Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta ce ta tsinke da sauri cikin in Ina tace
"Ina..za..mu je..?
Bai bata amsa ba, ya sunkuyo tare da ɗaga ta cak,
Nutsuwa ta samu kanta da yi a kan faffaɗar ƙirjinsa, a hankali ya juya da ita, ya bar ɗakin.

Har suka shiga nasa ɗakin bata daina jin bugun zuciya ba, a hankali ya sauƙe ta a tsakiyar daƙin yana kallonta kafin ya juya ya nufi toilet.

Gefen gado ta samu ta zauna, tana ƙare ma ɗakin nasa kallo, ba ƙaramin kyau ɗakin yayi mata ba,kasancewar bata taɓa shiga ba, mayen turarensa na *_SHUMUKH_* ya gama kama ɗakin.

Fitowa yayi daga toilet ɗin, yana daure da towel da alama, wanka yayi, a hankali ya dubeta kafin yace, ki shiga nan kiyi wanka, ki haɗo da alwala.

Da sauri ta girgiza masa kai tana faɗin,
Ah ah, zanje inyi a ɗakina.

Bai kulata ba ya ƙarasa jikin Kofar ya rufe da key, sannan ya zare key ɗin ya ƙarasa jikin mirror, yana gyara sumar kansa.

Babu yadda ta iya haka ta ƙarasa toilet ɗin.
Mamaki ta tsaya yi, yadda toilet ɗin sa yake abin sha'awa, kamar ba bayi ba.

A haka ta ƙarasa, sai da ta zare kayan jikinta, tayi wanka, sannan ta ɗauro alwala, bathrub ta sanya a jikinta, kalar skyblue kafin ta fito a hankali, tana leƙawa cikin ɗakin.

A zaune ta gansa a bakin gado yana operating system ɗinsa.
A hankali ta fito, cikin sanɗa, har ta iso tsakiyar daƙin, kafin ya ɗaga kansa yana kallonta.
Tura baki tayi, cikin shagwaɓa ta ce

"to Ni ai babu kayan da zan saka a ɗakinnan"

Shafa kansa yayi kafin ya juya ya fice a ɗakin, can sai gashi ya dawo, da kayan bacci, har da hijab.
Miƙa mata yayi, ta karɓa, sai da ta gama shiryawa tsab, kafin ya gabatar musu da sallah raka'a biyu.

Addu'o'i yayi musu sosai, kafin a hankali ya zare hijab ɗin jikinta, linkewa yayi da kansa ya ajiye yana mata murmushi.
A hankali ta miƙe, dan bacci take ji, ta nufi gadon, kwanciya tayi tare da shigewa bargonsa mai tsananin laushi.

Sai da ya gama abinda yake yi duka, kafin ya hauro gadon shima, a hankali ya janyota jikinsa, tareda yi Mata raɗa a kunne.

Zaro ido tayi waje tana kallonsa, ta buɗe baki da niyyar magana, bai bata daman maganan ba ya haɗe bakinsu waje ɗaya yana jin wani shaukin sonta na ɗibarsa.

Tun Noor na ganin kamar wasa, har abin ya fara wuce tunani da lissafinta, sai lokacin kuka ya zo mata, ta shiga magiya amma ina, Zannur ya riga yayi nisa, ya sha alwashin mayar da ita cikakkiyar mace, sannan Mrs Zannur Shuraim.

Ba ƙaramin wahala Noor ta sha ba a wannan daren, har sai da kukan ma ya daina fita.
sai bayan komai ya lafa kafin ya janyota jikinsa wasu hawaye Masu ɗumi na bin fuskarsa, albarka kam ta shasu kwando kwando. Ita kam Noor banda kuka babu abinda takeyi, sai sake birkita masa lissafi takeyi.

A ranar ya tabbatar yana ma Noor son so, irin sonda baya tunanin wani ya taɓa hasashensa.



***_10 years Later_*

Mrs Zannur Shuraim ce a zaune, a babban falon da ya ji komai na rayuwa, a hankali ta miƙe tare da yaron da ke kan Cinyarta wanda bazai wuce shekara ɗaya da watanni ba.

Daƙin yara ta kaisa, tare da kwantar da shi a kan gadonsa, tana lallaɓa shi, dan ta tabbata idan har ya farka, rikici zai saka mata, a hankali ta zare hannunta, tare da fita daga ɗakin.

Ƙasa ta sauƙo, ganin babu kowa a falon ya sata ƙarasa wa ɗakin hoto dan ta tabbatar duk suna can.

Daga bakin ƙofa ta tsaya tana kallonsu, yadda Zannur ya sa ƴaƴansu guda biyu a gaba, Fatima, da Shuraim, yana koya musu ɗaukan hoto

Fatima wacce suke kira da, Nihal tace

"daddy na ɗauka, wallahi i clicked it right! Adnan ka gani!"
ta faɗa tana tsalle tare da nuna ma Shuraim da ya kasa ɗaukan ko ɗaya.

Murmushi Zannur yayi yana faɗin

"shima yanzu zai ɗauka ki bar yi mishi dariya"

Ƙarasowa tayi cikin ɗakin a hankali tana murmushi,

"Daddy saura Ni"

Ta faɗa cikin shagwaɓa da sigar zolaya.

Juyowa sukayi Dukansu suna kallonta, kafin Shuraim yace

"daddy ni Ummi zan ɗauka, bazan ɗauki mimi ba, tunda ta min dariya"

"To shikenan, but is daddy allowed to join Ummi? Ya tambaya yana murmushi

"Eh kai kaɗai amma"

Matsawa kusa da ita yayi yace
"to my boy"
Ai Yana shirin ɗauka Mimi tayi saurin shiga ya ɗauka da ita, nan fa suka shiga rikici.


Noor ce ta ƙarasa tare da karɓan mini câmeras ɗin hannunsu, to ya isa haka, kuje lesson teacher ɗinku na hanya, don't keep her waiting.

"Toh Ummi" suka faɗa a tare, Da sauri suka juya suka fice a ɗakin dan ɗauko littafan makarantarsu.

Janyota Zannur yayi yana faɗin,
"me kikace ɗazu?, kikace saura ke? To muje in koya miki naki"

Turo baki tayi tana faɗin Nikam

"ah ah yanzu fa na samu sadeeq yayi bacci"
bai jira mai zatace ba, ya ja hannunta suka fice a ɗakin.


Yasira kam zuwa yanzu, ƴaƴanta huɗu, dan kuwa tun komawarta, Baba yayi mata aure da wani dattijo, mutumin yana da hankali sosai, kuma yana son Yasira sosai, a yanzu ta kwantar da hankalinta, ta riƙe mijinnata da ƴaƴan sa tana zaune lafiya da su.

Taufeeƙ da Amina duniya sabuwa, dan kuwa yanzu ƴaƴansu biyu, suna zaune cikin kwanciyar hankali da soyayyah.

Asabe tayi aure Ita ma, har tana da ya'ya biyu.

Papi da Ammi, suna zuwa Nigeria, duk sanda suka ji kewan su Noor, haka Abbu da Maami, kamar yadda suma suke zuwa musu duk sanda suka samu hutu daga wajajen aikinsu.

A yanzu ana shirin auren Farhaana, da saurayinta ashraf acan Dubai kenan, Noor ana ta shirye shiryen zuwa, dan kuwa itace ƙirjin biki.


Tammat bi hamdillah, anan na kawo ƙarshen littafin ABNUR, kuskuren da nayi ina roƙon Allah ya yafemin, da Ni da ku baki ɗaya,na taƙaita labarin saboda wasu dalilai nawa.
Alhamdulillah, Alhamdulillah Alhamdulillah.


Maimoon#

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment