Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sakin sabon kuka

Shafa kanta yayi, yana raɗa mata a daidai kunnenta

"everything will be alright, ba ke kika ce in bar damuwa ba"

Ɗago idanunta da suka kaɗa sukayi jaa tayi tana dubansa, sai kuma tayi murmushi tana faɗin

" dan Allah ka dawo, zan jiraka, kazo ka faɗa min abinda kace zaka faɗa min dazu"

Murmushi yayi shima, wanda kana gani kasan a iya fuska ya tsaya,

"kina son in fada miki ne!?"

Gyada kai tayi alamar eh

"To ki jirani komin dare zan faɗa miki"

"Do you promise?"

"I do" ya faɗa yana sakin hannunta da ke cikin nasa.


A hankali ta juya ta nufi barin wajen duk jikinta a sanyaye.


Da ido kawai ya bita, yana kallon irin baiwar kyau da Allah yayi mata, wanda shi bai taɓa lura ya gani ba sai yau, yanda take tafiya a hankali, cikin sanyi yake kallo har ta fice kafin ya sauƙe idanunsa yana sakin ajiyar zuciya.


Tana fitowa, da sauri bodyguard ɗin dake jiranta, ya fito yana zagawa ya buɗe mata motan yana gaisheta, shiga tayi ta zauna, tana kallon compound din asibitin, har suka fice, fuskarta ta juyar daga kallon window ɗin, ta mayar tsakanin cinyoyinta, tana sake tunanin wa yake son kashe Taufeeƙ a cikin gidan,kuma me ya musu.


Har suka iso ta kasa gano komai, yana yin parking, bata jira ya buɗe mata ba, ta buɗe motan ta fita, tana tafiya a hankali, a falo ta samu su Asabe, duk idanunsu sunyi jajir saboda kuka, Amina har lokacin kuka takeyi wiwi, suna ganinta suka nufo ta sauri,

"Madam ya jikin Sir Taufeeƙ"
kasa ce musu komai tayi.

Yasira da ke gefe tana jira a ce mata ya mutu, sai zare ido takeyi, ta kasa nutsuwa, da sauri ta bi Noor da ke ƙoƙarin haurawa sama


"Ma dan Allah ki faɗa min halin da yayana yake ciki, shikadai nake dashi, ya mutu ne?"
ta tambaya tana matsar kwalla


Dafa ta Noor tayi sannan tace

"kar ki damu bai mutu ba, kuma insha Allahu bazai mutu ba, yana nan da ransa kuma za'a gano duk wanda ya aikata masa hakan."


Dakatawa tayi da kukan da takeyi, hawayen ya ƙafe jin Taufeeƙ bai mutu ba, batasan sanda ta furta

"Bai mutu ba?" da ƙarfi tana zare ido


Da mamaki Noor take kallonta, kafin tace,

"kina so ya mutu ne?, nace miki bai mutu ba, kuma insha Allahu kwanannan zai dawo akan ƙafafunsa"


Da sauri ta sake fashewa da wani irin gigitaccen kuka, tana faɗin shikenan na shiga uku, yayana shi kaɗai nake dashi,

Abinda bakinta ke furtawa kenan amma zuciyarta tana raya mata, idan har bai mutuba ai kuwa ta kaɗe, ta shiga uku,


Ganin kukan da takeyi yasa Noor faɗin

"Yasira ki yarda da ƙaddara yayanki ya shiga coma, but insha Allah zai tashi da yardar Allah kiyi masa addu'a"


Kasa cewa komai Yasira tayi da sauri ta juya ta bar wajen, duk suka bita da kallon tausayi.


Sai da Noor tayi wanka sosai, duk da haka daga zaran ta tuna yadda jini ke malala daga jikin Taufeeƙ sai ta runtse idanunta,
wasu hawaye na sake taruwa a idanunta.

har ƙarfe goma babu Zannur babu alamar sa, tun tana jiransa, har bacci ya fara ɗaukan ta, a kishigiɗe haka tayi bacci, dan bataso ta kwanta bacci ya ɗauke ta batare da ya dawo ba.


A bangaren Zannur, tun bayan fitowarsa daga asibiti, kasancewar asibitin basa barin kowa a wajen majinyaci su suke kula da shi da kansu, tun da ya fito yake tunanin abinyi, tunanin cctv daya zo masa yasa shi nufar gida kai tsaye,


Ɗakin sa ya wuce ba tare da ya bari kowa yasan da shigowar tasa ba.


ƙuri yayi ma na'urar yana kallo, ganin babu footage ɗin Garden kwata kwata, da mamaki yake sake kallon computer, ya maimaita dubawa ya kai sau biyar, Amma still babu wannan footage ɗin, a hankali ya shiga duba sauran gurare na gidan, yana so ya gano taka maimai abinda ya faru.


Cak ya tsaya akan inda Yasira ta fito tana kuka, ta samu Taufeeƙ a compound, baya iya jin me suke faɗa, amma da alama faɗa sukeyi, sai kuma yaga sun nufi Garden dukansu, baiga fitar Yasira ba sai kuma yaga Noor ta shiga, pulsing yayi, ya miƙe da sauri ya fita a ɗakin.



Ƙasa ya sauƙo, sannan ya ɗau landline ya Kira ɗakin su Yasira, Amina ce ta ɗau wayan, a taƙaice yace


"Yasira ta sameni a falo immediately" daga haka ya kashe wayar.


"Ni kuma?, meyasa yake nema na?" Yasira ta faɗa tana kallon Amina da ta isar mata da saƙon Zannur,


"Idan kinje sai ki tambayesa Ni kawai cemin yayi kije"


Miƙewa tayi zuciyarta na wani bugu ta fice a ɗakin,


A zaune ta samesa, ita ma ta samu waje can ƙasa ta zauna, tana shirin gaishesa ya ɗaga mata hannu, fuskarsa babu alamun wasa ya soma faɗin

"Me ya haɗa ki da yayanki ɗazu?"


Ɗago ido tayi ta kallesa, kafin tace

"Ni.. babu komai" ta faɗa tana kame kame

"Babu komai?"ya sake tambayan yana kafe ta ido

Daburcewa tayi, sai ta soma inda inda,


"eh dama, au babu Fah, Amma dai kawai cemin yayi zai kaini gurin baba, shine nace masa bazan je ba, shine yake min faɗa, sai kuma yace muje can muyi magana, muna cikin magana sai Madam ta zo, ranta a ɓace, shine sai ya ce min in tafi, shikenan kawai sai muka ji wai an kashesa."

tana kaiwa nan ta fashe da matsanancin kuka, harda shesheƙa.


Kallonta kawai yakeyi, kamar mai ƙoƙarin gano wani abu, kafin a hankali ya furta

"Yasira kina jina?"

Gyaɗa masa kai kawai tayi, tana cigaba da kukan

"Yayanki zai samu lafiya, ki kwantar da hankalinki, kina jina?, na miki alƙawarin duk wanda yayi masa wannan abun, da kaina zan bincikosa, sannan in hukuntasa, ki cigaba da yi masa addu'a kinji?"


"To" ta faɗa tana fyace majina


"Tashi kije" ya faɗa a taƙaice, yana jingina kansa da kujera.


Miƙewa tayi, ta wuce, tana sake waiwayowa ta dubesa, a hankali kuma tayi murmushi, a zuciyarta tana faɗin

"Kaɗan ya rage na mallakeka Zannur, kuma nayi alƙawarin, duk wanda ya kawo min cikas wallahi sai na kawar dashi"

sai kuma tasa yatsa ta share guntun hawayen idanunta, sannan ta wuce ɗakinsu.


Miƙewa yayi daga kan kujeran, yana jin gabaɗaya kansa ya kulle, ta yaya ma Yasira zata cutar da ɗan uwanta, bazai yiwuba,

har ya koma ɗakin sa ya faɗa kan gadonsa yana cigaba da tunani,

to me ya kai Noor wajen Taufeeƙ?, kuma ranta a ɓace, me ya mata?, dole ne ta amsa masa waɗannan tambayoyin nasa, shin ko dai yayi kuskuren amincewa da ita ne?, wata zuciyar ta raya masa, da sauri kuma ya girgiza kansa, yana maimaita
"Allahummu ajirni fi musibati."


Gabaɗaya ya manta da wani tana jiransa, har bacci ya dauke sa.







Mun kusa dawowa kan labari🤓so get ready, gumurzun yana gaba




Maimoon#


*💖ABNUR💖*

*By maimoon*

*Elegant online writers* 📚📖


*Free book*


*Page 17*



Da safe ma kiran doctor ne ya tashe sa, akan yana nemansa da gaggawa, a gaggauce ya shirya ya bar gidan, ba tare da ya ma Noor sallama ba.


Noor kam, tunda tayi sallah, ta gagara koma wa bacci, tunani takeyi meyasa bai zo ba?, bayan ya mata alƙawarin zai zo komin dare.


"to ko bai dawo bane jiya" abinda zuciyarta ta raya mata kenan, Definitely bai dawo ba, tasan da zai shigo, to ko jikin Taufeeƙ ɗin ne, ya hanashi dawowa,

wani zuciyar ta sake raya mata, haka tayi ta tunane tunane, kafin daga bisani ta miƙe ta wuce toilet.


Wanka tayi, ta fito ɗaure da pink towel mai kyau, fararen ƙafafuwanta, sanye cikin room slippers pink,

jiki a sanyaye ta ƙarasa ta buɗe sif tana kallo, riga da skirt ta zaro na atampa, ɗinkin riga da skirt, ta ajiye akan gadon, kafin ta ƙara sa gaban mirror ɗinta, dake shaƙe da abubuwan anfaninta.


Mai ta ɗauka tana shafawa akan lallausa fatar ta mai santsi, amma duk tunaninta na wani wajen daban,

a haka har ta ƙara sa, kayan da ta ajiye ta ɗauka ta sanya, yadda suka zauna ajikinta tubarakallah masha Allah, kallon kanta ta tsaya yi a madubi, sai kuma ta ɗan yi murmushi, dan ko ba'a faɗa mata ba tasan ita ɗin mai kyau ce, akan laɓɓanta wanda suke pink shar, sannan kamar ta shafa musu lip gloss, saboda yadda suke koda yaushe da santsi da yalƙi ta furta

"Alhamdulillah"

Gefen gado ta koma ta zauna, tana kallon agogon hannunta, ƙarfe takwas saura, da sauri ta miƙe tsaye a ranta tana faɗin "bari kawai na dubo shi, anya ma ya kwana a gidannan."


Daga haka ta fice a ɗakin, tana tafiya a hankali, turus tayi a bakin ƙofan tana kallon Yasira, da ta fito daga ɗakin, daga ita sai kayan bacci wanda ko Cinyarta basu gama rufewa ba, idanunta da alamun, tana ganinta itama tayi saurin yin baya, tana kallon ta, sai kuma ta zo zata gilma ta,


Hannu Noor tasa ta dawo da ita, tana kallonta cikin ido tace

"Yasira me kike yi a ɗakin Zannur"

Ta faɗa tana zare mata ido, kamar zasu faɗo ƙasa

Cikin nuna tsoro da kuma kuka Yasira ta soma magana

"Madam dan Allah kiyi haƙuri, ba komai bane, kawai Sir yaga halin da nake ciki jiya saboda rashin lafiyan Yayana, shine yace nazo, to shine bacci ya ɗauke Ni a nan, ba komai bane"


Noor kallonta ta tsaya yi kafin cikin tsawa tace

"ƙarya kikeyi, aka gaya miki shi jahili ne da zai gayyaceki ki kwana a ɗakinsa, alhalin ke ba muharramarsa bace"


Cikin kuka wiwi, Yasira ta soma faɗin,

"wlhy da gaske nakeyi Ma"

"Ok to da ya kiraki ke kuma sai kikazo, saboda ke munafuka ce harda sako kaya irin waɗannan"


Ta faɗa tana nuna jikin Yasira, rai a ɓace idanunta sun gama canza kala


"Ma kiyi haƙuri Sir ne ya bani yace in saka, nima bansan dalilinsa ba, kuma Ni bazan iya yi masa musu ba shiyasa nasaka"


Girgiza kai kawai Noor takeyi, kafin ta sake Yasira ta juya a fusace ta nufi ɗakin ta, wato abinda ya hanashi zuwa gareta jiya kenan!

me yasa zuciya ta yaudareta da har take ganin kodai Zannur ya fara sonta ne, gadonta ta faɗa tana cigaba da rusa kuka wiwi.



Da sauri Yasira ta zaro dogon hijab ɗinta, a inda ta ɓoye ta zura, sannan ta koma ɗakin Zannur cikin sassarfa, inda tasan yana ajiye laptop ɗinsa ta nufa, kasancewar babu security yasa ta buɗe da sauri, sai da ta tabbatar ta goge wannan footage ɗin kamar yadda ta goge na Garden, kafin ta shiga tafa hannunta tana murmushin mugunta,

"Yaya Taufeeƙ, kayi kuskure, da har kake ƙoƙarin rabani da rayuwata, dan kuwa Zannur rayuwa ta ne, zan iya komai dan na mallakesa, amma bazan ƙi gode maka ba, saboda makarantar computer da ka sakani, har na zama computer guru, idan ba haka ba, da tuni asirina ya tonu, sannan ina mai tabbatar maka bazan taɓa bari ka farfaɗo ba,bare har ka tona min asiri, har sai Zannur ya Zama nawa."


Daga haka ta fice a ɗakin tana murmushi, da jinjina ma kanta.

******

"Congratulations, gaskiya dan uwanka, yana da matuƙar Sa'a, ba kowa bane ya ke shiga coma ya dawo da wuri, but da izinin Allah jiya ya motsa, kuma daga nan zuwa ko wani lokaci, zai iya farkawa."

Da sauri Zannur ya ɗago yana kallon likitan, jinjina masa kai doctor yayi alamar tabbatarwa,


"But saboda lafiyarsa, yasa bazamu bari ya gana da kowa ba, har sai bayan kwana uku"

Likitan ya ƙara sa faɗa yana gyara glass ɗin idanunsa, da murmushi a kan fuskarsa.

"Alhamdulillah, Alhamdulillah, alhamdulillah"

shine kaɗai abinda Zannur ke iya faɗa, ko babu komai, Taufeeƙ zai faɗi wanda ya aikata masa hakan da kansa.


Miƙewa yayi yana miƙa ma doctor ɗin hannu, suka yi musabaha, kafin ya fice a office ɗin yana jin matuƙar farin ciki, bai zarce ko ina ba sai gida.


Ɗakin Noor ya nufa, dan yana so ta amsa masa tambayoyin da ya kwana dasu,


Tunda ya shigo ɗakin taji shigowar sa, amma sai tayi kamar tana bacci, ƙarasowa yayi ya zauna a gefen gado yana kallonta, kafin a hankali ya sa hannuwansa duka biyu ya ɗago ta gabaɗaya,

yatsine fuska tayi kafin tace "miye hakan?"


Bai kulata ba ya zaunar da ita a tsakiyar gadon yana kallonta da fuskar da babu wasa yace " " " Noor! "

Tone ɗin da yayi maganar dashi, ya sata nutsuwa ta tsura masa ido tana saurarensa, duk da matuƙar haushinsa da takeji.


A hankali ya cigaba da magana

"Noor ina so ki faɗa min, me ya haɗa ki da Taufeeƙ, da har kika aikata masa haka"


Zaro idanunta tayi duka tana kallonsa kafin tace

"Me kake nufi na aikata masa haka, meyasa zan masa haka?, me ya min?"


Cikin ɓacin rai yace

"Noor na riga nasan komai, ina so ne ki faɗa da bakinki, miye Taufeeƙ ya aikata miki daya cancanci haka?"


Idanunta da suka ciki da hawaye, ta rintse ,kafin tace

"Wallahi tallahi, a haka na gansa, nima..."


"Ƙarya kikeyi", ya faɗa a tsawace yana miƙewa tsaye, gabaɗaya fuskarsa ta gama canzawa, hannunsa yasa a gashin kansa ya birkita kafin yayi ƙwafa yana faɗin

"nayi zaton zan iya amincewa dake, saboda kamilalliyar fuskarki, ashe zuciyar ki baƙa ce, Ni ina da shaidan cewa lokacin da kika shiga kika samesa da ransa, sannan babu wanda ya ƙara shiga bayan ke, wace irin zuciya ce dake, azzaluma mara imani"


Kasa haƙura tayi, idanunta ya rufe, a fusace ta sauƙo daga kan gadon tana kallonsa, hawaye wasu nabin wasu

Cikin Muryar kuka ta shiga faɗin

"abinda yasa ka kawo Ni gidanka kenan?, meyasa baka bar Ni a can na mutu ba, meyasa ka ɗauka ma Nenne alkawarin da bazaka iya cikawa ba?, nagode wa Allah, kuma bana buƙatar kowa ya yarda dani saboda Ni nasan kaina, Ni ba azzaluma bace, kuma Ni ba mai kisan kai bace, sannan Ni ba fasiƙa mai zina bace"

ta faɗa da ƙarfi tana rushewa da kuka.


Da sauri ya ɗago fuskarsa ya kalleta, a hankali ya tako dai dai inda take, fuskarsa tayi jajazir

"Waye fasiƙi mazinaci?"

ya tambaya yana kallonta.

Ƙin dagowa tayi da ƙarfi ya ɗagota yana kallonta
"nace miki waye fasiƙi mazinaci?"

Da zafin rai take kallonsa kafin tace

"ka ɗauka zan ji tsoronka ne in kasa maimaitawa, kai fasiƙi ne kuma mazinaci, kuma Allah bazai Barka ba"


Ɗif ta ɗauke wuta sakamakon wani shahararren marin da taji a fuskarta har sai da jinta da ganinta ya ɗauke na wasu sakonni


"Ni ne mazinaci?, Ni?"

sai kuma ya furzar da iska mai zafi, yana faɗin

"nayi dana sanin baki dama, nayi dana sanin tunanin kin cancanta na so ki, nayi da na sanin saninki, kuma ina mai tabbatar miki da kaina zan hukunta ki,bana buƙatar kowa, zanmiki mafi munin hukunci wanda bazaki taɓa mantawa da Ni a tarihin rayuwarki ba, yanzu zakisan waye Abubakar shuraim a baya Zannur kika sani "


daga haka ya juya ya fice a ɗakin, kai tsaye gidan ya bari, dan gidan ya masa baƙiƙirin ba zai iya zama a cikinsa ba, so kawai yakeyi Taufeeƙ ya tabbatar masa da bakinsa cewa Noor itace ta caka masa wuƙa, daga nan kuma zai yanke mata duk hukuncin da ya dace da ita.



Ɗurkushewa tayi tana wani irin kuka, ta shiga uku, shin dama fuska biyu yake dashi, sai da ya nuna mata ɓangarensa mai kyau, kafin ya nuna mata mafi munin ɓangarensa,

"Bazai yiwuba"
ta faɗa tana miƙewa tsaye,

Sai kuma ta nufi sif ɗinta kamar zararriya,

birkito kayan tayi, amma ta kasa ɗaukan ko ɗaya, jakanta ta nufa ta buɗe ta ciro atm dinta, ta zura hijab ɗinta tana rusa kuka kamar ranta zai fita.


Fitowa tayi daga ɗakin bata ko ganin gaban ta, da sauri Asabe da Amina da ke tsaye cirko cirko suka nufo ta, dan suna jiyo hayaniyansu daga sama, amma basa jin me suke faɗa, sai kuma sukaga Sir ya fita ranshi a ɓace,

"Madam lafiya, ko jikin Sir Taufeeƙ ne ya tashi?"

Ko kallonsu batayi ba ta nufi ƙofa,


Da sauri Asabe ta sha gabanta "ina zakije please madam, ki faɗa mana Please"


"Out of my way" tafaɗa tana zare dukkanin idanuwanta,

Da sauri Asabe ta matsa tana matsar kwalla, dan dai ta tabbatar ba fitan lafiya Noor zatayi ba yanzu

Ko dai jikin Taufeeƙ ne ya tashi, to ko Taufeeƙ ɗin ya mutu ne, da sauri ta juyo da nufin ta tambayeta, amma inaa har ta fice a falon, da ƙafa ta taka har gate, ba tare duk ma'aikatan gidan sunyi yunkurin hanata ba, dan babu wanda bai san Madam bace, dan Taufeeƙ da kansa ya sake tara su kamar yadda ya tara su a baya, ya shaida musu, matarsa ce, kuma subi dukkan umarnin ta.


Mai gadi dake tsaye jikin gate da sauri yace

"Hajiya meke faruwa?, ko jikin Taufeeƙ ɗinne? naga yallabai ma ya fita a fusace"


Ba ta basa amsan sa ba sai cewa da tayi

"baba buɗe min ƙofa"

Yadda yaga babu alamun wasa a tare da ita yasa shi saurin buɗe ƙofan yana faɗin

"Hajiya a dawo lafiya, Allah ya ƙara bashi lafiya bawan Allah."

Bata kulasa ba, tayi ficewarta, tafiya kawai takeyi, da kafa burinta kawai ta bar Area din gidan gabaki ɗaya,


Sai da ta iso main junction kafin ta samu abin hawa, yana tsayawa,
Shiga kawai tayi ba tare da ta ce masa komai ba.


Sai da ya fara tafiya kafin yace

"Hajiya ina zan kaiki?"


Rasa inda zatace tayi, dan babu inda ta sani a faɗin Abuja, ahankali tace

"ka kaini guri mai nisa daga nan ko nawa ne zan baka"

ta faɗa tana kifa kanta, shiru mai adaidaita yayi har suka iso inda yake ganin tayi nisa sosai da inda ya ɗauko ta.

Juyowa yayi yace

"Hajiya mun iso"

idanunta ta ɗago ta kallesa kafin tace

"bari in cire kuɗi sai na baka."


Dayake indaya kawota kusa da kasuwane, bata sha wahala ba ta cire a P.O.S ta bashi, godiya yayi ganin ta bashi fiye da kuɗin sa, yaja mashin ɗin sa yayi gaba.


Guri ta samu can gefe ta zauna, tana kallon área din, sai kuma ta miƙe, gurin wani mai sai da kati ta nufa a hankali tace masa, malam dan Allah akwai tashan mota anan, nuna mata yayi yace gashi can a gaba kaɗan

A hankali ta masa godiya kafin ta juya ta nufi tashan, dan gani takeyi har yanzu batayi nisan da ya kamata ba tunda suna gari ɗaya.


Tana shiga tasha, yaran tasha suka soma tambayanta inda zataje,

"inda yafi nisa"
kawai ta iya furtawa tana share hawayen da yaƙi tsayuwa a fuskarta

Yaron motan da ke son motan kano ya cika, yayi saurin faɗin,

"aikuwa Kano ne inda zakije, dan dai kam akwai nisa daga nan"

ya faɗa yana ƙoƙarin janta dan karta fasa tafiyan, miƙa masa ATM dinta tayi tace

"sai na cire kuɗin mota"

da sauri yace

"babu damuwa Madam, ga p.o.s nan ma"

sai da ta sake cirewa ta biya kuɗin motan, kafin ta soke sauran canjin, har mota ya cika tana jingine da window hawaye na sauƙa a fuskarta, sai da suka hau hanya sosai kafin ta lumshe idanunta a hankali ta furta


"Dama yaudarar kaina nakeyi, U never loved me,kuma zanyi nisa da kai, nisa na har abada."

(wannan shine dalilin Noor na barin gida har ta haɗu da su khamal)



Zannur kam tunda ya fito a gidan, direct hotel yayi booking, yana shiga ɗakinsa ya rufe kofar yana faɗawa kan gadon ɗakin, yana jin zuciyarsa na suya, shi zatace ma mazinaci, sai kuma ya yi ƙwafa, yana jaddada ma kansa,
bazai koma gidan ba har sai Taufeeƙ ya amsa masa tambayoyinsa nan da kwana uku, a lokacin zai kamata da hujja, daga haka ya miƙe ya wuce toilet.


Ranar da Taufeeƙ ya cika kwana uku, a ranar Zannur ya samesa a asibiti, da ƙyar Doctor ɗin ya bashi daman ganinsa.


Yana shiga, ya zuba ma Taufeeƙ idanu, yanda ya rame, oxygen ne a hancinsa, dan baya iya numfashi yadda ya kamata,

Kujera ya ja ya zauna kusa da shi ya riƙe hannuwansa, ga mamakin sa, sai yaga hawaye na gangarowa a fuskar Taufeeƙ.


Shafa hawayen yayi, kafin yace

"ka kwantar da hankalinka, ka sanar da Ni waya maka haka, duk da na riga na sani amma inaso inji daga bakinka, shin Noor ce ta caka maka wuƙa?"


Ya tambaya a ƙagauce

Zaro ido Taufeeƙ yayi sai kuma ya shiga girgiza kansa da sauri, sauƙe masa oxygen din yayi dan ganin kaman Yana son cewa wani abu

"Ba ita bace.. batasan komai akai ba.. watace daban..." kasa ƙarasawa yayi, jin an murɗa ƙofan ɗakin an shigo,

Yasira ce ta shigo, da basket a hannunta tana kallon yayannata, wanda shima ya ke kallonta, hawayen idanunsa na ƙara zuba,

juyowa yayi da niyyar cema Zannur ita ce, amma sai yaga Zannur ɗin ya miƙe, a hankali ya ƙara so ya maida masa oxygen ɗin, dan bayason suyi maganan a gaban kowa, shafa kansa yayi yace

"we will talk later ok"

Sai kuma ya juya ya kalli Yasira

"waya kawoki nan"

Da sauri tace "Sir dan Allah kayi haƙuri, na kasa jurewa, ina so inga yayana, shiyasa nazo"


"Babu komai" ya faɗa yana juyawa yabar ɗakin, dan hankalinsa gabaɗaya yana ga Noor a halin yanzu, dan kuwa ya tabbata ya mata laifin da zaiyi wuyan kankaruwa,

duk da Taufeeƙ bai faɗa masa wacece ta caka masa wuƙa ba, amma ya tabbatar masa ba Noor bace, hakan yana nufin zargin da yake mata ba daidai bane, fitowa yayi a gaggauce ya nufi motarsa, dan yana buƙatan magana da Noor ya wanke kansa.




Wlhy na gaji, naso mu dawo kan labari yau,amma dai saura ƙiris, mudawo.



Maimoon#

*💖ABNUR💖**

*By Maimoon*

*Elegant online writers* 📚📖


*Page 18*


A hankali cikin taku ɗai ɗaya, Yasira ta ƙaraso gaban Taufeeƙ, sai da ta sunjuyo dai dai fuskarsa, kafin tasa hannunta ta shafa fuskarsa.

"Yaya ya jikin?, Me kake faɗa ma masoyina?", ta faɗa tana kallon cikin idonsa.

Juyar da kansa yayi daga kallonta, yana jin ƙunar zuciya.


Sai da tayi ƙwafa, tana wani murmushi kafin tace

"Wato kana kan bakanka ko?, To bari kaji, Na rantse da Allah baka isa ba, yanzu zan ƙarasaka saboda bazaka ɓata min shiri ba".


Daga haka ta saka hannu ta cire oxygen ɗin, pillow ta ɗauko ta ɗaura akan fuskarsa, ta danna da iya ƙarfin ta.


Wani numfashi ya shiga fitarwa, yana miƙewa da kakkarwa a kan gadon, amma ko ajikin Yasira, sai ma sake dannawa da take da ƙarfi.


Jin numfashinsa na ƙoƙarin barin jikinsa, yasa ya ɗaga hannunsa yana bugawa a jikin gadon, cikin Sa'a kuwa hannunsa ya tabo madannin da mara lafiya yake dannawa idan yana buƙatar wani abu.


Ai kuwa ɗakin ya ɗau kuwwa, da sauri ta cire pillow ɗin tana mayar masa da oxygen ɗin cikin ruɗewa.


Nurses ne suka shigo,su kusan uku, da sauri suka ƙara so suna kallon Yasira, da ke gyara masa kwanciya.

"Madam wa ya baki daman shigowa nan?"

Daya daga cikin nurses ɗin ta tambaya tana kallon Yasira cikin tuhuma.


Cikin in ina tace

"dama yaya na ne, shine nazo na gansa, kuma...uhm"

Sai ta kasa ƙarasawa.

"Ok ke relative ɗinsa ce?"

Da sauri tace

"eh nice kaɗai Ƙanwarsa."

"Ok to but ba lokacin ganin mara lafiya bane yanzu!, saboda haka ki dawo right time."


"Eh dama abinci na kawo masa, dan Allah ku barni in bashi."


Ɗaya daga cikin nurses ɗin tace bakiji

"me akace bane, ki dawo lokacin da ake ganinsa Please"


Babu yadda ta iya haka juya ta fita, a ranta tana faɗin

"babu damuwa akwai wani lokacin, amma ina mai tabbatar maka bazan taɓa bari ka haramta min muradin zuciyata ba."


Daga haka ta fice tana murmushi.


Tunda Zannur ya shigo gidan, bai bi takan duk masu gaishesa ba, ya nufi sama, da sassarfa, Allah Allah,yake ya gansa a gaban Noor.

Murɗa ƙofan ɗakin yayi ya shiga, tsayawa yayi daga bakin ƙofan yana kallon kayan da ta zubo dasu daga cikin sif ɗin, ba tare da tunanin komai ba ya ƙaraso cikin ɗakin, ganin bata ciki yasa shi ƙarasawa ƙofar bandaƙin, dan ya tabbata tana ciki, jiki a sanyaye ya soma magana

"Noor, bansan me zance miki ba, wallahi ina matuƙar kunyar ki, Taufeeƙ ya tabbatar min zargina ba daidai bane." sai kuma yayi tsaki

"Mtseewww me ma nakeyi?" Ya faɗa yana dafe kansa, sai kuma ya cigaba

"Noor please ki fito ki saurareni, bakin ce kina so kiji abinda nake so na faɗa miki ba rannan?, to yau zan faɗa miki na miki alƙawari."

Jin bata fito ba ya sashi, ɗaura hannunsa akan handle ɗin

Yana shirin magana yaga

Please Login or Register in order to submit comment