Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ikrarin baka sona to ka sani nima haka.Yace ashe ilimin da kike ikrarin kina dashi karya ne,don mace mai ilimi iyakacin sanina(koda dai kince ni jahili ne)bata gudun mijinta,matsawar yana matsayin mijinta dolenta ne tayi biyayya ba maganar so agurin,don haka kiyi yanda nace,in kinki zamu gwada kashi duk da kince(yaushe kashina yayi kwari?)domin dole ne na banbance miki tsakanin babba da yaro,ni dake yau dinnan ba sai gobe ba,duk da faduwar da gabanta keyi bata fasa cewa baza‘a cire kayan ba kaji ko,salon kaje ka goga min cuta,fasiki kawai ban cire kayan ba kuma bazan cire ba ban dama rashin kunya har ma ka dubeni kace in cire ka....saukar marin data ji babu zato tana ta masifa shine ya katseta,lokaci daya ya saka kafa ya kwashe ta,ta yunkura zata taso ya sake sa kafa ya maida ta tare da fincike hijabin jikinta.Sun sha kokawa amma ga mamakin Bily Yarima kyaleta yayi take kici-kicinta,don daya tashi lokaci guda ya murdeta sannan ya yaga rigarta haka nan bada soyayya ko lalama yake son maida ta mace ba irin yanda take karantawa cikin littattafai ba,a‘a fyade yake nufi don haka sai ta bar mutsu-mutsu domin ta samawa kanta sauki ta sadakar sai kukan zuci da kiran Allah.Shi ko Yarima duk da ya fahimci budurwace matar tasa sam cikin zuciyarsa babu nufin rangwame,haka nan gyaran da aka mata zuwa kamshinta sun kara taimako gurin fidda shi daga cikin hayyacinsa,har ma ya kasa tuna dawa yake tare illa sunayan ‘yanmatansa da yake kira hakan ya kara ma Bily bakin ciki,ta shiga rera kuka.
[4:23AM, 12/28/2016] ‪+234 814 912 1821‬: 🏵MEKE FARUWA 49🏵

Abin mamaki mintina suka shude bayan wucewar sakwanni har aka shiga awa itama ta shude kai har amarya ta kasa fahimtar shin aduniya take ko ko a lahira?Kuma bacci takeyi koko ta mutu ne?Ma‘ana ta sume gogan bai san ma me take ciki ba har zuwa uku da rabi inda ya samu sukuni na kyaleta ba tare daya ko kalleta ba ya shige toilet jikinsa ya gyara sannan yazo ya haye gadonsa ya barta nan yashe bacci mai nauyi ne yayi gaba dashi cike da nishadin da yake ji na daban wanda tunda yake harkarsa da matan banza bai taba jin hakan ba.Sanyin asubahi ne ya farkar da ita,dishi-dishi ta soma gani kafin daga bisani idanunta suka washe,daga inda take yashe tana hango Yarima tsaf cikin gadonsa yana sharar bacci fitilun tsakiyar gado sun haske masa fuska,bakin ciki ya cika zuciyarta tayi ta kokarin yunkurawa ta tashi ta kasa dole ta hakura jim kadan ya farka cikin mika da salati tana kallon bakinsa yana karanta addu‘ar tashi daga bacci,sannan ya sakko ya tsallaketa ya shige toilet.Ruwa ya watsa tare da alwala sannan ya fito ya saka fara kar din jallabiya ya fita duk abinda yakeyi yana yinsu ne akan idanunta amma ko kallo bata ishe shi ba.Ta tuna da Mansu kawarta daren Mansu na farko da Faruk,Mansu tace kwana yayi yana lallashina, sannan da sassafe jiki yana bari yazo ya daukar mata Bily yana ta faman tarairayarta haka nan cikin littafai inta karanta mazan kan rasa inda zasu sa kansu,amma ita dubi abinda nata mijin yayi mata,sam bata son tunawa da daren farkonta zuwa shida na safe ta danyi karfin hali ta mike zaune ta jawo rigarta wadda duk ya yaga mata gashi duk rigar ta baci da jini haka nan ta zura ta dafa bango da dafa bango ta fito falo yana zaune yana kallon aljazira ya ganta tana kokarin fita,ya mike da sauri.Ke kina hauka ne zaki fita ahaka?Ko kallonsa bata yi ba taci gaba da laluben hanya,da sauri ya kulle kofar sauka kasan,sannan ya zauna ya dauko waya ya soma kiran layin Umma,bayan sun gaisa yace ta turo masa jakadiya Kamar minti goma jakadiya ta soma kwankwasa kofa,ya bude sannan ya nufi kujera ya zauna tana shigowa taci karo da Bily daf da kofa cike da salati jakadiya tace ‘yannan lafiya?Ta riketa tace,zomu koma ciki.Bily ta girgiza kai alamar a‘a,jakadiya tace yi hakuri ranki ya dade,ai ba kya fita haka ba.Ta rike ta suka juya tana cewa ikon Allah, a garin yaya akayi haka? Yarima dai volume din TV ya kara suka koma ciki. Haka jakadiya ta gargasawa Bily jiki,cikin katon bahon wankan na Yarima,kafin ta nufi sasan Bily don kawo ma Bily kayan da zata sa.Ita kuma Bily tayi wankan tsarki sannan ta daura tawul,jakadiya ta kawo mata kaya ta fita doguwar riga ce baka ta zura sannan ta fito duk jikinta babu karfi,jiri ma take gani.Jakadiya ta nado rigar baccin ta saka cikin leda sannan ta dan rike Bily suka fita kai tsaye dakin Bily suka nufa take cewa ikon Allah,wai gaddama kika masa ne har haka ta faru ni laraba?Bily dai shiru tayi.Jakadiya taci gaba da cewa,banda abinki yanzun wa ke yayin wannan?Yara kanana ma irin na kauye in an kaisu daki shiru kake ji tsakaninsu da miji bakaji ba ka gani balle ke da girmanki da iliinki kuma kinsan su maza ba kunya ce dasu ba,gashi ma shine ya kira azo a dubaki.Bily dai tana jinta,kala bata ce ba.Ta kwanta akan gadonta,sannan jakadiya ta fita,gurin Umma ta nufa tana zaune kan sallaya hannunta rike da carbi tana lazimi,jakadiya ta zauna gefe sannan tace ranki ya dade na dawo daga kiran na Yarima ta cira rigar baccin cikin leda tare da fadin Ubangidana yayi sa‘ar mace ‘yar gidan tarbiya,ranki ya dade amarya ta kawo budurcinta gidan miji.Umma tace,kai to menene kuma Yarima bazai bar ma cikinsa sirrinsa ba?Ai yanzu an daina wannan abin ilimi ya ratsa ko‘ina.Jakadiya tace ranki ya dade abinne yazo da matsala,dole ya nemi taimako,yarinya ce tayi gardama ne nake ga shi kuma dan yau babu hakuri,wallahi karki ga yanda yarinyar nan tasha wuya jini kyace an yanka karamar kaza,tana can kwance babu yanda take Umma tace to yanzun bari inyi ma Doctor Aisha waya tazo ta dubata Ke kuma kije ki sanar da masu aiki su shirya mata farfesu na kaji dana kan sa ko ta danji dadin bakinta.Haka ko akayi,doctor Aisha ta samu Bily kudundune cikin bargo kuka kawai takeyi,ta duba ta likitar da kanta ta hada ma Bily tea tace tasha don za‘ai mata allura ne.Bily ta dan sha sannan ta mata allura tare da bata magunguna duk na gajiya ne,tare kuma da huce radadi,haka nan ma likitar tayi mata mita kan cewa mai yasa bata ci abinci ba kafin mijin nata ya kusanceta?Shiru Bily tayi,doctor Aisha tace rashin cin abincin ya taimaka gurin galabaitar dake sannan kinyi kokarin hanasa kanki,kin matse jikinki har ya kaiga ji miki rauni.Cikin kuka Bily ta kwanta tama tsani yanda suke cewa ta hanasa kanta,basa ma tunanin koda ace ta hanasa kantanne ya dace ya bita asannu,bacci yayi gaba da ita wanda dama bata same shi ba jiya.Biyu da rabi ta farka kamar acikin mafarki taga Mansu da dady da Asma‘u,suna ta shan farfesu,da sauri ta tashi zaune jikinta ya daina ciwon sai dai ta jita fayau babu kwarin jiki,ta sakko tana cewa Mansu yanzun kika zo?Mansu tace tun dazun,munzo kina bacci muka je gurin Umman Yarima,Bily tace zo nan dadyna yazo ta dorasa kan cinya tana cewa,ina Abbanka?Ita ko Mansu dariya take ta kunshewa har dai Bily ta gaji tace wai dariyar mecece haka?Mansu ta dubi Asma‘u tace,auta keda dady kuje falo kuyi kallon cartoon suna fita Mansu ta koma gefen gado kusa da Bily tace aminiyata Umma tace baki da lafiya duk rigimar kin bar Mamanmu ne ko?Bily ta soma hawaye ta kama hannun Mansu tace,wallahi ba kukan rabuwa da Mama nakeyi ba,dama yaushe rabona da Maman da aka kaini aka tsare kamar nai sata,tasa yatsunta ta matse idanunta,sannan taci gaba wannan mutumin ne yayi min wani mugun wulakanci,wallahi nayi dana sani sosai na sanin Yarima bama aurensa ba.Mansu tace wane mutumi?Bily tace Yarima nace miki.Mansu tace hala ya zazzageki ne?Bily tace ba gara ya min duka bama da fyaden daya min,wallahi har suma nayi kwana cur yana aikin abu daya, wallahi ni bazan iya wannan bala‘in ba.
[4:26AM, 12/28/2016] ‪+234 814 912 1821‬: 🏵MEKE FARUWA 51🏵

Yarima yayi murmushi dama so yake ya kunna Magaji,kuma yayi nasara.Ya dubi Bily sannan ya wuce tare da cewa,wa ma sunanki? Biyo ni tace,Hum sannan tabisa ranta fal kunci gurin Umma suka soma shiga ta zauna gaban Umma kanta akasa tana gaida Umman,ita ko Umma Allah ya dora mata son Bily,don haka ta jawota jikinta tana cewa matso nan ‘yata,yaya jikin?Cike da kunya Bily tace da sauki.Yarima ko cewa yayi da Allah malama taso in kaiki ni sauri nakeyi,Umma ta daure fuska ta dubesa,bai sake magana ba,Umma tace babu inda ke miki ciwo ko?Tace a‘a to kina bukatar wani abu?Nan ma tace a‘a,har ta mike zasu fita Umma tace,amm Bily babana dai baya miki wani abu ko?Da sauri ta dubesa ya ko banko mata harara ta kautar da kai sannan tace ba komai Umma,tace ki gaya min in dai da matsala,ba komai Umma cewar Bily,tace to zanba jakadiya sako ta kawo miki,tace to suka fita duk tausayin Bily ya cika ta don taga hararar da Yarima ya mata da alama tsoransa takeji.Sun zaga ko‘ina sannan Yarima yayi hanyar fita ta bishi ta zata nan ma wani sassan ne,ya dako mata tsawa ke!Dabba ina zaki bini?Ta ja ta tsaya,sannan ta juya azuciyarta ko fadi take,ina da aiki.Daki ta koma ta hau gado tana karanta addu‘ar yaye kuncin zuciya,nan take taji zuciyarta ta wanke tayi fes,kuma tun daga ranar kullum sai taje ta gaida su Umma,Umma tana nuna mata kauna sosai.Yarima zaune agaban mai martaba yana cewa ranka ya dade,gobe ne ya kamata in koma makaranta, domin tun wancan satin muka soma karatu.Mai martaba ya gyara zama sannan yace to madallah,sai ka sanar da iyalin naka ta shirya ko?Ko ka shaida matan?Yarima ya danne damuwarsa na zaci nan zata zauna?Saboda karatuna yana bukatar nutsuwa.Mai martaba yayi dan murmushi,sannan yace yaro,yaro ne yanzu kai dama baka fahimci don ka nutsun bane nace lallai ina bukatar kayi aure?Ya dafa dan nasa kada ka damu Modibbo, yanzun ne ma zaka samu nutsuwa yanda ya kamata kuma kayi karatunka cikin nasara,tashi kaje Allah yayi muku albarka maza ka sama mata biza kaji ko?Yace to na gode ranka ya dade,ya fita zuciyarsa fal kunci
[4:28AM, 12/28/2016] ‪+234 814 912 1821‬: 🏵MEKE FARUWA 52🏵

Haka ya shigo pallon umman shi rai bace Bily yana ta fadin shi gaskiya an takura mashi tare da nuna billy wai umma da wannan abun zan tafi ai kau umman ta hau shi da fada sosai ita ko billy kanta na kallon kasa tana ta sharar da hawaye, Yarima ya mike ya fita Bily ta daure ta dubi Umma tace Umma nima nafi son abarni anan.Umma tace a‘a Bily banaso kice komai kinji ko,ke dai kiyi ta hakuri sannan kici gaba da addu‘a,share hawayenki kinji ko?Nan take tace to Umma,Yarima ya rasa yanda zaiyi dole shi suka je shi da Magaji suka kammala mata komai,yana ta zafin rai,ai ko suna dawowa har daki ya same ta yayi mata tatas,yace in har kika bini dama kisan kin nemi maganin hawan jini dana ciwon zuciya,don kam kaken dana miki yanzun ne zaki gane dalili,sannan in har kika sake, kika tafi da wata kuyanga bana ji ana wani cewa ai musu biza ba tun cikin jirgin zan turo ki in huta,kinsan zan iya banza wawuya ‘yar matsiyata ya fita,kukan da Bily tasha ranar babu iyaka daga karshe dai ta hakura ta kira Mansu ta gaya mata komai,Mansu ma hakuri dai ta bata,Bily cikin kuka tace,Mansu yaushe zanji dadi ne irin na kowa?Wai ni MEKE FARUWA dani ne?Haka zan dawwama Mansu,wallahi dana so aure saboda kuncin rayuwar gidanmu amma yanzu ga aure ga daula amma gara zamana na gidanmu gara ina gaban Mama su Gwoggo Ladiyo suyi ta min gorin yafi min yanzun.Mansu ma ta soma kuka tana cewa kiyi hakuri wata rana sai labari,haka suka yi sallama zukata abace.Sai da tayi kokari ta natsu sannan ta sake kiran Mansu tace mata ki kula min da Mamanmu.Mansu tace,kinsan wannan dole nane,ko baki ce ba,ni dai fatana ki kwantar da hankalinki duk me ya miki ki daure ki sama ranki cewa kina ibada ne,kinsan kuma bautar Allah sai da hakuri na sani kin sani no condition is permanent. Allah ma ya fada cikin Alkur‘ani kowane tsanani yana tare da sauki,lokaci yana zuwa da zakiyi dariya aminiyata cike da jin dadi Bily tace na gode Mansu,naji dadi insha Allah maganganunki zasu zamar min abin tunanina, duk lokacin dana shiga kunci,sukayi sallama katan guda biyu cike da begen juna. Yanda taga rana haka taga dare, tunani ne ya cika zuciyarta MEKE FARUWA da ita?Me yasa bata da sa‘a ne ita arayuwarta?Duk yanda Mamanta tasha wahala kanta ta kyautata rayuwarta taso kwarai ta samu mijin da zai kula da ita da mahaifiyarta,amma sai gashi wani can wanda bai san kimarta ba marar tausayi mara imani wanda in aka tsare sa koda bindiga ba zai nuna mahaifiyarta ba ya aureta ya kuma sameta abudurwa bai ko kula da hakan ba,wanda ada ita taci buri sosai akan budurcinta,domin tasan abin alfahari ne sai gashi amma shi ya keta ta ba tare da yako juya ba.Shin wane zama zasuyi a Malesia?Tasan sai tayi hakuri tasan zai bi mata,tasan sai dare zai dinga dawowa,tasan yana zuwa club,kila ma wata rana yazo mata a buge, tunani dai barkatai,lallai ta bakin nasa ta nemi maganin ciwon xuciya. Tun shigowarta gidan yau ce rana ta farko da taga ainahin gidan,mutane tankam an fitar musu da kaya,Umma dai tana ta nanata mata cewa,lallai in taji yaya ne ta kirata ta shaida mata,shi kuma taja masa kunne cewa ya kula da ita don ita din amana ce agaresa,kuma ta yabesa da cewa dama kai mai alheri ne,don haka ka lura da ita ka wadatata nan ya tuno da batun Modibbo jiya da yaje masa sallama,yace takwarana don Allah ka lura da matarka sosai,ka sani yanzu ka shiga wata rayuwa ce mai daraja kuma kaima ka zama cikakken mutum,yanzun ka kula da karatunka banda shirme.Yarima yace,insha Allah na kuma gode,an raka su zuwa filin jirgin sama inda Bily ta kara yarda Yarima dan gata ne,saboda ‘yan rakiyazuwa jami‘an tsaro ne,suka shiga jirgi zuciyarta cike da addu‘ar hawa abin hawa,inda Yarima ya zauna kusa da wani tana ta hangen inda zata zauna kusa da mace ‘yar uwarta tunda shi bai damu su zauna tare ba,don haka sai ta zauna ita daya akujerarta,wani kuwa yana shigowa ya zauna kusa da ita tare da gaishe ta,ta amsa tana satar kallon Yarima,don suna gabansa ne shi kam ko kallo bata isheshi ba,haka nan da jirgi ya tashi mutumin nan ya dameta da surutu har dai ta gaji ta soma baccin karya.
[4:31AM, 12/28/2016] ‪+234 814 912 1821‬: 🏵MEKE FARUWA 53🏵

Kai jama‘a!Anya mutane ana cewa babu kudi babu kudi,shin gaske ne?Gidansu take kallo tana fadin haka cikin zuciyarta tana tsaye tsakiyar falon gidan Yarima tana kallon tsarin falon irin dai gidajan da take gani cikin fina-finan turawa ko mujallarsu. Yarima ya nuna mata dakinta yana kusa dana sa ne,ta shiga gado ne madaidaici sai durowoyi wordrop da dai dan sauran abubuwa,ta kintsa daki duk da dai bashi da datti,ta shiga bayin karami ne ta tsaftacesa sannan tayi wanka da alwala wata tsohuwar baturiya ta shigo tana dauke da tire,tarkace ne ita jus din kawai tasha sam bata san wannan tarkacen ba,har wayewar gari bata fito ba,tunda tana da bayi kuma tazo da dambun nama dana kifi wanda Umma tasa akayi musu don haka bata da matsala,dama bata yi zaton Yarima zai nemeta ba,kuma hakance ta faru.Da safe ta lalubi kitchen taje shima ya tsaru,madam Dora tana ta ‘yan aikace-aikacenta suka gaisa,Bily ta soma hakilon neman abin karyawa,tea ta hada ta soya kwai babu ko bread taci kayanta ta koshi anan kitchen din take suna hira da madam Dora inda madam din take shaida mata cewa tana da kyau,shin ita ‘yar wace kasa ce?Tace mata ‘yar Nigeria ce,sai tace oh,ta manta dama Prince ya gaya mata cewa ita kanwarsa ce.Bily batayi mamaki ba tace,eh hakane.Madam Dora tace dan uwanki yana da kirki sosai,tun farkon zuwansa nan kasar nake masa aiki ni da sauran ma‘aikatan yasan darajarmu yana mana adalci.Bily ta danyi yake tace ai hakane halinsa yake,tace koya sunanki? Bilkisu inji Bilyn ta shaida mata madam ta kasa sai dai Bikis haka ko taci gaba da kiranta.Da dare tana zaune afalo tana kallon wani fim,zuciyarta ko tana tunanin cewa tunda suka zo bata ko saka Yarima cikin idanunta ba,sai gashi ya shigo kamar ta share shi,sai dai ta daure tace masa sannu da zuwa tamkar baiji ba kuma tasan yaji don haka ta share shi kusan awa daya ya fito cikin ‘yar T-shart fara da 3 kwatan wando ya nufi kitchen mai hade da dinning room.Can dai tana zaune sai taji wani abu yana kara,ashe intercom ne sai taga madam Dora tazo ta bude.Wata mace ce ta shigo tana sanye da siket da iyakar cinya,sai ‘yar bes kana ganinta kaga chanis,suka gaisa da madam sannan ta nufo ciki tana tambayar madam ko prince na nan?Madam tace yana dining room can ta nufa,madam tazo tayi ma Bily sallama da cewa zata gidanta don basu da nisa,Bily tace to mu kwana lafia sai dai tanayi zancen ne kawai amma zuciyarta na gurin su Yarima,shin wacece wannan?Jim kadan suka jero ita da Yarima suna ‘yan hirarrakinsu,suka zube nan falon.Tamkar a fim ko cikin mafarki sai ganin Yarima tayi yana wasanni da wannan macen,sam tamkar basu san da mutum agurin ba.Kasa jurewa tayi ta mike ta shige dakinta kan gado ta fada,har yanzun bakin Yarima take gani cikin na wannan matar, tasan bata son Yarima amma dole ne tayi kishin mijinta.Kai ko ba mijinta ba ba zata so taga wani musulmi yana kusanta kansa da zina ba,bare har ya aikata.Tasha kuka daga baya tayo alwala ta soma nafila tana kaima Allah kukanta.Washegari ko da safe misalin goma tayi yo kwalliyarta cikin super riga da zani tayi kyau,tana zaune kan dining tana karyawa ya shigo cikin shirin makaranta.Madam dora ta mika masa dan kofi da plate coffee ne aciki yana sha,suna gaisawa tana masa korafin sister shi tafi son tayi girki da kanta,yace eh ko gida ma haka take.Madam tayi ‘yar dariya sannan tace kuma Bikis tana da kyau,sai ya fita daga kitchen din yana cewa,chelen tana jiransa bari yaje.Can hanyar fita ya nufa,sannan ya aje kofin da plate din ya tafi abin tsoro mata gidan Yarima wasu suna shigowa wasu suna fita,kuma karka ga yanda yake wani shassha musu kamshi,abinda kullum ke bata mamaki har yau da take satinta daya agidan bai taba mata koda magana ba kuma koda ta gaishe shi baya amsawa, haka nan baya damuwa ko agabanta ne yayi yanda yake so da ‘yanmatansa hakan nan in sun nemi sanin ko ita wacece agabanta zaice kanwarsa ce.
[4:35AM, 12/28/2016] ‪+234 814 912 1821‬: 🏵MEKE FARUWA 54🏵

Hankalin Bily bai gama tashi ba,sai daran ranar data cika kwana goma a kasar.Ta fito zata kitchen saboda tana son tashi da azumin alhamis,me zata gani?Yarima ne da mata guda biyu tamkar zasu cinyesa,kowace tana son nuna masa karshen soyayyarta,kuma tana son burgesa har ya juyo gurinta,cikin tsananin tsoro tace, A'uzubillahi minash shaidani rajim.Suka dubeta su biyun banda Yarima wanda ya rungumo su duk da ya ganta juyawa daki tayi ko ganin hanya batayi don tashin hankali cikin sanyin jiki ta zauna tama rasa wane tunanin zatayi ne?Kodai don bata kai kanta garesa ne yake kawo su gida don ya bata mata rai?Inko haka ne ai gara ta kai kanta gurin nasa koda zai riga mata fyaden ne in dai zai daina kawo wadannan matan masu kama da bebyn roba ta sani ba sun fita kyau bane ta sani ba wai tana son Yarima bane sai dai tasan in don rashin zuwa gurin Yarima ne yake zuwa ya kawo mata,to tabbas tana da kamashon zunubi,kila ma nata yafi nasa.Tabbas Yarima baiyi kuskure ba daya ce ta nemi maganin ciwon zuciya dana hawan jin,har gari ya waye tana tufkawa tana warwarewa.

Yaya batun su Mamanmu? Duk wanda ya auri boka da ‘yan tsibbu lallai yana cikin dimuwa ba kuma zai gane ba,har sai ranar da karya ta kare,ga dai su Ladiyo nan anata fama yanzun ma da suke zaune gaba dayansu acikin dakin Karima suna tattaunawa ne akan duk malaman da suka je gurinsu,Salame tace abin kamar hadin baki malaman nan sunce mana inma an daura auren kwata-kwata ta dade tayi sati daya agidan mijin zai koro ta amma gashi yau mun shiga sati na uku.Ladiyo ta gyara zama ga kuma tsohon ciki tace yanzun ko bacci bana iyawa tunda akayi auren nan kullum ina raba idanu ne inga ta shigo gidan nan wutsiya zage,bani da buri sai na ganin bayan Bily.Karima tace kedai bari Ladiyo wallahi baki kaini ba,Ladiyo tace um um daina cewa ban kaiki ba,ni nan da kika ganni ko wannan cikin na jikina bana tunanin ranar haihuwarsa kamar yanda nake tunanin auren nan na Bily gashi kuma shiru. Salame tace mu koma mu sanar dasu aiki baiyi ba.Ni damuwata ma daya yanda mai adashen nan ke ta min sintiri naci na kasa zubi kudin da sune na bada muka kai gun malaman nan yaya tazo tana neman abin dauka, nace indai bani zaki dauka ba,ko yara ga sunan kwancar bani da wani abu dazan iya baki gaki dai ga dakin,in kinga abin dauka to dauki.Duk suka sa dariya,Ladiyo tace nima gado ne kurum yanzu ya rage min,Karima tace wa ma zai sayi wannan gadon naki,ko‘ina kudin cizo yayi kashi.Ladiyo tace eh,in zan saida ai dama wanke sa zanyi. Salame tace ai ko yaci klin din dari biyu dukkansu suka sa dariya,tace mu bar dariya mu fuskanci matsalarmu fa?Haka ko sukayi,washegarin ranar suka shiga mota suka nausa.kusan duk bokayan sunce musu kada su damu,aikin zaici ahankali. Shiko asalin bokan nasu cewa yayi yana zaton ma fa anyi sakin kila uwar yarinyar taki yarda su sani ne,sannan takai yarinyar gurin ‘yan uwanta.Ya kara musu da cewa haba ku sai kace ba mata ba?Ku kanku ma fa sharri ne mai zaman kansa cikin irin siyasarku ta mata da kissa ai kwaji koda gurin mijinku ne.Kai ita kanta yanayin amsar da zata baku zaku iya ganewa, suka ce hakane.Ladiyo tace malam sai dai fa maigidanmu da kake cewa zamuji gurinsa wallahi yanzun ya juya mana baya tunda yarinyar ta samu dan sarauta shikenan duk ya birkice mana.Malam yace a‘a kuce akwai sabon aiki kenan,to kuna da kudi ko?Suka ce zamu nemo, amma don Allah ai mana aiki mai kyau,yace musu don wannan kada ku damu,an gama kuzo dai da dubu takwas,sannan da kaji biyu.Suka ce to sun gode,sannan suka muke suka dauki hanyar gida.Allah kasa mufi karfin zuciyarmu, amin. Suna shigowa gidan sun samu Mamanmu zaune tana yiwa auta tsifar kai,nan suka kyafta ma juna ido alamar su bigi cikinta,don haka sai suka hada baki gurin yin sallama.Mama ta dubesu ta amsa,sannunku da dawowa suka ce yauwa. Karima tace munje barka ne matar wan Salame,cike da fara‘a Mama tace,Allah sarki to Allah ya raya,ai da kun gaya min da munje. Salame tace umh ni ai gani nayi na gaya musu bikin Bily sunki zuwa, shiyasa nace bazan gaya miki ba tunda abinba tsoro bane,su basa son zuwa
[4:36AM, 12/28/2016] ‪+234 814 912 1821‬: 🏵MEKE FARUWA 55🏵

Amma suna son aje musu.Mama tace,kai sai kace bin bashi?Ai lada ne in naje din,to Allah ya raya suka ce amin.Ladiyo tace,auta anata shan tsifa ne?Mama tace eh wallahi kin ganta nan kitson tunna bikin maigado taki tsefe sa,taje tasa anmata kitso yangu-yangu kuma sai da nace kar tayo kanana,amma da yake tana da kunnan kashi sai da tasa aka mata shi.Ladiyo tace ai duk haka suke,itama uwata gashi nan dama ita ba gashi ba yana nan kan duk yayi dugu-dugu ni dai ai bani da lokacin tsifa.Mama tace nifa tunda taki tsefewa ai tasan tawa tsifar sai na fece kai tas ta mun kuka in nade ta.Salame tace da kina can gidan amarya ai da kin huta.Asma‘u tace ba Mama ce tace adawo dani ba.Karima tace,ina ruwan amare,ana can dai.Duk suka kalli Mama suga yaya fuskartata zata nuna?Mama tace,um suna can,sun ma tafi ni wacce kasa ce inda mijin ke

1 Comments On ME KE FARUWA
avatar
fatima-8-5

1 year ago

Reply

Uhm

Please Login or Register in order to submit comment