Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na gano ɗin ko yaya kace?”.
     “Shike nan, in dai kina ganin babu matsalar kije ɗin, dan nima dai hakan zai fi sama min kwanciyar hankali. Sannan dan ALLAH ki lallaɓa Yousuf ya bata wayoyinta dan mu dinga jinta akai-akai”.
          “Karka damu idan yazo anjima zan masa magana. Bari na kawo maka abincin kaci namaje na dawo da wuri kafin yazo gidan”.
    Kai ya gyaɗa mata, ita kuma ta tashi ta fice idanunta na cika da ƙwallar tausayinsa. Yayinda zuciyarta ke faman kai kawon anya kuwa mijin nata yana lafiya? Dan ita dai gaskiya a wannan gaɓar ta fara jin al'amarin nasa da girma, wanan wace irin makauniyar soyayya ce? Haka fa idonsa yay masifar rufewa akan mahaifiyar yarinyar nan a lokacin tamkar wanda baya a hayyacinsa. Anya kuwa basuyi kuskuren nutsuwar fahimtar al'amarin nan ba a bai-bai tun a shekarun baya? Kuɗi kam na iya canja mutum fiye da abinda Daddy yayi a kan Mawaddat, sai dai akan ƴarsa Mawaddat kuma fa? Idan ance soyayyar mahaifiyarta ce ta dawo kanta gaba ɗaya ai abin nasa na neman wuce makaɗi da rawa kuma, sannan ko sanda ya auri Mawaddat yanada abin hannunsa, bayan auren nata ne dai ya sake bunƙasa za'ace, gaskiya tana buƙatar yin dogon nazari a wannan karon fiye da wanda sukeyi a baya game da shi. Koda ta kawo masa abincin ma lallaɓashi tai tayi sai gashi yaci, ta sake lallaɓashi yay wanka ya kwanta dan yau kam babu alamar zaije office ma. Ita kuma ta shirya ta fice a gidan kamar gaske gidan Lulun zataje. Yo ita zata biye masa ne su zama ɗaya miya ja mata wannan abin kunyar. Gidan Uncle Yousuf tai tafiyarta, tai sa'ar samun shima yau ɗin bai fita office ba wai zai ɗan huta a gida.......

      ____________★

           Duk yanda Lulu taso lallaɓa Asma'u ta zauna hakan bai yiwu ba, dan ita dai Asma'u tasan wanene yayan nasu. Haƙuri tai ta bama Lulu akan ai zataje ta dawo kawo musu abincin rana. Amma yanzu idan bataji maganarsa ta tafi ba ya fito zai iya zane ta. Mamakin Lulu sai ya sake ninkuwa, irin wannan tsoronsa da suke ai abin yayi yawa. Amma idan yasan wata ai bai san wata ba. Sai tayi duk yanda zatai Asma'u ta dawo gidan nan da zama kafin cikar sati ukun da zatatai a cikinsa kodan ta tabbatar masa itama ɗin ba kanwar lasa bace. Da ga haka tabarta ta wuce. Kasancewar gidan shiru ita kuma bata son kaɗaici yana tayar mata da hankali ya sata miƙewa ta ɗan zazzagaya, duk da kasancewar gidan ƙarami sosai, dan ko sashen masu aikinsu ya fisa girma bai hana gidan birgeta ba. Balle ma an sake ƙawatashi da kayan da aka zuba mata, wanda har mamakin sakasu tayi ita da zatai zaman sati uku. Sai dai batace komai ba akan hakan. Ta ɗan jima a waje tana shan iska sai kuma ta koma ciki, bedroom ɗin ta, a ranta tana raya gara ta ɗan sha abubuwanta ta kwanta itama tai barci, sai dai me koda ta duba babu ledar maganin ma gaba ɗaya. Shiru tai alamar tunanin ko ta ajiyesu a wani waje ne, kai ina a bedside drawer ta barsu. Da sauri ta buɗe drawer ɗinsa amma babu alamar su, maganganunsa na ɗazun bayan zuwan su Asma'u ne suka shiga dawo mata, to ko ya fahimci abinda tai jiyan. “Wayyo ni” ta faɗa tana dafe kanta. Dama fa tayi matuƙar mamakin jin ya ɗakko topic ɗin nan, sai dai kafin tai masa tambayar da tai niyya ya fita ya barta. “Mutum nan maye ne, ya akai yay saurin ganoni” ta sake faɗa tana faɗawa saman gadon da jan tsaki. Bataso haka ba gaskiya, dan tana ganin ta samu hanya mai sauƙi da zata dinga samun abinda take so cikin sauƙi tana wasa da hankalinsa. “Mugun kai fal gadara da ƙauyanci sai shegen wayo kamar ɗan dila” ta sake faɗa cikin nuna takaici. Da ga haka tai shiru lamo abinda ya farun yanzu babu jimawa a tsakaninsu na sake dawo mata. Tsaki taja mai ƙarfin masifa ta sake juya kwanciyarta dan sam bata son tunawa, dan duk ƙaƙarin aman data dinga yi bayan barowarta ɗakin nasa batai ba, sai ɓigewa tai da yin brush kusan sau huɗu amma hakan bai hanata cigaba da jin saukar lips ɗin nasa a nata ba har yanzu. Tsaki taja tana tunzura bakin gaba. Da ga haka ALLAH ya taimakata barci ya kwasheta mai ƙarfi. Dan koba komai akwai gajiya da ƙarancin barcin na kwana biyu a tattare da ita.........✍️

         




_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥



*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲




  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗



           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻


𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 6️⃣5️⃣



........Cike da matuƙar ɗoki Asma'u ta isa gida, kusa da Ammah ta zauna da ke kallonta ganin yanda take ta faman washe haƙora. “Auta lafiya kuwa irin wannan washe baki haka ko suruki na samu?”. Adda Sa'adah ta faɗa cike da zolaya. Su Adda Suwaiba da ke ta shirin wucewa gidajensu suma dai duk idanu suka zubawa Asma'un. Dariyar ta sake faɗaɗawa tana ɓoye fuskarta a jikin Ammah da faɗin, “Kai Gwaggo nifa ba haka bane, zan faɗama Ammah albishir ne”.
“A to muma sai a faɗa duk muji ai”. Cewar Gwaggo Sa'adah. Asma'u dai na dariyarta ta ce, “Gwaggo dama fa zan sanarma Ammah ne matar Yaya itace lawyer ɗin da take so ɗin nan mai taimakon mutane musamman akan harkar fyaɗe”.
Kallonta Ammah tai da sauri, dan haka cike da zumuɗi Asma'u ta sake faɗin, “Wlhy Ammah da gaske nakeyi. Barrister Mawaddat Jiƙamshi ce matar Yaya, dama tun shekaran jiya nake ta mamaki dana ga kamanninsu yayi yawa duk da ban taɓa ganin waccan a zahiri ba sai a tv, sai banyi magana ba sai yau dana tabbatar”.
Wani irin abu ne mai sanyi ya shiga ratsa zuciyar Ammah ta shiga sake tsarkake sunan ALLAH maji roƙon bayinsa. Tun a randa ta fara ganin yarinyar nan ana hira da ita a gidan tv akan wani case data cimmawa na fyaɗe har yarinyar ta kamu da cuta mai karwa garkuwar jiki da wanda yay mata fyaɗen ya goga mata a ranta taji inama ace ɗiyarta ce ita, ko kuma Aliyu ya sameta a matsayin mata. A ranar tai addu'a da fatan idan hakan zai iya kasancewa kuma ya zama alkairi ALLAH ya tabbatar, idan kuma har matarsa ce. Amma da ga baya sai ta cire hakan a ranta sakamakon jin yarinyar ɗiyace ga babban hamshaƙin mai arziƙi nan Alhaji Isma'il Ibrahim Jiƙamshi. Ta cigaba da ƙaunarta kawai a ranta da mata fatan alkairi a rayuwa. Tuna wannan al'amari ya sakata jin ratsawar wannan al'amari mai sanyi har zuciyarta na harbawa da sauri-sauri, tabbas wannan shine ɗaya da ga cikin alkairan son mutum domin ALLAH, dan ita kam taso yarinyar nan domin ALLAH ne......


★★....

Tunda Mommy ta fara magana Uncle Yousuf ya zuba mata idanu kawai yana kallonta har sai da takai aya. Ta ƙare da faɗin, “Gaskiya Yousuf zuciyata ta fara raya min wani al'amari mai girma. Anya kuwa babu lauje cikin naɗi a wannan al'amarin. Kasan mu mata munada wani hali na rufewar ido a duk sanda muke son ganin buƙatarmu ta biya akan abinda muke so. Ka tuna randa marigayiya ta fara ganin Yaya kuna tare, kuma kaine da kanka ka sanar min tunda yay mata kallo ɗaya ya watsar da lamarinta har kuka baro gidan a wancan lokacin bai sake kulata ba”.
       “Tabbas anyi haka aunty Kareema, amma miya alaƙanta wannan abin kunyar da yake yi yanzu da wancan?”.
     “Ba zamuce sunada alaƙa ba, ba kuma zamuce basu da shi ba. Amma inaji a jikina wannan soyayyar mai zafi da yakema Mawaddat bata lafiya bace.”
          Murmushi Uncle Yousuf yay da gyara zamansa. Ya ce, “Aunty Kareema ban katseki ba ko ƙin fahimtarki anan, amma ina roƙonki karki sakama zuciyarki komai game da abinda Yaya keyi da tunanin wani. Lafiyarsa lau ya kuma san mi yake yi sarai. Akwai dai abinda yake ɓoyewa shiyyasa yake kaffa-kaffa da Mawaddat, dan ba wai tsantsar soyayyar bace ba kawai. Abu na biyu tausayin rasa mahaifiyarta tana laɓuɓuwa ma ya taka rawar gani a kansa. Kin san mu maza munada wani abu akan ƴaƴan mu musamman idan ya kasance mahaifiyar yaro bama tare da su, sai mu dinga jin wadda ke riƙe da su zata cuta musu ne kawai. Shiyyasa zakiga maza da yawa suna samun saɓani da matansu akan ƴaƴan da uwarsu ta fita a gida, kota rasu ta bari.”
        “To haka ɗinne kuma. Amma inaga ya kamata ace munsan abinda yake ɓoye manan ko hakan zaisa mu fahimcesa”.
     “Karki damu zamu sani, lokacin mu sani ɗinne dama baiyi ba, ina kan bincike yanzu haka ma”.
     “To Alhamdullah ALLAH yasa muji alkairi.”
      Da Amin ya amsa mata, da ga haka suka cigaba da tattauna al'amarin Daddy ɗin har zuwa wani lokaci kafin tai musu sallama ta koma gida. Ta samu Daddy na ramuwar barci da ya gagara yi daren jiya, bata tashesa ba har sai da ya tashi da kansa sannan ta labarta masa abinda ya sakasa nutsuwa kamar yanda suka tsara da Uncle Yousuf. Murmushi yay da faɗin, “Ashe yaron nan nada hankali har haka”.
      Dariya Mommy tayi kawai batace komai ba. Shima sai bai sake bi takanta ba ya tashi ya shige bayi fuskarsa ƙawace da murmushi...

     __________★

        Gab da Azhar Smart ya tashi a barcin da yay, yaji daɗin yin barcin kuwa sosai, dan haka ya watsa ruwa da ɗaura alwala yasa jallabiya ya fice massalaci batare daya nema Lulu ba. Sai da aka idar da salla ya dawo gidan sannan ya nufi ɗakinta. Baccinta take hankali kwance, beauty face ɗinta ta sake yin wani fayau kasancewar babu ɗigon kwalliya, hatta lips ɗin ma yanzu babu ko lipgloss ɗin a jikinsa. Samun kasan yay da tsira mata idanun nasa na tsawon mintuna, tabbas ita ɗin ƙyaƙyƙyawace, sannan tana cikin jerin mata masu tsananin kula da jikinsu ta hanyar gyarashi kwaf-kwaf a kowane motsi. Ga izza da gayu da duk wani cikakken namiji bai isa mata kallo ɗaya ya ɗauke kansa ba, “Sai dai akwai kauɗi da masifa kuma ba” ya faɗa a fili yana ɗan taɓe baki da ƙarasawa gaban gadon ya tadata. Idanunta ta buɗe a hankali ta saukesu kansa. Yanda ya ɗan ranƙwafo kanta ya sata zabura, dan yanayin ya mata kamar wani abu da ya shuɗe a baya. Tashi yay shima tsaye da kyau yana girgiza kansa. Fuska ba wasa ya ce, “Tashi kiyi sallah”.
      Harararsa tai kamar zatai magana sai kuma ta fasa saboda yanda yay masifar kafeta da idanunsan nan da bata ƙaunar ya zuba mata su, dan duk wani ƙarfin gwiwar ta sai ya sare taji komai ya kufce mata. Dama fitsari take ji dan haka ta sauka a gadon tana wani yamutse fuska ta nufi bathroom ɗin. Sai da ya bata ɗan lokaci sannan yabi bayanta, anyi sa'a kuwa zata fara alwala.
        “To alwalan ma a gabanka zanyi?”.
     “Haka ya kamata, ya kuma dace, dan hakki ne a kaina sanin ibadarki da komai naki a yanzun”.
             “Kai a wa?”.
        “Mijinki”.
     “Kana son shigarmin rayuwa da yawa”.
“A ciki nake tsunduma ma ai”
   “Mafarki kenan”.
“Ni da ke duk a ciki muke, mai rabo a cikinmu sai ya fara farkawa ya fuskanci reality. Yi alwala lokaci na tafiya”.
        “Al....”
    Sai kuma ta kasa ƙarasawa saboda tuno abinda ya faru ɗazu a ɗakinsa saboda faɗar sunan nasa. Sai kawai ta ɓige da maka masa harara cikin ƙunƙuni ta furta “Zan koya maka hankali sannu-sannu”.
       Duk da yaji bai tanka ba, dan ya gaji da magana haka nan. Itama sai tai ƙwafa ta juya ta fara alwala. Shi dai yana kallonta harta kammala zata miƙe ya ce, “Dakata. Mawaddat ba haka ake alwala ba sam. Akwai kura-kurai matuƙa a cikin wadda kikayi. Dan haka ina son ki bani hankalinki nan duk abinda nayi kiyi, yanda ake alwala shine. Da farko yin niyya a zuci sannan ki ce Bismillahi, sannan ki wanke tafukanki na dama da na hagu kowanne sau uku. Sannan ki ɗebo ruwa ki kurkure bakinki ki zubar da ruwan sau uku. Sannan ki ɗebo ruwa ki shaka a hanci ki fatar shi ma sau uku. Sannan ki ɗebo ruwa ki wanke fuskarka gaba ɗayanta sau uku, ki lura cewa wanke fuska yana farawa ne tun daga farkon goshinki har izuwa karkashin haɓarki, wato kusa da makoshi a tsayinta kenan, a faɗi kuma tun daga gefen kunnen dama zuwa gefen kunnen hagu. Sannan ki wanke hannu tun daga tafuka har zuwa gwiwar hannu na dama da na hagu shima sau uku. Sannan ki ɗebo ruwa ki yi shafar kai wato a tafin hannu ki shafo tun daga farkon goshi har ki kai ƙeya sannan ki sake dawowa farkon goshi. Sannan shafar fatar kunnuwa na dama da na hagu. Sannan ki wanke ƙafafu na dama da na hagu tun daga tafin ƙafa har izuwa gwiwar ƙafa. Ina fatan kin fahimta, amma zan fara sai kiyi duk yanda zanyi”.
         Batace komai ba, sannan bata nuna zata ƙiyi ba. Dan ita dai tun maganarsa ta ɗazun akan mahaifiyar ta ya matuƙar sanyaya mata jiki, tsaf ta dingayin yanda yake yi har suka kammala, har cikin ransa yaji daɗin rashin gardamarta a wannan gaɓar. Dan haka ya ɗora da faɗin, “Akwai addu'a bayan kammala al'wala. Zan koya miki ita bata da wahala bata kuma da tsaho, sai dai ba yanzu ba sai na kammala shirina akan hakan. Muje kiyi sallarki”.
        Komai batace masa ba yanzu ma tai wucewarta ta fita shi kuma yabi bayanta yana jin wani kaso na takaicin abinda ya faru daren jiya akan sayen magani na raguwar masa a zuciya. “Yanzu bamu da isashen lokacin da zan miki filla-filla akan yanda ake salla, amma zan nuna miki kaɗan a ciki kafin mu fara karatu na musamman akanta.” bai damu data amsa ba ya shiga nuna mata da faɗa mata abinda zata iya fahimtarsa a yanzun, nan ma dai batace komai ɗin ba har ya kammala ya bata izinin kabbara sallarta. Da ga haka ya samu waje ya zauna yana kallonta har ta idar. Ya dubeta zaiyi magana game da addu'a ganin har ta miƙe da ga sallamewa kira ya shigo wayarsa. Ahmad ne, dan haka ya ɗaga yana kaiwa kunne. Shaƙiyanci sosai Ahmad ke masa da ga can, har sai da ya sashi furta, “Ɗan sa ido ina ruwanka to. Kai ni karma kazo min gida ka tsaya nan nazo na sameka mu tafi”. Ƙaramar dariyar da ta saka Lulu kallonsa yayi kaɗan saboda jin abinda Ahmad ya faɗa da ga can. Sai kuma shima Smart ɗin da ya miƙe zai fice taji yana furta, “Irinku ne masu takurama sabbin aure da zarya har sai an cinye kayan gara da k....” daga haka ya fice bata ƙarasa ji ba. Baki ta taɓe kaɗan da ajiye sallayar tana sauke ajiyar zuciya da bata san dalili ba, da ga haka ta ajiye batunsa tai zaman dirshen a kan gado ranta fal tunanin cases ɗin dake gabanta. Dole ne ma gobe idan ALLAH ya kaimu ta fita office, kwana kusan tara yau fashin yayi yawa ai haba. Bata sake jin motsin Smart ba har sai da Mubarak ya kawo abincin rana. Lokacinne ya shigo ɗakin cikin shirinsa da alama fita zaiyi dan yaci wani faran shadda ƙal harda hula baƙa, ƙamshi yake mai sanyi ya fito a angonsa dai kai tsaye. Da ga bakin ƙofa ya dakata yana faɗin, “Ga lunch can an kawo ni zan fita su Ahmad na jirana”.
         Baki ta taɓe kawai batare da tace komai ba. Shima sai bai sake cewa koman ba ya juya yay ficewarsa dan ya fahimci ƴan izza da masifar ne yanzu a kanta. Shi kuma bashi da wani isashen lokacin biye mata a yanzun..........✍️

         


_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥



*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲




  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗



           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻


𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 6️⃣6️⃣



........Ya samu su Ahmad na jiransa a ƙofar gida shi da wani cousin brother ɗinsa babban fan ɗin Smart akan ball, da yake kusan sa'ansu ne shima sai suke zumunci sosai duk da shi Smart ɗin yana jajja baya kamar yanda halayyarsa take na rashin sakewa da mutane. Ko Faisal yayi fushi sai kuma ya dawo dan matuƙa Smart ke burgesa a filin ƙwallo, damma ƙaddara ta hana komai gudu ai da yasan yanzu Smart na cikin manyan ƴan ƙwallo da Nigeria ke alfahari da su. Sun gaisa tare da zolayarsa irin na abokai musamman ma Ahmad da ya tasashi gaba sosai kafin su wuce Smart na roƙama Ahmad shiriya. Gidan Daddy suka fara zuwa. Inda suka sami tarba ta musamman da ga Mommy da su twins da basu koma ba. Bayan sun gaisa da Mommy sukai godiya tai musu iso falon Daddy da ya riga yasan da zuwansu. Ya ɗan sake musu fuska harda jansu da hira duk da sunata faman sinne kai musamman ma Smart. Dan koda aka kawo musu abin sha da ruwa da kayan motsa baki Faisal da Ahmad ne kawai suka sha ruwa. Shiko babu abinda ya taɓa. Wasa-wasa sun share kusan awa ɗaya da rabi kafin su baro gidan da wasu kayayyakin Lulu da Mommy ta saka Mubeen kai musu akan sai zuwa gobe idan ALLAH ya kimu za'a kai mata sauran kayan. Da ga nan gidan Uncle Yousuf suka nufa. Anan ɗin ma dai tarba suka samu ta girmamawa ga Aunty Saliha. Uncle Yousuf kuwa babu ruwansa zama yay cikinsu tamkar aboki tunda su duka ukun babu baƙonsa, gara garama Smart ɗin, amma su Ahmad ai tun suna dajinen majina ya sansu. Anan ma sun jima dan har sai da aka kira sallar la'asar sannan suka fito tare da Uncle Yousuf ɗin zuwa massalaci. Bayan sun dawo basu shiga ciki ba sai mota tunda dama sunyi sallama da Aunty Saliha. Anan ma dai an bada wasu kayan Lulu da wayoyinta da laptop da Uncle Yousuf ya amshe. Bayan sun baro nan Smart yace ma Ahmad yana son zaije yaga Malam tunda zuwa gidan Baba da sukai niyya ya rushe sakamakon sanar dasu Baba yayi tafiya Legos da Uncle Yousuf yayi. Ahmad yace babu damuwa. Sun nufi Yakasai wajen Malam Nasirudden. Sunyi sa'ar samunsa kuwa a gida bai fita ba. Bayan sun gaisa Ahmad ya janyo Faisal cikin dabara suka fito suka bar Smart tare da malam ɗin.
          Malam Nasirudden da ya fahimci akwai magana ya dubi Smart cikin murmushi da kulawa ya ce, “Idon Aliyu ango ne haka a waje, kai da ya kamata ace kana can gida sai bayan wata ɗaya ka fito”.
       Murmushi mai bayyana hakwara Smart ya saki a karo na farko, cikin sinne kai ya ce, “ALLAH ya gafarta malam idan hakan ta kasance ai kwa zaneni matsayinku na iyaye”. Dariya shima malam yayi da faɗin, “Ina ai idan hakan ta faru mun san lafiya ce ta ɓoye ka ai Malam Aliyu. Ya amarya da gajiyar biki?”.
            “Alhamdullah Malam”.
       “To Masha ALLAH, ince dai ba jikin bane ba ko?”.
“A'a malam jiki kam Alhmdllh, dan duk yau banji ciwon kan nan ba. Wani abu ne mai muhimmanci ya kawo ni dan ina buƙatar ƙarin haske da shawara”.
     “To Alhmdllh ALLAH ya ƙara lafiya mai albarka. Ina saurarenka mike tafe da kai?”.
    Zama Smart ya gyara yana sauke ajiyar zuciya da furzar da iskar bakinsa. “Malam akan ita matar tawa ne nake neman shawara. Kasan yanda al'amuran rayuwar nan suke tafiya a wannan lokaci musamman tarbiyya da ke neman zama wani babban ginshiƙi mai wahalar aiwatarwa ga iyaye ko riƙewa ga mu ƴaƴan, wasu zakaga iyayen nata iya bakin ƙoƙarinsu amma sai su fuskanci jarabawa a cikin ƴaƴan wasu su fanɗare, ko kaga tun fil'azal iyayen ne ma basu bi hanyoyin isar da tarbiyyar yanda ya kamata ba saboda soyayyar yaran. Wannan matsalar tana matuƙar tasiri akan addini da wasu ɗabi'un da takai a yanzu hatta ɗiyanmu mata na shaye-shayen abubuwan mayen nan a cikin gidajen iyayensu ko a gidan aure. Wasu sanadin abokai, wasu samari, wasu kuwa wani daliline kan jasu zuwa hakan. Karna jaka da nisa, ita matar tawa ta tsinta kanta a irin wannan halinne, sannan ba shaye-shaye ne kawai matsalar ba, hatta a ɓangaren ibada tana da matuƙar raunin da zan iya cemaka komai ma bata sani ba, saboda koda tasan wani to babban dalilai ya shafesu da ɓoye abinda ta sani ɗin. Kaina gaba ɗaya a cikinkushe yake yinin yau ka bani shawara dan ALLAH, dan ko mahaifana bana son su fuskanci wannan matsalar game da ita balle sauran ahalina saboda bana son mutuncinta ya samu rauni ko yaya a zukatansu”.
        Numfashi mai nauyi Malam ya sauke yana mai jinjina kansa. “Tabbas kai ɗan halak ne Aliyu, sannan ka matuƙar birgeni na kuma sake ganin kimarka a cikin idanuna. Domin ba kowa ALLAH ke azurtawa da irin zuciyarka ba a wannan ƙarnin. A koda yaushe, a ko wane irin kuskure mutanenmu sukan dubi mai wannan akin abin ƙyama, abin hantara, abin gudu, abin zinɗe, abin shune, a tunaninsu suma wayonsu ne ya hanesu da aikatawar ko ya hani nasu zuri'ar. Muna mantawa itafa rayuwar tamu gaba ɗayanta ma jarabawace, ba kuma lallai ne abinda ya kasance jarabawar waninka kai ya kasance taka ba. A duk sanda kaga gazawa ga wanin ka ba dandalin gulmarsa ya dace ka buɗe ba, da zunɗensa ko shunensa ya dace kayi ba idan zai gifta, ba ƙyamatarsa ya dace kayi ba ko hantara. Nema masa shiriyar UBANGIJI ya cancanta da tausasa masa a duk lokacin da rayuwarsa ta raɓi taka ko wani dalili. Wlhy Aliyu mutane da yawa sukan kasa gane cewar bakunansu ko ayyukansu ke jefa musu ƴaƴa cikin wata musifar. Zakaga kana iya bakin ƙoƙarin ka akan tarbiyyar yaranka, ALLAH kuma ya baka su nutsatstsu da ilimi yanda ya kamata, amma dare ɗaya yaro ya canja alƙiblarsa ka rasa daga ina matsalar take. Matsalar tana a tare da kai, bakinka shine matsalarka, ayyukanka sune matsalarka. Ɗan wancan dake famɗare ya gitta ka zunɗeshi da bama abokan zamanka labarin ai wancan yaron da kuke gani gagararrene, watsatstsene fanɗararre, baida aiki sai shaye-shaye, baida aiki sai bin ɗiyan mutane, baida aiki sai ɗauke-ɗauke. Ciki ta zubar babu adadi bar ganinta a cikin hijjab ɗin can karuwar gida ce, jibi yarinyar can babu abinda ta iya sai shigar banza, ta kwaile fata da bilicin ƴar isaka tafi ƙarfin iyayenta. Laifin uwarne ko ubanne basu bashi ko bata tarbiyya ba..... Waya gaya maka tsaiwarka akan tarbiyyar yaro ce kawai ke tsare maka shi ɗan uwana ko ƴar uwata? Muna mantawa akwai jarabawa, muna mantawa akwai ƙaddara, muna mantawa ƙyaƙyƙyawan furucinmu ga ɗiyan wasu kanyi tasiri ga namu ɗiyan, mummuna kanyi tasiri ga namu ɗiyan suma. A duk fa lokacin da ka ambaci ALLAH yayima wane albarka, ya shiryar da shi, sai kaima mala'iku suce Amin tare da kai da zuri'arka baki ɗaya. Idan kace ALLAH ya wadaran wane fanɗararre taƙadari ɗan iska, sai mala'iku su amsa da Amin tare da kai da zuri'arka baki ɗaya. To

Please Login or Register in order to submit comment