Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na damuwa diyana, zanyi tunani a kai dole na nemo mama inda zamuje chewar hiyana da sauri lamrat tace "to ko zamu nemo addan (yaya) bappa ne ba yataɓa faɗa mana yana da adda ba (yaya)
Hiyana tache "to ai na zamuganta kenifa baruwana da kowa, yauwa birni zamu tafi muje munemi aiki har musamu kudi
Taɓe baki diyana tayi tana faɗin to yanzu muda bamu san hanyar birni ba ta ina zamu tafi, karfa mu bar gidan nan muje mu haɗu da masu yan kan kai suyan ke mana kai, da sauri Amrat tace "wlh bappa yataɓa faɗamin akoi masu yan kan kai a birni, kara zaro ido lamrat tayi, tana faɗin "tab nikam ba zanje ba wlh gara na zauna a nan ta karisa maganar kamar zatayi kuka, kallon hiyana diyana tayi tace "to yanzu ya zamuyi Shiru hiyana ta ɗan yi kafin tace ke dai karki damu zansan yazamuyi, yanzu kan mu kwanta muyi barchi, da safe in munje ɗeban sai mukarasa maganar a rafi, har suna haɗa baji wajen chewa to

Suna kokarin kwanchiya kenan sukaga inna ta faɗo musu ɗakin kafin su ankara tafara sauƙe musu bulalun hannun ta ajiki, bugun su taƙe tana faɗin "buba ne bakiso ko to wlh koki mutu ko kiyi rai sai kin auri buba daga yau ba mai sake fita a gidan nan a chikin ku rufe ku zanyi a dakin nan ke hiyana gobe za'a kai ki gidan buba kukuma sauran yin'wache zata kashe'ku a chikin dakin nan dan kulle'ku zanyi ba inda zaku sake zuwa
Kuka suke sosai sun manne da juna diyana da hiyana sun haɗu sun karewa lamrat da Amrat ajikin su kawai bulalan ke sauka, inna kuwa bugun su take baji ba gani da iya karfinta,sai da ta farfasa musu jiki tukun nan ta kyalesu ta fiche daga ɗakin, kankame juna sukayi suna kuka a haka barchi ya ɗauke su


Kano ta dabo

Ammi na zaune a gefen katafaren gadan Abba shi kuma Abba yana kwanche a nitse da sanyayyiyar murya tace "ranka yadaɗe inasan muyi magana, mikewa Abba yayi daga kwanchiyar da yake ya zauna yana fiskantar ta "ina jinki Aishstu na manene yayi maganar yana kallan chikin idon ta, kasa da kai Ammi tayi chikin ladabi da girmamawa ta fara magana " daman inasan zuwa Yola ne wlh kwana biyun nan,bana jin daɗi ina ganin kamar akoi damuwa ina yawan mafarkin Ahmadu kasan shi ya ragemin kuma gashi na yaddashi, abun yana yawan damuna sosai, inajin a jikina kamar Ahmadu na chikin damuwa,tunaninsa har tafara yimin yawa, dogon numfashi Abba yaja kafin yace "ba'damuwa Aisha ae kin jima baki jeba kusan shekara 7 ke nanfa gaskiya yakamata kije, ki shirya sai kuje da su Safras su rakaki
"da murna Ammi ta juyo ta rungumi Abba tana faɗin ilove U ilove U
rungumeta sosai Abba ma yayi yana faɗin "eyeeee yau kam ba fullanchi ke nan,kara shigewa jikinsa Ammi tayi tana murmushi


( Nikoh nache oh ka jimin tsofaffin nan gaskiya Abba da Ammi kuna shaaninku tsufa bata hana soyayya)


Misalin karfe 4 na yamma gaba ɗaya ilahirin family alhaji Abubakar saraki ne zaune a fada
Abba na zaune a kugerar sarauta gasu, Ammi a gefensa gefe guda kuwa sarkin fada'ne dasu waziri ga uncle Aliyu ma a gefe DON da Aryan suna zaune saman sofa mai ma zaunin mutun 2 duk kansu fiskokin'su babu alamar wasa a ɗaure taƙe tam kamar basu san menene dariya ba kallo ɗaya zaka musu ka gane suna chikin baƙin chiki, Khalid da Yusuf suna zaune suma a saman sofa ɗaya mai ma'zaunin mutun 3 ko ajikin su sai ma murmushi mugunta da suƙe wa DON da Aryan

gyaran murya Abba yayi yafara magana a nitse gaba ɗayansu suka tattara hankalin'su suka maida kan Abba suna sau raron'sa
" Dalilin dayasa na tara'ku inason sanar daku lokachi yayi da zan sauka a kan kujerar murki in mikawa ɗana Safras asukwa'ne DON ya ɗago kamar zai yi kuka nan take fuskar sa ta sauya sosai jiyake kamar yayi ihu shi gaskiya baya san mulki ai sojan shi kawai yake so, chigaba da magana Abba yayi "gaba ɗayan'ku ina mai baki umarni ku'nemi transfer a wajen aikin'ku kudawo kusa dani kuchiga da aiki a kasar ku Aryan Ahmad Aiman Khalid Yusuf a sukwane suka ɗago suna kallon Abba, Abba ko ajikinsa sai ma chigaba yayi da magana,"yau azumi saura wata 2 bayan Sallah da sati 1 zan sauka daga kan kujerar mulki na a naɗa sabon sarki Safras, buɗe baki DON yayi zai yi magana sai idon sa ya sauka a kan face ɗin Aunty farida, girgiza masa kai tayi alamar yayi shiru kar yayi magana shiru yayi, yafasa maganar ya mai da kansa yana kallon kasa, "akoi mai magana a chikin kune chewar Abba yayi maganar yana kallon fuskokinsu shiru sukayi gaba ɗayansu Almost 10mnt ba wanda yayi magana "ok tunda bakuda magana kutashi kuje sai bayan Sallah da one week

Da sauri DON ya mike ya fice daman kamar a kan kaya yake da sauri Aryan ma ya miƙe yabi bayan DON da ɗai da ɗai suka watse kowa yayi nasa ɓangaren

Aunty amarya na fita tayi part nata sai huchi take, tana shiga ɗaki ta ɗau wayarta tafara neman hajiya sadeeya, bugu ɗaya hajj sadeeya ta ɗaga tana faɗin hello aunty amarya tache "hajjiya sadiya kina ina "ina nan kano mana meyafa "akoi matsala hajj ya sadiya ae bama abun da bai faruba, kinaji wai Safras za'a bawa mulki ba Aryan'ba "what? gaskiya bazai yiwuba dolene musan abunyi wlh dole Aryan ne zai karbi mulkin nan karki damu gobe zanzo mu tattauna chewar hajj sadiya "to shike nan sai najiki amma dan Allah kiyi sauri dan jinake kamar zuchiyata zata buga "kar ki damu hajj Hajara ae damuwar ki damuwa tache inshaa Allah zan shigo da wurima,"to kawai Aunty amarya tace san nan ta katse kiran ta haye gado tanata kunkuni

Zaune yake a Katafaren palon sa saman sofa mai mazaunin mutun 3 yana fuskan tar sofar da Aunty farida ke kai a zaune ga Aryan zaune a gefensa sun zubawa Aunty farida ido, Khalid da Aiman suna zaune saman sofa mai mazaunin mutun 2 sai Ahmad da Yusuf suma a kujera ɗaya suke zaune dukkansu sunyi shiru sun zubawa Aunty farida ido suna jiran suje me zatache ita maɗin dai shiru ta zuba musu ido DON ne ya katse musu shirun da chewa "Aunty farida yanzu me mafita wlh bazan iya rike mulkin nan ba, mulki baya chikin tsarin rayuwata aikin sojana kawai nakeso bayan shi bana bukatar wani abukuma,dogon numfashi Aunty farida taja kafin tache "kar'kadamu nan da bayan sallah fa Abba yache kaga da ɗan sauran lokachi zamu shawo kansa a hankali, shiya dazun na hanaka magana domin kuwa kokayi magana ba sauraran'ka zai yiba amma zansan yadda zamuyi kafin lokachin inshaa Allah ka kwantar da hankalin'ka duk yadda zanyi naga ba'a baka mulkiba sai nayi, da sauri Aryan yache "dan Allah Aunty farida kada'fa kibari idan Abba ya yarda akan bazaa bawa DON mulkiba Ni kuma a dawo kaina, dan Allah kar'kibar hakan tafaru,wlh nima banaso mulkin nan a bawa Aiman ko Yusuf " da sauri Aiman yache "tab wlh banaso sai dai Yusuf, wani harara Yusuf ya wurgawa Aiman kafin yace kaima dakake likita kache bakaso to inaga ni soja kuma me soja zaiyi da wani mulki sai dai abawa yaya Khalid ko Ahmad, da sauri Khalid ya buɗe baki zai yi magana, Aunty farida ta dakatar dashi da chewa "a'a Me abun rigima bayan ga uncle Aliyu yana nan da ransa ae shi yadache ya karbi mulkin "good my lovely aunty ina sanki wlh akoi ki da basira chewar Aiman harara wasa Aunty farida tamasa zatayi magana sukaji sallama
Dukkan su suka juya da gudu Aunty mardiya tazo ta rungumi Aunty farida tana faɗin "nayi missing naku sosai Aunty farida tache "sai yanzu kuka iso "eh yanzu shigowar mu Ammi ke sanar dani kuna nan Mikewa DON yayi shi da Aryan da Yusuf suka nufi hanyar betroom ɗin DON, jiki a sanyaye Aunty mardiya tache "bro kufa nazo gani ina kuma zakuje, tun bamu gai'saba tayi maganar kamar zatayi kuka,kuma dakaji muryan kasan a tsorache tayi maganar
Dukkan su ba wanda ya juyo bare ya tanka mata sukayi shige warsu chikin betroom ɗin, har ita kanta Aunty farida bataji daɗin abun da suka yima mardiya ba, a hankali ta dawo da kallanta kan Aunty Mardiya daniyar tabata hakuri, sai taga hawaye wani na bin wani a kan kumatun Aunty mardiya "kiyi hakuri Mardiya bai kamata kiyi kukaba duk da nasan basu kyau ta miki'ba amma kimu'su uzuri watarana sai lbr Chikin kuka mardiya tache "wai Aunty farida me namu'su ne dan Allah meyasa ni basa sona eh why? "suna sanki mana sudai haka halinsu yakene kawai amma suna sanki,wani dogon tsaki Aiman yaja kafin ya miƙe yanufi hanyar fita daga palon, chikin jin haushi Aunty farida tace "kai ina zaka kuma, a ta kaiche Aiman yace "ɗaki zanje batare daya jiya amsar Aunty farida ba yafiche da sauri, Aunty farida zatayi magana Ahmad ma yamiƙe da sauri yayi waje baki Aunty farida ta taɓe, girgiza kai kawai Khalid yayi ya mike ya dawo kusa da Aunty mardiya ya zauna yana bata hakuri, da kyar Khalid da Aunty farida suka shawo kanta tayi shiru, Aunty farida ta miƙe ta riko hannunta tana faɗin "muje ɗakin Ammi, koh, to kawai Aunty Mardiya tace san nan ta miƙe suka fice daga palon shikuma Khalid ya miƙe yabi bayan su DON ya shige chikin betroom ɗin shima,


Yola

Jama'a sun chika gidansu hiyana sai faman shirye shirye ake ga maza a kofar gida suna zazzaune a kan tabarma,liman ya miƙe yana faɗin "kowa ya nitsu yanzu za'a ɗaura Auren ina wali amarya daya daga chikin dattijan dake zaune awajen yace gani nan liman yace to ina waliyin ango Baban buba yace gani na to kumatso kusa zama malam liman yayi kana yache "malam audu kayarda kabawa dan wajen malam sani auren yarka hiyana malam audu yache...✍️


more comments an share
[7/3, 5:46 AM] Al~Quyraemey: *💫STAR LADY💫*

*DUK ƘARFIN IZZATA*

_💖Story And Written💖_
⬇️
*Star Lady*

Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawa

*Episode 6*


Malam Audu yace na..bai karisa ba sakamakon wasu If gudu Shahram da Abdol suka fito suka fara buɗe kofar motochin sai da suka bi kowani mota suka buɗe kofar san nan,suka dawo jikin motar su DON suka tsaya, a nitse Ammi ta sako kafarta waje kafin ta fito gaba ɗaya,sanye take chikin wata ɗankareriyar yace pink colour ɗinkin bubu wuyar ta da hannun ta sanye yake da ta sanya musu wani ɗankareren gold mai matikar kyau da tsada wani bakin al'khabba, mai shegen kyau an masa kwalliya da duwasu fari masu kyalli ta sa a kanta a mai makon mayafi bakaramin kyau tayiba inka ganta kache bata wuche 25 years ba a hankali kamar bata son taka kasa tanufi hanyar gidan su hiyana tazo dai dai zata shiga gidan sai kuma ta tsaya ta juyo tana kallon su malam liman, chikin ladabi ta gaida malam liman san nan tace "malam taron me akene haka, murya na rawa malam liman yace aure zamu ɗaura, to Allah yaba da zaman lfy ta kai karshen maganar tana shigewa chikin gidan tana tunani a ranta yanzu Ahmad zai kara Aure ne ko yasanar dani, zan haɗu dashine wlh, da sallama a bakinta tashigo chikin gidan nanfa kallo yadawo kanta gaba ɗaya matan dake chikin gidan suka zuba mata ido "sannun ku dan Allah ina habiba Ammi ta tambaya tana kallon fuskokin'su
inna na daga gefe a ɗan tsorace tamike tana fadin "gani nan lfy wacece ke,gyra tsayuwa Ammi tayi tace "Aisha che yar Ahmadu, baki inna tabuɗe "laaaa indo keche a lallai kinzo a sa'a yau ake bikin ɗiyar taki hiyana,daure fuska Ammi tayi tafara magana "hiyana kuma Ahmadu hauka yakene da zai aurad da hiyana yanzu kwata kwata nawa au shine naga jama'a a kofar gida, to bazai yuba wlh baza'a aurad da yarinyar nan nan zuba ina Ahmadu yake yazo ya mai da musu da sadakinsu dan wlh baza'a ae wan nan Aure ba Hons ni tafiya ma nazoyi dasu gaba ɗaya yaran, chikin tsawa inna tace "ke Indo kishiga hankalinki wlh banga uban daya isa ya hana a ɗaura Aure'n nan ba, Ammi chikin ta kai chi maganganun da Inna tamata ta kalli Inna daga sama har kasa kafin tafara magana "ke habiba ko Ahmadu bazai tsaya yana faɗamin magana ba amma yanzu zan nuna miki na isa bama a kan ƴa'ƴan Ahmadu kawai na isaba har, a kan shi Ahmadu da kansa ke, bintu fita waje kiche da Safras wan nan umarni'ne su watsa jama'a nan su dakatar da ɗaurin Auren nan,ta karisa maganar chikin fushi tana kallon kuyangun daƙe gefenta, da gudu bintu ta juya tanufi waje dan ta isar da sakon Ammi, wani tsalle Inna tayi ta damko wuyar rigar Ammi tana faɗin "lallai Indo kin manta wacece ni ke nan wlh kibar ganin kinyi Aure a birni yanzun nan sai namiki mugun duka, chikin fushi Ammi tace "habiba ki sakarmin wuyar riga habiba "Indo bazan sakiba wlh yau sai namiki mugun duka a gidan nan dan kin shiga abun da bariwan'ki, da gudu kuyangar dake gefen Ammi tafita waje dan ganin abun da Inna ke kokarin yi, hannu Ammi tasa tana kokarin chire hannun Inna daga wuyar rigar ta,

Kamar daga sama aka ɗauke Inna dawani gigitatcen mari wadda yasata faɗuwa kasa bashiri, da sauri Ammi ta ɗago tana kallonsa tsaye yake idon san nan ta sauya tayi jaa jijiyoyin kansa duk sun miƙe gaba ɗaya fuskar sa ta sauya sai wani huchi yake,kamar wani maƴinwachin zaki gadan gadan ya tin kari Inna dake baje a kasa tana ihu, da gudu matan dake gidan kowace ta kama kanta mace ɗaya che ya rage zaune bata gudu ba gudu ba, wani bugu ya kaiwa Inna a wuya nan taƙe numfashinta ya ɗauke hannu yasake ɗagawa a zuchiye zai kara kai mata wani bugun, da sauri Ammi tache "a'a Fahad ya isa tayi maganar tana karisa wajen da Fahad ke tsaye ganin Fahad na kokarin karawa inna bugune yasa Ammi tayi saurin shiga tsakanin su tana faɗin ya isa haka Fahad ka kyaleta, "Ammi pls ki kyaleni na bugu matar nan kina gani fa wuyar rigan ki ta riƙe wai ma wacece ita ? yayi maganar chikin matsanan chiyar ɓachin rai "aa Fahad ka kyaleta haka nan baka ganin ta sumane matar kawun ku che "Ammi idan matar kawun mu che sae ta riƙe miki wuyar riga "ya isa Fahad jike ka kiramin su Safras kaji a zuchiye ya juya yafita sai huchiyake,
Juyowa Ammi tai tana kokarin taɓa inna karaf idon ta ya sauka kan su diyana dake tsai tsaye a bakin kofar dakinsu sunyi chirkoh chirkoh da sauri Ammi tafasa taɓa Inna tanufi wajensu tana faɗin "ina Ahmadu hiyana jin an amba chi ina Bappa yasa ta fashe da kuka, turus Ammi ta tsaya murya na rawa tache "hiyana me kikewa kuka Ahmadu nache kuka hiyana tache "Bappa yarasu satin daya wuche
Nan take Ammi tayanke jiki zata fadi da gudu hiyana tai kanta tana kokarin tareta dai dai lokachin su DON suka shigo da sauri DON ya karaso yasa hannu shima yana kokarin rikoh Ammi har karo sukai da hiyana bai ma bi ta kantaba ya rungumo Ammi ajikinsa yana kiran su nan ta da sauri su Fahad dukayi kansa suna kiran Ammi, Ammi
ganin haka yasa hiyana tai baya

Chikin tsawa Fahad ya ɗago ya kallo su hiyana yafara "meyasa Ammi waya mata wani abun, yanzu nafita na barta lfy lau,
murya na rawa Hiyana tache "ta tambayeni Bappa ne shine nafaɗa mata ya rasu shine zata faɗi..bata karasaba maganar ba, ya daka mata tsawa ya isheni haka shiru hiyana tayi jikinta sai kerma yake
DON kuwa kwantar da Ammi yayi a kan tabarman dake wajen yaɗago ya dubi su Fahad dake tsaye a kansa "kai kubani ruwa kafin DON yakai karshen maganar ma, Fahad ya nufi waje chikin mota yashiga ya dauko ruwan faro da sauri yadawo chikin gidan ya mikawa DON Aryan dake duƙe kusa da DON ya karbi ruwan ya bude ya tarfa a hannunsa ya shafawa Ammi a fuska, wani dogon numfashi taja tare da sauke nauyayyar ajiyar zuchiya sai kuma tamike zubur kamar wadda akawa allura tana faɗin "ina bahaka bane kunne nane bai jimin dai dai ba DON ya matso yarike ta a nitse yache "Ammi meke faruwane lfy "ba lfy ba dan naji kamar hiyana na faɗamin wai Ahmadu na yarasu "kiyi hakuri Ammi kinji ya karisa maganar tare da sakin ta, juyowa Ammi tayi tana kallansu hiyana ta musu alama da hannu akan suzo, ba musu suka miƙe sukanufi inda take gaba ɗayan su suka zauna kusa da ita
Ganin Ammi ta dawo chikin hayya chinta sosai yasa Mikewa DON miƙe yanufi waje, Fahad da Aryan suka rufa masa baya

Riko hannun hiyana Ammi tayi tafara Magana "yaushe Ahmadu ya rasu, chikin shesshekar kuka hiyana tache "juma'ar data wuce juma'ar data wuche Ammi ta mai mai ta da mamaki to amma "shine kuma ko sadakar 7 ba'ayiba za'ayi taran biki saboda me ? Hiyana zatayi magana Diyana tai saurin chewa "duk shirin inna che hakan ban gane duk shirin Inna ba che Ammi ta tambaya tana kallan fiskar diyana, sai yamzu matar dake zaune awajen tun dazun wadda kowa ya watse yabarta tafara magana, tashiga bawa Ammi lbr duk abun da yake faru,duk irin a'zabbatar da Inna ke wa su hiyana, Ammi sai hawaye take wani na bin wani chikin muryan kuka tafara magana "duk laifin Ahmadu ne ba yarda banyi da shiba akan yadawo kano kusa dani yaki wai bazai bar garin iyaye da kakanniba, bayadda na iya dole na kyalesa na sai waya mai kyai na bashi dan murinka gai sawa da juna amma yaki ansa wai baya so yanzu har Ahmadu ya kamu, da chiwo akafa ya daina takawa duk ban saniba, innalillahi wainna ilaihir rajiun gaskiya rashin zumunchi bai yiba wlh nima ina da laifi duk dachewa ba zaman kaina nakeba a kar'kashin wani nake, amma yakamata ko wani ne inrinka ai kowa yana dubamin shi yanzu me amfani haka shekara 7 rabona da dan uwana wanda shi kadai yaragemin aduniya yanzuma babu shi wayyo ni Aisha gaskiya auren nesa Auren gidan sarauta bai yiba mutun ba zaifita yaje yasada zumunchiba hakadai, Allah sarki bayin Allah marayun Alla tayi magana tana shafa kan amrat da kyar ta miƙe ta dubi hiyana tache "ina zuwa ku jirani tana kaiwa nan tanufi waje

Kai tsaye wajen motarsu tanufa jakarta ta ɗauka ta chiro wayar ta ta danna kira takara wayan a kunne kana takoma daga gefe chan ta tsaya tana magana Almost 30mnt tana waya bayan ta gamane tazo tasamu su Doyn achikin motarsu tace "kai kujuya motochin zamu koma ta kai karshe maganar tana juyawa, batare da tajira amsar su ba ta nufi chikin gidan su hiyana
In data barsu awajen tasamesu "kutashi mutafi abun datache dasu ke nan ba musu kuma basu tambayeta ina zasujeba dan ita hiyana tasan Ammi yar Bappan,sune su diyana ne basu san taba mikewa sukayi jiki ba kwari, Ammi takama hannu amrat sukayi gaba su hiyana sukabi bayanta sukabar inna abaje a kasa
Suna fita suka samu an juya kan motochin kai tsaye motar ta tanufa, buɗe motar tayi san nan tache da su hiyana "kushiga bamusu suka shiga ita kuma ta juya tanufi motarsu DON
DON naganin Ammi tsaye jikin marfin motan da kansa ya buɗe mata motar tashiga ta zauna kusa dashi
Har anwa motochin key zasu tafi Ammi tache su tsaya bayan sun tsayane tache wa sojan da zai tukasu yashiga gidan su hiyana yakira mata maman bello, da sauri sojan yafita yanufi chikin gidan bajimawa yafito maman bello na biye dashi a baya har suka isa wajen motar
Ammi ta kalli DON dake zaune yanata latsa wayarsa hankalinsa ma ba akansu yakeba "kai idan akoi kuɗi ajikinka bani shiru ya ɗanyi kamar mai tunani sai kuma yasa hannnu ya buɗe wani dan karamin waje dake manne da jikin kujerar baya na motar ya zaro rapa rapan 1k Kowani rapa kuwa zai kai 100k rapa uku yamikawa Ammi, ansa tayi ta sauke glass ɗin motar ta mikawa innar bello ta ɗora da chewa "kibawa bello rapa 2 ke kuma ki ɗauki 1, innar belli ta washe baki sai zuba godiya take, Ammi batache da ita komai ba sai ma ɗaga glass ɗin motar datayi ta bada umarnin sutafi da sauri suka tada motochin suka bar kauye kai tsaye Airport suka nufa.

Innar bello kuwa ta juya ta koma chikin gidan su hiyana ta ɗebo ruwa ta zubawa inna a fuska, a'razane inna tafarka tana faɗin zanga uban da zai hana auren nan idan an isa ache menake, innar bello tache "to ni dai natafi sai anjima tajuya tayi fichewarta, inna kuwa tafara waige waige taga bakowa a gidan duk sun watse mikewa tai ko mayafi babu tayi waje kai tsaye gidansu buba tanufa

Zaune suke dukkansu a tsakar gida har da bello inna tashigo ko sallama babu nan tasamesu ga buba sai faman ihu yake yana fadin aradun Allah bazan barsuba nine zanzama ajalin hiyana indai baayi auren nanba to aradu saina mata asiri ta mutu saina mata sanda
Inna tache meyasamishi
Inna larai maman buba tache mutanen dasuka zo din nanne dasukache kowa yawatse bazaa daura aurenba shine shi buban yache basu isaba sai wani daga chikinsu ya daga buban yabugashi da kasa kana ya kama kafarsa ya karya
" karaya tayi maganar tana zaro ido
Inna larai tache "karaya kuwa shine yanzu malam yatafi kiran mai dauri

Mikewa inna tayi tana faɗin "zomuyi magana tana tana kai karshen maganar tashige ɗakin innar buba, inna larai tatashi tabi bayanta tana shiga inna habiba tache "kinji meyake faruwa koh kuma kinsan idan yaran nan basu mutuba a dokar kauyen nan ban isa intaba koda kafar kazane a chikin dukiyarsu bakoh
Inna larai tache kwarai kuwa yanzu me abunyi
Inna tache wajen malamin chan na bayan dutse zamu sake komawa mana yasan yadda zaiyi ya kashemanasu a chan ko dai a haukata manasu komaidai me ma amusu dan wlh bazan barsuba
Inna larai tache to kina da kudine " Inna tache zannemo ai zuwa nan da sati mai zuwa sai muje
Inna larai tache yauwa kiyi kokari dan allah
To kawai inna tache mata kana tafito daga dakin tayi waje

Kano ta dabo

Aunty amarya zaune take a gefen gadanta ita da hajj sadeeya
"sadiya yanzu tafiya Enugu ya kamaki dan bazan taba barin wani yayi mulkiba idan ba danaba
Sadiya tache gaskiyakam amma bayanzu zanjeba sai wata mai kamawa dan kuwa wlh inada tafiya dayawa a gabana
Aunty amarya tache wata daya baiyi nisaba kinfasan bayan sallah za'a dorasa a mulki nikuma danaga wan nan rana gwanda namutu
Sadiya tache karki damu ai da dan sauran lokachifa abunda idan najema sha yanzu magani yanzu zaamin dankuwa a wajen zansa gagara ba dau ya kashe Safras din kowama yahuta
Aunty amarya ya tache amma sadiya bansan bakida kwakwalwaba sai yanzu kifadamin idan muka kashesa muna da gadansane kina ganinfa yafi kowa kudi a gidan nan ai bakashesa zamuyiba sawa zamuyi gagara badau ya chusa mashi sun yar wajenki kinga dayafara san zulaihat shike nan insunyi aure sai sun haihu sai mukashesa inmun kashesa kinga a lokachin muke da gado
Washe baki sadiya tafarayi tana fadin ashe kinasona har haka bansaniba wayyo allah tayi maganar tana kokarin rungumar aunty amarya
Aunty amarya tache inasanki mana sosaima ai fin hakama yanzu dai kiyimana kokari akan afasa bashi sauratan nan daga nan kuma sai muzo muyi aikin zulaihat da murna

Please Login or Register in order to submit comment