Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da su. Su malam Abdullahi da ummey ƙwarai sunyi farin ciki matuƙa da wannan Sa'ar da ƴar su ta samu.


Bayan kwanaki biyar suka lula cennnn ƙasa mai tsarki, saida suka ƙwana suka huta sannan washe gari suka fara gudanar da taron nasu komai cikin larabci sukeyinsa wata balerabiya Anum dawood aka fara ƙira tafito cikin shiga ta alfarma ta kamilallun bayin Allah tafara raira karatun ta. Cikin zazzaƙar muryarta, Ana datso mata tambayi Cikin tsaƙiyar, al'QUR'AN mai girma tana kuwa cafewa tana bayar da amsar su daidai,lalle wannan baiwar Allah da baiwa take.





Alhamdulillah muhaɗu'a fejin gaba
Wllh ina ɗan wani uzirine ammafa kuyi haƙuri fejin gaba in Sha Allah zaku samu mai tsayi


By ammeyn laylah 🫶🏻*🔥❤️ KAREN BANA❤️🔥*


NA MARYAM NASEER MIRRAH ✨
*Ammey laylah 🫶🏻*


FREE BOOK
Page 🔟



081-04-49-32-15


*Alhamdulillah forever and always*



*IDAN KASAMI DUNIYA'A HANNUNKA TOKA BITA'ASANNU DOMIN ITAƊIN BA MATABBATA BACE*
*RAYUWA CE WATA RANA SAI LABARI*

*SHINE RAYUWATA KUMA DUNIYA TA❤️👌🏻🫂*

*MARYAM NASEER MIRRAH ✨ GARKUWAR MUSULUNCI💪🏻*



_________Haka akaci gaba da ƙiran bayin Allah ɗaya bayan ɗaya har akazo kan *MARYAM ABDULLAHI RANO* sanye take cikin Baƙar abaya kimuno da dogon hijjabin ta har ƙasa ruwan sararin samaniya, a hankali tafara takowa cikin abinda aka tanada domin masu karatun!
cikin nutsuwa take takawa tamkar wacce batason taka ƙasar wata irin ginshira ce kwance saman kamilalliyar kyakkyawar fuskar nata.......gaba ɗaya idanuwan jama'ar gurin ne yayi mata caaaa aka ji takeyi kamar ta nutse kawai ta huta;

Gida nigeria kuwa duk wani wanda yake da alaƙa da waɗannan bayin Allah masu sauƙar hakimce suke bakin tv suna kallo, masu sauraran radio nayi



*MASARAUTAR ADAMA*
*****************

Gaba ɗaya
jama'ar masarautar kowanne ɓangare suna hakimce gaban maka makan plazma ɗinsu

Dalilin *SARKI ABDULPHATA OMAR*
bai samu halartar Wannan taron sauƙar AL'QUR'ANI ba bisa wani dalilin daya riƙe shi........ *HAJIYA MARYAM*Da mai martaba sarki *ABDULPHATA OMAR* ne zaune gabansu sun zubawa plazma ɗin ɗakin nasu idanu tun farkon fara sauƙar suke gaban tv suna kallon komai har akazo kan wannan baiwar Allah.....Anum dawood cike da burgewa suke kallonta

A daidai loƙacin da aka ƙira sunan baiwar Allah *MARYAM ABDULLAHI RANO* atare zuciyoyin na mutum biyu suka buga' Alaƙaci ɗaya..


Cikin tarin nutsuwar ta taci gaba da takawa har zuwa kan ƙawataccen gurin karatun nasu!
cikin girmamawa ta amshi abin karatun haɗi da ɗage likaf ɗin nata!.... ƙyaƙyƙyawar fuskarta wanda wani irin annuri, da haiba, yake kwance saman cute face nata ya baiyana' jama'ar wajen da yawansu kasa haɗa ido suka yi da ita sakamon wani kwarjini dayayi ma fuskar nata ƙawanya ga ɗan wani irin ruwa-ruwa da ƙwayar id0n nata suka fara tarawa sanyi takeji sosae 'A jinin jikin ta
Ahaka ta gabatar da sallama!
ta gaida mutanen duk cikin harshen larabci,
fara rairo karatunta tayi cikin zazzaƙar muryarta da kuma ƙyaƙyƙyawar ƙira'arta cikin *SURATUL KHAFIH* saida taje wajajen tsakiyar kana aka gimtse ta....

Aka shiga kutso bata tambayoyi cikin juya ƙwaƙwalwar mutum da tunanin sa!!!


Amma Allah cikin ikon sa da buwarsa ta ringa bada amsoshin duk da aka ringa mata hadisai ne, sira ne, fiqhu ne, bulugul maram ne, tauhid ne, balaga ne, da dai sauran littattafan mu na addinin Islama haka aka ci gaba ta zakulo mata tambayoyi tana lashe su


Su ummey da malam Abdullahi! Dake gaban ƴar ƙaramar tv ster nasu suna kallon komai jikinsu duk yafara sanyi ganin irin tambayoyin da ake watsowa shalelen ƴar tasu



Anan cikin Masarauta kuwa 'A daidai loƙacin da aka bukaci fitar MARYAM ABDULLAHI RANO da loƙacin da ta , fito tafara tafiya suka ƙurewa tafiyar nata kallo da kuma loƙacin da ta cire likabin fuskar ta da maganar da,
tafara cikin ginshira da tarin nutsuwar nan nata mutane biyun nan suke kallon ta kurrrr
Kafin daga bisani Hajiya Maryam ta zube sumammiya ko motsi bata ƙara yiba shi kuwa mai martaba sarki Abdulphata omar duk yanayin jikin shi yaji yana sauyawa ka kuma ana cikin hakan amarya tashi ta zube 'A jikinsa summammiya



Saida kowacce ƙasa suka gabatar ta saukar tasu ne bayan sallar la'asar dab da magrib taron nasu ya tashi!...... Kana bayan sunyi sallar magrib aka kuma buƙatar ganin su!
Susu hudu

Anum dawood madinah

MARYAM ABDULLAHI RANO kano

Khadija habeeb niger

Zainab qasim Jigawa


Liyafa ta musamman aka shirya musu cikin babban masallacin birnin madinatul munaiwara



"Khadeeja Habeeb itace tazo ta hudu"

"Zainab qasim Jigawa ta uku

Anum dawood ta biyu


*MARYAM ABDULLAHI RANO*, Kano


Itace wacce ta lashe wannan gasar domin su, sauran dukka ,ana musu gyara ko waccensu anci gyaranta!!!

Da wani irin maɗaukakin mamaki farin ciki gaba ɗaya duk wani ahlin ɗan Nigeria murna sukeyi gani suke kamar ba gaskeba; malam isyaku el-yakub kuwa ji yake tamkar ya goya *JADDAH*, A gadan bayansa yayi ta juyi da ita tsabar farin cikin daya gama kewashi,



Ummey kuwa sujjadar godiya ma Allah tayi, domin shiya dubesu da idon rahama yaji ƙansu har ya zaɓi jaddansu ' matsayin wannan fitacciyar baiwa tasa kana kuma kaɗaitacciya,wa al'ummar *MANZON ALLAH {S, A ,W,}*


Wani irin zubewa da tayi ƙasa ne tana fashewa da wani irin kukan da bata san ko daga inda yake bane ya kwace mata kukan farin ciki, kukan daɗi, kukan komi ma kammmm Ita dai tayi! Daƙar Anum dawood ya ƙari sa gurin ta cikin harshen arabi take lallashinta ta ɗaura kan jaddan saman cinyar ta tana ɗan bubbuga bayanta, numfashin tane yafara sauƙa ahankali hakan, ya tabbatar wa anum dawood cewar baccine ya ɗauke ta a gurin ! Washe gari misalin ƙarfe sha ɗaya na safe aka kuma ɗibansu zuwa Makka domin kaiwa ziyarce ziyarce guraren tarihi da kuma ƙara ƙarfafawa MUSULUNCI baya




Bayan sati guda su jadda sun dawo, da tarin abun arziƙan dasu ka samo jadda ta tashi da, kyauta mai tsoka wacca ta girgiza zukatan su ummey da malam domin kuwa, iya tsagwaron zunzurutun kudi ma ta tashi da Naira biliyan biyar da kujerar maka, da keken ɗinki, da dukkan wasu littattafa dasuka shafi addinin Musulunci ambata



ADAMAWA
*************

Bayan kwanaki uku Hajiya MARYAM yisham ta farfaɗo amma fa da wani suna da: dake ta ambato ƙira take kukawomin *AYUSH* ɗina wallahi itace naji '
A jinin dake yawo 'a jinin jikina tabbas wannan ƴata ce ƴatace ƴata ce *AYUSH* wallahi bana ƙara yadda ' akuma cutatamin akan shafin rayuwana;..... Ruwan dake jikin tane ta fusge ta ɗiro daga, gadon asibitin cikin Masarautar!!!
Tafiya ta fara taku ɗaya biyu kana ta! Dakata tana faɗin jibi kalli tafiyar ta irin tawa sak! Sannan dubi tsarin kamanninta, da namu wallahi dukka abu ɗaya ne ya yimu dama ' inaji 'a jinin jikina Ayush ɗina bata mutu ba!
To inta mutu ina gawar ta!?

Ku ɗakko ku nunamin nasan dai wannan ba irin mafarkin dana saba yi bane, dama tana cemin Habibtee Ummu Naaa nakusa baiyana a gabanki!
Nasan *AYUSH* ɗina ba zata,taɓa saɓamin alƙawari naba kamar yadda mai sunan bata taɓa saɓa alƙawarin ita ma!!!!!



Mai martaba sarki Abdulphata omar, ne da ummu Abdulphata da uwar gidan sarki Abdulphata ɗin ne ƙewaye da gimbiya maryam kowa ido ya zuba mata
Suna kallon ta babu, wanda yayi yunƙurin hanata dukkan abin nan da takeyi....... Domin sun san da ciyo
Mutuwar ɗa ɗan ma kuma ace ko gawar sama ko ƙasa annemeta an rasa 'a cikin asbitin masarautar







*Muje zuwa yanzun aka soma*

*Wannan ɗin ba komai bane somin taɓine kawai*

*Dukkan wata cakwalkwalin cakwakiya tana gaba*

Kudai biyu

*MARYAM NASEER MIRRAH ✨ GARKUWAR MUSULUNCI*

*Abaya domin jin yacce al'amuran zasu kaya*



*Shin wacece wannan mata mai ikirarin *AYUSH* *
*ƴarta bata mutu ba?*

*Shin tayaya uwa ta haifi ɗa acikin cikin ta amma ace mata yarasu bayan ko ganin jinjiran bata samu gani ba?*

*Mudai je zuwa yanzu aka fara wasan*



*Karku mance fa ga Kashim baba dumu sumu hannun maleek taufiq*


*Bayan kuma shine da al'haƙin wannan case na kashin baban?*


*Shin wannan wanda irin al'mun dahana su kashim baba da abokansa suke kullawa akan bayin Allah da basuji ba basu gani ba?*


*Meyasa Ammey bata ƙaunar aikin sojan shalelen yaron nata?*



*By ammeyn laylah 🫶🏻*



*Wannan FEJIN SADAUKARWA ne ga yaa yaa SAPWAN AHMED🙏🏻❤️🫵🏻*🔥❤️ KAREN BANA ❤️🔥*



NA MARYAM NASEER MIRRAH ✨
*Ammey laylah 🫶🏻*



FREE BOOK
Page 1️⃣1️⃣


081-04-49-32-15



*Alhamdulillah forever and always*





--------Saida tayi mai isarta kana kuma Ummu Abdulphata tariƙe ta aka mata allurar bacci...... sannan aka buƙaci da kowa yabaje abarta ta huta da ƙar aka ɓanɓare lawiza autar ta a jikin ta tana ta kuka ita habibtee ɗin ta takeso



****Zaune yake cikin babban Ofishin nasa! system ce agaban sa yana ta latse latsen sa yashiga nan yafita cennn ahaka dai yasamu ya kammala aikin nasa saida yana ƙayataccen murmushin nan nasa!!!
Dam kuma gaban sa ya buga loƙacin daya tuna da trouble maker ɗinsa; Idan harba gizo idanunsa sukayi masa ba kamar itace yagani,
A television yayin taron haziƙan mahaddata QUR'ANIN nan! Saurin katse tunanin yayi ganin kanshi ya naiman fara masa ciwo
Yarasa maiyasa sammmm idan lissafi yashigo da mata sammmm baya ƙaunar abin baya ƙaunar yaji ana zancen abinda ya danganci matan! Sau tari yakan tambashi kanshi Allah kuwa lafiyar lau kuwa idan kuma yaduba yanayinsa da yadda yake saiya cire tunanin komai, to dai koma miye yana rokon mahaliccin sa ya sassauta mashi wannan abu; ajiyar numfashi yayi tare da miƙewa tsaye yana nufar bakin window ɗin ɗakin nasa wanda gaba ɗaya glasses ne ' a wurin!!

El-basheer yaƙub yagani shida wani mutumi dattijo kuma saiyaga kamar yataɓa ganin mutumin, gani yayi el-basheer ɗin na leke-leke alamun rashin gaskiya atare dashi....kafin kuma cikin sauri yaga! Ya zaro abu daga cikin aljihun gaban rigarsa ya miƙawa mutumin da, baigama tabbatar da ko waye ba
Cikin sauri dukka ninsu kowa yakama hanyar sa shi yafita, shi kuma el-basheer yaƙub yadawo cikin harabar wajen sojojin numfashi yaka yana barin wajen shima


Hajiya aysha galadima mace, zaune a babban falon gidan nasu ita da autar ta ummitah, wacce tayi matashin kai da cinyarta tana mata tsifa......Hajiya Lubna ce ta shigo ɓangaren na ammwyn maleek da sallama' amsata ammey tayi da murmushi a saman fuskarta, Hajiya kece yau 'a falon inata faɗin tunda kimdawo zanshigo, tun jiyan, allah kuma baiyi ba, gashi yauɗin kuma, wannan ƴar rigimar ta, tasani gaba wai dole saina mata tsifa! "Babu komai ai aysha ykk ya gidan ya fama da ayyuka"
"Alhamdulillah wallahi Hajiya ya London ɗin fatan anbarosu lafiya, kai amma kinsha London" cewar Ammey
Wallahi kuwa ba laifi ina yarona; dan nikam shina biyo banga shiba dake surprise naso yimuku baki ɗayanku! "Yana wurin aiki yace ma yau ba zama zaiyi ba wani ɗan aike ne kaɗai zaiyi ya dawo" kinga nima na huta da wannan sangartar nashi kuje cennnn abinku , nasamu na huta nimah! dukka ammey ce mai wannan maganar

Murmushi Hajiya Lubna tayi tana faɗin shikenan bara yarona ya dawo tunda haka kikace duk loƙacin da zanyi tafiya sai ina tafiya da yarona

Dama kuwa hakan kukeyi zaifi cewar Ammey


Shikenan bara na koma ciki saiya dawo tafaɗi hakan tana miƙewa tsaye tana nufar bakin ƙofar bayan tamiƙa ummitah wata ƙatuwar leda

Haba hajiya kullum baƙya gajiya ne kammm da abin arziƙi

Karna kuma jin hakan idan har ba raina min kikayi ba dannayi muku abu saiya zama laifi *AYSHA*



"To shikenan ubangiji Allah yabar ƙauna ta har abada mungode sosae Hajiya Lubna!"


Wani ɗan sukari Hajiya Lubna taji 'a can cikin kirjinta!
Tana shirin! Fita ne shi kuma yaron nata' ya sawo kai cikin falon da wani irin sauri ya zubar da kayan da yake rike a hannunsa ya rugo ya zuwa wurin

"Oyoyo Mommah taa oyoyo Mommah Naaaaa"
Yana ƙara so wa kuwa yakama hannuwanta ya cukuwkuye

*My son* momman nashi ta faɗa tana cirashi daga cukuwkuye hannuwan nata da yayi

Anan yabar dukkan kayayyakin nasa, na Office ammeyn shi dake ganin komai ce ta share kwallar farin ciki dajin nutsuwar dawowar momman nashi ta nufo wurin ta ɗebe mishi kayayyakin da ya zubar ɗin ta 'adana mishi 'a gurinta



Hajiya Lubna kai tsaye ɓangaren ta suka nufa suma suna tafe suna fira abinsu kaida ganinsu kasan akwai shakuw, mai girman gaske' a tattare dasu.......Hajiya talatu Turai dake fitowa daga cikin motar tane tabisu da kallo tanajin zuciyar ta kamar ta soye itafa ta tsani ' ahalin aysha haka kawai bata ƙaunar ganinsu, sunzo daidai inda take zaune cikin motar natane; yasata saurin,fitowa daga motar,
gaidata maleek yayi 'a matsayinta na matar mahaifinsa, wata kafurar harara data watsa musu ne duk su biyun yasa shi ɗauke kansa daga kallon ta! dan wallahi shifa badan tanacin darajar auren mahaifinsa dake kanta, da tuni yaka lahanta dukkan wani abu mamori a sassan jikinta!!!


Haka aka iya haka kuma za'a kare banza mai juya tunanin marar tunani wallahi kiji tsoron Allah mutuwa dai na nan kuma 'akwai makoma...


Ko ta kanta basu kuma biba suka wuce abinsu



Ita kuwa hajiya talatu turai mai makon ta wuce, nata ɓangaren sai kawai tayi ɓangaren hajiya aysha galadima ammey..... Baiwar Allah tana nan zaune inda take burun babu sallama, taji anturo ƙofar falon nata,

To munafika matsoraciya kuna zaune ana juya tunanin ku yadda akeso sai yadda akayi daku, kina nan zaune ' a doran duniya da ranki da lafiyarki anyi miki kwacen yaronki da ƙarfin tsiya, kina ganin kamar ƙauna ce hakan
Anbi dare, anbi rana, anyi komai domin asamu komai
Fuuuuuuuuu ta fuce daga falon hajiya ayshan

Ita kuwa Ammey dariya kawai tayi domin indai tujarar hajiya talatu ce aita riga da tasaba da ita nayau ma ai kaɗan tayi mata



Fusace da sarewa irinta mantan sarakan nan keta faman tashi tun asuba shi ' a cikin babbar harabar masarautar sakamakon babban ɗan sarki Abdulphata Omar dayake dawowa yau daga ƙasar waje...

Ɓangaren uwar gidan sarki Abdulphata Omar duk tafi ɗaukar jama'a dan kuwa cike yake makil da manyan bakin ta tare da ƙawaye ƴan duniya! Wata ƙwarya ƙwaryar liyafa ta haɗawa babban yaron nata suffyan Abdulphata Omar domin tayashi murnar kamma karatun sa lafiya 'a ƙasa mai tsarki

Sai cennn wajajen yamma,jirgin nasu ya sauka,motocin masarauta ne sukaje ɗauko shi

Saidai akayi sallar la'asari gaba ɗaya kantafanin harabar masarautar tacika da ƴaƴan sarki, da matansa, da jikokinsa, sai kuma mutanen arziƙi

Gimbiya maryam dake zaune ta tsume cikin wani ƙayataccen ɗanyan farin leshi ce ta saki murmushin farin ciki da murnar dawowar na hannun daman ta suffyan Abdulphata Omar ɗa ga abokiyar zaman
Gimbiya laurah ishaq adam
Wacce suke zaman mutumci da amana

Shi kuwa suffyan kai tsaye wajen Little momman shi yanufa yana zuwa babu wata wata ya faɗa jikinta, cikin rawar jiki sai kuma ya fashe da kuka yana faɗin wallahi little mommah naga wata mai kama dake kuma naji, ajinin jikina wallahi' ƴar uwaa taa cee mommah






Muje zuwa


*By ammeyn laylah 🫶🏻***🔥❤️ KAREN BANA ❤️🔥*


NA MARYAM NASEER MIRRAH ✨
*Ammey laylah 🫶🏻*


FREE BOOK
Page 1️⃣2️⃣



081-04-49-32-15



*Kusanyamin ita acikin adda'arku masoya tana da bukatan hakan Maman Dee__ Ƴar gaban goshin🥰*





_______S0sai little momman nashi ta ƙara riƙe shi jin jikinsa gaba ɗaya rawa yake yi, ka dagata my friend! Zamuyi maganan zuwa anjima kaga wurin nan duk sabo da kai ne muka taru anan wajen.... Hajiya laura ƙuwa idan ranta yayi dubu toya ɓaci ganin ɗan cikinta gudan jinin ta wanda ta ɗauki cikin sa tsawon wata goma da ƴan kwanaki, bai nufo inda take ba yau kimanin shekaru ɗaɗɗai har biyar basa tare....... Amma mai makon yazo gareta sai kawai yanufi kishiyarta; wannan wacce iriyar musiba ceee haka??


"Kaje wurin mum naka friend kafin nan muyi maganar" ...tafaɗa tana sakin masa murmushi, kai kawai ya iya ɗaga mata,. Kafin yanufi wurin mum nashi cikin sassarfa yana zuwa itama yazube jikin ta yana zagaye ta, da hannayensa sai kuma hawaye sharrrrrrr.... Hannuwanta tasa tana share mashi hawayen kana, takama hannunsa tana nufar wurin da aka tanada domin shi, ba laifi yasake sosae anyi waliman lafiya kafin kowa ya watse yakama gaban sa


Zuhriyya ce ta kama hannunsa tana ta zuba mishi surutu, shidai jinta kawai yakeyi domin kanshi harya fara juyawa da wannan ƴar hayaniyar da aka tara mishi' acewar sa kenan,kai tsaye ɓangaren mai martaba sarki Abdulphata yanufa! bayan sunga ganawa da mahaifin nashi yanufi ɓangaren sa kai tsaye 'A gurguje yashiga wanka ya kimtsa yasamu ya gabatar da salloli biyun da aka biyoshi, kwanciyar sa yayi hankali kwance bayan yage ɓangaren mahaifiyar sa da ɓangaren little momman shi!¡



Cikin muguwar zabura haɗi da kiɗima *JADDAH* take duba ko wanne gefe da gefenta, ganin babu komi ne yasata jan numfashi,, sai yaushe ne zata daina mafarki da wannan baiwar Allah mai zuwammata cikin famarkin ta kullum tana mata kuka haɗi da roƙon ta dawo gareta, Adda'o'i tayi kamar yadda ta saba kafin ta duba agogon dake jingine a ɗakin nata ƙarfe biyun dare da rabi ya nuna mata, ahankali ta fita tsakar gidan nasu bayi tashiga ta fito alwula ta ɗaura ta koma ɗakin nata salloli tafarayi ahaka, har taji ana ƙiran subashi! bayan tayi sallar subshi taci gaba da zama nan kan daddumar nata tana rokon Allah yashiga cikin wannan lamari na matar da take yawon mafarki da ita kullum cikin kuka

Hajiya talatu nera ce zaune gaban alhaji taufiq tayi irin zaman nan na tankwoshe kafafu, cikin faɗa faɗa take jaddada wa alhaji abinda yake wakana dan anga tafita anziga maleek yakama husna yamata dukan mutuwa dan haka yashiga tsakanin su, ai dama bayau aka fara mata haka ba 'a cikin gidan kawai dai haƙuri takeyi, to ita yau haƙurinta yaƙare dan haka aima tufkar hanci....... kallon ta kawai alhaji taufiq yake bayan ta gama koromai baya nan taa!¡!

"kina s0n kenan na hana maleek tsawatar da ƙannen shi dan sunyi ba daidai? Bayan kinsan haka kawai dan jin daɗi bazai kama yaranki da duka baaaa"!!!

A fusace ta miƙe dama na sani bazaka taɓa iya tsawatar mishi ba tunda tsoran shi kakeji ni da kaina zan ɗaukarwa kaina matakin daya gabata




KANO
*******

Duk suna zaune ne a ƙarƙashin bishiyar mangoron gidan nasu wani yaro ya shigo da sallama, wai ana magana da malam Abdullahi, cikin rawan jikin dashi kanshi baisan na miye ba yamiƙe zubur, yana bin bayan yaron....da fitar shi ƙofar gidan yaci karo da wasu manyan dattajai su biyu hannu suka miƙa mishi musaba sukayi kana suka, suka bashi wata farar ta karda inji sarki maleek ibn suffyan yana da buƙatar ganin sa ' a fada nan da gobe in Allah yakaimu da to ya amsasu; yana son ƙaƙalo miye haɗinsa da fadar Kano



___Zaune yake gaban abbeyn nashi gaba ɗaya yagama bada dukka hankulansa gareshi!
Kana jina ko abdulmaleek? Da sauri ya ɗago jin sunan da abbeyn nashi,yaƙira shi dashi kai tsaye domin da wuya kaji yaƙirashi da hakan saboda yana girmama sunan mahaifin matar shi aysha galadima ammey kenan:

"ehhhhhhhhh ina jinka abbey"


Dazune mai martaba sarki maleek ibn suffyan yaƙirani akan zamuyi wata magana! Bayan naje neee yake faɗa min zaman ka babu aure yayi yawa yau kana matsayin kimanin shekaru talatin da biyu amma ba mata kuma 'ahar kullum girman ƙara hawanka yake! dan haka dani dashi munyanke munzaɓa maka mata in Sha Allah tashi kaje nasanka da biyayya bazaka taɓa bani kunya ba dani da mahaifin mahaifiyarka;!


Tunda abbeyn nashi yafara wannan maganar yanemi jinshi ganinsa yarasa wata iriyar zuface take zubo mishi ako ta ina, duk kuwa da sanyin easyn dake falon!
Aure kuma shi, shin dama shi haryanzun bai wuce laƙacin auren bane taa yaa yaa maa , za'a masa haka?

To shi yace musa yana S0n auren ne ko kuwa sunga yaka sa riƙe kansa ne ko sunga alamar hakan ajikin sa ne bai sani ba?
Kai wannan tsoho da ganwa mutane magana yake amma ba komi zasu haɗu dashi neee


A baiyane kuwa kai kawai ya ɗaga abbeyn nashi yana barin falon gaba ɗaya


Bayan anyima malam Abdullahi iso babbar fadar sarki maleek ibn suffyan yakwashi gaisuwa ne
Yaji wani babban al'amari kamar daga sama kamar sauƙar aradu haka yaji maganar da soke shi

"Wata al'farma muke nema daga tsatson malam Abdullahi rano, idan har wani bai rugamu ba munas0n haɗa tsatso daga gareka, domin ina naiwama jikina kuma takwarana *MALEEK TAUFIQ* *AUREN* ƴarka *MARYAM*
Karka duba matsayin danake akai kafaɗi duk abinda yake zuciyarka malam, domin bazan taɓa S0n tauyewa wani ko musguna wa wani na ba ɗan ina akan matsayin danake da"


"Kai muke sauraro"


Cikin karayar zuciya da zuciyar sa dake S0n zugashi akan kada ya yarda da wannan haɗin shi *TALAKA NE* shi kuma mai *KUƊI* Amma ya ɗaure ya danni zuciyar sa cikin kamala yace Niiiii mahaifi ga MARYAM na bada *AUREN TA* ga jikan ka kamar yadda ka buƙata, ubangiji Allah ya sanya Alkhairi yasa ayi damu cikin aminci


Wata irin ƙima da ɗaraja sarki maleek yake kallon malam Abdullahi rano dashi cike da burgewa yake faɗin ameen ameen ya Rabbi ya sawati malam
Nan take yasa aka maida malam Abdullahi gidansa cike da girmama da kuma ƙwarin gwiwa



Shi kuwa maleek yana fita daga ɓangaren mahaifin nasa, nashi ɓangaren yanufa da wani irin ƙarfi ya tura kofar gidan nashi cikin azabar da bugun zuciyar dake S0n zautashi ya faɗa saman tattausan lafiyayyan gadon dafe da saitin zuciyar sa da yakejin tamkar zatayi bindiga ta fito *Innalillahi* yashiga mai mai tawa yanajin zafin zuciyar nashi yana raguwa cikin tuƙuƙin baƙin cike yake ayyana yadda zaiyi da duk yarinyar da tayi gangancin shigowa rayuwar shi ' a irin wannan loƙacin



Zaune yake gaban iyalan nashi harda yaya jamilu daya dawo daga wurin karatu jiya da dare...kallonsu yake ɗaya bayan ɗaya kafin kuma cikin jan numfashi yafara magana kamar haka

Farko ina mai s0n farawa da baku haƙuri bisa wani hukunci dana yanke ba tare da sanin iyalan nawa ba! Bayan zuwana fada 'a ɗazun mai martaba sarki yake mai neman wata al'farma daga gareni, tas0n haɗa iri dani,
Damm gaban kowanne su yashiga bugawa barin ma JADDAH baiwar Allah

Kana yaci gaba da faɗin anan yake faɗa min yana nemawa jikinsa *AUREN* ƴar wajena jaddah! Nikuma duba da kamalar mutumin da girman da yake da kana uwaa ubaa tattako da yake da
Nan take na amince masa ba tare da tunanin wani abu ba
Wannan loƙaci yayi daidai da loƙacin da jadda ta dafe zuciyarta idanun ta na S0n fidda wani ruwa-ruwa dake cikin su
Ummey ce dake ankare da ita, tayi saurin janyota jikin ta haba mar'atussa saliha haba uwar Muminai karki gaza mana kamar yadda nasanki da ƙwarin zuciya kiyima mahaifinki biyayya ta nan ne kaɗai zaki saka masa kinji *AUTAR MATA* kai kawai take kaɗawa ummeyn nata sai kuma ta ɗaga kanta tana , kallon ummeyn nata kana take tambayar ummeyn nata wai ta isa *AUREN KUMA* yaa yaa jamilu ne da tunda aka fara gudanar da jawabin baicw komai ba dangane da furucin na baban su yashi dungure kanta

Yana faɗin raguwa kawai bayan kina age na shakaru ashirin da ɗaya ma

Hararar wasa ta ɓalla masa tana tashi tabar musu falon....ɗakinta tawuce tana shiga ta fashe da kukan da kanta batasan kona miye shiba tana sake duban yadda take gani take yi kamar tayi *ƘANƘANTA DA AUREN*





*Kumuje da zuwa takuce ammeyn laylah ako da yaushe*



*Saimu haɗu a shafi na gaba*


*Wallahi idan banga ruwan comments naku ba tammmm zaku jima baku samu posting ba esheeeeeee nima na huta sosae yadda ya dace*


*By ammeyn laylah 🫶🏻💔**
*🔥❤️ KAREN BANA ❤️🔥*

MA MARYAM NASEER MIRRAH ✨
*Ammey laylah*


FREE BOOK
Page 1️⃣3️⃣


081-04-49-32-15


*Ina miƙa saƙ0n ta'aziyya ta ga ƴar uwaa Hadiza Tukur Maman Mama🙏🏻👏🏻 bisa rashi na maahifinta da tayi ubangiji yasa ya huta yasa Aljannah ce mako marsa🤲🏻🤲🏻*


*Godiya 👏🏻🙏🏻 marar adadi ga baiwar Allah bawan Allah dake turomin DATA kuma amma yane ɓoye kansa*

*Nasan dai ko waye, ko wace zata gani ubangiji ya biya da gidan Aljannatul fiddausi👏🏻👏🏻ngd*


______Ita fa gani take sammm bata isa AUREN ba inaaa ina tamayi ƙanƙanta gaskiya da wannan auren da akes0n ƙaƙaba mata
Kawai ma zataje tacewa ma da

Please Login or Register in order to submit comment