Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sani? Magajin Malam ya kuma dagewa tamkar gaske yace yanzun dai da mun gama waya zan sanar dasu don na hana Doctor Aisha ta sanar dasu, musamman da na fahimci da saninka zata zubar da cikin, magana daya dai yanzun ko Ku janye ra'ayinku kai da matar ka ko kuma wlh zan sanar da su, musamman in har kazo don na sanka sosai zaka iya cewa zaka zo kayi aikin da kanka.
Jikin Yarima ya mutu, sannan yace amma dai magaji kasan haihuwa ba ra'ayina ba ne ko? Tsaki magaji yaja sannan yace, wannan sai ka gaya ma ubangijin da ya baka cikin, ya kashe wayar shi.ya dubi bilkisu bar shi kawai, ba zai zo ba, suka yi ta dariya ita da magaji tayi mashi godiya sannan ya tafi.
[8:38AM, 12/28/2016] ‪+234 814 912 1821‬: 🏵MEKE FARUWA 81🏵

Ya kira bilkisu yana cewa, ya ya aka yi ta bari magaji ya sani? Tace ya shigo gaishe ni ne ya same ni cikin wani hali shi ne ya kira likita.... Ta soma kuka cikin kissa ni gaskiya ba zan iya ba, gashi yace zai gaya ma su Umma kuma kasan yanda su Umma suke murna za su dauki mummunnan mataki ne a kanmu, yanzu ya ya zan yi? Yace ya ya zaki yi kuwa in ban da hakuri? Kina nufin zan zabi bacin ran iyayena saboda ranki yayi fari? Ba ki kai wannan matsayin ba, ta soma sabon kuka wato danni baka kaunata in zan mutu ne in mutu ko shi kenan, ta kashe wayar sannan ta soma dariya tana cewa in kasan wata ai baka San wata ba, don ma kada ya dauka fushin wasa take yi sai ma ta kashe wayarta bayan ta kira Mansura ta mata bayanin komai, sannan ta ce zata kashe wayarta don kada ta nema ta ji shiru, Mansura ta kara ma ta wasu dabarun sannan suka yi sallama, hankalin ta kwance ta gode ma Allah tasan bata da matsala ta gefen Yarima, Allah yaga niyyarta Yarima da farko bayan ta kashe wayar cewa ya yi ke dai ki ka sani ko a jikina da bacin ran iyayena ai gara naki.

Amma kuma me?

Kunnuwanshi sun kasa daina jiyo mishi kukan da ta kashe waya tana yi yayin da zuciyar shi ta shiga cewa kamata ya yi ace ka lallashe ta ne, zugin zuciyar ya matsa mishi nuna mishi take yi bai yi mata adalci ba, haka dai ya daure yayi jarumta har zuwa washe gari inda abin ya ishe shi har ya nemi layinta cikin wayarshi amma a kashe, yayi ta kira shiru ya bata awa daya ya sake kira nan ma shiru, jikinshi ya yi sanyi, zuciyar shi ta dame shi yinin ranar babu kuzari duk wadanda suke tare dashi duk sun fahimci yana da damuwa, musamman Tina. Shi kanshi ya rasa dalilin damuwar tashi, akan matar da ya tabbatar ba sonta yake yi ba, wasa- wasa yau kwana hudu yana neman layinta babu dare babu rana, duk da ya kira magaji ya tambaye shi shin bilkisu tana nan? Magaji yace, ban sani ba sai dai ka kira wayarta, Yarima yace yau kwana hudu wayarta tana rufe, magaji yace to ka kira ta cikin gida mana? Yace bari ya yi hakan.

Umma ya kira bayan sun gaisa yace, Umma wai ya ya jikin bilkisu ne? Yaci gaba ina ta neman layinta amma shiru? Umma tace, jikinta da sauki babana, dazun nan ta shigo nan amma zan kirata in ji, yace to suka yi sallama.

Koda Umma tasa aka yi mata kiran bilkisu, ta tambaye ta ko lfy wayarta take ana ta nema ba a samu? Sai bilkisu tayi karya da cewa, batirin wayar tata ne ke da matsala, amma ta aika yanzu za siyo mata wani, Umma tace to dama maigidan ki ne yake ta nemanki, tace zan kira shi in nasa batir din.

Bayan taje daki sai ta kunna wayar ta cikin sa'a yana neman ta sai gashi ya samu wata irin ajiyar zuciya ya yi tun kafin ta dauka sai ya ji wani sanyi cikin zuciyar shi, sai da ta kusa tsinkewa sannan ta daga. Da sauri yace, beauty, beauty, kina jina? Ta soma shassshekar kuka,sai kurum ya samu kanshi da cewa innalillahi wa inna ilaihin raji'un, wai beauty me ke faruwa ne? Cikin kuka ta ce dole mana ka ce meke faruwa? Ka min ciki sannan ga wulakancin ka har da cewa baka damu da bacin raina ba to ni ba zan iya zama ba gidanmu zan tafi. Yana son yace ki tafi din mana, amma sai zuciyar shi ta ki furta haka,sai kurum ya ji bakinshi yana cewa, haba saurare ni ki ji.in ji wa ya ce ban damu da ke ba? Da kin tausaya min. Don Allah kiyi hakuri. Sai kuma yayi shiru yana mai jin haushin kanshi, yaushe ne yake baiwa mace hakuri amma zuciyarshi murna take yi musamman da taji bilkisu tana cewa shi kenan ba zan kara kashe maka waya ba, to kana son cikin? Yana tayi maganar cikin sigar shagawaba sai da tsigar jikinshi ta tashi, sannan nashi ra'ayin shi ne ya ce mata A'a amma ya kasa fadin hakan, sai ya samu kanshi da gudun bacin ranta, don haka sai yace ya ya zan yi ni dole in so shi tunda ni na diga shi, sannan shakuwarmu dake tasa ba zan guji duk abin da ke jikinki ba, tace kana nufin yanzun ka damu dani? Yace, ke baki damu dani ba? Tace na damu mana, sosai ma. Har fa tunanin ka nake fa zama in yi da baka nan.
[8:39AM, 12/28/2016] ‪+234 814 912 1821‬: 🏵MEKE FARUWA 82🏵

Ta marairaice murya,kai fa kana tunanina? Yace inna ce miki banayi ai zaki musa ko ban tunoki don komai ba ai na tunoki ko don hutu beauty,ina bukatarki kusa dani,tace kilama ka samu wata,da sauri yace haba dai ni yanzun naki ne ke kadai taji dadi sosai sannan tace nima haka,yayi dan murmushi na sani beauty tun ranar farko dana soma kwanciya dake nasan cewa nayi dacen mata,Allah yayi min baiwa,bai duba halina ba,bai hadani da ‘yar uwata ba wato mazinaciya, sai ya bani mai kofa a rufe nina budeta, tace ni ko kaga bana son in tuna wannan rana,yace don me?Dan wulakancin dakayi min, yayi ‘yar dariya niko abubuwa da yawa sun tsaya min a rai ranar,zan gaya miki in nazo,tace shikenan sai anjima?Yace kin kosa muyi sallama ne?Tace a‘a nace kona tsare maka aiki ne,yace shikenan zamuyi waya da dare,tace sai naji ka kenan itace ta fara kashe wayar shi ko tsayawa yayi tamkar wawa,yana son tuno tabargazar da yayi shin me ma yace mata?Kasa tunowa yayi sai ma wata annashuwa da zuciyarsa keyi,hira tayi dadi tamkar acigaba sam ya manta me yakeyi ne,ya nutse cikin tunaninta.Tina ce ta dafa kafadunsa da sauri ya dubeta tare da fatan Allah yasa beauty ce ganin Tina sai yayi tsaki, jikinta babu kwari ta sakesa ta zauna tuni itama ta soma sabawa da halinsa,sai dai Allah ya jarabceta da sonsa,shiko duk sanda yake kan begen beauty yakan manta da komai da kowa baya son a matsa masa,wanda nasa ganin shakuwa ce duk ta kawo haka.Bily kuwa yanzun hankalinta kwance ga tattalin da surukanta suke mata, labarin cikinta ya yadu ko‘ina,don ko su Mamanmu da Mansu ta sanardasu sunyi murna, sannan gashi Yrm duk ya birkice kanta,don da taba Mansu labari Mansu cewa tayi Allah sonki yakeyi Bily tace a‘a duk hirar da mukeyi bai taba cewa yana sona ba,yadai nuna kulawarsa gareni,so kam ai na riga nayi rashinsa bazan taba samun wannan kalmar ba,Mansu tace shikenan za kuma ki gane nan gaba.

Yarima da Tina an sake dinkewa,a zuciyarsa yana kara shige matane da tsawonta da tsawon gashinta suna tuno masa da beauty, ita ma ta fahimci yana da wata a cikin zuciyarsa domin in suna kwance sunan beauty kawai yake kira.sannan inya shiga wanka takan dauki wayarsa ta masa bincike tana son sanin wacece beauty din nan?Yaya take ne don ta samu matsayi mai girma gurin wannan tsadaddan yaron.Kimanin wata hudu kenan da tafiar Yrm,cikinta kuwa yana wata biyar kenan tana zaune tana cin kwakwa da tasa aka siyo mata, Sumayya ce ta shigo tana sanye da leshi ja da kuma ratsin baki yaune zuwanta na uku gidan,ta zauna tare da cewa Maman biyu,Bily tayi ‘yar dariya tace,Allah amin ya biya bakinki Sumayya tace amin.nan suka soma hira duk data hakura da Yarima amma duk sanda ta gansa ko taga hotonsa sai taji ma kanta haushin rashin samunsa, yanzun ma da take zaune kallon hotonsa takeyi tare da yaba kyansa, cikin zuciyarta. Bily tace,Sumayya kina kallon wuta ne fa,yakamata ace yanzun kin cire Yarima acikin rayuwarki,sannan ki godema Allah daya baki Magaji matsayin miji,tace ai tuni na hakura anty Bily, matsalata daya yanda zan cire shi daga zuciyata,ki dinga addu‘a inji Bily,ki rike mijinki Sumayya so da yawa abinda ka kwallafa rai kansa baka samesa ba to sai kiga alkairi ne rashin samun,ni kaina ban taba tunanin zan auri kamar Yarima sa‘ana ba,babu irin takaicin dabanyi ba game da auren amma yanzun sai ina ganin alkairai da dama acikin aurenmu.don haka ki kama mijinki ki samu ladan aure,Sumayya tace to nina rasa sam sai inga sam Yarima yafi Magaji komai, Bily ta hade fuska Sumayya lallai zaki daina zuwa gidana,domin babu wanda yafi wani gurin Allah face wanda yafi tsoronsa,in dai kina so mu shirya to ki kama mijinki. Sumayya tayi ‘yar dariya ganin ran Bily ya baci,tace na daina anty Bily,shima Magaji cewa yake duk ranar dana zo nan gidan wai bana bata masa rai,shiyasa yake son inzo gurinki,ina aiki da shawararki,nan dai suka cigaba da hirarsu.Wani dare Bily tana bacci sai kawai tayi mafarki wai ga Yarma an kawosa ya rasu,nan take ta farka duk tayi sharkaf da zufa,ta kalli agogo sha biyu da ‘yan mintuna duk da lokaci ba daya ba ne ji tayi bazata iya komawa bacci ba har sai taji muryarsa nan take ta kira layinsa daidai lokacin ya shiga wanka,Tina ce kwance rigingine a tsakiyar gadonsa,don haka wayar tana yin ringing ta dauka ta duba(beauty)taga an rubuta,da sauri ta daga wayar tare da cewa, wacece ke?Cikin harshen turanci. Bily ta tsorata, gabanta na faduwa tace,kiba mai wayar,Tina tace sai ta fada ko ita wacece,ran Bily ya baci dama Yarima yana nan yana harkarsa da matan banza,shine yace mata ya daina?Wani tukuki taji azuciyarta nan take ta kashe wayar cikin tane ya shiga murdawa,ji take tamkar zata haihu Yarima yana fitowa daga toilet din yaga phone dinsa ahannunta,nan take tayi saurin cewa an kiraka amsar wayar yayi ba tare da yace mata kalaba,koda ya duba yaga beauty ce ta kira kuma har ta daga nan da nan sai yaji hankalinsa ya tashi,da sauri ya soma kiran layinta,tamkar kada ta daga amma sai ta kasa tana dagawa sai ta saki kuka ya rasa me zaice,sai yace kiyi hakuri beauty na kasa controlling din kaina ne yau amma insha Allah bazan sake ba,na amsa laifina kiyi min addu‘a kinji?Cikin shesshekar kuka tace, Yarima baka min adalci ba,yaya na tsare kaina a gida kaika dinga bin wasu,ina tsoron kada Ayar Allah ta sauka akaina,domin Allah yace in har kabi matar wani sai anbi taka,in ‘yar wani kabi kaima za‘a bi tak,haka kuma mazinaci baya aure face sai da mazinaciya ‘yar uwarsa,ban kasance mazinaciya ba. Yarima ma jikinsa yayi sanyi yasan gaskiya ta fada ina ma gata gashi ne ya rungumeta tare da lallashinta, duk da haka sai yace na sani beauty ban kyauta miki ba,amma kada kiyi fushi dani zan shiga damuwa kinji?Tayi ajiyar zuciya,sannan tace bazaka daina ba Yarima ,yace ki daina fadin haka,insha Allah zan daina nidai kimin afuwa, tace Allah zaka roka donshi kayiwa laifi,da sauri yace zan rokesa,don Allah beauty kadaki kashe min waya kinji yanayin yanda yayi maganar sai taji dadi,tace bazan kashe ba
[8:40AM, 12/28/2016] ‪+234 814 912 1821‬: 🏵MEKE FARUWA 83🏵

Zuciyarta tayi sanyi domin lokutan baya Yrm yana neman matansa a gabanta, zai iya kwanciya da mace a gabanta,amma yau gashi wayarta kawai mace ta daga duk ya birkice, ta san ko har yanzun Yrm yana neman mata to ta samu wani matsayi agurinsa tunda yake boye mata baya son ta sani,bugu da kari Yarima ne harda bata hakuri,tayi mamaki domin tasan sa sarai baya daga cikin mazan da suke bawa mace hakuri,baya lallashin mace amma ita sannu a hankali ya soma yi mata abubuwan da yake ikirarin bazai iya yiwa mace ba, zata dage da rokon Allah har Allah ya shirya mata shi. Shi kuwa Tina ya tsirama idanu cike da bacin rai irin wanda bata taba gani ba,don haka ta tsorata har ta shiga bashi hakuri,cewa yayi ta fita kawai.tana fita ya fada kan gado yana rubuta ma beauty dinsa text na ban hakuri, sai daya gama sannan yayi shiru yana mamakin kansa,shine Yrm kuwa?Shine mai ja ma mata aji? Shine wanda mata suke bi bashi ne ke binsu ba? To menene yasa shi rikicewa kan beauty?Yanda ya dade dasu Vicky bai dade da Bily haka ba me yasa zuciyarsa bata shaku dasu kamar yanda ya shaku da ita ba?Me yasa ita baya jin ta gunduresa?Me yasa baya son bata mata rai ne? Domin inya bata mata rai zuciyarsa sai ta ringa yi tamkar zata fashe,bai saba da damuwa ba,don haka baya son zama cikin damuwa,inya bata mata rai sam cikin damuwa zai zauna shiyasa yake kiyayewa.

A kwana atashi babu wuya agurin Allah, yau gashi Bily an shiga watan haihuwa.duk wani abu daya kamata mai jego da jariri ‘yan gata su bukata, tuni Umma ta tanadeshi, can ma Zaria su Mama suna ta shirye-shiryensu na talakawa. Yrm ko hankalinsa ya kasa kwanciya ina ma a hannunsa beauty zata haihu baya son ya rasata,wayewar garin Alhamis ta tashi da ciwon haihuwa,tuni Umma tasa akayi asibiti da ita,inda take awo wato asibitin Doctor Aisha.har zuwa yamma shiru Modibbo ne yayi mata wasu addu‘o‘i ya tofa su cikin ruwa aka kai mata daidai lokacin Yrm ya kira wayarta har ya gaji,ya kirata cikin gida,Asabe ce ta dauka ya tambayeta Bily,nan take shaida masa tana asibiti zata haihu,yace tun yaushe? Tace tun jiya,nan take ya kira Magaji,Magaji yace duk suna asibitin ance nan da awa daya zata haihu,tsaki kawai yayi nesa bata maganin kusa,amma in yaga za‘a bata masa lokaci xai bar komai duk da suna tsaka da karatu,kasancewar sun kusa gama course din ya kira wannan ya kira wancan har awa dayan ta shige ya kara minti talatin duk yaji babu bayani,nan take sai ya soma shirin zuwa gida. nasa ganin likitar bata san aikinta ba,domin in shi zai amshi haihuwa ne yana ganin cikin awa daya mace zata haihu. sai washegari sannan ya samu tasowa, bai sanar da kowa cewa yana hanya ba kuma yana cigaba da kiran waya suna sanar dashi ta kusa harma ya soma tunanin ko ta mutu ne suke boye masa? Yana dira dama daga shi sai kayan jikinsa,yayi wa Magaji waya,wane asibitin?Suka masa kwatance ya nufa, doguwar nakuda Bily tayi likitar tace su kwantar da hankalinsu zata iya haihuwa da kanta. ana cikin haka sai ga Yrm,duk suka cika da mamaki, office din likitar ya nema ya shige ya nemi son ganin matarsa kasancewar tasan aikinsa ne bata musa ba,suna tafe tana masa bayani shiko saurarenta baiyi ba shi dai burinsa shine ya isa gurin matarsa.yana shiga ya ganta tana ta fama ga Nurse kanta a tsaye ya isa gurin da sauri ya kamota lokacin abun ya kan kama sosai,nan ya shiga aikinsa cikin minti tara dan ya sawo kai,nan Yrm ya jawosa ya mika ma Nurse bayan ya yanke cibi.bai ko tsaya kallon yaron ba shita matarsa yake,duk abinda ya dace shine yayi mata,sannan yayi mata allurar hutu. Koda ya fito ana ta kallon jariri wannan yaba wannan, wannan yaba wancan duk sai yaji sun bashi haushi,su ta yaro sukeyi ma ga matarsa can a galabaice.shi kam me zaija masa kara haihuwa?Gida kawai ya nufa,ya watso ruwa,yana dawowa tana farkawa. Ta dubesa da dan murmushi,me muka haifa?Ya dan daure fuska bakiyi murna da ganina ba sai abinda kika haifa ko?Ta yunkura ta tashi,yayi saurin riketa kada ki tashi tace naji karfi fa ya zauna kusa da ita,tace naji dadin zuwanka sosai mana.
[8:40AM, 12/28/2016] ‪+234 814 912 1821‬: 🏵MEKE FARUWA 84🏵

Kallon fuskarta yakeyi,ji yake tamkar ya bude kirjinsa ya sakata ciki,yace beauty kinji jiki,hankalina ya tashi sai zuciyata take sanar dani kamar zaki mutu ne tunda naga Allah ya kawo mana da sauki kila gobe na juya dama ina tsakiyar ayyuka,nan da wata uku zan gama in dawo mu zauna tare.tace yanzun ba zaka tsaya ayi suna ba?Sallamar su anty Salma ce ta katsesu,suka shigo suna faman taba baki,anty Fulera tana dauke da yaro,anty Fatima ce ta soma cewa,maijego kin tashi?Ai nazata bazaki iya tashi yanzun ba, saboda tsabar ragwanta. anty Salma tace gaskiya raguwa ce. Yrm yace kinfa san tun shekaran jiya take aikin abu daya,gaskiya tayi kokari,ni likitar cema naga alamar kamar bata san aikinta ba.suka ce ba wani nan ragwanta ne,Bily ta nuna ita dai tana jinsu yace to shikenan ku barta ta huta,suka mika masa yaron ya amsa yana kallon fuskarsa,sai yaji yaron ya burgesa,tunda ya amshi yaron shi take kallo ta gani shin yaya fuskarsa zata nuna,ga mamakinta sai taga yayi murmushi tare da cewa,yana da kyau bebyn,ta kalli su anty Fulera ta sunkuyar da kai,har suna hada baki gurin cewa munafunci in zakiyi magana yi mu kinga fitarmu,abinda haihuwarma kinyi kikayi kin tsaya sai yazo suka fita.Yrm yace,sun cika hayaniya,ya mika mata yaron yayi gashi ki ganshi ta girgiza kai,yayi dan murmushi yace,baki sonsa ne?Ta kallesa tana dan murmushi,sannan ta kalli yaron tace kai kana sonsa?Ya dago yaron zuwa bakinsa ya sumbacesa agoshi ina sonsa yanzun yana da kyau,tace kama da kai yayi?Yasa matashi a cinya kallesa ki gani,ta zata axuciya tace hasbunallahu wani'imal wakil,ya dubeta tace tsarki ya tabbata ga Ubangijin daya bamu wannan yaron,‘yar dariya yayi kin rude ko?Likitar ce ta shigo ta dubata sannan tabasu sallama tana tsokanar Yrm.yaso tafiya washegari, amma beauty da yaronta suna daukar hankalinsa har ya kara kwana,dazai tafi hadasu yayi ya rungume wayarsa ya fito da ita abin mamaki yana ta daukar hoton Bily da bebyn ta Lallai abin mamaki ne domin in kaga Yrm yana daukar hoto cikin waya to wani abu ne mai mahimmanci daya danganci aikinsa bazaka samu hotunan banza cikin wayarsa ba,domin bashi da lokacin zaman kallon hoto,tsiraici a hoto baya burgesa,yafi son ya gansa muraran.bayan ya gama yana bakin gadonsa itama ta zauna,idanunsa suna kan jaririn yace beauty ji nake tamkar kada na tafi, ya juyo da dubansa gareta yana kallon tsakiyar idanunta,nazo da sha‘awarki zan koma da abuna.ta matso ta kama tafukan hannunsa ta matsa,abin ya ratsasa har ya lumshe idanu tare da jn numfashi,tace daba don ina cikin biki ba,ko ban warke ba zan baka kaina har sai ka gaji,amma kada ka damu zan dinga zuwa maka cikin mafarki.ya tallabo fuskarta ya soma kissing dinta baki cikin baki,kukan yaron ne ya dawo dasu,shine ya rigata dauko yaron ya mika mata tasa shi a kafada yace no bashi nono in gani zama kiyi kyau da shayarwa?Tayi dan murmushi,ta soma kici- kicin ciro nono yana taimaka mata,yaron ya kama yana sha,Yrm ya tsura ma nonon idanu,sun cika sun kara girma, sannan basu kwanta ba,ya lura da kasan nonon yana da fadi,lallai ya taka sa‘a wannan baya faduwa komai tsufa,domin da irin masu faduwan ne ma gareta da sai yayi mata gyaransu sun mike.ya matso ya rataya hannunsa akafadarta ya saita wayarsa ya daukesu hoto su biyu ne suka fito don yaron yana cinyarta yana shan nono. Kwankwasa kofar ce ta dawo dasu daga shirman hotunan da sukeyi,Yrm ya bude kofar anty Saliha ce tace ina maijegon tun dazun nazo da baki ‘yan barka suna can a zaune tazo nan ta nane inba zata samu zuwa su gaisa ba to ta bani yaron.cikin fushi take maganar,yace haba anty tana zuwa muna sallama ne, ta juya fuu, yace taso kina da baki ni dai saura minti kalilan jirgin Lagos ya tashi,suka kalli juna tace sai munyi waya,yace to,sannan ya shafa kan yaron tare da sumbatar lebunanta sannan ta fita.yana rike da kofarsa yana kallonsu har ta sauka daga falon,yayi ajiyar zuciya ya koma yana hada shirginsa.Koda ta isa dakinta haka anty Saliha tayi ta mata masifa agaban dangin mijinta,wai ita ‘yar dadi miji,tabi ta like masa menene-menene, dhiru kawai tayi mata hardai suka fita haka akaci gaba da shagalin har zuwa ranar suna,inda yaro yaci sunan mai martaba,tun ana gobe suna ‘yan Zaria suka iso,Mansu kuwa tun kwana hudu da haihuwa ta iso.anyi suna irin na ‘yan gata,kyautuka dai maijego ta samu,kaya kuwa tasa har ta gaji,har washegarin suna jama‘a ce.sai da gari ya kara wayewa sannan Mansu ta tafi,bayan sun kammala komai ta bata kudade tasa mata cikin account dinta,don ita bazata samu fita zuwa banki ba.mai martaba doki yava takwaransa,Yrm yana kwance yana kallon hotunansu baya gajiya da kallon hotunan,wasu abokan course dinsa sunsha mamakin ganinsa yana kallon hoto harma suka tayasa kallo,sai gashi Yrm mai boye cewa yana da mata shine mai fadin matarsa ce da dansa,sun rude wanda har yaji haushin kansa me yasa ya nuna matarsa?Murna suka tayasa kan cewa yayi matukar dacen family koda yaushe Yrm yana nane da wayarsa,jira yake ya samu dan sarari zai kira beautynsa,waya ga ba sabon ba,su Yrm an shiga tarkon so sai dai shifa har yanzu bai san wai son matarsa yake ba kuma bai samu wanda zai sanar dashi ba.nata bangaren kuwa ba don har yau Yrm baice mata I love you ba data ce sonta yakeyi,koda bata san yaya so yake ba ai tana kallon fina-finai tana kuma karance-karance yanda Yrm ke nuna mata yasa ta bashi wata daraja cikin ranta.ita da Yrm yanzun kullum suna cikin lissafin kwanakin da suka rage masa,sannan anan gefen tana shirya masa kanta tana son ta tare shine yanda zai san tana da banbanci,sannan yasan har yanzu itace din dai,shiko nasa gefen tsaraba ce yake ta jibgo mata ita da danta,duk abinda ya gani sai zuciyarsa tace beauty zata so wannan,sai kawai ya loda in ma na yara ne sai yace kai bari in sai ma son,haka yake kiran yaron (son)wata rana kuma yace(my friend)wai yaron abokinsa ne tunda wai kwata-kwata da shekara nawa ya girmesa?Sai Bily tayi dariya.
[8:41AM, 12/28/2016] ‪+234 814 912 1821‬: 🏵MEKE FARUWA 85🏵

Tunda Yarima yace ma Bily beauty cikin satin nan zan diro,amma ba zance miki ga rana ba,ta kasa zaune ta kasa tsaye, harma su Umma sukai ta mata dariya.yau ta shirya wannan tayi wancan da kanta take shiga kitchen amma shiru sai kiga har dare babu labari,yau kam tasha alwashin ba zatayi komai ba,tana falon Umma bayan sallar la‘asar, Umma tana zaune kan kujera yayinda ta dora kafafuwanta kan tuf-tuf.yallabai wato jaririnsu Bily yana kan cinyarta,Bily tana zaune kasa kusa da kafafun Umma tana shafa mata maganin ciwon kafa,tare da dan mammatsa mata kafar Umma tace,‘yata yau baza‘ayi wa ubannawa girkin ba?Cike da tsokana tayi maganar,Bily tace,na gaji Umma,babankin nan ja min rai kurum yakeyi bawani zuwan da zaiyi.Umma tace,muma kinga ai munci girki kwana biyu, dama haka kika iya girki?Kafin Bily tace wani abu sai sukaji sallamar Yarima da wannan muryar tasa ta kasaita. Zaraf Bily ta mike tsaye tare da cewa, dama kana hanya? Shiko kallonsu yakeyi ransa yayi fari kar yanda ya samesu yaji dadi,Bily ji tayi tamkar ta rungumesa,shiko ita ya nufo sai tayi maza ta zauna ya kalli Umma yana dariya,sannan yasa hannu ya dauki dansa yana cewa, Umma son yayi girma fa,kuma ya kara kyau, gaskiya beauty ta iya haihuwa.Umma tayi dariya sannan tace, shirmen kan nan yana nan dai babana?To kaki sanar damu ranar dawowarka, kullum sai Bily tayi maka shiri na musamman in baka dawo ba mu da ‘yan gida kakarmu ta yanke saka sai mu kwashi gara, yace Allah sarki beauty yau dai gani ta dan harare sa cikin wasa tace,yau kam sai dai aci na gida nan ya gaida Umma sannan ya nufi sasansu Bily ta zauna zata cigaba da shafa ma Umma kafa tace a‘a-a‘a na yafe jeki gurin mijinki,haka ta bishi.

1 Comments On ME KE FARUWA
avatar
fatima-8-5

1 year ago

Reply

Uhm

Please Login or Register in order to submit comment