Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Smart Mawashi?”.
      Sai yanzu ma shi coach ya tuna ashe Aliyu a ƙarƙashin abokin nasa yake a yanzu. Dan haka ya bashi amsa da cewar, “Yess! Yes! Shifa wlhy”.
        “Ya Salam gani nan a hanya”.

   Kusan a tare Uncle Yousuf da Ahmad suka iso wajen. Kowanne ya fito a motarsa da sassarfa zuwa inda suke zagaye da Smart da ke kwance a ƙasa kansa bisa jikin coach da ke faman shafa masa ruwa yana fatan ya farfaɗo, dan bai son su kai shi gida a wannan yanayin musamman daya tuno irin tashin hankalin da Ammah ta shiga last da abin ya faru da shi. Har rige-rige ake tsakanin Uncle Yousuf da Ahmad, sai dai kowanne ya samu nasarar kai hannunsa jikinsa. Ganin yanda aketa faman saka masa ruwa babu alamar zai farfaɗo Uncle Yousuf ya cema coach “Hameed muje asibiti kawai dan banga alamar zai farfaɗo ba a hakan nan”.
       Cikin damuwa coach ya dubesa shima da bashi amsa da “Yousuf zuwa asibitin nan babu abinda zai canja. Dan mun gwada yin hakan a baya sai dai mu gama zaman banza dan su amsa ɗaya ma suke bamu zuciyarsa ta tsaya da aiki. Al'amarin nasa ne fa kamar abin sihiri gashi nan dai. Gida kawai ya kamata mu kaisa duk da gaskiya hakan na sakani fargaba dan tayarwa iyayensa hankali kawai zamuyi”.
        “Gaskiya kar a kaishi can Brother” Ahmad ya faɗa cikin damuwa. Bai jira cewar kowa ba ya cigaba da faɗin, “Mizai hana muje wajen mutumin nan da ya taɓa bashi magani sanda abun ya takura masa”.
     “Shawara mai ƙyau Ahmad, da ni duk nama rikice wlhy hakan bai zo min a rai ba. Kunga ku kamashi kusa a mota”.
    A bayan motar Uncle Yousuf aka saka shi kamar yanda ya buƙata, shi da coach suka shiga gaba Ahmad a baya ya riƙe Smart. Kai tsaye ƙofar ruwa suka nufa, gudun da coach keyi ya sakasu isa cikin ƙanƙanin lokaci. Gidane irin na talaka mai ƙaramin ƙarfi, sai dai da ga waje shafe yake da siminti tsaf da shi da milk ɗin fenti. Da ga gaban gidan kaɗan islamiyya ce ta ƙanan yara da keta karatu kasancewar akwai ta safe zuwa ƙarfe ɗaya. Tsaiwar motar ta saka wani saurayi da ke tsaye da ga jikin barandar Islamiyyar matsowa garesu yana musu sannu. Basu wani tsaya jan maganar ba suka buƙaci ganin Malam. Kafin ya basu amsa sai ga malam ɗin ya fito da ga gida..........✍️

         
_Yau dai Smart ɗin ku ya ɗan bani tausayi🥲_



_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070


VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥



*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲




  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗



           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻


𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣8️⃣


_Ya rabbi ka gafartama *Sheikh Abubakar Giro Arugungun*. Ka yafe masa kurakuransa, alkairan da ya isar garemu na wa'azantarwa da koyarwa kasa ya amfanar da mu duniya da lahira. ALLAH ya albarkaci zuri'arsa. Suma iyayenmu ALLAH ka gafarta musu, damu baki ɗaya 😭✍️_.



........Wata nannauyar ajiyar zuciya Smart ya saki mai ƙarfin gaske lokacin da malam ya shafa masa ruwan addu'oi da yayi tofi a ciki, sautin karatun suratul Naazi'aat da ɗaliban malam ce ta fara shiga cikin kunnensa da wani irin ƙarfi tamkar a iya cikin kunnen nasa akeyi. Ya sake sakin ajiyar zuciya sai kuma ya kai hannunsa ya dafe goshinsa dan kansa wani irin ciwo yake kamar zai tarwatse. Uncle Yousuf ne ya fara ambatar sunansa, dan haka ya sake yunƙurin buɗe idonsa a karo na biyu sai dai ya kasa. A rikice duk suka dubi malam. Ya karkaɗa musu kansa da faɗin, “Kamar yanda na faɗa muku tun wancan karon ku sake jajircewa wajen addu'a da sadaka akansa, dan al'amarin nasa akwai ruɗani kamar na sihiri mai ƙarfi. Sai dai ban tabbatar ba dan UBANGIJI shine kawai masanin gaibu. Amma gaskiya al'amarin nasa yana nuna kamar bugewar junnu ne. Na fara baku ruwan addu'oi a wancan karon amma sai aka daina zuwa a karɓa kwata-kwata, dama ba komai bane face addu'oin karya sihiri wanda ya kamata ma ace duk musulmi kan dingayi a gidansa domin shi da iyalinsa koda lafiya lau ake dan rayuwa kake baka san mike biye da al'amarin ka ba. Koba sirihi akwai baki (kambun baka) da yafi sihiri kaifi a wasu lokutan. Koda ma bazaku juri zuwa nan ɗin a karɓa ba to ku dage da yi masa a gida dan ALLAH”.
      A tare suka amsa da “In sha ALLAH malam” sai kuma suka ɗora da godiya. Ganin yanda Smart keta faman jujjuya kansa malam ya ƙara masa addu'a tare da basu umarnin kaisa asibiti mafi kusa. Godiya sukai masa dan a wancan karon ma haka yay musu. Suka ajiye masa sadaka shi kuma ya basu ganyen magarya da ayoyin da zasu karanta da ga cikin Alkur'ani mai girma. Kai tsaye asibitin suka nufa kuwa, inda aka bashi gado dan a kallo ɗaya idan kai masa dole ne ya baka tausayi, kai kace ba a yanzu kaɗai ya kasance a kwance ba yanda yay sharɓan. Sun bashi taimakon gaggawa har sai da ya samu barci suka ɗan samu nutsuwa. Sun yanke shawarar sanar da gidansu amma sai coach ya ce adai ɗan dakata idan basu sallamesa zuwa yamma bane sai a sanar musun. Hakan ya musu, dan haka sukai yunƙurin fitowa aka barsa da Ahmad ya zauna da shi kafin suje su dawo.....

          ★★★★★

   Duk yanda taso cigaba da gudanar da al'amuran gabanta na wannan yinin hakan sai ya nema gagararta. Ba ƙaramin tsaya mata a rai abinda drivern nata yay mata yayi ba. Dole ta hakura da tattara bayanan case ɗin da zata fara tunkara a safiyar litinin kan dukiyar wasu marayu da wan mahaifiyarsu ke ƙoƙarin handamewa dan zuciyarta a cinkushe take matuƙa. Steering da take murzawa ta kaima duka a karo na babu adadi. Ta cije lips da masifar ƙarfi da faɗin, “Sai na koya maka hankali!”. Kalmace data ambatata yafi sau shurin masaƙi. Ga takaicin daren jiya da ma na cigaba da ci mata rai dan a duniya tai masifar tsanar wani namiji ya raɓeta da sunan taɓata ko soyayya. Shiyyasa shima Tajuddeen lissafinsa ya shiga cikin jerin lissafin abubuwa masu ƙuna da ajiyewa a kudin tarihinta na wannan yinin da take ganin yazo mata a birkice. Office ta koma, inda ta tarar da baƙi kashi-kashi na jiranta. Tabbas batajin magana, sai dai a ɓangaren aikinta ita ɗin jajirtacciya ce, dan ma ɗabi'arta ta shaye-shaye na matuƙar maidata baya a lokuta da dama, dan badan wata hikima ta UBANGIJI ba da Lulu ta jima da daina zuwa wajen aikin ma gaba ɗaya ne. Mummunar hallayya mafi muni tattare da Mawaddat shine sakaci da addini, sam babu abinda ta sani akan addininta sai abinda ba'a rasa ba sakamakon karatun ta na lawyer. Bata san a kira salla ta tashi tayita akan lokacinta ba, to idan ma tayin babu maganar yinta a yanda MANZON ALLAH ya koyar damu. (Kuyi haƙuri ba Lulu kaɗaice a wannan matsalar ba. Wlhy da yawan mutane sunayin salla ne ba'a yanda MANZON ALLAH ya koyar ba. Dan bawai fa muna nufin Lulu bata san salla ba, a'a itama ta tashi ne a yanayin yanda akeyi kawai nakeyi batare da samun ilimin yinta ba kamar yanda da yawa mutane suka kasance. Mafi yawanmu idan da zaman tsayawa akan ibadarmu ta salla za'ai tun daga tsaiwarta ma zamu fara samun gyara.  Please Dan ALLAH a wannan gaɓar kowanmu ya nutsu ya kalla sallarsa da kuma bincike akan yaya ake salla kamar yanda MANZON ALLAH S.A.W ya koyar mu gani ko zamu ribantu da gyarawa). Sanda ta gadama take salla, tana kuma yin tane a yanda kawai taga anayi kasancewar karatun addinin ma gatan mahaifinta ya zame mata cutarwar da bata samesa ba. Masifarta kam wannan halitta ce, wani mai haƙuri wani saɓani haka. Sai ɗabi'ar shaye-shayen data jima tana binnewa wanda har yanzu bamu san tushen farawarta ba ko dalilinsa. Wulaƙanta mutane da takasu a duk yanda taso kuskuren mahaifinta ne da ya ɗorata a turbar komai take so zata samu. A duk sanda ka nunama yaro komai yake so zai samu tofa kansa zai ƙara girmane da tunanin yafi kowa daraja da power a rayuwa, sannan akan komai shine sama da kowa. (Iyaye sai mu kula hakan ba soyayya bace)....
       Yanda ta zube wayoyinta da zama jagwab cikin lallausar kujerar office ɗin nata ya sake bayyanar da ɓacin ranta akan fuska. Hand bag dinta ta jawo tare da fiddo key ɗin drower ɗin jikin decks ɗinta da bata yarda kowa ya taɓa saboda abinda take ajiyewa a ciki ta lalubo. Tana ƙoƙarin buɗe drower ɗin sakatariyarta ya shigo office ɗin da sallama. Wani takaici ya sata ɗago idanunta da suka kaɗe da gajiya. Sai dai gaba ɗaya tama kasa mata masifar da ta saba yi mata a duk sanda tai mata kuskure. Da sauri sakatariyar ta ce, “Please am sorry maa. Wlhy abinda matar can tazo da shi ne yay matuƙar tayarmin da hankali. Jiya ma tazo nace mata ta dawo yau dan kina up 2days sai yau ne zakiyi res.....”
       Hannu Lulu ta ɗaga mata alamar gajiya da saurarenta. Murya a shaƙe ta ce, “Zainab ba wanda zan iya saurare a yau koma minene akazo da shi. Ki sake bama duk wanda ya dace sabon appointment banda yau da gobe. Duk case ɗin da kuma kika sani bani da buƙatarsa a teburina karma mai shi ya shigomin office ok”.
             Zainab da damuwa ta bayyana ma a fuska ƙarara ta gyaɗa kanta da ke ƙasa. Sai kuma cikin rawar murya dan har ta fara hawaye ta furta, “Aunty matar can fa mijinta ne yayma yarinyarta da taje agolanci da ita gidansa fyaɗe. Kuma yarinyar shekararta tara kwata-kwata. Sunje asibiti da yarinyar amma anƙi karɓarsu tun jiyan wai sai da ƴan sanda. Taje police station ɗin kuma ƴan sandan nata mata yawo da hankali. Wlhy bakiga a yanda sukazo da yarinyar ba a jiya da yamma abin babu ƙyan gani....”
      Wani irin matse idanu da damƙe kujera Lulu da jikinta ya fara tsumar mazari tayi. (Mawaddat calm down. Mawaddat calm down. Mawaddat calm down). Wani sashe na zuciyarta ke ta ambata mata. Sannu-sannu ta fara sassauta damƙe kujerar da rumtse idanun nata da tai, sai kuma ta buɗesu gaba ɗaya sunyi jajur matuƙa kamar wadda tasha wani abu a lokacin.
“Shigomin da ita”.
    Ta faɗa ƙirjinta na ƙara ƙarfin sukar da yake mata. Ga jikinta bai daina tsumar da yake ba. Da ace tanada ilimin addini da addu'a tafi cancanta da harshenta a irin yanayin. Amma sai aka samu akasin hakan a gareta. Da sauri sakatariyar ta ta fice cikin matuƙar sassarfa. Minti biyu basu rufaba sai gasu sun shigo. Matar dai da ka ganta kaga wadda ke'a cikin mawuyacin hali, sai dai da zata samu kulawa ƙyaƙyawar mace ce dirarriya. A lamarin Lulu da talaka a teburin aikinta kawai suke iya shan inuwa ɗaya, shima akan abinda ya shafi aikintane kawai babu ruwanta da rayuwarka. Har ƙasa matar ta kai ga alamun ciki da ya turo a jikinta zata gaida Lulu. Bata hanata durƙusawar ba amma dukkan hankalinta na gareta, sai kuma katseta da ga gaisuwar data fara da tai...
        “Kinga wannan gaisuwar baida amfani faɗamin ina yarinyar take?”.
    Cikin gyaɗa kai da share hawaye matar ta ce, “Tana gidan ƴar uwata da ta rakoni nan jiya, saboda yanda jikin nata yake ne ƴar uwar tawa tace na dawo yau ita ta kula min da ita”.
            “Wane police station kukaje domin kai ƙarar?”.
       “Na nan unguwarmu ne sai kuma da mukazo nan wajen ƴar uwar tawa itama ta kaimu na nan ɗin. Sai dai shima basu ɗauki abin da muhimmanci ba shiyyasa ta ce zata rakoni nan inda take da tabbacin za'a share mana hawaye. Hajiya dan ALLAH ki taimakeni kamar yanda ALLAH ya taimakeki. Yarinyar nan marainiya ce mutuwar mahaifinta ta sani auren wannan tsinannen da tunda na aure shi ban sake farin ciki a rayuwata ba......”
     Cikin jan tsaki da takaici Lulu ta katseta da faɗin, “Kika zauna da shi kuma har ya miki ciki. Malama ni ba rayuwar aurenki nake buƙatar ji ba. Ki tashi kuje zan haɗaki yanzu da wanda zaku sameni a asibiti”. Ta ƙare maganar tana miƙewa cikin matsanancin ɓacin rai. Waya takai kunnenta, da ga can aka ɗaga. Kirari aka fara mata ta katse da faɗin, “Musa ka sameni a office yanzu kai da Shu'aibu Please inada emergency case.”
          “An gama ranki ya daɗe”.
Musa ya faɗa ransa fes dan yasan yau aljihunsu zai kasance a cike. Dan aiki da Lulu yafi masa zaman cikin station aita kayan hamma balle tsaiwar kan titi amsar na goro. Ɗan rubutu tai a takardar data yago ta miƙama sakatariyar ta dake tsaye har yanzu. “Idan sun zo ki basu wannan, suje da ita sai su sameni a wannan asibitin dana rubuta. Kibasu 5k da zasu saka mai a mota”. Daga haka ta fisgi hand bag dinta da ɗayar wayarta da key tai waje...
Batako kalli sauran mutanen da ke zaune a inda table ɗin sakatariyarta ya ke ba ta fice. Taja ƙaramin tsaki lokacin da take dana unlock ɗin motar tunkan ta ƙarasa gareta. Bazata iya jure wannan zirga-zirgar tuƙin ba fa gaskiya. Dan tun farko ita dama ba gwanar sonyi driving bace. Cikin ƙara jan tsaki lokacin da take ficewa a gate ɗin ta dannama Uncle Yousuf kira. Sai da ta shiga ta tuna abinda ya faru jiya da wasan ɓuyan data ƙudiri aniyar farayi da shi. Da sauri ta rarumi wayar zata katse sai dai harya ɗaga. Babu alamar wasa a muryarsa ya ce, “Lafiya?”.
      Kamar ta fasa ihu haka taji, amma sai ta dake cikin pretending da ƴar shagwaɓa ta ce, “Uncle Barka da safiya. Dama no ɗin mutumin nan zaka turamin koka kiramin shi Please ya sameni a Shira's hospital”.
       Ɗan jimmm yay kamar bazai amsa mata ba sai kuma cikin dakewar da takan bata tsoro a Duk sanda yayita ya ce, “Wane mutumin?”.
           Yanzu kam sai da taji bugawar zuciya. Da ɗan rawar harshe ta ce, “Driver fa my papa”.
    Har zaiyi yi mata tambayar yaya akai bashi ya kaita office ba sai kuma ya fasa saboda tare ya ke da abokinsa Hameed. “K kina ina yanzu?”. Ya faɗa cikin goce tunaninsa.
       “Ina hanyar Shira's hospital ɗinne ”.
     “Sai kin ƙaraso”.
Ya faɗa kawai yana yanke kiran.......✍️
         



_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070


VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥



*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲




  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗



           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻


𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣9️⃣



........Kaɗan ya rage ta bugama motar gabanta. Tai saurin take birkin da ƙarfi. Ganin yanda mai motar ya dakata shima da alama fitowa zaiyi ya sata sake mata key tabar wajen da saurin dan ba wannan ne a gabanta ba yanzu. Tana hango zagin da mai motar ke mata cikin daƙuwa da wanda wasu ke mata na gefen titi. Oho basu bane a gabanta. Furucin Uncle Yousuf ne ke mata kai da kawo. Ji take kamar ta koma su canja asibiti sai dai ta riga kuma tace su Sha'aibu su sameta a can. Sannan yanda uwar ke nuna yarinyar na cikin mawuyacin hali maganar sakaci daga gare ta ma bata taso ba, dan a yanzu al'amarin su drivern ta ya shafe a zuciyarta yanda zata yaga rayuwar mijin matar nan kawai take ƙullawa. A wannan fanin ba'a gayyacesu ba ma taka rawa suke balle sune da bikin. Ai rawa sai kalar wadda sukaso takawa wlhy.....
         “Da gaske dai Uncle You na asibitin nan? To mi ha kawoshi?”. Ta faɗa a fili tana parking idanota akan motar Uncle Yousuf dan babu ta yanda za'ai motocin gidansu su ɓace mata. Cikin rashin sanin abinda take buƙatar sani ta fito a motar. Sai da ta leƙa motar Uncle Yousuf ta tabbatar babu kowa a ciki sannan ta bar wajen zuwa cikin asibitin. A reseption kuwa suka haɗu da Uncle Yousuf ɗin. Karan farko a rayuwa taji bazata iya haɗa ido da shi ba, tsoron ma haɗuwar tasu take yi. Musamman kuma yanda ya zuba mata idanun nasa duk sai ta nema daburcewa. Shi ya fara ɗauke idanunsa da ga kanta yana kai wayarsa da aka kira kan kunne. Hakan ya bata damar nufar inda ake yankar kati, sai dai kuma fa ko sunan yarinyar bata sani ba ma fa ashe. Cikin ɗan yarfar da hannu da juyawa gaba ɗayanta tai facing ƙofa ta ke faɗin “Ouhhh! Saurin banza ma ashe nake”. Dai-dai nan motar ƴan sanda mai ɗauke da matar nan da yayarta da yarinyar suka iso. Shigowar Musa ya sata sauke ajiyar zuciya, shi ya sanar da nurses cewar akwai mara lafiya a waje kafin ya ƙaraso gareta. Kallo ɗaya da Lulu taima yarinyar ya sata rumtse idanunta takalminta har yana gullewa sai da ta dafe kantar reseption ɗin.......

         “★“★ ∆ ★”★”

       “Ranka ya daɗe yaron nan fa daka tada hankalinka kansa ba wani ɗan kowa bane face wani mutum da ake kira Malam Mika'il Idris Mawashi a anguwar fagge. Shi kansa mahaifin nasa a iya layin nasu kawai aka sanshi balle shi. Kuma da gaske drivern yarinyar ne kwata-kwata bai ƙulla sati huɗu da fara aiki gidan Alhaji Isma'il Jiƙamshi b.....”
      “Kace Alhaji wa?!!”.
   Alh. Baita yay saurin tarar numfashin yaronsa da suke kira Goga a kamar razane da jin sunan Alhaji Isma'il Jiƙamshin. Bashi kawai ba hatta Hon. Nakowa da ke tare da shi dan tunda suka baro gidan MM Atik Kumo da ya basu aro anan gidan hutawar Alh. Baitan suka ƙarasa kwanan nasu. Shine tun da farar safiya kuma suka nemi babban yaronsu na bangar siyasa Goga suka sakashi binciko wanene Smart ta hanyar ɗan bayanai da suka samu ga Nadiya wadda itama ta samune ga Lulu randa taje saloon shagonta....
        “Alhaji Isma'il Jiƙamshi nace ƙwarai da gaske oga. Dan shine mahaifin ita yarinyar ma ai.”
      “Babbar magana ƴarsa ta cikinsa?”. Hon. Nakowa ya faɗa wani irin abu mai ma'anoni da yawa na tsirga masa tun daga saman kai har tsakkiyar ƙafafunsa. Cikin tabbatarwa Goga ya gyaɗa masa kai. Tare da masa ƙarin bayanin da zai gaskata hakan duk da shi bai san dalilinsu na jinjina sunan ba tunda shi dai a ɗazun yaga hankalinsu akan yaron yake ba ita yarinyar ba.
      “Kaga jeka”.
Honorable Babale ya faɗa cikin katse masa tunani. Dai-dai Goga na miƙewa ya sake faɗin ka jiramu a waje nan zamu nemeka.” shi dai da to ya amsa musu ya fice kamar yanda suka buƙata. Yana kuwa fita Hon. Nakowa ya firta, “Tabɗi jan inji mata. Dama ƴar iskar yarinyar nan ɗiyar Isma'il Jiƙamshi ce? Haba shiyyasa bata zubar a banza ba.” sai kuma ya wani ƙyalkyale da dariya alamar hakan ya masa daɗi ƙwarai da gaske. Shima Alh. Baita dariyar ya fara. Sai kuma ya buga ƙafa da faɗin, “In kere na yawo zabo na yawo tabbas faɗar masu iya magana watarana za'a gamu. Honorable Please kira mana Hon. Misau mana. Dolene ai wannan shagalin da shi”.
      “Ƙwarai ma kuwa”. Cewar Hon. Nakowa yana wani bula-bula da babbar riga wajen laluben wayarsa. Cirota yay tare da yin danne-danne ya kai kunnensa......

      Tofa masu karatu wata sabuwa kenan. Mi'a haɗin Daddy kuma da su Honorables?🤔.

          ∆★∆★∆★∆

    Tun bayan wucewar ɗan nasa yake ta faman kai kawo a lafiyayyen office ɗin nasa. Abubuwa da yawa ne ke masa sukur-sukur a brain game da buƙatar autan nasa a karo na biyu. Tabbas zai fi kowa farin ciki da ƙulluwar wannan auren dan koba komai dai Mawaddat ɗiyar ƴar uwarsa ce Mawaddat. Ƙanwarsa mafi soyuwa garesa a duk cikin ƙannensa. Wadda yasha bama sirrin al'amuransa batare da tunani ko jin ɗar ba har ALLAH ya ɗauki ranta. Zai kasance mai yin farin cikin ganin jininsa da nata sun zama abu ɗaya. Sai dai kuma matsalar itace Isma'il. Isma'il shine babban bakangizo mai razani da ya gitta a tsakkiyar wannan ƙaunar zumunta mai cike da ababen burgewa ga duk wanda zai iya jin asalinta da wanzuwar ta. Dan tarihin ratsawar Isma'il a cikin labarinsa dana ƴar uwarsa uwa ɗaya uba ɗaya ya juya akalar waccan ƙayataccen labarin zuwa ɗimautacce mara armashi a yanzu. Ata wani fanin kuma kamar zai zo da sabon armashin kansa da kansa dan labarin zai canja ne da ga na shi da ƴar uwarsa zuwa na shi da Isma'il Ibrahim Jiƙamshi mijin ƴar uwarsa da ƴarsa. Ƴarsa da yasan yana matuƙar ƙauna fiye da komai a rayuwa. Kafin yau da faruwar matsalar farko na tusguɗewar aure tsakanin Mawaddat da Tajuddeen labarin ba a haka ya tsarashi ba, sai dai yana ganin wata dama ce da zai masa editing dan ya zauna dai-dai da zamanin nan na 2023 a ajiye wancan ƙarnin dan ya koma tsohon yayi. Ya wani lumshe idanu da dunƙule hannunsa ya ce, “Yess!! Sulaiman Sufi Ado Garko kai mai nasara ne akoda yaushe. Isma'il Jiƙamshi sabon game, sabbin players and sabon stadium ka zama cikin shiri”.

       Wata sabuwar kuma dai🤔.

★★★★★

         Duk da a yanda take jin matuƙar gajiya bata huta ba har sai da doctors suka rufu akan yarinyar nan da lamarinta ya taɓa duk wanda ya ganta a cikin asibitin. Dan hatta Uncle Yousuf tuni ya ajiye batun takaicin Lulu gefe da shi akai komai na ganin likitoci sun tsaya a kanta. Abin tausayi ita uwar ma zuciyar ta bushe ko kukan zahiri ta kasa sai na zuci. Ganin komai ya natsa dan ana neman  uku na rana ma Uncle Yousuf ya kai dubansa ga Lulu da alamunta suka nuna gajiyarta matuƙa. Dan sai faman yamutse fuska take. Tausayi ta bashi, dan haka ya cigaba da kallonta a kaikaice cikin tausasawa da mata addu'ar shiriya akan halayenta marasa ƙyau. Isowar Ahmad wajen ta sakashi maida hankali garesa. Fuskarsa da murmushi yay ma Lulu magana, amma sai ta amsa masa a ɗan ɗage. Bai damu ba dan ya santa ya san halinta. Hasalima ya taɓa nuna sonta amma ta taka masa burki lokacin tana farkon dawowarta da ga Uk. Uncle Yousuf da yanda tai masa ɗin ya bashi takaici ya harareta, sai kuma ya maida hankalinsa ga Ahmad ɗin da ke faɗin, “Yaya ya farka, doctor ɗin ma ya sallamemu dan ya matsa zaije gida. Kasan Mawashi fa sam bai son asibiti.”
       Murmushin Uncle Yousuf yay, cikin yanayin tsokana ya ce, “Kai haba kamar wani yaro ko mace”.
          Dariya Ahmad yayi, dai-dai nan Smart ya fito a wani ɗaki da ke kusa da inda suke. Coach riƙe da hanunsa kamar wani ƙaramin yaro sai ɓata fuska yake. Dan da gasken fa bai son asibiti shi sam a rayuwarsa. Kuma bai san allura. Yanzu ma ba ƙaramar badaƙala akasha ba kafin ai masa shine ma Ahmad yay fushi ya fito. Ilai kuwa hararar Ahmad ɗin yayi tare da ɗauke kansa duk a lokaci guda, cikin rashin sa'a ya saukesu akan Lulu da tai kicin-kicin da fuska saboda kasancewar Ahamd a wajen, ita ala dole kar a kawo mata raini, dan duk wanda ya taɓa furta cewa yana sonta ko ya nuna basa ƙara

Please Login or Register in order to submit comment