Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kallo. Sannu da zuwa suka shiga masa a zatonsu isowar kenan. Ya zauna yana amsa musu da tambayar lafiyarsu. Lulu na zaune a ƙasa tana shan fruits da aka yayyanka a bowl. Ta sauya kaya alamar wanka tayi, dan wando ne da riga marasa nauyi a jikinta. Kan babu ɗan kwali ya dai sha gyaran da sukayo yau sai ƙyalli yake yi. Idanunsa ya ɗan lumshe da sake lafewa cikin kujerar zantukan Ahmad na dawo masa a rai dalla-dalla. Shi yasan akwai ƙura, dan ko za'a kaisa jail sakinta bazai taɓayi ba koda a mafarki ne. Maryam ce data kawo masa abinda yace a masa cikin hikima ta janye su Amrah suka koma ɗaki tunda acan ma akwai tv. Lulu ta bisu da kallo tana faɗin, “Ku kuma ina zaku muna hira?”. Da dariya Maryam tace, “Aunty muna zuwa sirri zamuyi mu dawo yanzun”.
        “To ALLAH dai yasa bani za'a ƙullawa ba”.
    Dariya suka shige sunayi, yayinda Smart ya sakko ya zauna a ƙasan kusa da ita. Hannunta ya riƙo ya kai apple ɗin data ciro jikin cokalin bakinsa. Juyowa tai ta hararesa. Yay murmushi da ɗan kashe mata ido ɗaya. “Idan ma  ke zasu ƙullawa ba gani a kusa da ke ba sai na kunceki tsaf na maida igiyar kansu Madam”.
        “A'a Granny ƙarewar Madam”. Ta faɗa tana sake balla masa harara. Dariya yayi yanzu kam fararen haƙoransa na bayyana da ƙyau. Sai da taji wani zuuu cikin kanta amma tai azamar ɗauke idanun cikin basarwa. Shiko ya cigaba da faɗin, “Ai ki godema ALLAH da baki zo a kakar tawa ba. Gaskiya da Kinga takanki dan sai na addabeki”.
        “Sai dai ko mu addabi juna. Dan kaima kasan Lulu ƙamshi ba kanwar lasa bace.”
     “Niko nasan haka”.
  Ya faɗa cikin ɗage gira. Kankanar data tsiro ta tura masa a baki tana harararsa. Ya shiga shan abarsa yana murmushi. Itako ta maida hankalinta a kallon da sukeyi dan tana matuƙar son film ɗin duk da horro ne. Shima gyara zamansa yayi ya matsa jikinta sosai ya jingina bayansa da kujera kamar yanda tayi. “Wai sai sha kike baƙya bani ALLAH sarki autan Ammah akwai haƙuri”. Ya faɗa a mararairaice. Juyowa tai ta kallesa, sai kuma ta kalla fruits ɗin. “Oh kace kwaɗayi ya zaunar dakai nan ɗin ba kallo ba ashe?”.
        “To kusan haka”.
    Ya bata amsa yana shafar sumar kansa da bata da yawa can sosai, sannan tafi saisaye kuma. “Kwaɗayi dai mabuɗin wahala ne” ta faɗa tana tsiro abarba ta miƙa masa. Maimakon ya amsa cokalin sai ya riƙe hanunta ya kai abarbar bakinsa a haka da nata hannun. Batace komai ba ta janye hanunta daga nasan. Sai ta koma idan ta sha saita tsira ta miƙa masan, shi kuma ya riƙe hannun nata ya kai bakinsa. Harda ɗan kwanto kansa a kafaɗarta kaɗan. Shagala datai a kallon yasa bata maida hankali ba duk da tabbas tana jin kan nasa a kafaɗarta sai dai ba sakar mata nauyi yay ba sosai.
         “Wai ko ki tambaya inda naje, da zan tafi baki tambaya ba. Ina can munyi waya baki tambaya ba. Na dawo ma haka. Anya zaman tare yace haka Mawaddatan'warahmah”.
     Yanda ya kirayi sunan nata sai da taji zuciyarta ta motsa. Duk da kuwa Uncle Yousuf kan kirata da sunan lokaci zuwa lokaci. Kansa da ke a kafaɗarta ta ture da faɗin, “Mi haɗina da tafiyarka da dole zan dage sai naji. Ko salan a kirani mai gulma kuma”.
           “Haka ne kuma fa”.
      Ya bata amsa cikin rashin damuwa. Sai kuma ya jawo tray ɗin da Maryam ta ajiye ya buɗe ƙaramin flaks da ta saka kunun madara a ciki ya zuba a cup, kaɗan yasa suga. Ya fara sha ya lura tana kallonsa. Kofin ya miƙa mata batare da yayi magana ba. Sai ta ɗan yamutsa fuska tana girgiza kanta.
           “Da akwai daɗi fa, ɗan-ɗana kaɗan kiji”.
     Kamar bazata amsa ba sai kuma dai ta amsa ɗin, kaɗan ta ɗibo a spoon ɗin takai baki. Sai ta ƙara ɗibowa tana kallonsa. “Akwai fa daɗi, ni dana ga tanata haɗa-haɗa sai na ɗauka jagwalgwali ne kawai”.
       Murmushi yay mata da amshe spoon ɗin yana faɗin, “Karkuma ki shanye min to daga tayi”.
     “Oh ashe ba daɗi ni ka shanye mun fruits ɗina.”
             “Tofa gori ne abun? To shikenan musha”. Ya faɗa yana miƙa mata. Amsa tai ta sha ta miƙa masa itama, haka suka dingayi yanzun ma dai da spoon ɗaya suna kallo. Ya ƙare ya sake ƙara musu wani. Sai gashi sun shanye kunun flaks ɗin duka. Farfesun dake cikin kwanon kuma bai ciyu ba. Suna a falon har sai da Film ɗin ya ƙare. Shi ya kwashe kayan ya kai kitchen tare da kashe komai ya rufe ƙofar. Ita kuma ta tattara kayanta ta wuce ɗakinta ko sai da safe babu. Da kallo kawai ya bita yana girgiza kai, shima sai ya nufi nasa ɗakin. Sai da ya kammala komai na al'adarsa kafin kwanciya sannan ya canja kayansa zuwa na barci yasa turare yay brush ya fice. Lulu na zaune a tsakkiyar gadonta tana aiki a system ya shigo. Kallonsa take da mamaki daga sama har ƙasa. Kafin cikin ƙarfin hali ta ce, “Lafiya kuwa?”.
         “Ƙalau”.
     Ya faɗa a taƙaice yana hayewa gadon.......✍️


😜Wace gulma ta kawoshi ka to🚴

         




_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥



*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲




  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗



           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻


𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 8️⃣4️⃣



.......Sai da ya kai kwance duk tana kallonsa sannan ya cigaba da faɗin, “Zan kwana anan dan karma yaran can su fahimci wani abu daban har su faɗa a gida. Bazan so Ammah taji abinda bashi take fata ba a rayuwar gidana”.
               Duk da maganar tasa ta ɗan zabureta a zuciya sai ta kanne da tureta gefe ta ɗauke kanta. Sai kuma ta juyo da tura masa bargo ta ce, “To ga duvet nan koma sofa. Dan wlhy ban iya kwana da mutum biyu a gado ba, a cikin ɗaki ma kowa da makwancinsa ko yara ne takura nakeyi. Balle ma kai ƙato da kai ai saika sakani firgita”.
       Dariya maganar tata ta bashi, amma sai ya kanne baiyi ba yay ɗan murmushi kawai da kai hannunsa kan tarin fillos dake a gadon ya jawosu. Ita ya kalla da faɗin, “Kinga ɗan matsa gaba”. Matsawar tai shi kuma ya shiga jera fillos ɗin a tsakkiyarsu. “Gashi nan nikam an raba basai kin korani saman sofa ba dan bazan iya barci acan ba nima.”
       Harararsa tai da sake faɗin, “To nifa wlhy zan iya tsorata?”.
    “Saboda mi? Bayan kin san dai ni ne kuma bazan kawo wani hari ba inma yaƙin ƙasa da ƙasa kike tsoro”.
        Ba fahimtarsa tai ba ita kam. Dan haka kai tsaye ta ce, “Kawai dai bana son namiji kusa dani, dan yana tuna min abinda bana son na tuna?”.
     (Anzo wajen) ya faɗa a zuciyarsa. A zahiri kam sai yace, “Ai komai nada dalili. Miyasa hakan?”.
           “Humm manta kawai”.
     Ta bashi amsa tana maida hankali ga laptop ɗin tata. Shiru yay dan baya son nuna mata zaƙuwarsa na son ji. Sai ma ya lumshe idanunsa kamar wanda yay barci. Itama aikin ta cigaba da yi zuciyarta dai na wasuwasi akan kwanansa a ɗakin, wata kuma na ƙoƙarin nusar da ita na yau ne ai kawai. Bashi da wata manufa kuma tunda bai taɓa gwada makamancin hakan ba sai yau da yaran nan ke a gidan. Haka dai ta cigaba da saƙawarta da kwancewa har aikin ya nema gagararta, da ga ƙarshe dole ta kashe system ɗin da tattare takardun data baza. Juyawa tai tana kallon Smart da ke sauke numfashi a hankali, da gaske yanzu kam yayi barci dan a gajiye yake matuƙa. Sai ta samu kanta da sauke numfashi mai nauyi itama. Sauka tai a gadon ta nufi bayi, bata jima sosai ba ta dawo. Kasancewar dama wutar ɗakin ba wata mai haske bace can sosai ya sata ɗan tsayawa tana kallonsa da alama dai har yanzu zuciyarta na rawa, dan kallon da take masa bawai kallone irin na ka ɗauki hankalina ba, a'a kallone irin na nazari akan son yanke hukuncin na yarda ko kar na yarda?. Ta jima a wajen tsaye har ƙafafunta suka fara mata dayi sannan ta jasu da ƙyar ta koma saman gadon dai ta kwanta tana sauke ajiyar zuciya a jere. Addu'ar barci da yakan gargaɗeta ta dinga yi wanda Alhmdllh ta yi nisa kaɗan a koyansu ta fara, sai dai bata zaton takai ko rabi ba barci ya kwasheta. Dan itama ɗin dai akwai gajiya tattare da ita, sannan da rana bayan dawowarsu ta sha syrup kwalba ɗaya. Gaba ɗayansu kamar wasa duk sai barcin yay musu nauyi sosai, kusan gabannin asuba Smart ya farka, jin abu a jikinsa da ɗumin da baiyi kama dana bargo ba ya sashi buɗe idanunsa da ke cike da nauyin barci da ƙyar. Akan ƙyaƙyƙyawar fuskarta ya sauke cikin ɗan hasken ɗakin, barcinta take hankali kwance lafe a jikinsa kamar wata ƴar mage. Sai da ya ɗan waro ido na mamakin yaya akai hakan ya faru? Juyawa yay ya kallesu su da gadon, sai yaga tabbas shine ya ture filos ɗin tsakkiyarsu da ya jera ya dawo inda take. (Ɗan Ammah kaika fara kawo wannan harin na tsakanin ƙasa-da-ƙasa fa kenan) ya ayyana a zuciyarsa. Sai ya samu kansa da sakin murmushi yay ɗan luuu da idanu yana maida kansa ga filonta da ya dawo kai. Kamata yay ace ya koma inda yaken kafin ta farka dan kuwa dai yasan zai sha cara, to amma yana yin wani motsi fa zata iya farkawa matsalar da yake gudun ta afku saboda a jikinsa take sosai, sai kawai ya zaɓi zubama sarautar ALLAH ido tunda akwai sauran daren, shima sabo da tashi yin nafilfilin daren ne ya sashi farkawar. Gashinta da duk ya zazzame da ga cikin ribbon da aka ɗauresa yasa hannu ya gyara mata, sai ƙyaƙyƙyawar fuskar tata ta sake fitowa fes da ƙyau. Kwanciyarta tai ƙoƙarin gyarawa da sake mamuƙesa a cikin barci batare data sani ba, dan ta kasance mai ɗabi'ar rungume filos idan tana barci, a yanzun ma dai da alama hakan take tunanin tayi, batasan baban filos bane gaba ɗaya😂. Ba shiri Smart ya rumtse idanun da ƙarfi yana cije lips, (Wayyo ɗan Ammah itamafa ta kawo hari wlhy, shike nan ƴan tada zaune tsaye sun fara tattaro makamai) ya sake faɗa a zuciyarsa yana matse jikinsa a waje guda sai dai ina a jikin nasa take ma gaba ɗaya, ta kuma cigaba da barcinta hankali kwance. Wata wawuyar ajiyar zuciya ya sauke da buɗe idanun da ƙyar a kanta. Wannan fa shi ake kira siye da kuɗi yafi siye da bashi, dan fuskarta ta sake matsowa kusa da tashi sosai ga numfashinta da ke sauka masa a kan fuska na sake rikita masa lissafi. Maida idanun kawai yay ya rumtse, sai dai zuciyarsa da gangar jikinsa sunki yarda da wannan lallashin, har takai baima gama yanke hukuncin abinyi ba kawai ya sauke lips ɗinsa akan nata, tun yanayi cikin shakka-shakkar karta farka har ya dake kawai abinsa yama ɗaura hannunsa sosai a jikinta ya sake turata ciki. Sam Lulu bata da nauyin barci, dan haka ta farka kuwa jin baƙon al'amari a gareta, sai dai nauyin da idanunta sukai da ma jikin nata ya sata jan sakanni kafin ta fahimci mike faruwa. Wannan ma wata dama ce ga Smart dake shagulgulansa batare da yasan ƙasar da ya kaima harin ta farka ba. Lokacin da ya kamata ta ɗauki mataki itama jikin nata ya fara amsar harin nasa, sai ta samu kanta da ƙoƙarin maida murtani. Rikicewa Smart ya sake yi illahirin jikinsa ya shiga rawa, sai ya nema canja salo akan fiye da abinda yake yin. Anan ne fa Lulu ta dawo hayyacinta, jikinta daya fara rawa ta fisge taja baya, sai kuma ta shiga kallon gadon da sauri, cikin ƙarfin hali da dafe kai shima Smart ya tashi zaunen. Masifa take son masa, amma bata da wani ƙarfin yinta, sai kawai ta sakar masa kuka.
       (Ya ALLAH) ya ambata a zuciyarsa da janye hannunsa da ya dafe goshi ya ɗago idanunsa da sukai matuƙar kaɗawa ya zuba a kanta. Lips ɗinsa na ɗan rawa ya ce, “Mawaddat...” yama kasa ƙarasa abinda yake son faɗar, sai kawai ya sake dafe kan tare da komawa ya kwanta..
            Hakan da yay sai ya sa wani irin takaici sake mamaye zuciyar Lulu wato ma kenan yayi hakanne dama da shiri. Tattaro dukkan ɓacin ranta take a maƙoshi, amma ta kasa furtawa, sai kawai ta tura kanta cikin ƙafafunta ta sake sakin kuka. Har cikin tsakkiyar ransa yake jin kukan nata, ga bala'in daya ƙulle masa ciki ya sashi kasa koda iya motsawa, jin ta sauka a gadon ya sashi buɗe idanun nasa da ƙyar, dai-dai nan ta buɗe ƙofar ɗakin ta fita tare ba banging nata da ƙarfi har sai da ya rumtse idanunsa. Har aka kira asuba ya kasa tashi saboda halin da yake ciki, ita kuma bata dawo ba, addu'a kawai yake ALLAH yasa ba ɗakin yaran ta tafi ba, duk da baya jin zatai hakan. Duk da halin da yake ciki shi ya cancanci tausayi amma shi ita yake tausayawan, dan yau ya sake tabbatar da akwai wani abu a ranta da yasa take ma tsanar maza da ƙara ƙaimi wajen son ɗaukar mataki akan masu fyaɗe. Hakan kuma nada alaƙa da cin kashin da takema ƴan aikin gidansu, dan tun a wancan karon dama ya lura tafi taka mazan fiye da matan. Da ƙyar yay dauriyar sakkowa ya nufi bathroom ɗin ɗakin, ko kayan bai cire ba ya sakar ma kansa ruwan sanyi, ajiyar zuciya ya dinga saukewa a jajjere, yafi mintina goma kafin ya kashe shower ɗin ya zame kayan jikinsa, dole ya tsaftace jikinsa sannan ya fito, har yanzu dai da alama cikin nasa bai saki ba, a haka yay dauriyar fita a ɗakin ɗaure da towel ɗinta. Falo ya fara dubawa ko tana nan, amma bai ganta ba, sai kawai ya yarda wajen yaran taje. Lips ɗinsa kawai ya cije ya koma bedroom ɗinsa, sai kuma a mamakinsa ya ganta kwance anan. Dan yana buɗe ƙofar tana miƙewa zumbur cikin ɗan barcin da ya figeta bayan ta gama shan kukanta a dalilin abubuwa da yawa na rayuwarta da suka shiga dawo mata wanda bazata taɓa mantawa da su ba.
        “Nan ma biyo ni kayi? Aliyu ni zaka shiryama tuggu kamin fyaɗe! Wlhy ka sani nafi ƙarfinka kai da ma duk ire-iren ka, kuma da ga yau idan ka sake tunanin raɓata sai na ɗauki mataki a kanka dan zan iya maka illa, dan haka ka kama kanka kwanakin nan su cika batare da ka rasa wani sashe na jikinka ba!”.
       Sororo Smart yay kawai yana kallonta, yanda take maganar da dukkan gaskiyarta ga hawaye tanayi kuma, kalmar “Zan iya illataka Aliyu! Wlhy zan iya illata ka kamar yanda na kashe wancan tsinannen” ta sashi dawo hayyacinsa. Sai kuma ƙirjinsa ya shiga bugawa, amma sai yay jarumtar dannewa wajen faɗin, “Mawaddat relax ni fa mijinki ne, ki sani ni ba irin waɗancan da kike tunani bane, ALLAH ya halatta min ke duk abinda zan miki bada nufin cutarwa bane. Mawaddat aure yanada tarin abubuwa da suka banbanta da abinda zuciyarki ke iya hasaso miki. Dan ALLAH ki bar kukan nan haka ki nutsu bayan munyi salla muyi magana”.
        “Bazanyi magana da kai ba Aliyu, bakuma zan sake ganin mutuncinka ba wlhy, ban san haka kake ba ai kaina da ban ɗauke ka a yanda na fara ba....” fuuu ta fice a ɗakin nan ma tai banging ƙofar da ƙarfi har sai da ya ɗan zabura. Ya jima shiru abubuwa da yawa na masa kai da kawo a zuciya har aka fara ƙoƙarin shiga salla. A gaggauce ya shirya sai dai bazai iya fita massalaci ba dan cikinsa yay masifar ƙullewa dole a gidan yay salla. Bayan ya idar yana son zuwa inda take amma yana gudun kar yaran can su fahimci mike faruwa. Dole ya haƙuri akan har sai sun wuce, dan haka ya hau gado ya kwanta. Abu kamar wasa sai ga ƙaramar magana ta zama babba, dan kuwa dai zazzaɓi ne mai zafin gaske ya lulluɓe Smart harda su rawar sanyi.........✍️

         




_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥



*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲




  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗



           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻


𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 8️⃣5️⃣



.........Lulu duk da ranta a dagule yake tayi dauriyar dannewa saboda yaran, kasancewar Maryam akwai hankali tunda daddare ta tsara musu su tafi yau suba ma'auratan waje, sai kuma akai sa'a har su Amrah suka fahimceta. Koda gari ya waye sukaga basu fito ba basu damu ba suka gyara gidan tsaf sukai break fast. Nasu sukaci suka shirya musu nasu a table. Sun kammala kenan Lulu ta fito. Gaisheta sukai su duka cikin haɗa baki, ta amsa musu tana murmushin ƙarfin hali, dan girmamawa na ɗaya da ga cikin abinda Lulu keso gana ƙasa da ita. Wannan kuma shine mataki na farko da dangin Smart suka kama mata zuciya da shi, yau gashi har ƙannenta sun kwatanta abinda bata taɓa gani ba. Kamar yanda suka tsara Maryam ce ta sanar mata zasuje gidan ƙunshi su taho da mai ƙunshi da tace tana so. Lulu bata kawo komai a ranta ba ta ce, “Da sassafen nan kuma Maryam. Ku bari sai anjima ni ƙunshin ma kamar na fasa kuma”.
        “Kai aunty dan ALLAH karki fasa. Ai zamuje ne dan ta sani inma tanada wani aiki kinga ta kammala da wuri bawai yanzu zata zo ba”.
      “To shike nan, amma har ku duka zakije?”.
    A tare suka amsa mata da eh. Key ɗin motar ta dake a falon ta miƙama Amrah dan sun iya driving duk da dai ba basu mota ake ba sai ta kama. Cikin gargaɗi tare, “Banda ganganci Please”. Dariya kawai su Afrah sukai dan sun san dai aunty Lu.. ɗin su indai tuƙin ganganci ne ita ɗin master ce. Sallama sukai mata suka fice, dama sun fidda kayansu tun ɗazun..

      Kwanciya tai a falon batare da neman abincin da zata ci ba duk da kusan goma ne yanzun. Tana a wajen kwance ba barci take ba har sha biyu, tunanin abubuwa kawai take daban-daban, babu alamar su Maryam dan haka ta ɗaga waya tai kiran su Amrah. Cikin dariya suke sanar mata ai su suna ma gida, sai da suka fara ajiye su Asma'u ma sannan. Shiru kawai tai da mamakin wai ita yaran nan zasu yaudara, sai kawai tai ƙwafa ta yanke kiran. Ɗan jimm tai saboda abinda take jiyowa kamar ƙaƙarin amai, kamar zata share sai kuma ta miƙe da sauri jin abin na ƙaruwa. Sam batai tunanin Smart na gidan ba, ɗakin nasa ta shiga dan anan take jiyowa, nan ɗinne kuwa a cikin toilet, mamaki ya kamata duk da matsanancin haushinsa da take ji na abinda ya faru sai ta nufi bayin. Sosai gabanta ya faɗi, har bata ma san sanda ta afka bayin ba inda yake.
       “Lafiya kake kuwa?”.
   Bai iya bata amsa ba dan ya gama galabaita da aman, dole ta ajiye komai da ke ranta kuma ta shiga taimaka masa ya wanke bakinsa da fuska, da taimakonta ya fito ya sake hawa gadon ya kwanta.
            “Please lulluɓe ni”.
       Ya faɗa da ƙyar. Lulluɓe san tai hankalinta a tashe, dai-dai nan kiran Ahmad ya shigo wayarsa, har ya lumshe idanunsa ya buɗe, ita ya kalla yayinda ita kuma take kallon wayar. “Waye?”. Ya faɗa a hankali. Wayar ta miƙo masa da faɗin, “Besty kasa”. Sake maida idanun nasa yay ya lumshe da faɗin, “Ahmad ne ɗaga”. Kafin ta ɗaga ɗin wayar ta yanke, tana ƙoƙarin kira Ahmad ɗin ya sake kira. Ɗagawa tai ta saka a Hansfree da faɗin “Hello”. Daga can Ahmad ya amsa mata duk da yayi mamakin jin wayar a hannunta. Gaisheshi tai da sanar masa bai da lafiya.
         Hankali tashe Ahmad ya ce, “Ya ALLAH gani a ƙofar gate ai”.
   “Okay to bara ina zuwa”.
Tai maganar tana yanke kiran. Wayar ta ajiye ta miƙe, Smart da ke saurarensu ya buɗe idanunsa a kanta, a hankali ya furta “Please kar ki fita a haka kisa hijjab”. Harararsa tai batare da tace komai ba ta fice. Samun kanta tai da shiga ɗakinta ta ɗauka hijjab ɗin ta saka sannan taje ta buɗema Ahmad ɗin. Ita tai masa rakkiya har ɗakin Smart ɗin ta fito ta barsu.
         Bayan Ahmad yay masa sannu ya ce, “Tashi zakai mu tafi asibiti”.
Kai Smart ya girgiza masa yana ɗan buɗe idanunsa, “Basai naje asibiti ba zai bari da kansa in sha ALLAH. Tunda ma na samu nayi aman shike nan”.
      Ahmad ya riga da yasan miye matsalar Smart ɗin. Dan haka yay shiru kawai. Dai-dai nan Lulu ta shigo ɗakin da sallama. Amsa mata Ahmad yayi. Ta ajiye tray data haɗo abincin tana faɗin “Ya sanar maka abinda ke damun nasa kai ko?”. Murmushi Ahmad yay da bata amsa. “Kin san mutumin naki ai, yanzu ma fama nake da shi muje asibiti yaƙi”.
         Kallonta takai kan Smart, ganin shima ita yake kallo ƙasa-ƙasa saita janye nata da ɗan taɓe baki. Shi Ahmad ma sai suka bashi dariya. Dan haka ya miƙe. “Inaga bashi abincin ni bari naje na samo masa magani, dan tunda yace bazaije asibitin ba to bazai je ba”. Bai jira cewarta ba ya fice. Ɗan hararar Smart Lulu tayi, a taƙaice ta ce, “Ka tashi”. Sake buɗe idanun nasa yay ya zuba mata su na kusan minti ɗaya, ita kuma ta kauda nata dan tun ɗazun yanda idanun nasa launinsu ya sake canjawa suka fito a sak na macizan da take kiransu taji bata son ya kalleta. Hannu ya miƙa mata alamar ta kamashi. Kamar zata share sai kuma dai ta kama dan ya ɗan bata tausayi kuma. Harya faɗa kamar wanda ya kwana biyu yana ciwon. Shayin data haɗo masa ta miƙa masa, babu musu ya amsa tare da motsa lips ɗinsa kaɗan ya ce, “Thanks”. Koda ta miƙa masa soyayyan doyan sai ya girgiza mata kai alamar bazai ci ba. Kamar zatai magana sai kuma ta fasa ta maida doyar ta ajiye. Tana zaune ta ɗan juya masa baya tana latsa wayarta har ya kammala, kofin ya miƙa mata ya koma ya kwanta, ta tattare kayan ta fita da su, a lokacin kuma Ahmad ya dawo, ruwan da ya buƙata da Smart ɗin zai sha magani ta ɗakko masa, da ga haka ta koma falo tai zamanta...

      Ahmad bai bar gidan ba sai da Smart ya samu barci, bayan wucewarsa Lulu ta leƙasa, ganin yay barci ta ɗan sauke ajiyar zuciya da hararsa kamar yasan tanayi. Ɗakinta ta nufa ta ɗan kwanta itama dan shirun gidan kuma duk sai yay mata babu daɗi. Kusan a tare suka tashi bayan la'asar, tai wanka tai salla dan yanzu kam Alhamdullah, idan ma

Please Login or Register in order to submit comment