Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ga kanki gaba ɗaya”
      “Hakan yayi, to amma Uncle kasan fa baba da shegen bin ƙwaƙwƙwafin abu idan kuma ya gano fa?. Sannan ma wa zamu iya samu ya mana wannan aikin batare da an samu wata matsala ba?”.
            “Eh kuma fa kema kinzo da maganar dubawa gaskiya. Dan Baba kam zai ma iya sawa ai masa bincike. To amma ina ganin mizai hana shi wanda zamu samar ɗin kawai ki yarda kuyi auren contract da shi, komai mune zamu tsara masa ayi auren amma bayan wata ɗaya ya rabu da ke, sai dai da sharaɗin kada kowa ma yasan ya sake ki har sai bayan wasu shekaru.”
      Shiru Lulu tai tana auna zancen Uncle ɗin nata. Sai dai da ace tana da ilimin addini da ya kamata tai hasashen yin hakan fa zai iya zama kamar ta zurma kanta ne. Amma a maimakon hakan ita wani tunani take da ban, dan tana ƙiyasta faruwar al'amarin ne cikin sauƙi kasancewar a inda ta girma cikin turawa wannan ba komai bane yin auren yarjejeniya.. ganin yanda tai nisa Uncle Yousuf ya katseta da faɗin, “Mawaddat bamu da wani isashen lokacin dogon tunani a yanzun fa”. Firgigit ta dawo hankalinta, sai kuma ta langaɓe kai cikin shagwaɓa. “Uncle You ni gaba ɗaya ma kaina ya kulle ne, dan ban san inda zan samo wanda zamuyi hakan ba”.
         “To mizai hana ki yarda da batun Tajuddeen kawai, yaron nan yanada hankali da nutsuwa ga ilimi. Yana aikinsa sannan yana matuƙar sonki”.
    “Uncle wlhy ni bana son sa, na tabbatar kuma bazan taɓa son shi ba. ALLAH idan aka matsamin kan na auresa zan iya halakash....”
        “No! no! Kar na sake jin haka. Tunda har baki sonshi shike nan kawai abar maganarsa. Mu koma kan maganar mu kawai ta nemo wanda zai zame mana makamin kuɓuta da ga Baba.”
     “Uncle bazan ɓoye maka ba wlhy na tsani duk wani abinda zai haɗa mu'mulata da wani namiji bayan ku, balle ma ace mu kasance wai ma'aurata. Impossible hakan ya kasance dan bazan taɓa aure ba.”
        Har cikin rai kalmar (Bazan taɓa aure ba) ta daki Uncle Yousuf, dan a karo na farko zuciyarsa ta fara hasaso masa wani al'amari mai girma dangane da Mawaddat ɗin. Dolene akwai abinda ya kamata su sani da ke ɓoye a ƙasan zuciyarta, sanin kuma na nufin haƙurin bin matakan daya dace. Wannan tunanin ya sashi cigaba da faɗin, “Mizai hana muyi amfani da Aliyu, dan yaron nada nutsuwar da bazai taɓa iya bamu ciwon kai ba koda anan gaba”.
       “Aliyu kuma? Waye shi?”.
     *_“DRIVERN KI”_*
  Fitar kalmar da ga bakinsa da zaburowar zuciyarta tamkar ragabzane a tsakanin jirgi da jirgi a sararin samaniya. Badan Uncle You bane, da bayan zaburar da tai abinda zai biyo baya shine lailayo masa zagi mai kawuna bakwai ta dire masa shi a tsaye sannan ta tisa da wanke fuskarsa da marin da sai ya hango yanda yaƙin duniya na uku zai kasance tun kafin lokacin faruwarsa. Sai dai kash furucin ya fito da ga bakin da ko harara bazata iya binsa da ita ba balle ɗaukar mataki. Uncle Yousuf da ya zuba mata idanu, sai dai a ƙasan ransa dariya ce ke cinsa yana dannewa da ƙyar yay mata nuni da kujera, tare da faɗin, “Sit mana kika wani zabura kamar wadda na faɗama mummunar magana. Nifa ba nace dole bane, shawarace kawai dan neman mafita. Amma idan batai miki ba muje kawai dan lokaci ma ya cika gashi ana jirana a office. Kije ki zama cikin shiri da yin sabon tunani akan wani tunda naga baki aminta da zancen shi Aliyu ba”.
       Bakin data tura gaba ta buɗe zatai magana sallamar Daddy ta dakatar da ita. Alamar zip Uncle Yousuf yay mata wai kar Daddy yaji. Daddy da gaba ɗaya ya gama jin tattaunawar tasu dan tun ɗazun a laɓe yake dama sai ya sake fuskewa cikin pretending ya ce, “Wai mi ake tattaunawa ne kuka shige haka shiru?”.
        Cikin ɗan ɗage kafaɗa Uncle Yousuf ya bashi amsa da “Sirri ne tsakanin baba da ƴarsa yaya”.
     Dariya Daddy yayi, sai kuma ya juya hanyar fita yana faɗin, “Oh to bari nayi nan tunda ba'a buƙatar naji”.
      A karan farko Lulu tai dariya tana mai kamo hannun Daddyn nata cike da shagwaɓa. A haka suka fito suna ƴar dariya.....

      Fitowarsu tayi dai-dai da shigowarsa gidan. Kamar ko yaushe sanye yake cikin ƙananun kaya da sukai matuƙar amsar jikinsa. Ƴar ramar da yay ta ciwo ta sashi zama wani fayau da shi a idon mai kallo. Cikin girmama juna ya gaisa da su baba maigadi sannan ya ƙaraso inda suke tsaye. Anan ɗin ma da girmamawa ya gaisa da Daddy da Uncle Yousuf. Lulu da ke gefensu tana danna waya tai jiran jin ya gaisheta amma sai taji shiru. Karo na farko ta ɗago idanunta ta kallesa tana mai sake tsuke fuska. Ƙoƙarin barin ma wajen yake alamar ita bazai gaisheta ba kenan. Wani irin tuƙuƙin baƙin ciki ne da takaici ya shaƙure mata wuya har taji tama kasa yin magana, sai dai yanda take binsa da wani mugun kallo ya sa Daddy farga da ita. Ya kuma fahimci miya fusatata ɗin.
      “Aliyu!”.
  Yay kiran sunan Smart da ke ƙoƙarin komawa inda su baba maigadi suke. Cikin girmamawa ya amsa yana mai juyowa garesu. Uncle Yousuf da ya sha jinjin jikinsa da tunanin ɓaranɓaramar da Yayan nasa ke shirin yine yay saurin faɗin “Am yaya inaga muje na ajiyekan tunda malam Zaidun bai dawo ba, in yaso daga can sai ya sameka Office ɗin. Aliyu zuwa 1:30 ku samemu a Nasarawa G.R.A please karku makara”.
        “In sha ALLAH Alhaji”.
     Smart ya faɗa cikin gyaɗa kai abubuwa da yawa na masa kai kawo a rai musamman da Uncle Yousuf ɗin ya ambaci Nasarawa G.R.A. Huci ya ɗan furzar kaɗan, a yanzun ma dai bai kalla inda taken ba ya nufi motar da mai wanki keta faman gogewa alamar ita zasu shiga. Baya ya buɗe mata, batare da ya jira tazo ta shiga ba ya koma mazaunin driver ya shiga yana karanto addu'ar shiga abin hawa. Harta ƙudiri aniyar ƙin shiga, sai kuma mita tuna oho mata ta tako cike da yauƙin nan nata da yanga ta shiga. Mai wanki ya maida motar ya rufe yana jera mata addu'ar dawowa lafiya. Motar yaja suka fice, zuciyarsa cike taf da abubuwan da suka faru jiya a waya tsakaninsa da Uncle Yousuf....
       A daren jiya bayan ajiye motar Mawaddat da ya kai sakatariyarta Zainab gida shima gida ya koma abinsa. Kai tsaye wajen Abba ya nufa suka gaisa, sun ɗan taɓa hira da Abban sai dai hirar batai masa daɗi ba sosai kasancewar da ga maganar Hawwah ta juye maganar aurensa. Sosai Abba ya dinga zuba masa faɗa akan infa har bai nemo matar aure ba a cikin watannan tofa shi zai nemo masa da kansa duk da ba aƙidarsa bace yima ƴaƴansa auren dole. Haƙuri shi dai yayta bashi da tabbatar masa cewa in sha ALLAHU zai kawo matar auren nan kusa. Kamar Abba ya gamsu da hakan sai kuma shigowar Umma ta sake saka Abban hayewa sama. Dan kamar wadda dama take a laɓe tana saurarensu tana shigowa sai kawai ta shiga assasa wutar kan cewar shi dai baiyi niyyar yin auren bane kawai. Inba haka ba baga yarinyar maƙwaftansu ba nan Nazifa yarinyar na matuƙar sonshi amma yaƙi saurarenta. Kallonta yay da mamaki, dan kowa dai yasan wacece Nazifa a anguwar. Yarinya ce mara jin magana dan tsabar bleaching fuskarta har yellow takeyi. Tabbas Nazifa ta jima tana nuna masa soyayya, sai dai shi bai taɓa nuna yasan mi takeyi ba. Kai shi ko magana tai masa ma da ga gaisuwa bai sake kulata. Wannan halin watsar da ita ɗin da yake yi yasa tun tana juriyar bibiyarsa har tai fushi ta daina kulashi. Amma da har abubuwa take saye ta aikoma Ammah ko ta bama su Asma'u. Nan ɗin ma dai bata samu nasarar ba dan Ammah tace ita babu ruwanta, idan yaga zai aureta bazata hana ba, za kuma ta bisu da addu'a dan koba komai yayi jihadin raba Nazifa da rayuwar banza da kowa ya shaida tanayi. Yanajin Ammah ta bada goyon baya ya samu Nazifa yay mata gargaɗi na ƙarshen ƙarni ya kuma yima Yayanta magana akan ta fita sabgarsa, shi kuma Yayan yaji haushi ya gaggaya masa magana  bai kulashi ba shi dai dan ya yanke magana. Da ga ranar bai san miya faru ba bai sake ganin Nazifa ba. Amma shine dan tsabar sharri Umma ke tisa zancen a yanzu bayan shekara kusan uku kenan da ajiyesa gefe. Tuni Abba ya ƙara tujaresa da faɗa amma baice komai ba akan Nazifa, hasalima ya fahimci kamar faɗan nasa na son zama zargi ne ko minene bai dai fahimta ba. Jiki a sanyaye ya baro wajen Abba, ɗakinsa ya nufa dan bai buƙatar zuwama Amma a wannan yanayin. Ya gama cire kayansa kenan zai shiga wanka kira ya shigo masa. Yayi mamakin ganin Uncle Yousuf, sai da ya kalli agogo ƙarfe kusan sha ɗaya da rabi fa. Haka dai ya daure ya ɗaga cikin taraddadi.........✍️
     



_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070


VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥



*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲




  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗



           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻


𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣7️⃣



........“Alhaji badai wata matsala bace ba ko?”. Ya faɗa maimakon sallama da Uncle Yousuf ɗin yay masa. Murmushi da ga can Uncle Yousuf ya saki tare da gyara zamansa a kujerar falon da ya fito. “Babu komai sai alkairi Aliyu. Wata magana ce mai muhimmanci tasa na kiraka. Ina dai fatan baka kwanta ba na tasheka ko?”.
      “Ina dai shirin kwanciyar ne Alhaji. Amma dai lafiya?”.
    “Eh lafiya kamar yanda na sanar makan”.
    “To Alhamdullahi Alhaji, ina saurarenka”.
   Ɗan jimmm Uncle Yousuf yay kafin ya furzar da huci kaɗan. “Aliyu shawara nake nema a wajen ka”. Cike da mamaki ya amsa da, “Alhaji shawara? Sannan kuma ma a wajena?”.
          “Eh Aliyu. Kuma ina fatan zaka bani wadda zata fiddani da ga ruɗanin da nake ciki” bai jira cewarsaba ba ya cigaba da faɗin. “Kasan na faɗa maka an taɓa sakama Mawaddat rana da Tajuddeen ai. Amma ALLAH baiyi auren nasu ba wasu matsaloli suka gitta, mafi yawansu da ga Mawaddat ne sai dai kuma akwai ɓoyayyen sirrin saɓani a tsakanin Yaya da mahaifin Tajuddeen da shima ya taka rawar gani. So an share maganar aure kowa ya haƙura, sai dai kakanta na ɓangaren mahaifiyarta Alhaji Sufi Ado Garko ya ɗauki alwashin duk randa wani yazo domin neman aurenta koda yardarta ko babu zai amince masa ya aurar da ita. Wauta ya sata amincewa. Bayan nan magana bata ƙara tashi ba sai a yau ɗin nan a gaban Alhaji Sufi ɗin, shi Alhaji Sulaiman ya sake kawo maganar, amma Yaya yayi saurin cewar ai Mawaddat nada wanda take so.........” Tsaf ya kwashe komai ya sanar masa har zancen su Hon. HD Nakowa da Daddy ya sanar masa suma sunje bayan barowarsu. Hakan ya matuƙar bashi mamaki dan tuna abinda ya faru a tsakanin Mawaddat ɗin da su Hon. HD Nakowa. Cikin kasa daure abinda ke bakinsa ya ce, “To amma Alhaji naga kamar ita da shi Honorable ɗin sam basa shan inuwa ɗaya. Taya zaije yace yana sonta da aure?”.
       “Muma shine abinda ya ɗaure mana kai Aliyu. Shiyyasa muka kasa zaune muka kasa tsaye akan al'amurin, dan Hon. Nakowa nada ƙarfi sosai a wajen Baba, saboda yaronsa ne, hasalima shine ya zame masa kamar wani ƙashin baya a harkar siyasa.”
     “To amma Alhaji mizai hana ku sasanta shi Alhaji Babba da mahaifin shi Tajuddeen ku aura musu juna kawai a wuce wajen”.
          “Hakan bazai yiwuba Aliyu. Dan ita Mawaddat sam bata son Tajuddeen, ta tabbatar min idan aka aura mata shi komai zai iya faruwa. Sannan abinda ke tsakanin yaya da mahaifin Tajuddeen abune babba bawai yanda kake zaton zai sasantu cikin sauƙi bane. Kaga ko maganin ayi zumunci ya wargatse ai Gara kar a fara ko”.
      “Hakane kuma Alhaji”.
   “To Miye mafita Aliyu? Dan Baba fa sam baya magana biyu. In har gobe idan ALLAH ya kaimu Mawaddat bataje da wanda take son aura ba babu fashi cikin biyu dole ayi ɗaya. Shiyyasa ma na kiraka domin neman taimako. Ina son idan ban shiga huruminka ba dan ALLAH Mawaddat ta nunaka a matsayin kai ne zaɓinta, da zaran Baba ya yarda a wajen shikenan. Ni kuma zanyi ƙoƙarin ganin ta fidda miji kafin Baba ya sake magana”.
         “Ni kuma Alhaji?!!”.
      “Eh dan ALLAH Aliyu ka taimakemu. A yanda rayuwar Mawaddat take yanzu muna buƙatar nutsuwa kafin sama mata mijin da zai saita mata rayuwa. Ni kaina bazan so ta auri Tajuddeen ba duk da nasan mutumin kirki ne amma bazai iya control ɗin ta yanda yake so ko ya kamata ba. Sannan Hon. HD Nakowa, kai ne shedar a inda ka gansu tare, maimakon gyaruwar Mawaddat aurenta da shi sai dai ya ƙarasa lalata ta kawai, shi kuma Baba duk bai san waɗan nan halayyar ba. Amma kaga idan muka kuɓutar da ita a wannan gaɓar sannu a hankali sai irin mijin da muke fata ya samu, kai kawai ta nunakan a gobe shine kawai dan Baba ya aminta ya bar waɗan can ɗin. Amma na baka damar kayi tunani, sai dai bamu da isashen lokaci daren yau ne kawai......
         “Wai kai malam ba magana nake da kai ba! Tsabar baka san muhimmancin rayuwa ba kana driving kana ma mutane tunaninka na iska!!”.
    Firgigit ya dawo hayyacinsa tamkar wanda aka tada a barci. Sam bai san tunanin nasa har yayi zurfi irin haka ba. Gefen titi ya gangara a hankali tare da kai hannunsa saman goshi ya dafe yana mai furzar da iska. Gaba ɗaya ma ba hanyar da ya kamata yabi da su yabi ɗin ba tsabar hankalinsa bama a tuƙin yake ba gaba ɗaya. Karan farko a rayuwarsa da tunda ya fara aiki matsayin driver ɗinta ya furta mata “Am sorry”. Cikin tausasa harshe kuma. Cak numfashin Lulu ya nema tsayawa a ƙirjinta. Haka ma maganar bakinta kasa ƙarasa fita tai tsabar kalmar ban haƙurin tazo mata a matuƙar bazatar da bata taɓa tunanin hakan da ga bakinsa ba kasancewar kallon da take masa mai shegen girman kai. Har ya sake tada motar da juyawa bata iya sake yin ko tari ba kamar wadda aka ɗinke ma lips. A nashi ɓangaren bai kawo komai game da shirun nata ba, a tunaninsa maganar Uncle Yousuf ce ta jiya ke damunta kamar yanda shima da ya kasance ɗan karoro kawai a ciki take neman jefa shi a ɗimuwa. Har suka isa office babu wanda ya sake magana. Kafin kuma ya fita ya buɗe mata har ta buɗe ta fice. Kallo ya ɗan bita da shi, dan duk da yau ma dai irin kayan daya tsani gani a jikin mace tana yawo kan titi ne a jikinta ɗan zoɓawar rigar da ga baya ya taimaka wajen suturta wani ɓangare na jikin nata. Janyewa yay tare da furzar da huci. Dai-dai nan Zainab ta fito ɗaukar mata kaya dan babu abinda ta ɗauka tai shigewarta. Ganinsa ya saka Zainab yin murmushi, ta risina cikin girmamawa ta ce, “Yaya ina kwana”. Kalmar yaya da ta kirashi da shi ce ta sakashi maida mata da murtanin murmushin nata itama. Cike da kulawa ya amsa mata kuma. Handbag ɗin Lulu da laptop da riga ta ɗauka sai wasu tarkacen takardu, shi kuma ya fito a motar tare da kulleta ya nufi security ɗin nan na jiya dan su gaisa.....
        
Duk yanda Lulu ta so fuskantar aikin gabanta hakan ya gagara. Abubuwa ne da yawa ke cizon zuciyarta musamman shawarar Uncle You da yace ta nuna drivern ta matsayin wanda take so a gaban Grandpa ɗinta. Kai ina a gareta wannan ai ƙasƙanci ne ma, kenan ma ya samu hanyar cigaba da kawo mata raini fiye da wanda yake son gwada mata a yanzu, dan ma dai ita tsayayya ce yana shakkarta. Kai maganar gaskiya shawaran nan na Uncle You baiyi ba sam. To amma a yanda guri ya ƙure ɗin nan idan ba shi ba wa zasu samo yay musu aikin batare da an samu matsala ba?. Wannan tambayar ita ta shiga cizon zuciyarta tama kasa iya aiwatar da komai na gabanta. Tana buƙatar shawara, gashi ƙawarta kuma Nadiya ce kawai da har take iya faɗama damuwarta. Kai ina bazata kira Nadiya ba, dan sai ta koya mata hankali. Kai anya ma bada saninta wannan tsohon kwandon Hon. Nakowa yazo neman aurenta ba? Lallai akwai lauje cikin naɗi, dan zuwa yanzu ta fara shakkar al'amarin Nadiya, ita shiyyasa fa bata ƙawa musamman da ya zam ƙawaye sun taka rawar gani suma wajen bar mata wani tabo a zuciya da har yanzu gyambonsa ke kan yin ruwa da mata ciwo. Kodai Uncle Yousuf zata kira ne tace ta fasa a nema wani? Aminta da wannan shawarar ya sata kiransa.
        “Lafiya dai ko Daughter!”.
    “Uncle you ba lafiya ba, shawaran nan ne yaƙi zama a zuciyata. Kodai mu nema wani can daban yay mana aikin nan, kasan fa bana son raini”. Murmushi yay da ga can har tana iya jiyo sautinsa. “Mawaddatan'warahma!”. A hankali ta amsa da “Da yes papa”. Dan tana matuƙar son ya kirata hakan.
       “Ki kwantar da hankalinki Please, sannan ku tuna bamu da wani isashen lokaci, a yanzu haka fa awowi kaɗanne suka rage mana dan za'ai amfani da ɗan break na lokacin sallah ne wajen zaman meeting ɗin kafin kowa ya koma office. A tunaninki a irin wannan tsukun lokacin wa zamu samu mai amana da hankali kamar Aliyu da zai mana aikin nan batare da wata matsala ba? Ko kina son mu ɗakko wanda zai mana baragada har Baba ya gane ya zartar miki da hukuncin auren ɗaya da ga cikin waɗan da baƙya son?”.
        “A'a Uncle You... ALLAH idan yace sai na auri wani a cikinsu zaku iya rasani dan na tsane su”.
      “To mafita ɗaya ce ta kufce musu shine bin abinda muka tsara. Shin kin san da yaya ma shi Aliyun ya amince zai mana aikin? Da ƙyar fa na iya shawo kansa wlhy”.
          A zuciyarta ta ce (kuji ɗan iya, dama ya samu aka sakashi zai wani kawowa mutane iyayi. Mtsowww banda ma dai wannan Grandpa ɗin da matsalarsa shi ko'a mafarki ya isa ma na kallesa balle wani kalman so can na wofi. Bari ana gama zaman nan korarsa zanyi dan karma ya ɗauka ya samu wata damar kawo min raini.....)
       “Hello Mawaddat! Kina jina kuwa?”.
   Ajiyar zuciyar dawowar hayyaci ta saki, cikin shagwaɓa ta ce, “Shike nan Uncle sai mun haɗu”.
       Dariya yay sosai daga can bayan ya katse kiran. Dan harga ALLAH dariya suke bashi. Dama yanzu ya gama waya da Smart ɗin shima. Haka kawai sun sakashi komawa lauyan dole. Ya tsara wannan ya tsara wannan. ALLAH dai ya bashi nasara burinsa ya cika akan abinda ke ransa game da su su duka biyun........✍️

     🥱Ba abun faɗa.



_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070


VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥



*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲




  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗



           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻


𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣8️⃣




.......Ƙarfe ɗaya da minti biyar ta fito da ga office saboda kiran da Uncle Yousuf yay mata da gargaɗin karfa su makara. Kamar ko yaushe babu kwalliya a fuskar tata, sai dai an toshe idanu da glass. Tabbas glasses na mata matuƙar ƙyau shiyyasa da wahala ka ganta babu shi, gashi bata saka ƙarami sai in zatayi aiki. Duk irin manyan nan ne na manyan mata masu ji da gayu. Shima ɗin dai kiran Uncle Yousuf ɗin ne ya sashi dawowa, dan tun kusan sha biyu ya wuce gida. Yanzu kam ya canja kayansa zuwa shadda ash color da tai masa matuƙar ƙyawun da har ita sai da ta saci kallonsa irin wanda bata taɓa yi ba. Dan tunda ya fara tuƙata bata taɓa ganinsa da manyan kaya ba sai yau har da su hula. Gaba ɗaya sai ya sake mata wani kwarjini da cika waje, dan haka ta sake jan girma tai tamau da fuska tare da ɗauke kai sama kamar bata gansa ba. Ita a dole kar waccan maganar tasa ya kawo mata wargi tunda Uncle Yousuf ya tabbatar mata ya sanar masa. Shima ɗin dai tasa fuskar a ɗauren take, dan baya son ta taresa da wata maganar banza, ta wani ɓangaren kuma ransa ne a ɓace, dan zuwa gidan nan da yay ya samu Umma na tujara harda yima Ammah gori akan ƙaddararsa wai a bincike wannan ƙin auren nasa sai dai idan yana samun abinda auren ne kawai zai iya bashi a bayan fage. Kenan tana nufin shi ɗin mazinaci ne. Bai san miya kawo rikicin ba, bai kuma shiga gidan ba yaji ba'asi tunda muryar Umman kawai yake ji, dama kuma yasan Ammah bazata tanka mata ba. Ganin Lulu ta dogare tana wani huhhura hanci irin na ubangida da yaronsa ne sashi jan ƙaramin tsaki ciki-ciki, batare da yace komai ba ya buɗe mata ƙofar, shiga tai fuska a yamutse, shi dai baibi takanta ba ya maida ya rufe sannan ya koma mazaunin driver.
       A hankali yake murza steering Lokaci-lokaci yana ɗan furzar da iskar takaicin kalaman Umma da sukai masa kane-kane a zuciya. Yayi nadamar zuwa gidan nan ma....

     Kusan lokaci guda suka iso da su Daddy, dan haka Uncle Yousuf ya dakatar da shi a gate, fita yay a tasu motar yazo inda suke. Lulu da keta ɓata fuskar shagwaɓa ya kalla. “Mawaddat ya haka kuma? Maza koma gaba karma wani ya ganki”. Zatai magana yay mata nunin tai shiru kawai ta koma. Fitowa tai baki a sama ta koma gaban, kusan a tare ƙamshin turaren junansu ya daki hancinansu duk da dama tun ɗazun suke shaƙar. Shi dai baice komai ba, hakama Uncle Yousuf ya koma tasu motar shima, sun samu ƙaton compound ɗin gidan cike da motoci, ya dai samu gefe yay parking. Hango Uncle ɗinta Khamil na Abuja ya sata sakin murmushi, cike da zumuɗi ta buɗe motar ta fita.... Baki ya taɓe tare da ɗauke kansa. Sai ma ya lumshe idanunsa kamar mai shirin barci tare da kwantar da bayansa a jikin kujerar yay luf...
      Suna shiga aka fara taron dan kamar sune dama na ƙarshen zuwa. Ana tsaka da tattauna batun Tajuddeen ɗin da Lulu da aka kira amma ta botse musu akan ita fa bata son Tajuddeen, shi ko ya marairaice fuska kamar zai fashe da kuka yanata faman mata alamar roƙo amma tai kamar bata gansa ba. Takaici ya saka Alh. Sulaiman fara zagin Mawaddat ɗin, ana hakan saƙon isowar su Hon. Nakowa ya iso falon. Damar shigowa Baba ya basu. Su ukune kamar dai jiya. Shi mai gayya mai aikin Hon. HD Nakowa da aminansa Hon. Misau da Alh. Baita. Bayan anyi gaisuwar mutunci tsakaninsu da su duk da Alh. Sulaiman yayi mamakin ganinsu a gidan nasu Baba ya gabatar da su da dalilin

Please Login or Register in order to submit comment