Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da sassafe suka nufi Kaduna ta koma bakin aikinta.

Yarima yana kwance a dakin shi can malesia, ya rasa dalilin da yasa zuciyar shi ta cika da son ya tuno inda ya san yarinyar wadda zuciyar tashi ta mata lakabi da beauty, amma ya kasa, ya sani bashi da saurin mantuwa da sun taba haduwa kyanta ba mai saurin gushewa a rai ba ne da zai tuna, wata zuciyar tace meyasa ka damu kanka da tunanin inda kasan wannan yar kauyen? Tsaki yaja sannan ya mike yana ayyanawa a zuciyar shi, cewa cikin lokutan da ya tsara bai cire na tunanin kowa ba,saboda bai ga macen da ta isa ya tsaya tunaninta ba, can haka ya tashi ya nufi kicin don kora wani abin mai dan sanyi.

Dattijon ya maida hankali ne kan rokon Ubangiji ya karkato hankalin jikanshi ga aure, duk addu'o'in da ya yi mishi cikin ruwa da wadanda zai dinga karanta wa duk saboda hakan ne.

kwana uku tsakani zuciyar Yarima ta tsumu da sha'awar yarinyar da zuciyar shi tasa mata suna beauty, in suna kwance da chelen sai ya dinga rayo beauty, in su Vicky ma yanzu ana dai harka ne kawai, a tsarin shi baya son ya nemi yar arewa don baya son raini, su din basu waye ba, bayan haka ma baya son ya samu zubar da darajar gidansu, to meyasa ya samu kanshi da jin sha'awar yarinyar, ya tuno cikar kirjinta da yanda mazaunanta suke juyawa, lokacin da zata fita daga cikin masaukinsu na gidan kakanshi, tunanin yanda yarinyar take yaji irinta ta yaya, zai kai ga samun haka? Duk da ya kula sai saka yake yana warwarewa, kafin daga karshe ya yanke shawarar neman farooq, bayan sun gaisa ne farooq yace, lallai yau za'ayi ruwa da kankara Yarima yayi murmushi yace dan dai da ba ka da number ta ne shi yasa bana gaisuwa.

yace, haka ne kam dama ina son in tambaye wannan yarinyar ne wani Abu shin kana da number din ta? Farooq yace wace kenan? Yarima yace, wadda Ku ka zo tare din nan,. Ya ce OK kana nufin Bilkisu ba? Yarima yace, kila ita din ce, kawar dai matarka. Farooq yace kana sonta ne?

Ko kusa, zan dai tambaye ta ne wani Abu.farooq dai ya tura mishi number. Yarima ya soma tunanin yanda za ta dauki abin da zai gaya mata, amma sai yace bari ma dai ya fara sanin ina ta san shi? Kuma yaya suke? Ma'ana shi da ita
[8:47AM, 12/28/2016] ‪+234 814 912 1821‬: 🏵MEKE FARUWA 27🏵

Ta dan watsa ruwa don taji iska kamar yanda ta saba yi kullum in zata kwanta, ta shafa humra mai hade da wani turare mai dan karan kanshi, ta saka rigar baccinta haye gado. Mansu ta shigo tana cewa. Bily ga dan gidan ki wai yau ma nan zai kwana.

Ta jawo shi ta kwantar a bayan ta tace. Ai dama dadyna dan rigima nasan nan zaka kwana ko?
Yace, eh momy. Haka yake kiran su su duka. Momy Bilkisun ma yace momy mansu tace bari in je in kwanta kamshinki yana rinjayata. Bily tace kija mana kofa sai da safe.

Cikin bacci taji wayarta, cike da mamaki ta dauko ta daga saman kanta ba ko shakka kuskuren numba ne tunda ita ban da mansu da mijinta sai kannanta su Sakina sai ko abokan aikinta bata da mai kiranta amma duk da haka sai ta dauka cikin yana yin bacci tayi sallama daga can gefen ya amsa a kasaice, sannan yace.

A ina ne ki ka san Yarima?

Nan ta wartsake, haushin shi ne ya cikata tace rai a bace.

Wanene kuma Yarima? Ni ban san wani Yarima ba, kai Malam. Yayi shiru maganar ta matukar ba shi takaici,amma ya dake.

Kada ki damu please sanar dani.
Tace kai ni fa ban san shi ba.
Dole ne kin san shima don in da ba ki san shi ba ai baza ki nuna mishi sani ba,amma tunda kin ce haka menene dangantarki da Modibbo family?

Wadannan tambayoyin fa sun ishe ni haka, ta ce da shi.
Dole ne kuma ki amsa su. Shima yace a fusace.
Tsaki tayi sannan ta kashe wayar, ta kwanta zuciyar ta tam takaici.

A nashi gefen kam yafi ta bakin ciki sosai, bai taba zaton wata mace zata yi mishi wulakanci haka ba, wai macen ma yar Nigeria kuma yar arewa bakauyiya. Ya girgiza kai.
Alkawari ne sai na rama ko ta halin yaya ne. Ya yi niyyar share ta amma sai ya fasa. Kuma kiranta yayi
ta dauka, wai lafiya?
Amsa min tambaya ta, yace da ita sai ka zo ka shake ni na amsa maka din.
In kin fi son haka za ki samu.

Tace toh bismilla, ina jiran ka. Ta kuma kashewa.
Ya mike tsaye, ba a taba cin mutuncinshi haka ba,mace ce ma tayi mishi haka kai shi ko namiji ma bai taba mishi wannan cin kashin ba, bare Mace wadda bai dauke ta komai ba sai abin nishadi ya na bata daraja ta wannan fanni amma baya daukar raini, kwana yayi yana da na sanin kiranta kuma yanzun in ya barta haka taci nasara akan shi kai sai ya yagata.

Washe gari da safe yana kwance cikin bahon wanka tunani ne ya ci kanshi Sam ya kasa yin komai saboda takaici yana son ya samu mafita amma ya rasa sai dai zuciyar shi tafi tafiya kan Abu daya, ya yi soyayyan karya da ita ma'ana ya daure yace yana sonta sai ta shiga tarkon shi sannan ya yagata, ya gama wanka ya fito bai tsaya gurin shafe shafe ba, kai tsaye ya wuce bedroom din shi waya ya dauka sannan ya zauna kan wata kujera dake gaban dogon madubin nashi, ya soma kiran layinta dai dai suna karyawa ita da dady tana sauri ta fita ta dauki wayar tana dubawa shi din ne,dama ta zargi haka,ta dauka a dake yace.

Ki sanar dani in da ki ka sanni.
In an kifa?
Tace a fusace.
Zaki yarda ma,ba kamar ma in kin shirya yin aure? Dan nasan shi ne kawai zai yi maganin rashin kunyar ki.

A tsaye zancan yazo mata a ranta tace wannan kanshi daya kuwa? Amma a fili sai ta ce

Ba ka isa ka aure ni ba ka min kankanta ka min yaro, nasan kuruciyarka nasan yarintarka don haka ka min kadan kai kanin bayana ne don haka.....
Ya katse ta.
Ke!!! Kina hauka ne? Ni ki ke gaya ma haka ? Ki sani ban taba samun macen da taci min mutun ci irin haka ba,zan nuna miki ni yaro ne sai na aure ki kuma sai na ganar dake kurenki I promise za ki San wanene YARIMA
[8:47AM, 12/28/2016] ‪+234 814 912 1821‬: 🏵MEKE FARUWA 28🏵

Duk yanda Bily taso kada tasa
abin aranta sai da hakan ya faskara,domin kwana
tayi tana tunanin dalilin Yarima na cewa lallai sai
yasan inda ta sansa,bayan tun farko shine ya
dauko hanyar da bazai yiwu ya sani ba,domin
daya saurareta lokacin data nuna tasansa hakika
daya ji cewa cikin mafarki ne.Sai yanzun yana
nuna shi fa dole ne ma ta sanar dashi saboda
wannan dalilin shine har yake ikirarin aurenta
saboda ya wulakanta ta.Da safe bayan sunyi
wanka da Dady tana shafa masa mai,Mansu ta
shigo Dady yace Good morning Momy,tace How
are you my boy,Bily ta saka dariya tare da cewa
Iye! Yaron yayi hankali.Mansu tace waya koya
maka gaisuwa ne?Ya nuna Bily tare da fadin
Momy din nan ce tace inna gaida Momy da
Abbana zan shiga gidan aljanna,wai haka tace ni
Musulmi ne?Dariya suka kama sakawa,Bily ta
soma saka masa uniform Mamansa tana cewa
yaron nan Bily ya baci da surutu.Bily tace,barshi
yayi zaifi daukan karatu,Mansu tace to ina kwana
ko gaisawa bamuyi ba,Bily ta amsa lafiya
lau,yaya twins?Mansu tace,daina min fatansu,ni
yanzun ma dayan na kosa yayo waje,ciki tuntuni
ya fita watan haihuwarsa?Bily cikin tausayawa
tace,gurin Allah ne lokacin da saura.Daya cika
zaki haihu mu samu yaro ko Dady?Dady yace eh
mana,Abba ma haka yace,Momy zata je asibiti ta
siyo mana yarinya,suka fito a tare suna
dariya.Faruk ya fito sanye cikin suit
bakake,Mansu tace har ka fito baban Dady?Yace
naso in makara ma,yakamata yanzu ina office,Bily
ta dubeshi antashi lafiya yayana?Yace lafiya lau
sister,hakan take ce masa tun kafin ayi bikinsu da
Mansu,ya tafi Mansu tana biye dashi,Bily ta bisu
da kallo.Gaskiya lamarin Mansu yana son
gyara,ace kullum mijinka baya karyawa yake fita?
Duk da an san yanzun da ciki,to tun kafin cikin
ma haka take yi,amma bari ta haihu lafiya zasu
zauna dole ta sake tsari.
PRINCE Modibbo kwance cikin kwamin wanka,zuciyarsa tam da takaici tare da tunanin yanda zai bullo ma matsalarshi,yana sha‘awar yarinyar,yana jin haushinta cikin ranshi yana raya zai iya komai dan ya muzguna mata ciki harda aurenta,wata zuciyar tace masa,kai da baka son aure yanzu amma ka yarda ka aureta?Yaba kansa amsa da cewa,zan aureta ne don in nuna mata cewa ni da ita ba tsararraki bane,kamar yanda ta zata,kuma ta sanar dani labarin kuruciyata kamar yanda take tutiya,sai nayi Teaching din ta lesson,I promise.Hannu ya kai kan wayarsa dake gefen bahon wanka ya dauka,layin Bily ya soma nema duk da bai tanadi abinda zai gaya mata ba,shi dai burinsa ya bata mata rai da safennan don yasan yanzu su safiya ne a Nigeria.Suna karyawa daidai wannan lokacin wayar Bily ta shiga ruri,haka kurum taji gabanta yayi wani mugun faduwa,ta jawo wayar ta tsura ma number din ido(+)din data gani shine ya tabbatar mata cewa Yarima ne,domin bata da wanda zai kirata daga kasar waje sai shi,tsaki taja sannan ta ajiye wayar,ki dauka mana Bily,inji Mansu ko baki san number din bane?Kamar ta share sai kuma ta dauka domin in taki dauka Mansu zata so jin dalili,kuma bata shirya bata labarin rigimarsu yanzu ba,domin Mansu tana bukatar hutu da akwantar mata da hankali,tare da guje yin wata magana da zata saka ranta ya baci. Tana daga wayar ta saka akunne ba tare da tace kala ba,fuskantar da yayi an daga wayar shine ya saka sa ya soma magana. Ina son sanin abinda kike takama dashi da har kike gaya min magana son ranki? Me kike takama dashi nace? Wanene ya tsaya miki? Ke ‘yar wanene? In sarauta ce ke ‘yar wane sarki ne? Ko mulki kike takama dashi wane Gwamna ne ya haife ki? Ko ke ‘yar shugaban kasa ce? Ko ‘yar wani mashahurin malami ce? Dan kasuwa sananne ya haife ki? Bani amsa dawa kike takama?
Duk maganganun da yakeyi tana jinsa afuskarta ko wani murmushi ne irin na bakin cikin nan takeyi bata son Mansu tasan halin da take ciki don haka sai ta mike ta nufi dakinta,Mansu ta bita da kallo aranta ko addu‘a takeyi Allah yasa aminiyarta ta samu mai so ne.Bily ta zauna bakin gado daidai sanda yake cewa,ki sani ban taba samun mutumin daya bata min rai ba irinki,ko namiji dan uwana sai ke mace,macen ma bakauyiya.Ki sani sai na saki cikin damuwa fiye da yanda kika sakani,in har ki.....“kai! Ta katse sa da tsawa,saurara min.Taci gaba da magana da kakkausar murya,kai ba kowa bane,kuma kai ba komai bane,duk abinda kake takama dashi shirme ne,kuma ni na wuce da tunaninka,wanda ya tsaya min ya wuce da tunanin,wanda ya tsaya maka bama kai ba.Don sanin ko ni ‘yar wanene sai ka saka cigiya,aure ne dai nace baka min ba,yaushe ma kashinka yayi kwari?Yaushe aka daina yi maka tsarki....?“Hee!“Ya katseta you are very stupid,kin san me kike fada?Bari ma na gaya miki,kada kiyi zaton nima sonki ne yasa nace zan aureki,a‘a zan aureki ne on my own baki san ta hanyar aure ne kurum zan gasaki yanda naso ba tare da mutane sun zargi wani abu ba,domin ni nan ina gudun abinda zai bata sunan Masarautarmu,zaki gane kin maida ma prince magana.Ya kashe wayarsa tare da dauraye jikinsa ya fita daga bahon.Bily ta tsura ma wayarta ido tamkar Yarima yana jiki ne,bakin cikin maganganun daya gaya mata takeyi,amma sai ta danne tare da kudurin inta fita zata sayi layin (zain)don ta samu ta huta,ta mayar da (mtn)din.Lokacin data fito,Mansu ta nemi jin wanda ya kira Bilyn,sai ta shara mata karya da cewa,abokiyar aikinta ce take shaida mata cewa ta fito karfe goma domin yau wani gidan buga jarida za a tura su.
[8:47AM, 12/28/2016] ‪+234 814 912 1821‬: 🏵 MEKEl FARUWA 29🏵
Shi ko Yarima bai kara kulewa ba sai da ya gama shirinsa tsaf,don shiga school sai yaga karfe biyu har ma da rabi.Shi da zai shiga Lecture karfe daya,ya shiga wanka sha biyu da rabi ya tsara duk shirinsa zai gama komai zuwa daya don ya bata lokacin wankan sa ne afalo zaune yana tunanin mafita,har lokaci ya wuce.Ya shiga wanka da nufin yayi sauri ya fito,nan ma yarinyar ta masa sanadin rasa Lecture ya koma ya zauna.Ya rike kai bai taba tunanin akwai wata rana da zata zo ya shiga damuwar da zai shagala har haka ba a fili yana cewa dole ne ya dauki matakin gaggawa kan yarinyar nan koya samu nutsuwa karatunsa yana bukatar nutsuwa tare da kwantar da hankali.Cikin dare Mansu ta soma nakuda,Faruk ya buga ma Bily kofa duk sukayi asibiti har dady tunda gidan babu kowa,tasha wuya sannan Faruk ya saka hannu don ai mata aiki.Anyi nasarar ciro mata ‘yarta katuwa mai matukar kama da Faruk,satinsu daya suka dawo,‘yan Zaria da ‘yan Gombe kam gasu nan,sai da sati ya zagayo sannan akayi suna inda jaririya taci sunan Umman Bauchi,Mamansu Yarima kenan.Wannan kara ta jama ‘yar farin jini gurin daukacin family din mai martaba,don duk yayyan Yarima sai da suka zo suna tare da sha tara ta arziki,ga kuma na Umman Bauchin sannan gana mai martaba,dankareriyar sarka da ‘yankunne na gwal kirar Dubai.Kowa ina ka saka ina ka aje yake da yarinyar mai suna Sa‘adatu.Lallai tayi sa‘a,bayan an watse duk sun koma sai kannan Faruk,‘yammatan su uku Sumayya,Fauziyya da Safina.Bily tana kula dasu tare da duk hirar da sukeyi,kusan duka su ukun basu da labari sai na Yarima.Kamar yanzun data shigo ta samesu,Sumayya ce kwance tana zuba masu Fauziyya labarin Yarima tana fadi,kunsan Allah Safina?Nasha alwashin wannan hutun indai yazo ko na kwana daya ne sai naje zan kuma masa magana ince ina sonsa ko in fada ma Ummansa.Safina tace da kin more,ni kaina sonsa nake,Fauziyya kuwa cewa tayi,ai ke Sumayya banza ce,da nice na samu dama irin taki mahaifiyata da tasa ciki daya,ai koda burauba ma sai na auresa.
Bily tace “Assha! Ke ko Fauziyya menene na zunduma ashar haka?Babu kyau,don Allah ki daina“.Duk suka hada baki gurin cewa,don baki ga gayen bane anty Bily,yana da kyau ga aji,dan kwalisa ne na karshe.Bily ta zauna bakin gado tana cewa,ni dai inda zan baku shawara ku dauka,dana ce karku yarda kuce da namiji kuna sonsa, don su maza ba a musu haka,Sumayya tace anty don baki gansa bane,kuma ina bala‘in sonsa,duk hakurina ya kare,zan tunkaresa ne kawai.Safina ma tace Allah yasa ki iya,ya cika kwarjini ne da yawa.Bily ta kalleta aranta ko tausaya mata takeyi don Yarima da take magana bamai mutunci bane,ta sake cewa addini bai hana mace tace tana son namiji ba,amma Sumayya alkunya tana da kyau ko?Tamkar zatayi kuka tace,anty Bily nayi alkunyar bai ma san inayi ba,don haka ni zan gaya masa.Bily ta mike tana cewa,bari naje naga sahibata,na tsaya ina biye ma shirmenku.Safina tace,ba shirme bane anty,kema in kin gansa sai kin soshi,Bily tace Allah ya tsare ni.Fauziyya tace,kila kuma ita bazata soshi ba,tunda itama tana da kyau.Sumayya tace,mai kyaune kuma da mai kyau,anty Bily kuna kama da yaya Modibbo.Bily ta fita tana dariyan shirmensu.Ya sake kallon agogo,karfe takwas,yasan yanzu a Nigeria zai zama biyun dare kenan,tunda awa shidda ne tsakaninsu da Malesia.Bari dai ya bari sai yamma sannan,nan su rana tayi,wata zuciyar tace masa kafin yamma haka zakayi ta zama?Ka tuna fa yanda yarinyar nan taci maka mutunci,me zai hana kasan wanda take ikrarin ya tsaya mata din?Tuna hakan daya yi ya sakasa daukar waya ba shiri ya soma neman layin Magaji zuciyarsa tana kara tuno masa maganganu na batancin da yarinyar ta masa wanda yayi sanadin tsayawar al‘amuransa ciki harda karatunsa tare da holewarsa da mata ababen sonsa,bai taba zato akwai wata damuwa da zata shigar masa cikin huldarsa da mata tayi dumu-dumu ba hatta Chelen duk yanda taso taja shi bata iyawa saboda bacin rai.
[8:47AM, 12/28/2016] ‪+234 814 912 1821‬: 🏵MEKE FARUWA 30🏵

Wayar ta katse ba‘a dauka ba yaja tsaki sannan ya sake neman layin,ringing na uku Magaji ya daga wayar.Yarima yace,haba Magaji adinga rage bacci ana nafila mana,wannan bacci kamar ka mutu?Magaji yace,gara ma ni bacci nake,shima ibada ne wani ma ba‘asan ko shi da mata nawa yake ba,Yarima yace,na gode.Yanzu dai duk ba wannan ba,me kasani game da wannan yarinyar?Magaji yace,wacce kenan?Yarima yace,yarinyar da muka hadu gidansu Modibbo kawar matar Faruk din Umman Gombe?Magaji yayi ‘yar dariya tare da cewa,nasan dama wata rana sai ka min zancan yarinyar,domin irin taku ce.Ya dan saurara kafin ya cigaba,gaskiya bansan komai kanta ba,ni da farko ma na zata kun hada iri can cikin dangi.Tsaki Yarima yaja,sannan yace kada ka bani haushi fa Magaji?Tunda kace baka san komai kanta ba,na baka awa sittin da shida daga yanzun,ina son sanin who is she?Ya kashe wayar ba tare da ya jira jin me Magaji zai ce masa ba.Tun misalin goma na safe Magaji ya soma neman sanin Bily,da farko gidan Modibbo ya nufa gurin Hajiya Fati don son sanin wacece Bily?Don nan ya soma ganinta gurin Modibbo ya soma shiga suka gaisa,baice ma Modibbo komai ba game da bukatar Yarima na son sanin Bilyn ba.Sun dan taba hira har ma Modibbo yake cewa,ina labarin abokinka ne?Magaji yace,yana lafiya sannan yace,bari ya shiga su gaisa da kawu.Modibbo yace,kawunku yana Yola,na aikesa sai dai mai dakin tana nan ciki,yace to bari mu gaisa dama nazo gaisheku ne.Sun gaisa da Hajiya,sannan yace dama Hajia ina so in tambayeki ne shin ko kin san Bily kawar matar Faruk din Gombe?Haj.Fati tace,ikon Allah nifa nayi mamakin ganinka da safe tunda kuka zo Yarima na nan ba wani zuwa kuke ba sai sa‘a.Tayi ‘yar dariya sannna tace,wallahi ni ban santa ba,daga ita har matar Faruk din.Nima karo na farko kenan da fara ganinsu.Nan dai sukayi sallama ya fito,cikin mota ya soma tunanin wazai tunkara da wannan bukata?Yana ganin abinda sauki ashe duk ya wuce nan.Yayi tunanin to ko Faruk zai kira?Sai kuma yace,kai da Yarima yana son Faruk ya sani da shine mutum na farko da zai fara nema.
Nan Sumayya ta fado masa yarinyar da yake mutuwar so,yace bari ya kirata yau dai yaji muryarta tunda ya shiga ya fita da kyar ya samu number din ta gurin yaya Salma ya kasa kiranta,amma yanzu zai kira kila ma ya samu labarin daya fito nema.Dafda zata yanke Sumayya ta daga wayar duk da cewa wayar tana hannunta,haka nan bata gane ko number din wanene ba.Cike da yanga tace,hello! Ya lumshe ido don jin muryar da yake matukar so,sannan yace,Assalamu alaikum,Sumayya tace ,Wa‘alaikassalam,wanene please?Yace au baki gane ni ba?Tace,a‘a.Yace,to Magaji ne daga Bauchi,tayi ‘yar dariya.Oh,Magaji ban gane kaba,koda yake bamu taba waya ba,yaya Bauchi? Yace,Bauchi lafiya duk suna gaisheki tace,ina amsawa,yaya Yaya Modibbo?Yace lafiya,dama wani taimako nake so ko zan samu?Tace in baifi karfi na ba,ai bazai gagara ba,yace kin san kawar matar Faruk dinku?Tace anty Bily kenan,nasanta jiyannan muka dawo daga gurinsu.Yace,yauwa don Allah menene labarinta?Kamar ya?Ta bukata,yace,ina nufin kinsan tarihinta?Ta girgiza kai tamkar tana gabansa bansan komai kanta ba,face nasan ita ‘yar Zaria ce kuma ta gama karatu bansan me ta karanta ba,amma yanzu tana bautar kasa ne,yace to na gode,kina da number dinta ne?Tace,eh,amma sabuwar number dinta ne nace ta bani don ina sonta,kai ne zaka shiga?Yace ni wane ni,wani abokina ne.Da sauri tace,Yarima?Yace,a‘a.Tayi ajiyar zuciya har abin ya bashi mamaki,yace shikenan kiyi min text din number dinta,tace to.Da taso ta rokesa ya shigar da ita gurin Yarima,sai dai ta fasa,shiko zuciyarsa ta shiga rudu,kada dai Sumayya tana son yarima ne. Zuwa washegari,Magaji duk ya gama bige-bigensa shi dai bai gano komai ba game da Bilkisu,dole sai ya hada da zuwa Zariya.

Kwance agaban gidansa,cikin wani dan gado Yarima ne,daga gefensa Chelen ce tana sanye da Bra da pant,wasa takeyi da gashin kirjnshi,idanunsa lumshe zuciyarsa tana masa nacin me yasa yaba Magaji kwana uku?Ya matsu yasan ita wannan yarinyar ‘yar uban wanene


Ita ko Bily daidai wannan lokacin hankalinta kwance,tunda ta cire(mtn)ta saka(zain)sai dai bata yarda ba kamar yanda tasoyi da,saboda numbers din dake kan(sim)din,tana son ta ba Mansu labari sai sun zauna tukunna.Magaji ya shigo Zaria kai tsaye unguwar T/wada ya nufa gurin wani abokinsa da sukayi karatu a (University)nan Bauchi.Ibrahim dan Zaria ne,a unguwar T/wada.Da kwatance ya iso T/ wadan,nan kuma ya shiga kiran number din Ibrahim amma is switch off.Tun safe yake neman wayar taki shiga,nan ya shiga nemansa ta hanyar tambaya duk ba sa‘a,yayi parking nan kusa da wani Masallaci da nufin yayi magriba,zaije ya nemi masauki.Amma cikin yardar Allah yana sahun gaba sai kawai yaga Ibrahim a sahun gabansa.Don haka suna idar da sallah sai yasa hannu ya dafa shi,nan suka fita wajen Masallacin,Ibrahim yana ta mamaki.A dakin matar Ibrahim suna cin abinci,Magaji yana fada masa dalilin zuwansa Zaria,yace na shigo garinku ne don neman labarin wata yarinya Bilkisu.Ibrahim yace,ikon Allah!‘yar wace unguwa ce?Magaji ya kafa kofin ruwa yana sha,sai daya gama sannan yace,nan fa daya,wallahi bansan komai kan yarinyar ba,hasalima sau daya na taba ganinta.Ibrahim yace,to kai batayi maka kwatance bane?Magaji yace,nifa Bauchi muka ganta.Yarima ne ke sonta shine duk ya daga min hankali,yanzu haka gobe yake son jin ko ita wacece.Ibrahim yace,gaskiya ya baka aiki,Zaria tana da yawa,ta ina zaka soma nemanta?Magaji yace,shi yasa na biyo ta kanka tunda kaine dan gari.Babban misalin dazan iya badawa na yarinyar kawai shine,kyawunta nasan saboda tsabar kyanta bazata bata a unguwar da take ba.Ibrahim yace,to kafin a gano unguwar da take fa?Magaji yace to bari dai in mukayi Isha‘i sai mu soma tun yau.Haka kuwa,suna idar da salla suka shiga gari.Da G.R.A suka soma don zaton Magaji na ko ‘yar wani mai halince,gida-gida suka dinga bi cikin G.R.A sune har sha daya da rabi.Washegari ko suka soma da T/Wada,S/ Gari,haka sukayi ta yawon neman inda zasuji labarin Bily,amma shiru.Bayan sunyi sallar La‘asar,suka shiga Ojo da har zasu wuce amma MGJ yace su shiga.
[8:47AM, 12/28/2016] ‪+234 814 912 1821‬: 🏵MEKE FARUWA 31🏵

La'asar, suka shiga ojo da har za su wuce amma magajin yace su shiga anguwar.
Kai tsaye kusa da wasu samari suka yi dayan ko sai rantsuwa yake yi. Ibrahim yayi musu sallama suka amsa. In ban da dayan da yake ta zuba bai ma san ana sallama ba. Ibrahim yace, bayin Allah muna tambaya ne ko Allah yasa kun sani? Biyu suka hada baki gurin cewa,to magaji ya matso don Allah cikin ku ko akwai Wanda yasan wata Bilkisu? Yaci gaba. Yarinyar tana da kyau na ban mamaki. Samarin suka ringa kallon magaji kamar sunga wani sauna. Dariya ma ya basu, inda dayan yace Malam, Bilkisu suna da yawa a unguwar nan, kuma akasarin su kyawawa ne.Magaji ya yi shiru, can yace ita fa kyanta dabanne, kuma ta gama makaranta. Gaba dayan su suka sa mishi dariya har ma ya ji haushi zai tafi, sai daya daga cikin masu musun kwallon nan mai surutun tsiyan yace, Aa ko dai yana nufin Bilkisun gidan marina? Nan take samarin suka ce ita ce ma, don duk unguwar nan ita ce best a kyau. Magajin Malam da jin haka sai ya dawo yana cewa, don Allah yaro zo mu muje ka gwada min gidansu.Yace,to Magaji ya saka hannu cikin aljihu ya debo kudi ‘yan naira ishirin ya mika musu ba tare da ya kirga ba,yace na gode fa,suma suna ta godiya.Ibrahim yace,bari na zauna baya shi ya shiga gaba saboda zai dinga yi maka kwatancen inda zaka bi.Magaji yaji dadin haka,don yana son ya yiwa yaron tambayoyi musamman ma da yaga yaron zaiyi surutu.Ya dubi yaron,sannan yaci gaba da tuki,yace abokina kusa kuke dasu kenan? Yaron yace,E,gida biyu ne tsakaninmu dasu.Amma gurinta zaka?Magaji yace,eh,yaron mai suna Sule,yace ai ina ganin fa bata nan tana Kaduna,aikin gidan TV takeyi,ko bauta ma kasa naji ‘yan gidanmu suna cewa, suna zuwa yace da Sule ya shiga ya tambaya ko tana nan.Bayan fitar yaron ne Ibrahim yace da Magaji abokina zaka iya samun labarinta gurin yaron nan,don naga yana da surutu.Magaji yace nima na lura.Sule ya dawo da sakon cewa tana KD.Magaji yace,amma ka tabbata nan ne gidansu?Sule yace,nan ne,ko ba wata doguwa ba?Fara mai kyau?Magaji yace,itace,nan ne gidansu nan yaro ya labarta ma magaji

1 Comments On ME KE FARUWA
avatar
fatima-8-5

1 year ago

Reply

Uhm

Please Login or Register in order to submit comment