Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Da ga haka ya juya yay kwanciyarsa. Wani irin ƙarajin kiran sunansa ta ƙwala a matuƙar zafafe. Sai kawai yaja filo ya ɗaurama kansa ya toshe kunnuwansa ma ya maida idanunsa ya lumshe. Masifa ta fara zazzaga masa zuciyarta na raɗaɗi kamar zata fito ta baki, amma bawan ALLAHn nan yay biris da ita, da ya ga ma filon bazai masa ba sai ya ɗauki bluetooth ɗin sa da ke a bed side drawer ya manna a kunne ya saka ƙira'a abinsa. Fita tayi a ɗakin dan ta fahimci sai ta haɗashi da Daddy. Wayarta ta cira a handbag ta shiga dannama Daddy kira. Bugu biyu kuwa ya ɗaga dan fitowarsa a wanka kenan shima zai yi shirin office. Kafin ma yace wani abu ta sakar masa kuka da faɗin, “Daddy kaga mutumin nan ko? ALLAH ina raga masa ne saboda abinda Baba da Uncle You suka cemin, amma idan ya ce muyi ta inda ya ɓullo zan hargitsa masa rayuwa, nifa babu lallai babu dole zan dawo gida Daddy, garama komi Baban zaiyi yayi....”
       Duk da abinda Daddy keji na yunƙuro masa shima sai ya danne da ƙyar, cikin tausasa harshe ya ce, “Baby kinga relax mi yake faruwa? Mi yay miki?”.
      “Daddy Office fa zanje yabi ya kulle ƙofofin, naje ya bani key amma yay min banza yama saka bluetooth a kunne wai babu inda zanje sai next week, irin like kamar wata baiwarsa da ya saya a kasuwar bayi”.
    Ƙololuwar ɓaci ran Daddy ya kai, a taƙaice ya ce “Ina zuwa”. Ya yanke kiran, number Smart ya lalubo a karo na farko ya danna masa kira. Kasancewar bluetooth a kunnensa ya sashi jin shigowar kiran a bazata, hannu ya kai ya zare guda ɗaya yana kai hannu kan wayar tasa ya ɗauka dan ganin wanene mai kiransa haka. Bai san number ɗin ba, dan baida Number Daddy, kamar zai share sai kuma dai ya ɗaga gudun kar yay mistake.
       “To sannu isashshe”.
Kalmar data fara dukan kunnensa kenan a maimakon sallama.........✍️



_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥



*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲




  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗



           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻


𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 6️⃣9️⃣



........Cikin sa'a kuma ya gane muryar Daddy. Amma sai ya danne bai nuna ba, cikin dai nutsuwarsa ya ce, “Assalamu alaikum”.
    “Da sallamar nake da buƙata da ita zan maka ai. Miye dalilinka na hana Mawaddat fita office ka kuma kulleta?”.
          Shiru Smart yayi kamar bazai ce komai ba, sai kuma ya furzar da numfashi kaɗan yana gyara kwanciyarsa. Sake tausasa muryarsa yay fiye da ɗazun ya ce, “Kayi haƙuri Daddy sallama wajibi ne ga musulmi, haka ma amsata ga wanda akaimawa. Kai ya kamata ka tunatar da ni hakan a matsayinka na mahaifi. Dan haka kayi haƙuri ka amsa min sallamata kafin muyi maganar da kake son. Assalamu'alaikum!”.
       A cinkushe Daddyn ya amsa masa, Smart ya ɗan girgiza kansa sannan ya tashi zaune sosai. Cikin sake tsantsan da kai na girmamawa ya ce, “Daddy ina kwana”. Bai amsa masa ba nan kam. Shima sai bai damuba ya ɗora da faɗin, “Zan sake baka haƙuri a karo na biyu Daddy, dan ALLAH karka saka baki a wannan zancen dan a yanzu Mawaddat tana ƙarƙashin na ne. Inada damar zartar mata da hukunci akan abinda ya dace da kuma banbance mata wanda bai dace ba. Kai mana fatan alkairi kawai shi mukafi buƙata da sanya albarkar ku, na riga na gama yanke hukunci akan hakan babu kuma tunanin canjawa a tattare dani amin afuwa. Na Barka lafiya”. Daga haka ya yanke wayar tare da kasheta gaba ɗaya ya koma yay kwanciyarsa ransa fal mamakin halin surukin nasa.
     Ƙaramin hauka ne ya kusan samun Daddy da ga can jin Smart ya yanke wayar bayan ya gama datsa masa zafafan magana kamar yanda zuciyarsa ta fassara masa. Ƙoƙarin sake kira yayi amma sai wayar switch up. Kaɗan ya rage ya maka wayar da ƙasa. Amma sai ya fasa ya maida akalar kiran kan Uncle Yousuf. Suna zaune shi da yara da akaima shirin makaranta suna breakfast kiran Daddyn ya samesa. Bai kawo komai a ransa ba ya ɗaga, sai dai kiran sunansa da Daddy yay a tsawace ya sashi rumtse idonsa. Sai kuma ya miƙe yabar daining ɗin ya nufi bedroom ɗinsa. Cikin tausasawa ya ce, “Yaya lafiya dai kuwa?”.
       “Yousuf yanzun nan ka kira ɗan iskan yaron can ka faɗa masa ya sakar min yarinya tunda ba ubansa ya haifa min ita ba, har ni yake da bakin gayama Mawaddat ta koma ƙarƙashin ikonsa ya kuma yanke hukunci a kanta bazai canja ba kamar shine ya haifa min ita.”
      “Ya Salam. Yaya Please calm down dan ALLAH muyi magana mana. Wlhy sam ban fahimci mi kake son faɗa min ba. Mi Aliyun yay maka ne?”.
       “Miye ma bai mun ba, babu abinda ya manta na rashin kunya bai faɗa min ba. Shiyyasa tun farko na faɗa maka yaron nan ɗan zafin kai ne zai iya bamu matsa ta duk inda bamuyi zato ba. To gashi ya fara, ya kulle gida ya hanata fita aiki, ta masa magana ya ce sai next week babu inda zataje, ta kirani nai kiransa nai masa magana amma ya daddatsamin magana son ransa tsabar shi ya cika cikakken ɗan iska.”
         Girgiza kai Uncle Yousuf yayi, kafin ya ce, “Dan ALLAH kayi haƙuri ka kwantar da hankalinka, ka dai san mi ɓacin rai ke haifar maka a yanzu. Zan kira shi na masa magana sai naji dalilinsa. Sai dai ma yaya banda abunka ai bai kamata ka biye mata kai kiransa ba, karfa ka manta yau kwana biyu kawai da tarewarsu, ai bai dace ba ta fita aiki sai mutane suyi magana kadai san yanda al'amarin yake yanzu mutane sun bar damuwa da al'amarin su sun koma hango na wasu”.
          “Yousuf bana buƙatar jin komai, sannan ni babu ruwana da wasu mutane ko abinda zasu faɗa, farin cikin yarinyata kawai na sani. Shi wanene da zai tauyeta bayan da aikinta ya ganta, sannan waya faɗa masa shi ɗin har ma yanada wani ƙarfin iko a hannunsa a kanta da zaima mutane wani gadara koda ace auren nasu mai muhimmanci ne. Wannan shine na guda tun farko amma ka kasa fahimtata, shiyyasa kuma nace ayi komai a rubuce amma nan ma ka wani kakkaresa gashi nan tun kan aje ko ina ya fara nuna halinsa, a haka kwanakin da kace ɗin zai cika yay abinda ake so? an faɗa masa akan ƴata zai nuna gargajiyancinsa ne”.
       “Naji duk na ɗauka kayi haƙuri zanyi magana da shi yanzun.” daga haka Uncle Yousuf ya yanke wayar batare da ya jira cewar Daddy ɗin ba. Hannunsa ya kai ya dafe kansa, sai kuma ya girgiza a hankali ya ɗago yana murmushi mai sanyi. A fili ya furta, “Yaya yaya kenan, kai da gaske jiran cikar lokacin kake kenan? Humm aiki ya sameka. Aliyun dama shine ai dai-dai da kai game da lamarin Mawaddat duka kai da itan. Ashe babu daɗi lokacin da ka dakatar da Aunty Kareema fita aiki a dalilin Marigayiya, duk da hakan ya mata ciwo kuma ta haƙura iyakarta kuka ta share hawayenta, ashe ita daga sama ta faɗo? Kai gashi hana fitar kwanaki kawai da akai ma taka ɗiyar ya zafafaka har haka. ALLAH na gode maka da ka kaini da rai da lafiyar ganin irin wannan ranar, shiyyasa akace yanzu ma tun a duniya ake fara hisabi basai an mutu ba. Muje zuwa yanzu aka fara wasan ai. Mai ƙarfi sai yaci kofin”. Ya ƙara sakin murmushi. Ƙoƙarin kiran Smart yayi sai ya samu wayar switch up. Ya sake sakin murmushi da faɗin, “Kaga mazan ƙwarai”. Da ga haka ya miƙe ya fito abinsa. Ya samu yara har sun wuce, sai Aunty Saliha da ke zaune tana tsumayen fitowarsa dan ya sakata a ruɗani.
        “Abban Ra'is lafiya dai ko?”.
    Ajiyar zuciya ya saki yana kaiwa zaune, ta turo masa kunun data sake zuba masa dan wanda ya bari ya huce. Sai da yasha kusan sau uku sannan ya dubeta. “Yaushe zakuje gidan Mawaddat ɗinne?”.
       “Sai zuwa anjima kaɗan dan muje mu dawo da wuri ko”.
     “Inaga ku kuyi zamanku, su Hussain suje sukai mata, motocin ta kuma a barsu ba yanzu ba.”
          “Amma wani abu ya faru ne?”.
      “Zai dai faru Saliha.......” nan ya zayyane mata komai daya faru. Cikin damuwa ta ce, “Amma Yaya da bai kirashi ba ai. Dan Aliyun ya fishi gaskiya, yaza'ai amaryar da aka kai gidan miji shekaran jiya kuma a ganta a office yau dole zai iya zama abin magana. Inda waɗan nan ƙananun matsalolin zai dinga sawa iyaye na neman sakin ƴaƴansu ai da kowama ya zama babu aure kenan. Ni sai nake ganin kamar maganar Aunty Kareema zata iya zama gaskiya....”
        “Hummm ku mata kullum tunaninku iri ɗaya ne, miyasa komai a rayuwa idan yazo mana a yanayin da ba haka muke tunanin ganinsa ba sai mu dinga ɗaukarsa asiri. Nasan asiri yana ɗaya daga cikin abinda al'ummar mu suke kallon babbar mafita ga al'amuransu a halin yanzu, sai dai bai kamata muna tsuke dukkanin zukatanmu waje guda ba akan kowanne bigire muyi masa kallon asirin. Amma dai bari nai miki wata tambaya, shin ku minene dalilinku na kallon al'amarin Yaya matsayin asiri?”.
        Duk da maganganunsa na farko sun shigeta sai bata gaza wajen faɗa masa hujjojin da suke kallonba su. Ta ce, “Na yarda da zancenka nima, sai dai ka kalla wani abu Abban Ra'is. Kafin auren marigayiya kai da kanka ka bani labarin ba haka Yaya yake ba sam, sannan Yaya nada ilimin addini mai zurfi da yasan minene aure da ƙaddara. Amma kaga yanda idanunsa suke rufewa ta yanda idan wani aka faɗamawa da bai gani ba zai iya ma ƙaryatawa. Dolene muyi tunanin akwai sammu tattare da shi”.
          Murmushi yay da cewa “Hummm! Saliha kenan. Duk ilimin mutum bakwa tunanin son zuciya zai iya sakashi ajiye ilimin gefe ya aikata abinda baida alaƙa dana masu ilimin. A al'amarin Yaya babu wani asiri, akwai ɓoyayyen al'amarin da yake ɓoyewa dai tun kafin auren Mawaddat ɗin, sai da ya auretanne ya fara fitowa, wanda tamkar ALLAH ya jarabcesa da sanya masa tsoron faruwar irinsa akan Mawaddat ne, ba komai ya kawo hakan ba kuma sai dan itace mafi soyuwa a ransa ko kuma ana masa barazana da ita, shiyyasa ma tun farko ya gagara yarda da kowa game da kula da al'amarin ta, a tunaninsa shi zai iya kareta akan komai, sai kuma akai rashin sa'a ƙaddarorinta ba'a fatar jiki suke ba ko mahallin zamanta balle yay tunanin kuɓutar da ita a yanda yaso da kuma ƙarfinsa da wayonsa. Dan haka kuma bar damuwa da al'amarin sa ana gab da zuwa gaɓar da zai fallasa kansa da kansa batare da ya sani ba. Yanzu Mawaddat itace mafi ƙololuwar abar tausayi, dan ina matuƙar jin tausayin rayuwar yarinyar a dalilin halin data tsinta kanta a ciki.”
      Yanda ya ƙare maganar cikin matuƙar damuwa da ɓacin rai yasa Aunty Saliha tasowa ta dawo kusa da shi tare da dafa kafaɗarsa. “Kayi haƙuri Abban Ra'is, tabbas tausayin Mawaddat dolene ga duk wanda ya fahimci muhimmancin rayuwa. Sai dai namu addu'a ce a yanzu tsakaninmu da ita, mu kuma cigaba da bama Aliyu goyon baya akan abinda ya fara, dan a yau na sake gamsuwa da fahimtar hikimarka ta haɗa wannan auren. Inaga kuma lokaci yayi da shima zaka fara aiwatar da shirinka na taimakonsa da tun farko shine dalilin jawosa jikinka da kayi, dan namiji bazai yiwu ya rayu babu abinyi ba yakan ja masa ƙasƙanci tsakaninsa da mace, musamman irin Mawaddat da tunda ta tashi bata san minene babu ba”.
          “Hakane kam, insha ALLAHU kuma a yanzu haka ina kan shirye-shirye ni da Hameed, dan kin san al'amarin nasa sai anbi ta bayan fage yazo a bazata tamkar yanda maganar auren nan tazo a bazata. Dan bayyanawa na nuna zaburar da mai ƙullin ne”.
      “Tabbas hakane, ALLAH ya bada nasara yasa shima iyakar wahalar tasa ce tazo. Ku kuma da kuke ƙoƙarin ALLAH ya saka muku da alkairi ya hana bayanku kuka”.
     “Amin ya rabbi. Bara na kirata idan naga da yiwuwar kuje ɗin to”.
    “To ba damuwa”.........✍️



_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥



*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲




  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗



           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻


𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 7️⃣0️⃣


.......Zaune take a falo dafe da kanta dake matuƙar sara mata saboda ɓacin rai, a yanda take jinta zata iya aikata komai akan mutumin nan, amma ta zauna tsumayen kiran Daddy ne da yace ta dakacesa, sai dai an shafe kusan mintuna ashirin kenan shiru, hannunta ta janye tare da kallon wayarta da idanunta da sukai wani irin jazur. Wayar ta ɗauke da tunanin sake kiran Daddy ɗin kiran Uncle Yousuf ya shigo mata. Wayar ta tsaya tana kallo kawai, sai da ta kusa tsinkewa ta iya ɗagawa ta kai kunne, sai dai tayi shiru dan in har tai magana kuka ma zai iya ƙwace mata. Ƙaramin murmushi Uncle Yousuf yay da ga can da bazata iya jiyo sautinsa ba, kafin cikin tausasa harshe ya ce, “My Daughter yau babu gaisuwa ne?”.
        Nan ma shiru ta kasa magana. Tofa yasan an kai ƙololuwar ɓacin rai kenan, dan haka ya sake tausasa harshe cikin komawa serious ya ce, “Mawaddat miya faru? Ko baki da lafiya ne?”.
             Hawayen da take riƙewa ne tun ɗazun suka kufce mata, da rawar murya irin ta mai kuka ta ce, “Papa bazan iya ba, bana son damuwa gida zan dawo. Wannan ba rayuwan da zan iya yi bane...”
     “Kwantar da hankalinki sanarmin mike faruwa?” ya faɗa like bai san komai akai ba. Da ƙyar ta iya masa bayanin abinda ya farun kamar yanda Daddy ya sanar masa. Anan ɗin ma murmushi ya sake yi ɓoyayye. Kafin ya ce, “Mawaddat rayuwar aure haka take, a komai ita mace ƙarƙashin ikon mijinta ta ke, wajib ne kuma yimasa biyayya in har shima bai keta dokar UBANGIJI ba ko jagorantar ta saɓa masa. Anan kam ba'a yarda ta masa biyayya ba sam, dan ba'ama wani biyayya ko tarayya wajen saɓama ALLAH......”
         “Bazai yiwu ba Uncle You, domin ni da kai da shi duk mun san matsayin wannan zaman ba sunansa aure ba, Please Uncle kace masa ya sakeni idan ma bazai yi haka a yau ba zan dawo gida idan kwanakin da akai yarjejeniyar sun cika ya sakenin, zan iya ɗaukar komai amma banda kan aiki na, domin shine rayuwata, shine farin ciki na, shine mafarkina, shine babban burina tun kafin nasan kaina, shi waye da rana tsaka zai datse hakan da tunanin nuna gadara ko ƙarfin ikon abinda bashi da ikon!”.
       “Mawaddat aure kona kwana ɗaya ne sunansa aure, da auren nan baida kimar da za'a kirasa ko kwallonsa da wannan martabar da muhimman mutane basu taru cikin shigar kamala domin ɗaurashi ba. Da wasu mutane basu ajiye muhimman ayyukansu ba domin halartarsa. Ki kwantar da hankalinki komai ya tafi cikin tsarin da muke fatansa, Aliyu kuma zanyi magana da shi duk da nasan shima ba son hanaki aikinki yake gaba ɗaya ba tunda ya sanar miki next week zakiyu resuming be a good girl mana sweetheart, maybe ma yana tsokanarki ne dan yaga yaya zakiyi. Dan haka ina son ki zama jaruma mana kamar yanda ya sanki.....”
        “Amma Uncle fitan yanada muhimmanci fa yau. Kasan inada case ɗin yarinya da ke aibiti, tun juya kuma ya kamata naje na shigar da case ɗin court”.
      “Kar ki damu indai wannan ne yanzu zan fita ni zanje da maman yarinyar mu shigar da ƙaran, ke kuma sai ki cigaba da shirinki matsayinki na lawyer ɗin nata hakan yay miki ko?”.
            A hankali ta ce, “Eh”.
       “Yauwa ɗiyar albarka na. Ki daure kinji, kar Aliyu ya samu na tsokanarki, bamma so ki bari yaga hawayen nan, maza ki sharesu ki zauna kurum kamar ba'ai komai ba Kinga kinyi winning”. 
    Ta gamsu da zancen nasa ɗari bisa ɗari, dan dolene itama ta mannama velleger ɗin can haukan da sai ya gagara barci a yau. Da ga haka ta miƙe bayan sunyi sallama da Uncle Yousuf da ke dariya daga can ta nufi bedroom. Fuskarta taje ta wanko da canja kayanta zuwa wando da riga marasa nauyi na zaman gida, ta sake dawowa falon ɗauke da laptop ɗinta. Dai-dai nan ya fito shima, alamunsa sun nuna yay wanka dan sanye yake cikin ƙananun kaya da sukai matuƙar amsarsa sai ƙamshinsa mai sanyi da ke tashi. Zaune ya kai idonsa a kanta sai dai fuskarsa babu walwala, duk da taji motsin nasa ko sau ɗaya bata nuna alamar hakan ba balle ta ɗago, lap-top ɗinta kawai take ƙoƙarin kunnawa. Shi kuma sai ya tsira mata idanun nan nasa na macizai da take kira, ƙin ɗagowar tata bai hanata jin kaifin idanun nasa a kanta ba, amma ta dake ta cigaba da abinda take yi. 
        “Break fast fa?”.
     Ya faɗa a dake still dai idanun nasa a kanta. idan kujerar da ya ke zaune ta motsa to itama ta motsa. Cije lips ɗinsa yay yana wani sake ƙanƙance idanunsa a kanta. Kusan minti ɗaya yana kallon nata kafin ya miƙe tsam zuwa inda ta ke, lap-top ɗin ya ɗauke da ga jikinta ya ajiye gefe, karon farko ta ɗago ta kallesa da idanunta da suka kaɗa saboda kukan da tayi, fuskarta na nuna matuƙa ranta a ɓace. Nunawa yay kamar baiga kallon da take masan ba, kafin ta furta abinda ke bakin nata ya kwasheta gaba ɗayanta a cikin hannunsa yayi sama da ita kamar wata ƴar baby, (🤣dama abu ba abu ba sai masifa).
         “Bana son wulaƙanci malam miye haka? Dalla sauke ni”. Ta faɗa cikin matsanancin ɓacin rai tana kai masa ƙananun duka a ƙirji, amma ko gezau kansa tsaye ya nufi hanyar kitchen da ita, saman cabinet ya direta, ya juya ya sakama ƙofar key. Dai-dai ita kuma tana dirowa da ga inda ya ɗauratan ta iso ga ƙofar. Wani shegen kallo ta watsa masa da faɗin, “Matsa min”.
    “Idan kinyi abinda nace kenan”.
Ya faɗa cikin halin ko'in kula yana saka key ɗin cikin aljihun wandonsa da jingina da ƙofar yana mai harɗe ƙafafunsa waje guda. Ƙarshen ɓacin rai Lulu ta gama kaiwa, dan haka cikin kaushin murya ta ce, “Kasan na iya fiye da abinda kake tunanin ka'iya na rashin mutunci ko. Aliyu! Ka buɗe ƙofar nan ka bani hanya na wuce kafin na saka dana sanin sani na”.
          Jikin ƙofar ya bari da ɗan taɓe baki batare da yace komai ba ya nufi frizzier ɗin da ke kitchen ɗin ya buɗe, sai da ya ƙarema kayan ciki kallo sannan ya rufe ya nufi store. Daga sama har ƙasa yake bin store ɗin da aka tsatstsage da kayan abinci kala da iri da kallo shima, har da su doya da airish da ruwa da kayan miya da akaima ajiya irin wadda bazasuyi saurin lalacewa ba. Shi sai abin ma ya so bashi mamaki da dariya, to su da suka jibge waɗan nan kayan matar gidan ta iya abinci ne?....
      Shigowar Lulu a fusace ya saka tunaninsa yankewa, ya juyo gaba ɗayansa yana dubanta, huci take sosai idanunta sun juye gaba ɗaya har wani tara ƙwallan masifa sukeyi. Gashi yanda yaga sun ɗan kumburo tun ɗazun ya fahimci kuka tayi, yaji ba daɗi a ransa, dan sam baya son ganin wani ya shiga damuwa a dalilinsa, sai dai dolene yay abinda yayin dan ya fahimtar da ita da da yanzu ba ɗaya bane, yanzu komai sai da izini... Da sauri ya dubeta jin tana ƙoƙarin saka hannu a aljihunsa alamar son zaro key. Hannun nata ya riƙe yana ɗan waro idanu waje, duk yanda taso fisgewa bai sakar mata ba sai da ya zare key ɗin da ga aljihun nasa, sai kawai ya maƙalashi jikin belt ɗinsa ta inda yasan bazata ce zata ɗauka ɗin ba yana sakin wani shegen murmushin mugunta. Da sauri ta ɗauke kanta da ga dubansa gaba ɗaya tana jin kamar ta fasa ihu, a zuciyarta kuwa tace (ɗan iska).
        “Yanzu mi zaki dafa mana? Dan yunwa nake ji nikam ga shi nace su Ammah kar su ƙara aiko abinci injiki.”
     Harara ta watsa masa cikin gatsali ta ce,  “Ashe zaka mutu da yunwa kuwa a gidan nan”.
             “Zadai mu mutu, dan kema dai duk tsiya dole ki nema ai. A yanzu ma haka idan kina son fita da ga kitchen ɗin nan ki nema mana abinci, inba hakaba ALLAH anan zamu yini”. Ya ƙare maganar yana fitowa da ga store ɗin. Ɗaya da ga cikin kujeru huɗun da aka sakama table a tsakkiya yaja ya zauna. Hankalinsa kwance ya jawo wayar ya fara buga game ɗin ball, ya kuma ƙure ƙarar yanda ta cika kitchen ɗin da hayaniya. Lulu data gagara fitowa a store kanta ta dafe, sai faman haɗiyar rai take zuciyarta na ƙuna. Ta rasa yaushe ne guy ɗin nan yay mata irin wannan rainin har haka, bata taɓa haɗuwa da mutumin da ke latsata a yanda yake so da gadararsa irinsa ba, ya bala'i bala'in shigar mata hanci da yawa. Gadararsa da son nuna shi ɗin wani ne da iya taurin kai na cimata zuciya. Fitowa tai a bisa shawarar da zuciyarta ta bata, ta cije lips ɗinta tana jin kamar idan ta ƙarasa garesa ta shaƙesa kawai, amma sai ta ture tunanin gefe. Kujerar dake kallon wadda yake zaune ta dafa cikin ɗan sassauta zafinta dan ta fahimci ihun da take masan kamar tunzurashi yake da jin daɗin latsata. “Aliyu kafa san aiki nakeyi ka ɗakkoni ka kawo nan, kai miyasa baka bambance lokacin shiririta dana serious?”.
        Batare da ya ɗago ya kalleta ba hankalinsa ma akan game ɗin sa ya ce, “Yima mijinki girki ne ba serious ba?”.
     “Kai kasan mijin ma, Ka bani key na wuce, idan abincin kake so ai kasan gidan abinci, dan in har abinda zan girka zakaci ka siyama kanka wahala dan ban iya ba ma sai kabi wani sarkin”.
       “Hummm ashe kuwa in dai ba zakiyi abinda nake so ba kuma ya dace ga matar aure to aikin ma zai gagareki yi ne, duk da a farko banda wannan niyyar. Dan haka kina da zaɓi kenan, yin yanda nake so kuma na tsara a gidana, ki samu yanda kike so kema. Ko ƙin yi, kema ki ƙi samu. Abinci kuma duk yanda kika iya kiyi zanci a hakan ko baiyi ba”.
            Luuuu tai da idanunta kamar zata lumshe su sai kuma ta buɗe, komai ma ya gundireta, tama rasa yaya zatai da mutumin nan mai shegen taurin kai da gadara. Wai miyasa ma ta amince ne da wannan tsarin da shi? Miyasa bata bada damar a nema wani ba?. Tsaki taja mai ƙarfi da kai hannu ta dafe kanta, sai kuma ta janye tana mai watsa masa hararar zaka banbance tsakanin aya da tsakkuwa ta bar wajen. Da kallo ya ɗan bita ganin ta nufi hanyar store, tana

Please Login or Register in order to submit comment