Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

*💖ABNUR💖*

By maimoon🤓

Elegent Online writers

*Free book* page 1



Bismillahi ar-rahmani ar-raheem_______

Hasken farin watan daya haske illarin garin shiyake bata daman ganin inda take sanya ƙafafuwanta gabaɗaya she is not in her right senses tafiya kawai takeyi ba tare da tasan inda ta nufaba

Tafin hannunta ta sanya ta share hawayen da ya zubo mata a karo na ba adadi she really wish all dis was a dream cigaba da tafiyan kawai takeyi a ƙauyen da ko sunansa ma bata saniba Ita dai kawai burinta tayi nesa da inda ta fito

A daidai kofar wani gida ta ja ta tsaya saboda batajin xata iya cigaba da tafiyan saboda galabaitan da take sake yi rabonta da abinci tun breakfast shima ba wani sosai taci ba gashi a yanda xata ƙiyasta saboda yanayin shirun garin da kuma duhun dare aƙalla ƙarfe 11:00 zai iyayi

Guri ta samu ta zauna a ɗan dakalin dayake ƙofar gidan tare da kifa kanta tana cigaba da kukan da har takejin zuciyarta kamar ba'a jikinta yakeba batasan iya lokacin data share a zaune a wajen ba kawai dai taji idanunta na lumshewa alamar bacci takeji

Muƙewa tayi a hankali akan dakalin tana jin zuciyarta na mata zafi batason tuno abinda ya rabo ta da gida a cikin wannan tunanin bacci ɓarawo yy nasaran fizgarta duk da ba ɗaɗin baccin takejiba sam

Sanyin asuba tare da kiraye kirayen sallah a masallatan da suke ƙauyen yasata ɓuɗe idanunta a hankali waɗanɗa suka kumbura Sukayi jajir saboda tsananin kukan ta sha zaunawa tayi akan dakalin tana jin duk jikinta na mata wani irin ciwo ta shiga ƙare ma ƙauyen kallo tanason tuno inda take dafe kanta da ke tsananin ciwo tayi tana jingina da bango wasu hawaye Masu ɗumi suka sake gangaro mata

Hannunta tasa da sauri da kare fuskarta saboda hasken fitilar daya haske mata fuska
"Subhanallahi mutum ko aljan" mutumin ya tambaya da alamar tsoro a tare dashi yana tsaye daga ƙofar gidan da take zaune kasa cewa komai tayi sai hawayenta da ya ƙara ƙarfin gudu juyawa mutumin yy da sauri ya koma cikin gidan sai gashi ya ƙara fitowa tare da wani ɗan saurayi da alama shima alwala yayi na tafiya Masallacin

"Kaganta nan wlhy nidai har na tsorata" tsohon ya faɗa yana nunama saurayin ita da alama ɗansa ne ƙarasowa kusa da ita yy ya tsaya ɗan nesa kaɗan da ita yana faɗin " baiwar Allah " ɗago kanta tayi a hankali tana kallonsa hawayen idanunta na cigaba da kwarara tsura mata ido kawai yy sai kuma ya juya ya kalli babannasa yace "baba ko xata shiga ciki kafin mu dawo daga masallaci lokaci na ƙurewa "wani kallo babannasa yy masa yana nuna ta yace "ta shiga ina wai, kasan wacece ita xakace ta shiga ciki "miƙewa yy yana sake kallonta sai kuma kawai yy wucewarsa baban ma ya bisa a baya suka nufi masallaci

Har aka idar da Sallah gari ya soma haske tukun suka nufo gida tun daga nesa suka hangota still tananan zaune inda suka barta baba ya kalli kamal yace "anya wannan yarinyar mutum ce kuwa "murmushi kamal yy yace muƙarasa mugani "daidai kusa da ita ya durƙusa ya sake cewa "baiwar Allah" a karo na uku sannan ta ɗago kai ta kallesa murmushi yy mata yace "me ya sameki haka kike zaune anan da alama ma anan kika kwana ki faɗa min ko akwai taimakon da xan iya baki "nan ma shiru tayi ta sake miyar da kanta shiru yy kamar mai tunani sai kuma yace to ki tashi mu shiga ciki kiyi sallah nasan bakiyi ba ko kallonsa kawai takeyi kamar statue sai da ya sake maimaita abinda ya faɗa tukun ta miƙe a hankali jiri na ɗibarta saboda gaskiya tana buƙatar tayi sallolin da ake binta

Kallonta yy tayi saboda baiga alaman yar ƙauyen bace ko duba da irin suturar da ke jikinta kaɗai to itakuwa me ya kawota ƙauyennan haka har suka shiga ciki ta tsaya a zaure tana raba ido baba da tunda yaga kamal ya tsaya wajenta ya shige cikin gida ya samu a tsakar gida zauren ya nuna masa yace "wannan yarinyar baba nace ta shigo ko xatayi sallah "saída baba yy shiru sai kuma yace "kamal mutum fah yanxu abin tsorone kuma kwata kwata batayi kamar yar nan ba bawai bana son taimaka mata bane" kamal yy murmushi yana komawa zauren tare da faɗin "karka damu baba banji ajikina mai cutarwa ce kuma mu ai dan Allah mukayi da kyakkyawar nufi idan ma ta cucemu Allah baxai barta ba

A zauren ya sameta a rakuɓe yace baiwar Allah shigo yayi gaba tana binsa a baya har ƙofar ɗakin mahaifiyarsa sallama yy ta amsa sannan ya shiga itama ta bishi a zaune suka tarar da ita har lokacin akan abin sallan ta gaisheta yy ta amsa da fara'a tana kallon baƙuwar sai kuma tace " kamal wannan Fah a Ina ka samo ta" murmushi yy yana miƙewa yace" to muma dai a ƙofar gida muka ganta da alama ma anan ta kwana kuma taƙi magana shine nace mata ta shigo ko xatayi sallah" kallonta kawai umma takeyi sai kuma tace "to badamuwa bari tayi sallan idan mun karya sai muji daga ina take haka dan sam batayi kalar yan ƙauyennan ba" yauwa umma kamal ya faɗa yana ficewa daga ɗakin dan tafiya gona tare da baba dake jiransa a waje


Abuja nigeria_

A haukace yake sauƙowa daga matakalan da yake haɗesu uku uku hurhuɗu hankalinsa a matuƙar tashe ƙofa ya nufa da azama yana sake dialling din number a wayarsa ɗaya daga cikin securities ɗinsa ne ya ƙaraso da sauri yana faɗin "morning sir" wani kallo da yy masa ya sashi shiga hankalinsa ya sake faɗin "sorry sir" juyowa yy gabaki ɗaya yana kallonsa yace "ina take" a tsorace guard ɗin yace "sorry sir we have tried our level best but still we are not able to reach to her" cakumo wuyansa yy a zafafe Yana faɗin "what the heck do you mean baku ganta ba wata sani ,ina xata je she has no one but me so na baku nan da awa ɗaya ku nemo min *NOOR* duk inda ta shiga a garin Abuja" hankaɗasa yy baya tare da sake faɗin "sorry sir" sake kallonsa yy sannan yace "don't u dare ,keep ur fucking sorry to yourself , just make sure lokacin da na baku kundawo min da noor gidannan "sai kuma ya juya a fusace ya nufi motarsa ya fice a gidan a guje


To ABNUR has just started the story is yet to begin 🤓😇

*💖ABNUR💖*

*By maimoon*🤓

*Elegant online writers*

*Freebook*

*page* 2

Tunda ya fito gidan yake yawo a cikin gari yama rasa ta ina zai fara neman NOOR ,ina zata je ,wata sani bayan shi, ya tabbata bata da inda zata je da ya wuce gidansa ,har yamma yana gararamba.

Gefen titi ya samu yayi parking ya jingina kansa da steeryn motan, ya rasa ina zai nufa don neman ta, ɗago kanshi yayi da idanuwansa da suka gama rinewa sukayi jajir ya jingina kansa da seat ɗin motar .

Why Noor? ,am I really that bad to you da kika zaɓi ki barni? ,do you have any idea halin da nake ciki yanxu ?please Noor ki dawo gareni i promise I will mend my ways ,na miki alƙawari zan gyara please Noor.

Da ƙyar ya samu ya kai kanshi gida, har jiri yake ji dan rabonsa da abinci tunda ya fahimci Noor bata gidan .

Baibi takan kowa ba har bodyguards ɗin da suke gaishesa, ko takalmansa bai cire ba ya faɗa kan gadon katafaren ɗakinnasa yana kallon saman ɗakin, yana sake zurfi a tunanin ina zata shiga a garin Abuja .


Kamal ne ya fito daga ɗakin ,mahaifiyarsa na biye dashi ,zama tayi a tsakar gidan shima yaja ƙaramar kujera ya zauna yana fuskantar ta yace ,"umma da muka fita dama bata ce miki komai bane? ".


Ďan shiru umma tayi kamar baxatayi magana ba sai kuma tace," wlhy kamal nayi iya tambaya amma batace min komai ba, banda kuka babu abinda takeyi, yarinyar tana da babbar damuwa sosai ,amma rashin sanin daga ina ta fito shine babbar damuwar ".


Kamal yace ,"hakane amma gaskiya tana buƙatar taimako sosai ,kawai mu bari muga kwana biyu ko xata ji sauƙin abinda yake damunta, sai tayi mana bayani" .


Shiru umma tayi sai kuma tace "toh Allah dai ya kyauta gata kyakkyawa wlhy kuma daga dukkan alamu yar gidan masu kuɗi ce ,"kamal ya miƙe yana faɗin," wlhy nima haka na gani".


Fita yayi daga gidan dan yanaso ya je gidansu Abdul, dan yanaso ya amso kuɗin sa dake wajensa dan komai na gidannasu ya ƙare kuma gashi amfanin gona bai nuna ba bare ,
har ƙofar gidan yaje ya aika yaro ya kira masa shi, a ƙasan wani bishiya suka zauna Abdul ya kallesa yace "kuɗinka ko kamal" .


Kamal yayi murmushi yace "saboda bana zuwa wajen ka sai idan inason kuɗi koh ",Abdul yayi dariya yace "wlhy ba haka bane kawai dai nasan halin garin ne yadda babu kuɗi", shiru kamal yayi sai kuma yace "wlhy Abdul banso na tambayeka ba amma wlhy ina matuƙar buƙatarsu ".


Duk sukayi shiru kafin Abdul ya nisa yace" wlhy kamal bandashi nima ",shiru yayi sai kuma yace, "babu damuwa karka damu wlhy", daga haka ya miƙe yana faɗin "to sai mun haɗu anjima da daddare", Abdul ma ya miƙe yace "ba damuwa nagode kamal ".


Daga haka ya juya yana ta tunane tunane har ya iso a tsakar gidan ya samu umma tana ƙoƙarin shiga kitchen kusa da ita yaje yace," umma dama naje wajen Abdul ne ko zan samu kuɗin wajensa amma bansamu ba ",umma ta nisa tace ," to Allah ya kyauta amma dai yau yaza ayi kenan, yanzu babanka ma ya dawo bai samuba ,wlhy gashi muna da baƙuwa " .


D'an murmushi yayi yace "yanzu dai akwai wani ɗan canji a jikina idan na fita zan nemo mana abinda zamuci yau, amma dai gobe sai yadda Allah yayi da mu", duk juyawa sukayin jin motsin mutum a tsaye suka ganta tana kallonsu umma tace "ah ah Noor Kin fito ".


Girgiza mata kai tayi tace ,"umma inaso zan shiga bayi ne," da sauri umma tace "ayya gashi can bari na saka miki ruwa a buta ",da sauri ta karɓi butan hannun umma tana faɗin "laa umma karki damu dan Allah".


Ta wuce wajen randar ta ɗebi ruwan umma tace ."ga ruwan zafi idan zaki surka ,tace "toh" cup ta ɗauka ta ɗebi ruwan ta wuce bayi ,
Umma da kamal na nan zaune ta fito ta ajiye butan sannan ta nufi wajen tabarmar da taga sun shimfiɗa sun zauna.


Itama zama tayi sai kuma tace "umma dan Allah kuyi haƙuri da shiga rayuwarku da nayi, amma ina neman alfarma a wajenku dan Allah ina so in zauna da ku na wasu kwanaki, nasan ya dace na faɗamuku abinda ya raboni da gida , amma na muku alƙwari zan fada muku insha Allahu ".


Aai da ta ɗan yi shiru sai kuma ta sanya hannuta ta ciro ɗan kunnen gold ɗin dake kunnenta ta miƙama kamal tace "yaya kamal gashi ina so dan Allah ka siyarmin da wannan ɗan kunnen ".


Sai da ya kalleta ya kalli ɗan kunnen sai kuma yasa hannu ya karɓa yana kallo yace," tabb Gwal ne fa".


Tayi shiru tana kallonsa yace," sai dai bazan iya sayarwa a garinnan ba , sai dai gobe insha Allahu , tunda ranar kasuwan cikin garin kusa damu ne , su suna siya sai inje can na sayar miki ," ahankali tace "nagode sosai Allah ya saka muku da alkhairinsa ", duk suka amsa da ameen .

Washe gari kamar yadda sukayi haka ya shiga cikin gari ya sayar , duk da dai an masa an siya ba yadda kuɗin sa ya keba ganin cewa ɗan ƙauye ne, haka ya ɗaure kuɗin a mayafi ya dawo gida, a tsakar gida ya samesu suna hira da umma ya zauna shima yana warware wa ya miƙa mata.

"Yace gashi Noor ",ta karɓa tana murmushi ta ƙirga kuɗin sai kawai ta girgiza kai sannan ta kama hannun umma ta danƙa mata kuɗin.

Dubu biyar kaɗai ta ɗauka a kuɗin umma ta zare ido tana kallonta girgiza kai tayi tana kallon umma tace "umma dan Allah karkice komai kiyi haƙuri jiya naji hirarku da kamal dan Allah ku karɓi kuɗinnan ,na baku ne a matsayin yan uwana saboda kunyi min taimakon da bazan taɓa mancewa daku ba, kunyi min taimako alokacin da nake tsananin buƙatarsa".

Umma rungumeta kawai tayi tana sake jin son yarinyar har ranta, tana sake kwaɗaituwa da son jin dalilin ta na barin gida , a hankali ta share hawayen ta tace.


" Ni ban san me ya raboki da gida ba Noor, amma ke ɗin alkhairi ce a wajenmu, kuma mungode Allah ya saka miki da alkhairi kuma ya fitar da ke a cikin duk matsalolin da rayuwarki ke ciki".

Shidai Kamal kallonta kawai yakeyi sai kuma yace "Noor kuɗinnan", shhhh tace masa "yaya kamal pleaaaaase karkace komai".

Nurmushi kawai yayi yace "to shikenan nayi shiru Allah ya saka", daga haka suka ci gaba da hirarsu tana samusu baki jefi jefi, but hankalinta da tunaninta gabaɗaya suna wani wajen daban.

Wasu sabbin hawayene suka cika idanunta, she is sure baida buƙatarta a rayuwarsa, kuma bayida asara idan har bata tare dashi , he never loved her but tayima kanta alƙawari koda mai kama da ita bazai sake gani ba.

zatayi nisa dashi irin nisan da bazai taɓa cinmata ba, a hankali ta sanya hannu ta share hawayen tana ƙaƙalo murmushi, ganin umma tana kallonta sai kuma ta miƙe ta nufi ɗaki duk suka bita da kallo .

🥱🥱🥱🥱🥱🥱

#maimoon
💖 **ABNUR**💖

*By* *maimoon* 🤓

*Elegant* *online* *writers*

**Freebook**

*Page* *3*

Kwanci tashi asarar mai rai,yau kwanan Noor goma kenan a ƙauyen Marke dake jihar Kano.

duk da cewa har yau ba tayi musu cikakken bayanin abinda ya rabota da gida ba,amma sun fahimci ita ɗin mutum ce mai matuƙar daɗin zama, sannan bata da son magana sosai.

Hakan yasa suke zaune tare da ita, har zuwa sanda zata yanke shawarar sanar dasu ainihin abinda ya rabota da iyayenta ,

Umma tana matuƙar ji da ita, kuma hakan yasa basa ma ɗago maganar, saboda yadda daga an tambayeta, sai dai ta fara kuka, Sannan akoda yaushe maganar ta baya wuce"Umma kuyi haƙuri insha Allahu zan sanar daku ,har ma abinda baku tambaya ba".

A bangaren ZANNUR kam babu sauƙi, yayi iya ƙoƙarin sa ,ya haukace da neman ta har gidajen Radio,but har yau shiru ,ga baki ɗaya ya fita hayyacinsa ,bai taɓa tunanin za tayi koda tunanin hakan a zuciyar ta ba, talkless of aikata shi a aikace

Yau ma a gajiye ya dawo,bayan ya gama yawan nemanta kamar yadda ya saba ,duk da ya baza mutane sunfi a ƙirga da hotunanta ana nemanta, but shikanshi ya kasa daina wa.

kullum gani yake idan ya fita yau zai ci karo da ita ,bazai taɓa manta yadda abubuwa suka kasance ba shekaru biyu da suka wuce,ɗakinsa ya wuce ya zauna akan kujeran dake ɗakin yana jingina da kujeran "i can never give up on you, har sai na ganki sannan kin tabbatar min da bakinki zaki dawo gida na, idan ba haka ba, ban san tayaya zan yafe ma kaina ba ,I know I will never be able to
forgive my self idan har wani abu ya sameki".

Da ƙyar ya miƙe daga kan kujeran ya zare rigar jikinsa,ƙirarsa na ƙarfafa ya bayyana, duk da yanzu rabonsa da workout ɗinma tun ranar da Noor ta bar gidan, wanda a da yake cikin morning schedules ɗinsa da baya iya tsallakewa,

bayi ya wuce yayi wanka, yana fitowa kayansa kawai ya zura, yana jin yanda cikinsa ke kukan yunwa.

A hankali yake sauƙowa stairs ɗin, gaba ɗaya ya canza kamar ba Zannur ba, 'the master of all' harta masu aikin gidan sun san baya cikin kwanciyar hankali, duk wanda yake tareshi yasan yana cikin matuƙar damuwa.

Falon ya ƙaraso ya zauna yana rage ƙarfin ac, dan kamar sanyin zazzaɓi ma ya keji a jikinsa, Yasira ta ƙara so wajensa da sauri tana faɗin "Sir Should I serve your dinner?" Kallonta kawai yayi ,sai Kuma ya mayar da kansa ya jinginar, yama rasa me zai ce mata, bakinsa ya masa nauyi,sai da ta sake tambayan tukun ya ɗaga idanunsa,masu rikitarwa ya zuba mata su, sai kuma yayi gyaran murya yace "miss You Are fired!"

Zaro ido tayi tana kallonsa, nan take tafara hawaye tana faɗin "Sir I am very sorry Dan Allah Kar ka koreni" "why shouldn't i?" ya katse ta a tsawace , "sanda ta tafi ta barni why don't you stop her ?"

Ta buɗe baki zatayi magana, yayi saurin sanya yatsansa a baki , yace "shhhhh not another word, abinda nakeso dake yanzu shine,U Should get out of my sight immediately,before I lose my temper completely".

Da sauri ta miƙe daga tsugunan da tayi, takoma kitchen da sauri! ,Ƴan matan da ke cikin kitchen ɗin suka kece da dariya ,Amina tace "sai da nace miki kar kije! ,kwanakin nan Sir neman inda zai huce haushinsa yake".

Asabe da ke goge goge, tayi ƙwafa tana faɗin "sai kace sanda Madam ɗin takenan ya damu da ita" ,Ameena tace "Wallahi fah nima abin mamaki yakeban" ,Yasira dai bata bi ta kansu ba, ta wuce ta ƙofar baya dake kitchen ɗin, ta nufi shashen ma'aikatan gidan, a zuciyarta tana sake dana sanin zuwa tambayarsa da tayi.

Shi kuwa ko a jikinsa, kawai burinsa ta inda Noor zata ɓullo ,wayarsa ce tafara ringing,a hankali ya ɗaga wayan yana kallon mai kiran "Maami" da ya gani ya shashi shafa yalwataccen sumarsa, he has been avoiding her since, dan baisan me zai ce mata ba sam, shahada yayi ya ɗau wayan "sallama yayi daga ɗayan ɓangaren ammi ta amsa tana faɗin


"Habibi ina ka ajiye wayarka, I have been trying to reach you but baka picking calls ɗinka, I hope everything is fine there? " shiru yayi kafin ya samu ƙarfin halin haɗa kalmomin bakinsa "maami ya Dubai?" "lfy ƙalau habibi ina Noor" shiru yayi ya kasa cewa komai ,shirun da taji yayi yawa ya sata sake faɗin "Habibi are you there? "Umm...Maami" "are you okay my boy? mai yake faruwa me kake ɓoyemin? I hope you are not trying to hide anything!"
"maami babu komai fah don't you believe me"

"na yadda da kai mana my boy, to yanzu ina Noor? it has been long tunda mukayi magana da ita, kai mata wayan "

A ɗan daburce yace "umm wai Noor ..in kai mata wayan? to ai tayi bacci,batajin daɗine shine sai ta kwanta"
"ok shikenan maybe next time Allah ya sauwaƙe ka kira abbun ka, yace yakiraka baka picking " "a hankali yace "insha Allah Maami" daga haka yayi hanging Kiran yana sauƙe ajiyar zuciya.


Da sauri kamal ya shigo gidan, hannunsa riƙeda jarida wanda hotonta ke jiki ɓaro ɓaro ,ita kaɗai ya samu a tsakar gidan tana wanke kwanukan da suka ɓata da safe ,yanayin da taga ya shigo ya sata saurin ɗauraye hannunta,

tana ƙarasowa tsakar gidan dai dai umma ma ta fito daga ɗakin ta, tana faɗin "Noor Nikam Ina kikaga na ajiye goron da ke cikin ledannan ne?

tsayawa tayi tana kallonsu yadda sukayi cirko cirko a tsakar gidan. "Lafiya?" Ta tambaya tana kallon Noor "umma nima wallahi bansani ba, haka naga ya shigo kamar ba lafiya ,umma ta karkata akalar tambayan nata ga kamal da ke tsaye yana kallonsu,


miƙa mata jaridar yayi yana faɗin, Abdul ne ya shiga cikin gari ɗazu, shine nace masa ya siyomin jarida dan na karanta, shine fah kawai naga hoton Noor ajiki ,Umma ta karɓa tana dubawa, sai kuma tace to me aka rubuta ajiki? ko yan uwanta suke nemanta? ai dama dole su nemeta!! "


Kamal kallonta kawai yake ganin tana ƙoƙarin wucewa ɗaki ya sa yace"Noor!" Ta juyo Amma Bata dawo ba, a hankali yace "bakya tunanin 'yan uwanki suna cikin wani hali na rashin ganinki? kuma haryanzu baki ga buƙatar ki sanar damu komai ba!?"


shiru tayi ba tare da tace komai ba, a hankali umma ta ƙaraso inda take ta dafata tace"Noor bana miki kallon ƙasa da abinda na haifa, bakya tunanin idan ke 'ya tace kika bar gida irin haka, hankalin dole ya tashi to bare mahaifiyar ki, Yakamata ki faɗa mana abinda ya rabo ki da gida Noor, ko kina tunanin bamu kai musan damuwarki bane ?


da sauri ta girgiza mata kai tana faɗin"umma dan Allah karkice haka, wallahi kun kai kuma har kunfi haka a gurina"ta share hawayen da ya zubo mata tace "insha Allah na muku alƙawari yau zaku san komai game dani, amma ina neman alfarmarku, ku bari zuwa baba ya dawo zuwa dare, ina so na baku labarina a gaban sa "umma ta yi murmushi tana faɗin Allah ya kaimu Allah ya muku albarka "suka amsa da ameen

Maimoon#
*💖*ABNUR**💖

*By* *maimoon* 🤓

*Elegant* *online* *writers* 📚📖

*Free* *book*

*Page* *4*

Kamar yadda ta faɗa kuwa, hakan ce ta kasance, bayan sallar isha duk suka taru a ɗakin Baba

Please Login or Register in order to submit comment