Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ƙofar ta buɗe, alamar ba'a rufe da kyau ba, a hankali ya ƙarasa tura Kofar,
Wayam yaga banɗakin babu kowa.


Zuciyarsa ce tayi wani irin wawan bugun da ya sashi dafewa da sauri,

kafafuwansa da sukayi nauyi, ya ja da sauri ya juya ya nufi ɗakinsa, laptop ɗinsa ya nufa.


Kai tsaye kitchen ya duba, bata ciki, ya duba duk wani guri a gidan amma babu ita, cikin sauri ya shiga tariyewa baya 3days ago tun sanda ya bar gidan.

Wani irin miƙewa yayi yana faɗin

"shit"

Landline ya ɗauka yana kiran securities ɗin gidan

Yana ɗagawa yace

"where is Noor?
Why do you let her out? akan me ya sa kuka barta ta fita a gidannan ba tare da izinina ba." ya faɗa a tsawace.


"Sorry Sir"

"Shut up, na baku 30 minutes ku nemo min matata, idan ba haka ba..." sai kuma yayi ƙwafa yana katse wayan.


Dafe kansa yayi, yana riƙe ƙugunsa
Sai kuma ya durƙusa a wajen yana jin idanunsa na masa matuƙar raɗaɗi

"Why Noor, meyasa baki jirani na gano gaskiya ba?, Noor you are my life, Please ki dawo gareni, I promise to trust you completely, wallahi bazan sake kuskuran fahimtar ki wifey."


Sai lokacin, hawaye mai zafi ya sauƙa masa, bazai yafewa ko waye yayi sanadiyyar rabasa da Noor ɗinsa ba.


Bai san tsayin lokacin da ya kwashe a wajen ba trying to calm himself, kafin ya miƙe da sauri ya nufi downstairs cikin sassarfa.


(Finally we are back, and the story continues.....)

Numfashi ta sauƙe a hankali tana share hawayen idanunta, bayan ta gama basu labarin abubuwan da ta sani.

A hankali umma ta taso ta zo kusa da ita tana shafa kanta.

Kamal kam kallonta kawai yakeyi sai kuma ya sunkuyar da kansa, yana murza hannunsa, dan ya gagara cewa komai.


Baba ne yayi gyaran murya kafin ya fara magana

"Noor, munji labarinki, kuma a gaskiya kin yi haƙuri, kuma Allah ya jiƙan Nenne, yanzu abinda nake so dake kije ki kwanta insha Allahu zamuyi magana gobe, muga ya zamu samo mafita, Allah ya miki albarka."

"Ameen" umma ta amsa dashi, tana shafa kan Noor dake cigaba da kuka.

Jin kiran sallan Asuba, yasa Baba faɗin

"subhanallahi, ashe ma garin har ya waye, mun kwana a zaune fah kenan, to Allah ya kyauta, kamal tashi muyi haramar tafiya masallici, A'isha sai kuyi sallah kafin ta kwanta koh?."

"Insha Allah Malam"

Umma ta faɗa tana miƙar da Noor suka fice a ɗakin.

Sai lokacin khamal ya miƙe shima, suka fice da Baba, Dan tafiya masallaci kafin a shiga sallah.


************

Ƙarfe 1:30 daidai, jirgin *Emirate Airlines* daya taso daga *Dubai* ne ya sauƙa a babban filin jirgi na Kaduna wato *Kaduna international Airport.*

A hankali mutanen ciki ke sauƙowa, ɗaya bayan ɗaya a gajiye.

Farhaana ce ta fara sauƙowa, sai sudais da namra a bayanta, duk fuskarsu a jagule, daga bayansu kuma Ammi ce, sai papi a bayanta.

Haka suka jero suna sauƙowa abin sha'awa,

sai dai fuskokinsu babu wanda yake walwala, idan ka cire sudais kasancewar bai ma san me akeyi ba shi.


Sai da suka gama yin all the formalities, kafin suka zarce gidan da papi ya saya a garin Kaduna wanda ke unguwar GRA, har suka isa babu mai cewa komai.

Suna shiga, Farhaana taja su Namra suka wuce shashinsu, Ammi ma nata ta wuce suka bar papi a tsaye, shafa sumar kansa yayi, a zuciyarsa yana faɗin

"Na gaji da zama da haƙƙinki, a wannan lokacin babu wanda zai hanani nemanki, dan tabbatar miki da alƙawarina a gareki, ina fatan zaki yafe min, sannan kimin kyakkyawar fahimta".

Daga haka ya wuce shashensa shima yana jin matsanancin gajiya a tattare dashi.


**********

Zannur ne a zaune kusa da Taufeeƙ da ke barci ƙura masa ido yayi yana kallonsa, bai san miye dalilin Taufeeƙ na ƙin faɗan wanda ya aikata masa haka ba, yayi iya ƙoƙarin sa, amma Taufeeƙ yaƙi cewa komai.


Miƙewa yayi ya ƙarasa jikin window yana jin zugi a ransa, meyasa ƙaddara ta zo masa a haka?, da wanne zaiji?, da ɓatan Noor ko kuwa da rashin lafiyar Taufeeƙ?.

Taufeeƙ ɗan amanarsa ne, da bazai iya barinsa ba kuma sai ya hukunta ko waye ya aikata masa hakan,
Gashi ya kasa sanar da Maami abunda ke faruwa.


A hankali ya juya ya bar ɗakin yana jinsa kamar bashi ba.

Taufeeƙ daya buɗe idanunsa yana kallonsa, dan dama ba bacci yakeyi ba, hawayen da ya ciko idanunsa suka bi gefen fuskarsa, suna sauƙa akan gefen kunnensa.

A hankali ya buɗe bakinsa da yake a bushe, ya furta

"bazan taɓa bari a cutar da kaiba Sir, koda kuwa hakan na nufin ƙarewar rayuwata, hakan yasa na yanke shawaran ƙin faɗa maka, kayi haƙuri zan faɗa maka, amma sai a lokacin da ya dace, sannan nayi alƙawarin zaka zauna da Noor har karshen rayuwarka, sai dai idan kai kace baka sonta Sir, bazan taɓa manta halaccin ka a gareni ba, duk da Ni ba kowa bane, amma ka nuna min zallar soyayyah da kulawa."

Sai kuma ya juyar da kansa yana jin ɗaci a ransa.




Maimoon#

*💖*ABNUR💖**

*By Maimoon*

*Elegant online writers* 📚📖

*Page 19*


*Two days later*

Noor ne ta fito daga kitchen, hannunta ɗauke da kofin roba, tana sanye da abaya kalar baƙi, wanda khamal da kansa ya shiga cikin gari ya siyo mata da ATM ɗin ta, dan dama ta manta da shi ne ya sa har ta siyar da ɗan kunnenta.

Waje ta fito, ta samu waje ta zauna, a kusa da umma dake tsintar shinkafa, ajiye cup ɗin tayi ta shiga taya umma tsintan suna hira sama-sama.

Khamal ne ya shigo, da sallama, ya ja kujera ya zauna yana faɗin

"Sannu da aiki Umma"

"Yauwa sannu khamal ya gonan dai?"


"Alhamdulillah wallahi, ya gida?"

"Lafiya ƙalau"

A hankali Noor tace

"ina wuni yaya khamal"

"Lafiya"

ya amsa a taƙaice kafin ya miƙe yana faɗin

"Umma bari naje wajen Abdul"

"To sai ka dawo"

Sai da ya fice a gidan, kafin umma da maida dubanta ga Noor dake cigaba da tsintan shinkafan.

"Noor!"

"Na'am Umma" ta faɗa with full concentration.

Bakya kewan mijinki?, bakya tunanin kina so ki gansa?, Noor zaman aure da kika gani, wani abune mai matuƙar buƙatar haƙuri, da soyayyah, Noor ke mace ce, bakida inda yafi gidan mijinki daraja a wajenki.

Kuka Noor ta fashe da shi ba tare da ta bari Umma ta ƙarasa magananta ba.

Umma Ni bana sonsa, Umma ko ina sonsa zan hakura da shi, saboda idan har babu yarda to babu soyayya, me yasa bazai yarda da Ni ba?, meyasa zai yi tunanin zan iya aikata hakan ga Taufeeƙ?, laifin me yamin da har zan aikata masa haka?, umma na riga na yanke hukunci, banason komawa garesa har abada, idan kuma har kun gaji da zama da Ni ne please kuyi haƙuri."

ta faɗa tana cigaba da kuka

"Batun mun gaji da ke bai taso ba Noor, kawai ina faɗa miki ne a matsayinki na ƴata, dan ko da ace Ni na haife ki haka zan faɗa miki."

Cikin kuka Noor tace

"nagode Umma, amma dan Allah banaso na koma ga Zannur, please ki barni a nan."

Daga haka ta miƙe ta wuce ɗaki, Umma ta bita da kallo tana jinjina kai.

Baba da shigowar sa kenan ya tarar suna maganan, bai ce komai ba ya wuce ɗaki.

Miƙewa umma tayi tabi bayansa, a zaune ta samesa akan ɗan gadonsu yana matsa ƙafarsa da take ɗan masa ciwo.

Da sauri ta ƙaraso ta tsuguna ta sa hannu tana matsa masa ƙafafun,

"sannu Malam, ƙafar ce take ciwo har yanzu?"

"Eh wallahi Aisha, Amma ba sosai ba, Allah ya miki albarka."

"Ameen." ta faɗa tana cigaba da matsa masa duka ƙafafuwan.

"Yauwa Aisha naji kuna magana da Noor!"

"Wallahi Malam taƙi saurarata, kuma kasan halin yaran yanzu, tsoro na kar taga kaman zamu takurata mu neme ta mu rasa yanda mijinnata ya rasa ta."

Numfashi Baba yaja kafin yace

"hakane, amma duk da haka ai bazamu biye mata ba, yarintace kawai ke damunta, amma shima yaron dole na zauna dashi, kafin na bashi Noor, dole ne a aure ya zama akwai cikakken yarda da aminci, ai ba'a haka, yanzu so nake mu cire anfanin gona, idan mun siyar, kuɗin sai muyi anfani dashi mu maidata gidan mijinta, dan shine mutuncinta."

"Hakane kam Malam, Allah dai ya saka maka da alkhairi."

"Ya saka mana gaba ɗaya uwar ƴaƴana"

ya faɗa yana kallonta da murmushi.

Itama Murmushin tayi tana miƙewa tace bari

"naje na ƙarasa girki."

Daga haka ta fice a ɗakin.


***********


*_Kaduna Nigeria*_


What? Papi ya faɗa yana miƙewa tsaye,

"banganeba, me kake nufi?, papi ya faɗa yana ja da baya,

"Abinda kunnuwanka suka jiye maka nake faɗa."

Mai gari ya faɗa yana miƙewa shima.

"Yarinyar nan da ka gudu ka bari, ta rasu shekara biyu kenan sannan ƴarta tayi aure, ta auri wani ɗan Balarabe ɗan birni da ya zo garinnan, ya tafi da ita mu kan mu bamu san ina ya tafi da ita ba."

Girgiza kai papi ya shiga yi idanunsa sun kaɗa sunyi jajir

"Kana nufin Fatima tana ɗauke da cikina sanda na tafi na barta?, kana nufin ina da wata ƴar bayan su farhaana?, pleaaaaase ku faɗa min ina ƴata take ɗan Allah, ita ɗin jinin Fatima ce, matar da nafi so fiye da kowa a duniya."

A fusace Ammi ta miƙe tana faɗin,

" ba sai ka cigaba da maimaita cewa baka sona a gaban kowa ba razaƙ Abdulkarim, laifina ne dana so ka, sannan na biyoka Nigeria."

Daga haka ta miƙe daga kan tabarmar da take, tana riƙe hannun sudais,ta bar wajen.

Kasa cewa komai papi yayi, sai wasu zafafan hawaye dake sauƙa akan fuskarsa.

Farhaana ce ta ƙaraso inda yake, a hankali tace

"Papi zamu sameta insha Allahu, zamu nemo ƴar uwata a duk inda take a duniya, kuma Ammi zata sauƙo, but Please papi Kar kayi kuka."

Rungume ta kawai yayi, baice komai ba, shi kaɗai yasan me yake ji a cikin ƙirjinsa.

A hankali ya ɗago jajayen idanunsa, yana kallon mai gari,

"Dan Allah ko kuna da koda hoton ƴa ta ne, zan nemo ta duk inda ta shiga a duniya."

ya faɗa yana share hawayen da ya sauƙo masa.

Shiru mai gari yayi kafin yace,

"ai kuwa kayi matuƙar Sa'a, dan kuwa yaron da ya aure tan yana ɗaukan hoto, kuma bikin shekaran da akayi,
a shekaran da yazo garinnan ya musu hotunan, ina tunanin Noor ɗin na ciki, kuma ya kawo min wasu daga cikin hotunan, bari dai na duba, dan kuwa na adanasu dan tarihi ne."

"Noor!" papi ya maimaita sunan,

*kenan sunan ƴata da Fatima ta haifamin Noor"
sai kuma ya lumshe ido, sabbin hawaye na zirya akan farar kyakkyawar fuskarsa.

Miƙewa mai gari yayi, ya nufi cikin gida, can kuma sai gashi ya dawo da hotuna a hannunsa, sai da ya kalli hoton yaga da Noor kafin yayi wani Murmushi,

"aikuwa harda ita a ciki amma dai kam sai ka siya, dan bazan baka kyauta ba."

Da sauri papi yace

"zan siya ko da ace da dukkan kuɗin dana mallaka ne, pleaaaaase ka bani inga ƴa ta."

"Ah ah sai na fara ganin kuɗin"

da sauri ya miƙe yana zaro dukkanin kuɗin aljihunsa yana zube su gaban mai gari

"Idan basu isa ba, zan ƙara maka, akwai wasu a mota, a can mukayi parking sai naje na ƙaro maka."

papi ya faɗa yana miƙewa tsaye da alama baya cikin hayyacinsa.


Zaro ido mai gari yayi ganin bandir ɗin kuɗi har huɗu, ai baisan sanda ya watsar da hoton ba ya rungumi kuɗaɗe,

tsugunnawa papi yayi ya ɗau hoton yana kallo.

"Subhanallah, laa haula wala ƙuwwata illa Billah."

Babu inda Noor ta barsa, sai dai yanayi na Fatima data ɗauko.

Wasu hawaye Masu ɗumi ne suka wanke masa fuska, kafin ya miƙe, ba tareda yabi ta kan mai gari ba ya juya ya bar wajen Farhaana na biye dashi.

A jikin mota suka tarar da Ammi, ta cika tayi pam.

Bai bi takanta ba ya shiga Mota, suma shiga sukayi kafin ya tada motar ya bar garin gabaki ɗaya, a zuciyarsa yana tunanin ta inda zai fara neman Noor!.


************

Idan akwai abinda yafi tashi hankali, Zannur ya shigesa, gaba ɗaya ya rasa sukuni, ya rame, kamar ba Zannur ba, sai suma da ya tara har ya masa yawa.

Aƙalla yau watan Noor uku kenan babu ita babu labarin ta, yayi Neman har ya fara cire rai.

An sallami Taufeeƙ a asibiti, bayan jinya da yayi, a yanzu ya warke rass, sai dai baya cewa komai, sai an daɗe yake buɗe baki ya ce wani abu,

gaba ɗaya Zannur ya fita hayyacinsa, a yanzu ya ma daina neman wanda ya yi yunƙurin kashe Taufeeƙ, gabaki ɗaya hankalinsa naga inda zai ga Noor.


Yasira kam, komai ya jagule mata, dan kuwa Zannur ya koreta a aiki a matsayin chief staff na kitchen, hakan yana nufin, batada hurumin zuwa inda yake, sai dai zata zauna a gidan albarkacin Taufeeƙ, sai dai batada hurumi da mai gidan, dama da hakan take fakewa tana kallonsa tana jin sanyi a ranta, gashi yanzu Taufeeƙ ya toshe duk wata hanya da zata gansa, kwata kwata,

gabaɗaya tá rasa mai zatayi, tsoronta kaɗai kar ya faɗama Zannur, duk da a halin da Zannur yake a yanzu, bazai saurari kowa ba, dole ne tayi gaggawan ɗaukan mataki, kafin lokaci ya ƙure mata.


Yauma, a zaune Zannur yake a dakin Noor, Wanda ya jima da tarewa anan, Camera ne a gabansa, ya zuba ma hotunan ta ido yana kallo ko ƙiftawa bayayi.

Gashin kansa ya sauƙa gefe da gefen fuskar sa, he look pale, but duk da haka ya ƙara haske da wani irin kyau kamar wanda yake cikin kwanciyar hankali, ramar dayayi ne kaɗai zai tabbatar maka da halin da yake ciki.

"Habibi!" yaji an faɗa da ƙarfi

Ɗagowa yayi yana kallon Maami with suprise Dan baisan zatazo ba, Abbu da ya gani a kusa da Maami sai ya sake basa mamaki, amma sai baice komai ba, ya mayar da kansa wasu hawaye na taruwa a idanunsa.

Da sauri Maami ta yasar da jakanta, tana ƙarasowa gabansa, ɗago fuskarsa tayi

"Habibi talk to me, miye duka hakan?, Taufeeƙ ya kira mu yace muzo bakada lafiya me ya sameka, kaga yanda ka rame kuwa rabin raina?, meyasa bazaka faɗa wa Maami ba?."

Kasa cewa komai yayi, kawai dai ya rungume ta sosai yana sauƙe ajiyar zuciya.

A hankali ya buɗe bakinsa daya ƙafe yana faɗin

"Maami Noor ta tafi ta barni, Maami bansan ta ina zan fara nemanta ba, Maami where can I find Noor?, I need to apologise, idan wani abu ya sameta bazan yafewa kaina ba.

Shafa kansa tayi tana faɗin

"Habibi calm down, Taufeeƙ ya faɗa min komai, zamu sameta da izinin Ubangiji, ka kwantar da hankalinka."

cigaba tayi da shafa kansa, har taji sauƙar numfashinsa alamun bacci ya ɗauke sa, a hankali ta gyara masa kwanciyarsa a kan gadon.


Hannunta ta sa a cikin na Abbu dake miƙa mata hannunsa.

A hankali ya miƙar da ita suka fice a ɗakin, suka nufi ɗakin Maami, sai da suka isa ɗakin kafin Maami ta fashe da kuka


"Abbu ka ga Habibina kuwa?, meyasa Noor ta tafi tanar min yarona a haka?, kashe min shi takeso tayi ne?.

Ta faɗa tana sake fashewa da kuka.

rungumeta Abbu yayi yana shafa kanta, karki damu Hilwa, Zannur will be alright, kuma za'a sami yarinyar, ki kwantar da hankalinki Please."

Haka Abbu yayi ta rarrashin Maami, har sai da yaga ta samu nutsuwa kafin shima nashi hankalin ya kwanta.


************

Khamal ne ya shigo gidan yauma da saurinsa, da jarida a hannunsa, tun daga tsakar gida yake ƙwala kiran

"Noor! Noor! Ina kike?

A tare suka fito da umma, jin kiran yaƙi ƙarewa

"Khamal lafiyanka?"

Umma ta tambaya tana kallonsa.

"Umma bayan mijin Noor da ke nemanta, yau kuma wani ne yake nemanta, wanda yake ikirarin shi mahaifinta ne, gashinan dai hotonta ne ɓaro ɓaro akan jaridar, sannan yasa kuɗi mai tsoka ga duk wanda ya san koda labarinta ne."

Ya karashe zancen yana mikawa umma hoton.

A hankali Noor ta jawo ƙafar ta ta ƙara so gaban Umma, hannu ta saka ta amshi jaridan tana kallo sai kuma tayi wani murmushi tana tafa hannunta

"Kai a tunaninka kana da wayo ko?, umma ba fa mahaifina bane, Zannur ne zai raina min wayo, shine kaɗai yake da wannan hoton, shine ya ɗaukeni, ta yaya za'a yi mahaifina da koni kaina bansansaba zai samu wannan hoton, a tunaninsa idan yace mahaifina zan dawo ne hmmm."

sai kuma ta ajiye jaridar ta yi wucewarta ɗaki

Daga khamal har umma da kallo kawai suka bita, kafin khamal yace,

"Ummah kina ganin a barta kawai?, a gaskiya Nikam zan kira numbar da aka saka dan nemanta, in sanar dasu inda take, idan ma mijinnata ne gwara yazo a sasanta komai ta koma gidanta ko ya kuka ce."


"To khamal me zance maka, ka dai jira Malam ya dawo muji ta bakinsa koh?"

Bai sake cewa komai ba ya juya ya bar gidan.




Maimoon#

*💖ABNUR💖*


*By Maimoon*


*Elegant online writers* 📚📖


*Page 20*



Kamar yadda Umma tace kuwa, Baba na dawowa, khamal ya zo ya samesa da maganan

"Khamal gaskiya kayi tunani mai kyau, amma kaɗan jira kaɗan,yarinyar tana cikin damuwa, kuma nima ina tunanin mijin nata ne yace mahaifinta, dan yasan zata so haɗuwa da mahaifinta."

"Shikenan Baba, babu damuwa, duk sanda kuka ga ya dace a sanar da su, sai a sanar dasu."

"Yauwa khamal Allah yayi maka albarka."

"Ameen Baba" daga haka yayi ma Baba sallama ya bar ɗakin.


**********

"Abdul kaji yadda mukayi da Baba, Amma gaskiya ya kamata ta koma ga mijin ta, bana tunanin zamanta anan shi yafi"
khamal ya faɗa yana kallon Abdul da ke zaune a gefensa ya zuba masa ido.


Gyara zama Abdul yayi kafin yace

"to kai miye damuwarka ne, tunda ba akanka take ba, ka barta mana ai zasu maidata koh?"

"Bazaka gane ba, ni nafiso ta koma kawai, nima kaina bansan meyasa ba, ina mata kallon ƙanwata na jini, kuma ai kaga zanso ta zauna a gidan mijinta, kuma idan ka duba yarintace kawai yasa ta baro gida, idan ba haka ba ai alkhairinsa yafi cutarwarsa yawa a gareta."


"Hakane kam to mai zai hana kawai idan mun shiga cikin gari anjima, mu nemi waya mu kira kawai mu sanar da shi mahaifinnata, idan ma mijinnata ne ke ƙaryar mahaifinta, duk dai mu sanar musu, kaga da kansu zasu zo har nan su dauke ta, sai kace ba ka san ta yaya suka sani ba, ko ya ka gani."


Shiru khamal yayi kamar mai tunani, sai kuma yace

"kana ganin babu wata matsala?"

"Kaji ka da wani zance, ai taimakonta kake son yi ba cutar da ita ba."


"Shikenan to, Allah ya kaimu, sai muje mu kira ɗin."

"Yauwa abokina, Allah ai yaga nufinka"


Daga haka suka miƙe suka jera suna cigaba da tattauna maganan.



*_Kaduna Nigeria___*_

Papi ne a zaune a falonsa, ya ƙura ma hoton Noor idanu, yayi zaton abin zai zo masa da sauƙi wajen neman Noor, Amma yanzu ya gane aiki ne babba a gabansa idan har yana so ya gana da ƴarsa.


Miƙewa yayi da hoton, ya nufi ɗakin zane zanensa, a hankali ya zauna a kan kujerar zanen, ya shiga zana Noor, idanunsa na kawo ruwa, Fatima kaɗai yake tunawa, ta rasu ba tare da taji uzurinsa ta yafe masa ba.

Wayar sa dake gefensa ce tayi ƙara, a hankali ya juya ya kalli screen ɗin ganin babu suna ya sashi cigaba da zannen,
wani kiranne ya sake shigowa, a hankali ya kai hannu ya ɗaga yana faɗin
"Assalamu alaikum"

Mai shagon kiran jin an amsa ya mikawa khamal wayan yana faɗin
"gashi kayi magana"

Karɓa khamal yayi a nutse yana kallon Abdul dake gefensa yana gyaɗa masa kai alamun ya faɗa kar yaji komai.

Cikin sanyin murya ya amsa sallaman sannan ya ɗaura da faɗin

"Ina wuni?", ba tare da ya jira amsa ba ya cigaba

"sunana khamal, kai ne kake neman ƴarka data ɓata?"

A zabure papi ya miƙe yana faɗin

"Ni ne!, eh Ni ne, ka ganta ne?, ka san inda take?, faɗa min a ina take please zanzo yanzu"

"Uhm..eh Noor tana wajenmu, kuma yanzu haka mu muna Kano ne, a wani ƙauye mai suna Marke, Noor tana tare da mu a can"

"Alhamdulillah, Alhamdulillah ya Allah, pleaaaaase ka min wannan taimakon, kar ka bari ta bar inda kake, zan nemi Flight zuwa Kano yanzu, Please ku jirani."

Shiru khamal yayi kafin yace

"ranka ya daɗe ka bari zuwa gobe mana, idan ya so sai mu zo mu jiraka, ta yanda zamu iya yin waya da kai, dan wayar ba namu bane, na wani ne muka ara."

"Kar ku damu, dan Allah ku jira Ni zanzo bazan iya kai gobe banga Noor ba", ya faɗa yana fitowa da sauri daga ɗakinsa cikin sassarfa.


"To yallaɓai zamu gwada jiranka sai kazo."


Abdul da ke kallonsa bayan ya kashe wayar, yace

"wai jiransa zamuyi?"

"Haka dai yace"


"Tabb, ko da yake ba zai fi awa ɗaya ba zuwa da rabi, sai mu nemi waje mu zauna, sai kace wani abin yaƙi ya bari gobe mana."


"Nima haka nace amma yace kawai mu jira sa."



Papi na kashe wayan ya fito da sassarfa, Farhaana da Ammi dake falon ƙasa, suka miƙe suna kallonsa.

ganin yana shirin fita a falon yasa Ammi faɗin

"Ina zakaje haka?, ina fatan lafiya!"

Batare da ya juyo ba yaje,

"na samu ƴata, zanje in zo da ita."

Bai jira amsar su ba ya fice a gidan, ko driver bai nema ba yayi driving kansa zuwa airport, bai wani ɓata lokaci ba ya gama duk abinda zai buƙata, jirgi ya tashi da shi zuwa Kano.


A cikin awa daya jirgi ya sauƙa a Kano.

Layin da suka kirasa da shi yayi ta kira amma ba'a ɗauka, rasa yanda zaiyi yayi, idanunsa har sun kaɗa,

Sake dialling yayi a karo na bakwai, kafin mutumin wanda dama su khamal sun sanar dashi ko da an kira basa nan, ya kirasu dan babu wajen zama a wajen, ya ɗaga yana faɗin

"ranka ya daɗe sunje suci abinci"

da sauri papi ya ce,

"dan Allah a ina kuke, zanzo yanzu na samesu a nan"


"To babu damuwa bari na maka kwatance."

Da ƙyar papi ya samu ya isa inda suke masa bayani, dan ma mai motan da yayi shata ba inda bai sani ba a garin Kano.


Motan na parking yayi saurin fitowa, da sauri mai shagon yace

"ranka ya daɗe kai ne muke waya da kai?"

"Eh nine Ina khamal din yake? wanda ya kira Ni ɗazu"


"Eh suna zuwa ai, ina ganin bayan sunci abincin sun tsaya Sallah ne."

Bai rufe bakinsa ba sai ga khamal da Abdul suna tahowa.


"Yauwa gasu can ma, sune suka kiraka."

Ya faɗa yana nuna su khamal.

Suma tun daga nesa suka kallonsa,

"Tabbass wannan shine mahaifin Noor, ko kokonto banayi"

khamal ya faɗa yana dafa Abdul

"To mu ƙarasa mana"


Sai da sukayi musabaha, kafin yace

"wayene khamal wanda ya kirani yace min yasan inda Noor ɗina take a cikinku?"

Da sauri Abdul ya nuna khamal yana faɗin

"ai a gidan su noor ɗin take."

Rungume sa papi yayi, ba tare da tunanin komai ba,

"Nagode khamal, dan Allah ka kaini wajen ƴata yanzu ina so in ganta."



"Babu damuwa yanzu zan kaika, zakaga ƴarka insha Allahu" kamal ya faɗa yana ɗagowa daga jikin papi.


Sai da suka ma mai shago godiya kafin papi ya basa kuɗi masu yawa, ai kuwa ya zube yana ta godiya.


A motar da papi ya zo da ita suka nufi cikin ƙauyen, kasancewar mota kan shiga yasa har ƙofar gidan su khamal suka zo.


Sai lokacin khamal yayi tunanin, me su Umma zasuce masa?, amma sai ya share ko ma me zasu ce, shi ya haɗa ƴa da mahaifine.


Noor da ke tsakar gida tana kwasan shanya, taji zuciyarta ta buga da ƙarfi,
da sauri ta dafe ƙirjinta tana faɗin

"inna lillahi wa inna ilaihi raji'un"

"Lafiya Noor"

Umma ta faɗa daga zaunen da take a tsakar gida tana kallonta.

"Zuciyata ce ta tsinke Umma, babu komai"

daga nan ta cigaba da
Abinda takeyi.

Baba da ya fito daga ɗakin Umma yana shirin fita, sai ga khamal ya shigo jiki a sanyaye.

Sunkuyar da kansa yayi kafin yace

"Baba mun yi baƙo yana neman izinin shigowa"

Da mamakin duk suke kallon sa kafin, Baba yace
"wayene?"

Khamal bai amsa ba hakan yasa Baba faɗin

"kace masa ya ƙaraso, tunda kai ka kasa faɗan wayene."

Sai kuma ya juya ga Noor Yana faɗin

"Noor ɗauko wani tabarmar a shinfiɗa masa."


"To Baba" ta faɗa tana sake jin yadda zuciyarta ke bugawa.

Sallamar da taji ya sata saurin ɗagowa dan taji ta kwaɗaitu da ganin mai sallaman.

Cikin idon mahaifinta idanunta suka faɗa, da sauri ta dafe ƙirjinta tana kallonsa babu ko ƙiftawa.

Shikam hawayen idanunsa ne suka kasa tsayuwa, suka shiga

Please Login or Register in order to submit comment