Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gamsu da abinda ta faɗa tunda tabbas bai ganta ba a cikin gidan dan haka ya saka mata albarka. Ɗan jimm da tai ya sakashi fahimtar akwai wani abu, dan haka ya tambayeta. Sai da ta sake kwantar da murya cike da kissa ta zayyano masa dukkan abinda ƙanwarta ta tabbatar tajiyo, sai dai tace itace taji ba ƙanwar tata ba. Ta kuma kira ta faɗa ne dan kar abinda zasuyi ɗin ya taɓa kimar Baba da Family ɗin. Amma dan ALLAH bata son kowa yasan ita ta faɗa gudun abinda zaije ya dawo. Murmushi Baba ya saki irin na manya. Ya sake saka mata albarka sannan sukai sallama. Yasan Sulaiman zai aikata abinda ma yafi hakan, kuma shima yayi tunanin wani abun zai iya ɓullowa game da hukuncin nasa. Sai dai abinda ya bashi mamaki mi yake faruwane haka maneman Mawaddat ɗin keta karakaina a wannan gaɓar? Ko dai rawar data taka ne game da shari'ar mutumin nan ta kwanan nan data ɗauki hankalin mutane da yawa ce? Dan duk da baya ƙasar kunnensa da idanunsa na a Nigeria ɗin. Yafi zaton hakan shiyyasa bai ɓata lokaci wajen zurfafa tunani ba. Sai ma ya dannama Uncle Yousuf kira dan ya gama tsara kafin Sulaiman ya ƙulla abinda yake tsarawa shi zai tabbatar masa wanda ya rigaka kwana zai rigaka tashi......

          ★★.....

Sosai mamaki ya dabaibaye Uncle Yousuf da ke sauraren Baba. Dan ya masa bayani ne akan zuwan su M Atik Kumo kafin hukuncin da ya yanke a yanzu-yanzu saboda labarin da ya samu na shirin ɗansa da jikansa. Cikin girmamawa da godiya Uncle Yousuf ya tabbatar masa yanzu nan zai tura a isar da saƙon in sha ALLAHU. Suna yanke wayar kuwa yay kiran abokinsa Coach ɗin su Smart Abdull-Hameed, wanda ta sanadinsa ya fara sanin Smart ɗin dama. Tun yana waya da Hameed ɗin kiran Yayansa (Daddy) ke shigowa, bai ɗaga ba har sai da ya kammala da Hameed ɗin. Wani kiran ne ya sake shigo masa, ya ɗaga yana kaiwa kunne da faɗin, “Yaya irin wannan kira lafiya dai ko?”.
       “Inafa lafiya Yousuf! Wai kaji suma su M Atik Kumo sunzo nemawa ɗansu izinin neman Mawaddat. Anya abunnan na lafiya ne? Ni bama wannan ya damen ba, dan M Atik mutumin kirki ne, ɗan nasa ne kawai sai a hankali, dan wlhy da ace ya kasance mutumin kirki kamar mahaifinsa da hankalina zaifi kwanciya da aura masa Mawaddat fiye da yaron nan daka kawo....”
       Cikin gatse Uncle Yousuf ya ce, “To kodai a bama ɗan M Atik ɗin dama kawai, tunda shi dai ai ba wani abu ya taɓa aikata mana ba. Sannan a a bayyane ban taɓa jin ance ga aibun yaron ba...”
     “No no no Yousuf bar wannan maganar kai dai. Dan wlhy ina gama waya da Baba yanzu na ɗan fara bincike kan yaron wajen wani aminina al'amarin babu daɗin ji, dan akuyace lulluɓe da fatar kura bai gado uban nasa ba. Kayi haƙuri bakwai kushe yaron nan Aliyu nake ba. A'a kawai ina tunanin taya zai iya riƙemun yarinya bashi da aikin yi, danni ban ɗauki direbanci wani abunyi ba face hanyar maƙalewa domin rage matsaloli...”
           “Humm Yaya kenan. Nifa ban tsawwala ba, idan akwai wani da kake ganin hankalinka ya kwanta da shi game da Mawaddat ƙofa a buɗe take ka kawosa mu canjashi da Aliyu dan shi dama bawai ya ɗauki abun da girma bane tunda auren wata ɗaya kacal ne zai saketa, ni kuma na gaji da maimaita magana ɗaya”.
       “Ina ai zancen wani ma bai taso ba auta. Yanzu fa Baba ke sanar min kuma munafukin can abinda yake ƙullawa akan ɗansa. Kaga ko ai bamu da wani isashen lokaci. Mu ƙarasa da Aliyun kawai sai dai zamuyi komai a rubuce da ƙa'idoji dan karma da ga baya wani abu saɓanin wanda akai a rubuce ya biyo baya tunda mun samu Mawaddat ɗin ta amince babu rigima. Sannan zan basu gidan da zasu zauna a kuma canja masa aiki”.
       Sosai takaici yake neman shaƙure wuyan Uncle Yousuf. Amma sai ya danne ya ce, “Nima munyi waya da baban yanzu. Yanda kuma kake so haka za'ayi. Zan cema Aliyun ya tsaya idan ya kawota sai muyi maganar, idan kuma zamu bari ne sai zuwa weekend zaifi a nutse”.
     “Eh weekend ɗin yayi kawai ALLAH ya kaimu”.
    Sallama Uncle Yousuf yay masa tare da kashe wayar gaba ɗaya ma. Takaici yakeji na ɗan uwan nasa da halayyar da yake nunawa akan al'amurin Mawaddat mara fasali. Ya rasa wane irin soyayya yakemata irin haka. Ya kamata ace yayi nadama da neman hanyar gyara. Sai dai kash, nadamar tasa alokacin da ya ganta cikin wani hali ne kawai yake yinta.....

★★.....★

    Duk wannan cakwakiya da ƙura da take cigaba da tashi a wannan yini da ga mai gayya da aiki kam normal ne. Dan tuni ta tattara komai ta watsar ta tattara hankalinta akan case ɗin yarinyar nan da akaima fyaɗe dake neman caza mata kai. Tun bayan isarsu office bata wani zauna ba ta fito suka sake fita. Kasancewar hankalinta ga a inda yake ya sa yau tsakaninta da drivern nata babu masifa. Sun ɗanyi yawace-yawace har kusan bayan sallar la'asar sannan suka koma office. A hanyar komawar ne ya fahimci ana binsu a baya. Da farko bai kawo komai a ransa ba sai da ya ga bayan ta shiga office tai zaman kusan mintina talatin ta fito zai maidata gida a hanya ya sake ganin motar ɗazun ɗin nan dai da napep a biye da su. Yaji a ransa cikin biyu dole ai ɗaya. Kodai su Honorables, ko kuma Alhajin nan da ya sa aka sace shi wancan karan a yau kuma ya ganshi a gidan Baba. Yafi buƙatar ya kaita gida lafiya daga nan koma mizai farun ya faru, dan haka ya take motar ya tsere musu cikin salon canja titi gaba ɗaya..........✍️
         



_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070


VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥



*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲




  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗



           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻


𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣1️⃣



.......Mawaddat da ke da burin amsar saƙo ta kallesa fuska babu wasa. “Malam miye na canja hanyar? Dalla ka koma tacan ina buƙatar amsar saƙo”.
      Shiru kamar bazai tanka mata ba sai kuma ya bata amsa a taƙaice. “Akwai holdup ta canne, ga shi lokacin sallah ya kusa bana buƙatar rasa jam'i”.
          “To ɗan iya wannan kuma matsalarka ce. Bai kuma damen ba. Ka koma ta inda nace bana buƙatar sharhi”.
      Hanyar ya canja batare da ya sake cemata komai ba, amma kuma ba wadda dai take son abi ɗin ba dai ce. Dan zuciyarsa ta bashi kayan shaye-shayen nata ne zata amsa. Takaici ya turniƙe Lulu. Dama ga gajiya na nuƙurkusarta, ai tuni ta balbale sa da masifa amma yay biris da ita kamar yanda ya saba, bai ƙara tari ba har suka iso gida. Buɗe motar tai a fusace ta fito, dai-dai da shima yana fitowar da nufin buɗe matan. Ta zabga masa uwar harara da wani banzan kallo. Nunashi tai da ɗan yatsa tare da tattaro dukan ƙarfinta na zazzage masa abinda ke a ranta amma ko kalma guda ta gagara fita mata a harshe saboda yanda ya wani tsareta da idanunsa data raɗama suna irin na macizai. Sai lips ɗin ta ne kawai ke rawa kamar wanda ya ɗaureta da idanun nasa. “Kaje na koreka, da ga yau bana buƙatar sake ganin wannan shashashar fuskar taka illiterate velleger...!”
        A hankali ya lumshe idanun nasa sai kuma ya sakar mata wani shegen murmushi da ya kusa fisge mata numfashi gaba ɗaya. Jitai kamar zata zube a wajan tsabar wani ƙudu dun takaici da murmushin sa ya haifar mata. Dan bata fassarashi a komai ba face na rainin wayo. Fahimtar ya samu nasarar ƙular da itan da yake buƙata ya sashi matsota a hankali, cikin ƙasa da murya da wani maidata can ƙasan maƙoshi ya furta, “Oh! Kin fison sake ganin angon naki kawai a ɗakin barcinmu ke nan AMARYA, ba damuwa a bani albashina dan da shi zan biya sadaki”.
         “What!!!” ta faɗa da ƙarfi tare da kai ma fuskarsa mari da gaba ɗaya ɗan sauran ƙarfin da ya rage mata a jiki. Baya yay cikin wani salon da ta samu iska shuuu, ya ɗago yana murmushi tare da kashe mata ido ɗaya, sai kuma ya nuna fuskar tasa da yatsa yana ɗan sake matsota harda ranƙwafowa kaɗan. “Duk randa wannan hannun ya sauka kan wannan fuskar da sunan mari to kisa a ranki MAZA sun faɗi, faɗuwa irin ta MUTUWA. dan itace kawai damar da ƘYANWA zata iya samun yin birgima a gaban ZAKI yanda take so”. Ya ƙara kashe mata ido ɗaya yana ɗaga mata yatsu biyu da faɗin, “Bye *MATAR ILLITERATE*”. Yay gaba abinsa.
       Yuuuuu!! Lulu ta dinga jin hajijiya na neman kwasarta, wato itace ma ƙyanwar yake nufi. Dariya sosai Uncle Yousuf da ke cikin motar dake a kusa da su batare da sun san akwai mutum a ciki ba ke tuntsurawa harda ƙwalla. Ashe zaton da yakema yaron nan ya wuce nan. Kai jama'a har ya fara tausayin ƴar tasa gaskiya. Dan tabbas akwai babban wasa a wannan tafiya yanzu ne kuma za'a fara. Ganin yanda ta wuce tana haɗa hanya ga hawaye sun wanke mata fuska ya sashi daina dariyar ya buɗe motar ya fito, sai dai duk yanda yake son binta ya haƙura dan lokacin sallah yayi. Ya kai dubansa ga su Smart da ke alwala sai kawai ya nufesu yana gyara yanayinsa kamar bashi ya gama kwasar dariya ba a mota...

Bayan an idar da salla kusan a tare suka fito. Uncle Yousuf ya dakatar da Smart da ke sallama da su maigadi akan ya jira su wuce tare. Kamar zai ce a'a sai kuma dai yay shiru dan kiran da Abba yay masa suna ƙoƙarin shiga massalaci akan idan ya dawo gida ya sameshi falonsa yanzun nan. Yasan maganace da Abban, shi kuma da yayi niyyar bama masu bin san nan a baya dama dan ya tabbatar ba haƙura sukai ba su kamashi dan yana son yin magana da koma waye ya turosun. Babu yanda ya iya dole yabi Uncle Yousuf ɗin, shiko ya ƙaunaci ALLAH ya kaisa har gida yau. Tunda suka fito kuma yaga motar nan sai dai ba napep ɗin yanzu, motar dai ce ke cigaba da binsu yanzu ma. Suna isowa titin anguwarsu yaga sun dakata cikin takaici direban motar na kaina sitiyari duka alamar ba haka sukaso ba. Sai dai kuma abinda bai sani ba shima Uncle Yousuf ya san da su shiyyasa ma ya ɗakkosa ya kawo har gidan.
       “Alhaji yau na saka ka aiki, Nagode sosai”.
    Murmushi Uncle Yousuf da idonsa ke kan mirror yana kallon mutanen nan ya saki, tare da faɗin, “Har yanzu dai ina a Alhaji na? A tunani na na zama Uncle yanzu tunda ƴa zan bayar duk da auren wucin gadi ne”. Yanda Uncle Yousuf ɗin ya ƙare maganar ne ya saka Smart kallonsa, sai kuma ya ɗauke kansa yana sakin murmushi ya ce, “To ayi haƙuri Uncle”.
       “Shike nan na haƙura, dan dama ba'a san iyaye da fushi da ƴaƴansu ba.  Ina fatan zaka samu Abba da maganar yau ko?”.
     “Da wuri haka?”.
Smart ya faɗa da mamaki yana kallon Uncle Yousuf ɗin.
              “Dole ne muyi da wurin, dan ɗazun Baba ya sake kirana akan zuwan M Atik Kumo shima yana nemawa ɗansa aurenta, sannan Alhaji Sulaiman da ɗansa sun gama ƙulla matakin da zasu ɗauka a gobe idan ALLAH ya kaimu.....” tsaf ya zayyane masa komai shima. Mamaki ne ya sake lulluɓe Smart, yayinda a ƙasan zuciyarsa yake ta lissafi akan yanda zai canja salon wasan a yanzu tsakaninsa da Alh. Sulaiman. Kafin yanzu shi bai wani ɗauki zancen da muhimmanci ba, dan har ya gama ƙulla yanda zai kuɓuce wa al'amarin, sai dai a yanzun nan ya canja sabuwar shawara. Duk da bai san minene dalilin Alh. Sulaiman ɗin ba ya kamata ace ya nuna masa shima tsageran kansa ne a wannan gaɓar. Bai damu da zancen MM Atik Kumo ba.....
       “Aliyu kayi shiru!”
   Uncle Yousuf ya katse masa tunani. Iska ya ɗan furzar kaɗan sai kuma ya fuskanci Uncle Yousuf ɗin. Cikin sake furzar da wata iskar ya ce, “ Please Uncle kozan iya sanin yaya kuke da shi Alh. Sulaiman ɗin?”.
    “Yerh babu damuwa Aliyu. Alh. Sulaiman Sufi Ado Garko ɗane ga Alhaji Sufi Ado Garko. Sannan Yaya ga mahaifiyar Mawaddat uwa ɗaya uba ɗaya. A shekarun baya ɗan uwana mahaifin Mawaddat abokai ne da Alh. Sulaiman na ƙut-da-ƙut, dan sun haɗu ne tunkan ya auri mahaifiyar Mawaddat ɗin adalilin shi Baba da ya ja Yayana jikinsa. Sai dai a yanzu ba haka bane, dan bamu san minene ya shiga tsakanin wannan amintaka ba abokan biyu suka zama maƙiyan juna ta yanda ko inuwa ɗaya basa sha. Iya tambaya na yima Yaya amma yaƙi faɗa min komai. Shi iyakarsa fita harkar Sulaiman, amma shi Sulaiman a bayyane yake nuna tsanarsa garesa da mu ma ahalinsa gaba ɗaya shiyyasa Yayana yay ruwa yay tsaki wajen hana aure tsakanin Tajuddeen da Mawaddat dan yace akwai manufa. Wannan shine iya abinda na sani gaskiya”.
       Kai Smart yake jinjina wa cike da gamsuwa. Sai da Uncle Yousuf yay shiru sannan shima ya bashi labarin kamasan da Alh. Sulaiman ɗin yayi a randa yazo shi da Ahmad suka roƙesa ya koma aiki, ya kuma sanar masa aikin da yace ya koma yay masa tare da nuna masa motar yaran Alh. Sulaiman da ke tsaye a bakin layinsu kasancewar suna iya hango su da ga nan ƙofar gidan su Smart ɗin da ke a bakin titin.”
      Sosai al'amarin ya girgiza Uncle Yousuf ɗin, ya kuma tabbatar masa da shima dalilinsa na kawoshi gida yanzun. Dan tunda suka kammala waya da Baba yaji a ranasa Alh. Sulaiman zai iya ɗaukar mataki kowane iri ne akan Smart shine ya saka wani ɗan sanda zuwa office ɗin Lulu ya saka masa ido, ɗan sandan ne ma a Napep ashe, sai ko gashi bayan tahowarsu gida ɗan sandan ya tabbatar masa ana binsu... “Wato Aliyu idan na fahimta tun fara aikinka da mu Alh. Sulaiman na biye da lamarinka kenan? Kuma bana raba ɗayan biyu a wajen Tajuddeen ya sani. Lallai ya kamata musan dalilinsa danni zuwa yanzu har Tajuddeen ɗin ma na saka masa alamar tambaya”.
      “Sanin dalilinsa abunne mai sauƙi Alhaji, yanzu dai barshi na fara masa duka a ciki, bayan cikin ya ƙulle zai amayar da duk abinda ke a ransa da kansa. Sannan Tajuddeen bai zama lallai yasan komai ba, zata iya yiwuwa amfani uban keyi da shi batare da shi ma ya sani ba”.
    Murmushi Uncle Yousuf yayi tare da bubbuga kafaɗar Smart, dan tsaf ya fahimci inda zaurancen nasa ya nufa game da duka a ciki. Murmushi shima Uncle Smart ɗin yayi tare da buɗe motar yay masa godiya ya shige gida, shi kuma yaja motar yana ƙara jin ƙaunar yaron har tsakkiyar ransa. A rayuwa yana matuƙar ƙauna da son jarumin mutum. Musamman ma matashi irin Smart mai tsayyar zuciya. Wannan nagartar tasa ya fara hanga a filin ƙwallo ya shige masa zuciya, faruwar ƙaddarar data nema dakushesa da ga cikar burinsa ta fara sakashi jin tausayinsa da laluben hanyar da zai iya taimaka masa. Bayan yin dogon nazari ya yanke shawarar kusantosa gefensa domin ƙara tabbatar da halayensa kafin ya ja hannunsa hanyar da ya gama shiryawa domin kaisa ga cikar burin nasa. Sai kuma ga al'amarin ƴar ɗan uwansa ya gitta a cikin labarin tamkar bakangizo a tsakiyyar gagarumin hadarin da ke gab da zubda ruwa. Fatansa kawai ta kasance bakangizo mai amayar da ruwan da ta shanye bamai haɗiyewa ba har abada.........✍️

      

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070


VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥



*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲




  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗



           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻


𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣2️⃣




.......Bai samu ganawa da Abba ba sai bayan sallar isha'i ya samesa a falonsa. Bayan sun gaisa cikin dakewa Abban ya ce, “Aliy!”.
    Ya amsa da “Na'am Abba”.
  “Aliy!”
Ya sake ambata. Shima sake amsa masan yayi kamar farko. Malam Mika'il bai gajiya ba ya sake kiransa a karo na uku shi kuma ya amsa masan dai kamar yanda yay na farko da na biyu.
         “Na kiraka sau uku ko?”.
    Kai ya gyaɗa masa alamar eh.
“Na kiraka badan tisa maka sunan da ni na saka maka ba ne, na kiraka ne domin a yau zan tabbatar maka da magana ta ƙarshe ne akan aurenka. Dan duk maganganun da Yahanasu ta faɗa ɗazun akanka sun sosama mahaifiyar ka da nima kaina zuciya. Kuma mun ɗauki alƙawarin bazaka sake rufa wata anan gidan babu matar aure ba. Dan haka a yanzu ina son jin ta bakinka, idan kana da wadda kake so sai ka faɗeta, idan kuma babu mahaifiyarka ta maka mata, nima kuma na maka sai ka zaɓi guda a ciki.”
       Sai da ya ɗan rumtse idanunsa da jan numfashi, sannan ya ɗago a hankali ya kalli mahaifin nasa. Sai kuma ya sake maida kansa ya duƙar. “Kuyi haƙuri Abba duk ni ne na ja muku, amma insha ALLAH komai yazo ƙarshe, ba sai kun nemomin mata ba ni da kaina ma na samota”.
     Wata irin ajiyar zuciya Abba ya sauke a hankali, sai dai cikin dakewar san nan ya ce, “Wacece? Ƴar wanene? A ina kuma ta ke?”.
           Duk da yawan tambayoyin bai gazaba wajen amsasu ga mahaifin nasa. Ya ce, “Yarinyar da nake aiki gidansu. Ɗiya ga Alhaji Isma'il Jiƙamshi. A yau suma kuma suka buƙaci na turo iyayena dama in har na shirya”.
      “Alhamdullahi. Aliyu Hydar ka daɗe baka faranta min rai irin yau ba. ALLAH yay maka albarka. Ya yaye maka dukkan damuwarka. Ya ɗauraka akan maƙiyanka. Ya kawo maka mafita ga al'amuranka. Na amshi zaɓinka badan ta kasance ɗiyar Alhaji Isma'il Jiƙamshi ba, ko dan yana da kuɗi, sai dai dan nasan kai nagartaccen mutum ne da bazai taba yin zaɓen tumun dare ba.”
     (Abba ka gafarceni wannan dai kam zaɓen tumun asubace ma ƙarewar dare) ya faɗa a zuciyarsa. A zahiri kam murmushi kawai yayi da faɗin, “Nagode Abba. ALLAH ya ƙara lafiya da nisan kwana mai amfani. Ku gafarceni akan dukkan abinda nai muku ba dai-dai ba kuma insha ALLAHU zan cigaba da zama a fiye da yanda kuke buƙata”.
     Sosai Abba yay murmushin jin daɗi, Aliyu na cikin ƴaƴan da yafi ƙauna a cikin ƴaƴansa, sai dai shi kansa a wasu lokutan bai san mike danne soyayyar ba yayta kyararsa da hantararsa a dalilin ƙaddarar da wani bai isa ya canjata ba. Albarka sosai ya saka masa sannan ya sallamesa. Koda yabar wajen Abba cikin gida ya shiga, sai dai kai tsaye ɗakin Ammah ya shige yau bai gaida kowa ba a matan gidan. Ya samu tana shirin fitowa kaima Abba abinci dan yau itace da shi. Ya fahimci tana cikin damuwar da ya san babu makawa akan abinda ya faru ɗazune tsakaninta da Umma. Ƙannensa kansu yau basa cikin walwala. Suna gama gaisawa Ammah ta fice, annan ne Hawwah ke bashi labarin faɗan da akai sosai ne ai yau ɗin kuma duk a sanadinta ne. Da ga ƙarshe aka ƙare da musu goron halin da yake a ciki. Sosai ya ƙara jin zuciyarsa ta Zafafa. Sai dai komai bai ce ba yay musu sallama ya tafi makwancinsa......

          *_WASHE GARI_*

     Washe gari batare da sanin kowa ba Abba da tawagarsa suka nufi gidan Alhaji Isma'il Jiƙamshi nemawa Aliyu Hydar auren Mawaddat Isma'il Jiƙamshi. Sun sami tarba ta mutunci dan har Baba ma yazo gidan shima. Abinda zai birgeka babu ƙyama ko hantara irin ta mai kuɗi ga talakawansa. Abin farin ciki da mamaki ashema Alh. Sufi Ado Garko school mate ɗin Abba ne ma a secondary school. A take hira ta kaure a tsakaninsu har zuwa kan abinda ya tarasu. Sai dai kuma bayanin da shi Baba yazo da shi ya girgiza su a wajen. Dan a ganinsu babu wani shiri ai tare da su game da haka. Baba ya kwantar musu da hankali tare da tabbatar musu da dalilansa masu ƙwarin gaske ta yanda su duka suka gamsu da hakan. Sun ɗan ƙara tattaunawa sannan sukai musu sallama cike da jin daɗin karramawar da suka samu suka suka taho akan sai anjima idan sun haɗu ɗin....


★★......

Sam Smart bai san mima ake ciki ba. Dan hatta zuwan nasu Abba bai san da shi ba saboda yau bai ma fita aiki ba. Tunda ita tace ta koresa da kanta a ganinsa babu amfanin ya koma su sake raba hali. Dan haka ya zaɓi yin kwanciyarsa a ɗaki yayta buga game ɗinsa hankali kwance har lokacin sallar juma'a ya gabato. Yana shirin shiga wanka Ahmad yazo gidan. Zuwan Ahmad gidan ba sabon abu bane garesa dan haka bai damu ba. Haka koda ya bashi shadda sabuwa fil yace ita zai saka bai kawo komai a ransa ba dan Ahmad ɗin ya sha musu ɗinki irin hakan, haka shima kansa yasha yi musu ɗinki a taren.
     Bai wani ɓata lokaci ba ya fito a wankan, Ahmad na zaune har ya kammala shirinsa. Yayi ƙyau matuƙa kamar ka sacesa ka gudu. Ahmad ya wani shiga masa ruwan turare. Warce turaren Smart yay yana hararsa da faɗin, “Kaifa a duniya kamar baka san wahalar kayan duniyar nan ba. Anata wannan yanayin zaka ƙaramin turare haka dan neman hanyar talautani”.
           Dariya kawai Ahmad yay masa da kashe ido ɗaya ya furta “Am sorry Zakin zaki”.
     Shima dariyar yay a karo na farko. Dan duk sanda ya kira shi da Zakin zaki yana nufin shi ɗin na Coach Hameed kenan yayansa. Cikin nishaɗi da farin cikin tsokanar juna da suke na kiran tuzurai suka fita. Jan Ahmad yay suka shiga ciki gaida Ammah. Ta saka masu albarka tare da addu'a data so tsayama Smart a rai. Amma sai ya danne ta a ƙasan rai da tunanin Ammah tayi addu'ar ne kawai domin gabansa. Daga haka suka taso suka fita acewarsu zasuje sallar juma'a su dawo nan suci biranuskon da Amma keyi matsayin abincin rana...
        “Wai wane massalaci zaka akaimu haka ne?”.
    Cewar Smart yana kallon Ahmad dake drivering a nutse. Murmushi Ahmad yay masa idonsa a titi ya bashi amsa da “Mi kakeci na baka na zuba? Zaka gani ai”. Baki Smart ya ɗan taɓe da cigaba da game ɗinsa a waya. A haka suka cigaba da ƴar hirarsu har suka iso massalacin juma'ar. Zamansu babu jimawa aka fara khuɗuba, dan haka suka nutsu wajen saurare har aka kammala. Ana ƙoƙarin tada salla ya hango Uncle Yousuf da Coach da ke isowa yanzu, da alama sun makara ne. Baice komai ba ya gyara tsaiwarsa aka tada salla. Kasancewar bayan idar da sallar juma'a yin ɗaure-ɗauren aure a massalacin normal ne yasa bai kawo komai a ransa ba. Sai

Please Login or Register in order to submit comment