Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

AMANA suka taru suka mata ƙawanya"
"HAƊAMA!"
"ZANBA CIKIN AMINCI!!"
"TARE DA RASHIN SON CIGABAN NA ƘASA DA KAI!, SHIN INA AKE WANNAN INBA WANNAN ƘASA TAKU TA NIJERIYA!!!"
******************
Kashim baba
_________________________

***Alhaji Atiku inason nanda kamar 2 weeks a kammala ginin asibitin Nan domin kayan suna nan tafe, kamar yadda nayi alqawarin buɗe wannan asibitin zanyi, ammafa talakawan Nan sai sun rena kansu, sannan inason awa waɗan nan yaran magana inason sushigo da waɗannan kayan nawa na ƙasa...

Kitt ya kashe wayar dake manne da kunnensa.
Amaryarsa dake tsaye daga bakin ƙofar shigowa ne ta kafeshi da id0 mene takeji haka ne kunnenta suke shirin jiye mata.
Sai kuma tayi saurin shigowa cikin ɗakin kafin ya ankare da ita, gabansa ta ƙara so tana dire cupcakes ɗin daya buƙata da takawo masa, zama tayi kusa dashi tana ɗaukar yaronta daya fara qinqishin kuka sai kuma ta tashi ta fice a ɗakin baki ɗaya, cikin rawar jiki ta shige ɗakinta tana laluben wata n0 acikin wayarta
Sir maleek ta shiga cikin contact ɗin sa ta fara tura message kamar yadda ta saba, bayan kuma ta gama tura message ɗin dani kaina bansan na miye shiba ta kashe ƴar ƙaramar wayar tana ɓoyeta inda ta ɗauko taaaaaaa

Too faa tirkashi mene yake shirin faruwa neeee kammmm yauuuuu🙃🥺 Amaryar Kashim baba???
~~~~~~
________________________
MALEEK JADDERH
*************************
Cikin gigicewar yanayi ta farka daga mummunan mafarkin da tayi, bayan barcin wahalar da ɗauke ta bayan komi ya lafa tsakaninta da maleek, MALEEK kuwa jin azababben ƙara da ihun da tasaki ne yafarkar dashi tare da adda'oi fall bakinsa, itama saita shiga nanata dukkan adda'ar da yake faɗa.
Kafin kuma ya janyo ta jikinsa yana ɗan bubbuga gadon bayanta. ahankali kuma ya shiga hura mata iskar bakinsa acikin kunnenta tare da adda'oin sanya nutsuwa da daidaita tunanin mutum....
Kafin kuma ya ɗan ɗago da kanta yana zubawa fuskarta id0, daga cikin yanayin da fuskar nata yake a cikine ya fashimci akwai firgici tare da ita, sai kuma kawai ya kifa kanta a tsakiyar ƙirjinsa da babu riga.

"Menene yake faruwa dake AYUSH?"

"Mene ya hassada miki wannan tsoro mai girman gaske haka?"

Cikin sheshsheƙar kukan dayaci qarfin ta tafara faɗin

"Nima bansaniba, bansan koo mee nee ba kawai dai nasan ina yawan mafarki da wata mata! daban ko wace itaba tana kuka tana faɗin nadawo gareta"

"Nice rauninta!"

"Nice rayuwarta!!"

"Nice duniyarta!!!"

Sai kuma taja numfashi tana ƙara tsananta qarfin kukan nata kafin taci gaba da faɗin

"Tunda kamin nasan mene mafarki nake mafarkinta nake mafarki da ita, amma bantaɓa ganin fuskarta a zahiri ba"
"Domin duk sanda zan ganta zangantane cikin matsanancin duhu kawai inajin kukan tane da kuma sunan da take ƙirana dashi"

*AYUSH"

"Bantaɓa jin wani mahaluki ya taɓa ƙirana da wannan sunan ba sai kai, na jirjiza ƙwarai dajin loƙacin daka fara ƙirana da wannan sunan, saidai ko kadan bantaɓa nuna maka hakan;"

"Kullum idan zangan cikin wannan baƙin duhun nake ganinta! Saidai idan nayi addu'oi sosaene nake ganinta durƙushe ta juya bayanta tana ta kuka, duk loƙacin da nayi yunƙurin zuwa gareta kuma sai naga tamkar ana janta kafin kuma ɓatt ta ɓacewa ganina!"
"Bantaɓa faɗa wa kowaba koda kuwa BAFFANANE da UMMIENA, kawai nabar abin a cikin rain"

"Sai dai yau naga zahirin fuskar matar da nake gani acikin mafarkina,sai kuma ta fashe da kuka tana ƙanƙame maleek"
"Wallahi nice kawai nagani me hakan yake nufi ya maleek?"
"Saidai ita tafini manyan taa da kuma jiki"

MALEEK wani matsanancin tsoron Allah ne ya qara shigarsa jin wata kudira ta Ubangijin sammai da ƙassae, jin wannan babban al'amari haka, cikin ruwan sanyi yake haɗa ƴa da uwaa ta mafarkinsu, ikon Allah ikon gaske lallea lamarin Allah girma gareshi, sai kuma kamar wanda aka zabura tsamm ya miƙe tsaye da ita a cikin jikinsa yana qarasawa gaban mirrorn ɗakin ɗaya daga cikin wayoyinsa ya ɗakko yana buɗeta tare da shiga cikin gellary, cikin wata ɓoyayyiyar folder ya shiga wacce wani mayen sucurity yake akan folder ɗin, cikin fakar idanunta yayi saurin loda sucurity ɗin wani photo ya ɗauko tare da kawoshi dabb da fuskar JADDERHN.
Zabura tayi tana warce wayan a hannunsa ta zubawa photon qawawan idanunta babu ko qaftawa
" wallahi itace"
"kuma nice"
"Itace wacce nagani yau yanxuma"

"Dan Allah kasanta?"

"kasan inda take?"

"Kasan wacece ita ka kaini wajenta, nidai inason ta ko bansan ta ka kaini wajenta kaji ya maleek !" Ta faɗi hakan tana duban maleek ɗin da yayi mutuwar tsaye.
Sai kuma ya janyo ta jikinsa yana mata kyakkyawar runguma, sai kuma kawai ya sake ta ya faɗa toilet idanunsa ya kaɗa yayi jajur dashi, sai yanxun sai kuma yau yake tabbatar da tausayinta da yakeji yafi na kullum, haka ya sakarwa kansa shower ruwanda da azabar sanyi ya shiga dukan gangar jikinsa tamkar marar hankali yanaji yana gani haka ruwan sanyin nan ya ringa dukan gangar jikinsa da kansa, jadda kuwa a gurin ta durqushe tana risgar kuka, kuka take tamkar ranta zai fice.
Kukan da take yine na fitar rai ya ankarar dashi a qiɗime ya kashe showern tare da ɗaukar bethrobe yana ɗaurawa ya fito da mugun sauri.

A durƙushe ya ganta ta haɗe kai da gwiwa tana risgar kukan fitar rai kukan da batasan na minene kukan ta taji kawai zuwar mata yayi. Da sassarfa ya qaraso gabanta a sukwane ya isa gabanta haɗi da amshe wayan a hannunta baisan yanda zaiyi da ita bane, hakan yasa kawai yayi cikin toilet ɗin da ita yana shiga ya sakar musu ruwan showern tare duguwar rigan dake jikinta marar hannu mai shara shara ya sutale mata yana mannata da qirjinsa, kanta ta kwantar akan qirjinsa nasa tana sauƙe ajiyar numfashi, sun daɗe a hakan kafin kuma ya kashe musu showern tare da yi musu wankan tsarƙi haɗi dana sabulu ya fito dasu tana manne da jikinsa, domin kuwa cikin babban towel ya naɗosu a ciki, akan mirrorn ɗakin ya tsayar dasu tare da fara busar mata da gashin kanta kafin shima ya busar da nashi manshafa da wasu lotions masu daɗin qamshi ya shiga shafa musu.
Gaban wardrobe yayi da ita cikin dogwayen rigunanta ya zaɓo mata wata ruwan zuma mai ad0n duwatsu sosae like kuyi emeg nata kawai haɗi da bra da pant ya ajje mata a gefen gado shima ya zaɓo wata da kakkiyar shadda kalar sararin samaniya, domin yana masiyar qaunar colorn a gurguje suka shirya kana yace mata ta zauna ta jirashi yana xuwa.....
Kai tsaye yana fita sashen mahaifinsa ya nufa bayan yaje sun gaisa kuma ya nufi sashen ammeyn sa tare da tura qofar falon. ahankali yashiga cikin falon tare da sallama abakinsa, cikin girmamawa yashiga gaida mahaifiyar tashi cikin sakin fuska take amsawa tana hango wani irin ɓoyayyen annuri tattare da yaron nata, Ita dai kawai tsintar kanta tayi dayin hamdala ceen qasan zuciyarta, bayan sun gama gaisawa ne yace yana buƙatar zantawa da ita, batayi musu ba tace tana sauraronsa.
Babu musu kuwa ya fara jero mata bayanan daya kusan tarwatsa mata ƙwaƙwalwar kanta haɗi da wani azababben shoking ɗin daya ziyarceta loqaci guda, gumine kawai yake ta faman tsirgo mata,
"Ya ilahi MALEEK duk ina ina akayi wannan ɗin"
Sai kuma tashiga faɗin "innalillahi wa'innah ilaihir'raji'un innalillahi wa'innah ilaihir'raji'un"

"Kasan kuwa mai kake faɗi MALEEK jinin sarki ABDULPHATA OMAR nake tare dashi amma bansani ba?"
"Bayan kuma kai kasa Ni amma ka ɓiyemin kamin daidai kenan yanxu BABANA?"
Sai kuma idanunta suka tara kwalla kanta tashiga girgizawa tana faɗin.

"Tabbas biri yayi kama da mutum!"
"Tun ranar dana ɗaura idanuna akan yarinyar naji ta kwantamin! Ban ƙara tsinkewa ba saida naji maganar yarinyar, nasan tayin kama da wata ko wani wanda nasani, saidai kuma na manta ina ' a inane jin muryarta kuwa saidai naji gabana ya faɗi" kuma tabbas mai martaba sarki maleek nafashimci hakan a tattare da shi;"
"Ya Rasulullahi Manzon Allah"
"Yanxun dama jinin MARYAM ABDULJALAAL yana raye a doron duniya lallae waɗanda suka aikata wannan abu sun ciki marassa imani na gasken gaske, kuma insha Allahu Allah bazai taɓa barinsu haka baaa, yanzu dama JADDERH jinin ɗan ɗan uwanane
ABDULPHATA OMAR"

JADDAH da taji zaman qaɗaicin ya ishe ta ne yasa tayo ɓangaren ammeyn jin kuma kamar suna maganane kuma maganar ta danganci sirri ne yasa ta juyawa zata koma jin kamar an ambaci sunanta ne, yasata tsayawa, dumm dumm gabanta yabada wani irin sautin tsoro jin qarshen zancen ammeryn da kuma maganganun qarshe na MALEEK wanda bataji kuma nima mai dauko musu rahoto ba bansamu jinsuba....

Jin wani irin masifaffan jiri yana naiman Kaita qasane yasata ƙoƙarin shigowa Cikin falon saidai inaaaaa....
Bata samu damar hakan ba domin kuwa luuuuuuu tatafi ta zube ƙasa sumammiya, jin kamar alamar qarar faɗuwar abune yasa tsakanin MALEEK da Ammey har rige rigen fita suka domin ganin maine ne hakan.
Ganin JADDAH zubeeee a ƙasa babu alamar numfashi tattare da itane yasasu mutuwar tsayee,,,

Tofa mene yake shirin faruwa da mune haka

Kadai kuci gaba da nuna ɗinkin yadda zata kaya


Byyyyyyyyeeeeee kubuta lfy sai zuwa dare idan Allah ya bamu Aran rannn




*By Ammey laylerh 💔*
*🔥💔 KAREN BANA 💔🔥*


NA MARYAM NASEER MIRRAH ✨
*Ammey laylerh*

Page 2️⃣9️⃣

08104493215


The world is not paradise , May God continue to enlighten our affairs In happiness and peace Alhamdulillah ya rabb🙏🏻🙏🏻🙏🏻👏🏻👏🏻
_________________________
********


____A sukwane sukayi kanta gaba ɗayansu cikin wani irin tashin hankalin da suka jima basu riski kwatankwacinsa ba, ammey ce ta shiga girgizata kafin maleek ya sureta wanda tashin hankalin da yake ciki ya zarta misaltuwa kai tsaye kuma saman sopa ya nufa da ita yana zama akai tare da ɗaurata saman cinyarsa, cikin zallar kiɗima ya fara shafa saman kyakkyawar fuskarta tare da soma hura saman fuskarnata, ammey ce ta zo da ruwan me tsananin sanyi tana ƙarasowa garesu da ɗebo kaɗan a tafin hannunta, ta shafo dundaga saman fuskarta har zuwa gefen wuyanta, amma ko gezau bata yiba haka ammie ta shiga shafa mata ruwan Nan amma inaaaaaaa. bata da alamun farkawa shi kuwa maleek ganin taƙi farkawa ne yasa baimasan loƙacin daya nemi bakinta ba ya haɗe da nashi, yashiga zuƙo mata numfashinta, babu jima kuwa ta sauƙe wani irin wahalallen numfashin azaba, atare maleek da Ammey suka sauƙe numfashi sunawa Allah godiya.
Bayan tunani da kuma nutsuwar ammey sun dawo gareta neeee yasata laluben wayarta tare da dannawa *FATHER* ƙira saida ta gama ring ɗin ta kafin ƙiran ya katse, atake kuma wani ƙiran ya biyo baya kamar yadda ya saba, cikin azama ta ɗaga wayar tana karawa a kunnenta, cikin yanayin da take cikine yasa kawai fara faɗin "FATHER hasashe da tunaninika sun tabbata yau ga jinin MARYAM ABDULJALAAL tare da sarki ABDULPHATA OMAR a raye FATHER JADDERH itace itace itace wllh itace AYUSH ɗin mu mai suu naa naa" ta faɗi kalmomin ƙarshen ararrabe.

*****************

Wani irin cool smile sarki maleek ibn suffyan ya saki tare da daɗa gyara kishingiɗar da yayi akan kilisarshi, sai kuma yace mata.
"Nadaɗe da sanin hakan AYSHA na daɗe da fashimta" kitt ya katse ƙiran yana maida akalar ƙiran zuwa ga wata n0 wacce sunan ABDULPHATA OMAR ya bayyana akan screen ɗin wayar nashi.


____________________
ADAMAWA
*********************
Sarki ABDULPHATA OMAR yana kishingiɗa saman sopa gaba ɗaya abubuwan duniya sungama chaza masa kai.
Banda rigimar MARYAM da saida aka kai ruwa rana kafin yasamu ya shawo kanta, kan dole saiya saketa tabar 9j tunda ba amfanin zamanta haƙurinta yakai mazawar da bata cigaba da ganin abubuwan da suke faruwa da rayuwarta ba, saidai idan ta koma MADINA habebty tayi bandarta ta cinye ɗanya.
da ƙyar ya samu ya shawo kanta kafin ta haƙura, yana tsaka da wannan tunaninikan yaji busar sarewa na tashi cikin wata irin nutsuwarsa ya ɗan lumshe idanunsa tare da buɗesu ahankali, gabansa yaji yaɗan faɗi kaɗan jin irin ringtone ɗin dake tashi, domin yasan mutum ɗayane mamakin wannan ring ɗin, kawai yaji ya tsinci kansa cikin fargaban da baimasan yana da itaba.
Cikin sahalewar zuciya kuma ya janyo wayar nashi kuma yana amsa ƙiran ɗan uwan nashi, jin kuma muryar ɗan uwan nasa cikin yanayi na daban neeee yasa yadanji releif kaɗan.
"ABDULPHATA OMAR idan har babu damuwa inason kashigo Kano Amma tafiyar ta kasance ta SIRRI sannan ka taho da MARYAM ABDULJALAAL idan har hakan ba takurawa atsakani"
sai kuma ya shiga sauƙe ajiyar zuciyar irin wannan dogon jawabin da yayi.
Cikin yanayin daya gaza gane kansa Sarki ABDULPHATA OMAR ya shiga taune gefen laɓɓansa, yana ambaton sunayen Allah, cikin wata iriyar ginshira ya shiga ƙoƙarin tattaro kalmomin da zai samu ya bawa ɗan uwan nasa amsa, amma inaaaaaaa kawai hakan ya gagara, Tamkar kuma ya kwato maganar ya furta "zanZo" kitt ya katse ƙiran tare da kife hannayen sa akan kyakkyawar fuskarsa mai yanayi data JADDAH, saidai ita kuma tafi kama da mahaifiyarta amma exctly komai da komai na yanayinta SAKK na Sarki ABDULPHATA OMAR.
_______________
Wani irin kyakkyawan murmushi sarki maleek ibn suffyan yayi, jin irin amsar ɗan uwan nashi kuma babban abokinsa ya bashi, yasan duk yadda yakai gaji da mulkinsa to Sarki ABDULPHATA OMAR ya dameshi gaba da baya, domin shi hatta magana bai fiye yiba yafi gane speech of the deaf maganar kurame.

******************-

MARYAM ABDULJALAAL tana zaune akan shimfiɗeɗiyar dardumarta tana sallar nafila,...... ya shigo cikin izza irin ta masu mulkin da suka gama sanin kansu da kansu kana wanda jinin mulki gaba da baya suka gama ratsa shi.
Ɗaya daga cikin kujerun ɗakin nata ya nema ya zauna ya zuba mata idanunsa masu sanya nutsuwa yana kallon ta cike da S0 da kuma tsantsar ƙauna gami da burgewa yake kallon ta.
A duniya gani yake inba ita to kuwa rayuwarsa ta gama tashi a aiki domin itace komi nashi, idan yace komai to kuwa yana nufin komai ɗin,..... bayan idar da sallar nata tayi ƴan adda'ointa tare da shafawa atare suka shafa ita dashi dake zaune, ko kallon sa besamu tayiba bare kuma yasa ran zata masa magana, dama yasan za'a rina wai ance da gwauro ya iyali.
Tsammm kuwa ya miƙe tsaye yana nufo bakin gadon data haye tayi kwanciyarta ta juya masa baya.
Zama yayi daga bakin gadon yana tattare mata bakin lafayarta tare da ɗan juyo da ita zuwa gabansa suna fuskantar juna, fuskarta ya ɗago yana S0N su haɗa id0 amma taƙi bashi damar hakan, dan tasan shine abu mafi rauni gareta kallon cikin kwayar idanunsa, gane hakan da yayine kuma yasa cikin muryarsa daba kowanne mutum ne yake da ik0n ji bane ya furta mata "idan kin gama fushin naki sarki maleek ibn suffyan ya buƙaci muje Kano a yau, dan haka kitashi kishirya yanxun sannan fitar ta SIRRI ce ko mutanen gidan ban yarda dasu san da wannan tafiyarba"
Yana gama faɗin hakan ya fice abins@' cikin matsanancin tsoro da kuma jin wani abu daga ƙasan zuciyarta mai kama da wani abu na daban, ta tashi tana nazartar kalaman na ƙiran yayan mijin nata kuma baban babbar ƙawarta wanda da kaff duniyar bata da kamarta amma sama taka suka naimi ƙawance nasu suka rasa, amma ta gaza gano komaine yasa dole haka ta haƙura.
Tare da fara shiryawa cikin gaggawa kafin kace meee harta gama shirin nata tana nan zaune kuma mai martaba sarki ABDULPHATA OMAR ya shigo shashin nata ta wata ɓarauniyar hanya wanda babu wanda yasan da wannan harya sai shi sai ita, cikin shirin fita ya shirya kansa cikin wasu ƙayatattun kaya na gani na faɗa atare suka nufi wata ƙofa kuma ta daban tare da barin ɗakin baki ɗaya, haka suka dinga tafiya cikin wannan hanyar kafin su sami wata ƴar siriryar hanya su fita tacen bayan gidan sosae.

Kai tsaye inda privete jet ɗin sa ke fake suka nufa, bayan sun shiga ne kuma jirgin nasu ya kula sama sai Kano.
Cikin ƙanƙanin loƙaci suka isa Kano lafiya, daga cen kuwa shima mai martaba sarki maleek ibn suffyan ya shirya fitar sirrin shida uwar gidan sa Fulani mahaifiyar ga AYSHA GALADIMA wato mai martaba sarki maleek ibn suffyan kenan.
A wani keɓantaccen guri suka haɗu kai tsaye kuma cikin jirgin suka shige, tare da lulawa Abuja Birnin tarayya.

~~~Ana ƙiran sallar la'asari suka sauka Lafiya hakan yasa suna fitowa daga cikin jirgin suka shige cikin masallacin, suka mayan suka shige cikin gidan Alhaji TAUFIQ




Muje zuwa danjin yadda zata kaya*🔥💔 KAREN BANA 💔🔥*

NA MARYAM NASEER MIRRAH ✨
*Ammey laylerh 🫶🏻*

Page 3️⃣0️⃣

08104493215


*I really have no words to thank you for You are my world, my parents, my pride May God bless my father and may he rest in paradise*

*But I say that God will reward you with the house of Jannatul Firdausi*

*Alhamdulillah they are blessed May God bless you and give you the opportunity to take care of your baby safely and peacefully , marry them and give them peace with the blessing of the leader of God's work*
___________________


____Ana ƙiran sallar la'asar suka sauka lafiya,hakan yasa suna fitowa daga cikin jirgin suka wuce masallacin ƙofar gidan,sukuma matan suka shige cikin gidan Alhaji TAUFIQ ɗin...Fulanice agaba kana MARYAM ABDULJALAAL tana biye da ita, kai tsaye bangaren AYSHA GALADIMA suka nufa
Aɓangaren MARYAM ABDULJALAAL kuwa duk taku ɗaya da zata taka acikin gidan tanajine tamkar ranta take takawa saboda tsabar tsinkewar zuciyar da take ciki, wanda ta rasa na mene tsinkewar zuciyar. tana daurewane kawai gudun kada Fulani ta fashimci halin da take a ciki, ji take tamkar wani abu gagarumi na shirin faruwa da rayuwarta ko kuma yana shirin tarwatsa duniyarta kai harda ma rayuwarta cikin yanayin da takejin kanta cikine yasata soma ambatar sunayen Allah a cennnnn ƙasan zuciyarta cike da fawwala Allah al'amuranta.
Cikin ikon ubaniji kuwa taji sauƙin beating ɗin da zuciyar nata ke ciki Nan taci gaba da kamo sunayen Allah saman laɓɓanta, doguwar riga ce ajikinta baƙa wuluk kana ta ɗora lafaya akai tun daga saman kanta har zuwa ƙasan kafafunta sai niƙaf da ɗora saman kyakkyawar fuskarta, wannan shine dalilin da yasa kyakkyawar fuskarta ɓoyuwa, cigaba suke da tunkarar ƙofar palon ammeyn ita kuma baiwar Allah Maryam taka ƙafafunta kawai take domin zuwa yanxun da suke dab da shiga cikin palon gidan taji zuciyarta tayi wani irin tsalle haɗi da wani irin bugu a cikin ƙirjinta, idanuwanta ne suka soma lumshewa da buɗewa daidai loƙacin kuma Fulani ta tura ƙofar palon ƴar nata.
Tana zaune akan darduma wanda dukkan alamu suka bayyana cewa sallah tayi take kuma zaune a akan dardumar, ƙafafuwan ta a muƙi kan jaddah ɗore a saman kafafun nata,..taji jin kamar motsi ajikin ƙofar palon nata ne kuma yasata ɗago da kanta, wanda hakan yayi daidai da loƙacin da MARYAM ABDULJALAAL ta ɗage niƙaf ɗin ta xuwa saman kanta, a kuma daidai wannan loƙacinne JADDERH dake kwance saman ƙafafun ammey ta juyo da fuskarta zuwa ɓangaren dasu Hajiya maryam suke, atare JADDERH, MARYAM ABDULJALAAL, AYSHA GALADIMA, da kuma FULANI kowa ya shiga nuni da abinda ya kusa tarwatsa kyanyarsu.... kafin kuma maryam abduljalaal tayi baya luuuuuu zata faɗi, a kuma daidai loƙacin dasu mai martaba sarki maleek ibn suffyan da sarki ABDULPHATA OMAR suka is0 cikin palon wanda Alhaji taufiq ya musu jagoranci zuwa cikin palon ammeyn, da wani irin mugun sauri sarki abdulphata Omar yayi saurin taro matarsa dake ƙoƙarin sumewa hankali tashe sarki abdulphata Omar yashiga jijjigata tare da faɗin "mine ya ruɗar take har haka?" "Mene ya firgitaki har haka NOOR?"
"Wanda abu kika gani ko aka miki da yasaki shock irin haka loƙaci guda?" Kafin kuma yaci gaba da jijjigata tare da shafa kyakkyawar fuskarta, kafin kuma ya ɗago kansa zuwa mutanen falon, shima ganin nashi ne ya sauƙa a inda matar tashi da sauƙe ganin nata itama harya firgitata loƙaci guda, Azabure ya miƙe tsaye yana nuni da yarinyar da id0nsa ya sauƙa akanta.
"A! AH!! AHS!!! AYSHA" ya fusgi maganar domin wani irin mugum lugude da hautsinin da zuciyarsa take ciki,....jaddah da tun farkon shigowar waɗannan bayin Allah suka shigo take binsu da tun tana ji da ganin abinda yake faruwa da ki da ki harta daina fashimtar komi ta sume amma babu wanda ya lura da hakan.
Kowa ya kasa uhmm bare uhmm uhmm, sallamar MALEEK ne kuma yaja hankalin gaba ɗaya jama'ar dake cikin ɗakin, hankali tashe ummey da tun shigowarsu ɗakin idanunta suka sauƙa akan jaddah dake kwance a kuma sumeee da alama ma babu wanda ya lura da suman da tayine yasata nufar gurin jaddan cikin kiɗima.
Tana zuwa batayi wata wata ba ta ciro kanta daga kan ƙafafun ammeyn tana mayar mata gurbi da nata ƙafafun,sai aloƙacin kuma mutanen palon hankalin su ya dawo kan mutane biyun da suka shigo tare da maleek ɗin kuma baƙin fuskoki.
Amma banda sarki maleek ibn suffyan domin yariga da yasan dasu da kuma xuwansu, dan shine ma yasa maleek yaje ya ɗauki su a privete jet ɗin maleek ɗin,...kasan cewar sa PILOT matuƙin jirgin samane amma sammm baya ƙauna ko koɗan yafi son aikinsa na SOLDIER sama da PILOT ɗin, amma idan buƙatar hakan ta taso yakan tuƙa jirgin kamo daga Nan gida ko wurin aikinsu.
Idan tafiyar gaggawa ta kamasu yakan tukasu...sosae hankalin mutanen falon ya dawo kansu ummeyn tare da malam Abdullahi, maleek dake tsaye hannuwansa sarƙe a kafadunsa ne yayi ƙoƙarin zuwa gaban fridge ya buɗe ya ɗauko ruwa mai tsananin sanyi yana zuwa ya yayyafawa maryam abduljalaal tare da jaddahn.
ajiyar Habebty ta sauƙe tare da ƙara rumtse idanunta fatan ta da burin ta bai wuce ace yau mafarkin Nan nata ya tsaya iya nan ba tanason yaukam suyi magana acikin mafarkin da tasaba na ƴar nata, saidai kuma jin ƴar hayaniyar su ammey da suke hamdalar ganin ta buɗe idanunta ce yasa taji wani tukuƙin bala'i tsaya mata arai.
Sai kuma ta buɗe idanun nata wanda suka kaɗa sukayi jazur dasu, ganin dai tabbas ta buɗe idanun nata ne kuma ta kuma ganin wanda ko tantama babu gudan jinin tace yasa a sukwane tayi kan jaddah tana farɗeta daga cikin jikin ummey tana rungumeta tsammm acikin jikinta, sai kuma hawaye sharrrr suka shiga sauƙa asaman fuskarta,...sai kuma ta fara magana cikin sheshsheƙar kukan dayaci qarfin ta.
"Me yasa? Me yasa kuka rabani da gudan jinina? Mafi soyuwa acikin duniyata mene mai muku?!!! dana cancanci wannan muguwar sakayyar daga gareku kodan kawai s0n wani cik0n muradi naku marar tabbas marar ɗorawa!¡!"
"An ha'inceni anci amanata anrabani da duk wani sukuni na rayuwa shin dukk akan abin duniya ne kuke wannan abunnnn; bayan kunsan idan akan abin duniyar ne be shafeni ba! Bayan kuna da tabbacin cewar ba daga gidan tsiya na fito ba..."
"Muna da tarin dukiyar da kaff ahalinmu na MADINAH babu wanda yasan iyakar arzuƙin da iyayenmu suke dashi. kuma nasan ku ɗin ba akan komi kukamin hakan ba kuka rabani da rayuwata saidan kurayu da arziƙi iya kar ku! Meya hakan mene kuka aikata kenan?"
________

Gaba ɗaya jama'ar falon babu wanda ya iya furta komai face idanuwa da suka bita shi, ummey kuwa kusan mutuwar zaune tayi dan ganin wannan bahagon al'amari dake shirin faruwa dasu, jin Muryar matar kuma shine yaƙara rikita ta tare dasa mata wani irin tsoro mai tsananin gaske.
Ammey kuwa cikin ƙarfin hali ta matso kusan da FRIEND tare da ɗora hannun ta saman shoulder ɗin friend ɗin, jin hannun mutum kuma saman shoulder nata ne kuma yasa ta ɗago kanta domin ganin waye ya riƙe ta haka, cakk kuma ta dakata tas0n zancen da takes0n furtawa, ganin AYSHA MALEEK IBN MALEEK ce dafe da kafaɗarta hawaye shaɓe shaɓe saman kyakkyawar fuskarta, cikin wani irin sanyi da ammey ta tsinci kanta aciki ta farawa aminiyar Tata ta gani kasheni amma ADA CENN shekaru masu ɗan dama wanda aloƙacin tana ɗauke da cikin dake jikinta na jaddan wanda tayi ma ƙawar Tata alƙawarin zata sanya mata sunanta indai mace ta haifa za kuma taba MALEEK aurenta wanda loƙacin yana ɗan shekara goma sha biyu, amma sama ta ka kowannensu ya manta, da ɗan uwansa babu dalilin komi amma kowa yanajin kewar girman abotar dake tsakanin su.idan kuma suka zurfafa da tunanin junansu sai suji kansu yaɗaure da tsanin azabar ciwo tamkar zaya rabe musu gida biyu......

Ammey ce cikin sanyin da dake ciki ta shiga faɗin "kiyi kuka Maryama idan da abinda yafi kuka yau kiyi shi kiyi abunki FRIEND domin nafi kowa sanin ancutar da rayuwarki, bansan meye yasa ba ban sani ba bansan abinda ya raba girman abotar dake tsakanin muba MARYAM. kawai na tsinci kaina da mantawa dake da kuma kasa zuwa gareki,

Please Login or Register in order to submit comment