Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

deserve that, Amma bai san meyasa sam batun aure baya cikin ajenda ɗin rayuwarsa.


Fita yayi daga ɗakin, ya ja masa ƙofa ya fito waje, tafiya kawai yakeyi yana kallon garin mai cike da ni'imomi iri-iri,sai yamma ya dawo,a shirye ya gansa tsaf da alama fita zaiyi yace


"Sir zakaga garin ne" "eh" kawai yace ya sa kai ya fice, shima ya bisa a baya, sai da suka zaga garin sosai, sai da sukayi sallar isha, sannan suka dawo gida,a gaskiya garin yayi masa ba kaɗan ba,yasan zai samu abinda yakeso a nan.


Daga gidan mai gari aka kawo musu lafiyayyen abinci,har da su kaza, Taufeeƙ ne kaɗai yaci, shi kam kwanciya kawai yayi, daga haka bacci ya ɗauke shi



Ita kam Noor tunda ta koma gida,tundaga tsakar gida take ƙwala kiran "Nenne,Nenne,burina ya cika,rayuwarmu ta kusa canzawa Nenne,ganin Nenne bata fito ba ya sata ƙarasawa ɗakin,da sauri Nenne dake kwance tana fitar da numfashi da ƙyar, ta juya mata baya,dan bataso ta fahimci halin datake ciki,amma inaa ta makara,


Da sauri ta ƙara so ta tsuguna tana kallon Nenne,hankali tashe ta soma faɗin "Nenne baki da lafiya ne, me ya sameki Nenne na", cikin ƙarfin hali Nenne ta riƙe hannunta sannan ta shafa kanta tana faɗin,ki kwantar da hankalinki,babu komai fah kawai zazzaɓi ne yake damuna tun safe,kuma naji sauƙi sosai",Noor ta sauƙe ajiyar zuciya,tana faɗin Alhamdulillah, ai nazata ciwonki ya tashi",


Gyara zama tayi ta riƙe hannuwan Nenne duka biyu tana faɗin "Nenne na samu scholarship,gwamnati zata ɗau nauyin karatuna a cikin gari",

Nenne ta faɗaɗa
murmushinta tana faɗin "masha Allah, Allah yayi miki albarka Noor,ya haɗaki da alkhairi ko bayan raina", Noor bata wani kula da batun Nenne ba ta miƙe tana faɗin,
"Gobe ranar bikin shekara,dole ma na je na binciko abinda zan ci ado gobe dashi", ta faɗa tana miƙewa tabar ɗakin,


Ai kuwa ranar batayi bacci da wuri ba,sai kai komo take tsakanin dakinta,da ɗakin Nenne, sai wajen ƙarfe sha biyu tukun tasamu bacci ya ɗauke ta a ɗakin Nenne,

kallonta kawai Nenne takeyi yadda take baccinta,a nutse,tana fata da addu'ar Allah ya bawa ƴar ta kyakkyawar rayuwa,mai ƴanci ba irin nasu ba,shafa kanta tayi,sannan ta mata addu'ar bacci ta shafa mata,itama ta lumshe ido,take bacci ya ɗauke ta.



Washegari tun safe ta shirya acikin uniform ɗin ta na boko,sai lokacin waɗannan mutanen jiyan suka faɗo mata,to me ya kawosu ƙauyen su,more especially ɗayan ma,yayi mata kwarjini da yawa,ko me zasu je yi a gidan mai gari,
da wannan tunane tunanen ta gama shirinta tsaf ta yi ma Nenne sallama, ta fice a gidan,dan dai yau batayi latti ba,



Tun safe Sir Zannur yake zaga garin, Taufeeƙ dai binsa kawai yakeyi,idan yaga abinda ya birgesa sai ya ɗauka a hoto,mutanen ƙauyen sai kallonsa sukeyi,
wasu samari yaga sun zuba masa ido,ganin irin kallon da suke masa ya sa shi ƙara sa wa inda suke yace
"sannunku"
, da sauri ɗaya yace sannu bawan Allah,kafinma ya sake magana duk suka taso suka zo kusa dashi,suna masa sannu,

murmushi yayi yace "in ɗauke ku hoto!? Ya tambaya yana ƙoƙarin sakewa da su,da sauri suka ce "eh" ai kuwa suka hau jeruwa, ya ɗauke su yana nuna musu,
ai kuwa sai yaga mutane sunata ƙaruwa, wai suma a ɗauke su.

abin har ya bashi dariya, harda tsofaffi gyarawa yayi yana ta ɗaukansu a hoto,yana ɗan yin baya,don ya samu capturing abinda yake so,


buge mutum ɗin dayayi garin komawa bayanne ya sashi saurin juyowa yaga waya buge, bai sani ba, ita kam da har ta kai ƙasa, kasa ɗagowa tayi,

a hankali ya ƙarasa wajenta ya miƙa mata hannu,ɗaga kai tayi ta kalleshi,tabi hannunsa da yake miƙa mata da kallo,

miƙewa tayi ba tare da ta kama hannun nasa ba, tana karkaɗe jikinta,
A hankali yace "meyasa kina tafiya bakya kallon gaban ki"


Da batayi niyyan kulasaba, amma jin abinda yace ya saka juyowa ta kallesa da kyau sannan ta maimaita abinda ya faɗa sai kuma tace"malam sai kuma aka ce maka, kai ka dinga tafiya da baya da baya akan layin da ba siya kayi ba ko"



Kallonta ya tsaya yi,sai yanzu ma ya gane ta da sauri Taufeeƙ ya ƙaraso,yana kallonsu,


Bata sake cewa komai ba, kawai ta juya tayi wucewarta,baki sake suka bita da kallo, kafin yayi ƙwafa yana juyawa ya bar wajen,


Tun da aka tashi school ta dawo gida take shirin bikin shekara da ƙyar ta samu ta gama shirya wa, duk da bata yi kwalliya irin na yan ƙauye ba, sai dai ɗigon kwalli da ta yi guda uku a ƙasan haɓarta,sai fararen lumsassun idanunta da ta sanya wa kwalli,

ta fito rass da ita,sai da ta shiga tayi ma Nenne sallama, sannan ta fita a gidan ta nufi wajen bikin shekara wanda ake yinsa duk shekara a ƙauyen,duk wani al'adu nasu za'a yi a wajen.



Tana isa wajen ta tarar har an fara, can nesa ta samu ta tsaya tana kalle kalle,


Tun shigowar ta wajen ya lura da ita, ya tsaya da ɗaukan hoton da yakeyi yana kallonta,shi kansa bai san dalilin da yasa yake kallonta ba,samun kansa yayi da ɗaukan ta hoto ba tare da ta sani ba,
yayi mata yakai kala uku, kafin ta juyo, karaf idanunta ya shiga nashi,kallonsa tayi taga yana ɗaukan ta hoto ai kuwa ta wani murguɗa baki ya ɗauka a haka,

sai da ya kalli cikin
camera ɗin sai ya samu kansa da yin murmushi kawai,bai sake kallonta ba ya cigaba da ɗaukan abinda ake yi,



A ƙarshe aka kira ƴanmata,aikuwa ita da ƙawayenta suka shiga,waƙa aka saka musu na mutan ƙauye,suka hau yin rawar a nutse, a hankali, baya ya koma yana kallonsu, yadda suke rawar a tare suna juyawa, ba ƙaramin burgesa abin yayi ba, hoto ya shiga ɗaukan su,wanda duk nata ya fi yawa a ciki,



Ba a tashi taron ba har kusan magrib, duk aka fara watsewa, Taufeeƙ ya ƙara so inda yake a tsaye ya jingina da wata bishiya, yana kallon hotunan, a kan nata ya tsaya yana kallo, yanda ta murguɗa baki da taga yana ɗaukan ta murmushi yasake yi, a zuciyarsa yana faɗin"she is just Soo naive".


Taufeeƙ yace "Sir Are we leaving now,Yakamata ka huta fah,". Ɗagowa yayi yakallesa yana jin nishaɗi wanda ya daɗe baiji irinsa ba,ko dan bai taɓa ganin al'adu namu na ƙasar Hausa bane,shi kansa bai sani ba,


Batare da ya kalle shi ba yace "kaje zan dawo anjima, ina son na yi wani abu first".


Taufeeƙ ya buɗe baki zai yi magana ya ɗaga masa hannu kawai, bai sake cewa komai ba ya juya ya bar wajen.



Tsayawa yayi yana tunanin to me ya hanashi komawa gida,what is he waiting for,shi kansa bai sani ba,
kamar ance ya ɗaga kansa ya hangeta tana nufo inda yake,ita kaɗaice sai ɗan ƙaramin sanda,da ta riƙe a hannunta tana wasa da shi,

tsayawa tayi tana magana da su lantana, sai dariya takeyi, Camera ya ɗauka ya cigaba da ɗaukan ta hoto, yadda take dariyan ya sa ya kasa ɗauke idanunsa a kanta,

kamar ance ta juyo kuwa taga, yana ɗaukan ta, a fusace ta taho inda yake, tana kallonsa ta fara faɗin,


"malam wai lafiya", sai da ya kalleta kamar bazai yi magana ba sai kuma ya gyara tsayuwa yace, "me kika gani,na Sanki ne da zaki tambayeni lafiya".


Da mamaki take kallonsa sai kuma tace "baka Sanni ba, Ni ma ai ba saninka nayi ba, to meyasa kake ɗaukana hoto?,


Wani kallo yayi mata sannan yace"sai kuma wa ya ce miki ke nake ɗauka?, saboda ke kaɗai ce, sai ke zan ɗauka?,ga kyawawan ƴanmata nan in rasa wa zan ɗauka sai ke".


Sake baki tayi tana kallonsa sai kuma ta juya a fusace zata bar wajen ba tare da ta ce masa komai ba,
riƙe hannunta taji anyi, da sauri ta juyo tana kallonsa da mamaki, da sauri ya sake hannun nata yana kallonta da idanunsa da suke sakata jin ta kasa nutsuwa,



A hankali cikin lallaɓi yace, "ƙanwata me yake haɗa mu ne kam naga tunda nazo garinnan muke samun matsala da ke", jin a yadda yayi maganan ya sata faɗin"to waya sanine,"

murmushi yayi sai kuma yace to shikenan tunda baki sani ba, can we be friends? Da sauri ta kallesa sannan ta ce ƙasa ƙasa"Ni bana abota da maza"



Kallonta ya ƙarayi,shi dariya ma take basa wallahi, sai kuma yace "kinga Ni baƙo ne a garinnan, ko a garinku bakwa son baƙi ne?


Girgiza kai kawai tayi, yace yauwa ƙawata, to yanzu miye sunan ƙawar tawa a hankali ta ce "Noor"


"Ni kuma Zannur" ya faɗa yana kallonta,murmushi kawai tayi,sai kuma yace to,yanzu kinga tunda mun zama friends shikenan nima sai ki nuna min garinku koh!?, Gobe insha Allahu zan jira ki sai ki zaga dani in ga garinku, ko bazaki nuna min ba? Ya tambaya yana kallonta,

"Zan nuna maka " tafaɗa tana kallonsa, kawai mamaki takeyi daman ashe yana da sauƙin kai?,ai ita gani takeyi, yadda yake da kyau ɗinnan bazai ma kulata ba,



A hankali tace "sai da safe dare nayi zan tafi gida,

"To ƙawata sai goben zan jira ki anan"

Bata sake cewa komai ba ta juya ta wuce abinta,tsayawa yayi yana kallonta, shi mamakin kansa ma yakeji, sai kuma yayi murmushi, yana shafa kansa ya juya ya bar wajen,

a zuciyarsa yana tunanin maybe it's because the girl is too naive and tana da innocent face,bai taɓa tafiya da yayi masa daɗi irin wannan ba,yaje ƙasashe da yawa Amma the happiness daya samu a nan is something else,

ɗakin Taufeeƙ ya buɗe yaga har yayi bacci, kawai ya ja masa ƙofan ya koma nasa ɗakin


sai da wanka, yayi Sallah, sannan ya shirya acikin kayan bacci masu matuƙar taushi, ya kwanta bai daɗe ba bacci yayi awon gaba dashi.



Itama hakan ce ta ɓangaren ta tunani tayi tayi dama haka ƴan birni suke da sauƙin kai, ko dai wannan ɗinne ya fita daban,sake shigewa jikin Nenne dake bacci tayi, itama bacci yayi awon gaba da ita.




What will happen next is the unthinkable,ƙaddara a ko da yaushe dama akace ta riga fata🤗🤓



*💖 ABNUR 💖*


*By* *maimoon* 🤓


*Elegant* *online* *writers* 📚📖


*Free* *book*
*Page* *7*



Washe gari,haka kawai take jinta cikin farin ciki,wanda har Nenne sai da ta fahimci hakan,amma da ta tambayeta,sai tace babu komai,bata sake ce mata komai ba,ita dai fatanta irin wannan farincikin ya dauwama akan fuskarta.

Har taje makaranta ta dawo,murmushi bai gushe a fuskarta ba.

Wanka tayi, ta ɗauko riga da zanin ta sanya,tayi ɗigon da ta saba,guda uku a ƙasan haɓarta,sannan ta ɗauko ɗan kwali ta ɗaure tulin gashinta,da bai samu wani isasshen gyara ba.

fitowa tayi daga ɗakinta,ta shiga na Nenne,ta sameta, tana ninke kaya,wanda ƙarfin hali kawai takeyi, saboda bata so ta ɗaga ma Noor hankali, idan taci gaba da kwanciya.



"Nenne zanje gidansu lantana",sai da ta kalleta da kyau,sannan tace"kar ki kai dare, ki gaishe min da baabarta,



"Toh insha Allahu"ta faɗa tana barin gidan,a inda ya ce ta sameshi nan ta nufa, bataga kowa a wajen ba, ta lelleƙa bata ga ko wa ba,kawai taja tsaki tana diddire ƙafafunta.



Juyawa tayi,tana ƙoƙarin barin wajen,a ranta tana faɗin, "dama can,ba zuwa zai yi ba, kawai dai ya raina mata wayo ne,itama ina ita ina abota da wannan balaraben,

har tana jin ɗaɗi zai faɗa mata yadda birni yake kafin ta tafi karatun da gwamnati ta ɗauke ta"



Kamar daga sama taga mutum a gabanta,har ta ɗan tsorata, ta ɗanyi baya,tana dafe ƙirjinta,tana kallonsa.


"Kai ƙawata haka kike da tsoro daman?" ya faɗa yana kallonta yana murmushi.


Kallonsa tai tayi daga sama,har ƙasa, shigar da yayi ba ƙaramar kyau yayi masa ba.


Hure mata ido yayi, yana kallonta yace"kee wannan kallon fah,ko munina kike son ganine!?,ya faɗa yana ɗan dariya.


Ai sai ya sake shagaltar da ita, ashe ma kyau ɗin sai yayi dariya ma,
can kuma tayi ƙwafa tana kallonsa, tace
"Ku a garinku malami ne yake zuwa ya jira ɗalibi dama? Ta faɗa tana wani ɓata rai,



Kallonta yayi sannan yace toh"ashe Fah ke Malama tunda ke zaki nuna min gari, to afwan Malama,wannan ɗalibin bazai sake latti ba,ya faɗa yana kama kunnensa.


Dariya tayi,sannan tace "shikenan an yafe maka na yau".


Godiya yayi sannan yace "shall we"


Suka jera suna tafiya suna hira.


Taufeeƙ dake tsaye,yana kallonsu, mamaki ya kusa kasheshi a tsaye,
Sir Zannur Ne ya sake haka da mace,macen ma ƴar ƙauye,tabbass akwai wani al'amari,amma yana fatan ko miye ne yazo da alkhairi,sannan yabi bayansu yana murmushi,



Sun yawata sosai, tana nuna masa abubuwa na birgewa a garin, ko ina suka bi kallonsu ake ana mamakin, a ina Noor tasan wannan Balarabe mai ɗaukan hoton,




Wani dutse ya samu ya zauna,yana faɗin"kee bakya gajiya da tafiya ne,gaskiya bazan iya cigaba ba" ya faɗa a shagwaɓe.


Dariya ta dinga yi, tana nuna shi
"to miye hakan kaman ba wani namiji ba, Ni da nake ƙarama ma kuma mace ban gaji ba sai kai".
shagala yayi da kallonta kawai, ganin yana kallonta ya sa ta tsagaita tana faɗin,

"to shikenan, in ya so gobe sai in ƙara sa nuna maka koh!? Ta tambaya tana kallonsa,


kai ya gyaɗa mata, ita ma gefe ta samu ta zauna, tana kallonsa, sai kuma tace "nima ai na kusa komawa birni"


"Haba" ya faɗa yana kallonta,"Allah da gaske gwamnati ta ɗauki Nauyin karatuna a cikin gari"


Murmushi yayi yace "congratulations ƙawata".


Taufeeƙ ya ƙaraso wajen da suke, da Camera a wuyanshi shima, yana kallon Zannur,gaishesa yayi, ya amsa yana miƙewa tsaye,


"To ƙawata we shall talk tomorrow Koh?"
Ya faɗa yana kallon ta,


Ita ma miƙewa tayi tana faɗin,
"Allah ya kaimu",

sai lokacin ta gaishe da Taufeeƙ,ya amsa yana murmushi,sannan ya juya ga Zannur yace"Sir shall we?"



Bai ce komai ba ya juya ya soma tafiya, shikuma ya bishi a baya.


Itama gida ta wuce,kai tsaye,tana shiga gidan, ta samu Nenne a durƙushe a tsakar gidan, da sauri ta ƙarasa,tana faɗin


"Nenne me ya sameki,

Nenne bata iya cewa komai ba,sai girgiza kanta kawai takeyi,kuka ta soma yi, tana kiran sunan Nenne, sai kuma ta miƙe da sauri ta ɗebo ruwa tazo tana bata,
da sauri Nenne ta karɓa tana sha da alama tana buƙatar ruwan, wanke mata fuska tayi, sannan ta taimaka mata suka shiga ɗaki,



kuka ta ringayi tana kallon Nenne, Nenne dama baki da lafiya har haka shine kike ɓoyemin,
tafaɗa cikin kuka sosai,girgiza mata kai kawai Nenne tayi.


miƙewa tayi, da sauri Nenne ta riƙe hannuwan ta tana kallonta,"ki zauna da Ni Noor", "Nenne Ina nan tare dake,zan je in Nemo mai magani ne kar ki damu Nenne na".


Duk yadda ta so taje, sam Nenne hanata tayi, haka ta haƙura,amma sam bacci ya ƙaurace mata, a zaune ta kwana riƙe da hannun Nenne da ta samu bacci da ƙyar,

sallah kaɗai ta tashi tayi,ta dawo ta zauna.

har aka kira sallah,ta miƙe ta ɗauro alwala, sai da tayi nafila tayi raka'a tanul fajr sannan ta gabatar da sallar asuba kamar yadda Nenne ta koyar da ita, tun tana ƙarama.


Addu'a tai tayi , kan Allah ya bawa Nennen ta lafiya,sannan ta shafa ta miƙe.


Ganin har lokacin Nenne bata farka ba,sai bata tashe ta ba, ta fita tsakar gida, ta gyara ko ina ta share tsakar gidan tsaf,sannan ta share ɗakinta, ta hura wuta ta ɗaura musu ɗumame, sannan ta koma ɗakin.



a zaune ta samu Nenne akan sallaya, fuskarka looking so pale,a kusa da ita ta zauna, ta gaishe ta,Nenne ta amsa da ƙarfin Hali tana murmushi,tace yau bazaki je makarantar bane,sai da ta kalli Nenne, idanunta na cikowa da hawaye tukun tace



"Nenne ta yaya zan iya zuwa makaranta, bayan halin da naga kina ciki jiya, Nenne jiya naji tsoro...",sai kuma ta kasa ƙarasawa, ta fashe da kuka.


shafa kanta kawai Nenne tayi tace Noor Kar kiji tsoron mutuwa, mutuwa dolece, kawai ina fatan ki zama mai juriya akan duk abinda ya sameki.



Noor ta katseta tana faɗin"Nenne mubar taɗin mutuwar nan,Nenne tace shikenan mun daina Noor"


Ranar dai wuni tayi a gida, tana maƙale da Nenne, a zuciyarta tana tunani ko balaraben can yaje yayi ta jiranta,amma dai a yanzu batada abin da ya wuce kula da Nenne a wajenta.



Kamar kuwa yanda tayi hasashe,tun ƙarfe 2 yake tsaye,tun yana tunanin zata zo, har ya fara cire rai, Taufeeƙ dai kallonsa kawai yakeyi.



can da ya gaji da tsayuwar ya juya ya kalli Taufeeƙ,kamar zaiyi magana, sai kuma ya fasa,
can kuma sai ya sake ɗagowa, yace

"Taufeeƙ" da sauri Taufeeƙ yace
"Sir"
"Is this girl really going to come?

Taufeeƙ yayi murmushi yace "ko zan bincika maka gidansu ne Sir"

Ɗan shiru yayi sai kuma yace "uhmm... ok I think it will be better, we should check on her"

Taufeeƙ ya ɗan gyara tsayuwar sa yace "Sir amma zan iya tambayanka please if u won't bother"
ɗaga kai yayi ya kalleshi sai yace
"go ahead"

Taufeeƙ ya sosa kansa yace "Sir dama tambayan is too personal zan iya yi?

Ya sake tambaya, Zannur daya zuba masa ido yana kallonsa yace "go ahead"

"Sir do you have any feelings for the girl.....?"


Wani kallo da ya masa yasa sauran magana ya maƙale ya kasa ƙarasawa, da sauri yace
"Sorry sir"


Sai da yayi ƙwafa alamar ransa ya ɓaci sosai kafin yace
"how can You even think of that, dan kawai yarinya tana nuna min garinsu sai kace ko ina da feelings akanta.
I think ko da wani ya ce maka zanso mace irin wannan, kai ne mutum na farko da zaka ƙaryata"
da sauri Taufeeƙ ya sake faɗin
"sorry Sir"
bai sake ce masa komai ba but ga dukkan alamu ransa ya ɓaci sosai.


Taufeeƙ yace "Sir bari na binciko gidannasu"

Da sauri ya ɗagamasa hannu "No need, barta kawai, idan har kai zaka yi wannan tunanin,bansan kuma sauran mutane me suke tunani ba" daga haka ya juya ya bar wajen".


Taufeeƙ ya bisa a baya,jikinsa duk yayi sanyi.

sai da sukayi sallar isha sannan suka koma gida, but duk hankalinsa na kan me ya hanata zuwa


Juyawa yayi ya kalli Taufeeƙ sai kuma yace "ummm...mr, can You look for the girl's house yanzu,Yakamata mu duba ko bata da lafiya ne?"


da sauri yace "sure" sannan ya miƙe ya fice, shikuma Camera ɗin sa ya ɗauka yana kallon hotunan da yayi mata sanda tazo nemansa bata gansa ba.


Taufeeƙ bai wani sha wahala ba ya gano gidan ya dawo ya sanar dashi miƙewa kawai yayi yace "muje"


Taufeeƙ ya bisa a baya amma ya kasa daina kokon to a ransa, but yanzu ya yarda ba sonta yake ba maybe kawai, tausayinta yakeji,ganin bayi da amsa kuma bayi da hurumin tambaya ya sashi kawar da tunanin daga ƙwaƙwalwarsa.



A ƙofar gidan ya tsaya,yana tunanin ta yadda zasu yi magana da ita, gashi har kusan 9 o'clock duk da garin har yanzu akwai sauran mutane,but babu yara da zai iya tura wa ciki



Juyawa yayi ya kalli Taufeeƙ sai yace "jirani ina zuwa",daga haka ya kutsa kansa tsakar gidan,tsayawa yayi yana ƙare ma tsakar gidan kallo dake ɗauke da ɗakuna biyu kacal.



Fitowa tayi daga ɗakin Nenne da kwanon da suka ci abinci,duk da da ƙyar Nenne taci kaɗan, idanunta duk sun kumbura saboda kukan da tai tayi,
"wayyo Allah na!" ta faɗa tana ƙoƙarin komawa ɗakin da sauri ya riƙe hannunta yana faɗin "ke nine,babu wanda zan aiko ne shiya sa na shigo, abokinki ne".


Tsayawa tayi da zille zillen da takeyi tana kallonsa, sai kuma tace

"mai ya kawoka gidanmu"



Tsura mata ido yayi yana kallonta,yadda idonta ya kumbura,duk da babu wadataccen haske,amma hasken farin wata na bashi daman ganinta ,
"me ya sameki,baki zo ba,nayi ta jiranki"

Kuka ta fashe da shi tana faɗin "Nenne ne batada lafiya"


"Ok stop crying, zata samu lafiya, me ya sameta"

Nima ban saniba,tunjiya take wani irin numfashi,ɗazu har aman jini tayi"

"Subhanallahi"muje na ganta

Da sauri tace "ah ah.... " Bai saurari me zatace ba ya nufi ɗakin da ya ga ta fito,da sauri tabi bayansa.



Akwance suka samu Nenne sai numfashi take yi da ƙyar,da sauri ya ƙara sa wajenta ya durƙusa kusa da ita yana faɗin

"sannu mama"


Kallonshi tayi a wahale,sai kuma ta juya ta kalli Noor,da sauri ta ƙaraso wajen kafin ma Nenne tace komai ta fara faɗin,

"Nenne baƙo ne daga birni ya zo,shine yace in nuna masa gari, to shine yanzu da yaji baki da lafiya,yazo ya gaishe ki".


Kallonsa Nenne tayi,sai kuma ta ƙura masa ido,kallon shi takeyi kamar wanda takeso ta gano wani abu,sai kuma tace

"nagode"

"Allah ya ƙara lafiya," ameen tace a hankali
Yana ƙoƙarin miƙewa yaji ta riƙe hannunsa sai kuma tace "Noor ɗan bamu guri"
Cike da mamaki, Noor tace "Nenne.."

Kallonta yayi yace "kije mana" kamar bazata fita ba sai kuma ta juya a sanyaye ta bar ɗakin, kwanon da ta yar a tsakar gida ta ɗauka ta kai kitchen, ta fito ta zauna tayi shiru,tana tunanin wani magana Nenne zatayi da shi.


Yakai minti fiye da 20 sannan ya fito a ɗakin,idanunshi sun kaɗa sunyi jajir.

Da sauri ta tashi ta ƙara so inda yake bai tsayaba,sannan bai kalli inda take ba, yayi hanyar fita a gidan,tsayawa kawai tayi tana kallonsa, to me Nenne ta ce masa.

Har ya kai ƙofa,sai kuma ya dakata yace "gobe ku shirya zamuje asibiti a cikin gari", daga haka ya fice.



Tsayawa tayi tana bin hanyar da ya bi da kallo, ganin tsayuwar bazata fishsheta ba ya sa ta koma ɗakin,a kwance ta samu Nenne, idanunta a lumshe ta zauna a gefenta tana kallonta.



Tunda ya koma gida,hankalinsa ya kasa kwanciya, miƙewa yayi ya nufi ɗakin Taufeeƙ,ya samu har yayi bacci, tashinsa yayi,da sauri ya miƙe yana mutsuka idanu ahankali yace

"Sir is everything ok"


A hankali yace
"we will be leaving tomorrow, so ka shirya"


da mamaki yake kallonsa amma bai basa daman magana ba ya fice a ɗakin.



Cikin dare jikin Nenne ya tsananta, gashi ta ƙi bari Noor tayi Nesa da ita,ƙarfe 3 daidai na asuba Nenne ta cika, da kalmar shahada a bakinta, tana riƙe da hannun Noor.


Tashin hankali da ba'a sa masa rana.





Mafarin ƙaddara🤗
Maimoon#



💖*ABNUR*💖

*By* *maimoon* 🤓

*Elegant* *online* *writers* 📚📖

*Free* *book*

*Page* *8*


Innalillahi wa inna ilaihi raji'un,tashin hankali wanda ba'a saka mata rana.

Sam Noor Bata fahimci cewa Nenne rai yayi halinsa ba, ganin jikinta ya saki,sannan ta daina motsi,sai ta matso kusa da ita, tana faɗin


"Nenne kinji sauƙi ne!?,Nenne kiyi haƙuri da sassafe zamu tafi asibiti,wannan da ya zo ya gaishe ki,yace zamu je asibiti,insha Allahu zaki samu lafiya.


Jin Nenne bata amsa ba,sannan bata motsa ba,yasa hankalinta sake tashi,kukan ta ya ƙaru,

da sauri ta kama hannuwan Nenne duka biyu ta riƙe ƙam,tana kuka kamar ranta zai bar gangar jikinta,girgizata ta shiga yi tana cigaba da kiran "Nenne na ki tashi,Nenne ki taimaka min,ki tashi,idan baki tashi ba nima mutuwa zanyi.


Wani tunani da yazo ranta, ya sa tayi sauran miƙewa ta fice a ɗakin da sauri.


Ruwa ta ɗebo ta dawo da sauri tana shafawa Nenne,a tunaninta ko dogon suma tayi,but har lokacin Nenne bata motsa ba.



Wani kukan ta sake fashe wa dashi da sauri ta miƙe,fice a gidan,har lokacin kuka take.



Gidan Malam Habu,wanda yake maƙwabtansu ta shiga bugawa, duk da dare yayi amma ko tsoro bata ji, dan kusan asuba ne ma a lokacin.



Ta ɗan jima tana bugawa, babu ƙaƙƙautawa, kafin Malam Habu,ya buɗe ƴar langa langa kofar yana faɗin "waye ne da talatainin daren nan"

Cikin kuka sosai tace "Baba Noor ce".


"Ha'a Noor lafiya da darennan me ya faru kike kuka"


"Nenne, ce bata da lafiya, kuma ta ma suma,bata ko motsi, dan Allah ka taimaka min.


Da sauri Malam Habu yace "subhanallahi muje muga abinda zamu iya yi".


komawa ciki yayi da sauri ya taso matarsa Jummai, suka fito tare.



A tsakar gida ta tsaya ta kasa ƙarasawa ɗakin,tana jin malam habu da matarsa suna ta salati,
kasa gasgata abinda zuciyar ta ke sanar da ita tayi, a hankali tayi baya ta jingina da bango, tana maimata ma kanta

"Nenne bata mutuba, batada lafiya kuma zata ji sauƙi".


Jummai ta fito a ɗakin idon ta cike da hawaye,
gurin Noor ta ƙara sa ta dafa ta tana faɗin"Allah ya baki haƙurin rashi Noor, Nenne rai yayi halinsa,Allah da ya fiki sonta ya karɓi abinsa"



Ai bata ƙarasa jin abinda take sanar da ita ba ta yanke jiki ta faɗi a wajen sumammiya.




Ƙarfe 7:00 na safe ya fito cikin shirinsa, Taufeeƙ na biye da shi a baya,
bayan ya fitar musu da duk wani abu nasu trolley yake ja,yayinda shi kuma Taufeeƙ yake ɗauke da jaka na matafiya da kuma jakan kayan cameras ɗin su,


A hankali yake tafiyar amma duk zuciyarsa a cunkushe,

"do

Please Login or Register in order to submit comment