Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bello bai yi magana ba sai da ya isa wajen dayake zama inyazo gonar, wajen shinfiɗe yake da katifar chiyawa, akai ya kwantar da diyana da sauri hiyana ta karisa wajen ta zauna a kusa da diyana, tana fadin "diyana me yasame'ki waya bugeki waya pasa maki baki "hiyana kiyi shiru mana ki kyale'ta ta ɗan huta tun da kika gammu tare ai koma me yafaru zakiji chewar bello" hiyana dai hankalin ta bai kwantaba mikewa bello yayi yana faɗin ina zuwa san nan yakama hanyar fita daga gonar

hiyana na ganin yaya bello ya tafi, ta matso kusa da diyana ta rike hannun'ta murya na rawa tafara magana "diyana meyasame'ki, chikin sarƙewar murya diyana tache "buba ne ya bugeni, dafe kai hiyana tayi tana faɗin "diyana banache duk abun da buba zai miki kirinka hakuriba, ae'nafaɗa miki koma me kika masa a kan mu abun zai sake dawowa tun da mudai bamu da gata, bamu da mai tare mana fada ki dubafa kigani gaba ɗaya kauyen nan gudun'mu suke saboda kalar idon'mu, kinsa ni wasuma har mayu suke chemana, wai idon'mu ba irin na mutane bane irin na mayune bawanda yake kusantar mu kowa wai tsoro muke bashi, duk kauyen nan yaya bello ne kawai mai tausaya mana sai bappa, su biyu suka rage mana amma duk da kinsan da haka sai kije kirinka biyewa buba kina jawa kanki wata masifar koh
hiyana zata sake magana kenan idanta ya sauka a kan jinin dake jikin zanin diyana,a ɗan razane tace "diyana wai wan nan jinin kam na menene haka, chikin dashe war murya diyana tache "nima wlh ban saniba tunfa dana tashi yau da safe naketa ganin jinin yana fitowa yaki dai nawa, girgiza kai hiyana tayi tana faɗin "kuma kin duba bakiji chiwo'ba "ni banji wani chiwo'ba, shiru hiyana tayi tana tunanin a dai iya karatun da bappa ya koyamu'su tabbas yataɓa faɗa musu idan mace tafara girma to zata fara jinin haila, to ke nan wan nan shine, to idan koh hakane ae no yakamata nafara jinin ba diyana ba, tun da ni che babba amma yau zanje na tambayi bappa gaskiya dan muji wan nan jinin na lfy tayi nisa chikin tu naninta
sae' taji muryan yaya bello yana faɗin tashi kuchi abinchi, dawo da kallanta kan'sa hiyana tai yana rike da samira rufe da pai pai, a dayan hannun'sa kuwa kwaryar nono ne, ajiye musu yayi yana faɗin "kutashi kuchi dawuri "yaya bello bazan'mu iya chin abinchin nan,mu barsu amrat ba, basu chi komai bafa tun jiya da safe hiyana tayi maganar kamar zatayi kuka,yaya bello yace "hiyana karki damu kuchi kinji zanje in sayo muku rogo a dan dali sae' ku ɓoye ku kai musu yana gama faɗin hakan ya ɗau fatan yar'sa yanufi wajen da yake shuki, hiyana ta miƙe,ta kama hannun diyana ta tai maka mata ta miƙe zaune, san nan ta jawo musu samiran Abinchin gaban su ta buɗeq, ɗumamen duwon dawane mai kyau da miyar kuɓewa yaji man shanu gashi sai tiriri, yake kuma da yawa dan yakusa chika samiran nan fa sukafara chi, hannu baka hannu kwarya, saida suka chinye tas san nan suka jawo kwaryar nonon ma suka shanye, hiyana tamike ta ɗauki samiran da kwaryar nono ta nufi rafin ta wanke'su san nan ta debi ruwa a chikin kwaryar tash takuma kawowa diyana

wai shin wanene bello?

Bello dai dashi da buba babansu daya mamane daban daban baban su buba kuwa yaya inna habibache inna habiba kishiyar mamansu diyana bello yana da mata yayi aure kuma a chikin gidansu yake zaune da matar tasa shiyasa duk taimakon da zaiyiwa su diyana yakeyi a boye dan indai yabari inna habiba tasani to wlh sharri zata masa tache yana nemansune ta haddasa masa masifa tsakaninsa da matarsa shikuma yana matikar tau saya musune shiyasa yake tallafa musu wan nan takai checchen wanene bello ke nan

hiyana ta kawowa diyana ruwan ansa diyana tayi tasha san nan hiyana ta dubi diyana tache to barinaje na chigaba da ɗeban ruwan "aa mutafi tare dai dan yanzukam nasamu karfi ae "to muje jerawa sukayi har inda bello ke noma sukaje, suka masa godiya tare da sallama, to bello yace san nan yaɗora da chewa "an jima zan kawo muku rogon bari na gama noma naje dan dali ya sawo muku koh sai kubawa su amrat ɗin "to yaya bello mun gode sosai hiyana tafaɗa tana kamo hannun diyana har sun juya zasu tafi hiyana takuma juyo tache yaya bello wai dan allah me buba yayiwa diyana jiyane naga jikin'ta sai jini yake

Shiru bello ya ɗanyi kamar mai tunanin wani abu, a nitse yafara magana babu abun da yama'ta dayaso yama'ta fyaɗe'ne sai kuma Allah ya tsare najiyo ihun'ta shine naje na kwache'ta, amma lokachin dana shiga ɗakin buban, dai dai lokachin yabuga mata sandar'sa a kai shiyasa kikaga tasuma, batun jini kuma ina ganin girmane yazo mata amma kuje gida zansan abunyi a kai hiyana tace "yaya bello menene kuma fyaɗe "shikenan ku daije gida ba sai anmiki dalla dalla ba, chewar bello
Jiki ba kwari suka'nufi rafin suka ɗebi ruwa a kofu nan suka wuche gida da sallama suka shiga gida inna na tsakar gida tana ƙirgawa lamrat robobin nonon dazata tafi talla dasu a tsiyache innar ta ɗago tana kallan'su " kuzo ku ajiye kofin, ku ɗauki tallar nan kuje ku sayarmin idan kun dawo ko da dad darene kwa karasa ɗiban ruwan "da sauri sukaje suka ajiye cups ɗin a kichin, suka fito suka dawo gaban ta suka tsugun na

Kirga musu nonon inna tayi tana gamawa ta fara musu kashe di, "wlh ko kwana zakuyi a chan ku kwana amma karku dawo baku sayar da nonon nanba
to kawai suka che mata san nan suka ɗauki tallar kowa da nata kwaryar suka nufi hanyar fita daga gidan suna masu tau'sayawa amrat dan kuwa yanzu duk aikin gidan nan ita kaɗai zatayi innalillahi wa inna ilaihir rajiun suna fita "diyana ta dubi hiyana tafara Magana wai yanzu yazamuyi ne kinfasan mu ba'a sayan faran'mu, dan chemana suke mayu ajiyar zuchiya hiyana ta sauƙe kafin tace "Allah na tare damu ai, muje kekam muyi addua,
kai tsaye dandali suka nufa dukkan'su uku diyana hiyana lamrat sukabar amrat a gida daman ita amrat ba'a ɗora mata talla sai dai aikin gida kawai inna ke kasheta dashi
suna zuwa kowa ta ajiye kwaryar nonon ta nan take mutanen wajen suka fara matsawa nesa dasu, sudai ko ajikin su dan in da sabo sun saba zaman'su sukayi shiru bawanda yache dawani kala a chikin'su
wani

Wani katon mutunne mummuna baki yazo wajen dasu diyana ke zaune ko sallama bai yiba ya dubi diyana yace ke ki dama min fura da nono na naira 100 ki kawo min masauki na, ya karisa maganar yana nuna mata hanya da masaukin nashi yake "nifa bansan wajen masaukin naka ba diyana tabashi amsa "dakin fita daga dan dalin nan kika ɗan yi kwanar hagu zakiga wata bukka to nanne wajen nawa "to zan kawo ma chewar diyana, juyawa yayi yabar tafi,
Hiyana ta dubi diyana dake kokarin dama nono a kwarya dan ta damawa mutumin tache "aa diyana wlh bazaki kai masaba' nifa tunda nake zuwa dan dalin nan ban taɓaganin mutumin nan ba kai ni ko sau ɗaya ma ba a dan dalin kawaiba koma aina ban taba ganin'saba
Girgiza kai diyana tayi tana faɗin aa hiyana kibari nakai masa in bahakaba Kinsan dai bamai sayan fura da nono mu ko "to shike nan diyana kije,ki kai masa amma kiyi addua dan wlh in tsoran, karya sacheki kinga ba sanin sa mukayiba a diyana ta amsa da "to tafara dama furan

bajimawa tagama dama furan ta ɗauka tanufi inda mutumin ya nuna mata, a bakin kofar bukkan nasa ta tsaya ta masa sallama, yana daga chikin dakin ya amsa sallamar tare da faɗin "ki shigo mana, diyana ba musu ta shiga a zaune ta'sameshi a tsakiyar ɗakin, gabansa taje ta ɗuka ta ajiye masa damammi yar furan a gaban sa, tana faɗin a ban kuɗin murmushi yayi ya ɗago jajayen idon'sa yana kallan ta "yarinya mai kyau kinasan kuɗi koh, diyana zatayi magana sai taji ya riko hannun'ta yachi gaba da faɗin "ni zan baki kuɗi dayawa in kinaso ya kai karshen maganar, yana kokarin rungumar'ta
Da karfi diyana ta ture'sa tamike da gudu ta nufi waje, tana waige waige ko mutumin yana binta, a dai dai bakin kofar ta waje tayi karo da bello, baya tayi zata faɗi da sauri bello ya riko kafaɗar ta yana kallon chikin idon tana yana faɗin lfy diyana ita kuwa sai waige waige take, murya na rawa tache "yaya bello wlh shine ya kamamin hannu wai zai bani kuɗi
A'fusache bello yache "ae daman bayan'ki nabiyo, yanzu zuwa'na dan dali na tambayi hiyana ina kike shine fadamin kinzo kawo wa wani nono, yanzu dai ki koma dan dali ina zuwa yayi maganar tare da sakin kafaɗar ta
Da gudu diyana tawuche tanufi dandali, shi kuma bello yanufi chikin ɗakin mutumin zaune ya samesa yana shan furan da diyana ta kawo wani kallan banza bello ya bishi dashi daga sama har kasa kafin yache malam wanene kai " mutumin yaɗago kai daniyar yayiwa bello rashin mutunchi sai kuma yaga bello chikakken namiji'ne mai ji da karfi dan ko faɗa zasuyi bello zai masa dukan mutu, dan haka sae yanitsu chikin girmama'wa yace "ni bakoh ne rai a ɓache bello yafara magana "eh ae nasan kai bako ne tun da ban taɓa ganinka a nan ba chewa nai daga ina kake, kuma meyakawo ka garin nan shiru ya ɗanyi kafin yache "daga kauyen tongo nake kuma hanyache tabi dani tanan na tsayane dan na hutane, idan na huta sai nachigaba da tafiya "shine zaka lalata mana yara bello yayi tambayar chikin tsawa, shiru mutumin yayi
Yaya Bello ya chigaba da chewa aradun Allah idan kasake yiwa ɗaya daga chikin kannena magana wlh sae dai a ɗau gawarka murya na rawa mutumin yace "kayi hakuri bazan sakeba, bello bai sake magana ba yasa kai yafeche daga dakin a fusache,

wajen su diyana yanufa,suna zaune suna yar hirar'su bello yazo kusa dasu kamar mai sayan nono kasa kasa yafara magana "duk wanda ba zai sayi nono a nan ba sai dai abari, karku kuskura ku sake kai ma wani sai dai ya hakura san nan kuma ki damamin fura da nono na 100, da sauri hiyana ta bude kwaryar nono ta ɗauko roba biyu ta juyesu a chikin wani dan karamin kwarya tasa fura biyu ta dau ludayi tafa damawa, tagama ta juye masa a leda ta mika masa,hannu yasa ya ansa, yasa ɗayan hannun sa a aljihun ya chiro kuɗi naira 500 ya juya gabas da yamma dan yaga akoi mai kallan sane ko babu, dan bai san inna tasani, mikawa hiyana kuɗin yayi, Kin ansa tayi, tana girgiza masa kai alamar ya bar kuɗin kawai, kan pai pan dasuka rufe kwaryan nono ya ajiye musu kuɗin kasa kasa yache kichere 100 na nono kibawa inna, sauran 400 kisaya muku rogon 100 ki ajiye 300 kuma zai muku am fani gobe, bai jira amsar suba yajuya da sauri, dan ya lura hankalin mutane yafara dawowa kansu kar wata matsalar tazo tafaru

wuni zumbur su hiyana sukayi awajen ban da bello daya saya nonon bawan da yasake saya, shima mutumin da diyana ta kai wa nono bai basu kuɗin ba, haka sukayita zama da nono har karfe 6 na yamma, san nan hiyana ta miƙe tana faɗin kutashi mutafi gida, mikewa diyana da lamrat sukayi suka ɗauki kwaryar nono suka ɗora akansu suka kama hanyar gida
Suna tafiya ne diyana tache "wai lamrat waya saye furan ki na jiyane lamrat tace "ae dayake kinga jiya kasuwane akoi baki,ni kuma kinga ai idona ba irin naku bane ba wanda yake chemin mayya shiyasa bakin suka rinka sayan nonon
Hiyana ta girgiza kai tana faɗin "ae kema da idon ki yayi irin namu babu wan da zai saya koda bakin nema, suma chewa zasuyi ke mayya che
Diyana tache "yanzu ya zamuyi da inna, ɗaure fuska hiyana tayi tana faɗin "ya zamuyi kuwa dukane dai kamar yadda muka saba shi zamusha "Allah kakawo mana mafita chewar diyana, dukkan su suka amsa da ameen

Da sallama suka shiga gidan sai faman rakuɓe rakuɓe suke, muryan inna che ta daki dodon kunnen su daga ɗaki, tana faɗin "ae shiyasa nakesan hiyana ta Auri buban kinga ita hanyar mutuwar ta mai sauki ne, sukuma sauran zamusan yadda zamuyi dasu
amma bazamuyi kisa a chikin gidan nan ba dan kinsan al adar kauyen nan, amma na chi al'washin duk dabbobin nan nine zan gajesu wlh dukkan'su nizan zama sanadiyar mutuwar su , wata murya mara daɗin ji sukajiyo daga chikin ɗakin inna tana faɗin "ae wahalar da kike ba suma habiba am zata iya zama ajalin su, Wani dariya inna tayi san nan tace ae yanzu ma kara nin'ka musu wahalar zanyi, kuma sati nan mai zuwa za'a ɗaura Auren buba da shigiyar nan .

Baya baya sukayi suka fita daga gidan suna fita suka rushe da kuka,suna kuka suna tafiya har suka isa kasan itachen mangoro dake ɗan bayan gidan su zama sukayi awajen,suka sauke kwaryan nono dake kansu suka chi gaba da kukan su, sai da sukayi kukan mai isarsu san nan sukayi shiru dan kan su, dan duk chikin su ba mai rarrashin dan uwansa

Suna zaune awajen har aka kira sallar mangariba, tukun nan suka mike, suka ɗauki kwaryar nono jiki ba kwari suka nufi gida ko da suka shiga, a tsakar gidan suka samu inna jiki a sanyaye suka karasa chiki gaban ta sukaje suka tsugun na, suka sauke kwaryar,sukayi jugum jugum gwanin ban tausayi suna jiran hukunchi, inna naganin haka tagane basu sayar ba miƙewa tayi tanufi ɗaki ta dauko wani katan bulala tafito, tafara bugun su dashi
Diyana da hiyana suka hadu suka rufe lamrat bulala na sauka ajikin su, bugun su inna take baji ba gani abun tun suna iya kuka ma har kukan nasu ya daina fita duk sai da tamusu ruɗu ruɗu da jiki, ta kyale su ta kuma fiche daga gidan tana ta mai da numfashi, Amrat na ganin inna ta fita, itama tafito daga ɗakin bappa tayo wajen su da gudu tana kuka haka suka haɗu a tsakar gida suka rungumi juna sunata kuka, sai da sukayi kuka mai isar su
San nan su kamike jikin dukkan su jikin su sai karman yinwa da wahala yake, suka nufi dakin bappa da sallama suka shiga amma bai amsa musu ba, akusa dashi suka zauna yana kwanche idon sa Abuɗe yana kallan sama
chikin shesshekar kuka hiyana tace "bappa ina wuni shiru bai amsa ba " bappa bakada lfy ne diyana ta tambaya a ruɗe, nan ma shiru bai amsa ba Hiyana tasa hannu ta taɓa shi ko motsi bai yiba a firgiche tafara jijjigasa tana ihu tana kiran sunansa Amma shiru
Chikin kiɗima hiyana tafito daga ɗakin tayi waje tana ihu

London United Kingdom

Tsaye yake a tsakiyar babban palon su hannun'sa ɗaya na rike da trolley ɗayan hannun kuma yana rike da wayarsa yana latsawa, sanye yake chikin black jeans da blue t-shirt ya rage tsawon gashin kansa, yanzu gashin bata wuche zuwa iya wuyar'sa ba, yana sanye da booth black colour a kafarsa dakuma p-cap shima baki hannun sa na ɗaure da wani haɗadɗen agogon daimon mai kyau da tsada fiskar nan kuwa babu alamar annuri akanta a taure take tam kamar an aiko masa da sakon mutuwa amma yayi kyau sosai laɓɓansan nan kuwa kamar yasa jan baki jaa sosai ga sajen sa a kwanche yasha gyara bakaramin kyau yayiba, faffaɗar kirjin san nan kuwa a tsaye dam dam kamar zai fashe ga damtsen hannun sa a chike kamar zasu yaga hannun rikar, almost 10mnt yana tsaye

A hankali Aryan ke sauko daga saman stair ɗin shima shigarsa iri ɗaya dana DON abun mamaki shima ya yanke gashin kansa ya rage mata tsawo, rike da trolley shima yana ja sauko wa yayi yazo dai dai inda DON ke tsaye, da wan nan sexy voice nashin ya furta sorry bro,DON bai tanka saba yaja trolley sa yanufi kofar fita, da sauri Aryan yabi bayan sa sukayi waje tare, da gudu rundunar jibga jibgan sojojin masu ji da lfy da karfi sunsha trenin suka nufosu, da sauri abdol ya karɓi trolley hannun DON, Shahram kuma ya karɓi trolley hannun Aryan, suka samu su a chikin haɗaɗɗun motachin, da akajera musu dan tafiyar

Aryan yadubi DON yace "muje a mota ɗaya koh,DON batare daya amsa ba yace "wai ina Aiman da Ahmad ne "ae tunjiya suka wuche naija Aryan yabashi amsa yana kallan fuskar sa kama hanya kawai DON yayi batare daya sake magana ba yanufi motar, da sauri abdol yabuɗe masa kofar motar, slowly ya shiga ya zauna, ɗaga hannu Abdol yayi ya sara masa san nan ya rufe kofar motar, zagayowa ta ɗayan kofar motan Aryan yayi, da sauri Shahram ya buɗe masa kofar a nitse ya shiga ya zauna Shahram ya sara masa san nan yarufe kofar motar
Da gudu sojojin suka hau nasu motochin su suka tadasu, da matsakai chin gudu suka nufi gate ɗin tun basu kariso ba security suka wangale masu gate ɗin, da gudu suka danna hanchin motochin waje,motar sojoji 2 a gaba sai motar su DON a tsakiya sai motochi 2 na sojoji a baya gudu suke shararawa a kan mikakkiyar titin

Aryan ya dubi DON yace sai dai fa mutafi da jet ɗinka dan kuwa nawa yana naija dashi su Ahmad suka tafi "Ok kawai DON yache, chikin kankanin lokachi suka isa Airport Already angama shirya komai su kawai a ke jira, batare da ɓata lokachi ba suka fito daga chikin moton su suka nufi kyakkyawa kuma haɗaɗɗen privet jet ɗin DON mai ɗauke da tambarin sunan'sa PRINCE SAFRAS suna shiga batare da ɓata lokachi ba jirgin yaɗaga sai malam Aminu Kano international Airport Kano Nigeria

More comments and share pls
[7/3, 5:46 AM] Al~Quyraemey: *DUK ƘARFIN IZZATA*

_💖Story And Written💖_
⬇️
*Star Lady*



💖 The talent troupe writer's 💖

Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai


*Episode 5*


DON

Misalin karfe 5 na yamma jirginsu yayi landing a malam Aminu information Airport kano, wasu dan kare dan karan motochi 5 sukazo ɗaukansu ga motochi 3 chike da sojoji, basu wani ɓata lokachi a chikin jirgin ba suka fito tare suka jera, sai wani kara ɗaure fuska suƙe da ka gansu kaga wayan da akawa zuwa dole, musamman DON nashi daban ne, Abdol da Shahram suna biye dasu a baya,rike musu da trolley sojojin nan na ganin fitowar su suka jinro daga nasu motochin suka nufe su, Fahad na ganin fitowar su ya nufesu da sauri, yana ɗan murnushi hugging na DON yaje yayi yana faɗin "Wellcome back bro, hannu DON yasa yayi taying ɗin yana faɗin "missed U my blood "missed U too yayi maganar yana zare jikin sa daga jikin DON, yajuya yayi rungume Aryan ma, yana faɗin yaya Aryan nayi kewar ku sosai, rungume sa sosai Aryan yayi yace "nima nayi kewar ka sosai my blood, ganin DON yayi gaba ya barsu ne yasa Fahad ya saki Aryan da sauri sukabi bayan DON wajen motochin nasu suka nufa,nan take su Haidar suka fara musu sannu da dawowa ko kallan in da suƙe DON bai yiba bare su saran zai amsa musu, ya shige motar ya zauna yana yamutsa fuska, Aryan ma shiga mota yayi riƙe da hannun Fahad sai da suka zauna san nan ya dubi kannen nasu yace "yauwa to ku shiga mota muje gd koh sai mu gaisa a chan zaifi, da sauri suka koma chikin mota, drivers su kama motochin key da gudun gaske suka bar Airport ɗin gudu suƙe shararawa sosai a kan mikakkiyar titi, sai da suka kusa da bakin gate ɗin gida suka rage gudun motochin, batare da ɓata lokachi ba security daƙe tsaron gate ɗin su wangale musu gate ɗin a nitse suka kutsa chikin gd, kai tsaye parking space suka nufa suna kashe motochin, Shahram da Abdol suka fito daga nasu motar da gudu su kazo suka buɗewa DON da Aryan kofar motar, a nitse DON ya zuro kafafun'sa waje kafin ya fito gaba ɗaya bai bi ta kan kowa ba yanufi ɓangaren sa, Aryan ma ɓangaren sa yanufa riƙe da hannun Fahad suna tafiya suna hira, Yusuf ya karɓi trolley DON daga hannun Abdol yabi bayansa da shi Ahmad ma ya karɓi na Aryan daga hannun Shahram ya nufi ɓangaren Aryan ɗin, su Haidar kuwa kowa yakama kansa yayi part nasa

Ammi na zaune akan kujera a palan'ta tasha kwalliya chikin wata ɗankarekiyar lace baki da ratsin ja mai shegen kyau ga wasu gwala gwalan data zuba a wuya da hannu ta,ba karamin kyau tayiba inka ganta kace bata,wuce 25 years ba, Aunty farida tashigo da sallama ɗauke a'bakinta, da fara'a Ammi ta amsa mata sallamar, shigo chiki palon tayi ta zauna saman sofa mai zaman mutun 2,tana fuskantar Ammi "feeda dayake haka Ammi ke kiran Aunty farida feeda,ina junior yake "Junior yana wajen mardiya chewar Aunty farida " ok kawai Ammi tace tana kallan face ɗin Aunty farida "Ammi magana nakesan muyi dan Allah "ae feeda tun shigowar'ki Na fahimchi hakan, badamuwa ina jinki "Ammi daman, magana che a kan price, tun!bata kai karshen maganar ba Ammi ta ɗaga mata hannu, tana faɗin a'a feeda, kinsan dai bazan saka bakina a maganar bako,babu ruwana, dan kuwa kinsan mai martaba idan yayi magana baya chan'zawa "Ammi mun san Abba idan yayi magana baya sau'yawa, amma ae ke ki nasashi ya sauya magana koh, dan Allah Ammi, ki samana baki pls takarisa maganar kamar zatayi kuka "aa feeda babu ruwa'na wai ni ina ruwa da wani prince, ae wan nan ɗan Ummi ne ba ɗa naba kije kisamu Ummi ita tashiga masa amma ban dani "dan Allah Ammi kinfasan Abba yafi sauraren maganarki fiye da kowa a gidan nan" Feeda kin dai san in nache bazanyi abuba tofa bazanyin bane koh dan haka kibar maganar kawai,"to shike nan Ammi na barta barinaje namusu sannu da zuwa "baki Ammi ta taɓe tana faɗin eh lallai feeda ɗaure wa karya gindi,su da suke kannenki basu zasuzo su gaida kiba ke zakije ki gaida su lallai yaran nan suna abun dasu ka gadama
Aunty farida tamike tana faɗin kai Ammi kedai babu ruwan ki tsakanina da yan uwana ko inche yayyuna dan yanzu nabasu girma takai karshen maganar tana kokarin fita daga pallan bata tsaya ta jira amsar Ammi ba ta wuche abunta tana fita tayi part ɗin DON

Da sallama tashiga palan nasa babu kowa, kai tsaye betroom ɗin sa tanufa, yana tsaye gaban mirrow yana gyara gashin kansa,sanye yake da bakar jallabiya, da alama wanka yayi, jin sallaman ta yasa yaɗago green eyes nashi ta chikin miron yana kallan'ta, batare da ya juyo ba "yace Aunty babba yanzu nake tunanin inje in ganki, kafin inyi barchi
Harara wasa Aunty farida ta wurga masa tana fadin "daka ganniba dole kafaɗi haka nasan da banzoba ba zuwa zakayi ka nemeni'ba, slowly ya juyo ya zuba mata green eyes nashi nan kafin yace "a'a Aunty farida ae kema kinsan dole na nemeki


Karisa shigowa chikin ɗakin tayi tai, a bakin katafaren gadansa dake shinfiɗe da White bet shit ta zauna tana faɗin,"to ya hanya "Tafiyar da bada san ranmu mukayotaba Tafiyar dole,ya kae karshen maganar yana ɗaure fuska , guntun murmushi Aunty farida tayi kafin tace, "hmmm yanzuma nagama magana da Ammi kafin nazo nan, kara ɗaure fuska yayi yana faɗin "ai dama baki mata magana ba, da baki

Please Login or Register in order to submit comment