Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

taga iyayan suka nuna karara son dan nasu suke,haka nan manyan mutane abokan nasa da wasu da suka samu zuwa daga cikin danginsu sai ina ka saka ake dashi.Umma ko sororo tayi lokacin da suka hada idanu da Bily, tasa rai ta ganta tana daga kafa da kyar sai gata tangaran to ko dai karami ne ko kuma yabi jiki?Duk wannan tunanin Umma ne amma tasha alwashin zata tambaye su taji kar dai suna shan kwayoyi ne?Yin wannan tunanin sai da gaban Umma ya fadi tace,inko haka ne sun cucemu.Bayan shan ruwa sunci sun sha ana zaune ana hira kafin lokacin zuwa masallaci,Umma ta dubi Yarima tace,ubana na zaci zanga matar taka da tsohon ciki?Yarima yace,haba dai Umma tun yanzu?Tace kaji shashanci da sai yaushe mu da kullum addu‘armu muga ‘yayanka,yace dazun ma mai martaba fa cemin yayi wai to kai Modibbo in zamu tafi da matarka zamu wuce inta haihu sai ta dawo,abin ya daure min kai nace ranka ya dade tana da ciki ne?Sai cemin yayi kuji zancan banza, ni zaka tambaya?Suka kwashe da dariya, Umma da Magaji.Yarima murmushi yayi don shi baya kyalkyala dariya.Bily kam sai tayi kasa da kai, Magaji ya mike tare da cewa zo muje masallaci. Yarima yace kwarai muda bamu zo da wuri ba.Suna fita Umma ta dubi Bily wai da gaske ne ‘yar nan baki da komai?Kunya ta rufe Bily,kanta na cikin cinyarta tace,wallahi Umma ba komai,tace ko dai kwaya kike sha ne?Tace Allah bana shan komai,tace ko shine dai ke baki,yace kada ki fada?Don fa karki yarda ki dinga shan kwaya nan gaba ta miki illa,kinga shi namiji ne da zarar yaso ‘yaya zai iya karo aure,ke kuma an cuceki. Bily tace,wallahi Umma bama shan komai,to kun taba ganin likita?Cewar Umma,a‘a inji Bily,bamu taba gani ba,tace to wannan ai shirme ne,kafin mubar garinnan sai munje kunga likita. Gurin kwanciya, Bily ta shige gurin Umma dama su Yarima suna can masallaci suma zuwa sha biyu suka nufi masallacin, haka sukayi ta ibada har ranar sallah.
Bily kam ranar data ganta gata ga Ka‘aba,ai addu‘a sai wadda ta manta. Murna kuwa harda hawaye, domin arayuwarta bata taba tunanin yau rana zata zo da zata ganta agaban Ka‘aba ba.A cikin addu‘o‘in da Bily tayi ta roki Allah game da aurenta da Yarima,kan cewa in mai shiryiwa ne Allah ya shirya shi sannan ya daidaita tsakaninsu in kuma babu daidaitawa,to Allah ya watsa abin ya kawo mata karshen wahalarta,sannan ta roki Allah ya sassauta ma mahaifiyarta,game da abokan zamanta ya kuma sa mahaifinta ya dawo kan hanya.Ranar sallah mai martaba ya nufo gida,Umma dai ta tsaya sai sunga likita.Daran ranar Yarima ya kasa hakuri da jarabarsa ta motsa,dakin Umma ya shigo Ummar tana toilet sai Bily dake zaune,tana neman layin Mamanmu sun gaisa da kowa amma ta kasa samun Mamanmu ya dubeta ransa ya sake biyawa,amma girman kai ya hanasa yayi mata magana.Har zuwa sanda Umma ta fito,tace yaya ne babana?Ya danyi murmushi sannan ya dubi inda Bily take zaune yace ba komai dama nazo ne nace miki sai da safe. Abinka da manya,nan Umma ta gano nufin dan nata,don haka tace,Bily tashi kije gurin mijinki mana, ni sai naga ma kamar gudunsa kike tunda muka zo banga kina bashi wata kulawa ba.Tana wannan maganar ne bayan fitar Yarima,taci gaba da cewa kin san fa su maza ‘yan lallashi ne,suna san kulawa bare irinsu Yarima.Bily tace Umma ba kirana yakeyi ba,Umma tace kaji sokuwa, yanzun yaushe ake jiran kiran miji?Har dai Yarima dan jin kai?To maza tashi ki bishi dama zaman da kukeyi kenan sai yace zo? Tashi-tashi maza-maza kar in sake jin haka.Bily ta mike ranta bace zata tafi,Umma tace,haka zaki je ba ko dan saka turare?Bily kam ta cika ne da mamaki,da bata zata haka Umma take ba,kuma sai tana ganin kamar ko san kai ne Umma take nunawa,don dai Yarima danta ne,duk da ta sani Umma tana sonta.Hoda ta murza sannan tasa turare ta saka kayan bacci sannan tasa hijabi ta fita,yana zaune bakin gado ya rasa me ke masa dadi,kamar ya zama kuda ya dauko Bily yake ji. Ta shigo da sallama fuskarta daure, tamkar an jefa shi cikin gidan aljanna haka yaji,harda yin wata ajiyar zuciya,amma don jan aji irin na Yarima sai ya wani daure fuska tare da cewa, lafiya ?Bata yi magana ba,ta zauna can gefe kan kafet,kin shigo min daki kina ta wani daure-dauren fuska bayan ban kira ki ba.Shiru dai ta masa,yace ok,in baki da magana tashi ki kama gabanki.Ga mamamkinsa sai yaga ta mike zata fita,yasha gabanta, ai bazaki fita ba har sai naji dalilin zuwanki. Bily ta dubesa, Umma tace inzo,oh shine dan kin raina Ummar zaki koma can ko?Tan ki koma din,ya koma gefen gadonsa ya zauna sannan ya dauko laptop dinsa ya soma kunnawa tana dai tsaye.Ta dawo ta zauna inda ta tashi yaci gaba da tura wani assigment ya jima yana turawa har ya gama,lokacin ta soma gyangyadi yace,ke ta farka idanunta fal bacci yace zo ki kwanta ba don halinki ba,tace nan ma ya isa, yace ke komai sai kin min gaddama,harda kice nan ya isa ance miki ina kalanki ne?Kema gulma ta kawo ki ko da Umma tace ki zo nasan kina son zuwan ko don a sosa miki abinda ke miki kaikayi, bani da yanda zanyi tunda an makala min ke.Mikewa kawai tayi taje ta kwanta, sai daya gama mata wulakanci kala-kala sannan ya shiga yin abinda ransa ke so da ita,jikinsa har bari yakeyi duk da dai yau ma kamar kullum,gim ta masa kamar kullum,haka ma da safe gari yayi haske amma ya fake da cewa kada ta kuma dawo masa yau bari ya sallameta gaba daya,bashi ya barta ba sai da Umma ta kwankwasa musu ita dai ta sani arashin ‘yanmatansa ne ya kula ta shiyasa bata jin itama zata sakar masa kanta yanda ta kula yafi bukata, ta aje aranta yanda ta rasa wanda zaice Bily ina sonki,haka ta hakura da jin wannan dadin don a duk lokacin da Yarima yake kusantar ta zuciyarta tana gaya mata cewa makiynki ne ke son hutawa da ni‘imarki,don haka sai taji duk mugayan maganganun da yake gaya mata suna dawo mata,kuma sai taji tana kyamarsa saboda matan da yake hulda dasu, sannan burinsa na taji dashi dadi ba zata ji dashi ba har abada,sai dai yanda suka saba.
[6:28AM, 12/28/2016] ‪+234 814 912 1821‬: 🏵MEKE FARUWA 67🏵

Suna zaune gaban likita sun masa dukkan bayanin daya dace,sannan ya shiga dubasu.likitan ya tabbatar da cewa lafiayarsu lau,sannan ya basu wadansu kwayoyi wai su sha bayan sun dawo gida Umma tace,to su zo suje suyi tsaraba don ita gobe jirginsu zai tashi zuwa Nigeria su kuma sai gobe sannan zasu wuce Malesia tace wallahi Umma naso in biku gida nayi missing din Mamana.Umma tace,me zaki je Nigeria kiyi mijinki yana wata duniyar?Ke dai kiyi hakuri ba shekara mai zuwa bace zai gama ko ta sama ce? Kamar yau ne gurin Allah Mamanki ba kuna waya ba?Tace mu kanyi saboda yawanci sai sanda Mansu taje gidan sannan ta kira ni,Umma tace a‘a bata da waya ne?Tana da shi,inji Bily to ni yaushe rabona da wayata taga kati sai zuwanmu nan da Magaji yasa min,Umma ta kalli Yarima, me kenan babana?Yace to Umma yaya zan mata,ita fa tunda taje tafi karfin tace min tana son kaza,ko na ci ko a na sha bare kati, Umma tace to ke kuma ai wannan hauka ne, keda mijinki?Kusan shekara kin kasa sakin jiki dashi to dawa zaki saki jiki?Ki daina haka kinji ko, gaki kamar kanki a waye?Duk abinda kike so ki masa magana tace,to Umma yace kuma da kanta take abinci amma bazata ce tana son abu kaza ba,madam dora ce ma take gaya min cewa, tana cin taliya shine in sun zo shi cefane sai nace ya siyo mata,Umma tace ta daina haka Bily tace to insha Allahu bazata kara ba, azuciyarta sai mamaki takeyi shin Yarima da gaske ne da zata tambayesa abu zai mata?Tasan kila bazai ba don dai yaga mahaifiyarsa ne kurum.Sun shiga siyayya shagunan larabawa,nan taga mamaki Umma cewa tayi duk me take so ta diba na tsaraba nasu Mamanta ma ta dauka sai ta wuce dasu ta bada akai musu,amma ta kasa daukar komai sai Umma ce ke cewa, dau wannan dau wancan daga karshe ta daukar ma Asma‘u auta dankunne da sarka na gold ita da yarinyar Mansu,sannan ta yiwa Dady tasa haka suka yi ta shiga shaguna suna kashe kudi,Yarima dai ya jidi kananan kaya harda ‘yanmatansa yayi ma tsaraba,da Umma tace na Bily ne kai tsaye yace a‘a ya sayawa abokan karatunsa ne,kuma ga mamakin Bily Umma ba tace komai ba.
[6:30AM, 12/28/2016] ‪+234 814 912 1821‬: 🏵MEKE FARUWA 68🏵

Komai me lokaci yana da iyaka,su Yarima anyi jarabawa cikin nasara an gamata a sa‘a,ya zama cikakken likitan mata gwani,Doctor.Ana gobe za‘a tabbatar musu da zamansu likitoci,su Magaji suka iso tare da mai martaba,da kuma wasu daga cikin yayyansa,tunda Umma ta sanarda Bily zuwan bakin nasu,suka je kasuwa don shirin tarbar bakin,sun kammala komai,sannan bakin suka iso.Su anty Fulera sai ‘yan harare-harare akeyi,Bily dai ta kula da take-takensu amma ta share ita farin cikinta daya, kammala karatun Yarima zata gida taga Mamanta da ‘yan uwanta,ranar rantsar da likitocin rana ce mai mahimmanci gurin Yarima da mahaifinsa guri yayi guri,manyan mutane daga nahiyoyi sun halarta. Yarima shine dalibi mafi kwazo cikin daliban da suka hattama karatun,don haka hukumar ilmi ta kasar ta bashi lamba ta farko data yabo sannan ta bashi dama ya zabi duk kasar da yake so cikin jerin kasashe goma don yin wani course na daban har na tsawon shekara daya ko biyu,wannan nasara da Yarima ya samu tasa shi farin ciki shida masoyansa,sun shirya ‘yar kwarya-kwaryar party shi da abokansa. Can gida kuma suma suna tasu walimar.Mai martaba dai yana can masaukinsa,tun ranar suka so,a nade kaya farin ciki gurin Bily ba‘a magana, a daren ana gobe zasu dawo gida Yarima an samu nutsuwa,tunanin shi daya inya koma gida babu mata kenan, Allah sarki,Ashly yarinyar da suka hadu babu dadewa tana masifar ji dashi, shiyasa ma yake matukar sonta don shi yana son akula dashi,ko bai sallama da kowa ba dole ne yayi sallama da ita,suna hira ne da ‘yan uwansa amma ya mike can gefe ya kirata ya kuma sanar da ita cewa su hadu guri kaza. Ashly irin black american din nan ce,tana da tsawo da kiba,amma kibar ta a mazaunai ne da kuma kirjinta,tana son Yarima musamman data fahimci shi mai sha‘awa ne,tana matsa shi sosai kuma ba tsararsa bace,zata girmesa,kafin yaje gurin ta rigasa,sun lalace son ransu sannan ya tile mata kudi sukayi sallama,kuma ya mata alkawarin indai ya ga da sarari zai mata kwatance tazo Nigeria itama harda kuka,nan Yarima ya kara susucewa danshi yana so yaga mace ta mutu kansa. Sanda ya dawo suna ta hira da Bily,yana shigowa ta kallesa ta kauda kai tasan me yaje yay,haka nan Magaji.Washegari suka hau jirgi sai gida. Abuja suka sauka,Bily tana shakar iskar kasarta sai taji tamkar an sakata cikin gidan aljanna,nan suka hau wani jirgin zuwa Kaduna,Bily taji tamkar ta sauka zaria lokacin da suka dauki hanyar Bauchi. Lifaya sosai aka shirya musu,sunci sun sha ana ta hira ita dai Umma damuwarta rashin ganin Bily da tsini agaba,haka sauran kishiyoyin Umma sai da sukace amare har yau anata amarcin tukunna?Anty Fatima tace,mu bama son wani amarci,‘yaya muke bukata,mun gaji da sai dai aci ayi kashi.Umma tace kadaku matsa mata, haihuwa aita Allah ce,ni damuwata ma ko kiba banga ta kara ba ‘yar tawa. Anty Saliha tace, amma Umma aita murje,dibi yanda fatarta ke sheki,sai kace tarwada?Bily dai tana jinsu,ita dai matsalarta daya tana son ganin Mamanta,zata gwada tambayar Yarima ta gani ko zai barta?Da safe ta shiga gurinsa ta samesa zaune yana kallon(BBC)ta zauna dan kusa dashi tace ina kwana?Ya dubeta dama kin iya gaisuwa?Tace to inna gaishe kane baka amsawa,ya dan taba baki tare da cewa,kina bukatar wani taimako ne?Tace,em dama ina wannan ne ya dubeta kiyi magana bana son kwana-kwana,tace ina son naje naga mahaifiyata ne,yace yaushe?Tace duk sanda kace,yace shikenan kije sai sanda nace din,tace to yaushe? Yace bana son naci ki jirani tukunna,tace shikenan ta mike ta fita.Satin duk bata da sukuni ba ta zuwa sasan shi shima baya nemanta duk da yana bukatarta,jin shiru ne yasa ta sake nemansa taje da dare baya nan da safe zata shiga kenan tazo falonsa na kasa sai gashi ya sauko tayi sauri tace,ina kwana?Ya amsa da lafiya, zai wuce tace gurinka fa nazo,ya tsaya sannan ya juyo yana kallon lebunanta da matsala ne?Maganar zuwa gida kaga tunda nazo ban taba zuwa ba ka dubi tsawon lokacin?Ya soma tafiya da cewa duk sanda kikaga ya dace sai ki sanar dani,tasha gabansa da sauri yau ko gobe,yace fine ya fita ta tsaya shiru ko dai gatse yake mata?Kai takan rasa gane hali irinna Yrm,shi kullum ana tarasa nan yana botsewa data shiga gurin Umma suka gaisa ta sanar da Umma cewa tana son zataje gida don taga mahaifiyarta,kuma ta sanarda Yrm yace ko yau ko gobe,Umma tace sai dai goben don sai an sanarda mai martaba,tace to data shiga dakinta murna harda tsalle,sai kace karamar yarinya.Ta kira Mansu ta shaida mata cewa gobe tana zuwa,ta kira su Maryam da Sakina duk ta sanar dasu,ta kira Mama tace gobe tana hanya,Mama tafi kowa murnar zuwan Bily,saboda gorin da kishiyoyinta suke mata cewa sukeyi tir da wannan ‘yar ta samu daula ta mant da uwarta,gori harda surukarsu Gwoggo amarya,tace inda kwadayi to da wulakanci,an tura yarinya gidan miji gidan sarauta don kwadayi gashi nan kila ma tana can tana wahala,inba haka ba shekara nawa bata zo ba,kamar an saida ita.haka nan ‘yan unguwar akayi ta surutu,wasu ma sai sun hadu a sha‘ani sai kaji sun ce ina amare?Ana can dai,Mama kance um tana can da an dameni batayi aure ba batayi aure ba,yanzun kuma tayi an koma kan bata zuwa indai tana zaune lafiya acikin dakinta ai alhamdulillah, sai kaji mutane ana cewa hakane fa,Mama tana sa tare da cewa insha Allah maigado tazo garin nan sai nace ta shiga duk makotan nan ta gaidasu. Malam ya shigo tace, Malam gobe fa maigado tace tana hanyar zuwa,murmushi ne ya subuce masa cike da fara‘a yace ikon Allah,nidai dama kullum yarinyarnan tana raina,lallai muna da babbar bakuwa,Allah yasa ta iso lafiya,Mama tace amin.Bily daren ranar batayi baccin kirki ba, saboda tsabar murna,tunda duku-duku ta shiga gurin Umma, umman lazimi takeyi don haka gefe ta samu ta zauna bayanta gama suka gaisa,Umma tana murmushi tace,Bily kin kosa kije gida ko? Tayi dariya tare kuma da sunkuyar da kai,Umma tace to kinyi tsaraba ko?Bily tace,sai dai wadda muka yo daga malesia, tace a‘a wannan tayi kadan tunda kila wasu kika gayyade kika sai musu wannan ko ganin gida zaki je,gashi baki taba zuwa ba,sannan gashi kina gidan sarauta,ina Yariman?Tace am yana daki,ta dai fadane don ita yanzun dai bazata ce ga inda yake ba,Umma tace ya dace ma ace tare kuka je dashi,donsu gansa,tunda bai taba zuwa ba
[6:31AM, 12/28/2016] ‪+234 814 912 1821‬: 🏵MEKE FARUWA 69🏵

Bily tace to sai dai inya shigo ki masa magana kiji,Jakadiya ta shigo da sallama,sannan ta zauna ta gaida Umma suka gaisa da Bily,Umma tace Jakadiya a duba cikin store din nan afito min da bandiran zannuwa da kuma shaddodi,tace to ranki ya dade,zamu sha sababbin dinkuna kenan?Umma tace a‘a ba naku bane,Bily ce zata ziyarci mahaifanta. Jakadiya tace, a lallai gimbiya yau sai murna,Umma tace da Yariman ya shigo ai da kunje kuyi ma mai martaba sallama,kafin ta rufe baki sai ga dan halak din nan shikenan ma kuje ta yiwa mai martaba sallama kaima kuma ya dace ace kaje ka gaida surukan naka. Yarima ya dan ya mutsa fuska sannan yace gaskiya sai wani lokaci Umma,don yanzu ina Busy na shirye shiryen Zan je wani course wanda muke matsalarsa anan Nigeria ma‘ana in samu wani horo game da wata cuta wadda babu likitocinta sosai anan gida,Umma tace um Allah ya taimaka,amma ka sallame ta da tsara ba ko?Yace to ai batace min zatayi tsaraba ba,Umma tace to ni nace maka, yanzun ku shiga gurin mai martaba ta masa sallama. Mai martaba yaji dadin wannan ziyarar da zataje, sannan yace ki sanarda mahaifanki duk su biyun zasuje aikin hajji bana,ta shiga godiya,Yarima yana tayata mai martaba yace, babu komai wannan kyautar ya kamata ace tuntuni akayita, kasancewar basa kasar sai abin ya kwanta masa da murnarta take sanarda Umma tana godiya tayi tare da ce ma Yarima babana kadai ji kunya kaine ya dace ace kayi wa surukanka wannan kyautar,Yarima ya mike tare da cewa Umma bari nayi wani aiki cikin computer.Ya fita Umma tace kace dai bari ka gudu baka son fadan gaskiya. Bily tayi shiri sosai ga tsaraba Yarima ko kudi ya zube mata sababbi dal ‘yan dari bibbiyu,‘yan naira dari,‘yan dari biyar zuwa dubu daya,kasa magana tayi ta tsaya kallonsa,yace nace ne ki dauki yanda zai isheki tace ni nafi son ka bani da kanka,yace ni kuma nafi son ki dauka don kina sa Umma tana daukana marowaci,baki tambayeni abu ba yaya zanyi in san kina da bukata?Tace to naga karatu kakeyi shiyasa banason matsa maka, yace wannan ba hujja bace,tunda baki taba ganin don ina dan makaranta yau nace wayyo yaya zanyi bani da kudi ba. Don haka dauka in kika dauka duka ma ba matsala,ya juya zai fita tace,to bari na dauka sai ka wuce dashi cikin kowane dauri ta dauki daya,sannan tayi godiya yace a‘a ki gode ma Allah ya dauki jakarsa ya fita. misalin karfe sha daya su Bily sun dauko hanya ga tsaraba mota guda,farin ciki gurin Bily karki tona yau za‘a ga Mamanmu.Ita ko Mamanmu ba zato sai ga Maryam daga kaduna zuwa jimawa kuma ba sai ga Sakina ba,suna cikin gaggaisawa ne sai ga malam da kaji guda shidda yankakku,yace Fatima gashi ku tashi kuyi azama ku gyarama bakin nan me da me za‘a siyo na cefane?Su Sakina suka fito suna gaidasa tare da cewa,ai ko bari muzo mu kama aikin,cikin fara‘a yake cewa duk yanzu kuke tafe?Yaci gaba sannunku da zuwa,Allah ya shi muku albarka,cikin mamaki suka ce amin,yace kun samu labarin zuwan ‘yar uwar taku ne ko? Suka ce ta kiramu ne ta shaida mana yace to to madalla tunda gaku sai kuyi azama ku shirya musu abinci ko?Ya miko dubu biyu gashi sai kuyi cefane,ya zamana dai an shirya musu girkin mai kyau kan lokaci,suka ce to baba.Mamanmu dai ranta kar,yana tafiya sukace oh abin mamaki yanzu baba kara sonmu yakeyi dibi yanda yake ta rawar jiki,Mamanmu tace to ku addu‘a banza ce ‘yayan nan?Kuna fa gani babu dare babu rana ko yaushe cikin du‘a‘i nake.Sakina tace,kuma muma munayi bamu zauna ba,nan suka hau aiki,auta ma ta dawo daga aike itama nan ta hau aikin.Su Ladiyo ko sun ga shigowar malam da kaji don haka suka kafa dandali suka soma tsegumin nasu,karima tace tunda nake gidan nan ban taba ganin malam yazo da ko kaza guda yace a soya ba,sai yau. kodan su Sakina ne ya siyo?Ladiyo tace kince kaza ko kwai ya taba kawowa?Don haka kan kajin nan sai anyi tsiya,inma dansu Sakina ya sawo mu fa da ‘yayanmu suke zuwa me ya taba kawowa suka dafa?Salame tace,bana zaton donsu Sakina ya kawo nafi tunanin wani sabon wulakancin za‘a fara mana don ko ni ashirye nake dan ko daidai za‘a raba kajin nan,nan dai suka kasa suka tsare kowacce tana cika tana batsewa.
[6:32AM, 12/28/2016] ‪+234 814 912 1821‬: 🏵MEKE FARUWA 70🏵

Su ko su Sakina suna ta aikinsu girka wancan dafa wannan soya wannan har suka gama suka share gidan suka gyare dakin auta wato dakin Bily na da suka cire gadon suka shimfida babbar tabarma,suka jera abincin ciki.misalin karfe uku sai gasu Bily sun shigo birnin zazzau,jinta take tamkar anyo mata wahayi cewa an mata gafara.Sai da suka bita masarautar zazzau sannan suka wuto,ita daya ce sai kuyangi biyu Atika da Asabe,dayar motar kuwa dogarawa ne sai tsaraba,tunda suka shigo cikin unguwarsu take ta kalle-kalle,unguwar tana nan yanda ta santa,wasu gidajen sun kara lalacewa, wasu gidajan kuma sun samu gyara,daidai kofar gidansu motoci ne suka tsaya gidansu shima ya kara lalacewa sai dai duk da haka an share kofar gidan tas, yayinda mahaifinta da kannansa da kuma shi kansa mahaifinnata duk suna kofar gida suna ta alwala,nan suka tari su Bily da dogarawa aka bude ma Bily mota ta fito,subhanallahi,ganinta sukayi tamkar ba mutum ba don kyau,ta kara fari fatarta shar,duk da bata kara kiba ba daka ganta kaga hutu,durkusawa tayi tana gaida iyayanta suma kuyanginta haka sukayi, Asabe tana rike da jakarta suka shiga cikin gida, matan gidan suna nan gurin da suke suna sakawa suna kwancewa game da girkin da suka ga anyi an turasa cikin dakin auta,yanzun sun karkata tunaninsu kan cewa kila mazansu ne zasu zo shine akayi wannan girki,Karima na cewa wallahi bari zamuyi sai mazajan sunzo suna cikin cin abincin muje gurin Fatimar mu tada masifa muce sai an bamu hakkinmu, kunga mun kunyata ta gaban surukai.Ladiyo tace don surukai ba sufi surukai ba,namu surukan ko fiya wata ya taba sai musu?Sallamar Bily da kuyanginta ne ta tsaidasu daga hirar da sukeyi,cike da doki ta shigo tana cewa,sannunku Gwaggo,mamaki hade da firgici suka hanasu magana,bata kula ba ita dai burinta tayi arba da Mamanmu,tun kafin ta isa dakin ta soma kiran Mamanmu!Mamanmu!!Su Sakina ne su uku suka fito da gudu suka rungumeta suna oyoyo anty Bilki.Nan take hawayen farin ciki suka soma zubo mata. Mama tana zaune abakin gado cike da fara‘a,Bily taje ta zube jikinta Mamanmu tace menene haka?Nan suka zauna aka shiga gaggaisawa,su Asabe ma suka gaishe su daga nan sai dakin auta,nan suka zube suna cin abinci.Dogarawa kuwa sun wuce sallah ne tare da su malam ,suna dawowa yasa suka shiga dakin Sani,nan kofar gida ya shiga ciki ya amso musu nasu girkin.Nan kuma jikinsu Ladiyo yayi sanyi,sunma rasa me zasu tattauna ne akan wadannan mutanan. Mama ta kira auta tazo tace amso kwanukansu Ladiyo azuba musu mana,su Sakina ne da gaddama tun dazun ina cewa su zuba musu suna cewa baza‘a basu ba,auta ta samesu jugun-jugun tace,Mamanmu tace ku bada kwanuka asa muku abinci.Salame ce kurum tayi karfin halin nuna mata kwandon kwanukan ta dauka taje ta kawo musu ta aje su dai suna nan yadda suke.Bily ko bayan sunci sun sha sunyi sallah, sannan tace Mamanmu bari naje gidan Umman Mansu.tace to ki shiga sauran sasan gidannan ku gaisa,duk da nasan sunji kinzo,amma Gwaggon sasa ce kawai ta shigo wajan nan, sannan duk makotan nan ki shiga ku gaisa,tace kash!Gashi kuma ban tambaya ba,amma zan masa waya ko gobe ne sai na shisshiga tare da su Sakina da kuma kuyanginta suka nufi sasan,Asabe na rike da jakarta yayinda Atika take rike da wayoyinta kafinsu wuce sai data shiga dakunan su Gwaggo ladiyo suka gaisa, dukkansu jiki babu laka yaransu kuwa sai kallonta sukeyi nan tace,Asabe ban jakar nan ta ciri bandir din ‘yan dari bibbiyu ta mika ma auta,gashi ki raba ma yarannan sunsha alawa.Nan ko suka yance ta suna Asma‘u ni baki bani ba,iyayan suna lekowa suka gani nan kowa ta soma raya abinda zatayi da na ‘yayanta in sun kawo.Ta babban sasa suka fara inda gayyar gidan take,suna ko tsakar gida suna ta labarin zuwanna Bily yaran gidan suna ta bada labarin zuwanta suna cewa taci gayu ga wasu hadaddun motoci masu burgewa,kai kunga masu tsaronta sun rike wasu manyan bulalai, sallamarsu ce ta katse Mairo lokacin da take cewa,uwarsu yau sai ji da kai.Bily ta shigo tare da gayyarta,daki-daki tabi kowa suka gaisa yayinda Asma‘u ta shiga rabawa yaran dari bibbiyun.
Mansu ta kira wayarta, Atika ta miko mata wayar tare da cewa,ranki ya dade an kiraki.Ta amsa ta duba sunan Mansu data gani ne duk ta rude tana cewa mutuniyata kin iso ne?Tace mun kusa na jira dady ne ya taso daga islamiya, tace a‘a aminiyata kina son tafiyar dare,sai kin iso tawan,ki wuce gidan Umma don can zan nufa,tace to sai na karaso,amma fa gidana zaki kwana,ban tambayo ba.Cikin dariya Mansu tace yayi kyau,inna iso aida kawai waya akira

1 Comments On ME KE FARUWA
avatar
fatima-8-5

1 year ago

Reply

Uhm

Please Login or Register in order to submit comment