Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

makulli

Ƙwafa tayi,tana jin zuciyarta na suya, a fusace ta ƙarasa gaban allon ta yi wurgi dashi, tana faɗin,
"na tsaneki, ya zan yi da ke?, kin zame min annoba, kin kasa barina in ji daɗin rayuwata."

sai kuma ta juya a fusace ta bar ɗakin tana huci.

Falonta ta wuce, inda ƴan mata biyu da namiji ɗaya ke zaune suna video game, babbar cikinsu bazata fi 15 ba sai mai bi mata wacce ita ma bazata fi 10 ba namijin kuwa bazai fi 7 ba,

A fusace tace, "farhaana, ku wuce falonku, ku barmin falona bana son hayaniya yanzu"

Da sauri farhaana tace, "Ammi Are You ok, ke da papi ko?"

Bata kulata ba, sai zama da tayi ta riƙe kanta da duka hannuwanta, da sauri farhaana ta kora ƙannen nata suka wuce part ɗin su, tana tunanin sai yaushe papi zai koma kamar kowa?, sai yaushe zai zauna tare da su kamar yadda ko wani uba yake zama da ƴaƴansu?


************

Tunda Maami ta zo, Zannur ya canza mata,

gabaɗaya Noor ta rasa gane ina ya dosa, a gaban Maami kulawa yake bata da har take jin dama har zuciyansa yake mata hakan, amma inaa, bayan idon Maami banda harara babu abinda ke haɗashi da ita, a rashin sanin ta kuwa duk wani shiga da fitanta akan idanunsa takeyi, dan kuwa yana iya yini yana kallon ta a laptop ɗin sa, Taufeeƙ ya tafi Bangaladash saboda wakiltar Zannur akan wasu ayyukansa,hakan yasa bata ganinsa, Asabe da Amina kuwa, kullum cikin ɗebe mata kewa da sakata dariya suke, Yasira ta sake kamar babu komai a zuciyarta, but ita kaɗai ta san gagarumin abinda take shiryawa wanda zai ruguza farin cikin duka ƴan gidan.


Satin Maami biyu ta koma Dubai, da kewan Habibi da kuma Noor, dan kuwa shaƙuwa sosai ya shiga tsakaninsu, ta sake wayar mata da kai akan abubuwa da dama, sannan kafin ta tafi ta sa an nemo mata malamai har biyu na islamiyya da boko tana cigaba da karatunta, a halin yanzu Noor Bata da wata damuwa da ya shige ta Zannur, amma shiɗinma sam bata saka shi a rai ba bare ya hanata walwala.


12 ga watan August dai dai da cikar Noor shekara ɗaya da wata huɗu a gidan, shine ranar da abubuwa suka fara canzawa, ƙaddarar da bazata taɓa mantawa ba, da duk wani wanda yake gidan ya faru wanda yayi sanadiyar ruguza duk wani hasashen farincikin Noor.................



Kuyi haƙuri page ɗin yau yayi kaɗan, bana ɗan jin daɗi ne shiyasa, Amin uzuri


Maimoon#

*💖ABNUR💖*

*By* *maimoon*

*Elegant* *online* *writers* 📚📖

*Free* *book*

*Page* *15*



I DEDICATE THIS PAGE ENTIRELY TO MY NIMCYLUV, I LOVE YOU SO VERY MUCH, THANKS ALOT FOR THE SUPPORT, AND I WONT FORGET TO THANK DUK MAI KARANTA ABNUR, I REALLY APPRECIATE THE LOVE, MORE ESPECIALLY ABNUR GROUP, I CAN'T LOVE YOU GUYS LESS, AND YOUR PRAYERS ALWAYS GOT ME, BAN MA SAN ME ZANCE BA, YOU GUYS ARE THE BEST,


******

12 ga watan August,ya kama ranar Laraba, tun safe ta ke jin matsanancin bugun zuciyan, da batasan dalilinsa ba,
tunda ta yi breakfast tare da Zannur, ba ta sake sakashi a idonta ba, har wannan lokacin, wanda agogon dakin ya nuna mata karfe 3:30 kenan.



Littafin umdatul ahkam ɗinta da ta ke biyawa ta ajiye kasancewar muallimar bata jima da tafiya ba, a hankali ta dafe ƙirjinta da ke bugu.

Akan laɓɓanta ta furta "hasbunallahu wa ni'imal wakil,auzubillahi minashaiɗani rajeem, Allah kasa inga Alkhairi."


Sai kuma ta miƙe, ta nufi kitchen gurin su Asabe, nan ma bata iya zama ba, duk da yadda suke janta da hira amma ta kasa sake jikinta, daga ƙarshe takoma ɗakinta, kwanciya tayi taja bargo tayi shiru ko zata samu bugun zuciyar nata ya ragu.


A hankali ya buɗe ƙofar ɗakin nata ya shigo,

zurfin da tayi a tunani, yasa bata ma ji shigowar sa ba, harɗe hannuwansa yayi a ƙirji ya na kallonta a inda take kwance.

zuwa yanzu ya gama gasgata ma kansa, ya na matuƙar so da ƙaunar Noor, sake ware idanunsa ya yi a hankali a kanta, ya na jin yanda zuciyarsa ke bugawa, a cikin shekara ɗaya da wata huɗun da suka zauna waje ɗaya da ita, baya shiga harkarta, shi kaɗai yasan irin azabtuwar da zuciyar sa keyi bazai iya jurewa ba, ya gaji da kallonta daga nesa ko kuma ta cctv,dole ya sanar mata tsantsan soyayyarta dake zuciyarsa.



A hankali ya ƙarasa, kasancewar barci har ya fara ɗibanta, sam bata ji alamarsa ba, har ya hayo gadon, bargon ya shiga sannan ya jawota ya rungume ta sosai a ƙirjinsa, sai lokacin ta lura, ai kuwa ta buɗe baki zata kurma ihu yayi sauri toshe mata baki da hannuwansa, zare ido ta shiga yi, dan bata ma gama tantance waye bane, duk da ƙamshinsa na SHUMUKH da ya karaɗe ko ina, amma sam ta kasa nutsuwa, dan ta tabbatar Zannur, dai bazai taɓa hawa gadonta ba, balle har ya rungumeta haka,

ganin ta gagara ihun ya sa ta fara shure shure, ta ƙi nutsuwa.

Dariya ma ta bashi, ita a dole ga mai ƙarfi, a cikin kunnenta ta raɗa mata

"Baby, mijinki ne fah"

Wani banbaraƙwai taji zancen, amma sai ta rage shure shuren ta na ɗago idanunta ta kallesa, ganin ta nutsu yasa ya sake mata bakinta, ya lumshe idanunsa, sannan ya buɗe.

Tashi yayi da ita a jikinsa, ya zaunar da ita akan ƙafafunsa,sannan ya juyo da ita tana fuskantar sa, cikin murya mai nuna kulawa da tayi daban da na Zannur ɗin da ta sani yace

"Noor!"

Kasa amsawa tayi, saima sunkuyar da kanta da tayi, tana wasa da yatsunta, dan gaba ɗaya a takure take, kasancewar basu taɓa kasancewa very close irin na yau ba.


Jin bata amsaba, sai shima bai damu ba, ya cigaba da maganan sa,

"Noor, nasan Zaki yi mamaki, abinda ya kawo Ni ɗakinki har kan gadonki, but ba abin mamaki bane, idan kika yi la'akari da matsayina a wajenki, sannan yau yayi daban da duk ranakun da muka kasance tare da ke, a yau ina so in faɗa miki wani abu mai matuƙar muhimmanci da yafi komai muhimmanci a rayuwata yanzu,

sai da ya ɗan yi shiru kasancewar yayi maganan da yawa sai kuma ya nisa kafin ya furta kalma mai matuƙar nauyi a wajensa wato 'Please' dan dai banda Abbu da Maami, baya tunanin ya taɓa cewa wani please.


A hankali yace "pleaaaaase Noor, Ina so kiyi min kyakkyawar fahimta, sannan kar ki hukunta Ni akan laifuka na a gareki."


Jin yayi shiru ya sata ɗagowa suka haɗa idanu, da sauri ta sunkuyar da kanta, dan ta kasa gane inda maganganun sa suka nufa, sannan ita bai mata laifin komai ba, hasali ma bata da wani wanda take matuƙar darajawa da kuma so da ƙauna kamar sa, dan shi ya tsamota sannan ya tallafa mata bayan Nennen ta,

Amma ita tasan ya fi ƙarfinta har abada, bazata taɓa samun shi ba, cigaba tayi ta wasa da yatsunta, dan ta rasa me zata ce masa.


zagayo da hannuwansa duka biyu yayi akan cikinta, batasan sanda ta sauƙe ajiyar zuciya ba tana sake sunkuyar da kanta dan wani irin kunyarsa ce ta kamata lokaci ɗaya, muryarshi taji dai-dai kunnenta da har sai da tsigar jikinta ya amsa, cikin raɗa ya ce,

" kin bani dama in faɗa miki abinda yake raina da zuciyata, and you promise you won't judge me?"

Ya faɗa da sigar tambaya dan so ya ke ta buɗe baki tayi masa magana.


girgiza masa kai alamar Ah ah,
da sauri ya ɗago fuskarta yana kallonta,

"why" ya faɗa yana ƙoƙarin cigar da ƙwayar idonsa nata,amma ta ƙi.


Cikin inda inda tace

"saboda lokacin sallah yayi, ka bari ka dawo daga masallaci"

Wani ɓoyayyen ajiyar zuciya ya sauƙe yana jan hancinta, sai kuma yace,

"ok wifey your wish will always be my command."

daga haka ya ɗaga ta daga jikinsa, ya sauƙa a kan gadon.

A bayan gidanta ya yi alwala, sannan ya fice a ɗakin,

Ita dai da ido kawai take binsa, yau gabaɗaya ya canza mata, sai kuma tayi murmushi itama ta miƙe ta wuce toilet dan yin nata alwala

********

"Ka saurareni Sir Taufeeƙ, wallahi idan har ban samesa ba mutuwa zanyi, dan Allah ka taimaka min, pleaaaaase"

ta faɗa tana kuka wiwi kamar ranta zai fita
Wani irin kallo yayi mata na tsana, kafin ya soma magana cikin matuƙar ɓacin rai


"Yasira ke wace irin mara tunani ce, taya zakiyi tunanin Sir zai taɓa sonki, bare har ya zauna tare dake, kin manta irin taimakon da ya mana, a lokacin da namu dangin suka wofintar da mu, tayaya ma zaki fara tunanin rama alkhairi da sharri."


shiru yayi yana furzar da numfashi, kafin ya cigaba

"Wallahi tallahi, ni Taufeeƙ Muntasir, idan har ina raye bazan taɓa bari ki ruguza farincikin Sir Zannur ba, idan baki sani ba ki sani, Noor itace kaɗai wacce Sir zai iya rayuwa da ita, saboda shi kanshi ya fara sonta ne batare da ya sani ba, kuma idan har ina raye zai zauna da wacce zuciya, ruhi da gangar jikinsa keso ne, ba son raina ba, ko kuma son ran ƴar uwata Yasira Muntasir ba."


Daga haka ya juya yana shirin barin gun,

da gudu ta ƙara so ta riƙe ƙafafuwan sa tana faɗin,

"yaya wallahi bazan iya rayuwa babu shi ba, mutuwa zanyi, ita Noor ɗin mai ka haɗa da ita, da ka zaɓe ta akaina, wallahi zan iya kasheta akan na mallaki Sir Zannur, Ni kaina bansan wani irin so nake masa ba, pleaaaaase Yayana ka taimaka min"

Dakatawa yayi yana kallonta sai kuma ya naɗe hannuwansa a ƙirji yana faɗin

"ok to yanzu me kike so in yi miki"

hawayenta ta shiga gogewa cikin sauri tace

"yaya so nake Noor ta bar duniyan nan, ko kuma ta yi nisa da mu, yadda zan samu daman rayuwa da Sir Zannur Ni kaɗai"

Wani kallo da yake binta da shi yasa ta gagara ƙarasa zancen tana kallonsa

"Yasira when did you turn to be a monster ban saniba, how could you even think of that, kin San me kike faɗi kuwa, wallahi billahi, kiyi hanzarin cire wannan banzan tunanin daga kanki, sannan yanzunnan ba sai anjima ba zan je na sanar da Sir Zannur duk abinda kike shiryawa, yasan yanda zai yi dake, bana son yayi la'akari da cewa ke ƴar uwata ce, don kuwa kin zama guba a cikin mutane, idan har zaki iya tunanin kisa"


daga haka ya juya ya fice a ɗakin yana huci.


kamar zautacciya haka ta miƙe daga durƙuson, tana faɗin


"Zaka faɗa ma Sir, wallahi babu wanda ya isa ya rabani da Sir koda kuwa uban da ya kawoni duniya ne bare kai da muke ƴan uba, badai idan har kana raye ba to wallahi yanzu zaka bar duniyan nan."

daga haka ta fice da sauri, har tana haɗa wa da gudu ta nufi kitchen, su Asabe da ke aikin girki, basu ma lura da ita ba, da sauri ta zari wuƙa ta cusa cikin zaninta, ta fice a kitchen ɗin da sauri.


A tsakar gida ta riske shi, shi kaɗai yana Safa da marwa, tunanin abinda ƙanwar tasa take shirin aikatawa ya hanasa sukuni, ƙarasowa tayi ta na faɗin

"yaya"

Idanunsa da suka kaɗa suka yi ja,ya ɗago ya zuba mata, yana mata wani irin kallo

"yaya dan Allah kayi haƙuri, wallahi nayi dana sanin abinda na furta tun farko dan Allah yayana"


Juyowa yayi sai kuma ya kasa cewa komai.


"yaya dan Allah muje garden muyi magana,na maka alƙawarin, zanyi duk yadda yace."

Wani ajiyar zuciya ya sauƙe yana faɗin

"ok muje"


Har cikin garden ɗin suka shiga sai da ta tabbatar su kaɗai ne kafin ta soma kukan ƙarya tana faɗin

"yaya dan Allah, yanzu bazaka tausaya min ba ka duba halin da nake ciki"

Cikin ƙunar rai yace

"kina kan bakan ki kenan, ai nayi zaton kin haƙura ne shiyasa ma na biyoki nan, kuma banga amfanin zama na a nan ba, tunda bazaki ji magana ta ba, kiyi duk abinda zuciyarki ta raya miki, nima kuma ina mai tabbatar miki, zanyi duk abinda zuciyata ta raya min dan ganin ba abinda ya samu Sir Zannur ko kuma Madam Noor."


Daga haka ya juya zai bar gurin.

Cikin ƙaraji ta nufe sa da wuƙar, juyowa yayi da sauri, amma ko kafin ya farga, ta luma masa wuƙar a cikinsa, tana kuka, tana faɗin

"meyasa baka barni da zaɓi ba yaya, dan Allah ka yafe min amma bazan iya zuba maka ido ka ruguza min farin ciki na ba"
sake luma wuƙar tayi tana jujjuyasa a cikinsa, wani irin murmushin takaici yayi, amma ya gagara ko da motsi saboda azaban dake ratsa shi, sannan bakinsa ya gagara furta komai,

Dafa shi tayi ta zare wuƙar ta sake caka masa ita, dan bata so ko kaɗan ya tsira, tanayi tana kuka wiwi, daga ƙarshe ta hankaɗa shi ya faɗi a wajen.

Da sauri ta bar wajen tana bar masa wuƙan a cikinsa, ɗakinsu ta wuce, ta shiga banɗaki tana ƙoƙarin dai dai ta nutsuwarta, wanke hannunta tayi da fuskarta, sannan ta fito a bayin, sai data gyara fuskarta, sannan ta fito ta nufi ɗakin Noor, wacce ta idar da sallah kenan, tana jiran Zannur, dan ta ƙagu ta ji abinda yake son sanar da ita.


Knocking tayi, cikin sauri tace "come in."

A zatonta Zannur ne, ganin Yasira yasata ɗan haɗe fuska ba tare da tace komai ba, cikin in ina, ta soma faɗin

"Ma, daman Sir ne yace ki samesa a Garden yanzu"
ta faɗa tana sunne kanta,
Kamar bazata kula ba sai kuma tace

"kice ina zuwa"

"Ok Ma" ta faɗa tana barin ɗakin da sauri,

miƙewa tayi ba tare da ta cire hijab ɗin da tayi sallah ba, ta naɗe sallayan ta ajiye sannan ta zura takalman ta ta fice a ɗakin, dan gudun kar ta ɓata masa lokaci.

Yasira da ke tsaye, tana kallonta ta wuce, ta sauƙe ajiyar zuciya, duk ac ɗin dake gurin, amma gumi take haɗawa, tana tsaye sai ga Zannur zai wuce ɗakin Noor, da sauri ta fito daga inda ta maƙale tana mai shan gabansa,

dakatawa yayi ganin ta a gabansa, "lafiya" shine abinda ya furta yana kallonta yadda duk take a birkice

"Uhm babu komai Sir, dama ce maka zanyi, Madam bata ɗakinta, tun fitarka naga ta tafi Garden, da alama akwai abinda suke tattaunawa da Sir Taufeeƙ."


Shiru yayi yana karantar ta sai kuma yace
"Taufeeƙ?"

Da sauri tace "eh"

Bai sake cewa komai ba ya juya ya nufi Garden ɗin yana tunanin to me suke tattaunawa kuma da Taufeeƙ.


Cak ya ja ya tsaya, numfashin sa na ƙoƙarin fin ƙarfinsa, ganin Taufeeƙ cikin jini mala mala, ita kuma tana tsugunne a gabansa tana kuka wiwi, da wuƙa a hannunta, sannan duk hijab ɗin ta ya ɓaci da jini.


Kasa gane tunanin da zaiyi yayi, dan dai ya gagara gane me ke faruwa a wajen

Taufeeƙ dai, personal assistance ɗinsa,Wanda yake gani kamar ɗan uwansa, wanda ya riƙe da amana, yake jinsa a cikin jininsa, shine a kwance a cikin jini.

yayinda matarsa, wacce yake jin bazai iya rayuwa ba tare da ita ba, wacce ya gama gasgatawa kansa ta cancanci ta zama mahaɗin rayuwarsa, itace a durƙushe akan Taufeeƙ da wuƙa, no it's not possible.


Da sauri ya ƙarasa wajen yana ɗagota

Faɗawa jikinsa tayi tana sake fashewa da wani irin matsanancin kuka,

"Wallahi a haka na zo na gansa, bansan wa ya masa haka ba, mu kaisa asibiti kar ya mutu."


Kasa cewa komai yayi, saima ɗaga ta da yayi daga jikinsa, cikin tsananin tashin hankali, ya sunkuya ya rungume Taufeeƙ tsam a jikinsa sai kuma ya ɗauke sa cak, ya nufi barin Garden ɗin dashi, yana iya ƙoƙarin sa ganin ya hana kansa hawaye, gudu gudu ya fito dashi, daga cikin Garden ɗin jikinsa na wani irin rawa,

Da sauri bodyguards ɗin sa suka ƙara so, amma sai ya ƙi basu shi, ɗaya daga cikinsu ya buɗe masa mota ya kwantar da shi a baya, ya gagara furta komai a bakinsa, zagayawa yayi ya shiga mazaunin driver.

Noor da ta biyosa ganin zai tafi ya barta, ya sa tayi saurin buɗe motar ta shiga, bai ce mata komai ba, ya tada motar, ya fice a gidan, bayan ya hana bodyguards ɗin binsa.

Gudu kawai yake shararawa, akan titi, amma gani yake baya sauri sam, ita kam banda kuka babu abinda take, satan kallon sa tayi, taga yadda fuskar sa tayi jajazir, amma babu ko ɗigon hawaye, kana ganinsa zata fahimci tsantsan tashin hankalin da yake ciki.

Tafiyar minti talatin ne zuwa asibiti, amma a minti sha biyar ya isa, da sauri ya fito, ya ma rasa mai zai yi, cikin asibitin ya nufa har da gudunsa, ita dai tana, zaune a motan, taga sun fito daga cikin asibitin tare da nurses da gado.

Buɗe motan tayi ta fito, nurses ɗin suka ƙaraso, suka ciro Taufeeƙ aka kwantar da shi a gadon suka nufi cikin asibitin dashi.

Daƙyar Zannur ya samu suka yi attending ɗinsa, kasancewar sun sansa, dan cewa sukayi sai an saka police a cikin lamarin.

Tunda aka shiga da Taufeeƙ ɗakin, yake Safa da marwa ya gagara, zama, ita kanta ta gagara daina kuka.

A hankali ta ƙara so inda yake tana faɗin

"Kayi haƙuri insha Allahu zai samu lafiya"

Wani irin kallo da ya watsa mata ya sata saurin yin baya, dan bata taɓa ganin yayi ma wani irinshi ba, bare kuma ita.


Cije lips ɗinsa, yayi, amma ya kasa cewa komai,

Likitan da ya fito ne ya sashi, saurin ƙarasawa yana faɗin

"Doctor ya ɗan uwa na yake"
Dafa shi Doctor ɗin yayi sai kuma ya girgiza kai kawai"

Da sauri ya sha gaban doctor ɗin dake ƙoƙarin wucewa yace

"tell me is he alive"
Shiru doctor ɗin yayi sai kuma yace

"He is alive, but bayan nan babu abinda zan iya ce maka saboda cause he is in a very critical condition, dan he may slip into a coma"

Daga haka ya juya ya bar wajen.

Baya yayi jikinsa na wani irin rawa, sai lokacin yaji hawaye na sauƙa akan fuskarsa.......





Maimoon#




*💖*ABNUR💖**

*By Maimoon*

*Elegant online writers*📚📖


*Free book*


*Page 16*


Itama durƙushe wa tayi a wajen tana kuka,
ta ma rasa tunanin me zatayi, wani irin tsana ne da har zai sa mutum yayi ƙoƙarin kashe mutum ɗan uwansa, wannan wani irin ƙaddara ce da ta faɗa musu.


A hankali ta ɗago idanunta, tana kallonsa, yadda ya samu guri can gefe ya zauna, yayi shiru, kai tsaye bazaka taɓa gane me ya ke tunani ba, sam sai taji batason ganinsa a haka, zuciyarta bazata iya ɗauka ba.



A hankali ta nufe sa, har tazo dab dashi bai ɗago ba, kansa a sunkuye yake, gashin kansa ya sauƙo ya rufe fuskarsa, saboda sunkuyar da kan da yayi.


Tsugunnawa tayi dai-dai ƙafafunsa, ta lalubo hannuwansa ta riƙe gam.


Sai lokacin ya ɗago kansa, yana sauƙe idanuwansa a kanta, yadda idanuwansa suka kaɗa sukayi jajir, har sai da gabanta ya faɗi, amma sai ta dake.


Cikin ido take kallonsa, kafin a hankali ta soma magana, cikin muryarta mai matuƙar sanyi.

"Dan Allah kayi haƙuri, ka zama musulmin na ƙwarai, mai yarda da ƙaddara, yau koda ace Taufeeƙ ya mutu ne, babu yadda muka iya, saboda Allah ya riga ya rubuta kwanansa ya ƙare, bare yana raye, kuma insha Allahu zai farfaɗo, kamar yau zai tashi akan ƙafafuwan sa, nasan yana da muhimmanci a wajenka, but dan Allah ka masa addu'a, kar ka kasance cikin waɗanda basa komawa ga Allah idan masifa ta samesu, kuma na yarda da kai, ɗari bisa ɗari, zaka nemo duk wanda ya aikata masa hakan kuma ka hukunta shi, hukuncin da ya dace dashi."


A hankali hawayen da ta ke ta ƙoƙarin dannewa, ya sauƙo a kan fuskarta, dan ita kanta ba juriyar ce da ita ba, but ganin haalin da yake ciki yasa dole ta danne nata raunin.


Kallonta kawai yakeyi, ya kasa cewa komai, a hankali ya sa hannunsa yana share mata hawayen da ya zubo a samman kyakkyawar fuskarta, sai kuma ya ɗagota gabaki ɗaya daga tsugunnen da tayi a gabansa, kusa da shi ya zaunar da ita, yana sauƙe numfashi, ɗago idanunta tayi, suka haɗa ido dashi har lokacin hannuwansu na cikin na juna, a hankali kuma ya kwantar da kansa a kan kafaɗar ta, yana ajiyar zuciya,


Zare hannunta tayi daga nasa, ta maida a kansa tana shafa gashin, gyara masa sumar tayi, tana cigaba da shafa kansa, tana jin zuciyarta na ƙara tsananta bugu.


Har kusan magrib, suna zaune a haka, sai lokacin ya ɗago kansa, gani yayi ta jingina bayanta da kujeran, ta lumshe ido, alamar bacci ya ɗauke ta, tashi yayi ƙoƙarin yi, amma sai yaji ta sake damƙe dayan hanunsa da ke cikin nata, bai san sanda yayi murmushi ba, yana sake kallonta, irin kallon da bai taɓa nutsuwa yayi mata ba, kallo yake mata ma ƙurilla.



Juyar da kanta tayi tana ɓata fuska dan sam baccin kawai ya ɗauke ta ne, amma ba dan tana jin ɗaɗinsa ba, lips ɗin ta ta motsa a hankali, kamar zatayi magana, sai kuma ta maida su tana tsotsan na ƙasan, ƙuri yayi ma lips ɗin nata da ido, yana kallonsu, sai kuma yayi saurin juyar da kansa, yana shafa sumarsa, wacce ta ke ɗabi'arsa.



A hankali ta buɗe idanunta, sai kuma ta ɓata fuska tana gyara zamanta akan kujeran, motsinta da yaji, yasa ya juyo yana kallonta, sai kuma ya mata murmushi yana faɗin,

"Zaki tafi gida yanzu!"


Cikin innocent and calm voice ɗinta tace " tare zamu tafi?"


Ta faɗa da sigar tambaya, kwaikwayon yanda tayi maganan yayi yana faɗin

"ke kaɗai zaki tafi"

Sai da ya ɗan nisa kafin ya sake damƙe hannunta yana faɗin

"bazan iya tafiya na barshi ba, Taufeeƙ yana cikin mutane masu muhimmanci a rayuwata, zan iya cewa he is my only friend, saboda bani da aboki, but ya fiye min kowani irin aboki, for the past 16 years, da nake tare dashi, bai taɓa bani ƙofar da zanyi complain ba, he was with me tun Ƙanwarsa Yasira tana da shekara biyar, shine ƙadai gatan ta, duk da kasancewar ba ciki ɗaya suka fito ba, but sukaɗai suka taso, cikin maraici, da rashin gata,
a lokacin babansu was a drunkard, mashayin giya ne, wanda bai damu da iyalinsa ba, hakan yasa iyayensu mata suka bar gidan.
Taufeeƙ Yana son Yasira sosai hakan yasa da ya yanke shawarar barin gida, ya taho da ita, dan yana ganin she can't handle all that alone.

tunda na haɗu dashi nake matuƙar jinsa a jikina, saboda mutum ne shi mai amana, Maami kanta tasha faɗa min Taufeeƙ mutum ne in riƙesa, haka zalika Abbu, sai kuma yayi shiru, kallonta ya kuma yi sai kuma kawai ya jawota ya rungumeta sosai a jikinsa, kamar wani zai raba sa da ita, ita ma bata hanashi ba sai ma kwanciya da tayi shiru a jikinsa tana jin yadda zuciyarsa ke bugawa da ƙarfi.


Cikin ɗacin rai ya cigaba da magana

" bazan taɓa yafewa duk wanda yayi masa haka ba, koda kuwa waye ne shi a wajena, sannan zan gano ko waye ne, kuma zan hukuntasa da mafi raɗaɗin hukunci,"

sai kuma ya sake yin shiru yana sauƙe ajiyar zuciya.


Itama shiru tayi ba tare da tace masa komai ba, tana fatan Allah ya sassauta masa zuciyarsa, ya bashi daman yanke hukunci, cikin nazari, dan idan rai ya ɓaci, hankali gushewa yakeyi.


Ɗagowa tayi daga jikinsa, tana sake kallonsa tace


" ba zaka tambaye Ni me nakeyi a kusa da Taufeeƙ ba "


Da sauri ya juyo yana kallonta, sai kuma ya shiga girgiza mata kansa, ba tare da yace komai ba.


Kuka ta shiga yi a hankali, kafin ta buɗe bakinta tana ƙoƙarin faɗa masa abinda ya kaita Garden ɗin, har ta riski Taufeeƙ a haka


Da sauri ya saka yatsansa a bakinta yana kallon tsakiyar idonta


"Shhhhhh not another word, ko ki faɗa min, ko karki faɗa min, nasan a haka kika samesa, bazaki taɓa koda tunanin kisa ba, bare har ki aikata, i trusted you after so many trials, so baki da buƙatar yi min bayanin komai"

Kallonsa kawai takeyi, itama ta kasa cewa komai.


"Yanzu ki tashi, za'a kaiki gida, nima zan dawo idan na tattauna da Doctor ɗin kinji?"

Hawayenta ta share, kafin ta miƙe a hankali tana kallonsa, shima miƙewa yayi, har ta kai ƙofa, sai kuma ta dawo da sauri ta rungume sa, tana

Please Login or Register in order to submit comment