Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

you really think this is a good idea!?, is this the right step daya kamata ka ɗauka!?"

abinda zuciyarsa ke tambayan sa kenan.

Da sauri ya furta

"wannan shine right step ɗin da ya kamata na ɗauka, idan ba haka I will regret it for the rest of my life"


Da mamaki Taufeeƙ ya kalleshi yace

"Sir Are You ok"


Sai lokacin ya gane ashe a bayyane yayi maganar
"i am alright" ya faɗa a taƙaice yana cigaba da tafiya.


Dai dai layinsu yaja ya tsaya, yana kallon cincirindon mutanen dake tundaga farkon layin,
zuciyar sa ce ta buga da tsananin ƙarfi,da har sai da ya dafe ta, ya juya ya kalli Taufeeƙ ya ce
"what's going on there?"


Da sauri Taufeeƙ ya amsa da,
"I have no idea Sir,but ko na bincika maka...?"

kafin ma ya ƙara sa maganan, yaga ya sake trolley ɗin,ya nufi layin cikin sassarfa.


Taufeeƙ ya bishi da kallo, shidai daga jiya zuwa yau,he is confused, ya rasa me ke faruwa da Sir Zannur.



A dai-dai ƙofar gidan ya tsaya, yana kallon kowa, sai kuma ya ƙarasa wajen wani matashi da ke tsaye can gefe, hannu ya miƙa masa, suka gaisa, sannan ya tambaye sa abinda ke faruwa.

cikin alhini saurayin ya fara faɗa masa
"wallahi bawan Allah, matar gidan ne Allah ya mata rasuwa jiya cikin dare, abinda zai baka tausayin ma bazai wuce ƴar da ta bari ba.
Dama can batada uba, gashi tana da ƙarancin shekaru, ga maman ma ta tafi ta barta,wallahi tun jiyan an kasa gane kan yarinyar, abin tausayi wallahi", ya ƙara sa faɗa yana matso hawaye.



Baya yayi yana kallon matashin,kansa na wani irin juyawa,maganar da suka yi da ita jiya kawai yake tunawa,kenan wasiyya ta bashi ko me!?



Ya juya ya nufi cikin gidan, bai damu da mutanen da ke kallonsa ba,

mata ne birjik a cikin gidan,ya ma rasa ta ina zai fara nemanta,wata tsohuwa dake
Zaune akan tabarma tace"yaro lafiya daga ina haka" da sauri ya russuna yayi musu gaisuwa,suka amsa.


Kawai sai ya miƙe,dan ya rasa ma me zai ce,fitowa yayi waje ya koma can gefe ya tsaya.


Taufeeƙ da ya mayar da kayan su ya dawo,dan yaga alama babu tafiyar,ya ƙaraso wajensa yana tambayansa abinda ke faruwa.


"Taufeeƙ ta rasu,ta tafi ta barni da alƙawarin da bansan ta yaya zan fara cikasa ba,I thought zafin ciwo ne ashe wasiyya take bani,ya zanyi,tell me what exactly I should do!?


Ya tambaya yana kallon Taufeeƙ,wanda ya sake shiga cikin duhu,dan bai fahimci komai ba a cikin maganganun Sir Zannur ɗin,
amma ganin yadda hankalinsa yake a tashe,ya sashi dafasa ya ce

"first of all,You have to calm down Sir,kasa a ranka komai muƙaddari ne daga Allah, sannan ko wani step zaka ɗauka, ka tabbatar kayi tunani mai zurfi akansa,
though bansan abinda yake faruwa ba,but ina maka fatan ka ɗauki right steps,kuma Allah yana tare da kai, so Please ka kwantar da hankalinka".



Shiru yayi,yana sauƙe ajiyar zuciya kawai,bai sake cewa komai ba, but yaji nauyin ya ragu a zuciyar sa, a hankali ya furta

"Thank you"

"No please Sir,it's always my pleasure,ban cancanci kamin godiya ba Sir,dan komai nayi maka ban biyaka ba"


Murmushin ƙarfin hali yayi masa sannan ya juya ya bar wajen.



Tare dasu aka kai Nenne gidan ta na gaskiya,
har aka watse yana tsaye a kan kabarinta, Taufeeƙ ya ƙaraso wajen sa yace "Sir...."

Da sauri ya katse sa " I will meet you outside"

Juyawa kawai Taufeeƙ yayi ya bar wajen yana jinjina girman abinda Nenne ta faɗa ma Sir,da ya ɗaga masa hankali har haka.



Zama Zannur yayi a hankali,dai dai kabarin, a hankali yace,

"Meyasa kika zaɓeni, acikin duk mutane, bayan baki sanni ba,kuma kika tafi kika barni da responsibility mafi girma a rayuwata,


Shiru yayi kamar mai jiran ta bashi amsa, sai kuma ya miƙe da sauri.


Bai sake waiwaya wa ba, ya fice daga maƙabartar,yana jin wani nauyi a zuciyarsa.


Gidan su Noor ya wuce kai tsaye, ga mamakinsa sai yaga babu kowa kamar ba gidan mutuwa ba,ƙarasowa yayi,yana kallon yadda har tabarmar an naɗe,

bai gama mamaki ba sai da ya shiga cikin gidan, tsayawa yayi yana kallon tsakar gidan, nan ma babu kowa, mamakin sa yakasa ɓoyuwa.



Tsohuwar ɗazu ce ta fito daga ɗakin Nenne tana faɗin "to Allah ya ƙara bamu haƙuri".



Ganin fita zatayi yasa yayi saurin faɗin "Granny"
juyowa tayi badan ta gane me yace ba,sai dan ganin su kaɗai ne a tsakar gidan,
"yaro me ka dawo yi kuma"ta tambayesa tana kallonsa.


Cike da mamaki yace"ina kuke tafiya kuma Granny?,naga babu kowa, masu karɓan gaisuwa"


Tsohuwar ta kunce zaninta ta ɗauko jan goronta ta gutsura sannan ta kallesa tana faɗin
"yaro zaman me kuma za'a yi?, a wannan ƙauye ai ba'a zama, ana kai mutum, shikenan kuma kowa zai kama gabansa,wanda ya mutu ai ya riga ya mutu koh?

Ta faɗa tana kallonsa,
Baisan sanda ya furta
"to ita kuma yarinyar ya zakuyi da ita!?"


Tsohuwar ta ƙara kallonsa tana faɗin "ya kuwa zamuyi da ita,wanda ya ga zai iya sai ya aiko mata da abinci, kafin dai ta warware,
ai akwai inda Uwar yarinyar take aiki,gidan mai garin garinnan, Ni bance ma ƴar ta sani ba, ita ma sai taje ta dinga yi tana samun abinda zata ci,ah toh kowa ma fama yake da kansa"



Ta faɗa tana juyawa tana ƙoƙarin barin gidan.

"naga alama kai baƙo ne shiyasa har kake tambaya wai ya zamuyi da ita,to Ni kuwa me zan mata, ai kawai Allah ya bata haƙurin rashin uwa da tayi,
ƴar makarantar da take zuwa ma ai yanzu kam ta ƙare".
kallonta kawai yakeyi har ta fice tana cigaba da mita.


Sai yanzu ya gano dalilin Nenne,shiru yayi yana tunanin wasu irin mutane ne su, sai kuma ya nufi ɗakin da tsohuwar ta fito, yana tafiya a hankali.


A bakin ƙofar ya tsaya, yana kallon ɗakin,sai kuma ya ɗaga labulen a hankali ya ƙara sa ciki.


A can dungu ya same ta a raɓe, idanun ta sun kumbura sunyi suntum, har lokacin basu daina tsiyayar da hawaye ba,gaba ɗaya ta fita hayyacinta, kallonta yayi na kamar 5seconds, sai kuma ya ɗauke kansa duk da tausayinta da yaji har cikin ransa,


A hankali ya tako har gabanta ya tsuguna yana sake kallonta, sai kuma ya yayi gyaran murya, a hankali yace

"Noor"

Kin ɗagowa tayi, ya sake kiran sunan ta, nan ma bata ɗago ba bare yasa ran zata amsa,

Sai da ya sake kira a karo na uku,tukun ta ɗago jajayen idanunta ta zuba masa, wanda sai da yaji har zuciyarsa tayi rawa,
saboda yana iya hango tsananin ɗimuwa a idanunta.


Cikin rarrashi ya soma faɗin
"me yasa kike mata kuka?, kuka a gurin mamaci ba gata bane Noor!,babu abinda Nenne take buƙata a wajenki sama da addu'ar ki,ita kanta bazata so ta ganki a yanda kike ɗin nan ba.


Ai kamar ya zuga ta,ta sake fashewa da wani sabon kukan, amma ta kasa cewa komai, rasa yadda zaiyi yayi,kawai sai ya jawota jikinsa ya rungume,Yana bubbuga bayanta,dan yasan she really need a shoulder to cry on, mutuwar mahaifiya ba wasa ba, he can't even imagine rasa Maami, yasan sai ya fita shiga tashin hankali,


Sai da tayi kukan ta mai isarta, sannan ya ɗaga ta tsaye, hijab ɗin da ya gani ya sanya mata a saman ɗankwalin kanta,sannan ya kalleta a hankali yace

"Nenne tace in tafi dake, zaki bini" ya faɗa yana kallonta.


Ɗan dakatawa tayi da kukan tana kallonsa, ya girgiza mata kai.


Sai lokacin ta iya buɗe bakinta a hankali tace

"Nenne ce tace ka tafi dani?" a hankali ya gyaɗa mata kai.


Sunkuyar da kanta tayi, batace komai ba,
Shima bai jira ta e komai ɗin ba ya kama hannunta ya riƙe yace muje, yau zamu bar garinnan.

ba musu ta bishi har suka fito waje,yana riƙe da hannunta, gida ya wuce da ita,still bai sake hannunta ba,

kowa sai binsu yake da kallo, Taufeeƙ dake ƙofar gidan yayi saurin ƙarasowa inda yake yana tambayar sa abinda ya faru


"Taufeeƙ pack our things we are leaving right Now" ya faɗa yana jan hanunta ya shiga cikin gidan,

da sauri Taufeeƙ ya biyo bayansa yana faɗin,"ai kayanmu Are already packed bari in Kira faruƙ ya kawo mana mota", bai ce masa komai ba ya sake hannunta ya nufi ɗakinsa,


Taufeeƙ dai kallonta kawai yakeyi,to me hakan yake nufi?, ganin babu amsa yasa ya shiga ɗakinsa, jakunkunansu ya fito da su ya fitar waje.


dandazon mutanen da ya gani a wajen gidan ya sashi tsayawa kallonsu, ƙarasowa yayi yana faɗin "lafiya!?".

Wani dattijo yace rufa mana baki, ba gurinka muka zo ba.

Taufeeƙ ya buɗe baki da niyyar sake magana, amma sai yayi shiru, ganin Sir Zannur ya fito, hannunsa riƙe da na yarinyar,shima da mamaki yake bin mutanen da kallo,


Aikuwa fitowarsa ke da wuya,wajen ya ɗau hayaniya,kowa na faɗan albarkacin bakinsa,shidai har lokacin bai gane me yake faruwa ba,

da sauri Taufeeƙ ya ƙarasa wajensa yana faɗin

"Sir bansan me ya kawosu ba, na tambayesu sunce wajenka suka zo"


Juyawa yayi ya kalli mutanen yana sake haɗe ransa yace "ina sauraranku".

wani dattijo ne ya fara magana yana faɗin"asirin ka ne ya tonu, daga mutuwar uwar ƴar nan har ka ɗakkota ka kawo ta gidan ka,ko kayi zaton bama saka ido akan ƴaƴanmu ne".


Wani kallo yayi masa,sannan cikin takaici yace "saka ido akan yaranku?,shiyasa kuka barta ita kaɗai duk da ƙarantar shekarunta,abinda baku sani ba shine,a yanzun nan ba sai gobe ba, zan bar garinnan da ita, kuma babu wanda ya isa ya hanani tafiya da ita, saboda wannan wasiyyar mahaifiyar tace"



Da sauri Taufeeƙ ya kalleshi kamar yadda kowa ya zuba masa idanu yana kallonsa.


Wani tsohu yace"to a wani dalilin zaka tafi da ita,bayan babu abinda ka haɗa da ita,sannan ita ba muharramar ka bace, saboda haka ba inda zakaje da ita.



Wani yawu mai ɗaci ya haɗiye kafin yace "to idan ta zama muharrama ta kuma Fah!?"ya faɗa yana kallonsu duka


Duk shiru sukayi babu wanda ya masa.


Ya nisa yace, yanzunnan ba sai anjima ba, ina so in cika alƙawarin da na ɗauka ma mahaifiyar ta, ina so a ɗaura min aure da Noor"



Ba iya ƴan garin da Taufeeƙ ba, hatta Noor dake kuka sai da ta tsaya cak da kukan tana kallonsa,


Taufeeƙ ya ƙara so da sauri yana faɗin "Sir"


Bai bashi damar magana ba yace "that's my final decision".


Jiki a sanyaye wani tsoho yace to ai shikenan, sai mu ɗunguma muje gurin mai gari,idan dai har an ɗaura, kuma mun shaida, babu wanda zai hana ka tafiya da matar ka.



Hakan kuwa akayi,gabaɗaya suka nufi gidan mai gari, ba'a wani ɓata lokaci ba aka ɗaura auren _ABUBAKAR SHURAIM_ (Zannur)tare da _NA'IMA RAZAƘ ABDULKARIM_(Noor) akan sadaki Naira dubu hamsin lakadan ba ajalan ba.



Gaba ɗaya wajen aka shaida,ita dai Noor bin kowa take da Kallo,
meyake faruwa da rayuwar ta ne?,jiya mahaifiyarta ta rasu, yau an ɗaura mata aure, shin mafarki takeyi ko kuwa a zahiri komai yake faruwa?,


Miƙewa Zannur yayi,sannan ya miƙar da ita, yana riƙe da hannunta yace "mun barku lafiya"


Daga haka ya juya ya kalli Taufeeƙ wanda shima komai yazo masa a bazata, da sauri yabi bayansa,suka bar wajen,

tafiya kawai sukeyi babu mai cewa komai,yana riƙe da hannunta yana janta tana binsa Taufeeƙ kuma na biye da su da kayansu, ya goya jakan yana Jan trolley ɗin, har suka iso dai dai inda suka bar motarsu.


kasancewar Taufeeƙ ya riga ya kira faruƙ yasa basu jima a wajenba faruƙ ya iso da motar, bai kalli inda take ba ya juya ya shiga baya, Taufeeƙ kuma ya shiga gaba,tsayawa tayi tana kallonsu.

Ganin batada alamar shiga motar, yasa Taufeeƙ sauƙa a motar ya buɗe mata baya yana murmushi yace"Madam shall we?"


A hankali ta ƙara sa ta shiga Taufeeƙ ya rufe motar,ya koma gaba,faruƙ ya tada motar.
shi kansa yasan ba lafiya ba ganin yanayinsu gaba ki ɗaya,amma bayida hurumin tambaya yasa yaja bakinsa yayi shiru,

har suka fita a garin ba mai cewa komai sai ma faruƙ da ya gaishe da Sir Zannur, ganin bai amsa ba yasa bai sake cewa komai ba


Jinginar da kansa yayi da jikin kujera, yana tunanin abubuwan da suka faru,
itakam can dungu ta rakuɓe tana cigaba da kukan ta ƙasa ƙasa.




Maimoon🤓#
https://www.facebook.com/groups/1627491150723081/?ref=share



💖*ABNUR*💖

*By* *maimoon* 🤓

*Elegant* *online* *writers* 📚📖

*Free* *book*

*Page* *9*


Ƙarfe 12:40 suka shigo cikin Kaduna,har lokacin babu mai magana a cikin motan.

Ɗan juyawa yayi ya kalli sashen da take, sai yaga ashe ma bacci takeyi,yadda take sauƙe ajiyar zuciyar zakasan ba daɗin baccin takeji ba .


Ƙwafa yayi,yana juyar da kansa daga kallonta,ya maida kallonsa ga faruƙ da ke ƙoƙarin packing a packing space na hotel ɗin.


Sai da duk suka sauƙa,ganin bata fito ba ya sa ya ɗan ja tsaki,a ransa yana faɗin "tun yanzu!? .


Baibi ta kanta ba yayi wucewarsa ciki.

Taufeeƙ ma da sauri yabi bayan sa,sai da ya gama yin all the needful ya rakashi har ɗakinsa, sannan ya dawo motar da sauri,wanda dama basu rufe da key ɗin ba ganin tana bacci.


Buɗe ɗayan ɓangaren yayi,a hankali ya soma buga kujerar yana faɗin "Madam "

A hankali ta buɗe gajiyayyun idanunta tana sauƙe numfashi,sai kuma ta juya a sanyaye ta kalli Taufeeƙ dake mata murmushi.


Cikin girmamawa,yace "mun iso Ma,kuma Sir yace a ƙaraso da ke"

Kallonsa kawai takeyi,yana maganan kamar wacce batasan me yake cewa ba,
a hankali kuma wasu siraran hawaye suka sauƙo akan fuskarta,dan yanzu ta tuna ashe fa aure aka mata,sannan Nennenta ta rasu .



Sauƙa Taufeeƙ yayi ya ƙara sa ya buɗe mata sashin ta,a hankali tace

"nagode"



Bai ce mata komai ba,yayi mata jagora tana biye dashi,har ƙofar ɗakin Zannur,


sai da ya ɗan tsaya
yana tunani,dan bai san ya Zannur ɗin zaiyi reacting ba idan ya kai masa ita,shima da gangan yaƙi kama mata ɗaki,dan yafi so as soon as possible su koyi zama da juna.




A hankali yayi knocking a ƙofar ɗakin,sannan ya ɗan matsa ya tsaya yana jira a buɗe,dan dai ya san sau ɗaya ake masa knocking,Dan baya son hayaniya,



Har kamar baza'a buɗe ba sai kuma yaji an buɗe ƙofan, kallonsa yayi ganin ya koma ciki,yasa ya dubeta ya ce "muje".



Tana biye dashi a baya suka shiga ɗakin,yana zaune a kan gado,har yayi wanka ya canza kayansa zuwa three quarters da Riga na shan iska laptop ne a kan cinyarsa yana operating, ba tare da ya ɗago ba yace

"is anything wrong?


Da sauri Taufeeƙ yace

"Sir, dama,ummm...Madam ce....."

dakatawa yayi da danna keyboard ɗin ya ɗago manya manyan fararen idanunsa,aikuwa basu sauƙa akan kowa ba sai a kanta,tana rakuɓe daga bakin ƙofa kamar kace arrrr ta gudu.



Maida kallonsa yayi ga Taufeeƙ sannan ya ɗan haɗe rai yace

"what the hell is she doing here? me yasa baza ka Kaita room ɗin ta ba?me zata min anan?"ya sake tambaya.



Da sauri Taufeeƙ yace "Sorry Sir,but am so sorry to say,all the rooms were booked,shiyasa na kawota nan,but kayi haƙuri,i can vacate my room,in yaso sai ta zauna a ciki".

"Better"
ya faɗa yana cigaba da danna laptop ɗin, jiki a sanyaye Taufeeƙ ya juya,ita dai kallon sa kawai takeyi,gabaki ɗaya ya canza mata,kamar ba abokinta na ƙauye ba.



Har sunje ƙofa zasu fita,sai kuma ya ja tsaki,ya ajiye laptop ɗin sannan ya ce "Taufeeƙ" yadda zai ji shi,da sauri ya dawo yana faɗin
"Sir"
"Let her stay here" ya faɗa a taƙaice daga haka ya miƙe ya wuce toilet.


Murmushi Taufeeƙ yayi,a zuciyar sa yana faɗin "I will try my level best,to unite you both".



Koma wa yayi ya sake kiranta, dan har ta fita ita kam, har tsakiyar daƙin ta shigo ta tsaya,sannan Taufeeƙ ya juya zai fita,da sauri ita ma ta juya tana faɗin
"umm...tafiya zakayi ka barni a nan".
dan dai ita wallahi Zannur ɗin ya fara bata tsoro,dan lokacin da suke ƙauye sam ba haka yake mata ba.



Taufeeƙ bai tsaya ba,bare tasa ran zai amsa mata,ganin da gaske fita zaiyi ya sata juyawa da sauri zata bisa,dan gani take gaskiya yafi Zannur ɗin kirki nesa ba kusa ba



"Idan kika kuskura, kika sake ɗaga ƙafarki daga wajen, I will know how to deal with you"


Taji an faɗa daga bayanta, cak ta tsaya,sannan ta kasa juyowa, lokacin Taufeeƙ har ya fice a ɗakin ya ja musu ƙofa.



Bai sake cewa komai ba, shima yayi hanyar fita,hannunsa na ɗan ɗigan ruwa,sannan fuskarsa da leman ruwa,alama dai alwala yayi.



Ganin shiɗinma fita zaiyi ya sata saurin biyosa da sassarfa,dan dai baza'a barta a ɗakin nan ita kaɗai ba.



Jin alamun mutum a bayansa yasa ya tsaya da tafiyan da yakeyi ya juyo gabaki ɗayansa,fuskarsa a matuƙar ɗaure yake faɗin
"where do you think you are going? a tsawace ya sake maimaita"Nace ina zakije da kike biyoni"


Da sauri ta toshe kunnuwanta, dan babu abinda ta tsana a rayuwarta irin tsawa,jikinta har rawa yakeyi,

ganin yadda tayi ɗin sai ya tsaya kallonta kawai,bai sake cewa komai ba ya juya,ya fice a ɗakin itama bata sake gigin binsa ba, tana ji ya rufe ƙofar ta baya.



Sai lokacin ta samu daman ƙare ma ɗakin kallo,tana mamakin irin girmansa da ƙayatuwansa.


A hankali ta samu waje a ƙasa ta zauna,wasu hawayen na ture turen zubowa daga idanuwanta,


"Allah na gode maka,akan duk yadda ka so ka ga rayuwata, Allah ka jiƙan Nenne, Allah ka bani ikon cinye jarabawar da ka ɗauro min" abinda tayi ta maimaitawa kenan,tana jin zafin dake zuciyarta na raguwa.



Tana zaune a wajen har ya dawo daga masallaci,bata ma ji shigowar sa ba,saboda yanda tayi nisa a tunani,ƙarar rufe ƙofan ne ya dawo da ita daga duniyan tunanin, ta bisa da ido.


Ledan dake hannunsa ya ajiye a gabanta,sannan in a husky voice yace"kee,tashi kije kiyi wanka, ki cire waɗannan kayan na jikinki,kizo kiyi sallah".


"To" kawai tace ta miƙe, amma sai ta rasa me ma zatayi?,ina zata shiga?,juyawa tayi ta nufi inda taga ya shiga ɗazu,har ta kai ƙofa taji yace,
"kayan kuma fa" da sauri ta dawo ta ɗauka ta wuce toilet ɗin.


Da kyar ta samu ta iya gane yadda ake amfani da toilet, ɗin,sai da tayi wanka da soson da ta gani a toilet ɗin, sannan tayi alwala,ledan ta buɗe tana kallon kayan ciki,zaro su tayi,tana dubawa.


Nan ɗin ma da ƙyar ta samu ta saka shi dai dai,tanayi tana duba hoton matar da ke jikin ledan kayan.


Gashinta ta warware,sannan ta sake dunƙuleshi kamar yadda ta saba,sannan ya warware ɗankwalin kayan, ba laifi yana da girma,ɗaure gashin tayi dashi sannan da ɗau hijab ɗin da ta cire ta saka.


Tunda ta fito daga banɗakin yake kallonta ƙasa ƙasa,ganin ta maida hijab ɗin da ta cire,amma bai ce mata komai ba.


Can gefe ta ja ta tsaya tana kallon ɗakin from every direction,ganin bazata iya ganewa ba yasa ta aro jarumta tace
"umm dan Allah ina ne gabar,zanyi sallah"


Ganin bai kulata ba yasa ta juya ta kalli gefe kawai,zata tada sallah.


Miƙewa yayi ba tare da yace mata komai ba,sai da yazo dai dai da ita, sannan ya sa hannunsa a kafaɗunta ya juyar da ita,ta kalli gabar ɗin sannan ya miƙa mata sallaya.

Ƙuri tayi masa da ido tana kallon sa ,har ya koma ya cigaba da danna laptop ɗinsa tukun ta shinfiɗa sallayan ta soma sallah.



Tunda ta idar da sallahn tana zaune akan sallayan , Taufeeƙ yayi knocking ya tashi ya je ya buɗe ya karɓo abinci,a gabanta ya ajiye ya koma ya cigaba da abinda dake gabansa,da alama abin nada muhimmanci sosai.



Amma gaba ɗaya rabin tunaninsa naga yadda zai faɗa ma Maami abinda ya faru, how will she react, shikansa bai sani ba.


Har la'asar ya miƙe ya fice a ɗakin,ita ma sai da tayi sallan ganin bai dawo ba yasa ta ɗan jayo ledan abincin ta ɗan ci kaɗan,rufewa tayi ta ajiye a gefe sannan ta miƙe akan sallayan, nan da nan bacci yayi a awon gaba da ita.



Bubbuga gefen sallayar da taji anayi shi ya tada ita, a tsugunne ta ganshi gefenta,yana ganin ta buɗe idonta ya miƙe,yana faɗin "ki tashi kiyi sallah",

mutsuke idanunta ta shiga yi ta miƙe ta wuce toilet, sai da ta yi tsarki,sannan tayi alwala ta fito,karkaɗe sallayar tayi,ta sake shimfiɗawa sannan tayi sallah,duk abinda takeyi yana kallonta, sai da ta idar yace tashi
"kiyi isha",

kallonsa tayi sai kuma tace "anyi isha ne?",

"Ban sani ba" yace a taƙaice yana zaro wayarsa ya fara dannawa,

bata sake cewa komai ba ta miƙe ta yi isha sannan tayi shafa'i da wutiri, sai da tayi addu'a ta shafa sannan tayi kwanciyar ta akan sallayar,


Shima bai ce mata komai ba ya gyara kwanciyarsa a kan gadon,sannan ya kai hannu ya kashe wutar ɗakin yana shafa addu'ar bacci(asuba ta gari🥱).



Washegari da wuri suka ɗauki hanyan Abuja, duk da baiyi niyyan tafiya a mota ba amma ganin bata taɓa shiga jirgi ba ya sa yace su tafi a mota kawai,



Tunda suka iso garin Abuja take kalle kalle, yau gata a birnin da take buri kullum, amma ba tare da Nennen ta ba, a take taji wasu hawaye na shirin zubo mata,kallonta yayi ta gefe, a zuciyarsa yana faɗin
"wai Ni wannan yarinyar hawayenta anya bazai ƙareba kuwa".

girgiza kai kawai yayi ya juyar da kansa yana kallon window ɗin shima.



Tun kafin Taufeeƙ ya gama parking motar,bodyguards ɗin suka ƙara so da sauri, su ka tsaya, da sauri suka buɗe masa ƙofa, suna gaishe shi, a taƙaice ya amsa musu yayi shigewar sa ciki,



Ganin basu lura da ita ba yasa Taufeeƙ ƙarasawa ya buɗe mata ƙofan yana murmushi dan yadda yaganta duk a tsorace.



Ƙafafuwan ta zuro a hankali,waɗanda suke cikin flat shoes Wanda ya kawo mata tare da kayan jikinta,a hankali ta ƙarasa fitowa tana kallon ƙatoton mansion ɗin da aka kawota, a hankali take bin bayan Taufeeƙ ɗin har cikin main parlour na gidan,inda bodyguards suka riga suka shigo musu da kayayyakin su.




Da gudu Asabe da Amina suka fito a kitchen ɗin suna rige rigen ƙarasowa wajen Taufeeƙ,kallonsu yayi yana murmushi yace

" kukuma Fah "

da sauri Amina tace

" Sir Taufeeƙ yanaga kun dawo da wuri, Ni wallahi ban ma san ran dawowan ku nan da wata uku Bama wallahi"

ta faɗa tana kallon Noor ta ke tsaye kawai tana kallonsu"

"Sai kuma kika ganmu koh"
Taufeeƙ ya faɗa yana hawa da kayan Sir Zannur steps ɗin.

sai da ya kai ya dawo ya ɗau sauran sannan ya kalli Asabe da Amina yace

"ga baƙuwa,ku gyara mata ɗaki a sama, anan zata zauna and ku kula da ita sosai fah, idan ba haka ba ku da Sir Ni dai babu ruwana"

ya faɗa da sigar tsokana yana haurawa saman,

Har rige rigen ƙarasowa wajenta sukeyi, Asabe tace "sannunki da zuwa baƙuwar Sir" ta faɗa tana murmushi.

*💖ABNUR💖*

*By* *maimoon* 🤓

*Elegant* *online* *writers* 📚📖

*Free* *book*

*Page* *10*


Ita dai kallon su kawai takeyi,ba tare da tace uffan ba,
kallon juna suka yi sannan suka maida kallonsu gareta, Amina tace "Ni sunana Amina,wannan kuma......"



"Asabe". Asabe ta faɗa tana tarar numfashin Amina.

Murmushi kawai tayi musu ba tace komai ba.


Taufeeƙ da ke sauƙowa ya kallesu yace

"wai kun san waye ce ita kuwa kuka ajiyeta a tsaye, nace ku kaita ɗakin sama, baku Kaita ba kun tsaya kuna cika ta da surutu koh"

ya faɗa yana ƙarasa sauƙowa



"Sir Taufeeƙ dan Allah a ina kuka samu wannan kyakkyawar yarinyar son kowa ƙin wanda ya rasa,wallahi har ta shiga raina"

cewar Amina tana murmushi.



"Matar Sir Zannur ce"


ya faɗa a taƙaice yana nufan ƙofan falon dan dai baya son tambayoyi,
dan ya riga ya san halin su Asabe.

a ranshi yana ayyana irin zaman da za'a yi a cikin gidan tsakanin Sir da kuma Madam ɗin sa.


"Matar Sir ce", maganar daya doki ƙwaƙwalwar Yasira kenan wacce ke fitowa daga kitchen,dan yiwa su Amina magana suje su cigaba da aikinsu,

kasa ƙarasowa falon tayi daga bakin kitchen ɗin ta ƙura ma Noor idanu, wacce ke tsaye duk tsayuwar ma ta isheta.


Bata gama tantance
abinda kunnuwanta suka jiyo mata ba taji Muryar su Asabe dake ta murna kamar waɗanda aka ma bushara da aikin hajji



Asabe na faɗin "Sannu da zuwa Madam, wai da gaske ke matar Sir ce,ya ilahi,ina zansa kaina"

ta faɗa tana sake
kwashewa da dariya kamar taɓaɓɓiya,


Duk yadda take jin zuciyarta sai da ta ɗan murmusa ba tare da ta shirya Ba.

Amina tace"mun shiga uku, matar gida muka bari a tsaye, Asabe bazaki nuna mata ɗakin ba" ta faɗa cikin rashin sanin abinyi itama murnar ta kasa barinta.


A hankali tace"Sunana Noor, kuma ina so in yi sallah, a ina zanyi"

ta faɗa tana murmushi


Da sauri Dukansu suka fara rige rigen yi mata jagora zuwa ɗakinta,

tsaf ɗakin yake, hakan yasa suka barta tayi sallah,suka

Please Login or Register in order to submit comment