Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

lokacin shekarunta biyar, kawunta Aminu ya tafi da ita kallon hawan sallah, tana sha'awar kallon hawa ko a zariya tana son zuwa amma Mamanmu bata bari haka suke ce ma fatima, ba wanda ya burge Bilkisu gurin kallon hawan nan kamar wani dan yaron sarki ba zai fi shekara biyar ba tsaran ta kenan, an mishi nadi shima cikin wata alkyabba bayan shi runduna ce guda, yaron yana ta daga ma mutane hannu, itama sai daga hannu take tana mishi bye-bye, ai ko kullum bata da labari sai na Yarima. haka kawunta ya ce mata sunanshi har suka bar bauchi suka dawo zariya lbrin yarima take yi haka nan kuma sai ta shiga yin mafarkin yarima. kullum ta kwanta sai tace tayi mafarki sun wasa da yarima har abin ya ishi mamanmu tace kada in kuma jin zance yariman nan,
don haka ko tayi sai tayi shiru. kowane sassa zundenta suke wai ta ki dora ma yara talla gata da ya'ya mata, in ta tashi aurar da su saga ni me zata kai ma ya'ya daki? sam wannan bai damu mamanmu ba ita dai burinta shine taga 'ya'yanta sun samu tarbiya tare da kulawa. Bilkisu yarinya ce mai tsananin hakuri da zurfin ciki, tana da kwazon karatu da son karatu, sabanin Sakina mai fada da kin raini don haka duk kishiyoyin mamanmu ta tsane su matuka, Maryam ko sai dai fushi da miskilanci. Asma'u auta itama akwai tsiwa tun tana karamarta, yanda yayyinu suk dukan Bilkisu sai dai ta yi kuka. Asma'u kam bata raga ma abokan goyonta shi yasa rigima kullum. Salame ta shiga dakin karima tana fadin ke 'yar gari king uwar mata? Me tayi? In ji karima bayan ta bada dukkan hnkalinta, Yau kuma takalma silifas sababbi ta sai musu. kan ta yi magana sai ga Ladiyo, kunga uwar mata? A gindinsu zata kare an siyo musu silifa. Karima taja tsaki ai ta haifar ma kanta wahala mata kai ta musu bauta ko gidan Miji suka je ba ka huta ba, mu ko masu mazan da farko in sun kawo karfi sai dai mu kwanta su mana su ma kannansu matan. salame ta ce ai Allah ya taimake mu da muka fara da maza. Ladiyo ta ce ni duk ba wannan ya dame ni ba, irin in ma kalli Bilkisun nan yarinya kyau tamkar aljana? salame ta ce kuma tafi sonta ba, tsorona daya kada wani mai halin ya aure t. Ladiyo tace kada nima ina wannan tunanin amma ga shawara ta rada musu wata magana a kunnuwansu, suka saki dariya tare da fadin kin kawo shawara. Bilkisu da kannanta cikin kayan islamiya suka nufi islamiyya, sai da ta raka kannanta kofar ajinsu Sakina da mami, sannan ta tafi ajinsu, duk malaman makarantar sun son Bilkisu saboda kokarinta tare da hazaka ga ladabi ga kuma tsafta duk da cewa kayan makarantar tasu sun tsufa amma tsaf suke a wanke. ta shiga suka soma karatu, basu dade ba wani malami ya shiga da wata yarinya sabuwar zuwa ce, duk ba zata fi Bilkisu ba, ta shigo tana yan kalle-kalle alamun bakunta Bilkisu ta kalle ta cike da murmushi,
[8:45AM, 12/28/2016] ‪+234 814 912 1821‬: 🏵MEKE FARUWA 07 🏵

don haka sai ta je ta zauna kusa da bilkisu. Bayan sun tashi sun fita bilkisu tace yaya sununki? Ta ce Mansura Sadik, ke fa? Ta ce ni sunana B M S, da fatan zamu zama kawaye? Mansura cikin murna ta ce. Insha Allahu. Ta debo kannanta itama da kaninta Abba ta dakko shi daga ajin da aka kaishi suka jero suna hira. Gidan su Mansura ba shi da nisa da islamiya, don haka Mansura ta roki Bilkisu ta shigo ta gaida Ummanta, jikin Bilkisu yayi sanyi da ganin daular da su Mansura suke ciki, lallai Mansura ba abokiyar yinta bace, domin an ce kwarya ta bi kwary. hajiya mero mahaifyar mansura nurse ce mahaifinta kuwa ma'aikaci ne a {G T Bank} da ke kaduna.
makarantar bokonsu ta kudi ce mai tsada, haka ne yasa Bilkisu dan Jan jiki da Mansura, amma Mansura sai ta kara shige ma Bilkisu ta ki sai wata rana bata da lafiya don haka bata samu zuwa islamiyya ba hankalin Mansura ya tashi don haka kuwa ana tashi ta bi su Sakina don ta dubo Bilkisu. Sam Mansura bata damu da yanda taga gidan su Bilkisu ba, har ma da ta samu Mamanmu ta gama tuwo sai da taci, hakan ya sanyaya zuciyar Bilkisu don tana son Mansura musamman ma da ya ke Mansura iyayanta sun kasance yan gombe, tana ganin gombe da Bauchi kamar daya ne gunta tana son yan Bauchi dangin uwa masu sonta, tana ganin kamar bata da masu sonta sai yan Bauchi shi yasa duk inda ta ga yan Bauchi tana girmamamasu, Mansura tana da son tuwo don haka sai ta samu gurin zuwa.

Ko Bilkisu bata nan Mansura tana zuwa gurin Mamanmu jin ta take tamkar mahifiyarta waton Ummanta suka niyan gidan sai suka tsiri sakin habaici, Bilkisu ma nan ta saki jiki da Umma Umma da Mamanmu suka zama kawaye, haka ya sosa ran su Ladiyo musamman da suka ga tana basu kayan sawa zuwa dan abin marmari.

Bilkisu tana zaune ciki wani ciyayi mai kama da cafet guri sanyi da iska yanda yake Kore fatau ya bata sha'awa ga fararan tattabaru suna tashi wasu suna sauka. Can daga nesa sosai take hango dan matashin yaron tasaranta bisa kan doki yana isowa gurinta ya tsaya cike jin kai. Yace ke wa ya kawo ki gonata?

Ta dube shi nan ne gonarka? Kafin ya bata amsa sai ga wasu mutane su biyu suka kama mishi linzamin doki ya sauka, sannan ya isa wata kujera dake can gefe irin ta sarakannan ya zauna sai ga wasu mutane cikin jaja yan kaya sun tsaya a bayanshi, can kuma sai yace na sallame Ku. Suna tafiya ya dawo gurin Bilkisu ya zauna kusa da ita ke yar sakin wane lardi ne? Ta dube shi ba ni da alaka da sarauta. Ta bashi amsa, yace kin sanni? Ta dube shi cike da mamaki kai ba ka da gane mutane so nawa muna wasa da kai? Firgigita ta farka daga bacci yau mafarkinta ba irin na sauran ranaku ba ne, domin sauran ranakun tafi mafarkin suna wasan kwallon kafa, ko na raga koma na tebur, suna hira sosai, amma ya kan nuna bai ma Santa ba ne, tayi murmushi, tun tana yar shekara shidda take mafarkin Yarima gashi yanzun tana shekarar karshe a primary shekarar haihuwa kuwa sha daya su Bilkisu an soma zama yammata, kyanta kullum karuwa yake yi.
Hankalin mamanmu ya tashi domin ba ta da kudin da zata yi ma Bilkisu hidima dan zuwa secondary, duk da cewa ta ci domin makarantun gwamantin ma wannan zamanin sai kana da hali. Da kanta taje makarantar da Bilkisun ta ci sun mata lissafin tun daga rijista zuwa uniform da takardu dubu takwas har da dori. Hankalinta ya tashi bata da inda zata samo kudin nan, gidan hajara kawarta ta shiga don yin shawara, hajara ta bata shawarar me zai hana Bilkisu ta yi aikin gida ko na wata uku ne, in yaso sai ta shiga a zango na biyu tun da an amso form. Mamanmu jarumar uwa ce wacce samun kamarta sai an tona, tsamaranta cewa zata zamar wa ya'yanta uwa kuma uba, don haka ta ce ma hajara ni zan yi aikin da kaina wa ki ke ganin zan samu ya nemo min aiki? Hajara ta ce kada ki damu akwai mata masu hali da suke zuwa gurin malam zan dinga musu magana har a dace, shin maigidan naku zai barki?
[8:46AM, 12/28/2016] ‪+234 814 912 1821‬: 🏵MEKE FARUWA 08 🏵

Ta ce tunda ba bani zai yi ba ai batun hanawa ma bata taso ba, shi fa yanda na kula koma menene kije kiyi amma kada ki tambaye shi, sukansu kishiyoyin nawa da yake sonsu baya musu komai, amma don rashin tunani suna nan suna ta zabga gasar haihuwa,yaran bacin kirki bare sutura, karatu kuwa sai dai na zagi ashar kam, kwando-kwando za ki ga dan karamin yaro yana saukewa, gaskiya 'yan gidanmu su ne suke bata ma zage zagi suna, shin haka kowane gida suke yi? Hajara tace a'a akwai dai masu yin amma ba duka ba.. Cike da farin ciki tabar gidan hajara, ta samu Bilkisu da yan kannanta a cikin daki, tana koya musu darasin lissafi, nan ta zayyane ma Bilkisu komai, Bilki ta ce mamanmu ki bari ni nayi aikin in an samu, ta ce a'a nafi soe ni in yi bana son kije ki bata ma masu gidan har su sallame ki, bukatarmu ya zama bata biya ba. tace mamanmu amma kinsan bana fada ko? tace na sani maigado, amma ki bari sai dai an samu din kisan ke yarinya ce ba kowane abu ne zaki iya yin shi ba. Sallamar Mansura ta katse su, suka amsa ta shigo kusa da mamanmu ta zauna sannan tce mamanmu ina kwana? Suja gaisa ta dubi Bilkisu tace "Bily ya dai, yaushe zaki fara shiga school ni dai on monday zan fara zuwa. Bilki tace ni kam ba rana Mansu, kila ma sai second term. Mansura tace akan me? Tace kudi, mamanmu tace kin san ko mai yanzu sai da kudi ana cewa ne dai makarantar gwamnati amma suma duk shegiyar darin ce ga kudin motan zuwa makaranta kullum mansura tace bari Abbanmu yazo week end zan gaya masa. Bilki har suna hada baki da mamanmu, a'a kar ki yi masa magana shima yana ji da nasa iyalin. Mansura tayi shiru, amma a ranta ta raya sai ta fada mashi... Haka kuwa yana dawowa ta gaya mishi, ya tambaye ta ko njawa suke nema? Ta ce ya basu kowanne ita dai bata sani ba, kuma ta san ko ta tambaye su ba zasu fada ba. Dubu goma ya bata yace, gashi ki basu." sai da ta kai kudin mamanmu da yaranta suka je suyi godiya,Bilki kuwa sai da tayi kukan murna, sannan tana ta mamakin dama da gaske ne akwai iyaye masu yiwa 'ya'yansu hidima? Ba sabanin iyayansu mata da wahala? Cikin nasara ta shiga j.s.1 mansura kullum in za su je makaranta sai ta saka direbansu ya biyo sun dauki Bily, sunan da ta ke kiran bilkisu kenan, ita kuma Bilki tace Mansu, wani abin da yake kara ba Bilkisu mamaki shi ne, yanda mafarkin Yarima ke kara yawaita a gare ta, ko gyangyadi take sai ta yi bare barcin dare. saboda sabon da suka yi har ta saka mishi Yarima aboki, shi ko yana kiranta Beauty, tana son sanar da mamanmu amma tasan mamanmu zata ce shirme ne, shi yasa take bar ma cikinta don ko mansu bata taba ba wa lbri ba. cikin haka hajara tazo ta ce, an samu aiki. Mamanmu tace ai ko zan yi,
[8:46AM, 12/28/2016] ‪+234 814 912 1821‬: 🏵MEKE FARUWA 09 🏵

Suka je gidan hajara inda hajiyar da za a yiwa aikin take jiransu.Bayan sun gaisa tadubi mamanmu tayaba da tsaftarta don haka tace girki nake so zaki iya? Mamanmu tace me zai hana.Nan suka sasanta ita da hajiya kilishi, gidanta na nan tudun wada, sun sasanta kan dubu uku, kuma za'a dinga zuwa ana daukarta haka nan za'a dawo da ita ko da ta samu maigidan nasu da batun sai yace,shi ina ruwan shi,ta dai sani dole ran girkinta tazo shima ta mishi,dama tasan haka zai ce,tunda shi dama baya son ma mace tace ko da bani kudin kamu,wani lokaci takan zauna tana tunani, anya maigidansu yana son lahirarshi ta mishi kyau?In'yan abinshi suja motsa haka zai je ya nado tsiranshi yazo ya zauna gaban'ya'yanshi yana ci ba zai sammusu ba in ma yaga suna kallonshi sai yace kai daina kallona ka da ka saka ni in kware.Ko ya fita bakin titi da yamma ya sayi doyarshi da kwai ya zauna yana ci in an ce yara suzo suce yaba da kudin cefane sai yace kai zauna nan kayi wasan ka shareta,kuma fa in yaron nan ya zauna haka zai cinye ya hana yaron, halin wannan mutum sai shi hakika baici sunnanshi ba. Cikin sa'a Mamanmu ta soma aiki tana tafiya da safe in yaranta sun tafi makaranta da sha biyu suke maidota gida, in ta gama musu abincin rana domin tana son ta zo ta sallam yaranta. hajiya kilishi kan ce Dibar musu ki kai musu. Sannan karfe hudu zata koma tayi na dare, in ranar girkinta ne kuma sai shida take tafiya don ta samu ta gama na gida. Su kam su ladiyo, nan suka soma nuna hassada tare da canza mata suna daga uwar mata zuwa boyi. Su yi ta mata habaici tare da maganganu marasa dadi, kafin wani lokaci mamanmu da 'ya'yanta sun canza,sunyi kyau, saboda cima ta canza in ta kawo abincin takan dibar musu ta mika ma ladiyo tace su ba wa yara, suna zaginta suna komai haka zaki ga suna kason su sai kace daukin nama su da ya'yan suna ci tandar harshe. Hajiya kilishi tana da yara mata kusan sa'annin su Bilkisu don haka suna samun kaya. Rayuwa dai ta canza yanzu har da sabulu mai kamshi suke wanka. Cikin haka suka shiga J.S 2 lokacin alamun girma ya soma shigar ma Bilkisu, kyanta ya soma bayyana, duk layin kowa sai zancenta yake yi, sun kuma kara shakuwa da mansura duk in da kaga zara za ka ga wata.Bilkisu tana da kulafucin karatu don haka bata da lokacin komai sai na karatu. Azumi ya matso gashi, lokacin ana fama da rashin kudi a gari, 'yar doyar da maigidan ya kawo buhu daya ce, nan ya kasata gida hudu yace kowa ya kwasa sannan kada wacce tai mishi zancan geron kunu domin ba shi dashi, cikin haka Azumi ya kama. Saboda rashin hankalin su ladiyo sai suka ce ma maigidan su fa kowa tayi girkinta kenan suna kyashin taimakon juna, maigida yace wannan lalurarsu. Mamanmu ta ji dadin hakan domin ya'yanta hudu ne,kuma dama aiki yana mata yawa,ranar girkinta yanzu kam hajiya kilishi tace ki dinga hada girkin tare da yaranki,dama ga alale da kunun tsamiya na sadaka da ake yi ana bai wa al'ummar Annabi sai kurum ta huta da yin girki biyu,in ma dakinta yake sai ta dibi nashi cikin kwano samira da kunu a kofi. Bilkisu taje ta amso, wataran ta roki direban ya kawo nan zaka ga malam maman an baza tabarma tsakar gida ana kwasar gara, cefanan wani kai ka kasa, haka matan ke ce mishi,in sunga yana rawar kan cin abinci ran girkin mamanmu,haka nan mijinta da yayi rabon kayan azumi shinkafa, masara,gero,da kuma suga sai daya ba mamanmu kowanne buhu,jikin kishiyoyinta ya dauki bari bakin cikinsu ya kasa boyuwa ita kam kowa sai da ta dibar mishi har 'yan sauran sassan da su rukarta su goggon sasa tare da matan yayyin maigidan nasu da na kannai. Wato mamanmu mace ce mai rama alkairi ga duk wanda ya mata sharri, tana da matukar hakuri tare da sanin ya kamata, in ban da haka yanda kishiyoyin nan nata suke mata kai har shi kanshi maigidan yafi mata wulakanci akan sauran kishiyoyin nata, amma hakan bai sa tayi tunanin cin zarafinshi ko kishiyoyin ta ba sai ma kyautata musun da take yi, shi yasa kullum cikin ci gaba take. Hatta abincin sadaka ko nata in tayi sai ta basu..
[8:46AM, 12/28/2016] ‪+234 814 912 1821‬: 🏵MEKE FARUWA 10🏵

Bilkisu tana tafe amma duk wanda yasan ta in ya ganta yanzu zai fahimci tana cikin damuwa,duk da cewa dama ita ba mai son hayaniya ba ce, ko yawan dariya akan hanya,ta tsaya kofar gidan su mansura tace Sakina shiga kice ma Mansu in ta shirya tazo mu tafi,mun yi latti. Sakina na saka kai Mansura na fitowa,tace "ashe kun iso?Nima naga shiru nace bari naje gidan na gani shin lafiya?Bilkisu ta dan yi tsaki sannan tace, to lafiya,suka soma lafiya mansu tana korin cewa. Gaskiya bily ban yarda lafiya ba,idanunki kamar kin yi kuka.Tace kawai bana jin dadi ne.Ko a islamiya bilkisu babu kwanciyar hankali duk malamin da ya shigo sai ya gane,saboda zazzakar muryarta mai kayata karatun nasu in suna yi yau adusashe take,haka nan kyakkyawar Fuskarta yau kam a daure take tam.Mansu ma duk ta damu suna tashi bata shiga gida ba sai kannanta tace ma ku shiga gida ku ce ma umma zan gaida mamanmu in dawo, Bilkisu ta dubeta mamanmu tana gidan aiki,mansura ta kada kai na sani ina so ne muyi wata magana,suka nufo gidansu bily.
Sai da suka zauna sannan mansura tace wai me yake damunki ne bily? Bilki tace ba komai Mansura. Ta daga mata hannu alamar tayi shiru, ina baza ki fada min ba to in tafi gidanmu kawai bana son dogon labari. Bilkisu tace to ni ban san ta ina zan soma ba, abinne kamar tatsuniya kin gane! Tun ina karama ne muka taba zuwa sallah bauchi,shi kenan kawuna yaje dani kallon hawan sallah, naga dan sarki, shima yayi hawan, dan yaro ne tamkar ni a wancan lokacin shi ne fa tun daga nan kullum ina cikin mafarkinshi har yanzun. Mansura tace ban gane ba? Bilki tace ai ba zaki gane din ba.donni ma da bani ce ke yi ba zan karyata ne. Mansura tace wane irin mafarki ne haka kullum kina mafarkinshi ya kara girma ko yana nan kamar da? Sannan shi ne sanadin bacin ranki yau? Bilki tace, yana girma nasan zaki sha mamaki in na gaya miki tun daga randa na ganshi, nake mafarkinshi har yau din nan ko gyangyadi ne ya dan sace ni sai nayi mafarkin shi,sunan shi Yarima modibbo, yana da kyau kuma dan kwalisa ne komai nashi da ka'idarshi Komai da lokacinshi, misali baya cin abinci a lokacin karatu,kin gane irin abun yana ce min wasan da yake zuwa muna yi lokacin wasan kenan, awa daya da rabi muke yi sai ya tafi, wai baya son shiga lokacin wani abin, kuma shi ma'abocin son girma ne, baya son raini ni fa da shi har fada muke yace ya girme ni, ni kuma in ce karya ne yanzun nan zaki ga yayi fushi ya tafi nesa dani kafin lokacin tafiyar shi yaya. Mansura taja tsaki, ni don Allah ki gaya min damuwar yau. Bilki tace kin cika garaje baza ki gane ba ne hn ban miki dalla-dalla ba. Haka muka taso tare dashi cikin mafarkina shima yanzun js3 zai je, kin gane ai jiya kuma ita ce ranar da nayi mafarki mafi muni kin aji, wai sai na isa gurin da muka saba wasa, yau ma na riga shi zuwa kamar sauran lokutan, sai dai har lokaci yayi nisa bai iso ba, na soma damuwa ga hadari har an soma yayyafi, dan tsumman riga da siket din da ke jikina suka jike dama sun sha jiki sai suka matse min a jiki iska ta shiga kada min shi, ni kadai a filin Allah,

Kamar daga sama sai naji an dafa ni ta baya ina juyowa sai nagaYarima tsaye,yana sanye ne da riga da wando na farin shara-sharan yadin shi ma din duk ya jike,nace zan tafi dubi duk na jike,ya dubi kirjina,don kirgan dangin daya soma nuna yake kallo,nace zan fa tafi fa,in gaya miski mansu sai jina nayi a jikinshi,na soma kai mishi duk ina cewa,bani son iskanci an ce maka ni yar iska ce?Yace ke wawuya ce beauty wani wasa Zan koya miki In dai takaita miki wai sai gani ni da shi muna...Mansura ta rufe mata baki ita kuma ta fashe da kuka,mansu tace shi ne to na damuwa ba a cikin mafarki ba ne?Nace bara fa kiji tashi nayi na ganni cikin jini...Jini? In ji mansura,bilkisu tace eh shiyasa narasa yanda zan yi,kuma na kasa yaya ma mamanmu tsorona daya kada ace ina da ciki mansura tace gaskiya ne kin sani yanzun muje mu samu.Ummarmu tunda ita tana aikin asibiti ne zata sani,da sauri bilki ta mike.Sun same ta tana sallah suma suka yo alwala har zasu tada salla,mansura tace kin mata malam yace,inda jini jikin mutum bazaiyi salla ba Bilkisu tace ai yace jinin haila ni ko wannan ba haila bace bana ma yin wannan, wannan fa kin ji yanda aka yi jinin fa yazo, basu ji shigowar umma ba sai suka ji tana cewa wane irin jini ne? Tsuru-tsuru suka ji tace da ku nake fa, kuka bilki ta soma yayin da mansura ta soma magana cikin in-ina, gaya mata dai. In ji mansura, cikin kuka bilkisu ta shiga bai wa umma labarinta da Yarima har zuwa jiya, a karshen lbrin ta dora da cewa ni tsorona kada ace ina da ciki. Tamkar umma ta kwashe da dariya, amma sai ta boye tace kin san haila ko? Bilkisu tace malamin fikihunmu yana mana bayani amma ban santa ba, umma tace to haila ce ta same ki, batun mafarki kuwa sai dai na kiya ya dan tsoratani, yanda ki kace tun kina karama, Allah yasa ba aljanu bane suka fake da Yariman da ki ka gani? Kin san suma shu'umai ne, amma zan yi batun da mamanku.
Sannan ta dube su tace, yanzu abin da zan ce muku shi ne dake da ki ka balaga da ita din da bata soma ba na sani tana kan hanya, ku kula. ta dai ja musu kunne.ta fita sai gata da part ta nuna mata yanda zata yi amfani da shi, umma ta samu mamanmu sun zanta kan batun mafarkin Bilkisu, mama tace bana zaton maigado tana da aijanu, kinsan in ka kallafa abu a rai dole ne kayi mafarkinshi, tun tana karama da taga dan sarkin garinmu shi kenan bata da zance sai nashi. Umma tace to bilkisu tana da nutsuwa sai dai ki kara ja mata kunne ko in ce nasiha, tunda yanzun ta girma sai da saka ido, dan yau sai Allah. Mamanmu tace Insha Allah komai zai zo da sauki,Allah dai ya shirya mana daukacin ya'yan musulmi.Umma tace.Amin,yau din ce tayi wuya,sai ki ga yarinya ta tashi da hankali da nutsuwa,ki daga ki yi mata tarbiyar kwarai daga baya sai kiga samari ko wasu kawaye sun rusa komai. Mamanmu tace kwarai dole ne mu sanya ido kan ya'yanmu, wadannan irin kawaye ne suke tare dasu,haka nan kar mu yarda da samarin banza.
[8:46AM, 12/28/2016] ‪+234 814 912 1821‬: 🏵MEKE FARUWA 11🏵

Da wannan hirar suka yi bankwana.Tun daga wannan lokacin take tsoran maza sam bata son wata hulda ta shiga tsakaninta da kowane namiji,balle da mamanmu ta kara nuna mata cewa kar ta yarda da 'yan kananan samarin nana masu bata yara suna kai su suna barowa.Mamanmu tace ki lura don shi da namiji duk abin da yayi ado ne, ke kam mace ce duk in ki ka yarda aka bar miki abin kunya shi kenan rayuwarki ta lalace,koda ba ai miki ciki ba da an kau miki da budurcinki shi kenan,duk mijin da kika aura baki da wata daraja ko mutunci a gunshi in me kawaici ne zai daure ya barki da Allah,in ko mai zafin kishi ko in ce wanda ba zai iya hakurin bane kisha magana gori har yaranki suta so yana miki don haka ki kula. Bilkisu yarinya ce amma akwai zurfin tunani, domin tun daga nan tasa ma kanta da nazari kan maza ana ta ganin maza sun cika son kansu musamman in tayh duba ga mazan gidansu tun daga kan yayun da kannai na mahaifinta tare da shi kanshi mahaifin nata mazan gidansu daidai gwargwado suna samun kudi da irin sana'ar da sukeyi. Amma sam ba sa biyama iyalansu bukatu, ya'yansu babu boko babu islamiyya, sai yawon talla, kusan duk matan gidan su ke ci da kansu da kuma ya'yansu,ba sutura, amma abin da yake bata mamaki yanda su kuma matan ke faman gasar haihuwa tare da fada da kishi mai tsananin a junansu, saboda mijin da bai san darajarsu ba, ita kam ta gode Allah da yasa mama ta kasance uwa agare su don ta tsaya musu da tarbiya da ganin sunyi karatu sun zama yaran kwarai, kuma insha Allah baza su bata kunya ba, sannan su zama rahama

1 Comments On ME KE FARUWA
avatar
fatima-8-5

1 year ago

Reply

Uhm

Please Login or Register in order to submit comment