Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Please Papi, Ina so in kai ƴata da kaina gidanta."

"Ok babu damuwa, zan kira su a waya tunda sun bada Number ɗin da za'a yi contacting ɗinsu, in yaso zuwa Next week sai mu tafi."

"Allah ya kaimu"

Daga haka ya miƙe ya fice a ɗakin

Waya Ammi ta ɗauka ta kira wata balarabiyar ƙawarta, kayan gyaran jiki irin na amaren larabawa take só ta haɗa mata, and tana so ta turo mata zuwa gobe please it's urgent.

Sai da ta tabbatar mata babu damuwa, kafin ta kashe wayan, ta sake kiran wata ƙawarta wacce suka haɗu a Nigeria, watannanin da suka wuce, matar shuwa Arab ce, itama dai kayan gyaran jikin ta tambayeta, aikuwa matar tace mata zuwa gobe da safe ɗan ta zai kawo mata, a taƙaice dai Ammi sai da ta kira mutum kusan uku.

Washegari kuwa kaya suka iso, na Dubai ne kaɗai sai zuwa yamma.

Noor da bata san abinda ake ciki ba, washegari sai gani tayi Ammi ta saka ta a gaba da gyara, daga a mata wannan sai a mata wancan, daga a bata wannan sai a bata wancan, da ta tambaya sai Ammi tace, so take ƴarta tafi ta kowa kyau, ita kuwa Noor ta yarda ta zage tana karɓan duk abinda aka bata.


Zuwa kwana uku, Noor ta koma wata sabuwar halitta, wani irin glow da skin ɗinta keyi kaɗai har abin mamaki ne.

Ita kanta har tsayawa take tana kallon kanta, Farhaana kam tasa ta take a gaba, tayi ta kallo sai dai kawai tayi murmushi.


Papi sunyi magana da Abbu, dan har ya sanar ma Maami, amma ko da wasa, basu sanar da Zannur ba, dan so suke suyi masa abinda ake kira suprise.

Da yamma Zannur na sauƙowa daga sama, dan yau yana so ya ɗan fita, kasancewar ya kwana biyu baya fita ko ina.

Maami da Abbu dake magana sukayi saurin yin shiru, suka zuba masa ido suna kallonsa, Maami na sake gode ma Allah a ranta, wai wannan kyakkyawan cikakken namijin ɗan ta ne.

yana sanye da riga da wando na Louis Vuitton, Dan dai shi baya anfani da kowane kanfani idan ba wannan ba, sai dai gabaɗaya ya gama yin sanyi.

Ƙarasowa yayi falon yana kallonsu, sai kuma ya samu waje ya zauna yana faɗin

"Maami, Abbu me kuke cewa ne?, naga kunyi shiru da na zo, Ku cigaba da maganan mana, ina so inji"

Ya faɗa yana kallonsu

"Ehm dama batun komawa mukeyi, mun yanke shawara zamu tafi tare da kai
Ko ba haka ba Abbu?", ta faɗa tana ƙiftawa Abbu ido.

Murmushi kawai Abbu yayi ba tare da yace komai ba.

Cikin rashin damuwa da maganar yace

"Maami i don't wanna leave, ku tafi kawai ku barni."

Shiru Maami tayi Jin yadda yayi maganan, he sound very worried, sai taji kamar tace masa jibi iwar haka Noor tana tare da shi.

Cikin sanyi itama tace

"meyasa?, saboda Noor ne bazaka bi mu ba?"
Ta tambaya tana kallon fuskarsa

Kallonta yayi sai kuma yayi ƙwafa yana faɗin

"not at all since ita ta zaɓi ta barni, ba yanda zanyi da ita, I guess zan haƙura kawai, i won't force her into anything she don't wan't to, I will move on with my life, bana buƙatar in cigaba da tauye rayuwata a kanta, zan yi iya ƙoƙarina inga na saba da rashin ta."

Daga haka ya miƙe ya bar falon gabaɗaya.

Da ido duk suka bisa, Maami kam baki sake take kallonsa, kafin ta juya ta kalli Abbu, gyaɗa mata kai yayi tare da faɗin

"kar ki damu idan ya ganta komai zai dai-daita."

"Allah yasa" ta faɗa cikin sarewa.



Mutanen Kaduna sun gama shirin tafiya, wanda sam Noor bata san inda zasuje ba, dan ko da wasa babu wanda ya faɗa mata komai.

Tun a Airport take jin wani irin tsinkewar zuciya, a hankali ta kama hannun Papi ta riƙe tana maimaita duk addu'ar ta tazo bakinta.

Tunda aka kira passengers ɗin Abuja ta sake jin ƙirjinta ya buga, juyawa tayi ta kalli su Farhaana da Ammi da har sun wuceta.

Jan hanunta da akayi ya sata dawowa cikin hayyacinta, tana kallon Papi

"Daughter what are you thinking?, muje Mana" ya faɗa yana murmushi

"Papi zuciyata ce ke tsinkewa" ta faɗa idonta na ciko wa da hawaye

""Common not now Noor!, kiyi addu'a babu komai sai alkhairi, kinji?"

"To" tace, kafin Papi yaja hannunta suma suka bi bayan su Ammi.

Har jirginsu ya tashi, ta kasa samun nutsuwa.

In less than 30 minutes jirginsu ya sauƙa a Abuja, waya Papi yayi da Abba, akan sun iso, wanda dama tuni driver na jiransu a Airport ɗin.

Tunda suka ɗauko hanya daga Airport Noor ke zare ido, ganin in da suka nufa yasa Noor fashewa da kuka, janyota Ammi tayi tana faɗin

"miye hakan Noor?",
Kasa cewa komai tayi, sai shesheƙa da takeyi.

A hankali ta ɗago kanta, tana ƙare ma compound ɗin parking space ɗin kallo, tabbass su Papi gidan Zannur suka dawo da ita.

Body guards Ne suka ƙaraso tareda buɗe musu ƙofan motan, gaba ɗaya zama tayi kamar doluwa, tana bin kowa da kallo, a hankali ta zuro ƙafafunta ƙasa, tana jin wani iska na kaɗa ta, ta ko ina a jikinta.

Cikin nutsuwa ta sauƙo tana kallo su Papi da su Farhaana da har sun yi gaba abinsu.

Riga da wando ne a jikinta na *PRADA,* sai kimono da ta sanya a zamansu kalar maroon, veil ɗin kanta shima kalar maroon ne, sai karamar jakar dake rataye a kafaɗanta, gashin ta ya kwanta lub lub har gaban goshinta, da gefen fuskarta, fuskarta looks natural, Dan babu komai a fuskar, lips ɗinta sun yi pink shar suna shining kamar ta saka lip gloss, Wanda sam babu abinda ta saka, haka suke naturally, ƙafafunta sanye cikin flat shoes na *GUCCI* .

Papi jin baiji alamar ta ba, ya sa shi juyowa, sai kuma yayi murmushi yana dawowa inda take, siririn hannunta dake sanye da agogo na *CHANEL* ya janyo yana faɗin

"Ya kika tsaya anan daughter?, mu ƙarasa Mana."

Binsa kawai takeyi kamar wata sokuwa.

A ƙofar main parlour suka ci karo da Abbu da Maami, ai kuwa Maami na ganinta, da sauri ta ƙaraso ta rungumeta tana faɗin

"Noor, marhaban Noor, you are welcome back", ta faɗa wasu hawaye na cika a idanunta.

Abbu ne yayi ma su Papi iso zuwa babban falon.


Zannur dake Zaune yana danna wayarsa, gaba ɗaya ya gagara nutsuwa, danna wayar kawai yakeyi, shi kansa bai san me yakeyi a wayan ba.

Jin hayaniyar shigowar mutane, ya sashi miƙewa da niyyar haurawa sama, dan sam baya don hayaniya, kuma Maami batace masa zatayi baƙi ba, da bazai ma zauna a falon ba.

Cak ya tsaya da haurawa steps ɗin da yakeyi, jin ihun su Asabe dake faɗin

"Oyoyo Noor, oyoyo Noor"

In slow motion yashiga juyowa, har ya juyo gabaki ɗayansa sa, yana sauƙe idanunsa akan Noor, wacce ke tsaye jikin Maami,

Cikin idanunta, idanunsa suka shige, kasancewar itama shi take kallo..............





Maimoon#



*💖ABNUR*💖

*By maimoon*

*Elegant online writers* 📚📖

*Free book*

*Page 23*


Kallon kallo suka shiga yi ma juna, babu ko ƙiftawa, kallonta kawai yake yi, kamar ya samu tv, yama rasa me za iyi.

Juyar da kansa yayi, kafin yayi wani Murmushi yana shafa kansa,

da sauri ya shiga sauƙowa daga steps ɗin, bai damu da Papi, Abbu, Maami, Ammi, da kowa dake falon ba.

Wani irin kyakkyawar
runguma ya bata, da har sai da Dukansu suka sauƙe ajiyar zuciya, gaba ki ɗaya ya manta da wani fushi da yake da ita, ita kanta ta manta wai tana jin haushinsa, dan dama ita kanta tasan ƙarya take ma kanta, amma tasan tana matsanancin son Zannur, kuma tayi kewansa fiye da misali.


Ɗaga ta yayi yana juyi da ita a tsakar falon, gabaki ɗaya ya rasa ma me zai mata ya tabbatar mata da irin farincikin da yake ciki.

Dariya ta shiga yi, tana wuntsula ƙafafunta, shima kansa dariyar kawai yakeyi, yana jin kamar kar wannan moment ɗin ya taɓa wucewa har abada.

Direta yayi a hankali, yana faɗin

"Noor, Ina kika je?, inata nemanki, meyasa Kika yanke min the worst hukunci da za'a taɓa yankewa wani ɗan Adam?, Noor me yasa baki jira na gane gaskiya ba?, wallahi yanzu na gane komai, I will never misunderstand you ever again, please ki yafe min"

Ya faɗa yana kamo dukkanin hannuwanta.

Kowa a ɗakin kallonsu kawai yakeyi kamar suna cinema, Abbu da ya buɗe baki da niyyan magana da sauri Maami ta girgiza masa kai tana murmushi,
Shima murmushin yayi kawai, suka tsaya ganin ikon Allah
Shi kansa Papi murmushi yakeyi haka Ammi da su Amina.

Shiru Noor tayi ba tace komai ba, sai hawaye daya ciko idanunta,

"Noor!"

Ya Kira sunanta,

Kawar da kai tayi taƙi kallonsa.

Da sauri ya juyo da fuskarta,

"Don't do that Noor it hurts, Please kimin magana, what do you want me to do, me kike so inyi miki, so kike inyi kneeling in baki haƙuri"

Ƙin magana tayi amma a zuciyar ta dariya take yi tana faɗin "bazan kulaka yanzu ba ko me zakace."

Ɗurkushewa yayi akan gwuiwowinsa, yana faɗin
"Noor please ki yafemin I won't repeat my mistake."

Da mamaki take kallonsa, bata taɓa tunanin zai iya hakan ba, da sauri itama ta ɗurkushe a ƙasan tana faɗin

"Miye haka kake yi?"

hannuwansa ta lalubo duka ta riƙe tana kallon cikin idanunsa

"Na yafe maka, na jima da yafe maka, kuma har abada baka min komai ba, nima ka yafe min Please"

Tana kaiwa nan ta fashe da kuka, rungumeta yayi tsam tsam a jikinsa, ya lumshe idanunsa, yana jin wani relieve na sauƙa masa tun daga kansa har ƙafafunsa.

"Awnnnnn🤗"
Amina da Asabe suka faɗa a tare suna ƙyalƙyalewa da dariya.

Sai lokacin yayi saurin sakinta, Dukansu suka miƙe tsaye, Noor kaman zata mutu dan kunya, shikam shafa kansa kawai yayi, kafin yayi magana Maami ta riga sa tana faɗin

"To idan kun gama, sai kabar ta tazo ta zauna, daga tafiya take, ai ka barta ta zauna ta huta ko?"

Murmushi yayi kawai bai ce komai ba, saima ƙarasowa falon yayi ganin baƙin fuska, wanda ɗaya yayi matuƙar kama da Noor ɗinsa

Maami ma kama hannun Noor tayi, suka ƙarasa cikin falon, itakam sai sunkuyar da kanta takeyi.

Yasira dake tsaye a gefe, idanunta sun kaɗa sunyi jajir, ta share hawayen idanunta tana jin ƙuna a zuciyarta.

Taufeeƙ ne ya shigo falon, ganin mutanen da ke ciki ya sashi faɗin

"sorry I will come back later."

Da sauri Abbu yace

"ah ah Taufeeƙ a ƙaraso Noor ne ta dawo tare da mahaifinta."

Sai lokacin ya lura da Noor, Itama ido ta zuba masa, ganin ya warke rass kamar ba shi ba, sai kuma ta sunkuyar da kanta ƙasa.

Da sauri ya ƙaraso cikin falon da fara'a sosai akan fuskarsa

"Alhamdulillah, mun godema Allah da ya dawo da Madam Noor cikin ƙoshin lafiya, congratulations Sir ya faɗa yana dariya."


Zannur dai kasa amsawa yayi, sai murmushi da yake yi kawai, wanda ya daɗe rabonsa da fuskarsu gabaki ɗaya.

Asabe da Amina ne suka ƙaraso da sauri suna faɗin,

"Our Madam, Sannu da dawowa, wallahi bakiji yadda gidan ya zama ba da bakya nan"

Murmushi tayi musu, dan dai kamar an sace Mata kalaman bakinta ta kasa furta komai.

Kowa ka kalli fuskarsa cikin farinciki yake a falon, banda Yasira da ta rakuɓe can gefe tana tsiyayar da hawaye.

Juyawa tayi zata bar falon, da sauri ta dakata jin Muryar Taufeeƙ da tayi yana faɗin

"Yasira bazaki ma Madam Barka da dawowa gidanta ba, her rightful place, gurin da babu wani mahaluki da yake da iko sai ita kaɗai."

Turus tayi, sai kuma ta share hawayen da ya zubo mata, ta juyo a hankali.

Gani tayi gabaki ɗaya mutanen falon idanunsu na kanta, jiki a saluɓe ta ƙaraso cikin falon.

A gaban su ta tsaya kafin cikin ƙarfin hali tace

"Sannu da dawowa Madam"

Ta faɗa tana ƙoƙarin danne shahararren kukan dake zuwa mata.

Ko kallonta Noor batayi ba, bare ta sa ran zata amsa mata, hakan yasa Papi faɗin

"Daughter sannu da zuwa take miki"

"Na ji ta, Papi"

"To meyasa baki amsa ba?" ya tambaya yana kallonta da kulawa

Turo baki tayi tana shirin magana suka ji ance

"Saboda bata cancanci Zama a gidannan ba, talkless of amsa gaisuwarta"

Duk juyawa sukayi suna kallon Taufeeƙ

Cikin tsananin takaici ya soma faɗin

"Sir ka tambayeni several times, wanene yayi yunƙurin kasheni to ba kowa bace face ƙanwata Yasira."


Duk miƙewa suka yi tsaye, har shi kanshi Zannur ɗin.

"What Are You saying Taufeeƙ?, me yasa Yasira zata yi yunƙurin kasheka, bayan bata da kowa a duniya da ya wuce kai."

Zannur ya faɗa with disbelief yana kallon Taufeeƙ

Murmushi Taufeeƙ yayi kafin yace

"tabbass Yasira ita ce tayi yunƙurin kashe ni kuma ba komai ya sata aikata hakan ba face soyayya, soyayyarma naka Sir Zannur."

Gaba ɗaya ɗakin salati suka sanya, da Sallallami.

Taufeeƙ ya cigaba,

"saboda nayi yunƙurin hanata, hakan yasa ta gwammace in bar duniyan, har asibiti ta bini dan ta ƙarasa ni, Amma Allah bai bata iko ba"

Ya ƙarashe zancen yana jin wasu hawaye Masu ɗumi.

Cikin kuka sosai Yasira ta nufi Sir Zannur, akan gwuiwowinta ta zube tana kama ƙafafunsa

"Dan girman Allah Sir ka tausayamin, wallahi na aikata duka hakane saboda tsananin son da zuciyata ke maka, bazan iya rayuwa idan babu kai ba, wallahi kaine rayuwata" ta ƙarashe da wani irin kuka har shiɗewa takeyi.

Noor da idanunta suka gama rufewa, sai yanzu ta fahimci komai, tabbas tayi wauta da ta tafi ta bar Zannur, wato wannan duk sharrin Yasira ne,

Ƙarasowa tayi, ta sa hannu ta ɗago Yasira sai ji kake tassss ka wanke ta da mari, kafin ta farfaɗo ta sake wanke ta da wani marin,
Marinta ta rinƙa yi har sai da Zannur ya riƙe ta, nan take fuskar Yasira tayi fulu fulu yatsun Noor ne akwance a fuskarta ta ko ina.

"Allah ya isa tsakani na da ke, kuma wallahi sai dai ki mutu, amma mijina yafi ƙarfin ki"

Ta faɗa tana ƙoƙarin kwacewa daga riƙon da Zannur ya mata gabaki ɗaya idanunta sun gama rufewa.

Asabe da Amina al'ajabi ya kashe su a tsaye.

Papi ne yayi gyaran murya kafin yace

"kowa ya samu waje ya zauna."

Duk zama sukayi, sai Yasira dake tsugunne tana cigaba da kuka

Papi yace

"to bansan me zance akan wannan al'amari ba, abu dai ya riga ya faru, saboda haka dan Allah kukai zuciya nesa,
Ke kuma Yasira kike ko waye?, kije, duniya ta isheki riga da wando, bazan bari su miki Allah ya isa ba saboda ko a yanzu zuciyarki baƙace ina ga kuma kina ɗauke da Allah ya isan jama'a."


Abbu dake jin zafin abinda Yasira tayi shima ya ɗaura da faɗin

"Yasira i didn't expect that from you, ɗan uwanki, Taufeeƙ ya ma fi uba a wajenki, babu abinda ya nuna miki sai tsantsar soyayya, amma abinda kika saka masa da shi kenan, saboda haka na baki 20 minutes ki tattaro duk abinda yake naki a gidan nan ki fice ki bamu guri, kinci Sa'a bamu haɗa ki da yan sanda ba saboda kinci darajar Taufeeƙ amma ina mai tabbatar miki idan har kika wuce wannan lokacin, nan ne zakisan cewa bawai tsoronki mukeji ba zamu iya yanke hukunci akanki."

Kuka ta sake rushewa da shi, kafin ta rarrafa ta je wajen Maami

"Maami ki taimakeni, bani da wajen zuwa please ki roke su?"

Juyawa Maami tayi ta dubi Abbu kafin tace

"Abbu idan har na buɗe idona, naga yarinyar nan a gabana, wallahi duk abinda na aikata mata kar kowa ya sake ya min magana."

Yasira na jin haka ta miƙe da sauri ta nufi su Asabe tana faɗin

"please ku taimaka min"

Matsawa Amina tayi da sauri, tana jawo Asabe

"Ke Asabe matsa a kusa da wajen kar ta shafa miki zuciyar kafirai"

Asabe kam kallonta takeyi cikin ido kafin tace

"Wallahi Yasira, ba tun yau nasan cewa zuciyar ki baƙa bace, amma ban taɓa tunanin ya kai haka ba, Yasira Taufeeƙ Fah, Yasira ko kin manta waye Taufeeƙ a wajenki ne?, sannan kuma ki rasa wa zaki so sai Sir, ki ruguza masa rayuwarsa da matar da yake so, wallahi Yasira ko a hanya bana fatan na sake haɗuwa da ke."


Da gudu Yasira ta nufi ɗakinsu jin Abbu na ƙirga lokaci, ko abu ɗaya bata dauka ba, taji Abbu na faɗin

'ku shiga ku fito min da ita, idan taƙi fitowa ku ɗauko ta aka ku yasar min da ita a wajen gidannan."

Bodyguards ne har guda huɗu suka shigo, ganin da gaske suke yasa ba tareda ta musu gardama ba, ta biyosu suka fito, da kallo tabi Zannur, wanda ke rarrashin Noor da banda kuka babu abinda takeyi, har suka fice a falon, sai raba ido takeyi ganin bataga yayanta ba.


Sai da suka rakata har bakin gate,kafin suka rufe ƙofan, suka yi shigewarsu, a gurin ta ɗurkushe tana wani irin kuka.

Handkerchief ɗin da taga an miƙo mata ya sata ɗaga kai ta kallesa
Da sauri ta miƙe tana faɗin

"yaya!"

Ba tareda ya kalleta ba yace

"tashi ki shiga Mota muje."

Miƙewa tayi ta shiga motan, shima Taufeeƙ ya zagaya ya shiga ya tada motar ya bar unguwan.

Kuka kawai takeyi da ƙyar ta buɗe baki tana faɗin

"Yaya dan Allah ka yafemin, Ni kaina bansan meyasa na aikata hakan ba, wallahi soyayya ce ta rufe min ido dan Allah yayana ka yafe min."


Ta ƙarasa da kuka

Bai ce komai ba, sai da ya yanki kwana kafin yace

"Yasira Ni ɗan uwanki ne, ko me kika aikata a duniya bazan so inga kin tagayyara ba, amma Ni kaina bazan iya zama da ke ba, saboda ke guba ce a cikin mutane, saboda haka yanzu zan saka ki a mota, ki koma ƙauye wajen Baba, Allah ya sadamu da alkhairinsa."

A daidai lokacin yayi parking a bakin tasha, fita yayi, itama ta sauƙo tana jin wani irin kuka na taso mata kamar zata haɗiye ranta.

Babu yadda ta iya, haka Taufeeƙ ya sata a mota, sannan ya bata dubu ashirin ta riƙe a hanunta, daga haka bai sake kallon ta ba ya juya ya bar wajen.

Tana kallonsa har ya tada motarsa ya fice a tashan gabaki ɗaya kafin ta sake rushewa da wani matsanancin kukan.





Maimoon#


*💖ABNUR*💖

*By Maimoon*

*Elegant online writers* 📚📖

*Page 24*


Kwanan su Papi uku, suka tattara suka koma Kaduna, cike da kewar Noor, bayan Papi ya zaunar da su gabaɗaya ya musu nasiha sosai.

Duk da yadda Abbu da Maami, suke kula da Noor, amma sai da tayi kewar Ammi da Papi, da su Farhaana, daƙyar suka rabu a Airport, tana kuka kaman zata shiɗe.

Rungumeta Zannur yayi, yana aikin rarrashi, amma sam Noor taƙi yin shiru, har suka shiga Mota Noor kuka take, ya rasa yanda zai yi da ita tayi shiru, ya yi rarrashin, yayi daɗin bakin amma duk a banza.

Har suka iso Noor taƙi yin shiru, yana yin parking tayi saurin ficewa daga motan, da gudu ta ƙarasa cikin gidan ta haura sama tare da shigewa ɗakinta har da murza key.

Murmushi yayi kawai, tare da shafa sumarsa, a ransa yana faɗin

"Zakiyi bayani yarinya."

Bai bi takanta ba yayi wucewarsa ɗakinsa, shiryawa yayi ya fice a gidan tare da Taufeeƙ.

Sai da ta gaji dan kanta tayi shiru, har bacci ya ɗauke ta.
Ƙarfe 12 dai-dai ta farka, a hankali ta miƙe daga kan gadon, tare da yin miƙa.

"Hmm" Zannur ya faɗa yana gyara zaman laptop ɗin dake kan cinyarsa.

Miƙewa tayi daga kan gadon, ta wuce toilet, Yana kallonta har ta fito, ta gama shiryawa cikin riga da wando band ta saka a kanta, kafin ta ɗauki hijab ɗinta ta zura, sai da tayi sallah, tayi addu'o'inta kafin ta miƙe ta naɗe sallayan, ta zame hijab ɗin ta naɗe ta ajiye.
Gadon ta sake haurawa, ta ja bargo tayi kwanciyarta.

Murmushi yayi, a zuciyarsa yana faɗin
"kin gaji da kukan kenan?"
A hankali ya rufe laptop ɗin, kafin ya ɗau wayarsa ya kira kitchen.

Asabe yasa ta kai mata abinci kafin ya kashe wayarsa.

Har yamma kafin ya dawo, a falo ya sami Maami, da Abbu, wanda suma zuwa jibi suke shirin komawa Dubai.
Kasancewar Maami ta gama zaga danginta, dama abinda ya jinkirta tafiyan nasu kenan.

Zama yayi a falon yana ɗan hira sama sama da su Maami, amma gabaki ɗaya hankalinsa na ga Noor.

Daga ƙarshe miƙewa yayi kawai ya nufi sama.
Ƙofan ta da yaji a kulle ya sa shi yin murmushin da bai shirya ba,
kenan fushi takeyi da shi.

Juyawa yayi ya nufi ɗakinsa, laptop ɗinsa ya bude yana kallonta, ganin tana cin abinci da aka kai mata ya sashi shafa kansa, a fili ya furta

"Silly girl."

Bai sake ganinta ba, sai ranan da su Maami zasu tafi, kasancewar tare zasu kaisu Airport ya sa ta shiryawa cikin abaya kalar ja da fari, da yayi mata matuƙar kyau.

Har suka isa Airport, taƙi kallonsa, ita a dole fushi take dashi, ai yana ganin tana kuka amma ya shareta.

Shidai satan kallonta kawai yakeyi ta mirror, idan suka haɗa ido sai dai yayi murmushi, ita kuma ta galla masa harara.

Nan ma dai bata fasa kukan ba, ganin su Maami zasu tafi, dan ta saba da Maami sosai.

Kallonta kawai yakeyi, a ransa yana tunanin ina zata kai saurin kukanta.

Sai da jirginsu Maami ya ɗaga kafin suka bar Airport ɗin, amma sam Noor taƙi kulasa.

Shima bai kulata ba har suka iso gida, buɗe motar tayi a fusace ganin ya ƙi tankanta ta bugo murfin da ƙarfi, ta nufi cikin gida.

Girgiza kansa kawai yayi, shima ya fito daga motan, sannan yayi mata key ya nufi cikin gidan.

Har dare babu wanda ya kula wani, Noor kam ta cika tayi fam.

*********

Ƙarfe 12:00pm Zannur ya rufe laptop ɗin, kasancewar ya gama aikin da yakeyi.

Miƙewa yayi ya nufi ɗakin Noor, jinsa a rufe ya sashi komawa ya ɗauko spare key, a ransa yana addu'ar Allah yasa ta cire makullin jiki.

Cikin Sa'a kuwa Kofar ta buɗe, wani ajiyar zuciya ya sauƙe, kafin ya ƙarasa cikin ɗakin a hankali, ya maida ƙofar ya rufe.

Kallonta ya tsaya yi, yadda ta duƙunƙune a bargo, ta ɓata fuska, sai kawai yayi murmushi tare da ƙarasawa, botiran rigan baccin sa ya buɗe gabaki ɗaya, kafin a hankali ya haura kan gadon, tare da jawota gaba ɗaya jikinsa.

Wani ajiyar zuciya suka sauƙe a tare, cikin bacci Noor ta jita a jikin mutum, hakan yasa ta sake gyara kwanciyar ta a kan bare chest ɗinsa, tana turo baki.

Hannunsa yasa ya zare band ɗin kanta, gashin ta ya barbaje, kafin ya sa hanunsa a cikin sumar, yana shafawa, a hankali.

Buɗe idanunta dake cike da bacci ta shigayi, kafin ta miƙe da sauri, fahimtar da tayi ba mafarki takeyi ba, a jikin mutum take da gaske.

Da sauri ya maida ita ya matse a jikinsa yana hura mata, iska a fuska.

Ɓata fuska tayi, tana faɗin

"Miye hakan ka shigo min ɗaki?, ta ina ma tukunna ka shigo bayan na rufe ƙofar?"
Murmushi yayi a hankali ya raɗa mata
"Dama baki san cewa mijinnaki aljani bane, ɓullo wa kawai nayi"

"Hmm" kawai tace tana sake yunƙurin tashi daga jikinsa.

Ƙin saketa yayi, a hankali yace

"Baby, meye na?" ya faɗa yana marairaicewa

Dukansa ta shiga yi a ƙirjinsa, kafin ta fashe da kuka,

"Ni bansani ba, baka damu da Ni ba, ka mayar da ni wajen Papi, baka so na!"

Da sauri ya birkito da ita, ya koma Samanta, yana kallon cikin ƙwayar idanunta.

"Don't ever say that again, wallahi ina sonki kaɗai yayi kaɗan, akan abinda nake ji tattare dani akanki, ina sonki, irin son da babu wani namiji da kema matar sa irinsa,
Ina sonki fiye da duk yanda wani mai kwatance zai kwatanta, i never knew you were the reason I live, sai da kika barni Noor."

Ajiyar zuciya kawai Noor take sauƙe wa, tana kallonsa, yadda yake confessing soyayyarsa a gareta, da sauri ta sa yatsanta a bakinsa tana faɗin

" Shhhh, Its enough, ya isa haka, na yarda mijina, nasan kana sona, ko da ace baka furta komai ba."

Ta faɗa hawaye na sauƙa a gefen idanunta. Sai da ta yi shiru kafin ta cigaba

"Wallahi nima ina sonka, fiye da yadda zaka iya misaltawa, bansan sanda na fara sonka ba, amma abinda na sani a yanzu shine, bazan iya rayuwa ba tare da kai ba..."

Kasa ƙarasawa tayi jin bakinsa a cikin nata, wani hot kisses ya ke bata, da ƙwaƙwalwarta ta gagara ɗauka, jikin sa har rawa yakeyi, gabaɗaya ya gigata mata lissafi."

Sun shafe tsawon lokaci a haka, kafin a hankali,ya mirgina ya koma gefe yana sauƙe numfashi, idanunsa sun kaɗa sunyi jajir, batare da ya ce mata komai ba ya sauƙa a kan gadon, zagayowa yayi, a hankali ya riƙe hannuta yana kallon ta,

"Zo muje"

Zuciyar

Please Login or Register in order to submit comment