Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

lallai kasan koni wace ba!, Lalubene kawai acikin duhu kakeyi maleek! Baka da hujjar da zaka sa kotu tayi aiki a kaina.
Cikin wani irin salo maleek ya karyar da wuyansa gefe, tare da faɗin atafin hannayena kike komai Mommah, domin tundaga ranar dana gama sanin ke ko wacece, hakan yasa naci alwasai akanki Mommah, tun ranar da kika ɗauke min RAYUWA ta tun daga ranar nasan asalin ki! Sannan nasan wacece keeeee. Zanso ki hasaso ranar Mommah keda aminiyar haɗin ki Laura!. Dama! damammaki!! Rana! Ranaku!! Loƙaci da loƙuta duk a lissafe suke kuma tafiya suke cikin tsarin ubangiji sammai. Abu mafi haɗarin kuma nine jagoran tafiyar!, Wannan shi ake ƙira da ƙarangiya, kin haƙa ramin da zai rufta dake! Gurnanin zaki kaɗai yakan sa sauran namun su girgiza, ya hana su samun kwanciyar hankali. Hausawa sunyi gaskiya tabbas na yarda KAREN BANA shike maganin ZOMON BANA Mommah. Ya faɗi maganar daidai lokacin da su Jawad suka ƙara SO da sauran masu laifin.
A kuma daidai loƙacinne shel kwafta na sojojin 9j ya dira a tsakiyar babban filin campanyn, nan aka yi gaba dasu Ibrahim nera tare da sauran miyagun yaransu.
*****

ACEN GIDAN MALEEK kuwa.

Idan hankalinsu yayi dubu toya tashi, ummie dake tare da AYMAN suna kwance akan 3ster acikin parlour. Barci ya fara ɗaukar ta sama sama, ita kuwa jadderh tana cikin bedroom ɗin ta tana barci itama.
Ƙawai sai farkawa sukayi sukaga babu ayman babu dalilin sa, da ummie tasha tana barcinne yayi kuka bata ji ba, shine uwarsa ta fito ta ɗaukesa, sai kuma da taga shiru shiru ko motsin jadderh batajine yasa jikinta bata kamar ba ƙalauba.
Hakan yasa ta nufi bedroom ɗin jadderhn, amma me zata ga sai taga wayam babu alamar jariri a tare da jadderhn, hakan yasa ta shiga tashinta koda ta tashin take kuma tambayar ina kuwa AYMAN. Tace mata ai yana wurinta Nan fa hankalisu idan yayi dubu toya tashin jin baya gurin kowanne acikin su, ai kuwa jadderhnku ta taqarqare ta zunduma uban ihun daya ɗau hankalin uban jami'an da maleek ya zuba. A 370 suka shigo cikin parlourn gidan ganin matar ogansu ta dage sai uban kuka take hakan suma ya tashi hankalin su kwarai da gaske. Jin anshigo har cikin gidan an kuma ɗauke AYMAN wanda su kansu haidane yaron shine DUNIYAR ogansu maleek, ai kuwa Nan kowa ya shiga tashin hankali marar iyaka a cikin su, wasunsu harda masu fara hawayen tausayin kansu da kansu.
Cikin tashin hankali marar qarewa ummie ta qira ammey take faɗa mata wannan tashin hankali da suke ciki, ai kuwa itama idan hankalinta yayi million dollars toya tashi, cikin qanqanin loƙaci sai gata a gidan maleek ɗin.

Abinda zaifi baka dariya da tausayi kuwa gaba ɗaya jami'an tsaron gidan maleek ɗin, sunyi knel down suna wata waƙa dagaji irin ta sun shiga tsaka mai wuyar nan ce.
Abu mafi tausayi kuma kowa a parlourn hawaye yake ɗauke wa daga saman kuncinsa, ammey kuma faɗi take "dama nasan da wata a ƙasa ba kuma banza tunda yaron nan ya zuma mana uban jami'an tsaro acikin gidayan! Hankali na yaƙi kwanciya da hakan, ashe ashe kuwa da abinda yake shirin faruwa damu! Shi yasa sammm bana qaunar wannan aiki NASHI, amma idan nayi woni tunanin kuma sannan nayi duba da hadisan Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama! Sai na fawwalama Allah al'amurran sa, amma dama na daɗe jin wannan aikin nashi sammm babu alkhairi acikin sa!"

"Ya Allah! ya malikul zuljalalu wal Ikram ya Ubangijin talikai ya Ubangijin sammai da ƙassai ya Ubangijin Al'arshi! Ka karemin yarana da yarona a duk inda suke, ya Allah🤲🏻".

Ɓangaren su maleek kuwa kai tsaye babban barikin sojojin Nigeria dake Abuja suka nufa dasu Kashim baba, suna shiga harabar barikin sojojin gaba ɗaya sojawan wurin suka hau wani irin iface ifacensu da masu hankalin cikinsu da marasa hankalin, Nan da aka garƙame su Ibrahim nera bayan anyi uwarka ubanka tsakanin sa da vp ɗinsa isa gwal aikuwa saida ya kuma jama kansa domin Anan ma saida maleek ya ladaftar dashi sosai. Ganin AYMAN yana kuka ne yasa Chief of army staff cewa yaje wa iyalansa ko safi samun kwanciyar hankali da nutsuwa tattare dasu. Baiyi musu ba kuwa domin shima yana da buƙatar hakan. Hakan yasa aka shirya masa motocin rakiya har guda shida, tashi a tsakiyar su itace ta bakwai ɗin. Haka suka rankaya sai gidan maleek ɗin.
A loƙacin wajen qarfe biyar da mintuna, suna shiga cikin harabar anguwar suka fara sakin jiniyar sojoji, hakan yasa gaba ɗaya mutanen parlourn fara rige rigen fitowa. Har xuwa wannan loƙacin kuwa abinda yaga cikin su Ammey, kowa ya gaza iya cin komai koda kuwa ruwane.
Haka suka jeru tamkar wasu sojawa, haka suka ƙame a tsayen da suka.
Har sanda maleek ya fito daɓe da AYMAN a qafaɗarsa, gaba ɗayansu har rige rigen qarɓan AYMAN suke.
Ita kuma jadderh a guje ta ɗiba, tana zuwa ta haɗe da maleek ɗin da AYMAN ta rungumesu duka, tana sakin kuka mai tsananin azabar gaske.

Not editing🙃

Kuyi joining group ɗin kana kuyi shering pls👏🏻
*🔥♥️ KAREN BANA ♥️🔥*
NA MARYAM NASEER MIRRAH ✍️
*Ammey laylerh*

✯D͟A͟Z͟Z͟L͟I͟N͟G͟ S͟✯T͟✯R͟'✯W͟R͟I͟T͟E͟R͟S͟

Page 4️⃣1️⃣&4️⃣2️⃣

08104493215

=================
Cikin tsananin tausayin yaran nasu ummie da ammey,suka nufi wurin yaran nasu. ammey ce tayi saurin amsan ayman tana haɗe shi da qirjinta, jin sai faman shan zuciya yake ne, yasa Ammey nufar wurin jadderh wacce take rungume cikin maleek har yanxun.
Cikin muryarn tausayinta ammey tace mata "amshi Ayman ki bashi abincin sa Ya sha, da dukkan alamu abincinsa yake da buƙata". Hakan ne yasa maleek zare ta daga cikin jikinsa tare da wuce su cikin hanzari dan kada su fuskanci halin da yake a ciki.
Ummie ce ta amshi ayman tare da riƙo kafaɗun jadderhn su kayi cikin parlourn, a kujerar farko ammey ta zauna tana nunama jadderh da ummie wurin zama kusanta. Gaba ɗayansu zaman sukayi jadderh tana zaro mama dan bama ayman abincin sa, tamkar irin wanda ya shekaran nan bai samu abuncinsa ba, haka ya kaima nonon uwarsa cafka, cikin shogoɓar data zame mata jiki, ta callara qara, tare da faɗin
"wash ammey nonona"
gaba ɗayansu kuma sai ta basu dariya da tausayi duk loƙaci guda, tabbas zataji zafi dole. Ace tun safe rabonsa da abincinsa, ay dole taji zafin tsotson.
Suna Nan zaune har maleek ya sauƙo cikin jallabiya, kai tsaye masallaci ya nufa tunda yaji ana qiraye qirayen salla, suma kai tsaye miqewa sukayi tare da cikin ɗakin domin gabatar da Sallah. Bayan idar da Sallah suka dawo palon ammey na shirin tafiya gida kuma tunda anga ayman ɗin. Tana sanya qafarta woje maleek na sanwo tashi ƙafar, Ganin Ammeyn shi na qoqarin fitowa ne yashi dakatawa, tare da ɗan rusunawa "Barka da dare ammey Naaaaaa"
"Barka" kawai tace masa domin tana da buqatar sanin komai daya faru ayau ɗin.
Key na hannunta ya amsa tare da wuce wa gaba, ganin hakan yasa tabi bayansa dan sanin taka maiman abinda yake nufi ɗin. Tana shiga cikin motar ya mata key tare dayin reverse yana nufar bakin get ɗin gidan, cikin ƙanƙanin loƙaci ya kaita gidan. Suna faka motarsu motar Abbie na sanyo kai gidan.
Hakan yasa maleek dakatawa da niyar fita da yake a cikin gidan nasu, Abbie kuwa yana fitowa ya kafe maleek da ido yana kallon sa babu ko qafta ido. Ganin irin kallon qurillan da mahaifin nasa yake binsa da shine yasa, yaji gaba ɗaya ya sare kuma bai kyautama mahaifin nasa ba, wajen kama matarsa uwar gidansa Hajiya lubna, cikin wani irin tsananin kunyan mahaifinsan yake qoqarin durqushewa Dan gaida mahaifin nashi. Cikin sauri Abbie ya taro shi tare da haɗe jikinsa dana maleek ɗin, dan bayansa ya shigawa bubbugawa kafin ya ɗan janye shi kaɗan yana faɗin.
"Tabbas kai namijin gaske ne YARONA! Imani da niyar gyara itace manufa yarona, irinku duniya take nema maleek. Ka sani shi marar jin magana sai ammasa hukuncin jaki! Domin kawo gyara acikin al'umma,dole sai wasu sunsha duka dole wasu sai sunsha jijjiga, kafin wasu su rauraya kayi amfani da damar da mahaliccin mu ya baka! Wajen kawo qarshen zalumci da azzalumai".


"Kamar yaya kenan"

Cewar ammey shi kuwa maleek.
Gaba ɗaya duk wata jijiya mai rai a jikin maleek babu wacce bata motsa ba jin irin furuncin dake fita daga bakin mahaifinsa, duk kuwa da cewar harda matarsa uwar gidansa acikin manyan masu aikata laifukan.

Cikin haqiqa nin zallar tsagwaron zallar gaskiyar dake danqare acikin qirjin Alhaji taufiq, ya dubi tsabar idan Hajiya Aysha galadima yace mata

"Misali ace kece na kama da laifi, domin kawo gyara dole saikin fuskanci hukunci, daidai da laifinki daga wurina. To yanxun ke a ganin ki mai zaki ɗauki hakan?"
"Gyara" ta faɗi hakan tana sauƙe ajiyar zuciya, dan Tasan da wani abu a qasa, tunda suka fara mata wannan kwanakwanar.

Murmushi Abbie yayi tare da faɗin "kin tabbata?"
"Tabbas na tabbata Alhaji"
"To kamar dai haka ne! Hajj LUBNA tana daga cikin miyagun qasurguman masu aikata miyagun Laifuka"
Yana kaiwa Nan yayi saurin wucewa cikin coumpaun na gidan nashi.
Tsaye take qam gaban maleek ta kasa koda kwakkwaran motsine, jin wani irin tashin hankalin da maganar ta Abbie ta sanya mata. Hakan yasa ta shiga jijjaga maleek cikin wani irin tsananin tashin hankali, take faɗin "mene haka maleek? Menene kayi kenan? Kana nufin matar ubanka ka kama, kakai kotu! To wanne dalalin?, Sabo da me? Duk bana ce a rabu da wancan maganar bane, taje ita da Allahn daya halicce ta ba MALEEK? Ashe ban isa da kai ba dama MALEEK" ta qarisa zancen cikin ɗauke maleek ɗin da wani irin gigitaccen mari. Wanda da ace badan kasan cewarsa tsayayyen soja ba da babu abinda zai hana shi somewa a wurin. Dan kuwa kyakkyawan marine ya samu daka Ammeyn nashi.
Hannunsa ya zira cikin aljihun jallabar dake jikinsa, tare da kuma sunkuyar da kansa qasa dan jiran ko Ammeyn nashi zata kuma ɗaukar woni hukuncin akansa.
Kamar rugujin sauqar aradu sukaji sauqar maganar Abbie ta saman benen dake nashi ɓangaren, komai daya faru akan idon sane. Ganin kamar ammey na shirin qarama maleek woni marin ne yasa shi dako mata tsawar da zata iya rantsewar tunda suke bai taɓa mata koda kotan kwacin taba.
"Kina qara kuskuren taɓa min yaro ranki sai yayi mummunan ɓaci,! Tunda baki san daidai da rashin daidaiɗinba AYSHA, meye laifin MALEEK dan kawai aikinsa ya kawoshi gareta? To kisa aranki koda ce ke ko da kuwa nine to tabbas irin wannan abun da MALEEK TAUFIQ yayi shine daidai, kuma shine hukunci na gaskiya bawai zalumci ba! Kina Nan kamar wayayya amma anbi dare anbi rana ana neman ruguza miki farin cikinki kota halin qaqa"
daidai loƙacin ne kuma ya ida sauƙowa qasa xuwa inda ya bar su ita da MALEEK ɗin da hannu ya nuna ta yana faɗin.

"Wacece ita? Menene hasalin abinda ke acikin zuciya da kuma manufarta a gareki? Babu baki da amsar wannan tambayar, dan haka in ba zaki iya kallo ba to kiba masu wuri suyi aikinsu na cikakkun mazajen gobe"
Ya faɗi hakan yana kama hannun maleek tare da kaishi har bakin get ɗin gidan, "kaje da safe zan nemeka. Allah yaci gaba da shiga cikin al'amuran ka duniya da kahira MALEEK TAUFIQ tsayayyen namijin mazajen fama, tabbas rabbi zaici gaba da haskaka al'amurran ka zaici gaba da maka jagora a koda yaushe! Zaici gaba da zame maka gata a dukkan inda kake faɗin DUNIYAR Nan!"
"Yes sir." Yace tare da wani irin Sara ma mahaifin nashi irin na cikakkun jaruman qasa.
Ba tare da ya kuma cewa komai ba ya kama hanya ya nufi gidansa dake asokoro a qasa duk kuwa da cewar akwai ƴar tazara sosai tsakanin su da gidan nashi.
Haka ya rinqa tafiya cikin tafiyar Nan irin ta sojojin nan masu ji da kansu da kuma maganin tsagerun kwaɗi, haka yaringa keta hanya duk inda ya gimla acikin anguwar da yabi sai an rakashi da idanu, domin ya xuwa yanxun gaba ɗaya gidajen talabijin da rediyo sun kama haska komai daya faru safiyar yau ɗin. Hakan yasa matane dasun ganshi suke nuna shi da baki wosu kuma da hannu, wasu kuma tserewa suke ana kare kawai,
Yana kaiwa qofar gidansa ana shiga sallar isha'ee, hakan yasa kai tsaye masallacin ya nufa dan yana da yaqinin alwulansa nanan daram. Ana idar da Sallah yayi gaggawar shigowa cikin gidan nashi, tare da linkin tsaron da aka kuma qaro masa, gudun abinda kaje Yazo.
Cikin tafiyar sassarfa yake taka mata kalar benen wasu ba bibbiyu yake takawa, kai tsaye bethroom nashi ya nufa jin zuciyarsa na, masa wani irin luguɗen masifa gaba ɗaya maganganun su Kashim ne suka shiga dawo masa tsaƙar kansa .
********************
Sama da 30 minutes kenan daya ɗauka a tsaye ruwan showern daya kunna na dukan jikinsa, wanda amatsayinsa cikakken Namiji me motsa jiki haka kuma soldier, yasa samm baiji ajikinsa cewar ya gajiba da tsayuwar ba haɗi da dukan ruwan.
Yanayin yanda ruwan ke dukan jiki da kuma kansa kawai, ya Isa bayyana maka cewar lallai ba'a cikin tunani da kuma hayyacinsa yake ba. Domin duk yanda yaso da yayi zeroying mind nashi abun yaci tura. Ahankali yakai hannunsa ya kashe showern, tare ɗaukar wata kakkaurar bathrobe ɗin dake gefensa ya sanya a jikinsa, ba tare daya tsaya tsane gashin kansa ba ya nufi qofar fita cikin bathroom ɗin.
Hannunsa ya ɗaura akan handle ɗin qofar, ya buɗe yayin da yake jin qirjinsa na amsawa aduk wani taku da zai yi.
A irin yanayin da yake cikine yasa samm baiji zai iya tsane gashin kansa dake ɗigar ruwa ba, wani dogon trouser kaɗai ya sanya ba tare daya sanya riga ba.
Qarasowa jikin windown ɗakin nasa yayi,wanda daga Nan inda yake yana iya hango compound ɗin gidan, inda sojoji suke tsaye suna ta faman kai kawo, har yanxun zuciyarsa zafi take yi masa yayinda, da wani irin ɗaci yake daɗa mamaye maƙoshinsa, idanunsa da suke a lumshe ya ware saboda baya jin, zai iya jurewa gizon da amsa kuwwan maganganun su Kashim baban dake dawo masa tamkar, dai yanxun abin yake faruwa.
Ayanxun baya buƙatar komai domin brain nashi gab take da juyewa, wanda hakan kuma yayi sanadiyyar hautsinewar tunanin sa.
Yayinda da har yanxun maganganun Kashim baban ke masa yawo a tsaƙar kansa da kuma tunaninsa.
*KALMAR*
"Idan nagama dakai zanbi ahalinka ɗaya bayan ɗaya na sheƙesu, sannan na aure matarka uwar yaronka ayman, waɗanda na tabbata sune rayuwarka MALEEK!¡!"
Daya faɗa masa ita mafari abinda yafi haukata masa zuciyarsa, duk kuwa da cewar yasan suna komar hukumar sa ayanxun haka, amma jin kalmomin yake tamkar fitar rai, "ZAN AURE MATARKA, UWAR YARONKA AYMAN".
A zafafe ya kaima glass na windown wani irin bugu, jin zuciyarsa tamkar zata bar gangar jikinsa, tamkar kuma zata tarwatsa masa ƙwaƙwalwa da zuciyar sa.
Jin qarar fashewar abune yasa gaba ɗaya sojawan coumpaund ɗin gidan yin wata iriyar, katan tanwa tare da cira hancin bindugunsu sama, cikin zafin nama kuma suka fara qoqarin harba bindugunsu, wannan abinda ya faru ne ya ɗau hankalin su ummie dake cikin ɗakin jadderh suna rarrashin AYMAN dake ta faman rigima tun fitar su maleek ɗin, tare da ammey cikin tsananin tashin hankalin abinda yake kuma shirin faruwa suka fito cikin tsakiyar parlourn, ganin babu komai ne yasa jadderh miƙama ummie Ayman tare da hayewa saman maleek kai tsaye, yana tsaye inda yake hannunsa sai zubar da jini yake gashi duk glass sun yanyankeshi, turus jadderh taja da tsaya tana kallon ikon Allah, kafin kuma cikin hanzari ta qariso gaban maleek ɗin tare da kama hannayensa tana faɗin " meya faru dakai Cwthrt? Mene ya samu hannuwanka haka rayuwata?" Gaba ɗaya ta shiga masa tambayoyi ajejere, ba tare da barin taji amsoshinsu ba jin hannuwansa cikin tattausan hannun jadderhn ne yasa shi faɗa wa jikinta.
Tare da yagaye ta da hannuwansa masu ɗauke da raunuka, kansa ya ɗaura a dokin wuyanta tare da matseta tsamm acikin jikinsa, tamkar zaya mayar da ita Cikin cikinsa.cikin wata iriyar muryarn da bata sanshi da ita bane ya shiga faɗin.
"Mene mutane suke naima a wannan DUNIYAR ne kammm? Da suke cire tsoron Allah a ransu, suke aikata manyan lefuka akan abinda bazai amfa nesu ba Ranar gobe ƙiyama? Uyummmmmmmm na rasa, na rasa gane kan mutane da gaba ɗaya yazam kowa kansa da kansa yake so! Kowa baya da buri da kuma fatan daya zarce yaga yana quntatama qaninsa? Akan me?, Akan me hakan yake faruwa! Kina son kicemin dukka Son zuciyane ko son kai uyummm?" Ya faɗi Maganar yana ɗago haɓar jadderhn tare da qureta da idanunsa, wanda suka kaɗa sukayi jawur dasu.
Cikin abinda yafi komai ƙonama jadderhn rai da kuma RUHINTA ta shiga faɗin " tabbas son zuciya ne ya MALEEK, da kuma rashin tunani! Idan har burinka/ burinki/ ƙuntatama wasunku tokai miye ribar taka Rayuwar, tabbas Zamani ya sanja ya kuma zo mana da abubuwa maban banta, masu ban tsoro, za kaga mutum iya mutum tsantsar ambatar Allah akowanne furuci nashi! Amma tashin farko da zaka auna zuciyarsa to tabbas FANKO CEEE ya MALEEK! Kamar dai ta Mommah.
HAKA kuma zaka mutum ana masa kallon shi ba kowa bane kana babu abinda ya sani, samm baisan daɗin rayuwa ba,kuma kowa kallon qas qas tance suke ake masa, amma zaka duba shiɗin zuciyarsa tsarkakakkiyace ba kamar yadda ake tunani ba! Kana kuba zak tadda mutum baya da aiki sai kushewa jama'a da faɗar maganganu mara sa daɗi amma koda dade da misqana zarratan bazai taɓa iya cutar da wani mahaluki daga halittar Ubangijin muba! Wannan shine halin da ake ciki a yanxun, burin kowa yaga kowa ya tagaiyara amma banda shi kamar dai Mamie talatu nera".
Cikin wani irin zallar mahaukacin abinda yake ji daga cikin zuciyarsa ya qare matse jadderh sosea, yace .
"Haka kuma zaki ga mutum baya da burin daya wuce yayi zalumci wa abokiyar zamansa, kamar dai Ammey na da Mommah, babban burin ƙishiya shine taji ana faɗar aibun kishiyarta, anan zaki ga har gyara zama take domin bada kanun labaran qarya da qaraiyari, kamar dai woni loqaci naje qiran da abbu yamin, ina dosar ɗakin naji abbiena yana faɗan ammey tayi masa ba daidai ba, amma cikin zallar makircinta take faɗin saidai haquri alhajis, danma ba kaine kake zaune da ita ba ta kaga abubuwan mamaki na ban al'ajabi da jin tsoron zamanta mata a gareka, saidai banzar bata sani ba duk acikin shirinmu ne nida abbiena! Dan duk abinda Mommah take muna sane da ita kuma loqaci muke jira kamar dai YAU! Dake a tsare a hannunmu. Qarqashin jagorancin shugabana Chief of army mai girma TAUFIQ NASARA shugaban sojojin Nigeria soldier THE ARMY and the COUNTRY as a whole tabbas yau burina ya cika dan ganin qarshen azzalumai da zalumcinsu!"
Inda abinda yafi ruɗu to tabbas jadderh ta shiga, jin mahaifin maleek shine Chief of army, cikin zallar madarar mamakinsa tace "kasan abinda kunnuwa suka jiye min kuwa RAYUWA TA!?, Jifa nayi kace"
Shiiiiii
Ya katse ta ta hanyar alamun tayi shiru da yatsansa daya mata.
Hakan yasa taja bakinta tayi shiru tana jan hannunsa zuwa gaban First aid kit tare da somawa maleek tritment na raunikan daYa samu.
*******************
Ummie dake tsaye har loqacin ayman bai dane rigima bane yasa ta ɗauki telephone dan qiran ɗakin maleek, a Kuma daidai loqacinne suke sauƙowa qasa tare da jadderhn tana riqe da hannunsa, zama yayi a ɗaya daga cikin kujerun parlourn yana amsan maleek a hannun ummie, lafiyayyan abincin da jadderh ta haɗa masa da kanta.
Bayan fitarsu da ammey ta shiryo masa cikin wormers masu azabar ƙyau da tsari, gefe guda kuma ga lafiyayyan kunun gyadar shin na gado, ganin hakan ne yasa ummie miƙew tsammm dan basu wuri ganin yau a parlour maleek zaiyi dinner, serving nashi ta shiga yi bayan ta kammala ne ta tura masa gabanshi, haɗi da qoqarin amsan ayman, hannuntan ya riqe dake qoqarin ɗaukar ayman ɗin.
Tare da jawota jikinsa yana ɗibar abinci yana nufar bakin ta tare da faɗin "Oya open your mouth", kanta ta noƙe tare da ƙin amsan abincin cikin ta ya shafa tare da faɗin "nasan wannan cikin harya zuwa yanxun baici komi ba tun safe ba dan haka ya zam dole na kula dashi"
Ganin da gaske yake ne yasa ta buɗe bakinta tare da fara amsan abincin, itama tana bashi ga AYMAN sai famar mutsuniyarshi yake irin na yara, dan yana cikin kwana na talatin da bakwai a duniya.
Harya faro wayo abinsa cikin sa yayi tsam tsamm abin gwanin ban sha'awa.
*🔥♥️ KAREN BANA ♥️🔥*

NA MARYAM NASEER MIRRAH ✍️
*Ammey laylerh*

Page 4️⃣3️⃣&4️⃣4️⃣

08104493215

✯D͟A͟Z͟Z͟L͟I͟N͟G͟ S͟✯T͟✯R͟'✯W͟R͟I͟T͟E͟R͟S͟
=======================

*~Why do some people not understand?,why the life of these people knows,why are we so quick to cut the person If you don't know him, you don't know how his life is?~*

Pls and pls for God to stop and fix his life, It's not like you stop watching someone else's life.

God is always the thing to be thankful for, and to you we extend our issues.
Allah ka iya mana badan iyawarmu ba🤲🏻🙏🏻

********************************
Washe garin wannan rana, haka gaba ɗaya labarin nan ya karaɗe social media, duk inda ka wuce zancen ne kawai ke faman tashi agarin na Abuja.
Kafin kace me kuma gaba ɗaya duniyar yanar gizo taci gaba da haskaka fuskar, TAUFIQ MAI NASARA mahaifi ga maleek wanda yake a matsayin Chief of army.
Kana kuma wanda akafi sani, da shahararren ɗan kasuwar nan na sarrafa motoci.
Wanda wani dalili nashi yasa bai taɓa baiyanarma duniya matsayin saba, yace ba suna ko matsayin yake da buqata ba, sabo da girman Allah yake komansa, wannan dalili yasa kowa yake ma Chief of army staff GENERAL ABDULLAHI BELLO makama.
Kallon shugaban sojojin Nigerian, wanda dukkan wani tsarin abubuwan dake gudana kuwa Alhaji taufiq mai Nasara shine ja gaba,kuma ragamar wannan tarin nasarorin da suka samu.

***********
Shi kansa Alhaji taufiq ya girgiza loqacin da ya gama kammala kallon gidajen talabijin ɗin da suka wannan bin nannen tsohon sirrin nasu.
Shi kuwa mai girma Abdullahi Bello makama yayi hakan ne dan nuna halaccin sa ga shugaban sa. Wato taufiq mai Nasara uba ga yaro mafi qazo acikin tafiyar rundunar sojojin Nigeria baki ɗaya.
Cikin zallar abinda yake yake zuciyar sa na alkhairinsa ga mamallakin, wannan jigo kuma jagora yaci gaba da bayyana ma duniya waye Alhaji TAUFIQ MAI NASARA.
Adalin shugaba

Gammmm ya rumtse idanunsa daidai wurin da GENERAL ABDULLAHI BELLO makama yake faɗin.

"Tabbas irin ka DUNIYARMU take da buqata generally TOUFIQ MAI NASARA! Kaida yaronka irinku duniyarmu muke da buqata Aiki domin sadaukar wa al'umma Rayuwa!"
"AIKI domin sanya ma zukatan bayin Allah nutsuwa!!

Please Login or Register in order to submit comment