Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mana sosaima yanzu dai jekisa kaya," da farinchiki a face ɗinta tajuya tanufi sip ɗin kayan'su doguwar rigar da Aunty farida ta kawo musu ta ɗau koh, zatasa ke nan " Zahra tace diyana yakamata kisa bra kafin kisa rigar nan zaifi zama maki da kyauu dan kinga yana da igiya inba bra, aka ɗaure igiyar baya kyau " yauwa Aunty Zahra idan dai zanyi kyau kawai kisamin diyana tafaɗa tana murna " shiru Zahra tayi tana tunanin wai ita'kam diyana inazata kai kyau'ne, duk wan nan kyan da Allah yamata, bai isheta'ba take neman kari, duk wani abun da kacewa diyana zai ƙara mata kyau tofa koda abun bai mataba sai tayi amfani dashi itadai kawai taji anche taƙara kyau, Zahra tayi nisa chikin tunani bata an'karaba kawai sai taji " diyana na taɓata Aunty Zahra kisamin abubuwan bra ɗin " to juya nasa miki " juyawa diyana tayi zahra tasa mata karfen bra ɗin " hiyana dai baki ta taɓe tana ganin ikon god" komawa diyana tayi gaban sip ɗin ta ɗauki rigarta tasa, ta ɗaura igiyar rigar tayi kyau sosai ta ɗauki mayafin rigar ta rufa akanta tanufi wajen shoe rack nasu high heel blue kalar rigar ta ɗauƙa tasa tanufi waje kwas,kwas,kwas, abunta "
baki buɗe hiyana ke kallan diyana har tafita ajiyar zuchiya ta sauke ta dawo da kallanta kan Zahra"Aunty Zahra kinsan me " Zahra tace aa bansaniba hiyana am sai kin faɗa " wlh inaga nan gaba kasuwa kwalliya gaba ɗaya za a'ɗaukowa diyana " dariya Zahra tayi tana faɗin eh gaskiya kam naga alama nima " hiyana zatayi magana sukaji kwas,kwas,kwas, " ba ko sallam diyana tashigo da sauri gaban mirrow takoma ta ɗauki kwal'bar turare hunrar da Aunty farida ta bata ta shafa a jikinta dan Aunty farida ta faɗa mata indai batasa turare bazatayi kyau ba da sauri ta ajiye kwal'bar tanufi waje " su dai su hiyana sunga abun dayafi karfin'su " miƙewa hiyana tayi daga kan daddumar takoma kan gado ta kwanta " zahra Kuma ta ɗauki hijabin'ta tasa tatada sallah

A gurguje ta haɗa masa coffee ta ɗauka tanufi ɓangaren'sa da sallama tashiga palon babu kowa kai tsaye tanufi betroom ɗin sallama tayi a bakin kofa, bata jira an amsa'ba kawai tashige chiki " kwanche yake a katafaren gadonsa idonsa a lumshe farin singlet da short ne kawai a jikinsa asalin kirar'sa na jaruman maza ya bayyana ga wani gashi baki kwanche a chin yoyin'sa har zuwa kafofin'sa damtsen hannun'san nan kuwa kamar zasu fashe saboda karfi " kan ɗan karamin table na chikin ɗakin ta ajuye coffee ɗin tanufi bakin gadon, zama tayi kusa dashi a nitse da cool voice kamar mai raɗa tafara kiran sunansa, tana ɗan bubbuga hannun'sa yaya Aryan, yaya Aryan katashi na kawoma coffee karyayi sanyi " slowly yafara ware ash eyes nashi wanda suka chanza zuwa launin jaa, sauke idan nashi yayi a kan face ɗin ta, ƙara waresu sosai yayi yana kallan'ta " diyana sai data tsorata ganin yadda idonsa suka chanza launi" mikewa tayi zata gudu " hannu yasa da sauri ya riƙo hannun'ta, ya jata baya, ta koma ta zauna" kallanta yake sosai, nan take yaji wani sanyi na ratsa zuchiyar'sa wani farinchiki yaji, jiyake wani bakon yanayi na ziyartar zuchiyar'sa" turo ɗan bakin nan nata tayi kamar biro a shagwaɓe tafara magana yaya Aryan kayi hakuri kaji dan Allah karka bugeni, ta karisa maganar kamar zatayi kuka "shiru yayi yana kallan'ta, yakasa magana almost 10 mnt suna zaune haka yanata kallan'ta,kamar yamai data cikin'sa yakeji"turo baki diyana tasakeyi tana faɗin yaya Aryan dan Allah fa nace kayi hakuri ba dan niba" ɗan firgita yayi yadawo daga duniyar tunanin dayashiga" calmly yafara magana baki iya gaisuwa bane kuma wayace kiyi kwalli da daddaren nan" kayi hakuri to, ina wuni tafaɗa tana kun bura kumatu" sakin hannunta yayi tare da mikewa zaune " itama ganin yasaketa tamiƙe tana kokarin tafiya " ina zakije ya tambaya yana kallan'ta from head to toe " ɗaki zanje " nace kitafine " aa kayi hakuri "to dawo nan ki zauna yayi naganar yana nuna mata drawer kefen gadon " saman drawer taje ta zauna tana fiskantar kofar toilet
"juyo nan ki kalleni magana zanyi dake, a nitse ta juyo tana fuskantar'sa,ganin itayake kallo yasa tayi ƙasa da kanta tana murza yan yatsun hannun'ta " dawo da kallan'sa yayi kan hannun'ta sosai yake yakara waro idan'sa yana kallo lallenta, ba'ƙaremin kyau lallen yayi masaba " wayamiki wan nan abin yayi maganar yana nuna lallen nata " laaa Aunty farida ta kaimu a kamana mana kuma kasanme takawo min kayan kwalliya dayawa" zuba mata ido yayi yana kallan yadda take murmushi take magana a zuchiyar'sa yace thank God nima nasaya kayan kwalliyar
afili kuwa yace baki bani amsa taba nace wayace kiyi kalliya da daddaren nan" nan take ta ɓata fuska ta daina murmushi ta turo baki tana faɗin yaya Aryan baa kwalliya da da'ddare'ne "anayi mana kuma kinyi kyau sosai kawai dai nine banasan kirinƙayi " nan take kuma tafara murmushi tace laaaa yaya Aryan da gaske nayi kyau ta tambaya " girgiza kai kawai yayi ya zuba mata ido yana kallan yadda take dariyar azuchiyar'sa yake faɗin kekam komai kikayi kyau yake maki inkina dariya ki ƙara idan kina murnushi makura che ke, kai ko kuka kike kyau yake miki " katse mishi tunani tayi dachewa yaya Aryan intafine" girgiza mata kai yayi alamar aa "kallansa tayi sosai sai kuma tace laaaa Yaya Aryan kayi rashin lfy ne" me kikagani yayi maganar da ɗan mamaki a face nashi " ae Naga karame'ne tafaɗa tana kara kallan'sa sosai " yayi mamakin sosai da jin abun da tace,a zuchiyar'sa yake faɗin wow intelligent girl,tabbas ni kai na nasan na rame amma bawan daya gane hakan ko DON damuke tare bai gane hakan ba sai ke wow,

Ajiyar chiya ya sauke ya ya juyo da idansa yayi kanta yaga itama shi take kallo," sai yace aa banyi rashin lfy, jeki kawomin coffee ɗin karyayi sanyi " da sauri ta mike tanufi inada ta ajiye coffee ɗin ta ɗaukoh,ta dawo tamiƙa masa " ansa yayi yana faɗin to zauna muyi magana" zama tayi a inda tatashi ta zuba masa ido tana kallan,yadda yake shan coffee ɗin,"yaya Aryan kasan me" ɗago ido Aryan yayi yana kallanta batare dayayi magana'ba " tachigaba dacewa Allah yaya Aryan kana kama da wan da yayi film ɗin Bahubali, nan Amma fa kafishi kyau, yama sunan shi, taƙarisa maganar tana ɗaga kai kamar mai tunani" da mamaki yake kallanta yana tunani wae daman yarinyar nan tana kallan mutane ne, murmushi kaɗan yayi yace nima bansan sunan shi ba ae " to zan tanbayi Aunty Zahra sunan shi sai nazo nafaɗama " batare da ya amsa mataba yace tashi kije ki ɗaukoh min trolley ɗin chan yayi maganar yana nuna mata inda trolley yake da hannun'sa " da sauri ta miƙe tanufi wajen tayi tunanin trolley bai da nauyi, sai tasa hannu ɗaya zata ɗauka amma sai taji a'kasin hakan dan kuwa ko motsa trolley ta kasa, shi kuwa Aryan ya zuba mata ido yana kallan'ta
Dad dagewa tayi da iya karfin ta ta jawo trolley baya baya tayi tafaɗi trolley ya faɗo mata a kan kafa kara ta fasa mai sauti " a sukwane Aryan ya ajiye cup ɗin hannunsa ya ya miƙe ya nufuta hannu ɗaya yasa ya ɗaga trolley ya ajiye a kan gado, ya dawo kusa da ita ya duƙa yasa hannu ya kama kafar nata yana faɗin, menene abun kuka kuma, " yaya Aryan wlh da zafi tafaɗa chikin muryan kuka" a haka kike chewa zaki auri soja matan sojoji fa jarumai ne " turo baki tayi ga hawaye na zuba a kunchin'ta chikin shagwaɓa tace Allah yaya Aryan nima jaruma'ce " zuba mata ido yayi yana kallan yadda take Magana gwanin burgewa, hannu ya kai kan fuskar'ta zai share mata hawayen sai dayaji wani shock saboda laushin da tsasin fatar ta, da sauri ya janye hannun'sa baya yamiƙe tsaye yana faɗin to tashi kizo ki karɓi tsaraba yayi maganr yana hawa kan gadon'sa " a sha'gwaɓe tace wayyo Allah yaya Aryan Allah bazan iya tashiba "a sukwane Aryan ya juyo yana kallan'ta, dan yadda tayi maganar, " a hankali kamar bayasan buɗe bakin nasa yace ki daina kukan nan ko gashi nan ae kina ɓata kwalliyar'ki " da sauri tasa hannu ta goge hawayen tana faɗin yaya Aryan kwalliyar ya bacine " dariyace ta kubche masa dan yadda tayi maganar,"bai bachiba yabata amsa yana murmushi " da kyar tamike tanufi kan drawer tana ɗingisa kafa ta zauna "hayewa gadan yayi yajawo trolley ya ɓuɗe, wasu ma tsakaitan jakun kuna guda uku yachiro, daga chikin trolley ɗin, ya juyo ya dubeta yafara magana,"wan nan farin tsarabar kine a chiki, wayan nan bakake biyun kuma kibawa'su Zahra "da sauri tamiƙe ta haye kadon itama ta jawo jakunkunan tana faɗin Yaya Aryan har da kayan kwalliya"kallan'ta kawai yake yadda take zumuɗi, da farinchiki, bai ma san sanda yace, daman farinchikin da dariyar ki kawai nake burin, gani "sai jin diyana yayi tana faɗin to Yaya Aryan dariyana yana da kyau'ne " firgigit yayi yana kallan'ta kwashesu kije ɗaki kiɓuɗe a chan" to kawai tace san nan ta saukoh daga dagon tasa hannu tajawo jakunan amma takasa ɗauka sunyi nauyi bazata iya ɗauka dukkaba" ido yazuba mata yana kallan'ta" turo baki tayi zatayi kuka " da sauri yace aa karkimin kuka ki ɗauka mana ɗai ɗai ae bawanda yace dole ki haɗa'su koh " nasu Zahra ta ɗauka ta bar nata zataje ta dawo suma da kyar ta iya ɗauka gakuma high heel a kafarta
har tafita kallanta Aryan yake, wani ajiyar zuchiya ya sauke yamike yanufi toilet dan yin wanka

lokachin da diyana ta dawo ta ɗauki ɗayan jaka'r Aryan na toilet yana wanka bai fitoba ɗaukar jakar tayi yajuya har takai bakin kofa saikuma tajuyo ta ɗaga murya yaya Aryan sai da safe tana gama faɗin hakan tayi waje, ko data'dawo ɗakin'su su Zahra har sun buɗe jaka'r nasu tsarabar dogayen riguna'ne masu kyau da perfumes masu kanshi da tsada sai murna suke, zama tayi a bakin gado itama tafara kokarin buɗe nata jakar amma sai'taga nata jaka'r an sawa zip ɗin kwa'ɗo, tayi tayi yaki,ɓuɗuwa sai ta ɗauki jakar tanufi sip dashi tana faɗin sai da safe na kaiwa yaya Aryan ya buɗemin,ajiye jakar tayi,tachire kayan jikinta ta ɗaura towel tashi toilet tayi wank atazo gurguje tasa kayan barchi tanufi kichin ta haɗa coffee tasha tadawo ɗaki ta haye gadon'ta nan take barchi awon gaba da ita

Yau tun asuba ake shirye shiryen walima da naɗin sarauta " Ammi tasha kwalliya da wata ɗankarekiyar,shadda tasha aikin har kasa Blue colour tasa wasu shaggun sarkan da abun hannu na gold mai shegen tsada ta ɗaukoh wani ɗankareriyar al'khaiba baki anmasa kwalliya da wasu suwasu mai kyalli fari tasaka a jikinta kai kace yar shekara 20 sosai kyanta yasake bayyana,"wayar'ta ta ɗauka tafa kiran layin Zahra, kira ɗaya Zahra ta ɗaga tare da faɗin hello Ammi" Ammi tace kuzo gaba ɗayan'ku kusameni a ɗaki tana gama faɗin hakan ta katse kiran, ta zauna a kan gado tare da ajiye wayar'ta a kusa da ita

Da sallama su Zahra suka shigo sunsha kwalliya sosai riga da sket na atamfa Zahra hiyana diyana sukasa,"amrat da lamrat kuma duguwar riga, karisa shiga chiki ɗakin sukayi " Ammi tace aa harkun shirya ne" har suna haɗe baki wajen chewa eh "ae ba wan nan kayan zaku saba Zahra'u tashi ki buɗe drawer kayana ki ɗaukoh muku kwalin kayan da zakusa, sai ku koma ɗaki ku chanza " da sauri Zahra tamiƙe ta ɗaukoh musu sarine irin na indiyawa, kwali biyar kowa da kalan nasa " Zahra baki,hiyana pink, diyana blue,lamrat jaa,amrat maroon" da zumuɗi diyana ta ansa nara tana faɗin Aunty zahra irin kayan danake ganin indiyawa suna sawa a TV nan ne " Zahra tace eh shine" to ae Aunty Zahra ban iya sawaba tayi maganar kamar zatayi kuka " dariya Zahra tayi tace to muje na koya miki" da fara'a diyana tamiƙe har suna haɗe baki wajen chewa Ammi mungoɗe

Dakin su suka koma Zahra tafara nuna musu yadda ake sawa wow kayan yamusu kyau sosai da sosai hiyana da amrat nasu najaa a kasa sosai dan yafi tsawon'su
yau make up sosai sukayi dukkan'su baƙaramin kyau sukayiba, hiyana kamar ita tayi kanta yau asalin kyanta ya bayyana datayi make up, Zahra sai santin kyan hiyana take har ita kanta diyana sai da tayaba kyan da hiyana,tayi" Zahra tace kai kuzo mutafi fada dan nasan yanzu gaba ɗaya an haɗu awajen kar ayi bamu kuyi sauri tayi maganar tana kokarin fita ɗakin " da sauri suka bi bayan'ta

Yau fada chike yake tab da jama'a baki dayawa sunzo dan naɗa sabon sarki da za'ayi Abba yasha kwalliya irin na sarakuna sosai yayi kyau yana zaune a kan kujerar sarauta Ummi Ammi Aunty amarya suna gefensa ga wasu kugeru a gefe dama da a ka jera wanda su Khalid, Aiman, Ahmad, Yusuf, Fahad, Haidar umar Aunty farida Aunty salma Aunty, mardiya, Aunty, Maryam, ne zaune awajen, "kujerun gefen hagu kuma manya manyan saraku daga sassa daban daban na Nigeria da ma makwabtar kasashe irinsu niger,Cameron, Ghana,chadi, da dai sauran'su , ga manya manyan yan siyasa a gefe guda " DON da Aryan ne kawai basa wajen, fada yayi tsit kamar babu mutane a chiki kowa yayi shiru suna jiran juran jawabin Abba

Da sallama ɗauke a bakinsu suka shigo fadan, gaba ɗaya jamar waje suka ɗago suna kallan'su kamar wasu taurari sai wal'wali da kyalli suke " gaban Abba sukaje suka duka hiyana'ce tafara ɗagawa Abba gaisuwa "yusuf sai kallon lamrat yake yakasa ɗauke idonsa haka shima Khalid sai kallan Zahra'n sa yake " da fara'a Abba ya amsa gaisuwar tasu ya ɗora dacewa kutashi kuje kuzauna kusa dasu farida, to sukache tare da miƙewa suka nufi wajen'su Aunty farida " diyana kije ki kiramin Aryan ke kuma hiyana kije ki kiramin Safras Abba yafaɗa yana ɗaure fuska dan Aryan da DON sun ɓata masa rai tun dazun ake juran'su amma shiru" da sauri diyana ta juya ta fita, itakuma hiyana tafiya take kamar wadda kwai yafashewa,a chiki kamar zatayi kuka tafito daga fada ta nufi chikin gd

A hankali ta tura kofar ɓangaren nasa tashiga, sallama tayi a palon, kasa babu kowa kamar zatayi kuka ta shigo chikin palon babu kowa, a nitse ta haura stair ɗin tsayuwa tayi a bakin kofar betroom ɗin tanata doka sallama amma shiru shiru almost 20 mnt bataji wani motsi'ba, a hankali ta hannu ta tura kofar tashiga, tana shiga taji kofar yayi kara alamar ya rufe kanshi juyawa tayi tana bin ɗakin da kallo wani katafaren gadone mai girma da kyau yana shinfiɗe da betshit na alfarma Sky Blue ga wani haɗaddɗen sofa guda ɗaya a gefe sai wasu tagwayen kofofi da alama ɗaya kofar toilet ne ɗayan kuma kofar shan iskane,

shiru ta tsaya tana tunanin,kuɗin da aka kashe a ɗakin nan jin karar buɗe kofa yasa tayi saurin kai kallanta wajen zubawa kofar ido tayi dan taga wanene zai fito " DON ne yafito ɗaure da towel a kugun'sa ga jikinsa da ruwa da alama wanka yayi " wani kara hiyana tayi wadda yasashi juyowa a sukwane dan baiyi zatan da mutun a ɗakin'ba " juyowar dayayi bakaramin rikitata yayi ba a guje ta juya taruɗe tama rasa ina zata nufa kawai sai tanufi kofar bangaren hagu tunda taga kofar a buɗe yake tana fita tayi rashin sa'a ta taka sarin'ta dake jaaa a kasa ta kai kai ta tafi kasan bene kallamar shahada kawai take dan tasan mutuwa zatayi..✍️✍️

Tanbaya a nan shin hiyana zata faɗi kasan benen nan kuwa? Shin intafaɗa zata rayu kuwa? ko'ko kar ku manta bene hawa ɗaya tafaɗo daga sama kudai sai mun haɗu

More comments pls 🙏🙏
[7/3, 5:51 AM] Al~Quyraemey: *💫STAR LADY💫*

*DUK ƘARFIN IZZATA*

_💖Story And Written💖_
⬇️
*Star Lady*

*Episode 21*


💖الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر💖

Kalmar shahada kawai hiyana take tagama saddakarwa mutuwa zatayi "kamar daga sama taji an damki kafarta ɗaya,wani dogon numfashi taja tare da sauke nauyayyar ajiyar zuchiya" gaba ɗaya kayan jikinta ya zame ya dawo wuyar'ta daga ita sai ɗan karamin wandon da iya chinya ya tsaya mata ko bra bata saba tula tulan boobs nata awaje "da sauri, DON ya kawar da kan'sa kefe,yana faɗin mikomin hannunki yafaɗa yana ɗaure fuska, hiyana kuwa kayan jikinta ya rufe mata fuska bata ganin'sa hannu kawai ta ɗaga masa " dogon tsaki yaja san nan ya kama hannu nata ya saki kafarta,ta juya suna fiskantar Juna amma idon ta a lumshe "a hankali ta buɗe ido karaf idonta ya sauka chikin nashi, da sauri ta kawar da idon'ta daga kallansa " Ke taka karfe ki hauro yafaɗa yana kara ɗaure fuska " dan Allah yaya prince kayi hakuri wlh bazan iya takawa'ba tayi maganar kamar zatayi kuka " shiru yayi yana tunani wai meyasa ma naka matane, meyasa ban barta, tafaɗa ba wlh badan yanzu idan nasake'ta ta faɗa tamutu nina yi kisan kae ba da sai na saketa, yayi nisa chikin tunani yaji hannunta na zamewa daga chikin nasa,zata faɗa kasa, da sauri yajawota da karfi tafaɗa kan faffaɗar kirjin'sa" hiyana duk tunanin'ta sakin ta yayi tsabar tsorata datayi sai da numfashin'ta ya ɗauke "jin jikinta ya saƙi ne yasashi kallan fuskar'ta hannu yasa ya ɗago haɓar'ta da'alama ta sume "dogon tsaki yaja yana turnuƙe fuska ya saɓeta a kafaɗar sa yajuya chikin ɗakin da ita a saman sofa ya kwantar da ita ya juya yanufi wajen mirrow
Mayukan sa masu kamshi da tsada ya shafa ya feshe jikin sa da perfumes masu kamshi da tsada a nitse ya gyara gashin kan sa sai sheki da kyalli gashin keyi, gashi dark black ga tsansi, a hankali yake takawa kamar baisan taka kasan yanufi dressing room almost 30mnt yayi a chiki san nan yafito chikin suite baki sosai kayan suka masa kyau asalin kirar kijin'sa na jarumin namiji ya bayya half cover baki yasa a kafarsa ga wata ɗankareriyar agogon daimon a hannun sa sai kyalli yake yana ɗaukr ido ya sake fesa,Dubai perfume a jikinsa yadawo gaban drawer ya ɗau wayar'sa yanufi waje, a hankali yake takawa kamar baisan tafiya dakaga fuskar nan tashi kasan yana chikin bachin rae

A bangaren diyana kuwa da sallama ta shigo palon Aryan baya palo Kai tsaye tawuce betroom nashi, sallama tayi a bakin kofa bata jira ya amsaba,tashiga tsaye yake a gaban mirrow, yagama shiri yana fesa turare, dressing iri ɗaya da DON sukayi,jin anshigo ɗakin'ne yasashi ɗago kai ya kalle'ta tachikin mirrow, "asukwane ya juyo domin ya tabbatar wa da idon itace ko aljana che sosai yake kallan ta "itama shi take kallo dan yau baƙaramin kyau yayi ba " ina kwana yaya Aryan tafaɗa tana kawar da kanta daga kallan sa "kasa amsa gaisuwar nata yayi ya zuba mata ido yakasa ɗaukewa "Abba yace wae kazo da sauri tana gama faɗin haka ta juya daniyar tafiya,"da kyar ya iya buɗe bakinsa yace inazakije kuma "juyowa tayi a hankali fada zan koma tafaɗa tana turo baki,"ok to jira muje yana gama faɗin hakan ya ɗauki wayar sa,ya nufota "a tare suka jera kamar wasu taurari, kyau iya kyau "kayan nan sun miki kyau sosa, yafaɗa yana kokarin jan kofar palon "Yaya Aryan to tunda sunmin kyau kamin hoto dan Allah ta karisa maganar a shagwaɓe "to tsaya namiki guda biyu da wuri kinga Abba na jiran mu,"to hutona wajen guda 15 ya ɗauke'ta batare daya sani ba,"har sai da tace Yaya Aryan baka gama bane," nagama amma matso nan na mana mu biyu "da sauri ta matso kusa dashi,ya juyo da wayar yamusu selfie kala 5 san nan yace,to muje "to ae baka nunamin hoton ba a shagwaɓe tayi maganar tana turo baki "mika mata wayar yayi yana faɗin,to muje muna tafiya kina kalla har mu iso, "to tace tare da fara tafiya

Da Sallama suka shiga fada,gaba ɗaya kallo yadawo kansu," a sukwane Khalid ya ɗago yana kallan su kama yajuyo yana kallan Yusuf yayi da shima Yusuf ɗin kallo Khalid ɗin yake," Abba naganin su atare ba faɗa ba ɓachin rae a fuskar Aryan sae ma annashuwa daya gani a tattare da Aryan ɗin gawani ɗan murnushi da Aryan ɗin keyi yakai kallansa,kan diyana dake gefensa sun gera kafaɗa rike take da wayan Aryan tanata sakin murnushi"wani daɗi Abba yaji ya lulluɓe sa baima san lokachin daya fara sakin murmushi ba,chikin ransa yana faɗin alhamdulillah alhamdulillah, Allah na goɗema saura Safras kuma ya Allah ka kar'katomin da hankalin sa shima yadawo mutun
"kasa kasa Umar yace wa haidar wai haidar ba wayar,yaya Aryan bane a hannun yarin yar nan,"shine mana haidar yaba shi amsa yana taɓebaki,"Aunty amarya kuwa kamar zata mutu dan bakin chiki tayi kwafa a zuchiyar'ta tana faɗin wlh,nakusa kawo karshen ku,"Ammi da Ummi kuwa ko ajikin su

"jerowa Aryan da diyana sukayi kamar wasu taurari,sae taku suke a nitse diyana na kallan waya Aryan kuwa ya ɗaure fuska yana kallan kasa sai da suka iso tsakiyar fada, Aryan ya juya yanufi wajen zaman su " da sauri diyana tace yaya Aryan wayan,kafa ta tambaya tana kallan'sa "baga ɗaya jamar wajen ido kawai suka zuba musu "Aryan baiyi magana ba har sai daya kae wajen zaman'l su ya zauna kusa da Khalid san nan ya ɗago ya dubeta kije da wayar idan kingama kallan hoton sai ki kawomin,"mamakine yakama gaba ɗaya family Abba musan man Aiman Aunty mardiya Aunty salma Umar haidar Ammi dakuma Ummi,
"Abba da Khalid da Yusuf kuma sae murmushi suke,"Aunty farida kam tafi kowa murna da hakan, "Aunty amarya na sanyin magana tana tsoran Abba gakuma taron jama'a kar aji kunya,Amma tachi al'washin yin maganin abun " Aunty Maryam kuwa kamar,zata mutu take ji dan bakin chiki,"kusa da Aunty farida diyana taje ta zauna tana faɗin Aunty farida ki kalla tayi maganar tana nunawa Aunty farida wayar Aryan,dake hannun'ta "ansar wayar Aunty farida tayi tafara kallan hotu nan, mamakine ya bayyana a kam face ɗin ta a hankali ta ɗago kae tana kallan inda Aryan ke zaune,"shima ita yake kallo, suna haɗa ido yama alama da ta kashe masa wayar kar tabari kowa yaga hotan, Jinjina kai kawai Aunty farida alamar to san nan ta kashe wayar ta sa chikin jakarta,"ta chiro wayar ta tamikawa diyana "da sauri diyana ta amsa tana murmushi tafara buga game " tunani Abba yashigayi ba hiyana ba DON anya lfy kuwa buɗe baki yayi zaiyi nagana sae ga DON yashigo shi kaɗai "taku yake irin na jaruman maza gaba ɗaya Jamaar wajen,sai kallansa suka dan yahaɗu sosai mazama burge'su yake bare mata, kusa da Aryan yaje ya zauna " gyaran murya Abba yayi ya dubi DON yafara magana Safras ina hiyana take " shiru DON yayi yana ɗan tunani wacece kuma hiyana,kodai wan nan yarinyar da aka aiko takirani " Abba ne ya katse masa tunani dachewa wai ba kai nake tambaya ba "da sauri yace tana ɗaki Abba yafaɗa yana turnuƙe fuska "gaba ɗaya idon kowa yadawo kansa "to meyasa kabarta a ɗakin Abba ya tambaya yana karewa DON kallo " akule yace suma tayi Abba zan zuba mata ruwa kuma na manta Fahad yaje ya'zuba mata ruwa yayi maganar yana nuna Fahad da hannu " a ruɗe Ammi tace me kamata tsorata kayi koh " ka daure fuska yayi yana faɗin tazo zata faɗine na riketa ta tsorata da yawane shiyasa ta suma, ya karisa maganar kamar zae fasa ihu dan haushi,a ransa yana chewa wlh badan iyayena,ke min wan nan tambayarba da bazanyi maganaba haba dan Allah ayita sa mutun magana, "Ammi zata sake magana,Abba ya ɗaga hannu alamar tayi shiru "mikewa Fahad yayi

Please Login or Register in order to submit comment