Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ashirin da huɗu tana cikin ta biyar, mai karatun matsayin cikakkiyar lauya da duk wanda ta tsayama a shari'a zai iya alfahari da itace babu wata ƙyaƙyƙyawar alaƙa tsakaninta da UBANGIJINTA a ɓangaren bauta masa irin haka. Wane irin sakaci sukan sukai da shagala akan al'amarin yarinyar nan har haka?.....
        “Uncle You! please kayi haƙuri kar kai fushi da ni”.
    Kalamanta cikin damuwa suka katse masa tunani. Tuni ta rarrafo gabansa ma hijjab ɗin na harɗeta batare da ya sani ba. Idanu kawai ya zuba mata dan shi kam tausayi ma take bashi wlhy. Shi mutum ne mai zafi amma kuma yana da saurin sauka da kuma sauƙin kai shiyyasa yaran ɗan uwan nasa ke sonsa, dan ya taso ne kamar duk shi ya raine su. A hankali ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi. Muryarshi a rissine bakamar ɗazun ba ya ce, “Mawaddatan-wa'rahmah!”.
        A hankali ta ce, “Yes Uncle”.
   “Mi kikayi haka?”.
“Uncle salla mana da kace”.
“Bani nace ba ALLAH ne yace ayi kuma ba haka akeyi ba. Mawaddat wannan ranar ita nake gudun zuwa gareki shiyyasa nake zaneki idan kikaƙi zama Islamiyya a shekarun baya kafin abar ƙasar nan da ke, shiyyasa kuma na dage a nema miki malamin da zai koyar da ke addini bayan Yaya ya maidaki can. Yanzu ace kamarki, ɗiyan musulmi hausawa ƴar ƙasar Nigeria a arewa amma baki iya salla ba? Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un. Mawaddat da duk mi kike yi ke kuwa a duniyar nan haka? Mi kikaima kanki tanadi na tunkarar UBANGIJI da har kikejin ƙwarin gwiwar baje kolinki a duniya da abinda ke cikinta kawai? Anya kin yarda zaki mutu kuwa? Za ki kuma kwanta kabari? Za kuma a tasheki? Za'a kuma miki hisabi sannan ki ƙarɓi sakamakon makomarki?. Makomar da gida biyune kacal dole kuma ka tsinta kanka a ɗaya wuta ko aljanna.........”
       “Uncle Please kabar zancen mutuwan nan mana. Badai sallan bane kuma nayi. Kaga inama da zuwa court zuwa ten ga shi har nine na neman wucewa.”
    “Wato shi zancen sallan baida muhimmanci ko?”.
    “Noo Uncle You! Bance ba fa. Kawai dai ni.....”
    Sai kuma tai shiru. Kansa kawai ya girgiza dan y fahimci ba irin wannan zaman na kai tsaye Mawaddat ke buƙata ba. Yana buƙatar yin nazari akan al'amurinta kafin ya nemo mafita mai ɓullewa. Da hannu yay mata nunin ta tashi da faɗin, “Okay jeki shirya”.
     “Yawwa Sweet Papa na!!!”.
Ta faɗa da ihu tana miƙewa. Kansa kawai ya girgiza yana mai karanto mata addu'ar shiriya wajen UBANGIJI kamar yanda ya saba akoda yaushe ya tashi ya fice dan bata damar yin shirin....

∆•••∆ ★ ∆•••∆

    Da ƙyar ya iya buɗe idanunsa da sukai masa tsananin nauyi ya fara bin inda yake da kallo. Falo ne babba mai ɗauke da kaya na alfarma. Sai garadan samari guda biyu dake tsaye a kansa da alama sune suka ajiyesa a wajen. Akan mutumin dake zaune cikin kujera mai zaman mutum ɗaya ya tsaida idanun nasa. Shima kallonsa yake yi. Fuska ya ƙara tsukewa tare da kauda kansa, babu alamar tsoro tattare da shi ya ce, “Su waye ku? Mi nakeyi anan?”.
      A karo na farko mutumin yay murmushi har ana iya jin sautinsa. Kansa ya jinjina da faɗin, “Abinda duk aka faɗamin game da kai naga fiye ma da hakan. Sanin ni wanene gareka baida amfani. Abinda ya kawoka nan kuwa shine aiki. Idan kaso zaka iya ɗaukarsa a business ɗin da zaka ƙaru kaima, idan kuma kai tunanin bijirewa ko cigaba da wannan zafin kan naka to komai zai iya faruwa. Sunanka shine *_Aliyu M. Idris Mawashi._* Mata huɗu ne a gidanku ƴaƴa talatin da biyu. Mahaifiyarka itace ta farko a wajen babanka, ku biyar ta haifa ɗaya ya rasu. Kai kaɗaine namiji biyu sunyi aure kanada kanne mata biyu yanzu haka Maryam da Asma'u. Yanzu haka suna a ajin karshe a sakadire, islamiyya suna ajin hadda. Babbar yayarka na auren Alhaji Abubakar Azare itace amaryarsa. Bata sonshi mahaifinku ya haɗasu, yaranta biyu duk maza. Kanwarka dake bimaka tana auren abokinka Sa'id Ibrahim, yarinyarta ɗaya da ciki. Kana cikin matsanancin rayuwa sosai akan al'amuranka daba sai nayi zaman lissafasu ba ka sansu kaima”.
       “Daka sanni har kamar haka, amfanin mi zai maka?”. Uncle Smart ya faɗa cikin zafin rai.
   Ƙaramar dariya mutumin yayi yana wani ɗage kafaɗa. “Amfani masu yawa kuwa, ciki harda abinda zuciyarka bata kawo maka ba. Dan duk wanda na buƙaci alaƙa da shi dole ne ya amince min. Inba haka ba zai fuskanci abinda babu shi a lissafin rayuwarsa. Idan kuma ya amince lafiya zamuyi mu gama cikin mutunta juna na ƙaru ya ƙaru”.
      “Sai kuma gashi ni ba'aimun barazana?”.
    “Ba barazana nake makaba nima. Ina faɗa maka abinda zan iya yine koda a yanzu ne da kake gabana. Aliyu Mawashi! Ko nace Smart Mawashi ni bana faɗar abinda bazan yi ba. Idan na faɗa maka zanyi to na gama shirya yanda zanyi ɗin ne. Ka kwantar da hankalinka aikin da zakamun bamai wahala bane ba, sannan kaima zaka fita a ƙangin damuwar rashin abunyi da kake a ciki, maybe ma ka tsallake ƙasar nan insha ALLAHU a wannan karon ka samu cikar burinka. Mahaifiyarka ta samu kwanciyar hankali da samun salamar hantara daga kishiyoyi da miji, rayuwar ƙannenka ta inganta kamar yanda kake fata. Mahaifinka ya cire zargin da yake maka da fifita ƴan uwanka a samanka duk da bawata tsiya suma suke tsinana masa ba.....”
      “Waye kai?”.........✍️


*_Ku ƙara haƙuri dani dan ALLAH. Idan na ɓalle typing har sai kunce ya isa haka in sha ALLAHU🙏😩_*



_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070


VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥



*_ALLAH ya gafartama iyayenku😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲




  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗



           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻


𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 9️⃣


........Dariya sosai Alhajin ya kwashe da shi. “Karka damu da sanin ni wanene saboda nasan kai waye? Sanin aikin da zakai min kawai ne yafi muhimmanci. Dan na sanka fiye da yanda na faɗa maka a yanzu. Kaɗan na tsinkulo a sanin danai maka kawai. Gidan daka ajiye aiki nake so ka koma ka cigaba da min aiki. Duk wata zan baka albashin naira dubu hamsin bayan albashin da su suke baka dubu ashirin”. Ya ajiye masa wani envelope gabansa da cigaba da faɗin, “Wannan shine kundin ayyukan da zakamin a gidan Alhaji Isma'il Jiƙamshi. Zan iya baka dama ta kwana ɗaya kaje kayi tunani, sai dai ka sani ko'a cikin ɗakinka idanuna a kanka suke, dan haka da zuciyarka kawai nake buƙatar kayi nazari. A duk sanda nake buƙatar magana da kai zan nemeka tanan” ya ajiye masa waya akan envelope ɗin daya ajiye gabansa. “A yanzu bana buƙatar cewarka anan, kaje kayi nazarin na barka lafiya. Ku maidashi”. Ya ƙare maganar da duban yaransa cikin bada umarni
       Da wani irin kallo mai nuna tsananin zafin zuciya Uncle Smart ya bisa. Sai dai da alama ran ƴan maza ya ɓaci dan ya kasa furata komai.....

        Kamar yanda Alhajin ya bada umarni sun maidoshi har kan titin anguwarsu. Kasancewar magrib yayi a gurguje ya ƙarasa gida domin watsama jikinsa da yay nauyi ruwa. Ya samu wasu daga cikin samarin ƙannensa sun dawo gidan. Wanda ya samu a waje suka gaishesa. Da hannu ya amsa musu kawai ya shige ɗakinsa. Shi mutum ne mai tsafta sosai da ƙwanƙonin tsiya, dan haka ganin ɗakin a yanda ya barsa ya sashi jan tsuki yana ɗan dafe kansa dake masa ciwo. Har yanzu abinda suka shaƙa masa bai gama sakin masa jiki ba. A karan farko ya laluba aljihunsa neman wayarsa, cikin sa'a ya jita. Ƙanwarsa Maryam ya kira, suna zaune a falo suna karatun Alkur'ani kiran ya shigo, cike da zumuɗi Asma'u da wayar ke'a gefenta ta ce, “Lah Yaya ne”. Kallonta Ammi da Maryam ɗin duk sukayi, ita kuma ta ɗaga da sallama. A hankali ya amsa mata cikin muryarshin nan a dake da wasu ke fassarawa da girman kai da suke kallonsa da shi saboda shiru-shirunsa, batare daya bata damar cewa wani abu ba ya cigaba da faɗin, “Zan samu ruwan zafi a wajenku?”.
       “Eh Yaya”.
Ta amsa masa cike da girmamawa. Tana ajiye wayar Maryam tace, “Ya dawo ne?”. Kai ta ɗaga mata da faɗin, “Ya dawo, cayay na kai masa ruwan zafi, inaga wanka zaiyi”. A hankali Ammi ta sauke ajiyar zuciya, sai dai batace da su komai ba ta cigaba da laziminta. Tun safe hankalinsu ke'a tashe, dan bai shiga gidan gaishesu ba kamar yanda ya saba. Da farko Ammi tayi zaton koya fita wani uziri ne, sai da ta shiga gaida Abba ya yanka mata baƙar magana son ransa, kamar yanda ta saba yin shiru akan ƴaƴanta idan yana faɗa haka yanzu ma ta haɗiye, sai da ya gama ta bashi haƙuri, sai dai furucinsa akan zai bar masa gida ya matuƙar tayar mata hankali, har ta aika Maryam kira mata shi ko yana ɗaki amma suka samu baya nan ɗakin ma a buɗe, neman number sa ta shiga yi amma sai ba'a ɗaga ba, daga ƙarshe ma ta daina samunsa. Da wannan damuwar ta yini yau ita dasu Asma'un.
        Koda Asma'u takai masa ruwan zafin sai da ta gyaro masa toilet sannan ya shiga, ɗakin ta shiga kimtsa masa shima. Kafin ya fito harta kammala ta fice. Kasancewar anyi sallar magriba yay tashi a ɗaki sannan ya fice massalaci yin isha'i. Bayan an idar gidan ya sake komawa. Abba bai shigoba, dan haka ya wuce cikin gidan. Kamar yanda ya saba sai da yabi duk ɗakunan matan gidan ya gaidasu. Da ɗakin Aunty Amarya ya fara. Mace ce mai yawan fara'a da son mutane, sai dai kuma bata da yawan magana itama. Duk da zai iya sa'anni da ita hakan bai hanashi girmamata saboda yanda take girmama Ammi a gidan itama kamar ba kishiya ba. Ya gaidata cikin mutuntawa, ta amsa masa da kulawa. Yaranta dake sabgogin gabansu a falon tun shigowarsa duk suka nutsu dama. Duk sun gaidashi, yayinda ƙaramar tazo jikinsa tana kawo masa ƙarar ɗan uwanta dake bima babbar ɗakin nasu cewar ya karya mata pencil ɗinta tana homework. Da sauri yaron mai suna Abbas ya ce, “Yayanmu ƙarya take ita ta karya abunta a makaranta suna faɗa da Ameer. Kuka ta saka itama tana faɗin, “Ƙaryane Yaya shine”. Hannu ya ɗaga musu duk sukai shiru. Aunty Amarya tace, “Ai inba ubansu kaci ba Yayansu ba barin kunnen mutane ya huta zasuyi ba. Tun ɗazu suke rikicin nan ni harna gaji ma da magana”.
      Faɗa yama yaran cikin sigar nasiha, yace da safe kafin su wuce makaranta Anisan tazo ɗakinsa ta amshi sabon pencil. Da ga haka ya fito zuwa ɗakin Umma. Itace ta biyu a gidan, amma itace mai manyan ƴaƴa a sakamakon rashin samun haihuwa da Ammah bataiba da wuri, kusan duk sunyi aure kuma. Sai dai tanada sauran ƴammata biyu a yanzu haka da samari biyu da basuyi aure ba. Ta amsa masa a ɗan fisge, bai damuba dan hakan ba sabon abu bane a garesa. Nusaiba autarta dake gefenta zaune tana cin abinci ta gaidashi itama. Amsa mata yayi yana miƙewa. Dakatar da shi Umman tayi da faɗin, “Yau lafiya kuwa bamu ganka da safe ba?”.
    Ɗan murmushin ƙarfin hali yay mata da faɗin. “Ba komai Umma na fitane da safe sosai wani uziri”.
     “Uhhm to yayi”. Ta faɗa a taƙaice.
     Iska ya ɗan furzar da ga bakinsa kawai ya miƙe yana ficewa. Ɗakin Mama ya nufa, mace ta uku a gidan, sai dai ya samu tana sashen Abba dan itace da girki yau. Mansur ƙaninsa ɗanta na huɗu kawai ya samu a falon da yarinyar ƙanwarsu (jikar gidan) tana barci a kujera. Gaishesa Mansur ɗin yayi yana wani nannoƙe kai na rashin kunya, sai dai babu damar yi dan suna tsoronsa a gidan ba kamar sauran yayunsu maza da suke iyama rashin kunya ba. Amsa masa yayi yana kallon askin kansa na rashin tarbiyya.
      “Idan na wayi gari na ganka da wannan askin bisa kai kayi kuka da kanka”. Daga haka ya fice. Baki Mansur ya tura gaba yana ƙunƙuni da yarfa hannuwa. Sai dai babu damar yi da ƙarfi.

      Ammah na zaune su Maryam a gefensa suna cin abinci da kallo film ya shiga da sallama. A tare suka amsa masa da gaishesa cikin girmamawa. Ya amsa musu da kulawa yana kaiwa zaune. Ammah ya gaida da bata haƙurin rashin shigowarsa da safe. Dai-dai nan Maryam ta ajiye masa abinci da fure weter. Ɗakinsu suka shige da abincin dan sun san akwai magana a bakin Ammah. Suna shigewa kuwa ta dubesa da ɗauke kai ta ce, “Lafiya ka fita tunda safe?”.
       Samun kansa yay da faɗin, “Lafiya lau Ammah naje wajen aiki ne”.
        A hankali ta sauke numfashi. “Nasan ba son aikin nan kake ba Hydar. Sai dai mai haƙuri yakan dafa dutse har yasha romonsa. Kafi kowa sanin yanda gidan nan ya koma yanzu, miyasa bazaka sakama kanka haƙuri da mutane ba ka karɓi rayuwa a duk yanda tazo maka. Kowane bawa daka gani akwai irin tashi ƙaddarar, amsarta da haƙuri kuma shine mizanin imani. Zuwa yanzu yakamata ace kun bar mahaifinku ya huta dako ciyar da kune, shekarunsa yaja yana buƙatar hutu na rayuwa dana jiki. Yasha matuƙar ɗawainiya da ku tun kuna ƙanana har girmanku, bai tauye kowannenku ga ilimi ba da ci da sha da kula da lafiyarku har girmanku. A yanzu kune ya kamata ace kun rungumesa shima tare da ƙannenku da suka rage a gabanmu, dan wataran kune zaku maye gurbinmu garesu a yayin da ƙasa ta rufe idanunmu”.
        Gaba ɗaya jikinsa ya ƙarayin sanyi da nasihar mahaifiyar tasa. Idanunsa sun kada sunyi ja, cikin gyaɗa kai da tausasa harshe ya ce, “Inasha ALLAHU Ammah zaki sameni fiye da yanda kike buƙata. Kuyita haƙuri damu kuma kuci gaba da mana addu'a”.
    “Addu'a kullum cikin yimuku muke babu fashi”.
    Sun cigaba da hira da mahaifiyarsa da ƙanensa da suka fito ya nuna musu assagment har zuwa ƙarfe tara da kusan rabi sannan ya fito. Ɗakinsa ya koma dan yasan yanzu Abba ya riga ya kwanta. Sai da yay shafa'i da wutiri ya samu kwantawa, abinda ya faru a yinin ya shiga dawo masa dalla-dalla. Envelope ɗin nan ya ɗakko ya fara dubawa. Takarda ce kawai a cikinsa ɗauke da rubutu mai ɗan tsaho, abubuwan da aka rubuta ɗin ya matuƙar bashi mamaki harma ya rasa wane kalar tunani zaiyi a kai. Shi dai har yanzu babu abinda zai iya ƙaraswa akan Jiƙamshi family na ƙwarai ko akasinsa. In ma akwai abinda zai iya faɗa to maybe akan wannan ballagazar yarinyar ne ta jiya, siririn tsaki yaja saboda tunota da yayi. Takardar ya yasar gefe ya kwanta yana mai lumshe idanunsa dake cike da barci......

    _______________________★

        Washe gari da abubuwa da yawa ya tashi a cikin rai. Mafi girman jagorantar ƙarfin gwiwar sa nasihar Ammah, sai kuma wani dalili nasa akan mutumin jiya da son sanin manufarsa ta haƙiƙa, dan yasan in ma bai amshi aikin ba zai iya saka wani yay masa, shiko duk da bai gama sanin suwaye Uncle Yousuf ɗin ba sai yaji bazai iya sakacin barin ƙofar da za'a cuta musu ba har sai yasan gaskiya a kansu. ƙarfe bakwai da kwata a gidan Uncle Yousuf ɗin yay masa. Yana zaune a gate wajen maigadinsu suna ƴar hira kasancewar mutumin Dattijo ne nutsatstse mai aikinsu ta kawo breakfast. Cikin girmamawa ta gaidashi shi da maigadin. Hannu kawai ya ɗaga mata ya ɗauke kansa. Harta juya zata koma maigadi ya tsayar da ita da tambayar Alhaji ya fito ne?.
      “A'a nadai ji aunty na batun tadoshi an kirata a waya wannan masifaffiyar aunty Lu suke kiranta ko ta gidan Alhaji Babba bata da lafiy.....”
    Bata gama rufe baki ba sai gashi ya fito kamar a ɗan rikice. Tun daga nesa ya ƙwalama maigadi kiran ya buɗe masa gate. Miƙewa maigadin yay da hanzarinsa, hakan yasa Uncle Smart ɗin shima miƙewar ya nufesa. Ganin yanda ya daburce yama kasa tantance motar da ya ɗakkoma key yay masa sallama. Juyowa yay ya ɗan kallesa, har ya ɗauke kai sai kuma ya sake jiyowa.
      “Alhamdullah” ya faɗa yana miƙo masa key ɗin batare daya tuna cewa yanzu fa ba ƙarƙashin su yake ba. Babu musu ya amsa key ɗin, dannawa yay motar tai ƙara, dan haka ya nufeta. Sai da ya dai-daita ta sannan, yana batun fitowa ya buɗe masa yaga ya buɗe gaban motar ya shiga yana faɗin, “Yi sauri Please da alama abun babbane, dan duk ciwon Mawaddat da zai iya saka Aunty Kareema ruɗewa irin haka ba ƙarami bane ba”.
         Gudu kawai ya ƙara batare da yace komai ba dan ba fahimtar akan wa ake maganar yay ba shi dai. Bawani nisane tsakaninsu ba, dan layinne kawai ba ɗaya ba.........✍️


_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070


VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥



*_ALLAH ya gafartama iyayenku😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲




  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗



           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻


𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 🔟


........Ko parking bai gama yi da ƙyau ba Uncle Yousuf ɗin ya fice, ba'a rufe mintuna biyar cikakku ba sai gashi ya fito ɗauke da Lulu yaran gidan biye da shi cikin tashin hankali. Shi ya buɗe masa motar, sai lokacin ma yasan itace. Wani iri yaji a ransa musamman tuna abinda akace game da ita a takardar jiya da Alhajin nan ya bashi. Da wannan tunanin yaja motar suka fice a gidan. Kai tsaye wani babban p-hospital mai suna *_SHIRA'S HOSPITAL_* suka nufa. Yanda aka tarbesu zai tabbatar maka da an san da su. Har yay zamansa a mota sai kuma ya fita yabi bayansu, dai-dai nan suma ƴan gidansu da suka biyo bayan su motarsu ta iso cikin asibitin.

       Duk wani kai kawo da ake a kanta shi dai nashi ido ne. Yayinda acan ƙasan zuciyarsa yaketa tufƙa da warwara akan abubuwa da dama. Musamman akan abinda ya dawo da shi aiki cikin wannan family ɗin a karo na biyu. Tabbas ya amshi aiki, sai dai kuma bada manufar wanda ya bashi aikin ba. Dan ko kaɗan baiji wani kurari daga gargaɗinsa sun tsoratashi ba. Hasalima shi wanda ya bashi aikin da yasan shi ɗin wanene maybe dabai bashi ɗin ba. Amma zaiyi, dan in bai amsa ba zai bama wani da zai iya masa yanda yake so... Ringing ɗin wayarsa ne ya katse masa tunani, ya ciro wayar daga aljihu yana miƙewa ya fito. Sallama yay bayan yakai wayar kunnensa, daga haka bai sake magana ba sai saurare. Bayan ya katse kiran ya cire wayar a kunnensa yana furzar da iska kaɗan. Cike da iya nazari yake bin farfajiyar asibitin da kallo a kaikaice, can idonsa ya sauka akan abinda yake nema. Basarwa yay ya share na wasu mintuna, kafin ya nufi fita gate ɗin a nutse. Dai-dai inda almajirai ke zaman bara ya dakata, naira ɗari biyu dake aljihunsa ya ciro ya saka a kwanon barar wani gurgun almajiri dake kan katako mai tayu, almajirin ya shiga jera masa addu'a. Yana ƙoƙarin juyawa matashin saurayin dake gefensa kaɗan yazo ta gefensa suka bangaji juna, kallon juna sukai kamar cikin jin haushi. Sai dai shi saurayin yay saurin faɗin, “Yi haƙuri abokina ban lura bane ba”. Kai kawai ya kaɗa masa yabar wajen batare daya tanka ba.
      Maimakon komawa cikin asibitin sai ya samu waje a harabar ya zauna abinsa, can kusan mintuna uku yay ƙoƙarin ciro wayarsa a aljihu sai yaji takardar da saurayin nan ya saƙala masa a aljihu sanda sukai karo batare da ya lura ba. Zarota yay ya warware cike da mamaki, sai kuma ya shiga ɗan waige-waige amma babu alamar saurayin ko wani da zai ce hankalinsa a kansa yake.
        _“Ni kamar iska nake, a duk lokacin data kaɗa sai anji sautinta a dukkan ƙofofin gashi na jiki. Idan kuma nai shirin zuwa waje matsayin guguwa tarwatsa komai da kowa na gari nake hatta ruwan kogi baya tsira da ga mamayata. Ka kula, in ba hakaba ni na ƙulleka a cikin ƙullina Aliyu Hydar Mawashi”_.
     Wani irin tashi tsigar jikinsa ta farayi na ɓacin rai. A take zuciyarsa ta fara kaikawo da sauri-sauri cikin ƙirjinsa. Takardar ya ninke ya maida aljihu, yana batun tashi waya ta sake yin ringing a jikinsa. Wayar dai da Alhaji nan ne ya bashi jiya, yana kuma ƙyautata zaton takardar nan ma da ga garesa take duk da ya kirashi ne ɗazun a wayarsa. Shi sam yama manta da wayar. Cirota yayi daga aljihun, kamar bazai ɗaga ba sai kuma miya tuna ya ɗaga tana gab da tsinkewa ya kai kunne. Baiyi magana ba daga can ma akai shiru, ganin ana neman shafe minti guda ya katse shirun da faɗin, “Inada abinyi fa Malam”.
     Ƙaramar dariya akai daga can tare da faɗin, “Wannan girman kan naka da gizago kesani ƙara jin ka dace da buƙatar aikina Smart Mawashi. Mutanena sun sanar min ka koma aiki, weldone daka kasance mai biyayya irin haka da saurin gane abu....”
           “Na koma ne badan kurarinka ko farfagandarka ba! Ko a tunaninka sakawa ana bibiyata da kawomin wasu banzayen saƙwanni a takarda ko kiran wayata zaisa nayi abinda kake so?”.
    Ya faɗa cikin katseshi murya a dake. Dariya akayi da ga can, Alhaji ya ce, “Muɗauka haka ɗinne to. Sai dai ka sani ni samaniya ne mai rufe rufin kowanne gida da daji. Abinda kaga ya faru har ya kawoku asibiti yau ka ɗauka shine signing na contract ɗinmu da kai. Ya rage naka ka fara aiwatar da ayyukanka yanda ya dace ko kai kuskuren nunamin zafin kai na cigaba da nuna maka sauran kalolina. Dan a duk inda Jiƙamshi family suke ni nan da kake ji da gani zagaye nake da su har a cikin ɗakin kwanansu, har ma da kai kanka a yanzu....”
     Baki ya buɗe zai yi magana ƙittt aka yanke wayar, da sauri ya cirota daga kunnensa, ƙoƙarin kiran layin ya shigayi sai dai yaƙi shiga, ya koma wajen massage danya tura sai ya gama babu app na massage a wayar kwata-kwata. Cikin tsarguwa ya ɗan fara dube-dube, sai dai babu alamar wani da hankalinsa ke a kansa a eriya ɗin wajen gaba ɗaya. Wayarsa ya ciro ya kwashe number da zummar yin kira sai dai kuma taƙi shiga, wadda aka kirashi a farko ya gwada kira itama taƙi shiga. Yay ɗan shiru ransa a dagule, tunanin kiran wani abokinsa yay da zummar masa tracing layukan sai kuma ya fasa saboda tuna maganar mutumin. (A duk inda kake idanuna a kanka suke koda a cikin ɗakin barcinka ne). Fasawa yay ya maida wayar aljihu yana jin zuciyarsa ta masa nauyi da tunani kala daban-daban. 

        Gaba ɗaya wannan yinin haka ahalin Jiƙamshi gaba ɗaya suka yisa a asibitin tare da shi. Bai yi yinƙurin komai akan son sanin abinda ke damunta ba. Yana dai biye da motsin kowa har zuwa azhar da Uncle Yousuf ya buƙaci ya kaishi gida zai ɗan watsa ruwa. Sai da suka hau hanya yake tambayarsa ya mai jiki. Cikin damuwa Uncle Yousuf ya ɗan furzar da nannauyar ajiyar zuciya tare da dafe kansa ya ce, “Da sauƙi za'ace, dan tunda muka zo sai yanzu ne aka samu kanta har barci ya ɗauketa. Shiyyasa

Please Login or Register in order to submit comment