Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲



🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗


𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻


𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 1️⃣


*بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم*

_Da sũnan ALLAH, Mai rahama, Mai jin ƙai._



........Ƙarfe uku da mintuna ashirin da biyar jirgin daya taso daga birnin tarayyar Nigeria Abuja ya sauka a *_AMINU KANO INTERNATIONAL AIRPORT_* da ke a Kanon dabo. Cikin nutsuwa duk wani passenger dake a cikinsa suka fara fitowa. Vvip section ƙyaƙƴƙyawar budurwa dake cikin ado mai tsananin ɗaukar idanun duk wanda ya kalleta ta miƙe a hankali tana ɗan wani ɓata fuska tamkar mai jin warin mutane. Sanye take cikin wasu shegun wando da riga da sukai tsananin fidda cikakkiyar surarta musanman ma wandon jeans ɗin da ya kasance fari tas, an ɗan faffasashi daga cinyarta da gwiwa har ana iya ganin kalar fatarta. Siririn veil kalar pink mai haske da yay dai-dai da kalar rigar jikinta shima data ɗan yana a saman kanta ya matuƙar ƙawata adon nata da fidda zagayayyar fuskarta, sai bag fara tas da adon stones pick and blue daga gani kasan mai tsada ce. Ga wani shegen takalmin mai tsananin tsini sai dai ya matuƙar ɗauki ƙafar tata musamman da wandon ya kasance baije ƙasa can sosai ba kuma yabi jikinta ya lafe luf sai ya bama siririyar sarƙar ƙafarta da taji adon stones pink and blue damar fitowa ɗar. Yanda ta rufe idanunta da eyeglasses blue ya ƙara saka fuskarta kwarjini da bayyana ƙyawunta mai sanyi, sam fuskarta babu alamar wata fara'a, sannan babu kwalliya ko ɗigo idan ka cire ɗan lipstick kalar pink mai shining data zizara ma laɓɓanta. A kallo ɗaya zaka ɗauka bata san minene ko murmushi ba, sannan zaka iya kiranta da ƙabilar kudancin ƙasar, dan babu ta inda tai kammani da Hausawa ko yankin arewacin ƙasar musamman inda addinin Muslunci keda ƙarfi irin su kano.
A hankali taja ƙaramin tsaki dai-dai tana miƙewa da tura wayarta cikin aljihun wandonta, headphones ɗin kunnenta kalar pink ta gyarama zama, tare da gilashin idonta sannan ta ciro ledar chewing gum ta ɓare ta jefa a baki tana ballama saurayin dake ta bayanta kaɗan harara, tun ɗazun ya dameta da kallo dan jaraba har zuge labulen da ya rabasu yayi. Bag ɗinta ta fisga ta ɗora a kafaɗa ɗaya sannan ta ɗauka Apple laptop ɗin ta tana sake jan siririn tsaki ganin shima ya miƙe tai ficewarta cikin takunta na ƴammata marasa jin magana..

Yanda take taku tsinin takalmin nata na bada wani irin sautin jan magana, ga sautin madaidaicin akwatinta da take gungurawa tamkar a gajiye ya jawo hankalin mutane da yawa gareta. Caaaa idanu da yawa a kanta, wanda basu iya gani suyi shiru tuni sun fara tankawa, wasu ƴammatan kuwa kishine ya lulluɓesu, yayinda samari da yawa sukai mutuwar tsaye da ganin wannan ƙyaƙyƙyawar halitta. Ita dai daka ganta kaga cikakkiyar baƙar fata haihuwar Africa sai dai ɗabi'u da shiga duka ba namu bane. Ga wani shegen ƙamshi da duk wanda ke a kusa da ita kaɗan dolene ya jisa saboda yanda ta bulbulashi kamar ba mace ba. A yanda take juya madaidaita lips ɗinta a taunar chewing gum ɗin bakinta kawai dole ya tada hankalin mai kallonta. Dan duk namiji mai tsantseni ya dubeta sau ɗaya bazai sake yarda yay na biyu ba kodan tsoron ALLAH...
*_Mawaddat Isma'il Ibrahim Jiƙamshi_* kenan da akafi kira da suna _Lulu ƙamshi_ ƙyaƙyƙyawar budurwa mai kimanin shekaru ashirin da huɗu a duniya. Itace ɗiya ta uku a gidansu. Mahaifinta sananne ne da kowa yafi sani da Engineer Isma'il l. Jiƙamshi. Babban ɗan kasuwa ne kuma mamallakin *_Jiƙamshi Motors_*. Mawaddat yarinya ce da batajin magana, gata masifaffiyar gaske ta bugawa a jarida. Ƴar gata ce shalele kuma ƴar shagwaɓa a gidansu musamman wajen mahaifinsu Engineer Isma'il Ibrahim Jiƙamshi da Kawunta Yousuf Ibrahim Jiƙamshi. Gatan data samu da rayuwar turai data tashi a ciki ya sata zama fanɗararriyar gaske. Ga rashin kunyar tsiya. Dan kowace irin shiga Lulu ƙamshi zata iya fita da ita waje ko zama a cikin gida in har ba Uncle ɗin su Yusuf yana kusa ya tsawatar mata ba. Mawaddat ta samu wadataccen ilimin boko, dan a yanzu haka ita ɗin lawyer ce mai zaman kanta, duk da dai karatun ma da ƙyar ta iya kammalashi saboda rashin jinta, gaba ɗaya karatunta a ƙasar ƙetare ta yisa idan ka cire Nursery school datai a Nigeria. Sai dai a ɓangaren ilimin addini kam fanko ce, dan ko faatiha Lulu ƙamshi ba lallai ta kawo maka ita dai-dai ba. Sam bata son harkar talauci, ba kuma ta son talaka. Abu ɗaya ne ALLAH ya taimaketa da nisantata da shi duk da rayuwar turai data tashi a ciki, shine kasancewa da namiji. Ko kai ɗan uban waye a kuɗi ko nasabar zuri'a baka ishi Lulu ƙamshi kallo ba, dan ko turawan sun buga sun barta kam, hannunka ma yace zai yi gigin zuwa jikinta komai shigar rashin mutuncin da tai zata sauke maka kwando-kwandon masifarta. Ta dai yarda ta shiga club aci uban rawa ayi nishaɗi tai gaba. Sai sirrintaccen harkar da takeyi da har yanzu babu wanda ya sani a gidansu, dan tana aikatawa ne cikin taka tsantsan da kula, shiyyasa har yanzu babu wanda ya ganota duk da an ɗan taɓa samun akasi tsakaninta da Uncle Yousuf dai ya kusa harbota ta kuɓuta da ƙyar.

Wannan itace Mawaddat Isma'il Jiƙamshi (Lulu ƙamshi) a taƙaice.

Saurayin nan da suke tare tun daga cikin jirgin sauri yake na son cin mata, duk da yanda take takun nata cike da yauƙi da yanga. Wannan ita kaɗai ce damar data rage masa, gashi kuma tana neman kufce masa. Tunanin hakan babbar asarace a garesa ya sashi ɗaga murya wajen faɗin,
_“K! Sarauniyar mata. Son kowa ki dakata mana!!”._
Ɓuɗaɗɗiyar muryarsa da tsarin adon dake nuna shima ɗin wani shege ne ya saka mata da yawa tsayawa cak, sai kuma suka shiga juyawa suna kallonsa. Sai dai abin mamaki ita ko nuna lamar ma tasan yanai batai ba tafiyarta take. Ganin ya cigaba da ƙoƙarin cimmata ƴammatan da duk suka juya garesa suka shiga taɓe baki da yatsine fuska. Ko kallo basu ishesa ba sai ƙoƙarin cimmata da yake yi dai-dai tana ƙoƙarin isa ga inda motocin ɗaukar mutane keda hurumin tsayawa. Wani shegen kallo ta watsa masa fuskarta na sake tsukewa.
Fuska ya marairaice yana mai haɗe hannayensa waje guda alamar roƙo gareta, amma saita ja masa tsaki zata cigaba da tafiyarta. Sake shan gabanta yayi da faɗin, “Haba mana Babie ki saurareni koda akan abu ɗaya ne Please. Address ko phone number abeg you”.
Cike da yauƙi da yanga ta furta, “A matsayinka na wa?”.
Duk da yay mamakin jin hausa a bakinta sai ya shanye, cikin murmushi ya ce, “Neighbour naki a jirgi mana beauty!. Sunana MM Atik Kumo. Mahaifina M Atik Kumo sunane da duk wanda ya kwana ya tashi a Nigeria dama ƙasashen Africa ya sansh.....”
“Kai dalla can ka isheni da zance yannn-yannn!! kamar tsohuwar akorukura. Bani hanya kona wanke banzan face ɗin nan naka zubin alakoro da mari stupid”. Ta faɗa cikin katsesa da yarfi ta bi gefensa ta wuce. Tamkar gunkin da aka sassaƙa domin tarihi haka yay tsaye ƙiƙam yana kallonta, hakama duk wanda ke kusa da su sai da yay mutuwar tsaye akan abinda tayi. Dan kowa dai yasan wanene sunan MM Atik Kumo, amma yarinyar nan mai zubin yahudawa tai masa wannan yarfin. Kuma ko'a jikinta kamar yanda shima babu alamar zai ɗauki wani mataki.....

“Laahhh *_Uncle Smart_* ga Aunty Lulu ɗin nan”.
Wani ɗan ƙyaƙyƙyawan yaro dake saman jibgegiyar mota baƙa siɗik ya faɗa yana nunata. Wanda ya kira Uncle Smart dake gefensa tsaye kansa a ƙasa da keypad waya ƙirar Nokia a hanunsa ya ɗago a hankali tamkar mai ciwon wuya.........✍️


_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09018600202

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

Ƴan Niger kuma ga naku. Kuyi magana ta wannan number ɗin👇

+22799643131

VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥



*_ALLAH ya gafartama iyayenku😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲




🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗



𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻



𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣


........Ƙyakykyawan saurayi ne chocolate color mai cikar kamala da nutsuwa. Baida hayaniya a yanayinsa na zahiri bai kuma da fara'a sam akan fuska. A halittar jiki da cikar kamalar fuska mai nuna barazana ko maƙiyinsa dole ne ya yarda yaci wannan suna na *_Smart_*. Maimakon kallon wadda yaron yay nuni da kira Aunty Lulu sai ya ɗaga shi cak ya sauke ƙasa kawai tamkar ma baiji ba. Da gudu kuwa yaron ya nufeta cikin farin ciki da ihun kwakwazo yana mata oyoyo Aunty Lu.
         A hankali ta saki murmushi daya ƙara ƙawata ƙyawun fuskarta a karo na farko tana mai tsayawa cak har yaron ya ƙaraso gareta. Yana dab da zuwa gareta ta ajiye laptop ɗinta a saman akwatin dake ɗayan hanunta ta tarbi yaron. Dai-dai nan MM Atik Kumo da ya biyota ya ƙaraso wajen. A hankali murmushin dake a saman fuskarta ya fara ɓacewa, cikin ƙanƙanin lokaci fuskarta ta koma asalin yanda take. Cikin fushi da tsananin ɓacin rai ta watsa masa kallon nan nata na raini da wulaƙanci. A fusace ta furta, “Halan kai babu zuciya a ƙirjinka? Nifa a duniya na tsani wasu *_MAYUN MAZA_* wlhy”.
          _(Mayun Maza!!!)_ Kalmar tai wani irin amsa kuwwar maimaita kanta a cikin kunnensa duk da bashi aka faɗawa ba. A hankali ya ɗago fararen idanunsa masu girma karan farko ya saukesu a kanta. Dai-dai nan itama cikin tsiwa ta nuna MM Atik Kumo da yatsanta mai ɗauke da farce data ƙara a duk farautan hannuwan nata biyu da ƙafafu. Ɗauke idanun nasa yay da sauri wani irin sukar baƙin ciki na tokare ƙirjinsa, a duniya ya tsani mace irinta da zata iya saka kowane irin kaya ta fita kamar yanda take, tun daga samanta har ƙasa babu suffar mace musilma bahaushiya a tare da ita. Siririn tsaki yaja yana sake tamke fuska sai dai kunnensa na garesu.
         Itako da bata san yanayi ba yi take kamar zata tsole ma MM Atik Kumo ido da yatsanta data nunashi da shi. A cikin kaushin murya take faɗin, “Wlhy! wlhy! idan ka sake gigin zuwa gabana a karo na uku saina wulaƙantaka a wajen nan, mafi munin wulaƙanci, na yaga maka rigar mutunci kuma, danni *_FURAR DANƘO CE, A SHEKARA ANA DAMU BA FARAU-FARAU!!._* Mtsowww ban san damuwa ok”. Fuuuu ta figi hannun yaron da ya tsaya kawai yana kallonsu tare da lap-top ɗin ta tai gaba batare data ja akwatin ba.
     Babu alamar gargaɗin nata ya zafi MM Atik Kumo, dan wani murmushin ma ya saki da bin ƙugunta da kallo a ransa yana maimaita kalmar (_Furar danƙo a shekara ana damaki baki farau-farau_). Wani shegen yawu ya haɗiye yana lumshe idanunsa da suka wani ƙanƙance tare da lashe lips ɗinsa.       
        A gaban motar da Uncle Smart ya ke tsaye taja birki, cikin hucin takaici tai masa kallon sama da ƙasa fuska a yatsine. “Kai kuma malam haka ake aiki a garinku? Kana kallon mutane da kaya bazakaje ka amsa ba!!?”.
       Idan motar nan ta motsa to shima da ke jingine a jikinta ya motsa. Wani irin baƙin cikine ya sake turniƙe mata zuciya, “Kai sakarai kai waye da har ina maka magana zaka ɗauke mun kai? kan bala'i.....!”
     Da sauri yaron ya katseta da faɗin, “Aunty Lu! Uncle Smart ne fa! Shi bai san ihu, muma idan zai kaimu school ca yake muyi shiru a mota, kuma Daddy ma baya masa ihu ki bari kem.....”
          “Kai dalla yimun shiru. Shi ɗin waye da baza'a masa ihu ba. Shashasha da shi driver mai jiran wata tayi a bashi dubu goma”.
    Ƙwal-ƙwal yaron yay da idanu kamar zai yi kuka. Ya kalleta ya kalli Uncle Smart ɗin da ya ɗauke kansa kamar ma bada shi take ba. Itako idanu rufe ta cigaba da zazzaga masa masifa kamar mai jiransa dama. Da yawan mutane hankalinsu ya fara dawowa kansu. A hankali ya raba jikinsa da jikin motar, batare da ya sake mata kallo na biyu ba bayan wanda ya mata sanda take gaban MM Atik ya buɗe motar ya shige abinsa, da wani irin ƙarfi ya fisgeta yay reverse ɗin daya saka taron fashewa ganin zai takasu, fuuuu ya ɓace da ga wajen yay hanyar fita airport ɗin baki ɗaya..

Tuni wasu da abin ya birgesu suka shiga ƙyalƙyala dariya da faɗin hakan da yay ya musu dai-dai. Wasu ko mamakin ƙarfin halinsa sukeyi. Duk da dai tabbas guy ɗin ya haɗu iya haɗuwa, sai dai duk wanda ya kalli uniform ɗin dake jikinsa ya san kalmar driver data kirashi da shi kam gaskiya ne. Wasu ko dariya suka shiga kwasa da yaɓa mata baƙar magana musamman ganin wulaƙancin da taima MM Atik Kumo da har yanzu yana tsaye a wajen duk da body guard ɗinsa da sukazo suka zagayesa shima yana kallon komai.
       Lulu da gaba ɗaya ta koma butum butumi da wulaƙancin driver ɗin nata tuni jikinta ya fara tsuma. Numfashinta har wani irin fisga yake dan ɓacin rai, da sauri MM Atik ya matso gareta, yayinda security ɗinsa suka fara yima mutane nunin su tafi dan ALLAH. So yake yace wani abu amma wlhy shi tsoronta ma yake ji, bai taɓa ganin masifaffiyar yarinya irinta ba, ga azabar kwarjinin tsiya kamar wata babbar mace mai shekarun dattijantaka. Da ƙyar ya iya furta, “Please calm down Babie...”
       “Anƙi ai Calming down ɗin kai kuma!. Har ni sakarai irin wancan guy ɗin mai aikin tuƙi a gidanmu ƙarƙashin ikona zaima wannan walaƙancin? Mi yake taƙama da shi....?” Da sauri yaron nan yace, “To Aunty Lu bana faɗa miki Uncle Smart baya son ihu ba ki daina masa...” Hannu ta ɗaga zata fallama yaron mari MM Atik ya janyesa da faɗin, “Please Babie karki aikata haka”. Idanu ta rumtse da masifar ƙarfi dan kuka ma take jin yana taso mata tsabar baƙin ciki da tuƙuƙin da zuciyarta ke mata duk da kasancewarta mutum mai shegen taurin kai akan abu.. Duk yanda MM Atik Kumo yay ƙoƙarin ganin ta shiga motarsa hakan ya gagara. Dole ya haƙura cikin bodyguard ɗin sa yay mata kiran ɗaya daga cikin taxi ɗin dake wajen da dama su aikinsu ɗaukar manyan mutanen. Nanma ƙin shiga taso yi, sai da ya dinga magiya da roƙonta sannan. Kuɗin dake a aljihunsa ya ciro batare daya irga ba ya ajiye masa kusan dubu goma. Godiya sosai mai taxi ya dingayi tare da tambayar ina zai kaita. Cikin ɗar-ɗar ya dubeta, sai ma yaji ya kasa cewa komai ganin yanda take uban huci.. mai taxi da ya fahimci shima bai sani ba ya dubeta ta mirror. “Hajiya ina zamuje...?”
       “Gidan ubanka!! Dilla malam kaja mota ban san shiga sharo ba shanu”.
   “ALLAH ya baki haƙuri”.
Mai taxi ya faɗa yana kunna mota........✍️


*_Kai kai wannan yarinya ta cika jaraba. Anya zan iya kuwa😲😏? Bara dai muga ko zamu iya cigaba da bin al'amarinta😔🤔. Nasan dai Uncle Smart ya higa uku yau🥱._*


_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09018600202

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

Ƴan Niger kuma ga naku. Kuyi magana ta wannan number ɗin👇

+22799643131

VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥



*_ALLAH ya gafartama iyayenku😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲




🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗



𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻



𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣


........Da sauri MM Atik ya nufi tasa motar yana sanarma bodyguard ɗin sa su bisu. Wani saurayi dake jingine jikin motarsa da ke kusa da su MM Atik ɗin ya dubesa. Komai a gabansa ya faru, dan haka yay murmushi da duban MM Atik ɗin. “Ranka ya daɗe Bama sai ka wahal da kanka ba indai sanin gidan su Lulu ƙamshi ce. Sai dai zan baka shawara karka wahal da kanka dan ba lallai ka samu yanda kake so ɗin ba. Kamarka ma ɗan manya daya fito a gidan mutunci ka wuce da ajin wadda ta gama zama gawurtacciyar karuwar turawa tun tana mitsitsiyarta”.
        Ƙaramin murmushi MM Atik Kumo yayi, ya matso kusa da saurayin yana mai girgiza kansa. “Abokina karka damu da son nuna min abinda na gani da idona. Kai dai kawai faɗamin inda zan sametan tunda har ka mata irin wannan sanin haka”.
     Cikin rashin damuwa saurayin ya faɗa masa cikakken adireshin gidan su Lulu ƙamshi. Sosai ya masa godiya ya shige motar da aka buɗe masa fuskarsa ƙawace da murmushi......

         *_Manseer M Atik Kumo_* kenan. Ɗa na farko a wajen Hon. Mustapha Atik Kumo. Babban ɗan siyasar nan kuma tsohon gwamnan Kano da ya sauka, a yanzu haka kuma yana ɗaya daga cikin ƴan takarar shugaban ƙasa na wannan zangon da ake kan fara campaign. Sannan shi a karan kansa ma matashin ɗan kasuwa ne da kuɗi ke kaɗa masa gangar lokaci. MM Atik Kumo shegen kansa ne shima a wajen rashin jin magana. Dan duk wani mahaɗar marasa ji na ƴaƴan manyar ƙasar sune ɓoyayyun limamai. Manemin mata ne ƙwararren gaske, dan duk yanda mace takai da iya kame kanta sun san yanda zasu kutsa kai cikin mutuncinta har saita koma jin maganarsu fiye data iyayenta. Mahaifinsa mutumin kirki ne dattijon arziƙi abin alfahari, dan haka yake taka tsantsan akan iya shegensa ba ko'ina yake yarda ya nuna halinsa mara ƙyau ba, idan ma akace maka yana aikata wani abu makamancin hakan zaka iya ƙaryatawa dan ya iya takunsa sosai sosai....

   Wannan kenan.

     ∆••••••∆ ★ ∆•••••∆

          Tafkeken gida daya amsa sunansa gida a anguwar Nasarawa GRA drivern taxi ɗin yay horn kamar yanda ta umarcesa. Leƙowa maigadin yayi, ganin ba motar gidan bace ya wani yamutse fuska zai farama mai taxi ɗin wulaƙanci idonsa ya sauka a kanta. Wani irin rawa jikinsa ya fara da gudu ya koma ciki ya buɗe gate ɗin. Ko gama parking mai taxi ɗin baiyi da ƙyau ba ta ɓalle murfin motar ta fice cikin takun nan nata da ke motsa duk wata hallitar jikinta kamar tarwaɗa. Abinda zai baka mamaki ko rawa ƙafarta batayi a dalilin matsiyacin takalmin ƙafarta mai shegen tsini. Duk wani ma'aikaci dake gidan da ga kallo ɗaya baya sake mata na biyu zakaga ya nutsu cikin tashin hankalin ganinta. Dan halin masifarta da iya taka kowa a duk lokacin da taso buɗaɗɗen abune ga duk wani ma'aikaci na gidan. Duk tsufarka duk ƙanƙantarka zata iya gogeka tas idan ka kuskure mata koda a ƙanƙanin abu ne, tsiranka gareta kawai kada ka shiga shirginta, idan kuma ta saka ka abu yi ƙoƙarin mata a yanda ta buƙata babu kuskure. A duk lokacin da tai tafiya daɗi kowa keji a gidan, idan kuma ta dawo zakaga hankalin kowa a tashe. Satin ta biyu kenan da tafiya Abuja wajen ƙanin mahaifiyarta domin yin hutun aiki data samu acan, har addu'a suke ALLAH yasa karta dawo da wuri, sai dai kuma da alama addu'ar tasu bata amsu ba😂 dan gata ta dawo ɗin a bazata.
         Shigowarta a fusace katafaren falon gidan ya saka duk wanda ke ciki ɗagowa ya zuba mata idanu. A tsakkiyar falon ta tsaya tana harare-harare da cika da batsewa kamar wata kububuwa.
    “To aunty masifatu, lafiya kika shigo kina kumbura da ga dawowa kuma?”. Ɗaya da ga cikin wanda ke a falon ya faɗa cikin taɓe baki. Kamar mai jira a taɓata a fusace ta ce, “Shi ɗan uban waye a ƙasar nan da aka aikashi ɗakkoni? Miyake taƙama da shi?...”
         Kusan a tare suka shiga kallon-kallo, sai dai kafin wani ya bata amsa Dattijo mutumin dake a kujerar zaman mutum ɗaya da jarida a hannu ya miƙa mata hannu, “Kinga zo ki zauna naji miya faru Baby na?”.
         “Daddy babu maganar zama a fara faɗa min uban waye shi?, dan sai na wulaƙanta rayuwarsa a gidan nan wlhy, sai yayi dana sanin shigowa gidan nan yin aiki, idan kuma bazaku faɗamin ba ALLAH duk wani ma'aikaci da ke a gidan nan yau sai ya bar gidan...”.
      Sun san zata iya aikatawa, kaɗan daga aikinta kuma babu abinda Daddy ɗin nasu zaiyi saboda makahon son da yake mata a gidan. Ƴar budurwar da zata iya kai shekaru goma sha bakwai ce ta bata amsa da “Aunty Lu! Uncle Yousuf ne ya kawo shi, sabon driver ne ko sati biyu ma bai yiba

Please Login or Register in order to submit comment