Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sauƙa akan fuskarsa.

Da sauri ya ƙara so ya na faɗin

"Noor!"

Da kokonto, wai gashi ga ƴar Fatima kuma ƴarsa, ko dai mafarki yakeyi ne?

Itama tuni hawaye ya jiƙa fuskarta, dan tabbass bata buƙatar ace mata wannan mahaifinta ne, kamar da takeyi da shi ma kaɗai ya wadatar.

Da sauri ya nufe ta, yana faɗin

" yarinya ta ashe kina nan?, ina ta nemank...."

Hannu ta ɗaga masa da sauri idanunta na kwararar da hawaye,

"Kar ka ƙaraso kusa dani, Ni ba ƴarka bace, kuma bazan taɓa zama ƴarka ba, da ace Ni ƴarka ce bazaka taɓa wofintar da rayuwata da ta mahaifiyata ba, bana son ganinka Dan Allah ka tafi ka barni, in cigaba da rayuwa kamar yanda na faro."


With shock yake kallonta, amma ya gagara ƙara ɗaga ƙafan kamar yadda ta faɗa

"Noor ki saurareni, ban wofintar da ku dan son raina ba, hasalima bansan da akwai cikinki ba Noor, kuma wallahi duk duniya babu wanda ya kaini sonku ke da Fatima."


"ƙarya kakeyi kai ba mahaifina bane, kuma bazan taɓa ɗaukan ka a matsayin mahaifina b........"

Tass!, sauƙar Marin da taji a fuskarta, ya sata haɗiye sauran maganan da ke bakinta, tana kallon Umma da shock,

Jawota Umma tayi ta rungume, tana kuka itama tana faɗin,

"Noor mahaifinki ne shi, ko me yayi miki bai cancanci ko wani irin magana daga bakin ki ba, ki sauraresa kiji dalilinsa, daga nan sai ki yanke duk hukunci da kika ga ya dace dashi."

Fashewa tayi da kuka tana sake rungume Umma,

"Ummah baya so na, bayason Nenne, shiyasa ya tafi ya barmu, kowa baya sona, Zannur baya sona, wani irin rayuwace irin tawa."

Ta faɗa tana ɗurkushewa a wajen, tana cigaba da wani irin kuka mai taɓa zuciya.


Da sauri papi da ya gama daskarewa a tsaye, shima ya kai ƙasa ya riƙo ta gabaɗaya, fuskarsa ta gama yin jajazir.

'Wayace miki banasonki Noor" ya faɗa jikinsa har rawa yakeyi,

"wallahi Noor nafi kowa sonki, pleaaaaase ki yafe ma papi kinji daughter."


Rungumesa tayi tana sake fashewa da sabon kuka, shi kanshi ya kasa daurewa, hawaye kawai ke fita daga idanunsa, ya rungumeta sosai a jikinsa yana jin kamar ya maida ita cikinsa ya sake haifo ta, saboda tsananin son da yake ji yana mata.

Sun ɗauki tsawon lokaci, kafin kowa ya dawo nutsuwarsa.

Baba da ke tsaye har lokacin yayi gyaran murya yana faɗin,

"To masha Allah, Allah mai hikima"


Umma da ta ƙarasa shinfiɗa tabarmar da Noor ta yasar tace,

"Alhaji bismilla."

Khamal kam da Abdul kallon ikon Allah kawai sukeyi.

Kafin kowa ya sami waje ya zauna, Noor kam tana jikin papi, Dan shi kanshi ya ƙi bari ta matsa daga kusa da shi.

Sai da kowa ya nutsu kafin Baba ya faɗa ma papi komai da ya faru, daga haɗuwarsu da Noor zuwa yanzu.

Jinjina kai kawai papi yakeyi kafin yace

"nagode, nagode, bansan da wani kalma zan yi anfani in gode muku ba, dan kun riƙe min yata mafi soyuwa a gareni, bani da abinda zan biyaku da shi, sai dai ina muku addu'ar Allah ya saka muku da mafificin alkhairinsa."


Ameen duk suka amsa dashi kafin papi ya ɗora da fadin,

"kuma ina neman alfarmarku, ku barni in tafi da Noor yau, dan Allah."

Da sauri Umma tace

"Alhaji da dai an bari zuwa gobe, yanzu yamma tayi", ta faɗa hawaye na ciko idanunta dan sam batason rabuwa da Noor.


"Ah ah Aisha ki barshi ya tafi da ƴarsa, ai da nan da can duk ɗaya ne, kuma ai zumunci ba yanke wa zai yi ba, Noor ƴarkice har abada."

Da sauri papi yave

"wannan haka yake, har abada zumuncin ku da Noor ba zai taɓa yankewa ba na muku alƙawarin hakan."

"Shikenan Alhaji mun gode sosai",

Umma ta faɗa tana matsar hawaye.

Babu abinda Noor ta ɗauka, daga ita sai kayan jikinta, sai gyalen abayar a kanta suka fito daga gidan, su Umma suka musu rakiya har bakin mota,

Zare hannunta Noor tayi daga na papi, da sauri taje ta rungume Umma tana kuka,

A hankali Umma tace

"Noor ki kwantar da hankalinki, insha Allahu zamuzo muga inda kike bada jimawa ba kinji."

Gyaɗa kai tayi kafin taje gurin Baba dake tsaye shi kansa daurewa kawai yakeyi

"Baba zan tafi'
ta faɗa tana rufe fuskarta saboda kukan da ya ci ƙarfin ta,

"Allah ya miki albarka Noor, sai munzo."

Ya faɗa yana shafa kanta, juyawa tayi zata shiga motar, khamal yace

"Wato Ni kadai ne baza'a ma sallama ba koh Noor?"

Da sauri ta juyo tana kallonsa

Murmushi yayi yana faɗin ba

"laifinki bane wato anga Baba, an manta da yaya ko?"

Kuka ta fashe da shi, da sauri Baba yace

"khamal ka kiyayeni fah."

Dariyar ƙarfin hali khamal yayi ya matso kusa da ita yana faɗin

"wasa nake miki ƙanwata, Allah ya kiyaye hanya ya kai mana ke lafiya Noor, sai munzo."

Ɗago idanunta tayi kafin a hankali tace

"nagode"

Bai ce mata komai ba ya buɗe mata baya ta shiga, papi ma sallama yayi musu ya shiga motar, driver ya tada motar suka bar ƙauyen suna ɗaga ma juna hannu.






Maimoon#


*💖ABNUR💖*

*By Maimoon*


*Elegant online writers* 📚📖


*Page 21*



Har suka isa Airport, babu mai cewa komai a motan, daga Noor har Papi, kowa da irin tunanin da yake a zuciyarsa.


Juyowa Papi yayi ya kalleta, yadda ta matsa can jikin window, ta jingina kanta, idanunta a lumshe, sai kayi tunanin bacci takeyi.

Amma a bangaren Noor tunani kawai takeyi,

gwara ma tayi nisa da Zannur, idan ta tafi tare da mahaifinta, bazai sake ganinta ba, bazai sake jin ɗuriyarki ta ba, ta fita daga rayuwarsa na har abada.

Tsayuwar da motar yayi, shi ya dawo dasu daga tunanin da suka lula, a hankali suka sauƙo daga motar, kowannen su jikinsa a sanyaye yake.

Har papi ya gama duk abinda zasu buƙata, hannunsa na cikin Noor, haka suka shiga jirgi yana riƙe da hannunta.

Duk da Noor bata taɓa shiga jirgi ba, but ta daure sosai, har jirgin ya daidaita a sararin samaniya.


Ƙarfe 8:00 na daren ranan Papi ya shigo da Noor cikin gidansa, a matsayin ƴarsa halak malak, wacce zai iya nunawa duka duniya with proud yace

"Noor ƴatace."


A Falon ƙasa suka sami Sudais da Namra, suna hide nd seek, suna ganinsa suka nufosa da gudu suna faɗin
"papi"

Ɗaga sudais yayi yana dariya kafin yace

"kazama ƙatoto kaima fa"
duk suka tuntsire da dariya, Namra tace

"papi you are welcome"

ta faɗa tana kallon Noor.

Jawo hannunta yayi yace

"oya common, greet your elder sister"

What's her name?

Namra ta tambaya tana cigaba da kallonta, dan ganin tsananin kaman da sukeyi da papinta.

"Noor"ya faɗa yana murmushi.

Ƙarasowa tayi gaban Noor kafin tace

"Ina wuni anty Noor"

Wani sanyi Noor taji tundaga tsakiyar kanta har babban yatsanta,
Yanzu waɗannan ɗin ƙannen ta ne?
Wani irin sonsu taji ya shiga ranta fiye da tunaninta,
Ta tsura ma Namra ido bata ko ƙiftawa.

Ammi dake sauƙowa daga sama, Farhaana a biye da ita, suka ƙaraso Falon, fuskar Ammi babu yabo babu fallasa, tace
"sannunku da zuwa." cikin harshen larabci.

Da sauri Farhaana ta ƙaraso tana kallon Noor, sai kuma ta juya ta kalli papi da sauri.

Gyaɗa mata kai yayi yana murmushi.

Ai da gudu ta ƙaraso ta haye jikin Noor tana faɗin

"ukhty, Finally mun sameki, muna ta nemanki up and down, Ina kika shiga kika sa Papi kuka"

Dariya kawai Noor tayi, sannan tace

"gani ai na dawo"

ta faɗa tana matsar da Farhaana daga jikinta ta nufi Ammi dake Zaune, tsugunnawa tayi a hankali tace,

"ina wuni Nenne"

Wani kallo Maami tayi mata, kafin tace

"point of correction, Ammi, Ni ba Nenne bace, Ni Ammi ce."

Ta faɗa tana miƙewa ta bar falon.

Da ido duk suka bita, kafin papi ya ƙaraso ya riƙe hannun ta

"don't worry daughter, that's how she is, but zata sauƙo kinji, muje in kaiki ɗakin ki kiyi wanka kiji abinci, kiyi bacci, kin gaji, gobe sai ayi introducing ɗinki ga kowa duk dama kowa ya sanki,kece dai baki san kowa ba."

Batace komai ba tabi bayansa, har ya fara hawa steps ya juyo ya dubi Farhaana, kafin yace

"kuje ku kwanta dare yayi"

"Night Papi" duk suka faɗa a tare

"Night Papi's Angels"

Daga haka ya ja hannun Noor suka haura sama, sai da ya kaita wani katafaren ɗaki, da ya gaji da haɗuwa, kafin ya ce mata

"Daughter kiyi wanka akwai kaya a cikin siff ɗin, kafin zuwa gobe muje muyi shopping, za'a aiko miki abinci, sai kici ki kwanta kinji rabin raina?"

Kallon sa kawai takeyi, har ya miƙe ya je bakin ƙofa ya tsinkayo muryarta tana faɗin

"Meyasa ka tafi ka bar Nenne na,sannan ka kasa dawowa har sai bayan bata raye" ta faɗa idanunta na ciko wa da hawaye.


Cak ya tsaya da tafiyan, kafin ya juyo a hankali, dawowa yayi ya shafa kanta shima nasa idon na cika da hawaye

"daughter kin gaji, ki samu ki huta, zamuyi maganan gobe alright?"

Ya faɗa yana kallonta, dan dama ko bata tambaya ba gobe dolene ya sanar da ita.

Daga haka ya juya ya fice a ɗakin yana jin sanyi a ransa.


Sai da ta yi wanka, sannan ta shirya cikin kayan bacci masu laushi, riga da wando, band ta sa ma kanta, kafin ta juya ta kalli tray ɗin dishes ɗin da aka ajiye akan ɗan madaidaicin dining table dake ɗakin, ƙarasawa tayi ta zauna ta buɗe abincin.

Bata wani ci sosai ba, ta dai ɗan tsatsakura, kafin ta miƙe, taje ta ƙarayin brush, tare da alwala, sallah tai-tayi tana godiya ga Allah da ya sada ta da mahaifinta, cikin lafiya da kwanciyar hankali.

A bangaren papi ma haka ne, ya kasa bacci, shima alwalar yayi, ya hau sallaya, yana ƙara gode ma Ubangiji da ya haɗa sa da ƴarsa sannan yayi ma Nenne addu'o'i sosai yana jin he is relieved from a very big burden.



A daidai wannan lokaci kuwa a garin Abuja, Zannur ne akan sallaya, babu abinda yake roƙo da addu'a akai sai Allah ya sa dashi da Noor.

Har ƙarfe 2:00 kowannensu na kan sallayarsa, kafin dukaninsu suka miƙe kamar suna ganin juna, kowa ya kwanta tare da addu'an bacci, da tunani iri, iri acikin ransa

(Asuba ta gari 🌝).

Washegari Noor ta tashi cikin matuƙar farin ciki, tare sukayi breakfast da duka ƴan gidan, kafin papi ya faɗa mata sunayensu da shekarun su,sannan suka zaga da ita ko ina a gidan, ita dai murmushi kawai takeyi.

Ammi kam daman suna gama cin abinci tayi wucewarta ɗakinta.


Kamar yadda papi ya faɗa kuwa haka akayi, shopping suka tafi har da su Farhaana.

Noor taga gata, wanda ake kira gata, dan daga ƙarshe fashewa tayi da kuka kawai na tsantsan farinciki.

A gajiye suka dawo da kaya niƙi niƙi, kamar masu buɗe supermarket, tare duk suka shirya kayan tsaf, kafin Papi yace

"Noor kiyi wanka sai ki sameni a ɗakina."

Noor tace "toh papi"
Fita yayi ya bar su, ya koma part ɗinsa.

Sai da ta gama duk abinda zatayi kafin ta nufi part din papi, a can ta samu Ammi, da alama Papi ne ya kirata, waje ta samu ta zauna, kafin papi yayi gyaran murya ya fara faɗin

"Noor, nasan zakiso kiji, miye dalilina na barinku danayi, a yanzu zan sanar dake."
Gyaran murya yayi kafin ya cigaba.


"Ni asalina ba ɗan ƙasar nan bane, mahaifina da mahaifiyata duka ƴan Dubai ne, ƙaddara ita ta haɗani da Yusuf a makaranta, ɗan Nigeria ne da yake karatu a Dubai, sakamakon scholarship da ya samu, tunda na haɗu da Yusuf, muka shaƙu sosai, har ya zamana kamar shine best friend ɗina, sannan ina matuƙar sha'awar Yaren Yusuf wato Hausa, da Yusuf yaga ina so, sai ya fara koya min, kasancewar ina da saurin koyan abu, cikin lokaci ƙalilan na fara gane Yaren Hausa, amma sam iyayena basason abota na da Yusuf, a ganinsu shi bak'ar fata ne, ɗan Nigeria, wanda Ni sam bai dame Ni ba.
Kullum Idan Yusuf ya tashi zuwa Nigeria ganin iyayensa, sai naji kamar na biyosa, saboda yadda nakeson ƙasar a raina, amma ina tsoron iyayena.
Ana haka sai muka gama makaranta, Yusuf yace min idan ya tafi ba lallai ne ya sake zuwa ba, alokacin na masa alƙawarin zanzo Nigeria gurinsa, Yusuf ya dinga jin daɗi.
Bayan tafiyan Yusuf, sai na rasa me zan ce ma iyayena, su barni na zo Nigeria, kasancewar Ni architecture ne yasa nace musu na samu wani contract, da zai iya ɗauka na aƙalla wata shida, a wata ƙasa, amma banyi kuskuren ce musu a Nigeria ba.
A zatona, wata shida ya isheni, in San Nigeria, da komai nata, in iya yarenta, sannan in zauna da Yusuf Abokina.
Iyayena basuyi kokonto ba, suka barni na tafi, tunda nazo Nigeria na ringa mamakin irin gidan da Yusuf ke ciki, gida ne ƙarami, mai ɗakuna biyu kacal, kuma a unguwar talakawa, hakan yasa na kama mana apartment guda muka zauna, a cikin garin Kaduna.
Kullum sai mun je mun zaga gari, mun ga abubuwa iri-iri, farinciki nakeyi sosai, kasancewar wannan shine abinda nake so.
Ana haka Yusuf yace min zaije ganin iyayensa, amma bazan iya zuwa ba, saboda a ƙauye ne, ai kuwa nace bai isaba, ko a jejine sai naje.
Haka muka shirya, muka nufi Baulawa, wanda shine ƙaddarar haɗuwa ta da Fatima.
Yusuf ɗan mai gari ne,hakan yasa muka sauƙa a gidan mai gari, amma kullum sai mun fita, ganin gari, saboda yadda garin keda matuƙar kyau.
Tun ganin farko da nayi ma Fatima a wani bikin shekara da ake yi a ƙauyen, Allah ya ɗaura min matuƙar sonta, har mamaki nakeyi, tayaya za'a yi na so ɗan Nigeria, iyayena baza su taɓa amincewa ba.
Amma babu ruwan zuciya, tun ina binta bata yarda, har itama ta fara kulani, soyayya mai matuƙar tsafta ta shiga tsakani na da ita, duk da sati ɗaya mukazo yi da Yusuf,amma sai nace masa Ni bazan tafi ba, Yusuf yayi ta min dariya, yana faɗin

"ka dai ga ƴar fara kyakkyawa"

sai dai kawai nayi murmushi.
Babu yadda na iya bayan mun cika kwana goma, haka na tafi na bar masoyiyata Fatima, tare da alƙawarin zan dawo idan Yusuf zai sake zuwa, dan kuwa makarantar da Yusuf ke koyarwa sun nemesa.
Hankali na bai tashi ba, sai da na yi waya da mahaifiyata, kwana biyu bayan dawowan mu daga Baulawa, ita take sanar dani wai kar nakai wata shida na dawo, za'a haɗani da ƴar uwata Nadiya aure, saboda yadda take mutuwar sona.
A take nace mata, Ni bana sonta, amma sai ta ce min, ai sun riga sun amince.
Ƙarshe sai ce mata nayi, ai bazai yiwu in dawo ba tunda contract ne, su jira six months ɗin.
Haka suka aminci badan ransu ya so ba.
Ni na uzura ma Yusuf, muka sake komawa Baulawa.
tunda naga Fatima, nasa a raina, bazan iya rayuwa babu ita ba, kasancewar a hannun matar mahaifinta take, sam bata samun kulawa.
Ai kuwa ina zuwa na zame mata cingam, ko ina zata je sai na bita, har mutane suka fara saka mana ido.
Ranar da bazan taɓa mantawa ba, a rannan ina zazzaɓi, hakan yasa banje ko ina ba, tun safe bamu haɗu da Fatima ba.
Yusuf kuma yaje gurin mai gari, ina kwance, sai naji an buga ƙyauren a hankali, miƙewa nayi da ƙarfin hali, na buɗe, ga mamakina sai naga Fatima.
Dana ce ta shigo, sai naga kaman tana tsoro, sai nace mata babu komai ta shigo, idan bata shigo ba bazan kulata a wajen ba, dan jiri nakeji bazan iya tsayuwa ba, hakan yasa ta shigo, kwanon abinci ta ajiyemin, tace wai ta kawo min inci, murmushi nayi na ɗauka ina ci muna hira da ita, amma duk ta kasa sakewa.
Can kuma sai ta miƙe tace min, ita zata tafi, hakan yasa nima na rakota ƙofa.
Mutanen da muka gani a bakin ƙofa ya sani matuƙar mamaki, dan kuwa kusan rabin ƴan garin suna bakin ƙofar mu.
Haka suka ƙeƙashe suka ce wai ɓata mata tarbiyya nakeyi ai sun jima da ganin take-takena, abun ya bani mamaki, alokacin sai ga Yusuf, shima yayi iya ƙoƙarinsa ya fahimtar da su amma sam suka ƙi fahimta, a nan take suka ce sai dai muje a ɗaura mana aure, dan su ba'a ɓata musu yara a zauna lafiya,
Bayan ɗauki ba daɗi da akayi tayi, ganin Fatima na kuka, kuma nasan Ni na janyo mata, kuma ina sonta yasa na amince, ai kuwa ba'a ɗau lokaci ba aka ɗaura mana aure wanda nake jinsa yamin banbaraƙwai, su wasu irin mutane ne, babanta bai damuba, haka ma kishiyar mahaifiyarta, washe gari muka bar ƙauyen, muka taho cikin Kaduna, anan muka zauna.
Wani irin tsabtataccen soyayya muke shimfiɗawa, wanda har nakejin rayuwata tafi ko yaushe daɗi, bana son tuno cewa wata shida nayi da mahaifana.
Kwanci tashi, har wata shida, ya wuce, amma bana tunanin komawa gida, iyayena sunyi kira har sun gaji bana ɗauka, a wata na takwas na samu mail daga baba na, yayi bincike ya gano ina Nigeria, kuma idan har ban koma ba a cikin sati na gaba, shikadai yasan abinda zai min.
Nasan halin mahaifina, yana da matuƙar zuciya, hakan yasa na yanke shawaran komawa, but zan je in shayo kan iyayena, in dawo in tafi da Fatima.
Na yi ma Fatima bayanin komai, ta amince, amma ta sa nayi mata alƙawarin zan dawo gareta.
Nayi iya yi na, inga na fahimtar da iyayena, amma sam suka nuna basu san da maganar ba, har ƙoƙarin tsine min sukayi idan har na cigaba da wannan maganan.
Sannan basu ɓata lokaci ba suka ɗaura min aure da Nadiya, sannan sai da mahaifina ya tabbatar ya goge duk wani abu da zai haɗa Ni da Yusuf, bare har inji lafiyan Fatima, bayan haka, mahaifina da mahaifiyata, suka ce, idan har na taka ƙafa na a Nigeria, to wallahi bazasu taɓa yafe min ba.
na shiga wani hali, har sai da na kwanta a asibiti, amma kasancewar bani da mafita ya sa na hakura na auri Nadiya, Wanda Alhamdulillah yanzu muna da ya'ya har uku da ita.
Yusuf kam ganin kuɗin gida ya ƙare, kuma bazai iya sake biyaba, yasa ya tattara Fatima ya mayar da ita Baulawa, amma acikin kuɗi mai yawan da na bashi kafin na tafi, sai ya siya mata gida, sannan yace musu nayi tafiya ne kuma zan dawo.
Sam bansan akwai cikinki ba, ita kaɗai tayi renon cikinki ta haife ki.

A yanzu haka da nake faɗa miki, mahaifiyata da mahaifina, sun rasu a wani plane crash a hanyar su ta zuwa Iraq, Amma kafin tafiyarsu sun tabbatar min zan iya zuwa Nigeria. Naji matuƙar daɗi ashe sune zasu barni, dan tafiyan da basu dawo ba kenan.
Sai dai kash, ina zuwa sai mai gari ya sanar da Ni Fatima ta rasu, ke kuma kinyi Aure.
a wajensa na samu hoton ki, na bazama nemanki, amma na rasa ki, sai bawan Allah khamal ya kirani yace kina wajensa."

Ya faɗa ya share hawayen idanunsa.

Itakam Noor kuka take wiwi, ita kanta Nadiya kuka takeyi, dan bai taɓa bata labari ba, kenan Nenne yake zanawa duk kwanan duniya?

A hankali ta taso ta ɗago Noor tana faɗin

"kiyi haƙuri Noor, insha Allah zan maye miki gurbin Nenne."

Da mamaki yake kallonta, kafin yayi murmushi yace

"Nadiya na gode."

Sai da suka ɗan lafa, kafin ta sake basu labarin tasowarta da rasuwar Nenne, zuwa aurenta da Zannur har kawo yau.

Duk shiru sukayi suna jinjina al'amarin, kafin Noor tace

"To papi Ammi da su Farhaana kuma a ina suka iya Hausa?"

Murmushi Ammi tayi tana faɗin

"ai kowa ya zauna da shi sai ya iya Hausa, sai da ya tabbatar mun iya"

ta faɗa tana dariya,
Shima dariyar yayi.


A ranan sun wuni cikin farinciki a gidan, jifa jifa takan tuno Zannur, amma sai ta kauda a ranta, dan bataso tana tunoshi.

Rayuwar Noor a gidan iyayenta, rayuwa ce mai cike da kulawa, gata, da soyayyah, babu abinda ta nema ta rasa, hakan yasa ta sake kyau, ta sake zama ƴar gayu, dan kuwa, Ammi basuga wannan shopping center ɗin, basuga wannan.

Zannur kam.......



Maimoon#


*💖*ABNUR*💖*

*By Maimoon*

*Elegant online writers* 📚📖

*Page 22*


Zannur kam, gaba ɗaya ya rasa me ke masa daɗi, ya canza kamar ba shine Zannur the master of All ba, tun Maami na ɗauka da wasa, har hankalinta ya soma tashi, kwata kwata ya daina walwala, ko magana ba yayi sai dole.

sometimes Maami har kuka takeyi, sai dai Abbu ya rarrasheta, zuwa yanzu shima abin ya fara damunsa.

Yasira ta rasa yanda zatayi, gabaɗaya komai ya kufce mata, ita sam ba haka ta so ba, to yaushe ma Zannur ya soma son Noor har haka?, lallai tayi mugun sake.


Amina da Asabe kansu sun rage walwala, da yake yanzu Amina ce chief of kitchen staffs, kullum ta gansa, cikin damuwa take ganinsa, duk da cewa a da ma ba wani shiga harkarsu yakeyi ba, sai dai Taufeeƙ, amma yanzu daga shi har Taufeeƙ sun zama wasu iri, hakan yasa gidan kowa baya cikin farinciki.


*******


"Habibi wai meyasa yanzu baka jin maganata ne?, rabonka da abinci tun yaushe?, Please Habibi kaci abinci kaji?" ta faɗa da alamun damuwa a tattare da ita


Bai ɗago ba, bare tasa ran zai tanka, hakan yasa ta ajiye tray ɗin akan center table na ɗakin ta juya ta bar ɗakin tare da ja masa ƙofa.


Tray ɗin abincin ya ƙura ma ido, yana jin zuciyarsa na bugawa da sauri, bai taɓa sanin yana ma Noor irin Wannan matsanancin son ba, har sai da tayi nisa dashi.

Ɗaga idanunsa yayi yana kallon saman ɗakin, kafin ya shafa kansa, yana gyara kwanciyarsa a kan gadon Noor.

***********

"Abbu ya zanyi?, yarinyar nan ta cutar min da yarona, me yasa in the first place zata tafi ta barsa?"
Maami ta faɗa tana fashewa da kuka.


Jawota Abbu yayi ya rungume, shi kansa daurewa yakeyi, a hankali yace

"Hilwa, listen to me, ki kwantar da hankalinki, idan har tana raye za'a sameta."

Ya faɗa yana shafa sumar kanta, ɗayan hannun kuma yana share mata hawaye


Shiru tayi tana kallonsa, kafin tace

"Abbu ya zamuyi mu taimaka ma Habibi ya sami yarinyar nan?, don itace kwanciyar hankalin mu duka."


Shiru Abbu yayi kafin yace,

"ga shawara"

Da sauri ta miƙe daga jikinsa tana faɗin

"Dan Allah Abbu faɗa min, zan yi ko miye ne"

Murmushi yayi yace

"Me zai hana mu siyi gaban mujallar gobe, mu da kanmu on behalf of Zannur, mu roƙi Noor ta dawo."

Shiru tayi sai kuma tace

"Shikansa Zannur ɗin ya sa an buga mujalla ana nemanta, but ba'a sameta ba."

"Nasani Hilwa, but still zai iya yiwuwa, shi tana jin haushinsa, amma ai mu zata ji kunyar mu ta dawo, mu dai kawai ba burinmu Noor ta dawo ba?"

Shiru Maami tayi, kafin tace

"Allah ya sa mu dace, wannan yarinya dai ta taimake Ni ta dawo."

Kamar yadda Abbu yace, haka mujallar washegari ta fita da jawabin Abbu da Maami, da hoton Noor ba tareda ko shi Zannur ɗin ya sani ba.

Papi dake karatun jaridar safiyar ne ya ci karo da hoton Noor da kuma bayanin su Abbu, wanda duk banbaki ne, da kuma sanar da ita haalin da Zannur ke ciki akan rashin ta.

Murmushi yayi a hankali ya furta akan laɓɓansa

"Daughter kinyi punishing ɗinsu enough, it's time ke ma kiyi rayuwa kamar kowa da mijinki"


Daga haka ya juya ya fito a ɗakin, Ammi ya samu a ɗakinta tana shirya siff ɗin ta, a hankali ya ƙaraso da sallama, kafin ya samu guri a gefen gadonta ya zauna yana kallonta

Ƙarasawa tayi, itama tazo kusa dashi ta zauna tana faɗin

"Is anything wrong?"

Murmushi yayi mata yana jan kumatunta,

"Babu komai Fah, look how you are worried for reason"

Murmushi tayi itama tana faɗin
"dole na damu na ganta kamar abu na damunka."

Shiru yayi sai kuma yace

"Ina Noor?"

"Tana ɗakinta, I think bacci ma takeyi."

"Ok", ya faɗa yana ɗaura mata jaridan akan ƙafarta

Sai da ta gama karantawa kafin tace

"to yanzu kai me ka yanke akan hakan?"

"Zata koma gidan mijinta mana, babu abinda yafi mata daraja kamar wannan, sannan ai sun gane kuskurensu, and am sure they won't repeat"

"Ok but da munji ta bakinta"

"Nope ki ce mata ta shirya zamuyi tafiya, i will return her myself, sannan in yi magana da mijinnata"

"Ah ah sai dai mu tafi tare

Please Login or Register in order to submit comment