Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ko tayi sallar isha'i, ya kuma duba ko zazzaɓin ya sauka. Sai dai me, yana taɓa ƙofar ya jita a kulle. Shiru yay yana kallon hannunsa da ke saman handle ɗin, sai kuma ya ɗage kafaɗunsa alamar ko oho ya juya ɗakin da ya fito yay kwanciyarsa dan barci yake ji matuƙa. Dan shi a tunaninsa ko Lulun tayi hakanne dan kar ya nema wani abu a gareta.....

       _WASHE GARI_ koda ya tashi sallar asuba sai da ya ƙwanƙwasa mata ƙofa, ganin zai makara saboda ya tashi shima a ƙurarren lokaci ya sashi ƙyaleta ya wuce. Ana idar da sallar ya dawo gidan, ɗakin nata dai ya sake nufa ya ƙara knocking. Lulu da ke kwance a ƙasa ta buɗe idanunta da sukai matuƙar nauyi da ƙyar ta iya miƙewa cikin takaicin damunta da ake tun ɗazun ta nufi ƙofar ta buɗe, dan ta manta ma a ina take, dai da ta ɗan jingina da ƙofar na wani ƴan sakanni sannan ta murɗa key ɗin ta buɗe kaɗan. Da farko bai niyyar shigowa ba, dan haka yace da ita, “Kin tashi kinyi salla ne?”.
          “Zanyi”.
      Ta amsa masa cikin yanayin muryar maye da tura ƙofar zata rufe dan abun bai gama sakinta ba. Da sauri ya riƙe ƙofar gabansa na faɗuwa, bata da wani isashen ƙarfin dan haka ya samu nasarar shigowa. Yanda ya kafeta da idanunsa da suka kaɗa sukai ja a ƙanƙanin lokaci ya sata zabga masa harara itama da nata dake a juye ta bar masa wajen cikin ɗan tangaɗi na rashin ƙarfi ta je ta faɗa saman gadon a rufda ciki gashinta dake a hargitse ya lulluɓe fuskar tata gaba ɗaya. (Ina ta samu abinda tasha?) Zuciyar sa keta kaikawo wajen son hasasowa amma iya hasashen ya auna a ɗan tsukun lokacin baro gidansu zuwa nan hakan bamai yiwuwa bane, sai dai idan dama tana tare da abunta. Inda take ya ƙarasa ya ɗauki handbag ɗin ta gaba ɗayanta ya zazzage a saman gadon. Babu komai a ciki daya danganci ƙwaya, jakkar ya ajiye cikin furzar da iska sai idanunsa suka sauka kan ledar maganin jiya daya sayo mata, jawo ledar yay ya fiddo maganin, an ƙara ɗiba kusan shida a ciki, ya tsirama maganin ido kallon da yaron pharmacy ɗin ya dinga masa lokacin da ya bashi takardar na dawo masa a rai da zuciya. Tabbas wannan maganin tasha. Kallonsa ya maida gareta ya zuba mata idanu kawai maƙogwaronsa na kai kawo a cikin wuyarsa da ɗan sauri-sauri. Da ga ƙarshe ma sai ya tashi ya fice da ga ɗakin kawai.....

     ____________________★

           Cikin ɓacin rai yake dubansa ganin yanda yake neman haukata kansa. Gaba ɗaya kwanakin nan baida wani aiki sai shaye-shaye tunda ya baro Kano. Ƴar ƙaramar robar giya da ke a hannunsa ya fisge cikin masifa. “Wai mi kake son maida kanka ne kai kuwa MM? Akan mace! Ka zauna ka susuta rayuwarka. Tunda ka dawo da ga kano an kasa gane kanka, ka bar zuwa aiki ka barma fita a gidan nan gaba ɗaya sai shaye-shaye, kana ganin hakan da kake shine zai baka damar samunta? Yarinya sai kace wata autar mata ko hurul-ayni Mtsowww!!!”.
        Murmushin takaici MM Atik ya saki sai kuma ga hawaye sharrrr. Ya miƙa hannu zai amshi ƴar robar giyarsa da abokin nasa ya karɓe amma sai ya hanashi. Lips ɗin sa ya ciza da ƙarfi da faɗin, “Bazaka gane ba Asim, duk yanda zan faɗa maka bazaka gane ba. Aure fa sukai mata, aure da wani bani ba. Idan ban mallaketa ba zan iya rasa raina, ina matuƙar sonta da buƙatarta Asim, wlhy da gaske nake ina sonta da gaba ɗaya zuciyata..”
        “A haba gyara dai zancenka my man, kana dai sha'awarta. Kai har kasan wata soyayya ne. Ni yanzu Indai dan batun yarinyar nan ne ka nutsu dan ALLAH ka dawo hayyacinka. Ba igiyar aure ba ko ɗaurin kabari sukai mata namaka alƙawarin sai ta dawo taka...”
   Wani irin zuba masa ido MM Atik yayi, sai kuma yay murmushi da lumshe idanunsa ya buɗe a lokaci guda, “Asim karka yaudari kanka nima ka yaudarani. Kasan minene aure a ƙasar hausa kuwa?....”
       “Mtsoww kafin wannan zamanin yake wani abu a ƙasar hausar, amma a yanzu bana jin wasu matan na tuna matsayin auren, dan ajiyesa suke su shigo barikin ko ƴammatan basu kaisu iskanci ba. Balle ma ita munada hanyoyi kala-kala na kamata a tafin hannunmu. Ko an faɗa maka wani son auren take, to nayi bincike mai zurfi na gane komai har ma yanda aka ƙulla auran. Kai dai kawai ka dawo a hayyacinka kasha labari”. Ya ƙare maganar yana tattare sauran kwalaben giya da su cigarette da shisha da MM Atik ɗin ya baza, sannan ya zo ya kamashi ya kai toilet yasa a ƙarƙashin shower ya sakar masa ruwa. “Malam yi wanka ka cire wannan dattin sai warin hayaƙi kakeyi”. Daga haka ya fice ya barsa.

         _____________★

     Da mamaki Ammah ke kallon Umma da ke faman murmushi riƙe da basket irin na saƙar kaba ɗin nan mai ƙyau shaƙe da kulolin kayan abinci wai karin kumallo ta shirya za'a kai gidan Smart. Umma data fahimci Ammah zata iya bata matsalafa sai ta sake faɗaɗa fara'arta da katse mata tunani da faɗin, “To kodai banyi dai-dai bane Hafsatu? Dama dai ganin haka akeyi a gidan washe garin da yaro ya tare da matarsa shiyyasa, kuma kinga dai ai ba'a barki da haɗa  abinci ba duk gamu cike da gida ko, sai dai kuma naga kamar hakan bai miki ba”.
      Murmushi Ammah tayi da ɗan girgiza kanta. Cikin nutsuwar nan tata ta ce, “Ko ɗaya ba haka bane Umman Nasiba, naga kawai an sakaki aiki ne tunda safen nan....”
    Caraf Umma ta amshe da faɗin, “Yo minene ALLAH na tuba. Ai an riga an zama ɗaya. Hydar a gidan nan kuma ai ya cancanci fiye da haka. Shi kaɗaine yaron da bai gajiyawa wajen binka har cikin ɗaki ya gaisheka kullum kuma cikin girmamawa da mutuntawa. Bari kiga Huwaila ta miƙa musu tunda tace zata gane gidan lokaci na ƙara ja”.
          Murmushin ƙarfin hali kawai Ammah ta saki da faɗin, “To ALLAH ya saka da alkairi”.
    Umma ta amsa da “Amin”. tana ficewa
       “Anya wannan al'amarin Hafsatu ba akwai wata a ƙasa ba. Matar da tunda aka fara bikin nan ta kasa ɓoye hassadarta ce zata girka abinci akaima Babangida kuma a barta?”. Addah Rukayya ce mai maganar cikin jimantawa. Kafin Ammah tace wani abu Gwaggo Sa'adah ta fito a ɗaki ita da Addah Suwaiba. Har rige-rigen faɗin, “Wannan yaudara ce akwai wata a ƙasa” suke su biyun. Adda Suwaiba ta cigaba da faɗin, “Babu ma wani batun ai mata kawaici magana ta gaskiya fa, kawai a dakatar da su ba ga Hawwah can na musu girkin ba shi kuma ai yaya da shi?. Matar da bata taɓa ƙaunarki ba tun da jajayen sawu sai yanzu ne zata ƙaunaceki Hafsatu, ai daga ji ma kasan akwai ƙulunboton data shiryama abincin. Ita idan yaran nata sunyi auren barinku take ku girka abinci ku aika musu ko sai ke, naga Yalwati ma ta aurar da yara maza har uku a gidan nan ai batai mata hakan ba dan tasan bama yarda zatai ba sai ke sarkin kawaici”.
         “Addah ni a ganina ku barta, idan ma wani sharrin take nufi ai ALLAH bazai bata nasara ba. Ballema ni sai nakega kawai dai tayi hakane saboda tujarar da malam yay mata jiya da dare”.
     Gwaggo Sa'adah ta ce, “Humm Addah kenan. Yau ya fara mata tujara ne da har hakan zai sakata saduda. ALLAH ki yarda ke dai akwai wani abu a ƙasan kawai. Bakuma zamu gane hakan ba sai anje ankai musu abincin sun cutu mudawo muna dana sani”.
        Duk da zuciyar Ammah ta sake raunana sai bata iya sake cewa komai ba, sai ƴan uwan natane ke cigaba da tattaunawa dan na cikin ɗaki ma duk sun fito. Gwaggo Sa'adah ce ta nufi kitchen inda Hawwah ke girka karin kumalon da za'a kai gidan Smart. Cikin sa'a ta iske ta kammala tana kan zubawa ne. “Yauwa kin haɗa ne Hauwa'u?”.
      “Eh Gwaggo” cewar Hawwah. Gwaggo Sa'adah ta ce, “Yauwa to sannu, bara na turo su Asma'un suyi su tafi rana nayi”. Da ga haka ta juya ta koma. Ƙwafa Umma dake leƙarsu ta window tayi, jitake kamar ta fito ta shaƙe wuyar Gwaggo Sa'adah. Oho dai tata ƴar aiken ai harta wuce. Kafin kuma su isa ta tabbatar Hydar da matarsa sunci nata abincin. Tai wata ƴar dariyar gatsa-tsa tana barin window ɗin har ɗiyarta Ismaha na kallonta. Amma sai ta basar dan tasan wacece Ismaha da ɗan banzan jan wa'azin tsiya.........✍️

         




_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥



*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲




  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗



           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻


𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 6️⃣1️⃣


........Ƙarfe kusan tara Lulu ta tashi da ƙyar a dalilin kaɗawar alerm ɗin ƙaramin agogon da ke a side drawer ɗinta da ya gallabeta tun takwas. Amma nauyin da jikinta yay mata yasata kasa kasheshi ko ta tashi har zuwa yanzu da ya sake buga taran. Ƙaramin tsaki taja da ɗan kai hannu tana lalube, sai dai sam babu ma alamarsa kusa da itan. Tamkar wadda aka ƙwalama kira sai kuma ta miƙe zumbur, yau fa ya kamata ta shigar da case ɗin mijin matar can court, dama tai alƙawarin sai ya kwana bakwai a police station su Shu'aibu sunci mata ubansa gwargwadon iko sannan, yau kuma kwana bakwan cif. Wayoyinta ta shiga nema, sai kuma ta tuna sunafa hannun Uncle You nan kuma gidan da aka kawota jiya ne. Ƙaramin tsoki taja da dafe kanta da yay mata matuƙar nauyi, dole ta sakko a gadon cikin ɗan tangaɗi kaɗan sai dai bana mayen bane na nauyin jikine dan abinda tasha ɗin sun saketa sai abinda ba'a rasa ba. Bayi ta shiga ta tsaya ƙarƙashin shower batare data cire komai ba daga jikinta ruwa ya fara sauka mata a haka. Ajiyar zuciya ta dinga saki a jajjere, sai da ruwan yay mata sharkaf ta gamsu ta ƙara komawa garau da take buƙata sannan ta fara zame kayan jikin nata ta fara wanka. Tana kammalawa ta jefa kayan a injin wanki dan komai na ƴar gata an ajiye mata shi, sai da ta gamsu sun wankun sannan ta ciresu ta maida indai zai busar. Sai ga kaya ras ta fitar sannan ta fito. Tana buƙatar waya domin kiran Zainab sakatariyarta da kuma su Shu'aibu ɗan sanda, dan haka ta fito da ga bedroom ɗin nata daga ita sai rigar wanka da towel ɗin data naɗe gashinta da take son ruwan data jiƙashi da shi ya naɗe. Sautin muryarsa yana raira karatun Alkur'ani cikin suratul An'aam daya karaɗe corridor ɗin ya sata gane yana a ɗakin dake kusa da wanda take. Sai da ta sake gyara yanayinta dan karma ya kawo mata wani raini sannan ta murɗa handle ɗin ƙofar ta shiga kanta tsaye ba batun neman izini, sallama ma sai da ta gama shiga tayita ciki-ciki. Ƙamshin shower gal dana haɗin turarrukan wankan da masu gyara mata jiki suka shirya mata na musamman ne ya fargar da shi shigowar ta, dan cikin abinda baifi sakans ba ɗakin ya gauraye da masifaffen ƙamshinta. Kasancewar yazo inda ya kamata ya tsaya ya sashi rufe Alkur'ani ya ɗago ya kalleta. Kanta ta ɗauke daga kallon da take masa, shima sai ya janye nasa idanun yana ajiye Alkur'anin. Cikin izzar nan tata da gadara ta ce, “Ɗan bani aron phone ɗinka na kira Uncle You ya bada nawa a kawo min”.
       “Kinyi salla?”.
    Ya faɗa maimakon amsa mata abinda tazo nema. A yamutse tana balla masa harara ta ce, “Ina ruwanka. Ka bani aron waya idan zaka bani”.
      “Idan kina buƙatar waya kije kiyi salla. Shin ke bakiji kunya ba a wannan shekarun naki ace sai an tuna miki abinda zai kusantaki da UBANGIJINKI, banbanci kafiri da musulmi shine sallah, duk wanda yabar salla baida maraba da kafiri, sannan duk wanda yabar salla zai iya aikata kowanne irin mummunan aiki, salla itace abinda za'a fara bincika mana a cikin ayyukanmu ranar sakamako, yin salla akan lokaci na ma masifu katanga da samunmu. Salla na ƙaramana kwarjini a idon al'umma da cikar kamala. Taya mai barinta zai samu waɗan can tagomashin dana lissafa wanda kaɗanne da ga cikin nasarorin da mai salla ke samu. Yinta zai baki damar yima mahaifiyarki addu'a da nemar mata rahamar UBANGIJI, sai ruhinta ya kasance cikin sallama tai alfahari da haihuwarki da jin bata bar bayan a banza ba. Mawaddat babu ruwan mutuwa da yanzu kika fara rayuwa, tana ɗaukar ɗan cikin ciki ma tabar uwa, alokacin da kike jin ke kin fara rayuwa wani ma a ranar aka samar da cikinsa. Ki dawo cikin hankalinki ki koyi darasi a duniya ba sai duniya ta shirya koya miki ba. Dan ita ɗayan biyu ce. Ko ka koya a yayin da take koyar da waninka, kota koyar da kai a lokacin da guri ya ƙure maka. Zaɓi ya rage naki”.
     Da ga haka ya tura mata wayar ya miƙe yay wucewarsa toilet. Harara kawai ta bisa da shi ƙasa-ƙasa. Dan gaba ɗaya jitai kamar an danne mata baki a sanda yake maganar. Bakin ta taɓe da matsawa ta ɗauka wayar tasa ta fice abinta. Sai dai tana komawa ɗakin nata ta zauna a bakin gado da nufin kiran Uncle Yousuf hakan ya gagara. Maganganunsa ne suka shiga dawo mata, musamman akan yima mahaifiyarta addu'a kuma zatai farin ciki da ita daya faɗa, samun kanta tai da kiƙewa zumbur ta nufi toilet, babu jimawa sai gata ta fito da alamar alwalar tayi. Wardrobe ta buɗe ta ciro abaya ta saka tare da naɗa gyalenta a kanta ta kabbara sallar.. dai dai nan ya shigo ɗakin shima, dan haka kawai zuciyarsa ta kasa nutsuwa harya fara cire kaya zai yi wanka ya fasa ya biyota dan yaga zatayi sallar. Karo na farko zuciyarsa ta tsarga ganin yanda take salla babu wani bin ƙa'idojinta yanda ya kamata. (Tofa wata sabuwa) ya ayyana a zuciyarsa da ɗunbin takaici. Ashe dole abubuwa suke rikicema yarinyar nan dan babu nutsuwa ko nagarta a cikin al'amarin ibadarta. Tabbas rashin tsaida ibada tamkar wani dafin allura ce a jikin ɗan adam mai karya masa garkuwar nagarta da ɗaurasa akan laifuka. Ashe al'amarin nata ya gawurta da yawa har haka. Zafin rai da takaicin iyayenta ya sake mamaye masa zuciya, domin fa in har ɓera da sata to a bincika itama daddawa nada wari. Shin mi mahaifinta da matar babanta dama Uncle Yousuf keyi haka har balagaggiyar yarinya mai shekaru da yake da tabbacin sun haura ashiri amma bata iya salla ba? Amma a ilimin boko da anyi magana zata iya bugar ƙirji ta kira kanta mai ilimi. Oh ALLAH a wane irin zamani muka tsinta kammu da tarbiyya ke neman kufcewa iyaye saboda soyayyar ƴaƴansu?. Wannan al'amari ya tayar masa da hankali matuƙa, ya tuna lokacin suna yara, idan lokacin salla yay sukaƙi barin wasa suje suyi sai dai kaji saukar tazbahar Ammah a jikinka kawai. Idan ko bakayi ba ranar ko kulaka batayi sai tace ita bazatai magana da wanda yafi son shiga wuta ba. Amma yau sai ga shi wadda ke amsa sunan matarsa bata iya salla ba. A hankali ya jingina da ƙofar yana mai harɗe hannayensa a ƙirji da lumshe idanunsa abubuwa masu yawa na masa kaikawo a zuciya, lallai akwai aiki, dan yaƙine babba garesa akan yarinyar nan, shi duk ma sai yaji tausayinta ya ƙara kamashi..
       A ɓangaren Lulu tunda ta idar idanunta ya sauka akan Smart kamar wani mayan ƙarfe. Sai da taji gabanta ya faɗi musamman da abinda ya faru jiya ya shiga dawo mata a rai, amma sai ta basar tama miƙe tana naɗe abin sallar. Sam Smart shi bai san da ta idar ba. Dan idanunsa a lumshe suke ya afka duniyar tunani. Samun kanta tai da tsura masa idanu, yayinda kalaman Nadiya na waccan ranar na dawo mata a zuciya. Kamar wadda aka tsawatarwa sai kuma ta ɗauke idanunta cikin yamutsa fuska tana jan tsaki. Duk da bai san mi take jama tsakin ba saukarsa a tsakkiyar kansa ya sashi ɗagowa cikin nutsuwar nan tasa ya buɗe idanunsa a kanta.
     “Gadin na miye?”.
  Ta faɗa cikin ƙarfin hali dan ba ƙaramin tasiri idanunsa keyi a duk sassan jikinta ba. Maimakon bata amsa ɗauke kansa yay, hakan kuma sai ya tunzura mata zuciya. Ta buɗe baki zata fara masifar tata yay gyaran murya kaɗan, kamar zata share sai kuma dai ta jiyo ta ɗan kallesa cikin harara tana ƙoƙarin warware gashinta. Ido suka haɗa ta mirrorn ta balla masa harara ta ɗauke nata. Shima ɗauke nasan yay ya maida kan gashinta mai tsaho da alamun samun gyara ya sashi yin wani ƙyau na musamman da sheƙi duk da a jiƙe yake a yanzu. Knocking gate da ake da ɗan ƙarfi ya sashi haɗiye maganar da yay yinƙurin yi. Agogon dake a ɗakin ya kalla sai kuma ya buɗe ƙofar ya fita. Ƙaramin tsaki yaja lokacin da ya fito harabar gidan sosai yaji bugun ƙofar babu ƙaƙƙautawa, sai da yasa key ya buɗe sannan ya zare sakatan. Da sauri Huwaila taja baya tana sissine kanta. Sai da ya gama kallonta ita da kwandon hannunta sannan ya matsa mata fuskarsa na ƙara tsukewa, dai-dai nan napep ta tsaya a ƙofar gate ɗin, dakatawa yay da ga yunƙurin rufewar da yake saboda hango Asma'u na fitowa a Napep ɗin. Fuskarta da murmushi ta ƙaraso garesa tana faɗin, “Yaya ina kwana”.
        “Lafiya Lau” ya amsa mata idonsa akan kayan hannunta, itama kallon hannun tayi har sannan fuskarta da murmushi ta ce, “Yaya abincinku n.....” sai kuma ta kasa ƙarasawa saboda hango Huwaila da tai a ƙofar shiga falon ɗauke da kayan abinci itama, da sauri ta kalli Yayan nata kamar zatai magana dan ita bata san da zuwan Huwaila ba. Ganin yay gaba abinsa ya sata bin bayansa batare data faɗi abinda ke bakin nata ba. Kallon juna sukai ita da Huwaila da ke hararta ta ƙasan ido, Asma'u ta ɗan girgiza kanta cikin basarwa ta ce, “Adda ai ban san nan zakizo ba da mun taho tare”.
       “Zaku shigo ne ko zaku tsaya surutu”. Smart dake kaiwa zaune cikin kujera ya faɗa. Shiga sukai da sauri, kowa ya ajiye kayan hannunsa suka gaishesa. Amsa musu yay da kulawa, sai kuma Asma'u cikin zumuɗi ta ɗora da faɗin, “Yaya ina auntyn?”. Ɗan jimm yay sai kuma ya nuna mata hanyar bedroom ɗin da Lulu ke ciki.
      “Yaya dan ALLAH barci takeyi?”.
Kansa ya sake girgiza mata nan ma. Miƙewa tai, kafin ma yace wani abu harta kusa zuwa ɗakin, ƙoƙarin dakatar da ita yay dan shi dai yasan wacece matar tasa, kuma baya buƙatar ƴan uwansa su fara sanin wacece itan su tun a yanzun, sallamar da Asma'u tai da ɗan knocking ƙofar ya katse masa tunani.
       “Asma'u!”.
   Ya kira sunanta kamar a kasalance, amsawa tai da “Na'am Yaya”. Tana jiyowa.........✍️


(😂Lulu karki bamu kunya dan ALLAH)


         




_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥



*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲




  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗



           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻


𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 6️⃣2️⃣



.......Dai-dai nan Lulu ta buɗe ƙofar ita kuma waya a kunne ta tana magana da Uncle Yousuf cikin shagwaɓa akan a aiko mata da wayoyinta. Miƙewa Smart yay ya nufosu, sai dai yana isowa Lulu da batama lura da shi ba ta riƙo hannun Asma'u suka shige ciki tana mata murmushi. Turus ya ɗan tsaya yana bin ƙofar da kallo, sai ma ya rasa wane irin tunani zai yi. Sai kawai ya ɗan furzar da isa ya nufi ɗakin daya kwana al'amarinta na ƙara ɗaure masa kai, ya fahimci gane ainahin yarinyar nan sai an shirya.
       Huwaila da ke kallon komai ta cika tai fam, dan ita babu abinda zuciyarta ya bata sai wulaƙantata da nuna mata wariya. Wayarta ta ɗauka tai kiran Umma, bugu ɗaya kuwa ta amsa, daga can cike da zumuɗi Umma ta ce, “Ya ya kin ɗebo ko?”. Sosai Huwaila ta tunzura baki gaba, idanunta akan hanyar corridor ɗin nasu kamar zata saki kuka ta ce, “Umma bayan munafukar yarinyar nan itama tazo, gashi can ya jata sun shige ɗaki wajen matar tasa sun barni ni kaɗai a falo, dama tunda ya buɗen ƙofar yake min kallon banza kin san shi dai da baƙin halin tsiya, balle yanzu yana ganin ya auri ƴar masu kuɗi kamar yafi kowa a gidanmu.”
         Ƙwafa Umma tai da ƙarfi zuciyarta na sake ƙuntata, cikin fusata da jin haushin lusarancin Huwailar ta ce, “To ke bazaki tashi ki bisu ba. Kije duk ma uwar da akeyi a ɗakin ayi da ke. Ki kuma tabbatar kin kwaso min abinda na sakaki”. Ƙitt ta yanke kiran batare da Huwaila ta sake samun damar cewa wani abu ba. Tasan hanlin Ummar su sarai akan jarabar tsiya, dan haka ta miƙe ta nufi inda taga Asma'u ta shiga. Ba knocking ba komai balle aje batun sallama ta afka musu. Asma'u da ke gyaran gado tai saurin jiyowa, hakama Lulu da ke waya da Sakatariyarta Zainab yanzu idanu ta zubama Huwailar.
       “Kai Adda Huwaila ALLAH har kin ban tsoro shigowa haka ba sallama”. Asma'u ta faɗa cikin jin takaici sai dai ta tausasa harshenta. Harara Huwailar ta zuba mata da taɓe baki ta nufi sofa ɗin bedroom ɗin mai azabar ƙyau da ɗaukar ido ta zauna, itama sai Asma'un ta watsar da ita ta cigaba da gyara gadon cikin takaici. Harta kammala ta shiga toilet shima dan ta gyara Huwaila na cigaba da harare-harare, sai dai fa ɗakin ya mata masifar ƙyau, ji take inama a cikin ƴan ɗakinsu ne suka samu wannan duniyar haka.
     Lulu kam tun kallo ɗayan datai mata bata sake ba tana cigaba da wayarta da Zainab da kuma gyara gashinta data kammala busarwa, so take sai ta kammala taji wace ita da kuma dalilin shogo mata ɗaki haka ba knocking. Asma'u data fito daga Bathroom alamar ta kammala ta yafito da hannu, koda ta iso batare da tayi magana ba ta miƙa mata ribbons da yimata nuni da gashinta alamar ta ɗaure mata. Amsa Asma'u tai da murmushi akan fuskarta, ta shaƙi fitinannen ƙamshin da gashin keyi ta lumshe idanu tana tattarosa cikin hanunta. Dai-dai nan Smart ya shigo ɗakin da sallama. Yayi masifar ƙyau cikin wani kwantaccen yadi da ya sake fiddo nagartarsa ta cikakken bahaushen arewacin Nigeria nutsatstse, daga ita har Asma'un ya zubama ido, sai kuma ya ɗan kalla Huwaila da ke gefe ta baje cikin couch tana ta wani faman hura hanci, sai dai shigowarsa ta sata ɗan nutsuwa dan tasan halinsa sarai.
“Ku tashi mu wuce ku kuma ko?”.
Ya faɗa babu alamar wasa tattare da shi. Asma'u ta ce, “To Yaya can gidan zaka kaima”. Kansa ya ɗaga mata kawai batare da yace komai ba, amma sai Lulu da ke ɗan kwallonsa ta cikin mirror ta juya kujerar tana dubansa da ƙyau tare da janye wayar kunnenta alamar ta kammala. Kallon ido sukaima juna, kowanne ya janye nashi cike da basarwa. Ƙasa-ƙasa ta ce, “Please ka barmin Auta anan dan su

Please Login or Register in order to submit comment