Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zaka sake kiranta.tsaki yayi sannan ya jefar da wayar kan gado,itama duk ta damu sai tana ganin cewa in har biyayyar zatayi me zai hana tayin yanda Yarima ke so, wannan duk laifinta ne yau gata zata kwana ita daya,tana kewar kamshin Yarima ,ranar ko an tafka ruwan sama haka suka kwana jin sanyi duk da bargo da kowannansu ya shiga sannan babu wani bacci sai juye-juye.Oh! Allah shin me yasa suka damu da juna haka?Da safe bayan Bily tayi wanka,nan ta soma daddaga kayan taga wanne ne ya dan fi dama-dama,tasa dan taje bandaki,shi ko Yarima kosawa yayi lokacin zuwa gaida Umma yayi don yaje gaisheta ko zai ga Bilyn,don zuciyarsa ta daina zugi.Bily koda kyar ta samu wani siket gashi dai har kasa dogo sai dai tsagu tun daga kasa har cinya,sannan rigar bata rufe cibiya ba,kuma daga sama duk kirjinta waje,sannan kuma baya ma kusan rabi awaje ta sama,haka dai ta daure ta saka tare da sa takalmi daya daga ciki mara tudu sosai,hijabi ta dora sannan ta fito,amma kafin ta saka hijabin sai data kalli kanta a madubi tace oh,dubeni sai kace ‘yar iska,ko irin ‘yan good evening din nan Tana shigowa falonsa na kasa shi kuma yana sakkowa, zogin da zuciyarsa keyi sai ya tsaya cak,wani sanyi yaji yayinda ya ganta tamkar ya ruga ya rungumeta sai wata zuciyar tace masa yana sai ka nuna mata ka damu?Nan take ya dake sannan yayi nufin fita,da sauri tasha gabansa sannan ta cire hijabin,wani dadi ya rufesa amma sai yasha mur,tace me zaisa ka daure,kalli fa banyi kyau ba ne?Ya kalli kwayar idanunta masu hanasa yayi mata gaddama,yace Beauty kina son ki bani wahala me yasa ko yaushe burinki raina ya baci?In zaki min adalci nima fa dole aka min kamar yanda kema aka miki,amma bana son in matsa miki ke ko kinfi son ki ta bata min.ta dubi fuskarsa na daina duk abinda kake so shi zanyi,yayi ajiyar zuciya sannan yajata zuwa kirjinsa, sai yaji tamkar sun shekara basuga juna bane,harma baisan lokacin da yace I miss you ba,sai dai yaji tace me too Nan suka manne juna,ji suke tamkar su shige cikin juna,ko saboda menene?Oho!Bayaji su kansu sun san dalili.Nan suka nufi falonsa suna manne da juna,sai gashi ranar tare suka karya, har ma Yarima yana tunani aransa cewa dama cin abinci da mace haka yake da birgewa?Duk sanda zaisa abinci a baki sai ya kalli idanun nan nata masu narkar masa da zuciya,tana murmushinta dake kara mishi sanyi cikin zuciya,koda aka jima sai ma ya barcin abincin bai san ya zuba tagumi yana kallonta ba.a zuciyarsa son yake ya gano shinme yasa ita wannan ta fita daban cikin duk matan da yayi harka dasu?Sauran ‘yanmatansa baya damuwa in sun samu matsala ko su zo ko kada su dawo ko ajikinsa, sannan duk lokacin daya gama biyan bukatarsa dasu,sukan fitar masa arai,sai dai ya daure amma wannan tunda ya hadu da ita ta sauya masa wasu abubuwan da dama shi ada baisan damuwa ba,baisan tunani ba, kullum yana samun kansa sayau ne,amma sanadinta duk yasan wannan,ga tunaninta gashi baya son tayi nesa dashi,haka nan duk lokacin daya kusanceta, inya samu nutsuwa wani sabon sha‘awarta ne ke shigarsa, kullum yana son yaji ta manne cikin kirjinsa,yana bala‘in son dumin jikinta.
[6:39AM, 12/28/2016] ‪+234 814 912 1821‬: 🏵MEKE FARUWA 76🏵

Yanzun ma da suke karyawa jinsa yake tamkar wata rahamace ke sakko masa cikin jiki,ta hura masa iska da bakinta a fuska,sai ya lumshe manyan idanunsa sannan ya budesu kar akan fuskarta tace ka koshi ne?Gira ya daga mata alamar eh.ta mika tafin hannunta ta sakalo nashi ta hada yatsunta da nasa ta matse gam,dim yayi yana jin wani abu yana ratsasa,shin me yasa kullum jikinsa ya hadu da nata sai yaji tamkar ranar suka fara taba juna?Ya mikar da ita tsaye ya zagayo da ita inda yake kan cinyarsa ya dorata, sannan yace jikina ya shaku da naki,tace nima haka har na soma tunanin inka tafi course dinka yaya zanyi?Ta tsura ma fuskarsa idanu,yayi murmushi zanso muje tare,me yasa bamu saba ba alokacin zamanmu a Malesia?Tace kaine kaja sai kayi ta kawo mata bayan gani, yace in kawo su ko su kawo kansu?Kema da kina kawo kanki da mun saba,tace nazo ka min wulakanci ai to mubar wannan zancan,anjima zamu je ki gyara gashinki ko?Nima ina son yin aski duk nayi muni,ta dubesa ni ko bana ganin muninka,ya kwanto da ita kan kafadarsa saboda me?Tace saboda kana da kyau,yayi murmushi. Sallamar Magaji ce kusa dasu tasa suka daga kai yace,tun a bakin kofa nake zuga sallama anyi min shiru,Bily ta soma kokarin silalewa daga jikinsa,ya riketa yana cewa,wane kauyanci kenan?Magaji bakonki ne?Magaji yace yi zamanki,in Allah yaso muma mun kusa shiga wannan ajin. Sunne kai tayi ga kunyar kayan jikinta,gata ganinta da yayi jikin Yarima. magana sukayi akan dinner din ya tafi yana cewa to gimbiya nina wuce tunda yau kam ko gaisuwa babu. Yarima ya mike zo muje daki ki dan danna min bayana,tace da mun gaida Umma mun dawo ko?Ki bari koda yaushe ne ma gaisa,ya zura hannunsa cikin rigarta yana matsar na shanunta tace toh muje. Bikin Magaji ya kacame ranar daurin aure aka kawo amarya,su Mansu kirjin biki,dakin Bily ta yada zango har dasu auta Asma‘u ta biyo Mansu. ranar kuwa aka yi dinner Mansu tayi musu dinkin kayan da zasu saka ita da Bily,da suka shirya gaskiya sun hadu,Mansu ta kalli Bily tace,sai kace kece amarya?Kin tsaru fa. Yarima yana falonsa sun gama shirinsu ya soma kiran layin Beauty kamar yanda ya rubuta cikin wayarsa,amma sai yaji wayar tana ringing nan kusa dashi,ya dauko wayar ya duba sai yaga tasa Sweetheart.ya tsura ma sunan idanu,da gaske ne shi sweetheart dinta ne?Sai kuma ya samu kansa da jin dadin hakan,ya dubi Magaji kaga ita wannan ma anan tabar wayar tata,ina son ince suyi sauri donni bana cikin tsarin nan na African time. Magaji yace hakane, sai gata ma ta shigo, shagala Yarima yayi da kallonta,tayi kyau cikin riga da siket din na wani yadi golden mai walkiya dinkin ya fito da surarta tsan-tsan ga kuma net da aka nada shi dan daidai,takalmi mai tsini ne Magaji yace,gaskiya Bily kada fa kufi amaryata kyau,tunda Yarima yake sai yau yaji ya taba jin kishin mace a ransa, domin ji yayi baya son kallon da Magaji yake yiwa Bily,don haka sai yace,me yakai idanunka kan adon matata?Fita ka jirani ina zuwa, Magaji ya fita yana dariya tare da jin dadin yanda ‘yan kwanakin nan abokin nasa ya soma hawa kan layi. Yarima ya dubeta ina ta kiran waya ashe ma nan kika barta,tace eh wallahi mun gama shirin.ya sake kallonta sama da kasa,tayi murmushi nayi?Kai ya daga kawai, sannan yace muje tace bari in dauko jakata in sanar da Mansu taje ta fito da amarya. Mota daya suka shiga da amarya su Yarima kuma da ango,sun riga zuwa sannan amaren suka iso,shi Yarima sai ya samu kansa da zare idanu yaga ta inda Beauty zata bullo domin kwalliyar datayi yana ganin kallonta kawai mazan gurin zasuyi,ita ko tunda suka rako amarya sai suka koma gefe ita da Mansu suna labarin kayan harka tana ce mata sai in mun natsu zan baki ai naga acan keda Yarima naki,tace wallahi wani sa‘in in kin gammu zaki zata tun dama can mu masoya ne,Mansu tace,zama kuso juna ne,Bily tace ina ai nayi rashin wannan kalmar har abada,bazan taba samun mai sona ba wanda zai dubeni yace,Bily ina sonki.wannan tunanin ma tuni na ciresa cikin raina,tunda na riga nayi aure,mijin kuma bawai yana sona bane bare ya dinga gaya min.Mansu tace ke wata rana zai so ki ne.
[8:33AM, 12/28/2016] ‪+234 814 912 1821‬: 🏵MEKE FARUWA 77🏵

Bily tace ban yarda ba,nida shi zaya yi wuya mu so juna,don Hausawa suna cewa in mutum yaki ka da safe sannan da yamma yazo yace yana sonka wallahi karya ne, kuma Yarima bashi da rufi yana gaya min cewa yanda ba so nake ba akayi aurenmu shima haka ne bawai yana sona bane, nidai zaman lafiyan da mukeyi ne yanzun yayi min.suna ta zuba basu sanshi can Yarima ya shiga rudanin rashin ganinta ba,don haka ya ciro wayarsa ya shiga neman layinta zuciyarsa kuma tana raya masa cewa kilama wani namijin ne ya kirata.abinda bai taba yiwa wata mace ba shine ya kirata fiye da daya don inya kirata mace sau daya bata amsa kiran ba ko da bata gani bane to yabar kara kiranta amma yau kira harna biyar,wayar tana cikin jaka batama sani ba sai ana biyar din ne ta an kare da vibration din da takeji,tana ciro wayar call din na yankewa,5 missed calls ta gani,ta dubi Mansu, Yarima na nemana bari naje.Mansu tace nasan tare zaku zauna ni bari mu zauna dasu auta,Bily tace Faruk ya gudu ana gama daurin aure tace shima dole ne kinsan yanayin aikinsu,Bily ta nufi gurin Yarima wanda zuwa lokacin ya cika yayi dam,koda tazo ta zauna bai ko kalleta ba,ta dubesa sai ta samu kanta da shakkarsa,tace gani ya mata banza tace,ina fa tare da Mansu ce,sai ma ya kalli gurin Magaji yana cewa gasu Shettima can da Yakubu Sunusi dama sunzo ne?Yace eh sunzo bamu hadu dasu bane mun daiyi magana ta waya,jin suna hirar abokansu sai taja bakinta tayi gum nan dai guri ya kacame,masu ciye-ciye nayi masu shaye-shaye nayi shiko Yarima sarkin kalkali ana ta faman shan kamshi sai dai zuciyarsa taki nutsuwa,gani yakeyi kusan duk mazan gurin beauty suke kallo,don haka duk sai yaji zaman gurin ya ishe shi. lokacin da amarya da ango suka fita domin yiwa masu waka liki nan Yarima ya tashi yana yiwa amininsa ruwan ‘yan dubu- dubu, Sumayya kuwa sai ta soma zuba ma Yarima Magaji da Bily sun san dalilinta na yiwa Yarima liki amma shi bai san ko me take nufi ba. Ita Bily ta shigo tana ma ango da amarya liki sai Yarima ya juyo yace fita tace liki fa nake amarya da ango yace ibada ne ko kuwa tazo fita kawai wani ya biyota yana mata liki har wurin zaman ta ai kau ta tsorata ta juyo tace kai malam lafiya ni fa matar aure ce yayi murmushi yace nima ai mijin aure ne sai tayi banza dashi Yarima kau ashe ya ga abun da ya faru rai bace idanunsa har da canja kala kawai ya fita daga hall din billy.tayi sauri ta bishi amma ina tana zuwa har yayi reverse ya ja motar da wani matsiyacin gudu ta dawo wurin Mansu tace na shiga uku Mansu Yarima yayi fushi nasan kan na shawo kan sa sai naji jiki Mansu tace ki kwantar da hankalinki mu koma gida haka dai har aka tashi hankalin ta baya kwance suna isa gida Mansu tace taje wurinshi ta lallame shi tace nifa tsoro nake ji ko in bari dai sai ya huce
[8:36AM, 12/28/2016] ‪+234 814 912 1821‬: 🏵MEKE FARUWA 78🏵

Mansu tace ai baki sani ba,in kika ki zuwa sai yafi jin haushinki fiye da in kinje,kije kawai ki kwantar da kai inma yayi fada ne kadaki nuna kin damu,ki bashi hakuri. a haka ta fito jiki a sanyaye.Dakinsa ta nufa yana kwance kan doguwar kujera,kafafunsa suna kan hannun kujerar yana karkada su,fuskarsa tana kallon silin.wani zugi zuciyarsa keyi daya rufe idanu gayen yake gani sanye da farin yadi yana yiwa beauty liki.Ta shigo da sauri ta tsugunna gaban kujerar shine zaka taho ka barni?Ya dubeta ga mamakinta sai taga yau kwayar idanunsa tayi jajir,tsawa ya daka mata fita-fita nace, tace bazan fita ba sai ka gaya min me na maka?Ya mike zaune a fusace,kina nufin baki ma san me kikayi min ba?Tace yi hakuri kwantar da hankalinka, sai ka gaya min,yayi tsaki nace dai ki fita ko? Bana son kina damuna, in kuma zaki koma ne gurin wanda ya tsare kin har kamar ni in kiraki sau biyar a waya ki ki dagawa don kina tare da wani sannan ko kunya bakuji ya fito fili yana miki liki? Da sauri ta dafa kirji tare da cewa, a'uzu billahi! Kasan me kake fada kuwa?Wallahi-wallahi bansan shi ba,hawayen takaici ne ya soma zubowa daga idanunta, kasan daga Allah babu wani,ni da Mansu muka tsaya wannan mutumin bansansa ba,lokacin kawai na gansa yana min liki kuma na fita agurin amma in kana tunanin na sansa ka barni da Allah. Kuka ya kufce mata ta mike tana cewa ko ina hauka zan saurari wani ne, alhalin na sani sarai ina da aure?Nan kuma zuciyarsa ta shiga jin zafin kukan da takeyi,ta mike zata fita,ya kasa daurewa ya janyota jikinsa da sauri, tsam ya rungumeta ba tare da yace kala ba,sai shasshekan kukan ta dake tashi.sun jima ahaka sannan ya dago fuskarta ya saka yatsansa yana share mata hawaye. Idanunta yake kallo cikin idon har sai daya manne bakinsa cikin nata,daga nan sauran abubuwan suka cigaba da wakana, zancan bai kuma tashi ba. Washegari data shigo gefenta Mansu ta soma yi mata tsiya da cewa,daga zuwa ba miji baki shikenan sai muji shiru?Tace um ai sai da nayi kukan bakin ciki wai fa tsayawar da mukayi da kece yake zaton wanda nace miki yazo yana min likin nanne ya tsaidani, Mansu tace kishi kenan!Wallahi ina zaton Yarima yana sonki ne tunda in baka son mutum baka kishinsa,Bily tace ba wani so,haka akeyin so?Shi dai kawai rigimarsace ta motsa,sukasa dariya. Mansu tace,rigima sai kace yaron goye?To ba garama dan goyen ba da abinda Yarima yakeyi,inji Bily.haka akaci bikin Magaji aka cinye, washegari su Mansu suka nufi Gombe,daga can suka nufi KD duk kwanakin Bily karfin hali kawai takeyi kuma bata son Yarima ya gane,don ta tuna wata rana suna kwance take ce masa har tausayi Umma take bani saboda son taga danka, inda zaka yarda kurum ka sake aure ko matar zata haihu,ya tashi zaune ya dubeta bakida lissafi,ni yanzu kina ganin ko cikin kika samu zan barshi ne?Ai bamu isa haihuwa ba tukunna,ni dake har yanzun babu wanda yakai so kibar wannan batun ballatana har in wani kara aure,God for bid. Ta masa shiru yace ke na gane kina son ki haihu ko?Tace,no bawai ina son in haihu bane, kananan yara suna birgeni ne,ya kalleta da wutsiyar idanu sannan ya taba baki gami da cewa in kina so yayyena suna da yara sai ki amso,amma ki ajesu gurin Umma,shiru kawai tayi masa,tuna hakan da sukayi ne bata son ya san cewa tana da ciki burinta dai ya tattara yayi gaba ana gobe zai tafi suna kwance yanata wasa da yatsun hannunta lallan da aka matane yayi matukar birgesa,ya kamo dayan hannun wanda ba‘ayi mata lalle ba yana dubawa sai kurum tagaya mike zaune yana sake kallon gurin kunbunanta, da sauri yace ke tashi ta tashi zaune cire rigarki ingani,tace menene?Tsawa ya daka mata nace ki cire ko,cikin rawar jiki ta cire ya tsurama nonuwanta idanu,ya kama kan yana dubawa yace tun yaushe rabonki da al‘ada? Gabanta yayi mugun faduwa,tace ai ai lokacin ma baiyi ba,yace kada ki raina min hankali yau ba 20 ba date?Yaci gaba kina zaton tunda na soma kwanciya dake sosai bana lissafe da lokacin al‘adarkine
[8:36AM, 12/28/2016] ‪+234 814 912 1821‬: 🏵MEKE FARUWA 79🏵

Tayi zaraf tace,to ai on 27 nake yi,yace on 17 ne ina sane,tace Allah on 27 ne,kadai manta ne,nan take sai kuma ya rude, kwakwalwarsa ta shiga caji ya kasa tunawa,ita kuma ganin haka sai ta shiga kawo masa hujjoji ita wai nan a dole zata tuna masa a karshe cikin dar-dar tace in kuma baka yarda ba ne ka iya yimin test kila kafi yarda dani,jin haka sai yace is ok na manta ne.a hankali tayi ajiyar zuciya shi kuma ya rungumo ta yana cewa har hankalina ya tashi da cikin daren nan zaya shige toilet.Washegari ya shirya komai amma kuma sai me?Zuciyarsa ta shiga cikin damuwa,wai bata son rabuwa da beauty,yaja tsaki yana jin haushin zuciyar tasa,me zaisa ta matsa masa inma don tana son ta nishadu ne ga mata can ‘yan garari masu ji da iya soyayya, lokacin dayaji shigowarta sasan sa sai ya daga idanu yana kallonta,so yake ya gane me tafi sauran mata da zuciyarsa ta damu da ita haka?Ta rusuno daidai fuskarsa ta hura ma idanunsa iska tace,kallon fa?Kamshinta ya shaka ya lumshe idanu,sai bakinsa ya furta cewa,ina tunanin yanda zan rabu dake ne.ta ware idanu cikin mamaki tace, kana dai tsokanata ne kawai kaida zaka tafi zaka manta dani,cikin sigar shagwaba tayi maganar, yanda ta lura muryarta bai san sanda ya mannata jikinsa ba.yaya zan manta da hutuna ina nufin gurin hutawa,bayan kinsan ni dan hutu ne?Ta daga idanunta tana kallon nasa cikin idon,tace da kaje nasan abokan hutun su zaka fara samu kai din sai ya samu kansa da gudun damuwarta don haka sai taji yana cewa,a‘a na daina ki sani cikin addu‘a bazan sake ba.dadi taji ta kara rungumesa to yaya zakayi ne gashi baka da hakuri ko dai zakaje dani ne?Ya sanyaya murya bansan yanayin gurin ba amma ki bari innaje naga gurin yana da tsarin da matar aure zata iya zama sai nazo na tafi dake ko kuma zai yiwu in zauna ba yaya zakayi?Yace ki bani shawara tace ka riga yin azumi ga lada sannan zai dauke hankalinka daga shagala,tsam ya sake matseta yana cewa na gode beauty. Haka ya hada kayansa ya tafi Magaji ya kai shi airport tare da billy sai sumayya da ta biyo mijin ta ko a airport sai da ya kara rungume billy sumayya dai ta kauda kanta suka yi bankwana ya shige jirgi sai.da suka ga dagawar su sannan suka juya billy cike da kewar mijinta
[8:38AM, 12/28/2016] ‪+234 814 912 1821‬: 🏵MEKE FARUWA 80 🏵

Hakika Yarima yana son mata shi likitansu ne,sannan yanzun cikin course din nan ya gano zasu iya maida tsohuwa yarinya,domin ana iya canza fata suna dasa nono daga zubabbe ya koma tsayayye har yake tunanin na billy inda ba tsayayyu bane da sai yayi mata aiki ya gyara su toh amma yayi sa'a nata masu kyau ne sosai tsaye suke kyam irin wanda ko tsufa baya sawa suyi sharab dinnan sai dai su dan russuna .yana zaune cikin dakin daya zama mallakinsa,wani abu yake son sani cikin laptop game da course dinsa, yarinyar bata fi sati daya itama da zuwa ba,ita ‘yar mutanen Maroco ce,tana da kyau sosai itama tazo yin course ne irin na Yarima tun ranar daya soma ganinta ya shiga rudu,sannan jinkai da sarauta suka motsa.yana dago kai ya ganta tsaye cikin dakin,ya tambayeta shin tana bukatar taimako ne?Bada bata lokaci ba tace,tana son yin magana dashi ne,yace mata babu matsala,amma fa sai dai ba yanzun ba domin yana da abin yi,tace to ta iya jiransa?Yace,inbata da abinyi ta iya yin hakan mana.tace shikenan,ya nuna mata gurin zama yaci gaba da aikinsa.tana kallon Yarima komai nasa yayi mata,tana sonsa tun sanda idanunta suka soma ganinsa yana da kyau sosai,tsawon awa daya da mintina sannan ya gama komai,ya dubi agogo sannan ya dubeta tare da cewa,lokacin sallarsa ya kusa shigowa,amma zata iya yin maganar cikin minti sha biyar?Tace bazai kai ba ma,ita kawai tana son su zama abokai ne kawai,yace me yasa tayi tunanin su zama abokai?Tace haka nan kawai ne taji ya kwanta mata cikin rai,sannan ta lura yana son yayi abinda ya kawosa ne, tana son mutum mai kwazo da ilmi.yayi godiya tare da mika mata hannu,sunnan shi ya sanarda ita wato Prince Al‘amin,cike da jindadi tace,ita kuma sunanta Tina Abraham. Tun daga ranar suka zama aminai duk da cewa basu taba aikata wata masha‘a ba,suna dai sha‘awar juna amma duk sun danne.sai wata ranar lahadi yana waya da Bily ta shigo,zama tayi tana kallonsa tare da sauraron yaren Hausar da yake magana da ita,sai daya gama sannan tace masa tana son ta iya wannan yaren,yace to gaskiya bai alkawarin koya mata ba,amma inya samu lokaci zai dan kwatanta,ta matso kusa dashi tana shafa gefen wuyanta tare da lasar lebunanta tace masa ita in tana kusa dashi sai ta samu kanta cikin wani yanayi,shin zai yarda su dandani juna? Baice kala ba kuma bai mata tsawa ba sai data zo kusa dashi ta rungumesa, wasu abubuwan data soma masa sune suka sa shi kasa daurewa,harma ya fito mata da kwarewarsa awannan harka.Tina ta raina kanta da kwarewarta agurin yarima, ta kuma kara samun kwarewa tare da sonsa mai tsanani, tun daga ranar ta tare a dakinsa suka cigaba da lalacewa,Allah ya kyauta musu.Bily tana zaune cikin kujera bayan ta gama kwara amanta,sanyi ne takeji tana zato na zazzabi ne.Jakadiya ta shigo tace da jakadiya taje ta kawo mata bargo. jakadiya taje gurin Umma tana cewa,ranki ya dade gimbiya Bily fa duk kwanakin nan batajin dadi,ba ko za‘a kira likitar nan ta dubata ba ko mun samu karuwa ne?Ai jin haka da sauri Umma tace,bani wayar can, jakadiya ta miko,Doctor Aisha ta kira tace mata tazo yanzun,kamar minti hamsin ta iso.bayan gwaje-gwaje da ‘yan tambayoyi ta gano cikin wata biyu da ‘yan satittika, nan take ta sanar da Umma, murna gurinsu ba‘a magana,nan dai aka daura mata karin ruwa. mai martaba harda goron albishir ya hadama doctor Aisha dashi.ita dai Bily damuwarta daya,in Yarima ya samu labari yaya za‘a kwashe?A dare ko ya kirata sai tayi tunanin ta sanardashi kuma ta nuna masa ita bata so don in wani ya sanardashi to zasu kwashe ta babu dadi,yanzun ko ta siyasa zata bi.yace beauty yaya ne?Tace,um kai dai bari,muna cikin matsala fa,ya gyara zama tame kenan?Tace banga al‘ada ba gashi har na soma rashin lafia,Umma ta turomin doctor Aisha ta dubani bansan me tace ba naga dai gidan ya cika da murna,nidai gaskiya banason in haihu ka fada min me zanyi? Yarima ya kasa magana ma don takaici can yace gaskiya matsalar ma babbace, ko dai inzo ne acire shi? Gabanta ya fadi,amma sai ta daure tace kada kazo in akwai wata kwaya mai karfi ka min text dinta in aika asiyo min insha,yace yauwa kin kawo shawara, to amma wazaki aika?Tace Atika don batayi karatu ba kuma in gargadeta nasan zataje, yace shikenan zan turo inbai fita ba ki gaya min,tace to amma fa insu Umma sun kiraka sun maka murna kadaka nuna baka so don inmun cire kadasu gane ko su zarge mu. yace, haka ne beauty kada ki damu kin ji? Tace to sai na gani.
Hankalin Yarima ba karamin tashi yayi ba,shin wace kwaya zai ba wa beauty? Nan take ya shiga cikin asibiti gefen magunguna ya bincuko, nan take yazo ya turo mata su in ta samu kuma ga ka'i'dojin su, sannan ya kira ta yace ta gani? Tace, ta gani ta share ta ci gaba da sabgarta, shi ko kullum nacin tambaya ya ya fita? Tace Aa yace to zata iya ganinshi a kowane lokaci. Zai zo ya cire mata shi tace to gara haka din ma, ya ce ai su Umma sun kira ni har da mai martaba na dai nuna musu murnata tace to sai na ganka, ai suna gama waya ta kira magajin Malam a waya tace tana Neman shi yanzun nan, cike da far gaba ya zo don bata taba kiran shi ba.
Bilkisu ta sanar dashi Komai tace in yazo kasan dole ne ya cire cikin nan, ni yanzun ban san ya ya zan yi ba, kuma bana son in fada ma Umma, magajin Malam yace to lallai Yarima, amma kada ki damu ki barni dashi ni nasan yanda zan mishi in hana shi zuwa, nan take ya kira shi. Yarima ya soma mishi tsiya ango kasha kamshi, sai yau aka ga damar kiranmu? Magaji yace kai me ya hana ka kira ni? Yarima yace Aa bana son in takura maka ka samu gurin Hutu gashi kuma abun ya hada maka biyu, wato ga sabon shiga ga ka tuzuru yace ba komai, dama na kira ne in ce maka ina murna da samun baby, yaci gaba sai dai wani abu da bai min dadi ba, shi ne na shiga gaida bilkisu na same ta a galabaice, sai da aka dauko Doctor Aisha nan ta gano tasha wata kwaya ne don zubar da cikin, a tsorace Yarima yace yanzun ya ya ake ciki, su Umma sun

1 Comments On ME KE FARUWA
avatar
fatima-8-5

1 year ago

Reply

Uhm

Please Login or Register in order to submit comment