma sai qermar sanyi take
murmushi yai mata kana yace uwale wuce daki kichanxa
kayan jikinki kamin nakawo maki rushin wuta kigasa
jikinki to kawai tace mashi kana tashige daki
tana shiga ta iske yalwa itama zaune kobata tambaya ba
tasan itama cikin gidan takwana
ba abinda suka cema junansu iyaka dai uwale taje
tachanxa kaya kana tatura wa yanda tacire waje ta dawo
taxauna
bata dade dazama ba mlm iro yashigo da rushin
saida ya aje kana yajuya yatafi yai alwalla yatafi masallaci
ita kuma hainan tadauki tulu tatafi rafi kamar yadda
uwale tabuqata cewa ko anyi ruwa dole taje rafi
saida uwale taji tqdan dawo dai dai kana takalli yalwa
tace
😘Ansholly😘
[3/8, 1:07 AM] +234 703 962 5239: 😭BAKAR IZAYA😭32
wannan page nakine churber💋 dake da dukkan masoya
baqar ixaya
😘Ansholly😘
saida uwale taji tadan dawo dai dai kana takalli yalwa
cikin murya dushashiya tace yalwa tunda nake
bantabacin axaba irin tajiya ba
yalwa dariya tasama uwale kana cikin dariyar datake
tace basaida nace kidaina ba amma kikai kunnan uwar
shego dani
sai gashi hardani kika jamawa itadai uwale daure fuska
tayi tamkar bata taba dariya domin tana ganin tamkar
yalwa taraina mata wayo
yaza aitana fada mata ixayar dataji takama yimata dariya
yalwa dai dataga kawar tata tahau saita nemi hanyar
saceta
uwale miyena hushi inajin kamin wannan ranar tazo
gunki nitafara zuwa guna kuma ko jiyan yadda kikasha
azaba nima haka nasha abinne yaban dariya naganmu
manya mu biyu amma yarinya qarama tabamu wahala
uwale sai yanxu tasaki fuskarta wace dukta kumburi aina
dauka nikikema dariyar
wata dariyar tazo mata amma tadoje domin batasan
tabata shirin amma ko kallan fuskar uwale kayi dole
tabaka dariya
to uwale waiya akai keda nabari bisa ita amma naganki
akasa harda ihu
saida tayi Jim kana tafara mgn kedai bari kina juyawa
nafarajin jikinta yafara tauri tamkar dutse kamin nayi
wani yinquri tuni tamaqare man wuya aradun Allah jinai
tamkar wani qatan mutumne yamaqaran amma itace
tsaye da dan hannuta tamkar ludayi ni nasan saura
qadan na mutu Allah ne baisa kwanana yaqare ba
yalwa tace aini aradu saida namutu nadawo domin har
mala ikan daukar rai nagani da nawa kiri
kefa naki yalwa mai sauqine nida aka kaini cikin dodanni
mlm iro da tundazu yake jinsu yai sallama yashiga
dakin yana masu dariya nan yaba yalwa lbrn abinda
sukai yace yalwa mutane kika gani kikecewa kinga mala
ika inkin ganshi aiko baxaki dawo duniya ba
kema uwale mune kika gani atsaye kikecewa kinga
dodanni
nidai shawarar dazan baku shine kudaina neman
makasar hainan uwale inkina da tunani keda kanki zaki
gane inhar dukan hainan xakiyi ba abinda ke
faruwa dake amma inhar zaki nemi makasarta to kema
sai kingaba dai dai ba
bawai nahanaki kimata abinda kika gadama bane a,a
inaso kibari sai kinhaifa man dana saiki dora daga inda
kika tsaya yatashi yafita domin tafiya kiwo
ita kanta tayarda da mgn mlm iro shiyasa yanxu tasha
fama hainan lfy amma duk aikin datake bata dainaba
hardana makwabtan abinci ko saitayi da gaske take
samu haka dai rayuwa take tafiya
har gashi yau sati daya da baccin hainan
hmm wannan karin komi xai faru arugar jalo
*Abuja*
*Ansholly*
[3/8, 1:07 AM] +234 703 962 5239: 😭BAKAR IZAYA😭33
😭Ansholly😘
dai dai asibitin sukai parking fitowa yayi yashiga cikin
assibitin ya yinda sojoji suka take mai baya yana cikin
office yana waya da nafi yaji anturo qofa
dago kanshi yayi cikin masifa domin yahana ashigo
mashi office ba excuse
da sauri yatashi tsaye amma bai kashe wayarba ajeta
kawai yayi domin yanasan nafi taji yadda zasi da
bergidiya general
saida yaqame tamkar gunki kana yace gud morning sir
nafi wace tayi niyar kashe wayar domin tayi mgn taji
shiru jin an ambaci sir yasata saurarawa
morning kawai yace kana yace yaxauna xama dr bashir
yayi kana ya kalli haisham ranka yadade kana buqatar
wani abune maimakon kakirani
daga mashi hannu yayi alamar yayi shiru hakanan
saida haisham yajima shiru kana yafara magana wanda
hakan yana cikin al adarshi
inaso kanemo man wata mai irin cutata nanda kwana
kadan dan inaso inyi aure kuma wannan mgnr tazama
sirri tsaka nina dakai inhar kabari wani yaji to kasan
sauran
yana gama mgnr shi yajuya yafita ya yinda nafi murna
take tamkar tataka kan jariri shima haka dr bashir dan
yasan dole adama dashi cikin gidan birgediya general
wayarshi yadauka kinji nafi plan dinmu yayi wallahi nida
naganshi zansa yagano gaskiya zowa yayi yasa akamani
hmmm yayana kenan ai har abada bazai gano gaskiyar
ba kamanta saida nasa boka nakan dutse aiki kana muka
tunkare shi bazai taba guje makaba yaje wata hospital
din da batakaba indai har wannan kwalbarna hannuna
dariya sukasa natuna fa amma dan Allah kiqara riqe
kwalbarnan da kyau karkiyi wasa da ita tamkar ran
mune ni da ke
karka damu yayana yanxu yaushe zaka shigo musan
yadda za ai inaji kamar wurin 5:00pm
gaskiya zanfita dan inada bako asharaton hotel yanxu
nafi bakon haryafi abinda xamu tattauna yafi mana
dominshi wannan kudi zan samu kai kumafa mgnr
bakice xamiyi
barni dai yayana naje nasamu kudi nafi kinfini san kudi
wallahi
dariya tayi haba yayana nifa inaji tun ina yar shekara 9
nasan namiji
to dammi nabada kaina kaga dan kudi abin ajinina yake
shima haisham danyana da ya'yan banki shiyasa yasamu
wuri azuciyar nafi kuma ga kyau
hakane ke sainazo karki cinyeman kudin waya da
surutinki wanda baya qarewa
dariya sukasa kana yadatse wayar cikin farin ciki domin
yana ganin haqarshi takusa cumma ruwa
haisham koda yaje office kasa aikata komi yayi gashi
yanada aiki sosai amma jiyake bazai iyayin komi ba haka
dai yaita zama idan yagaji yakwanta har lokacin tashinshi
yayi yafito yatafi gida
rugar jalo
😘Ansholly😘
[3/8, 1:08 AM] +234 703 962 5239: 😭BAKAR IZAYA😭34
wannan pagen nakine yar uwa 🌷🌷sawdat ina kaunarki
nima hainan nagaisheki
😘Ansholly😘
yaune yakama sati daya da baccin hainan kowa na cikin
rugar yatashi cikin tsoro da wasu wasi har ita kanta
hainan din
domin tasan bazata wanye lfy ba uwale ce tabuga wata
uwar qara mlm zoka gani wallahi baxan yarda ba
mlm iro da sauri yafito daga cikin daki har yanacin
tuntube yayi wurin uwale wacce ketsaye wurin garken
shanun daya ce yaba dan da uwale zata haifu mashi
miya faru uwale naga shanun nan akwance tamkar basu
motsi
hmm mlm miko zai faru bayan ibinda wacen annobar
yar taka tayi kasanfa yaune tacika sati daya da baccin
datai arafi
mlm iro kuka yasa yanzu shanun dana mallaka wurin
baffan nawane suka mutu wanda sukade nake gani naji
dadi
takashe man baffan nawa takasheman inna ta amma
duk bai mataba wannan karin shanun nawa takashe ai
aradu saitaci ubanta
wannan karin nixan daketa da hannu na yana rife baki
saiga hainan tashigo gidan sai kuka take jikinta duk jini
mlm iro bai tsayaba shima yajawo dorina yayi kanta yaci
gaba da dukanta saida yaga ta sume kana ya qyaleta
yanata buga huci tamkar yayi fada da babba kamin yace
wani abu yaji makwabcinshi yana sallama
da sauri yafita A,a mlm lawai bakatafibwurin kiwanba ina
Zani kiwo bakaji yarima dan sarki ya mutu ba
mlm iro cikin kidima ya kalli lawai mikace lawai aikaji
abinda nace wanda ardo yafiso acikin yaranshi yusufa
dan amaryarshi shine yamutu
mlm iro xare hular kanshi yayi zufa nakaryo mai yana
gogewa domin yasan duk rugar nan ba wanda baisan
ardo nasan dansa yusufa ba
kallan lawai yayi to yanxu lawai yakake ganin xa ai kamin
lawai yayi wata magana sukaji ihun matarshi da gudu
yashiga gidan shima mlm iro bai jira komi ba yabishi
abaya
😭BAKAR IZAYA😭35
😘Ansholly😘
*wannan nakune masoya baqar ixaya irinsu asma u
mahamud lawai d Mira sai Nanette dake kuma qawar
alkairi maryam rimaye da duk wa yanda ban ambata ba
kuna raina ngd da kula warku*
Matar lawai suka iske riqe da danta wanda shika daine
dasu domin sunjima basu samu haihuwa ba sai ashekara
biyun data gabata kana Allah yabasu yanxu kuma gashi
zai mutu
gurin matarshi yaqarasa da sauri abu miyasa meshi cikin
kuka take magana mlm tun fitarka yake tayin wani abu
nixan sama rashin lfy ce kawai saina jika mashi itatuwa
nabashi
yanzu nashiga bayi nafito na iskeshi haka hannu lawai
yamiqa ma matarshi alamun tabashi shiyagani yana
amsarshi yasanba rai ajikin dan nashi
kuka yasa mlm iro dake tsaye tamkar gunki danji yake
uwa xuciyarshi xata buga
domin yasan annobar diyarshi ce duk taja wannan bala
in waidan xata cika shekara goma
shima hawayan yake yanaji inama tun farko baisan uwar
hainan dijah ba kara sawa kusa da lawal yayi yadafa
kafadarshi kayi haquri abokina
aje yaran kawai lawai yayi yashige daki wata zabgegiyar
dorinace yafito da ita hanyar barin gidan yayi daga mlm
iro har abu ba wanda yayi koqarin riqeshi domin suduka
sunsan inda zashi
mlm iro ma binshi yayi abaya ya yinda sukabar Abu
tanata kuka fitowar mlm iro daga gidan lawai saida
zuciyarshi takusa bugawa domin mutane yagani sunkai
goma
daga wannan yace raqumanshi sun mutu sai wannan
yace matarshi tamutu hakadai kowa ke fadin albarkacin
bakinshi
kallansu mlm iro yayi to yanxu mikukesan ayi kaminsi
mgn sukajiyo ihu acikin gidan mlm iro rige rigen shiga
aka farayi
suna shiga suka iske ashe lawaine ke dukan hainan bako
tausayi ihu take duk jikinta ba inda baya zubarda jini
amshi lawai ko ajikinshi dukanta kawai yake daya shigo
gidan ya tadda ita asume kamar yadda mlm iro yabarta
uwale naga ninshi taji wani irin dadi yama mayeta
domin tasan lawai da xuciya tasan kuma ba abinda xai
kawoshi inba hainan yazo duka ba saida taqara kallan
dorinar dayazo da ita wace in aka zugama mutum ita
saudaya dole ya sume
dan girmanta tambayarta yayi ina hainan nuna mashi ita
tayi hanyar wurinta yayi azuciye saida yada dage tamkar
zai doki dan uwanshi namiji kana ya zaula mata itace tai
sanadin tashinta tasa ihu wanda yai sanadin shigowarsu
mlm iro
dukanta yake iya karfinshi cikin mutanan dasuka shigo
ba wanda yayi qoqarin hanashi dukanta wasuma casuke
yaqara mata
duk jikinta yafashe jini kawai ke xuba idanta ne yarine
yakoma tamkar jini chan saiga jini yafara xuba daga
cikin idan
wanda suka lura da abinda ke faruwa suka juya zasu fita
da yalwa sukai kicibis asoran gidan ko kallanta basiba
sukai hanyar kofa itama cikin gidan tashige
suna zuwa kofar zasusa kafarsu waje sukaga wani qatan
zaki wanda girmanshi yawuce misali damasu ukkune da
gudu suka koma cikin gidan
yayinda lawai yana cikin dukan hainan saiyaji
*Abuja*
ANSHOLLY
Copied By
HAYATU BABA ZUBAIRU
(admin
Arewa hausa novels
Novels villa
Duniyan novels
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
And
Cool novel, makeup and cooking)
WHATSAPP NO:
+2347039625239
😭BAKAR IZAYA😭
36 to 37
😘Ansholly😘
nakine wannan page Anti ta I love you wujiga wujiga 😁
dr bashir ne shida nafi zaune a palonta kalanta yayi ce
nafi
miye gudan plan din saida tagyar xama kana tafara mgn
plan dinmu nabiyu shine xaka kira haisham kace mashi
kasamu mai irin ciwanshi kuma ka auna kaga cutar tamu
iri daya ce xan iya auranshi Idan yace maka ya akai
nasamu cutar kace mashi mijina ne ya mutu ni kuma
kabarni d sauran aikin gobe xanje wurin bokana
dr bashir murmushi yasakar mata shiyasa nace kinfini
san kudi amma dan Allah karkice inkin auri sir haisham
kindaina kulani yajawota ajikinshi
danbaxan iya haqura da jin dumin jikinki ba haba
yayana kaima kasan baxan tabayi maka hakaba nasaba
da maxa dayawa dan haka kaga namiji daya bazai
isheniba nandai suka cigaba da romance din juna
haisham tunda yadawo gida yaji wani irin kunci
nashigarshi domin daya zauna saiyaji kamshin hafsa
yasake Palo amma nanma kamshinta ke tashi duk palon
gidan ba inda bai zauna ba amma daya zauna saiyaji
kamshinta shi saima yanxu yaga chan xawar da palon
sukayi domin yaga ansharesu kana ammaida komi
wurinshi
atuna ninshi masu aikinshine suka gyara tashi yayi yanufi
hanyar dakinshi domin kamshin hafsat da yakeji yanasa
shi yaji yafara tunaninta yana tura bedroom din yaga
komi tsaf angyara wanda shi kaca kaca yafita yabarshi
domin yana saurin fita shiyasa
abin yabashi mamaki domin yasan dai masu yimasu
shara basa shiga dakinshi bathroom yawuce yana
budewa shima yaganshi tsaf sai kamshi yake dawo wa
baya yayi yasan ko bai fadaba hafsace tazo gidan ibar
kayanta shine tagyara mai daki
take santa da tausayinta suka dawo mai axuciya amma
daya tunami taimai sai yaji tsanarta amma wata xuciyar
natuna mai halayan hafsa yana ganin anya zata iya aikata
abinda akace toni miyasa banyi binkiceba nayanke
hukunci cikin gaggawa
to amma aikaje asibiti andubaka ance kana dauke da
cutar tsaki yaja yana ganin miyasa zuciyarshi take
tunano hafsa gani yake yaka mata yafidda ta daga cikin
ranshi
wata xuciyarce taqara bijiro mai dawani tunanin abinda
mahaifinshi yace mashi
to yanxu yanada tabbacin wace zai aura xata bashi
abinda mahaifinshi yace wato jika shi miyasa yasaki
hafsa aikyau yabarta suzauna atare yaita gana mata
axaba kala kala ba wanda yaji ba wanda yagani amma sai
xuciya tadi beshi yai saki har guda ukku gobe yanaji
kaduna xaima tsinke dansu dai daita da matarshi saitai
auran kisan wuta tadawo mashi kiran sallah dayajine
yakatse mashi tunanin daya ke toilet yashiga yayi alwalla
yatafi masallaci
bai dawo ba sai wurin goman dare domin yaje wurin
shugaban kasa dan suyi wata shawara duk da shugaban
kasan zaiba haisham 5 years amma suna mutunci
tamkar abokai dan kusan matsayinsu daya
tunda yadawo yakwanta amma bacci yaqi daukarshi
tunani kawai yake har asuba tayi tashi yayi yadaura
alwalla kana yatada sallah saida yayi raka atainir fijir
kana ya dauko qur'ani yafara karantawa sallah dayaji
wani wuri anfara shiyasa shi rufe Qur'anin
yatashi ya kabbara sallah domin bazai iya zuwa
masallaciba wani irin baccine ke fisgarshi yana gamawa
anan kan sallayar ya kwanta
nafi tunda asuba ta haushiri domin tanaso wurin qarfe
tara tana chan kawarta sadi tatada kina zuwa wurin boka
ko baki dawata matsala da sauri sadi tatashi xaune niko
keda matsala bari nadan watsa mutafi toilet tashige tana
fitowa tazira kayanta bawata maganar sallah sukadau
hanya cikin motar nafin civic wace taima sadi alkawarin
bata ita indai harta auri birgediya general
8:45AM dai dai suka isa cikin dajin da bokan yake dajin
shiru ba motsin komi inbanda sautin tafiyarsu daga gani
sunsaba zuwa danba tsoro suke tafiya amma tunda suka
shigo ba wanda yaqara mgn hakan nadaga cikin qa idar
bokan dan duk wace tai magana to aljannunshi zasu
tsotse mata jini dan harka shigo kafita baka magana
shine xai gayama duk abinda kakeso shiyasa suke cemai
mai gani har hanji
wani katan dutse suka nufa suna isa suka sunce kayansu
duka kana sukayi cikin dutsan tamkar fadar sarki dan
tsarowan wurin ba abunda babu harta Ac akwai
kaiwurin yatsaro iya haduwa bakacewa fadar bokaci
saikaga tsubirin kayan aiki zama sukai
suna zama wurin yakama girgixa tamkar xaya tsage wuri
biyu
wani katan mutumne yafito bakyan gani tunbinshi
yakusa hadewa da cinyo yinshi cikin aman murya yace
😘Ansholly😘
😭BAKAR IZAYA😭
38 to 39
*anti ta naga saqo nagode sosai 👏🏼👏🏼 Allah yabarmu tare*
*page nan nakine deejah siba Ansholly fans1*
😘Ansholly😘
lawai yana cikin dukan hainan saiyaji tamkar ankarya
mashi hannu ihu yasaki atake yasaki bulalar kasa bulalar
tatasu dakanta tatafi hannun hainan
su mlm iro naganin haka sukayi hanyar waje domin
dama sallamar yalwace tadauke masu hankali
kicibis sukayi dawa inda suka fara fita suna ganin su mlm
iro suma suka koma baya sunasa qafa zasu fita sukaga
wani qatan zaki tsaye sukai sun rasa yazasi gashi kuma
sai ihun lawal sukeji ga dukkan alamu hainan bakar ixaya
take gallaza mashi
wanine yaga daya koma cikin gidan kara yafada ma zakin
nan dan gani yake tamkar rufa idone ake masu baiyi
shawara da kowa ba domin yanaso yafita inya gansu yayi
masu dariya dan yana daya daga cikin wa inda ke
tunxura lawai wurin bugun Hainan
cikin jin dadi yasa kafarshi waje yana fita yaga ba xakin
juyowa yayi yana dagama su mlm iro hannu yana masu
dariya sukuma sunyi tsaye carko carko kamar xakaru
cikin fargaba domin xakin nan suka gani yayo kanshi
ganin dayayi ba wanda yabiyo shi kana fuskarsu da
tashin hankali cikinta kuma bayanshi suke kallo yasashi
juyawa
abinda yagani shiyasa shi faduwar gaba da sakin zawo
awando dagudu yayi hanyar komawa cikin gidan amma
gani yayi qofar tabace mashi ya yinda su mlm iro suna
kallan duk abinda yake faruwa saidai ba damar tai mako
taku daya zakin nan yayi ya iso gurinshi yana ihu yana
komi xakin nan yai fata fata da naman shi yalwa kuka
tafashe dashi itada uwale hakanan tana zaman zamanta
tace bari tataho gidan uwale gashi yanxu tajama kanta
bala I
ganin da sukai zakin yayo kansu yasasu komawa cikin
gidan ba shiri suna shiga gidan yadinke da duhu
maitsanani wanda ko tafin hannunka baka gani kamin
suyi wani yinquri
duka sukaji kota ina suduka ihu suke yalwa da uwale dan
tsananin ixayar da ake gana masu kukan ma bai fita sosai
abinda yabasu mamaki duk iya ihun da suke tamkar
xasu hargetsa gari amma ba wanda yakawo masu dauki
ya yinda cikin rugar kowa yamanta da akwaisu matar
lawai tama manta ina mijinta yayi haka yan uwanshi ba
wanda yai maganarshi iyaka amma yaro wanka anje
anrife haka gidan sauran sha aninsu kawai suke sunma
manta sunada wasu yan uwa
ihun da lawai yayine yasa hankalin sauran dawo wa duk
da wurin yayi duhu dayawa
da sannu duhun yasoma yayewa lawai suka hango
kwance rai ahannun Allah ga dukkan alamu suma yaye
hainan sukaga tayi kanshi tana dariya idanta nazubar da
jini
daga bulalar hannunta tayi wace suka gani tamkar
anqara mata girma tashau da mashi cikin firgici yatashi
kamin yai wani motsi tafisgeshi tawurga shi cikin su
yalwa kara yasaki wace ga dukkan alamu kafarshi takare
ganin da sukayi tayo kansu yasasu shiga taita yinsu
bakamar yalwa wace tasan xafin dukan hainan tun tana
yarinya ma to ina gayanxu ta girma
ya yinda mlm iro yaqara gyara xama yasan dai bazata
dakeshi ba tunda shi ubanta ne har cikin zuciyarshi
yanada wannan yaqinin dan yasan daxuma data hada
harda shi tadaka dan yana cikin duhu
saukar bulalar dayaji ajikinshi itace tasashi shedewa
wanda saida tuna ninshi ya dauke nawucin gadi kamin
yadawo daga tunanin yaqara jin wata aituni yai kasa
sumamme
wata bulalar yaqaraji wace takusa sanadin fitar
numfashinshi ga dukkan alamu bataso tana dukan
mutum ya suma dumin inka suma to wacce xataima
saikaji inama baka sumaba
suduka dukansu take tamkar tasamu jakkai duk jikinsu
yai jina jina amma ba alamar tausayi ko gajiya awurinta
Dan dariya ma take abun mamaki gata ita kadai ke
dukan amma suduka jisuke ana zaula masu bulala
cikinsu ba wanda bai samu tijaba ga jini nazuba tamkar
anyanka dabba mlm iro ko yafita haiya cinshi sosai dan
tunda yake duniya bai taba shan bakar ixaya irinta yauba
bama amaganar su uwale domin da qyarne incikin da
ake taqama dashi bai zube ba
yalwa kamtasha ixaya dan yau harta iyayanta sunsha zagi
da suka haifota dantana ganin dabasu haifotaba
baxatasha
wannan bakar ixayar ba sai kuma uwale wace tace
abuta da ita takare koda itace tarage mace daya aduniya
*Ansholly*😭BAKAR IZAYA😭
40_41
😘Ansholly😘
*wannan pagen nakune masoya bakar izaya ina godiya
da kaunarku*
*today I'm very happy welcome home baba buhari
Allah yaqarama lafiya mai amfani yakareka daga sharrin
maqiya*
cikin aman murya boka yafara mgn kinxo adai dai
domin dabaki zoba to asirinku nagab da tonuwa dan yau
yai niyar zuwa garinsu wurin matar daya saka
dayaje zata fada mashi itabata da aids kinga xaiyi bincike
sosai kuma dole ne yagano ku
hotan haisham ne yamaye duka bangon dakin tamkar
ana kallo yana zaune yana daura agogo acikin qaya
tatcen bedroom dinshi kallansu boka yayi kana yafara
magana acikin muryarshi marar dadin sauraro
kunga wannan shirin dayake yi to xaije wurin tsohowar
matarshi ne amma tunda kunxo yanxu zan dakatar dashi
wasu surutai ya shigayi cikin lokaci kanqani saiga wani
dan yaran aljani yazo jikinshi duk jini
bokan yafara yima wannan aljanin magana tareda nuna
mashi photan haisham kaga wance nakeso kaje
kamantar dashi matarshi karya qara tunaninta koda
sunanta yaji bazai iya tunataba
kana inka gama aikinka zasu baka jini jinin yarinya
kakeso kona babba da hannu kawai yaima bokan alama
yabace bat shi bokan yasan komi yace
juyowa yayi wurinsu nafi kunasan kuce miyasa nace
abatar wa haisham tunanin hafsa to hafsa kadaice wace
xata tuna maku asiri kuma baxata iya zuwaga haisham
ba harsai inshi yaje gareta
domin munsa mata wata katanga tsakanunsu
yau zamu tunxuroshi yazo gareki kisa manyan kaya kiyi
shigar mutunci kana xamu mantar dashi cutar dake
jikinshi domin bikinku yayi dadi inba hakaba bazai
yiwata hidima ba
domin abun nadamunshi azuciya wani maganine yaba
nafi karbi hannu naqerma takarba wannan inyazo kamin
kifita kitabbatar kinyi wanka dashi wani yakuma miko
mata da kwalli da turare wannan turaran inhar kika
shafashi yaji kamshin shi to soyayyarki xataimai dirar
mikiya
wannan kwallin ko inhar kika shafa karki kuskura kikalli
wani inbashi ba akwai qalo bale wurin iyayanshi dan
haka dole kikoma wurin uwarki kamin lakacin
nafi mgnr boka tabata tsoro totaya zata koma wurin
mutanan da shekara goma yanxu bata qara wai wayarsu
ba tasanma bazata karbu garesu ba
bokane yakatse mata tunanin datake kidaina tunanin
cewa basu karbeki ba domin kina dani kina cika mana
duk alqawarin dakika daukar mana dan haka aljani dan
kundalo yana tare dake
nafi batayi mamaki ba jin boka nazai yano mata abinda
take tunani domin tasaba jin abinda yafi haka indai
wurin boka maigani har hanjine
wani magani ya bata mai kamar turare dakin dauki
hanyar garin naku to kishafa wannan ba abinda suka isa
suce maki
kallanshi yadawo dashi kan sadi da idanuwan shi masu
firgita mutum babu wani alheri acikin tarar yaki da
wanda kika kawo nan dan tunda kuka hadu

Please Login or Register in order to submit comment