Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

aka kama cikin katon filin asibitin akayi taron inda manyan likitoci,kwamishinonin lafia,zuwa ministocin lafia,ga kuma ‘yan uwa da abokan arziki. Su Tina an duro domin tana ganin sakon sai taji tamkar yayewar matsalarta ce,don haka bata yi kasa a gwiwa ba,ta amsa gayyatar, domin tana azabar son Yarima.taro yayi taro,bayan yin duk abinda yakamata aka bude asibiti inda mai martaba ya wakilta sarkin musulmi ya bude asibitin mai suna(Dr. Yarima Hospital)an dunguma cikin asibitin don ganin cikinsa,hatta bakin kasashen wajen sun jinjina dukiyar dake cikin asibitin,wato kayan aiki zuwa kayan kawata asibitin kafin sati daya tuni asibitin ya kama aiki gadan-gadan.gashi dama ya tanadi likitoci da kuma nurses kwararru.Tina ma ta yarda da gayyatar da Yrm yayi mata,amma sai taje ta dawo. Al‘amura sunci gaba da tafia yanda yakamata,beauty kam yanzun ta gama yarda Yarima nata ne,yanzun ne ta gane cewa halayan Yrm masu kyau ne in ta cire neman matansa wanda ayanzun take tunanin ya daina yana da kyauta ga sadaka yana da kulawa gami da ibada.girman kan da ada take ganin yana dashi yanzu ta gane shi mutum ne mai matukar saukin kai da kuma tsokana duk da bai cika dariya ba,zaya tsokaneka yayi fuska tamkar bashi yayi maganar ba,tuni ya soma ginin gidansa babu nisa sosai da asibitinsa, son ma tuni ya soma takawa shiko Yarima kudi sun kara zaunawa dama dogo ne ga kuma ‘yar kiba irin ta hutu, azumi yana gabatowa tuni Bily ta cire son daga nono,yana gurin Umma tana son zuwa zaria kafin azumi,amma Yarima yace a‘a. Auta Asma‘u tunda ta gama karatu tana gidan gurin Bily duk dangin Bily daga Asma‘u sai su Sakina, Yarima ya sani sai dai yana musu aike ko yanzu da take hankoron zuwa zaria kafin azumi,tana son ne takai musu kayan azumi,bata san tuni Yarima ya tura musu dashi ba,sai gashi babansu yayo waya yana cewa tayi musu godiya gurin Yarima ,azumi yana ishirin suka nufi saudi, wayewar garin sallah suka dawo.rayuwar Bily abin sha‘awa,yanzun ta manta da komai da duk matsalolinta na baya kuma ta yarda da batun Mansu cewa suna son juna koda Yarima baya sonta ita dai tayi imanin tana matukar sonsa, shiyasa kishinsa yanzun yayi yawa azuciyarta, harma bata iya boyewa, duk da bata da masaniya game da Tina sai dai tana zargin kamar yana neman wata,in tayi magana ya kalallame ta da baki kan cewa shifa nata ne ita daya Ranar wata litinin tana kwance a falonta, asma‘u ta miko mata waya cewa ana kira,tana dubawa sunan Umma ta gani tana dagawa ta shaida mata ta fito suje gidan Modibbo zasu dubashi yanzun nan akayi mata waya kan cewa jikinsa yayi tsanani,ta mike da sauri ta nemo mayafi ta soma kiran layin Yarima ,yanayin muryarsa yasa ta wani zargi tace lafia naji muryarka wata iri?Yace na gaji ne kawai tace to zamuje duba jikin Modibbo inji Umma,sai taji yace umh humh sai kuma taji an kashe wayar.yanayin sautin muryar yafi kama da wanda yake tare da mace, don kada Umma suyi ta jiranta sai ta nufi gurinsu Umman,suna mota ta kuma kiran wayar a kashe, sauran layikan kuma suna ta ringing ba‘a daga ba. zuciyarta tamkar ta fashe don bakin ciki,amma dole tayi hakuri ta shanye.suna isa gidan suka shiga gurin nasa Umma ta tallaboshi lokacin ya dubeta duk sukayi masa sannu yana tayi musu godiya,sauran kishiyoyin Umma sun dawo sun barsu acan ita da Bily,ya dan samu bacci suka shiga cikin gidan, kamar minti goma Kawu ya shigo hankali tashe yana ce musu Modibbo dama ashe baccin nan tafiar kenan?Hawaye ne suka soma zirya akan kumatun Bily,ta sani in zata tuna da tarihin rayuwarta to zata tuna da Modibbo,Allah ya jikansa ba zata gushe ba gurin yi masa addu‘a duk sallah.ta soma neman layin Yarima taci sa‘a an kunna a zuciyarta tace an gama kenan,wani irin takaici ne yasa taji sabon hawaye ya zubo mata ya daga wayar da cewa,hello beauty.wani tukuki taji, itace banza ya raina mata hankali cikin shasshekar kuka tace inka gama ne sai kazo nan gidan Modibbo Allah yayi masa cikawa,ta kashe wayar ta shiga neman ‘yan zaria. Yarima yaji rasuwar sosai,dole yayi wanka kafin ya nufi gidan,don haka sai da yaje gida saboda a cikin gidan Tina dake nan asibitin ya tara da ita kuma bazai iya yin wanka a gidan ba. bayan dawowa daga makabarta su Yarima suka shigo cikin gidan,Bily kam ko son ganin Yarima batayi,tana zaune da carbi kanta na kasa,Yarima ya zauna kusa da Umma yana mata gaisuwa,ya dubi Bily,beauty yaya muka ji da hakuri?Banda Umma dake gurin da sauran mutane da bazata amsa ba Amma duk da haka bata dubesa tace mun gode Allah,Umma tace Bily ta kasa daina kuka shi Modibbo yanzun ai sai addu‘a, a ranta kuwa cewa tayi yaya ma zata iya daina kuka alhalin mai tayata addu‘a akan Yarima yanzun babu,sai yanzun ne data kamu da son Yarima shine zai koma bin matansa,ita kam ta gaji da hakuri bazata iya ba.har ranar da akayi uku Yrm ya kasa gane kan Bily,sam ta fita harkarsa galarin gabanta kawai takeyi ko tana dariya ne data gansa sai kawai ta daure fuska. washegari bazasu je gidan rasuwar ba domin an riga ya anyi sadakar uku,har ya fita sai kuma gashi ya dawo kusan misalin karfe sha daya tana kwance cikin dakinta ya shigo,Asma‘u ya fara gani a falo yace mata ina antynki?Tace tana ciki.ya shiga tayi rigingine fuskarta tana kallon sama tunani takeyi koda iyayanta suka zo gaisuwa Yarima bai ma zo sun gaisa ba har suka tafi,duk da yayi ta kiran waya yana cewa gashi nan zuwa wai yana duba wanine sai bayan sun tafi sannan yazo.ya zauna gefen gadon beauty tashi muyi magana,ta tashi zaune ba tare data kallesa ba,tace ina jinka yace a haka zamuyi maganar kina kallon wani guri ta juyo ta kallesa sai dai ranta a daure yace wai ni shin menene ya faru ne kika saka ni cikin damuwa?Me yasa kika saba min da kanki da hirarki da dumin jikinki kinsan ba zaki dore ba?Shin ko rasuwar nan ce duk tasa kika koma haka?In ma rasuwar ce niya kamata infi jinta, domin duk yanda zaki damu ni zaki yiwa kara.ta dubesa rai bace, in kana zaton kara nayi ma donna damu da rasuwar Modibbo kayi kuskure, domin duk wanda yayi kukan mutuwa kansa ya yiwa,kuma da zaka ce na saba dayi maka kaza da kaza ina ce yanzun ka samu madadina ce?Ya dubeta ban gane ba?Tace ai bazaka gane ba,bari kaji nifa yanda na juri huldarka da mata da yanzun bazan iya ba,Allah sai in kama gabana. A haka kowa ya ganni zai zata ina jin dadi ana min kallon sha‘awa da hutu amma zuciyata ba hutu?Ya daga mata hannu saurara min,me kike nufi da zuciyarki ba hutu,me na miki? In kana so dole sai na sanarda kai zan iya domin kayi ne dama don inji kana kwance da mace na kira,ai sai kaki daga wayar amma don ka cuzguna min sai ka daga, kana ce min wai ka gaji,saboda ka raina min hankali,ya mike don yin abin nan da hausawa suke cewa tabarmar kunya da hauka ake nade ta.ke ki shiga taitayinki,kin tabbata ina tare da wata ne?Kin yarda Allah ya tsaida ke ranar shaida?Tayi shiru ya cigaba da cewa,shikenan tunda da ina neman mata yanzun bani da damar nayi wani dan kuskure sai ace ina tare da mace,to duk yanda zakiyi kiyi,tace haka kace?Shikenan ya dubeta ko da sanda nake yima baki daga min hanakali irin haka ba sai yanzun? Tace gara da lokacin baka gabana kuma kaima baka damu dani ba,ballantana kasan kona damu ko ban damu ba,sannan ko banza lokacin baka boye gaskiyarka, amma yanzun fa?Shikenan kawai tunda kace duk yanda zanyi inyi ni kuma zan nema ma kaina mafita,ta mike ta shige toilet.ya rike kansa tare da yin ajiyar zuciya sannan ya fita.wasa-wasa rigima taki karewa ranar ya ritsata da cewa wallahi shi bazai iya ba,yaya yana matsayin mijinta zata barshi yana walagigi shi in ta ci gaba da wannan halin zai hadata da Umma, tace zanfi son haka domin sai tasan me kakeyi,kila in tayi maka fada kaji nata,ta cigaba da shafa manta,yace to yanzun naji na amshi laifina shikenan me kike so inyi miki ki huce?Ta dubesa alkawari zaka dauka tsakaninka da Allah cewar bazaka sake bin mata ba,yace naji zanyi amma kinsan mutum yace zai dauki alkawari tsakaninsa da Ubangiji ba karamin abu bane,nasan muhimmancin alkawari nidai ina bukatar addu‘arki kuma zanyi kokarin kiyayewa, kenan ka yarda kanayi?Yace a‘a bawai na yarda bane,don dai ranki yayi fari ki daina fushi shiyasa nace miki na yarda,don Allah kinji? Ta tsura masa idanu,yazo ya rungumeta,don Allah beauty in na sake ki mini duk hukuncin da kikeso, tace shikenan ya wuce, duk da haka tana masa komai amma ta kasa sakewa dashi kamar da, yanda take wasa ajikinsa suyi ta wasa ta bashi abinci abaki amma yanzun batayi.
[8:43AM, 12/28/2016] ‪+234 814 912 1821‬: 🏵MEKE FARUWA 89🏵

Ya kuma samunta da complain shifa bawai tamai abinci yaci ya kwanta da ita ne farin cikinsa ba,yanzun farin cikinsa bai wuce ta saki jikinta ta koma normal ba,data zauna tayi tunani da tayi banzan nan dashi in yayi gaba can zai tare inda kadangarun bariki suke sai yaga dama bacci zai kawosa amma shi yana ta faman binta sai ta kara rikosa tare da jansa jikinta saboda ta samu ta rabashi da kowace,cikin kwanakin suka koma daidai da sharadin cewa inya kara duk hukuncin data ga dama ta masa shi yaja. yaita kokarin ganin bai kuma barin wata baraka da zatasa beauty ta gane yana tare da wata ba.Hankalinta kwance yanzu,damuwarta bata wuce son samun ciki ba,wanda in tayi magana sai yace ta daina damun kanta,kwata-kwata shekarun son nawa da za‘ace sai anyi masa kani?Sannu a hankali ta soma zargin cream din da yake shafawa in zasu kwanta, domin ta kula inya kare komai matsuwar da yayi da ita yakan hakura,don haka sai ta dauko salon cewa ita dai tana jin zafi maimakon ce matan da yayi cream din zai sa su jin dadi,ta tubure tace ita sam bata so ga zatonta zai bari sai taga yayi matukar daukan zafi da ita harma ya fita harkarta, gami da kaurace mata, ita ma ta yarda da hakan suka share juna na kimanin sati uku,su duka sunji jiki domin shima duk da yana da Tina ya gane bawai biyan bukata ne kawai amfanin beauty ba tana da wani matsayi wanda mata da yawa basu takashi ba a cikin zuciyarsa.ita kuma babu abinda yafi kona mata rai yanda ya daina cin abinci agida wani sa‘in ma sai tayi kwana biyu bata sashi a idanunta ba,kuma zuciyarta ta dinga raya mata cewa yana can tare da matan banza.Ganin bazata iya cigaba da wannan zaman ba yasa ta samesa, sai ce mata yayi indai bazata yarda suci gaba da amfani da wannan cream din ba sai dai su zauna a haka Ga Allah ta koma ta cigaba da gaya masa kafin wani tsawon lokaci sai gashi ya soma sakkowa,tana zaune yazo ya sameta yace tayi masa tuwon semo,bata tsaya jan aji ba ta shirya masa tuwo miyar danyan kubewa,sannan tayi kwalliya irin wacce bata taba yi ba,lokacin da yazo cin tuwon sai ta bayyana donta zuba masa tun yana satar kallonta harma daga karshe ya zage da kallon nata ita kuma tayi amfani da wannan damar ta saki jikinta tamkar wani abu bai taba faruwa ba.ganin haka shima yabar cin abincin suka koma wani fanni,sai da suka tausaya ma junansu,aranar lallai sun fahimci sunyi missing din juna daga nan suka ci gaba da harkokinsu. amma kuma sai me?Data samu ciki wata daya biyu sai ya zube kuma ya dubata acewarsa ba wata matsala anyi haka har kashi hudu,inda abin ya soma damun Umma,su anty Saliha kuwa cewa sukayi ita ke cirewa shi kuma tsabar son mace ya hanasa ya gane hakan, tsana suka kuma saka mata tare da zuga Umma akan Yarima ya kara aure, umma cewa tayi babu ruwansu amma anty Salma sai data kirasa tace, lallai ne ya sake aure,sannan sukayi kungiya suka samu Bily suka ce inma tana cire ciki ne don tayi sisi to su karuwa suke so kuma Umma tace dole ne ma ya sake aure.hankalin Bily yayi matukar tashi,jin cewa harda Umma cikin lamarin.da sauri ta kira Mansu ta shaida mata halin da take ciki,Mansu tace mijinki ya canza miki?Tace,a‘a shi yana boye min maganar nema bai san sunzo har gida sun gaya min ba,tace to ko da wasa kada ki canza masa kinji ko?Tace to sannan kadaki yarda ki sanar dashi duk abinda ‘yan uwansa suke miki tace shikenan Mansu tace shawara daya itace ki dage da addu‘o‘i,nafilfilu kiyita gayama Allah,tace to cikin kwanakin shi kansa Yarima ya fahimci tana da damuwa,haka nan inya farka sai ya ganta tana nafilfili,wannan karon data samu ciki bata bari ya sani ba,don tana tunanin da sa hannunsa yawan barin ta tunda bai taba nuna damuwarsa kan cikin ba don ya fita,sai dai ya damu da lafiarta,ita kanta tana son ta sake haihuwa ballantana ga bala‘in danginsa duk da nuku-nukun data ke har cikin yakai wata uku. Nan fa ya farga ya tambayeta kan cewa ciki ne da ita ko?Tace me ka gani?Yace, alamu da dama,tace shine don Allah ka tayani addu‘a wannan karon Allah ya bar min,yace to yanda yake amsa zancan tasan bai kai zuci ba,sai dai zatayi taka tsantsa da duk wani magani da zai bata.har aka kwana biyu bai bata komai ba kuma bai canza mata ba,yana ma taji da ita ne,ashe yana amfani da wani mai ne in yayo wanka sai ya shafashi cikin toilet din a gabansa da zaran ya kwanta da ita sai cikin ya fita wannan karon ma haka yayi bayan ya fita,zuwa asibiti misalin sha biyu sai taje fitsari nan taga jini,da sauri ta fito taje ta shirya ta nufi gurin Dr. Aisha,bayan gama bincikenta ta gano cewa Yrm yana amfani da wani sinadari ne dan fitar mata da ciki,sannan tace wannan cikin ma fita zaiyi.Bily bakin ciki ya isheta,Dr. Aisha tayi mata allura tace taje gida.har zata gida sai kuma taga ba zata iya daurewa ba sai taje asibitin ta tabbatar masa ta gano komai kuma zata shaida ma Umma komai,tana zuwa baya office nan nurse din dake kula da marasa lafian dake shiga gurinsa ma‘ana mai kai masa katuna tace yanzun nan ya fita gama marasa lafia suna jiransa zai dubasu da yake sun san ita matarsa ce,tace ina to yaje nurse tace,kila suna wani aiki ne a cikin gidan Tina,har zata shiga office din ta zauna sai kuma tace am nurse ina ne gidan?Tace gashi can bari in nuna miki suka fita ta kaita har bakin gate din gidan kai tsaye ta shiga ta ratsa dan tsakar gidan mai kyau da furanni ta isa kofar da take zaton ta falo ce,ta tura sai taci sa‘a abude ne ta tura ta shiga ta shiga falon mai kyau ta waiga ko‘ina babu alamun mutum sai dai taga kofofi guda uku.ta juyo da nufin ta fito sai taji maganar TV cikin wani daki ta nufi gurin har zata kwankwasa sai dai ta fasa ta kama murfin kofar ta murda sai taga kofar ta bude,duk da gargadin da zuciyarta ta rika mata kan cewa ta fa yi gangancin shigo ma mutane gida,hakan bai hanata leka dakin ba,TV ta hango sai ta cusa kai,take numfashinta ya soma zarya da kyar ta iya furta Inna lillahi wa‘inna ilaihi raji‘un da karfi. Wanda hakan yayi sanadiyar jawo hankalin Yarima da wanda kamu ta masa irin wanda ake cewa turmi da tabarya, da kyar ta lalubi hanya ta fita,tana mai data sanin wannan zuwan da tayi. data jirasa ya koma gida ta zauna acikin mota ji tayi jinin yatsunko mata gaba daya da sauri ta ciro wayarta ta kira direbansu tace dan Allah ya hau mashin ya sameta asibitin Yarima tazo ne bazata iya dawowa ba,babu jimawa sai gashi ya jata zuwa gida,dakyar takaicin gidan yasa ta isa dakinta ganin halin da take ciki ne direban ya shiga gurinsu Umma ya shaida musu.lokacin da jakadiya ta iso ciwon baya da mara sun tirnike ta,nan take jakadiya taje tana ya mutsa baki tana cewa Umma wannan mata ta Yarima bata da dabi‘a to gata can ta kuma yo allurar zubar da cikin tana ta murkususu jini yana zuba,Umma ma haushi ne ya kama ta, amma duk da haka sai tace jeki kula da ita jakadiya,ba laifinta bane laifin mijin ta ne da tun farko ya nuna mata bacin ransa daga na daya ai bazata kuma ba,bari in kirasa yazo ya dubata su dai suka sani,ni menene nawa Allah na tuba jika wane iri ne ban gani ba.lokacin da Umma tayi masa waya ya zaci ko tazo ta fada ne a tsorace ya daga wayar,tace masa sai kazo ga matarka nan kila barin zata kuma yi ta kashe wayarta,lokacin daya iso tama sume bata san wanda ke kanta ba a firgice ya dauke ta zuwa mota Asabe ce kurum ta bisu suna isa asibitin a gigice ya sureta zuwa Emergency su uku ne kanta shi ya kasa yi mata komai ma,cikin ya fita sukayi mata wankin mara sannan suka kaita daki na musamman ta farka ne ta ganta a dakin asibiti. kwananta biyu duk babu wanda yazo dubata kaf dangin Yarima ance sai Umma lokacin tana bacci su Salma cewa sukayi bazasu zo duba taba tunda tana sani.Yrm ne ko yaushe yana dakin sai dai ya kasa ce mata komai kamar yanda ko ganinsa bata son yi shi dai bashi da tacewa ne, sannan ga carin da ‘yan gidansu suka rutsa sa suna masa yayyinsa ne suka tsara shi a gaban Umma sunce matarsa tana zuwa tana cire ciki yakasa yin komai akai saboda ta mallakesa, don haka zasu nema masa aure, Nan take anty Saliha tace ‘yar mijinta Nafisa ta jima tana son Yarim kuma Nafisa tana da hankali sosai,shidai jinsu kawai yakeyi shi damuwarsa daya mummunan kamun da matar tasa tayi masa, yanzun bai san yaya zasu kwashe ba in ta warke, gashi shi ne silan wannan wahalar da tasha duk da yana zaton bata san shi ne sila ba inda ma yake jin da dan sauki kenan.da yamma su Magaji suka zo dubata tace haba Magaji maimakon kabar Sumayya ga tsohon cikin nan?Yace to nace ta zauna tace ita dai zata zo Bily tace shikenan na gode, duk surutun da akeyi cikin gida Magaji yaji sai dai bai yarda wani Bily ce ke cire cikin ba sai dai ko Yrm so yake ta fito daga asibitin yaji komai kuma yasha alwashin sai su Umma sunji. washegari ta fito daga asibiti,Yarima yazo yace an sallameta tazo ya kaita gida,bata musa ba dama kala bata ce masa ba ta shiga mota suka nufo gida. nan shima ya dan zauna shiru sannan ya fita jim kadan su anty Salma suka zo sukayi mata ta tas,har da cewa dama dan talaka bai iya samun guri ba,anty Fulera tace zaki ga tsiya aike baki ma iya abun ba inma cin dukiyar kike so dakin haifa kin tara dakin samu,yanzun kuma zamu kawo wadda zamu karu da ita ‘yar masu dashi, suna fita ta tashi zaune ta ma rasa meke mata dadi duniya,nan ta dauko jakarta ta dibi ‘yan kayanda basu fi biyar ba sai dai kudi ta dauka ta zari makullin mota ta fita.sai data hau titi tama rasa ina zata?Kai tsaye ta dauki hanyar Kaduna, gidansu Mansu taje ita kanta tasha mamakin tukin da tayi domin bata taba fita cikin Bauchi da mota ba,Mansu bata Kaduna suna zaria kuma daga nan zasu wuce Gombe saboda hutun karshen shekara da Faruk ya samu,maigadin ne yace mata basa nan tace ta sani itama wani aiki zata yi a Kaduna ta shiga ta aje kayanta cikin dakin Mansu,sannan ta zauna ta rubuta ma Yrm text kamar haka.
[8:43AM, 12/28/2016] ‪+234 814 912 1821‬: 🏵MEKE FARUWA 90🏵

Na baka guri ka shakata sannan kasani bazan iya zama dakai ba, ka kasa tsaya wa akan halalin ka alhalin ban rage ka duk wani jin dadi ba. Baka sona baka son karuwa dani, burinka in mutu gurin cire min ciki ta hanyar da kai ka sani ni bansani ba, amma naje gurin likita ta min bayanin komai dama ance duk mutumin da baya kaunarka zai iya yi maka komai ciki harda neman rayuwarka. Da fatan daka samu sakona zaka rubuto min sakina koda ta waya ne sai ‘yan uwanka su aura maka wadda suke so ‘yar masu kudi kuma wadda zata tara musu ‘yaya kamar yarda suka ce,tana turawa ta kashe wayar gaba daya.shiko Yarima yana ganin sako ya shigo ya duba ai a rikice ya nufi gida, ta tabbata nan kuma babu motarta yaje yace ma Umma ina Bily? Umma tace ni ban sani ba bata nan ne?Yace a'a na zaci tazo ne ya fita,gidan Umma ya nufa yana tafe yana neman layinta amma a kashe,bayan sun gaisa sai yace shin ko Bily ta iso?Umma tace ta nufo nan ne?Yace dana ce tazo ne ina zuwa kila tana gida ya fita duk inda yasan Bily tasansu sai da yaje har magariba ta shigo ya dawo gida ta gurinsu Umma ya shigo tana sallah son ma yana ta binta sallar.ya fita ya nufi sasansu,ya daure ya watsa ruwa sannan yayi sallah ya ci gaba da neman layinta shiru sannan ya kira Magaji bai boye ma Magaji komai ba,Magaji yace shikenan gaskiyarta ne tunda ta tafi ba sai ka huta ba? Haushi ya kama sa yace haba Magaji na kiraka ne fa don ka taimaka min yanda zan bulloma al‘amarin ka kuma dauko wata caftar, Magaji yace to in ba haka ba me zance?Yarima yayi shiru can yace da zan iya dana ce tayi tafiyarta amma na kasa ba zan iya ba, cewa fa tayi wai in sake ta? Magaji yace ka saketan mana to yaja tsaki,sannan ya nuna ma Magaji kofar fita,fita baka da amfani,Magaji ya mike ya fita Yarima yabi shi da kallo. Bacci ranar sai dai barawo amma kasa bacci Yarima yayi,baya son su Umma susani amma dole ne suji,sai dai zai ce musu taje gaida iyayenta ne,to kuma zasu ce babu ko sallama?Haka yayi tayi ya saka ya kwance,har gari ya waye.Magaji daya koma gida sai ya kira layinta yaji sa akashe, washegari ya fito ya shiga gidan sasan Yarima ya shiga lokacin Yarima shima ya gama tunanin cewa dole ya koma gurin Magaji,domin shine yasan zaria, kai shi abin kunyar nasa ma yana da yawa shekara nawa shida matarsa bai san kowa nata ba sai wanda ya kawo kansa yanzu gashi zai je dalilin yana bukatar ta dawo?Magaji ne ya katse sa da cewa abokina yaya ne? Yarima ya dubesa mun tashi lafia?Lafia lau inji Magaji sukayi shiru can Yrm yace ko can gidan iyayanta zamuje? Magaji yace to sai muje,kaga kaima tunda yanzun tayi dalili sun san kai Yarima yace to sarkin sheri naji yanzun yaushe zamu tafi?Magaji yace ko yaushe,Yarima ya mike yace jeka shirya mu tafi.sun iso zaria misalin karfe biyun rana,unguwar suka shiga kai tsaye, kallon unguwar yakeyi yana mamakin dama beauty a irin wannan unguwar take?Duk da an ce iyayanta talakawa ne da za‘abarsa inya iso(G.R.A)zai nufa nemanta,bai kara tsinkewa ba sai da suka tsaya akofar gidan,yace Magaji don Allah nan ne gidan iyayan beauty?Magaji yace tabbas Yarima yace,amma baka kyauta min ba da ka kasa sanar dani kamar ni ace surukaina suna cikin wannan gidan, ai samuna yazama na banza.Magaji yace lokacin gyaran ne baiyi ba shiyasa Allah bai horeni da sanar dakai ba amma yanzu ai kaga lokacin yayi tunda ance gani ya kori ji.suna fitowa daga mota Asma‘u tana fitowa daga gida,tace a‘a yaya Yrm sannunku da zuwa,Yrm cikin zumudi yace Asma‘u beauty tana ciki ko?Asma‘u tace wace antynmu?Yace eh,tace bata zo ba.Magaji yace babanku yana nan?Tace yana ciki,yace to shaida masa ga baki. Da sauri ta koma tace Mama ga yaya Yrm mijin anty,ta mike da sauri tace,to ina malam kirasa dakin Salame ta sanar dashi da sauri ya fito sai daya canza ‘yar riga mai haske

1 Comments On ME KE FARUWA
avatar
fatima-8-5

1 year ago

Reply

Uhm

Please Login or Register in order to submit comment