Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[8:45AM, 12/28/2016] ‪+234 814 912 1821‬: 🏵MEKE FARUWA🏵

Yana kwance cikin tafkeken bahon wankan da ke cikin tsfkeken bayin, Sam bai yi kama da bayi ba, domin yana da girma kwarai. Bahon kato ne haka nan daga inda bahon kana iya kallon TV manne jikin bango can daga nesa kadan ga gurin da zaka zauna don yin bahaya (toilet) tsararre ne mai tsafta.
Kwance cikin baho Modibbo ne, daga in da yake cikin bahon da ya cika da ruwan dumi da kuma ruwan sabulu mai shegen kamshi yake canza tashar da yake kallo zuwa (CNN) daga inda yake yana jiyo karan kawankawasa kofar bayin. Shin wanene? Ya tambayi kanshi amma ci gaba yayi da kallonshi. Da ya tuna duk Wanda ya matsu ya jira shi kusan rabin sa'a sannan ya soma cuda jikinshi, ya cire abin da ya toshe rariyar da ruwan ya tsiyaye sannan ya kunna wani dake zubowa daga inda aka rataye su ya rufa a jikinshi sannan ya dauki karami yana goge sumar kanshi. Bayan yazura lallausan silifas a kafarshi zama yayi kan wata kujera duk dai nan cikin bayin ya shafe jikinshi da mai mai kamashi tare da turaruka ya gyara sumarshi tare da shafa mata nata kalolin.
[8:45AM, 12/28/2016] ‪+234 814 912 1821‬: 🏵MEKE FARUWA 02 🏵

Modibbo yana kashe ma kanshi kudi fiye da zaton mai tunani,mikewa yayi cikin tafiyarshi ta kasaita ya nufi dakin barcinshi don saka tufafi ya kalli kofar da zata kaishi falo sai ya tuna ana jiranshi, din taski yaja sannan ya rufe kofar (bedroom) din shi bayan ya shige tare da fadin ko ma waye zai tafi ne don yanzun lokacinan na kar2 ne. Shirayawa yayi cikin wandon {jeans blue} da rigarsahi mai dogon hannu ya isa kan durowa ya kwashi takardu tare da wayoyinshi ya zuba su cikin aljihu, takalmanshi sawu ciki ne ya saka sannan ya fita.
Vicky ce zaune a falon tana jiranshi,ji yayi tamkar bai ganta ba duk da tsananin son da yake yi mata. Ya nufi hanyar fita, ta taso da sauri tana kiran shi.

Darling prince D P
Ci gaba yayi da tafiya, ta soma gudun sassarfa ta cinma shi ta dafa kafadarshi tana cewa cikin turanci.
Duban ta yayi tamkar ba zai magana ba sannan yace amma kin yi saurin hucowa. Ya taba baki" ina zaton kin manta ni wanene shi yasa kike yi min fushi, bani da lokacin lallashin ya mace duk da son da nake musu. Ki gane bani Yarima Modibbo ke bin mata ba, ni suke bi. Je ki ci gaba da fushi dan kin ganni da wata. " yaci gaba da tafiya yana sake fadin Yanzu lokacin kar2 ne ba na surutu ba.

Ta tsaya ranta a bace,hawaye ya soma zubo mata tana tunanin yaushe ne zata daina kuka saboda prince? Yaron da take matukar so, yaron da mata suke rububinshi, yaron da yake ma mata jan-aji, yaro mai kyau da kwarjini, ta zube ta soma kuka.
Kafin ke dubin ki sun yi Vicky .
Yarima Al-amin kenan. Kenan dan sarki Ismail jikan Abdullahi mai mulkin yankin Bauchi. Matashin yaro dan shekara ashirin da biyu Wanda aka fi sani da YARIMA MODIBBO A malesiya gurin kar2 ake CE mi shi prince

A ZARIA FA?

Katon gida ne ginin kasa mai dauke da sassa kusan goma sha biyu, gida ne ginin kasa tun na da wato ginin gargajiya. Kafatanin 'yan gidan dangin juna ne in ka dauke Fatima'yar mutanen Bauchi da aure ya kawo ta gidan. Yanzun da haka fatimar ce zaune tana tuka tuwon dawa, Bilkisu ta yi sallama ta shigo jikinta sanye da atamfa java, ta rataya jaka kana ganinta kasan daga makaranta take. Bilkisu kyakkyawa ce ta bugawa a Mujalla, domin idan har za'a zuba gasar kyau ta shiga ciki babu abin da zai hana ta lashe gasar 'yar kimanin shekara ashirin da biyu CE. Ta isa gurin mahaifyarta Fatima tana fadin.

Mamarmu sannu da gida Ta dube tace da kulawa duk da kasancewarta'yar fari ta ce "yauwa sannu maigado. { shi ne sunan da ake kiranta da shi } ma'ana mai gadon zinar. Kirarin maisuna Bilkisu.
Yau kin dawo da wuri. Ta ce " Eh, Mamarmu wata kawar mu muka je dubawa da tuni na dawo. Ta ce Allah sarki, bata da lafiya ne?
Zazzabin cizon sauro ne, nan sabon gari suke.
Allah ya bata lafiya. In ji mamar. Amin . Bilkisu ta amsa. Sannan ta nufi dakin mamansu duk da gajiyar dake tattare da ita sai da ta share dakin fes tare da gyara shi. Sannan ta fito ta share tsakar gidan duk da cewa ba'a siminte yake ba, yakan ba da sha'awa in an share .

Asma'u Auta ta shigo da sallama, ta dawo daga Islamiyya tace, Sannu Mamarmu, sannu Aunty Maigado. Bilkisu ta harare ta da sauri ta gano laifinta ta ce, Na manta ne, yi hakuri. Tana yar dariya . Bilkisu ta ce ban son Aunty ki ce min Bilkisu kawai don bana son maigado . Ranar da ki ka kara fada sai na fasa miki baki. Mama ma ta ce. To ai sai a hankali zata saba, mu dai ai ba yanda za ai damu.
[8:45AM, 12/28/2016] ‪+234 814 912 1821‬: 🏵MEKE FARUWA 03🏵
Ta dubi Asma'u.
Auta amso min kwanukan mutanan gidannan in kwashe tuwon nan. Dakuna uku duk da na su hudu sashen Babansu malam mamman kenan matanshi hudu ya'aya ashirin da takwas, don haka kwanukan da Asma'u ta baje gaban Maman mu sai ke ce za'a kaima gidajan layin gaba daya ne, yawancin kwanukan duk sunyi tsatsa da kuma lamba, haka Mamanmu ta ci gaba da kwashe tuwon nan tana zuba ma kowane. Bilkisu ta fito daga daki tana cewa, Mamanmu bari in debo ruwa in kin gama sai na dora ina son na yi wanka.

Tace, ai fa ke kam ko kwado ya San da zamanki gurin wanks. Dariya tayi sannan ta dauki bokiti zuwa gurin rijiya. Kananan yara sun kai hudu suna wasa da kasa a bakin rijiyar, maza uku mace daya macen mai suna Safiya tana zaune tsakiyar tabon da suka kwaba, rigarta duk koko haka nan fuskarta, kanta rabi a tsefe rabi da kitso. Tsaki Bilkisu taja sannan ta ce da su. Kai Ku ta shi a nan kazaman yara kawai." Bala dan babba a cikin su ya kalle ta.
To ina ruwanki dama za ki ce mu ta shi?
Ta samu kanshi ta dan buga dai dai da shigowar mahaifinsu Malam Mamman. Yace ke ke ke kar ki sake ki duke shi, ki shafa mishi bakin jininki
Ta dakata. Me yayi miki? Ko zalinci da mugun Abu za ki nakasa min da namiji gashi ke uwarki bata iya haihuwar ya'ya maza ba. Ya ja tsaki kai Bala. { hahahah wai bala dama bala sunane?} Idi, kuzo muje ciki domin zata iya jefa Ku cikin rijiyar nan yan ubanci ba karya ba ne. Allah ya kyau ta.
Bilkisu hawaye suka zubo mata, ita dai tana matukar mamakin irin tasanar da dukkan dangin mahaifinta 'yan dai-dai-ku suke yi mata ta dibo ruwan ta dawo, yanda taga fuskar Mamanmu tasan cewa ta ji duk me baba yace mata, don haka ta ce kiyi hakuri Mai gado wata rana sai labari .
Da daddare kwance take kan gadonta, gefenta Asma'u ce tana ta shara barcinta, ita kam ta zurfafa cikin tunanin cukurdaddan al'amarinta, kullum tana tambayar kanta shin me ke faruwa da ita ne? Tana da kyau na gani afada, tana da hankali ta sani domin mutane suna fada, tana da ilimi duka biyu wato islama da na boko. Natsuwa da kamun kai kuwa ba a magana, amma me ya hana ta burge maza? Me yasa ba ta da saurayi?me ya hana wani yace yana son ta? Kuka ya kufce mata Wanda ya zama dan kullum. A fili tace. Meke faruwa ne da nine? Wa zai bani amasar tambayata? Shin ko Ubangiji bai kaddaro ni cikin wadanda zasu yi aure ba ne? Allah kai kadai ne mafi sani......... Ta daga hannuwanta Ya Allah Ya Ubangiji halitta kai ne majibancin al'amurana, kafi ni sanin halin da nake ciki, Allah ka zaba min mafi alkairi. Ta maida kai ta kwanta ta soma tuno ita wacece?
Uhm sai an jima.

GIDAN MARINA, shi ne sunan da ake kiran gidanmu a unguwarmu, wato Ojo saboda 'yan gidanmu ita ce sana'an da suka gada daga kakanninsu, kuma ita ce har yau yayanmu suke yinta wato rini. Gidanmu katon gida ne mai dauke da sassa sama da goma. Asalin maigidan shi ne Malam salisu, shi ne mahaifin su Babanmu. Yana da mata hudu 'ya'yanshi talatin da bakwai maza guda goma sha biyar sauran duk mata ne, mahaifinmu yana cikin ya'yan Goggo Amarya shi ne da na uku a gurin ta yana bin mata biyu, kakanmu malam salisu mai rini mutumin kirki da sanin ya kamata, ya rasu tuntuni lokacin ma ba'a haife ni ba, uwargida ma lantana Allah ya yi mata rasuwa, yanzu saura mata uku. Tun rasuwar malam salisu gidan ya lalace rigingimu tare da matsaloli sukayi ma gidan yawa. Gidanmu ba'a cika auran bare ba sai dai dan wannan daki ya auri 'yar wancan daki, suma su ja na su sasan ko kuma cikin dangi na wani gu ya auro kuma dangi na wata unguwar ya auri yar gun, haka suka ke yi har zuwa kan mahaifinmu, wanda suka yi bikin wani abokinsu aka kawo Amarya daga Bauchi, cikin kawayan Amarya idon shi ya kyallo Fatima yar mutanan Bauchi daya daga cikin kawayan Amarya, nan ya birkice kun san bazazzagi da mace. Nan fa ya shiga zarya tsakinin Bauchi da zariya, Fati ta yarda itama tana son Muhammadu, wanda yan gidan basu goyi baya ba, saboda tuni yasan da hatun ladiyo yar kanin mahaifinshi baba isa dake jushi, hakan yasa duk yan gidan kin amin cewa da batun har da mahaifiyarshi goggo Amarya .

Goggonsa ce kurum ta ce ai hakuri ba a san rabo ba, tasa'ya'yanta su shige mishi gaba gurin neman auran, bayan kai-kawo aka biya sadaki sai bikin, ya gina sanshi kamar sauran'yan gidan ginin kasa ciki da falo, aka kawo Fatima dakinta, zaman nasu ba laifi sai dai bata jin dadi'yan gidan sai Goggon sa kurum.
[8:45AM, 12/28/2016] ‪+234 814 912 1821‬: 🏵MEKE FARUWA 04🏵

Bayan'yan watanni sai rayuwa ta canza tun da gara ta kare shi kenan mataloli suka kunno kai cikin zaman nasu, farko ya sakar mata sayan su sabulu, man shafawa, daga baya suturar a shekara dama yake mata itama ya daina, daga baya ma sai ya zama abinci in ya kawo masara ko dawa ko kuma doya to batun cefane can ta gane, cikin haka dangi suka soma tsegumin shekara biyu babu haihuwa gaskiya sai dai ya sake aure, haka ce ta faru. Ladiyo tana jiranshi nan ko aka soma shirin biki Fatima ta zuba ido domin sabon shafi ne na wulakanci ya bude tsakaninta da dangin mijin da kuma shi kanshi maigidan saukin ta daya goggon sasa tana yin kuli to sai tana bata mirji da suya tana biyanta a haka Goggo ladiyo ta shigo cike da gadara da jin kai har zama yayi zama kafin wata biyu ladiyo ciki ya bayyana.

Nan dangin miji suka sakota gaba ko yaransu suka hana ta aika, sukan ce ta abr musu'ya'yansu in taga dama ta haifi nata, ya zama sai dai in tana son aike sai taje, ko kuma ta fita makota ta aika yaransu. Duk wannan ba shi ne tashin hankalinta ba irin yanda Ladiyo ta tsiro tsirfar bata son warin tuyar kuli kuma in taga tunkuzar kuli tana sakata yin amai, kenan'yar sana'ar tata ta barta a halin da ita ne take samu tana rufa ma kanta asiri.
Tabbbas nufin Ladiyo ta samu ta raba ta da sana'arta, maigidan kam ya ce baya son ya kuma ganin kuli ko tunkuza, ta ce amma kasan cewar da wannan sana'ar na dogara ko? Nan take ya fusato, kenan ke kike ci da kanki? Ta ce menene marabar dambe da fada? In ka kawo min hatsi ko doya shi kenan, ba kudin cefane ba na nika ko na ice, sabulu, man shafawa duk a jikina suke fita, ya ce to koma menene dai a daina min kuli, tace gaskiya ba zata yiwu ba, ni kenan kullum sai dai dangi su taimaka min? Ya ce kanki aka soma? ai ba kanki mata suka fara cefane ba, don haka ki canza sana'a, ta ce amma ai ita Ladiyo kana bata ba dan baka dashi ba ne kake hana ni, saboda haka yanzun na soma yin kuli in ba'a so in yi sai a tsare min komai, " ya fita tare da fadin To bismilla, kiyi ki gani, haka ko washegari ta amso aikinta ta shiga yi, Ladiyo ta fito shi ne kike kulin dan ki ga bana son warin so kike cikina ya zube ne tun da ke ba ki iya samun cikin ko? Bata tanka ba ta ci gaba da aikinta, makira mijin na shigowa da gudu ta shige daki ta hau gado tana ta burgima tare da kakarin amai. Yana ko karasowa ya shiga masifa har da zaginta, a karshe ma dukanta yaso yayi ta shige daki. Washe gari kam ta ce ta gaji gida zata tun da tana da gatanta hakuri kuma ba hauka ba ne. Wannan tsiya, yau miji ya maka gobe mutan gida, uwarmiji sai ta shigo har sasansu ta zage ta tas tana cikin wannan tunanin tana hada kaya, taji muryar Goggo Amarya.
Ina kike 'yar mulki da iko da an ce ki daina aikin kuli saboda mai cikin haihuwa ke naki cikin ban da kashi ba ya iya daukar komai shi ne za ki bar gidan, itama mai baki aikin ai munafunci ne ga mata da yawa kowane sashe ta mika aiki ai yi zasu yi amma dan gulma ta fi son ta ba ki shi yasa bata ciniki to mai farar kafa ta taba ba dole yayi kwantai ba?

Fatima kam shiru ta yi tamkar bata nan, Goggo ta gama masifarta ta fita,itama ta dauko kayanta da saka su cikin garin yayi zafi ta fita a waje yayyan maigidan ne su biyu sani da Rabi'u suka ce ina za ki? Ta ce zan yi tafiya ne, suka ce in dai yaji ne kiyi hakuri, ta ce kai ita ta gaji gara taje garin su.

Daf da magriba ta iso Bauchi, sanda ta shiga gidan su mahaifiyarta tana alwala ta ce lafiya kuwa? Murmushi taye tare da fadin lafiya kalau bayan sun yi sallah sun ci abinci nan ta shiga zayyano ma Umma abin da ya faru tare da halin da take ciki. Umma ta ce bari Malam ya shigo.

Iyayanta suna da mutunci tare da sanin ya kamata, suna son Fatima sosai, saboda ita kadai ce ya mace a cikin 'ya'yansu maza guda biyu. Aminu da Abubakar wadanda suke kasuwancinsu a nan babbar kasuwar Bauchi, kuma suna da iyalansu suna matukar kula da iyayansu da kuma Fatima.

Sun hada mahaifinsu da yayyanta sun yanke shawarar in yazo biko za'a ja mishi kunne sannan ta koma, ta ce ita in so samu ne a raba Auren amma sai mahaifinta ya ce ba zai yiwu su kashe mata aure ba, ta je ta ci gaba da hakuri. Satin ta daya sannan 'yan uwanshi suka zo shima sakamakon yanda 'yan uwanshi suka matsa mishi da magana har da makota sannan ya yarda yazo bikon tare da'yan uwan nashi.
An ja mishi kunne 'yan uwanta sun hada mata jari tare da dunkuna sun ce taje ta sayi fridge ko ruwan sanyi ne tana saidawa, ta dawo dakinta ta ci gaba da hakuri tare da yan sana'o'inta haka nan ta sai fridge din tana kuma samun alhairi haka Ladiyo ta haihu suka yi ta rawar Kansu har aka yi suna hankalinta kawance, tunda tana sana'arta. Cikin watan ya sake ta da wani dakin yana gamawa ya rigimo Auren karima bazawara ce daga unguwan kaura aka sha biki itama tabi sahun yin cefane da kanta, wankau ta ke yi, shekarara danta sunusi daya ta kuma samun ciki sai fa suka soma gasar haihuwa ita da karima Fatima ta da dai zuba ido ya'yansu maza suke Haifa.
[8:45AM, 12/28/2016] ‪+234 814 912 1821‬: 🏵MEKE FARUWA 05🏵

Kamar wasa ya kuma tada daki ashe zai cika ne wannan karon 'yar yarinya ya dauko musu daga kauyan Turunku Mara kunya nan suka hada kai su uku suna mata habaici wai juya su kam sai zazzaga haihuwa suke, cikin ikon Allah sai ga Fatima itama ta wayi gari da ciki. Kwanci tashi har haihuwa tazo, komai na gama da ciki don kayan yara duk ita ta siya, domin da ta tambaye shi cewa yayi shi dama bai taba sayan kayan jarirai ba kuma kanta ba zai fara ba. Suko sauran kishiyoyin nata sai zundenta suke wai ba saban ba su wance anyi ciki.

Bisa ga yardar Ubangiji ta haifi'yarta ita daya kuma cikin dare, maigidan dama dakin Amarya yake, ita ce ta yanke cibi da kanta dama tana da sabuwar rezarta, sannan in ta zaga sasan Goggo sasa takan tambaye ta yanda zata yanke cibi saboda ko zata haihu cikin dare, ba zata samu mai kira mata Goggo ba. Ta nade' yarta cikin zani da ta huta ta tashi ta kwashe jinin. Da Asubahi Allah ya kara mata karfin jiki ta fito ta dora ruwan wanka, ta wanke 'yarta mai matukar kyau sunusi babban yaron maigidan nasa dan gidan Ladiyo ya leko wai in ji Goggo salame ( amaryarsu kenan) ta ce ki bata kwanon koko, ta ce babanka fa? Ya ce ta yana dakinta ta ce kaje ga kwanonin ka kai sannan ka ce babanku yazo na haihu, da murna yaron ya tafi kun San yara da dokin haihuwa, sai ko gashi ya shigo ba yabo babu fallasa fuskarshi ya dauki yarinyar ya gani ba ko addu'a ya aje ta kilama bai iya addu'ar ba ta ce don Allah ka siyo min dan kayanta mana? Ya dube ta ke Fatima dube ni ba kanki na soma haihuwa ba, bare ki min tsurfa in za ki sha kunu kisha duk sauran kunu ake dama musu.
Ta ce to yanzu wa zai je ya fado ma'yan Bauchi? Ya ce wannan kuma ya rage naki, ni dai bani da kudi haihuwar nan ma ki samu ko masarar fate in Samar miki kada ki sa rai zan yi wata karya dan bani da hali. Ta dube shi cikin takaici tare da da na sanin auranshi. Ta ce duk matan ka ka fifita su kai na, domin ganin idona kana sai musu kayan (shayi) sannan ka musu ragon suna har ma da dan dinkin suna, ban sani ba ko sun fini yi maka biyayya ne? Tsaki yayi sannan yayi waje, tayi ta tashi wani dan saurayi jikan Goggon sasa ta mishi kwatance ya tafi Bauchi don shaida ma iyayanta.

Washe gari kanwar Umma ta biyo dan aike suka dawo ta ci gaba da kula da ita a zaman Inna hausi ta tabbatar Fatima tana matukar hakuri domin komai da kanta take saye don abincin gidan nasu baya ciyo ga Inna hausi sai daiu su yi yar miyarsu haka ake har suna tun ana gobe yan Bauchi suka zo, masara kurum ya miko ko gishiri bai bada ba ita ce ta yi komai, dangi sun hada mata shatara ta arziki, ya kuwa ta ce suna Bilkisu mai gadon zinari. Tubarkalla Masha Allah haka kowa ya ke cewa in ya ga Bilkisu shi ko ubanta ko kaza bai yanka mata ba bare rago amma ta zuba ido kuma ta bar ma Allah.

Haka Bilkisu ta taso cikin sha'awa da kuma birgewa amma gurin uwarta domin mahaifinta bai taba mata ko da wasa ba daga nesa bare ya dauke ta, a haka ta kuma samun cikin Sakina sannan Maryam sunnan Umma ne don haka suke kiran ta momy, sai Ku Asma'u lokacin tana goyon Asma'u abubuwa sun mata yawa ga yara maigidan baya biya musu bukatun 'ya'yansu cima ba dadi, in kana son ci da dan galmi sai ka bude bakin jakarka yara babu karatu su sun usima da suke maiya ya dai saka su amma ya bar iyayan da siyan takarda da biyan dan kudin jarabawa, don haka suka hana yaran zuwa makaranta kowacce ta kama Sana'a tana dora ma ya'yanta suke nan da yake son su bare Fatima wadda ita da ban za duk daya, gidan Hajara ta shiga wato aminiyarta, suka shawarta tace hajara shawara na kawo miki, ta ce ina jin ki Fatima, tace kina dai kallon rayuwar da muke yi a gidanmu. Ba cin kirki sai gasar haihuwa, to ba zan iya ba so nake don Allah ki ma Malam maigidan ki magana ya taimaka min da wani dan taimako haihuwar nan ta tsaya in samu in ji da tarbiyar wadannan ma balle ni mai'ya'ya mata ta ce kin yi tunani zan ko gaya mishi haka ko aka yi rubutu yayi mata haihuwar ta tsaya ta samu ta saka Bilkisu firamare..
[8:45AM, 12/28/2016] ‪+234 814 912 1821‬: 🏵MEKE FARUWA 06 🏵

Sana'o'i ta ringa yi sbulu, omo, manja,mangyada, lallai ana shan wahala da rayuwa,haka nan tayi ta kula da yaranta har suka soma tasawa. wata karamar sallah tazo nan ta shirya ita da yaranta, don zuwa bauchi, Bilkisu yarinya mai kyau da shiga zuci,

1 Comments On ME KE FARUWA
avatar
fatima-8-5

1 year ago

Reply

Uhm

Please Login or Register in order to submit comment