Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Aiki da ayyuka domin sadaukar da tasu Rayuwar wa rayuwar al'umma!!!, Shin mene za kuce game da waɗannan bayin Allahn?, Ku dai duba rayuwarsu! kudai duba irin sadaukar warsu gareku bayin Allah, MATARSA UWAR gidansa uwar ƴaƴan sa tsare a kotu, tare da..

Cikin wani irin zallar abinda ɓacin ran da ya daɗi bai shimfiɗama fuskar nasa ba, ya miƙe tsaye tare da fincike gaba ɗaya wayarin na plasma ɗin parlourn nashi, inda ammey take zaune ta kasa koda kwakkwaran motsine, cikin fusata ya fice a parlourn baki ɗaya yana barin gida baki ɗaya, kai tsaye tashar da yasan suna kan haska bayanan da GENERAL ABDULLAHI BELLO makama ya nufi.
***********
Da qarfi ya janye general abdu makama daga gaban abin haskawar, ya fara magana cikin ihu da qaraji.
"Kana tunanin abinda kayi shine zai sanya tarin alkhairinka juyewa zuwa gareni MAKAMA?, To tabbas indai ta haka ne ba zai taɓa karɓuwa ba! Ka taɓa ganin alkhairin wani ya juye zuwa wani? Ka taɓa ganin inda mai duka yake ma madaki sannu? Kamar haka ne" ya faɗi hakan yana haɗe hannayensa biyu, wata kwallar zallar tsagwaron Imanin daya kuma wanzuwa a zuciyarsa abdu makama ya share, tare da bin bayan generally TOUFIQ MAI NASARA daya kama hannunsa dan barin wurin baki ɗaya.
**********************
Gaba ɗaya mutane kuma sai jikkunansu sukayi sanyi qalau, vp ɗin take zaune a office nashi kuwa wani irin hawayene masu zafin gaske sauƙo masa, bayan hannunsa yasan ya share hawayen tare da faɗin "Alkhairin Allah ya tabbata agareka tare da Ni'imominka da tsarewar ya Allah! Allah kaci gaba da shiga cikin dukkan al'amurran wannan bawa naka"
A inda yake yaci gaba da zama dan yama rasa mene zaiyi taka maimai, shi yasan waye wannan bawan Allah, kana shi yasan irin tarin ayyukan alkhairinsa ga al'ummar Musulmi.
Tabbas shima yana son yayi koda kwatankwacin irin abinda wannan bawan Allah yake aikatawa na lada.

***************

Zaune suke a babban parlourn ammey suna tattauna maganganun da suka gama kewaye duniyar yanar gizo, inda anan sukaji tabbacin banda 2 week's za'a yankema su Mommah hukunci, inda yaune jadderh ta cika kwana arba'in ciff da haihuwa, a yau din ne kuma zata koma adamawa, inda ammey ta naimawa jadderhn alfarmar maleek ya barta ganin gida.
Dake shima yana tsaka da ayyukan sane yasa shi barin ta suje cenñnn adamawar, ƴaƴan Hajiya lubna kuwa hankalin su idan yayi dubu miliyan toya tashi, jin mahaifiyarsu nada hannun acikin wannan manyan masu aikata laifukan, da aka garƙame.
Inda ba Anan abin yake Bama saida Alhaji taufiq ya kunna Cameran da maleek ya mannawa kowa acikin ɗakinta tsakanin ta da Hajiya talatu nera, aikam sun qara shiga tashin hankalin ganin, iriyar rayuwar da mahaifiyarsu ta gudanar, inda Hajiya talatu nera ta shiga cikin taitayinta, lallai sai yau maganganun jadderh suka kuma dawo mata sabi fil a tsakar kanta.
"Indai har ahaka kika shimfiɗa rayuwar aurenki , to tabbas anci da rabon ki Hajiya, anyi amfani da damar ki an dama abubuwan da Allah ne kaɗai yasan iyakar abinda aka dama ɗin, kana ina baki shawarin idan zaki faɗi magana kika sanin yadda saqon zaigewa mai amshe ta, kika sanin zancen da zaki dinga faɗa wa jama'a"
Wannan maganganu sune ta dinga maimaituwa acikin RAI da RUHINTA, ai kuwa taɗau darasi na har abada, dan ita tunda take bata taɓa nufar kowa da mugun nufi ba, kawai dai bata da danne ɓacin ranta ne da kuma cutar hassada hassada dake damunta, da kuma qarincin ilimin addinin Islama data ke da.

A private jet ɗin maleek aka kai su ummie Adamawa, inda aka haɗa mata sha tara ta arziƙi.
Suna zuwa labarin yasha banban dan kuwa sun tadda woni sabon rikicin ne da tashin hankalin haukacewar Hajiya Laura, mahaifiyar Sufyan friend, inda sai tone tone da banƙato irin asiran data ɗin ga zabgawa abokiyar zamanta MARYAM ABDULJALAAL take.
Inda tace itace ta hana mahaifiyarta waiwarta itace itace kai komai ma itace sanadi, tsabar kunya da nadamar rayuwa friend qasar ma ya bari baki ɗaya, dan yace baima san da wanne idone zai kuma kallon Little momien nashi ba, inda mai martaba sarki abdulphata Omar yasa aka killace a ɓangaren guda dan ta girbi abinda ya shuka, dama ya jima da sauwaqe mata
Inda da magiya da naci da komai mai martaba ya yarda bisa jajircewar MARYAM ABDULJALAAL malam Abdullahi yake ma Hajiya Laura adda'oi, cikin hakuncin Ubangiji take samun sauqi, saidai abinda suka lura dashi shine bata iya magana ba kuma ta iya motsa ko ina na jikinta, loqacin da jadderh taje ganinta kuwa idan da abinda yafi kuka to tabbas tayi.
Gashi dai dukkannin waɗannan abubuwan data aikata a banza abinda take gudun kuma ya riga ya gama faruwa, yau gaya amma tamkar babu ita, yau gata amma gidan da dukiyar data kema duk yazam saidai gani daga nesa hanqoro NOOOOOh kuma, yau ga ƴar jaririyar daga wullar taso kashewa tun cikin mahaifiyarta, yau gata da nata jaririn itama cikin gata so ƙauna.
Tana son tayi magana amma babu bakin maganar, sai yawu yalala da yake zuba daga cikin bakinta mai azabar yauqi da warin masifa, adda'oi sosae jadderh ta mata haɗi da naima mata afwa wurin mahaliccin ta.
Don rama cuta ga macucu ba shine Nasara, ka barshi da Allah ma kaɗai babbar musifa ce acikin rayuwarsa,dan idan mutum ya zalumceka kayi gaggawar ramuwa to kamar kayi kutsene acikin al'amurran Ubangiji, shi yasa kabar mutum ma da fitowar rana da faɗuwar tama kaɗai isharace.


******
Two weeks later

Zaune suke a babban parlourn Alhaji taufiq.
Inda Cikin zallar hikima da tarin baiwar da ALLAH ya masa yace

"Nigeria wata qasace mai tarin tseko mai labarai cike da! , damfara da rashawa, inda mai qaramin qarfi yake wahala!, A hannun talauci da kuma yunwa.
To amma dai koma meye! namu ba tsokaci da qorafi bane, abinda muka sani kawai mu bada rayuwarmu domin TUTARMU taci gaba da kaɗawa, da kuma kawo qarshen zalumci wa qasata Nigeria baki ɗaya, dama Duniya. Tabbas kaine tauraro mai haskaka wannan tafiyar MAKAMA! Dan haka"
" Prepare to answer your position forever and ever MAKAMA, God continues to be our privilege."
Cikin wani tsananin qaunar Alhaji taufiq ɗin ya zube a gabansa, cikin zubar da hawaye yace..
"Ba irina qasa take da buqata ba! Ƙasar mu dole mazaje take nema irinsu MALEEK TAUFIQ!, Tsayayyen namiji mai aiki da rai da rayuwarsa mai burin zamewa 9j uba, uban data riga da ta rasa.
Tabbas maleek shine ya cancanci zama
International military bawai niba!, Duba Nan ka gani" ya qara faɗin maganar yana ɗan kama Abbie wasu tarin takardu masu kama da files, cikin sanyin daya rasa daga inda ya sameshi ya amsa files ɗin Yina dubawa.
Kansa kawai ya kuma yin qasa dashi,idan yace zuciyarsa bata motsa ba yayi qarya, yana ina? Yana ina hakan ta faru? Gaba ɗaya wannan takardun na shaidar qarin girman maleek ɗin ne. Inda suke ɗauke da shaidar sa hannun sauran shugabanni da kuma sarakun musulunci, na sun amince MALEK The head of the Nigerian army.
Yana daga inda yake ya gaza koda kwakkwaran motsine sukaji gaba ɗaya gidan ya ɗauka Parade na zarratan mazajen fama, soja mar mari daga nesa soja birginar hankaka,
Gaba ɗaya suna cikin gidan an gama shirya komai da tsara komi na qarama maleek girma da kuma girmamawa, inda gaba ɗaya makama ne yayi wannan shige da ficen ayyukan, tabbas da sunso barinsa a matsayin da yake da, amma cikin kamala da tattako irin nashi, ya nuna sammm baya da buqatar hakan ga maza a gabansu.

Tsittt kuma wurin ya yi tamkar anyi ruwa an ɗauke sakamakon buɗe ma maleek toufiq mota da akayi ya fito, cikin Military uniform nasu. Daidai loqacinne kuma Abdu makama ya fito da TOUFIQ Nasara, suman tsaye Abbie yayi ganin ɗansa gudan jininsa ɗa mafi soyuwa acikin zuciyarsa wato MALEEK TOUFIQ Nasara tsaye qamm cikin wani irin hasken taurari masu haskaka duniya baki ɗaya, cikin wani irin kwarjinin dashi kansa maleek ɗin ya masa, yasa baisan loqacin da shima ya qame ɗin qamm ba kamar sauran sojawan, dan danan hasken cemaras suka fara aikinsu.
Dan tun daga inda aka qaro masa girman suke tare dasu, har ya zuwa rakiyar da aka yoma MALEEK ɗin gida.
Cikin wani irin nauyin dayaji ya zauna daram a tsakar kansa, shima ya sara ma mahaifan nashi. tare da zare p-carp ɗin kakin dake jikinsa, ya rusuna gabansu alamun su sanya masa albarka.
Wohoho fan's zanso kuga yadda MALEEK ya zama tauraro acikin taurari a wannan Rana, tabbas duk wanda kaga ya qona runbunsa yasan inda toka take daraja, domin gaba ɗaya zukatan bayin Allah sun cika da murna da farin cikin wannan lamari, hakan yasa gaba ɗaya garin Abuja ya ɗauki wani irin zallar tsagwaron murna, yara da manya tsofaffi da matasa, dan kowa ya sanya yaqini ne aransa cewar qarshen zalumci yazo tabbas.
Zuba da Yadda abubuwa suka wakana

Kansa Abbie ya dafa ya shiga kwaranyo masa ruwan adda'oin samun nasarar rayuwa, tare da ɗorewar wanzuwar zaman lafiya a qasa

"May God take care of your problems, my son May God enlighten your life As you plan to enlighten the souls of others"

MAKAMA ne mai wannan adda'ar wa maleek, maleek zubewa kawai yayi jikin mutumin da yake ɗaukar sa tamkar mahaifi a garesa, tun kamin yasan matsayin sa a wurin mahaifin nashi. "tabbas rayuwa bata qarya, haka kuma rayuwa tana zuwarma ko wanne bawa a yadda ya ɗauke ta. Allah ne gatanmu kuma shine zaici gaba da zame mana gata"
cewar Abbie cikin gida aka shiga dashi tamkar woni sarki, inda gaba ɗaya family suke Nan tun kwanaki uku da suka shuɗe, saka makon qiran da Abbie ya musu.
Sammm basa da wota masaniya akan hakan, shine dalilin da. Yasa babu wanda ya tsammaci hakan, duk kuwa da cewar malam bahaushe na cewa tsammaci abinda baka yi tsammani ba, gashi kuwa yau ya tabbata akan ahalin TOUFIQ MAI NASARA families.

Jadderhn dake zaune dasu ammey a babban parlourn ammey ne Hajiya talatu nera data dawo hayyacinta ne ta miqar da ita tsaye tana yalyala guɗa, tare da fara musu kirari, Nan da nan Abbie, ammey, maleek,da sauran yaran gidan suka shiga kara mata nera domin takenta kenan HAJIYA TALATU NERAH, Nan aka shirya walimar da babu shirinta koda da wasa ne kuwa.
Anyi walimar murnar qarin girma tare da taYa ɗan su ɗan uwansu murnar.
Inda saida yamma lissss maleek ya sami kansa tun asuba shi kuwa ta akazo aka ɗauke shi a gidansa.

Cikin rakiyar zaratan sojawan da aka qara masa dan tsaron lafiyarsa ciki kuwa harda IHSAN FANDALLAH, suka nufi qayataccen gidan maleek ɗin, wanda ya qara gyara tsarin gidan nashi loqacin jadderh tana Adamawa, parking motocinsu suka yi a tsakiyar compound ɗin wurin da aka tanaja dan ajje motoci, wanda a qalla wurin ka iya ɗaukar motoci sama da guda goma domin duk yadda kuke tunanin gidan maleek, to kuwa ya zartas haka.

Suna gama daidaita parking ɗin su a parking lot ɗin gidan aka buɗe ma maleek motar tsakiya wacce tafi ko wacce mota ɗaukar hankali a wajen, samfurin qirar Bugatti 2023/2024 baƙa wuluk.
IHSAN FANDALLAH ce ta ratso tsakiyar tafin dandazon taron mazajen sojawan, itama ta haɗe cikin kakinta wanda ya kame mata jiki kam kam, dai dai gaban maleek ta ja da tsaya tamkar dai irin riƙaƙƙaun ƴan barikin Nan, ta wani tale qafafunta tana mirgina wuya, tace


"INAAAAAA🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥹😉😉

Byeeeeee mu haɗe a next page insha Allah
*🔥♥️ KAREN BANA ♥️🔥*
NA MARYAM NASEER MIRRAH ✍️
*Ammey laylerh*

Page 4️⃣5️⃣&4️⃣6️⃣

08104493215

✯D͟A͟Z͟Z͟L͟I͟N͟G͟ S͟✯T͟✯R͟'✯W͟R͟I͟T͟E͟R͟S͟
=============================

_____________________
"Ina sonka maleek! Har abada abadan abada, harya zuwa numfashi na qarshe"
cewar IHSAN.
Tassss' jadderh ta ɗauke ta da mari, wacce ta fito daga cikin motar maleek.ayman saɓe a qafaɗarta.
"Kina sanin inda za kina akuyan cinki,bawai Anan ba! dan gaba idan kika kuma to tabbas bawai mari Zaki sha ba"
Hmmmmmmm kawai ta fesar da numfashi tana barin wurin fuuuuuuuu baki ɗaya.
Cikin zallar isar sa ya tako gabanta, yaja ya tsaya yace mata "ke wai wacce iriyar dabbace acikin dabbobi? Da kika kasa tantance gobenki, shin bazaki tahi kiyi taki rayuwarba, kullum burinki a rayuwa kutse acikin al'amurran mu! I sey Get out of my house"

"Mene aibun hakan dan kawai nace ina so ka?"

A fusace ta fice a gidan. Cike da wani irin takaici baqin ciki marar misalta.
*****************
Ko ganin gabanta batayi haka take taka qafafunta. Gaba ɗaya idanunta a rufe yake bata ko kallon gabanta, tana zuwa parlourn ta zube jikin rug.
Tare da qara rungume ayman qamm a kafaɗarta, tana sakin ajiyar zuciya.shigowa y ayi cikin dakewa tare da zama gefenta, ayman ya amsa yana shilla shi sama, shi kuwa sai wangale baki Yake irin na yaran nan.

"AYUSHHH Kada kiji ba daɗi akan hakan!"

Taji sauqar muryar maleek ɗin cikin daddaɗar sautinsa.

Cikin iya sarrafa kalamanta tace..

"Ko wacce mace tana S0n a sota! A kuma girmamata, sannan a kyautata mata mu'amala!.
Ba tsohon burin kowa bane a rayuwa, ace ya zam bayada kima da daraja irinta ƴa mace.amma ƙaddara tana da nata tsarin! Ba komai na mata uziri!! na yafe mata!!!"

"Idan har kana da buri da kuma muradin auren IHSAN bisimillah qofa a buɗe take"

Murmushin jinjina ma wayonta da iya sarrafa magana maleek ɗin yayi. Dan ya riga da ya gama sanin dukka halayenta, tunkan Tasan kanta itama.

Amma dake neman magana yake, sai yace mata

" Ai ita ƙaddara abace marar tabbas Nan ta ke, take sauyawa"

Cikin zallar fusata jadderh ta miƙe tsaye ta nuna shi da yatsa tace..

"Kada ka shafama rauni na gishiri, ta hanyar sauyamin zance MALEEK!"

****
Shima tsayen ya miqe ayman saɓe a qafaɗarsa.yace mata "Sosai indai a lamarin $0n kune, tabbas na daɗe da kurmancewa ko zuciyata ban iyaji yayinda take tare dake. Ina son kisa aranki maleek na kine ke kaɗanki AUTAR MATA" ya faɗi hakan yana saka hannunsa ɗaya ya zagawo qugunta dashi.

Kamar ba zatayi magana ba sai ku ya tsinkayi muryanta, tamkar wacce aka fusga take masa.

"To kenan ya za'a yi na fashimci hakan?"

"Alqawarin zamowa haske tsananin haske maras yankewa, Alqawarin zamowa ga ta,
Gata marar qarewa, alqawarin zamowa farin ciki marar yankewa AYUSHHH!. Kece Duniyar maleek, sai dake maleek yake iya kwakkwaran motsi. You are my life! You are my world!!, You say everything and everything is mine AYSHA ABDULPHATA OMAR"

Gaba ɗaya wani irin daɗi ne ya gama gigita duniyar jadderh, jin Waɗan nan tsadaddun kalmomi daga bakin SADAUKInta JARUMInta abin alfaharinta, kuma duniyarta dariyar ta mijinta uban yaronta ayman uban sauran ƴaƴan ta masu xuwa insha Allah.
Zama maleek yayi tare da kamo AYUSHAN shi ya zaunar ta a cinyarsa, tare da hura mata iskar bakinsa ganin tamkar ta tafi wata duniya ta daban ba wacce suke a ciki ba.
Rumtse idanunta tayi qamm tare da qara qanqame jikinta wuri guda,a qalla taɗau minti biyu zuwa uku kafin ta saki ajiyar zuciya.amma ba tayi motsin kirkiba balle Magana.

Hakan ne yasa maleek murmusawa dan tsabbb ya gama gane abinda yake akwai🥰.
Hannunsa yasan cikin ya fara mata wasu irin abubuwan da baki basa iya faɗar girmansu. Saidai gani a aikace, qoqarin janye wa take hakan yasa maleek qare sakale mata waist ɗin ta, tare da birkitota jikinsa yana ci gaba da murmusawa, cikin wata iriyar muryarn dashi kansa yasan yana kwance mata notuka ya raɗa mata "duk ka dama kinyi missing nawa har haka ne? Amma ake min rowa! Yau kima nin watanni biyu da woni abu uhmmm"
Kulle idanunta tayi jin iriyar muryarn da yayi amfani dashi wajen wargaza mata numfashinta.

Shafa fuskar yayi sannan ya manna mata wani irin birkitaccen kiss a dokin wuyanta, yummmm taji gaba ɗaya rassanta sun ɗau yumumumu.
Hakan yasa tayi saurin tashi a zabure jin tamkar maranta zai ɓalle, tayi saurin nufar bedroom na ta, ayman da yayi nashi gefene tun ɗazun ya fara wuntsil wuntsil ɗin fara rigima hakan yasa maleek dakatawa da bin bayan jadderhn da yayi niyar bi.
Ɗaukar sa yayi yana zama ya ɗora shi saman cinyarsa, ya shiga magana shi kaɗai " me yasa cwthrt kake son katsema Abbunka jin daɗinsa, kamar wanda yasan me mahaifin nashi yake faɗa ya shiga wuntsil wuntsil ɗin da kyawawan qafafunsa. Suka soma ne yasa maleek sakin wani kyakkyawan murmushi, inda ya miqe kai tsaye bedroom na jadderh ya nufa.
Bai tarar da ita a ɗakin ba, motsin ruwan dayaji a cikin toilet ne hakan ya bashi tabbacin tana toilet ɗin, ita kuwa jadderh gaba ɗaya duk wata nutsuwa nata ta nemeta ta rasa, hakan yasa kawai ta sakarma kanta shower , ko taji dama dama abinda take ji ɗin ya ragu, Ahankali ya kwantar da ayman daya fara barci, cikin tafiyar sanɗa yake taku a hankali harya qarasa bakin toilet ɗin. Ahankali ya mirza handle ɗin qofar tare da turawa kaɗan, gudun kada taji motsin sa. Tana tsaye ruwan Yina sauqa a jikinta gaba ɗaya bata cikin hayyacinta, wasu irin abubuwa ne suke taso mata masu kama da sukar allurai. Hannayensa ya naɗe a cikin qirjinsa,tare da ware lumsassun idanunsa yana qare mata kallo tun daga kan yatsun ƙafafunta har zuwa samanta, idanunsa suka soma fitar da wasu irin sheƙin ruwan dake kwance a cikinsu, ganin tana Nan tamkar dai bata haihuba komi nata yana a inda yake cassss daram, rabon da idanunsa su mashi irin wannan kyakkyawan ganin tun kamin ta haihu. Bayan tayi arba'in kuma abubuwa suka sha masa kai, dan burinsa bai wuce ace an yankema azzalumain ɗaya cafke hukunci su ba, hakan yasa sammm bai samu damar da sai sake da iyalin nashi ba, gashi yau wajajen su wata biyu harda woni abu akai. Qara harɗe hannuwansa yayi cikin qirjinsa tare da takawa zuwa inda take tsayen, yana xuwa ya haɗe ta jikinsa, nan take ruwan yaci gaba da sauqa ajikinsu tare, kayan jikinsa ya cire tare da na tan itama sukayi wanka na gaskiya da gaskiya, amma ansha fama dan saida tayi da gaske kana ya sarara mata a cikin toilet ɗin.

******************
A yaune za'ayi zaman kotu dan kawo qarshen azzalumai irinsu Kashim baba.
Kowa yana a zaune a wurin da ya dace, inda kotu ta buqaci da maleek ya fito dan ya nunama duniya, farin cikin daya ke ciki na samun nasarorin sa a cikin rayuwa.

Babban lauyan MUHD BALA ne tsaye da abin magana manne a qirjinsa, cikin son ya yabawa maleek bisa jajircewar sa wa aikinsa ya soma magana cikin amsa kuwwa, yace

"Ina da tarin bayanai ga wannan JARUMI kuma tsayayyen sojan matasa! Wato maleek. Duba da irin tarin qalubalen daya dinga fuskanta ta hanyar Bara zana wa rayuwarsa tare da gwagwarmayar rayuwa, wajen ganin ya kawo zalumci wa ƙasar sa.
Hakan yasa yasami lambar yabo da kuma girma a wannan hukumar tsaro ta nigeria.ina matuƙar farin ciki da wannan.
Ka na inawa wannan JARUMI daya sanya muka farka daga nannauyan barcin daya ɗauke mu, kwarai Mutun ne da babu kamar sa wato.
MALEEK TOUFIQ MAI NASARA" gaba ɗaya ɗakin taron ne ya kaure da hayaniyar mutane, KOOOTUUU.
Alƙali ya doka hidimarsa. Tsittt kuwa wurin ya ɗauka shiru tamkar babu rai mai numfashi acikin sa,

"Kotu tana da buqatar ganin wannan matashin jarumiy."

Cikin zallar jarum taka ya fito cikin babbar kotun nahiyar Abuja, kotun musulunci mai yanke hukunci akan zallar gaskiya, da kuma aiki da amana.

Kai tsaye abin maganar ya amsa tare da faɗin.

"Alhamdulillah, alhamdulillah, alhamdulillahi, Allah shine abin godiya ako da yaushe, a kuma duk halin da muke.
Actually wannan babbar kotun da tayi qaurin suna wajen tace zallar gaskiya komi ɗacinta. Yau kimanin shekaru goma sha uku kenan ina aiki da hukumar rundunar sojoji.
Inda na samu tarin nasarori ta hanyar kawar da masu laifi acikin wannan ƙasa tamu.
Tabbas da ace matasanmu zasu aiki irin haka ta hanyar gina gobensu akan gaskiya da kuma aiyukansu, to da tabbas ƙasar mu ta zauna lafiya ta hanyar sanin babu wani sauran tsekon daya musu aaura, acikin zukatan al'ummar duniya baki ɗaya.domin MATASA sune abokan tafiya!. Dan haka nake roqon wannan kotu mai gaskiya tada zanke hukunci dadai da masu laifi"

Bayan gama dukkan wani jawabi da maleek yayi, aka kawo shaidu da hujjoji masu qarfi inda kotu ta yanke hukunci daidai laifukansu.

Yau ne dubban jama'a suka shaida hukuncin da aka yankema azzalumain qasa, inda aka ma Ibrahim nera kisa ta hanyar rataya, kasan cewar shi shugaban qasa ga laifin an kama shi da cin amanar ƙasa,ga kuma laifin kashe-kashen da suka sa aka yi.
Inda sauran aka yanke musu hukuncin ɗaurin shekara ashirin da biyar a gidan yari tare da aiki mai tsanani, inda aka yankema Hajiya lubna hukuncin ɗauri na shekaru goma sha biyu tare da tarar Naira miliyan biyu, bisa abubuwan data aikata ma ammey da kuma yin qurin qisan da tayi, Kashim baba anyanke masa hukuncin ɗauri na tsawon shekaru goma sha daya, idan ya cika wannan shekarun kuma a rataye sa, wannan shine hukuncin babbar kotun Abuja ta musulunci, aikuwa nan iyalan waɗannan bayin Allah suka dinga iface iface harda masu iskoki.

Inda gaba ɗaya familynsu MALEEK kowa yake zubar da hawaye musamman ma ƴaƴan Hajiya lubna, dan gaba ɗaya sun gama fita hayyacinsu kai idan ka gansu dole ne su baka tausayi.
Loqacin da aka fito dasu kuwa za'a wuce dasu kar kuzo kuga kuka na tashin hankali, inda Hajiya lubna tana kuka ƴaƴan ta na kuka tana roqon su naima mata yafiyar su Ammey da maleek, gaba ɗaya sun shiga tashin hankali marar iyaka,
Inda suna ji suna gani aka hankaɗa kewarsu zuwa gidan maza.

Gaba ɗaya jadderh kuka take sosae dan ta qara tsorata da duniyar baki ɗaya, inda ammey kammm ko magana ta gaza yi domin ita kaɗai take jin suyar da zuciyar ta take ciki.
Zaman tsakani da Allah tayi da Hajiya lubna sese da rana ɗaya

Please Login or Register in order to submit comment