Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gd tare koh

Gyara tsayuwar su sukayi har lamrat ta kariso, sanye take da kayan fulani farache tas itama mai dogon hanchi kamannin'ta ɗaya da hiyana sai dai idon su ba iri ɗaya bane idon lamrat baki ne idon hiyana kuma blue ne lamrat bazata wuce 13 years ba " lamrat kindawo chikin harchen fullanchi diyana tayi maganar " lamrat tace eh Aunty diyana nadawo "Allah yasa kin sayar da nonon chewar hiyana "eh aunty hiyana nasayar dukka "murmushi diyana tayi tana faɗin alhamdulillah nagodewa Allah dayasa kika sayar yanzu kinga inna bazata bugekiba " nifa aunty diyana duk dukar da inna takemin bai dameni'ba nidai kawai bansan naga tana bugun ku,in nika'ɗai zata yita bugu bazan damuba "to aimuma hakanne bamusan inna ta bugeki ya'fimana tabuge'ni nida diyana tabar ku ke da amrat "hmmm hiyana yakamata mushiga gd kunji anfara kirar sallar mangariba koh chewar diyana " hiyana tace gaskiya kam mutafi tayi maganar tana mikawa lamrat ledar gyadar dake hannunta "aa Aunty hiyana nasan tun safe baku chi komai'ba, ni kuma kinga bintu tabani abinchi awajen talla kuchi kawai " hannu hiyana tasa aledar ta debo gyadar ta mikawa lamrat tana faɗin abinchi daban gyada ma daban " lamrat tasa hannu ta amsa gyadar kana tayi godiya haka suka jera har chikin gida

da sallama suka shiga innar tasu na tsakar gida tana zaune ga amrat zaune a gefen ta, tana tuka mata tuwo, wuchewa kichin hiyana da diyana sukayi dan juye ruwan dasuka ɗebo lamrat kuma tazo ta sugunna a gaban inna ta chiro kudi tamika mata
inna ta karba ta irga kudin san nan tace "yau Allah ya rufa miki asiri kitashi kije ki daukoh wanke wanke kimani,murya na rawa lamrat ta fara magana "inna dan Allah kibari nayi sallah dan wlh ko a'zahar da la'asar banyiba ga kuma mangarib.. bata karasa maganarba ta'farajin saukar duka, da karfi tafara ihu tana faɗin dan Allah inna kiyi hakuri, da gudu diyana da hiyana suka fito daga kichin ɗin sukayo wajen inna suka duka kasa suka kama kafarta suna faɗin inna dan Allah ki kyale ta mu ki dakemu a madadin ta dan Allah inna kiyi hakuri, kafa inna tasa ta shuresu ta ɗau koh itachen a chikin wuta a murhun da amrat ke tuka tuwo tafara bugun su dashi, suna ihu kamar ran su zai fita, amrat na tuƙa tuwo tana kuka, haɗesu inna tayi tamusu duka mai isar duk ta gun bura musu jiki, zama tayi a saman dutse tsakar gidan tana mai da numfashi, "ke diyana ke da hiyana kutashi kutafi ɗiban ruwan ku wlh tun ban tashi na ɓaɓɓala ku ba chikin tsawa inna tayi maganar ke kuma lamrat kitashi ki kama aikin dana saki, ba kun che bakuji ba to wlh zan gyara muku zama a gd nan

da kya hiyana da diyana suka mike ga yinwa ga gajiya ga wahala ga duka gashi ko sallar azahar basuyiba ga mangariba tayi ga dattin da jikin su yayi haka suka mike suka dauki cups ɗin suka nufi waje suna hawaye lamart kuma tamike tanufi kichin ta tattara wanke wanke ta fito ta ɗebo ruwa ta fara wanke wa tana kuka mara sauti

Misalin karfe 9 na dare,tafiya suke achikin duhu suna kuka suka shiga chikin dabbobin su, suka juye musu ruwan suka fito, diyana ta tsaya akusa da bishiyar mangoro kofar gidan su A gala baice hiyana tace "diyana muje saura mana sahu biyu ne ae "wlh hiyana ba zanjeba Allah sai dai inna ta kasheni yau tayi maganar tana kokarin zama awajen "to shike nan kizauna a nan kihuta bani kofin naki naje nadebo har da rabon ki, amma dan Allah karki koma gida dan in kika koma nasan inna zata buge ki, ki zauna har nagama, ɗebowa sai mushiga gida tare, diyana dai ko magana takasa jin hiyana kawai take,
juyawa hiyana tai chikin duhu tanufi hanyar rafin, diyana kuwa kwanchiya tai a kasar itachen ba jimawa barchi ya dauketa, hiyana tana tafiya chikin kun gurmin dajin nan tanata surutu ita kaɗai," ya Allah kaba mu ikon chin wan nan jaraba wan Allah ka mikarma na da bappan mu yafara takawa da kafarsa ya Allah kajikan innan mu ya allah kakaremin yan uwana Allah mungode mungode alhadulillah alhadulillah, Allah karkabari a ɗaura aure na da buba ba'nason sa ko kaɗan, wayyo Allah na wai meyasa bappa ya Auri inna habiba ne meyasa bai yi zaman sa haka nanba tunda dai shi da kansa kullun yake chemana baya santa to meyasa ba zai che tatafi gidan suba, wayyo ni hiyana ya zanyi Allah kadubi mu da idan rahma, hakadai hiyana tayi ta addu'oe da surutanta, harta karisa ɗebo sauran sahu biyun dasuka rage,

tadawo wajen da diyana ke kwanche kasan itachen, tafara kiran sunan ta, wajen duhu ne bata kallon komai,"diyana kitashi mutafi gida nagama ɗiban ruwan, shiru diyana bata amsa ba kara kiran su nanta hiyana tayi nanma tasake jin shiru, da saurin hiyana ta duƙa kasa tana laluɓe kozata tabota amma shiru bataji diyana awajen ba, Arude tamike zubur tayi chikin gida da gudu, ɗakin su ta faɗa ko sallama babu, amrat da lamrat tasamu zaune suna fiskantar ɗan fitillar kwan dake ɗakin sunyi jugum jugum "lamrat ina diyana,hiyana ta tambaya tana zaro blue eyes nata waje "chikin rau'nanniyar murya lamrat tace ban ganta ba, hiyana zata sake magana amrat tamiƙe ta riƙe hannun tana hawaye chikin muryan kuka tace "Aunty hiyana yinwa nakeji chikina chiwo yakemin sosai, dan Allah kine momin abunda zanchi ko kaɗanne hiyana batasan lokachin da hawaye zuba wani na bin wani yafara zuba a kuma'tun taba, da wanne zata ji gaji'yar ɗebo ruwa ko kuma yinwa, ko ɓa'tar diyana, gasu amrat na kukan yinwa, riko hannun amrat ɗin tayi chikin dashe war murya tace "jeki zauna kinji yanzu zannemo miki abinchi duk inda yake "to kawai Amrat tace san nan takoma wajen zamanta ta zauna, da sauri hiyana ta juya tafito daga ɗakin tana tunanin mugunta irin na inna watarana su suke girka abinchin gidan nan amma inna bata basu sai ran da taga dama ko bappan suma babashi take ba, kai Allah wadaran zuchiya irin na inna

Da wan nan tunanin tanufi ɗakin inna bakinta ɗauke da sallama, kwanche ta isko ta a kan figaggiyar gadan chiyawar'ta " bata amsa sallamar ba kuma idanta biyu Murya na rawa hiyana tafara Magana "inna banga diyana bafa "to idan bakiga diyana ba sai me ina ruwana dawata diyana zaki'tashi kifita min a ɗaki'ne ko sai na tashi na babballaki, mikewa hiyana tai tafita tana tunanin tafaɗawa bappa ne kuma intafada masa ma hankalin sa ba karamin tashi zai'yi ba, gashi ba lfy ne da shiba, kai gwara dai naje tanemo ta da kaina basai na faɗawa bappa ba, da wan nan tunanin nufi waje.

KANO

Aunty farida Ammi Ummi da Aunty amarya sai Khalid da Zahra zaune suke awani katafaren palo mai girman gaske, mai ɗauke da manya manyan Sofa masu matikar kyau da tsada ga laushi set biyu launin milk colour, ga wata makekiyar Tv daga gefe, sai table ɗin chin abinchi mai ɗauke da gujeru 12, idan nace zan tsaya zayyana muku kyan palon nan tofa zamu kwana a nan, zaune suke shiru,sallama Fahad yayi ya shigo palon zama yayi a saman 1str yana gaidasu Ummi, da sallama haidar da Umar ma suka shigo da alamadai family meeting zasuyi Almost 20 mnt suna zaune ba wanda yake magana kowa da abun da yake daga masu latsa waya sai mai daddan na laptop "wayar Aunty farida che yayi kara alamar shigowar kira, ɗaukar wayar tayi tana bin screen ɗin da kallo,ganin sunan my prince, yana tamiƙe da sauri tayi waje,daga gefen bakin kofar ta waje ta tsaya san man tayi picking call ɗin tare da kara wayar a kunnenta tace "hello prince daga ɗayan bangaren DON yace "kun gama meeting ɗin ne "aa yanzu dai zamu zamu fara Abba muke jira yafito "to amma kina ganin zamuyi nasara kuwa "kai prince kabari dai idan mungama mayi magana, naji muryan Abba yafito bata jira amsar'saba da sauri ta katse kirar, ta koma chikin palan, wajen zamanta takoma ta zauna
Abba kyakkyawar dattijo ne mai chike da kalama, kallo ɗaya zaka masa ka gane duk yaran gd ka'maninsa suka yo farine tas mai dogon hanchi ga manya manya ash eyes yana da dogon gemu da lallausan saje, gashin kansan nan a kwanche kamar na larabawa zama yayi saman sofa mai ma zaunin mutun1 bin yayan sa yake ɗaya bayan ɗaya da ido yana kallan su shiru palon yayi Almost 5mnt san nan Abba yayi gyaran murya, yafara magana ina Aliyu yake,yayi tambayar bai kai ga rufe baku ba uncle Aliyu yashigo da sallama sanye yake chikin wata dakakkiyar shedda fara tas mai kyau da tsada, kaman'nin sa ɗaya da Abba, gaba ɗaya palon har suna haɗa baki wajen amsa masa sallamar da gudu Zahra tamike ta nufe sa tana faɗin "oyoyo uncle Aliyu oyoyo ta faɗa jikin sa, rungumeta yayi shima tana faɗin "oyoyo autar'mu oyoyo autar'mu san nan ya zare daga jikinsa ya rike hannunta suka nufi wajen Abba saman sofan dake kusa da Abba uncle Aliyu ya zauna tare da zaunar da Zahra a gefen sa, a nitse uncle Aliyu yace ina kwana yaya da fara'a Abba ya "amsa lfy, juyowa yayi ya gaida su Ammi, suma da fara'a suka amsa masa san nan matasan gidan suka fara gai dashi yana amsa musu ɗaya bayan ɗaya da murmushi a face nashi
A nitse Abba yafara magana to ku bani hankalin ku nan,duk suka nitsu suka zubawa Abba ido suna saura ren sa chigaba da magana Abba yayi "nataraku a nanne dan inasan magana daku gaba ɗayan ku amma baku gama haduwa'ba dan haka farida ki kiramin sauran yan uwan naki awaya kifada musu duk Abun da suke subari nan da rana ita yau ina bukatar kowa a nan,"
Aunty farida zatayi magana Abba yaɗaga mata hannu aa farida umarni'ne kuma banasan ɗaya daga chikin ku yamin wata magana kutashi kuje zamu sake magana rana ita yau
sai yanzu nagane aina su DON suka ɗau koh idan sunyi magana basa chan zawa ashe awajen Abba ne tab aiko akoi kallo wayyo
[7/3, 5:45 AM] Al~Quyraemey: *DUK ƘARFIN IZZATA*

_💖Story And Written💖_
⬇️
*Star Lady*

💖 The talent troupe writer's💖

Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

*Episode 4*


YOLA

Almost 11 na dare hiyana na waje tana neman diyana amma shiru shiru ba diyana ba lbrn'ta hiyana tayi kuka har ta godewa Allah kamar zatayi hauka, ta juyo ta dawo gida jiki a sake ba kwari, yanzu tama daina jin yinwar da takeji burin ta kawai taga ƴar uwar'ta
tana shiga gida ɗakin su tanufa kwanche tasamu lamrat da amrat manne da juna sunyi barchi, ga hawaye nan abushe a fuskar su da'alama sunyi kukan yinwa har sun gajine barchi ya dauke su
zama tayi akasa kusa dasu su,ta zuba musu blue eyes nata, wasu siraran hawayen takai'ci nabin kunchinta duniyar tunanin inda diyana take tafaɗa, kamar daga sama taji an bude kofar zanan ɗakin nasu an shigo, zubur tamike tana kallan sa ɗauke yake da wani abu a'kafadarsa kamar mutun hasken fitilar baya haska su sosai shiyasa bata gane me yake ɗauke dashi ba, murya na rawa "tace yaya bello kaine, kasa kasa bello yafa magana "eh nine kana ya raɓa ta gefen su lamrat ya kwantar da diyana, a ruɗe hiyana tace "yaya bello me yasame'ta'? aina kagan'ta? Ta mutune'? Naga bata numfashi
"hiyana kinitsu mana bata mutu ba suma tayi, kinga yanzu dare yayi zanje gida da safe in kunzo ɗeban ruwa saimuyi magana,in bahaka ba kinsan idan inna ta ganni to nashiga uku, dan haka kiyi shiru karma taji wani motsi, yana gama faɗin haka yajuya ya fiche daga ɗakin
itakuwa hiyana ta gyara zaman ta, tana kallan fuskar diyana tana kuka, haka ta kwana kamar yadda taga rana haka taga dare

washe gari tun asuba inna ta shigo ɗakin nasu hannu ta riƙe da tulu mai ɗauke da ruwa da karfi ta zubawa diyana nan take diyana ta farfaɗo tana ihu, inna bata bi ta kanta ba ta juya ta zubawa amrat da lamrat a razane suma suka farka, juyawa inna tayi ta zuba sauran ruwan a awajen Kwan chiyar hiyana a tunanin ta hiyana na ɗakin,Amma sai taga akasin haka ba hiyana a wajen a fusache ta juyo gun su diyana zatayi magana taji diyana na sambatu, tana faɗin "dan girman allah buba ka kyale ni kayi kahuri, wayyo allah hiyana ta ina kike kizo ki chech..bata karisa maganar ba taji saukar duka ta ko ina ajikin ta, ihu diyana ta fasa wayyo Allah na shiga uku hiyana kizo ki tai makeni buba zai kashe ni, wani bugu inna ta kai mata a baki sai da bakin nata ya fashe, ihu a zaba diyana ta saki, shake mata wuya inna tayi tana faɗin "me buba na yamiki da za kiche ya kyale ki, ko kinga buba a nan ne eh, kodai wani mugun abun kuke shirya masa, jin maganar inna yasa diyana ta dawo chikin hayyachin ta, da kyar ta iya faɗin "inna kiyi hakuri zan mutu dan Allah ki sake min wuya, naushi inna ta sake kai mata a baki tana faɗin "ki mutu mana ina ruwana daman uban me kuke tsinanamin a gd ba gara ku mutu kowa ya huta ba, kara shake diyana inna tayi sosai sai dataga blue eyes nata sun fir fito waje sosai tana kokarin mutuwa da gaske,da sauri ta sake ta tana mai da numfashi, juyawa tayi tana kallon amrat da lamrat in da suka takure waje guda suna hawaye chikin tsawa tace "ke lamrat kitashi kije ki ɗoramin girki idan kin gama kizo kitafi talla, ke kuma amrat ki wuche kije kimin wankin kayana kiyi shara da wanke wanke, itakuma wan nan shai ɗaniyar ni zata sa na zubar da ruwa a kasa koh to wlh gaba ɗaya ruwan gidan nan sai na zubar dashi ku ɗebo wani, ke diyana ki tashi ki ɗauki kofin ki nemo wan nan shai ɗaniyar kufara ɗebomin ruwa kuma wlh daga nan zuwa karfe 10 ku chika komai na gd nan, dan dole yau ku jemin tallah ba zanyi asara ba, tana gama faɗin hakan,
ta juya tayi nufi hanyar fita har ta kai bakin kofa sai kuma tace wlh idan kuka bari na kai tsakar gd baku fito ba na lahira sai yafi ku jin daɗi, jiki ba kwari lamrat da amrat suka mike suka fice suka bar diyana kwanche baki na jini sai kuka mara sauti dake

Inna na fitowa tayi karo da hiyana a tsakar gida hannun ta rike da cup guda biyu da alama ruwa take ɗebowa "ke ni zakiwa iskanchi to wlh barikiji duk ruwan dake gidan nan saina zubar dashi a kasa kun ɗebo wani, san nan kuma ke kafin kifara zubawa a randu nan nan, sai kinyi sahu 10 kina ɗebowa kina zubar wa a kasa har sau 10 tukun nan, kifara zubawa a tulu, ni zakisa nayi a sara ruwa ba nashiga ɗaki zan tashe ki ashe ba kinan ki kasani na zubar da ruwa a kasa koh, ke gaki mai wayau tun asuba kintafi ɗebo ruwa, kuma barikiji duk yadda zakuyi kuyi nan da karfe 10 dole kuchika ko ina na gidan, nan san nan ku jemin talla dan yau bazanyi asaraba, tana kaiwa nan ta wuche tanufi kichen, tafara zubar da ruwan dake chikin randu nan da kuma tulu nan,sai da ta tabbatar babu wani tulun daya yage da ruwa a chikin sa san nan tafito tawuche ɗakin ta ta haye gado, babusallar asuba
Dur kushewa kasa hiyana tayi ta rushe da matsanan chin kuka, mai tsuma zuchiyar mai sauraro, kuka take kamar ranta zai fita sai datayi kukan, mai isar ta san nan ta ɗago kai tana kallan su amra dake tsaye a bakin kofar dakin su, alama ta musu da hannu aka sutafi sufara aikin su kar inna tafito ta gansu, ganin babu diyana a wajen ne na yasa ta mike da kyar tanufi ɗaki dan tadubo ta

Kwanche ta samu diyana sai kuka take "ita chikin muryan kuma tace diyana kitashi mutafi mu fara aikin mu tafaɗi hakan chikin shasshakar kuka "wlh hiyana bazan iya tashiba jinake kamar zan mutu chikina murdamin yake saboda yinwa "to diyana ya zamuyi kinsan dai in kika zauna inna ta dazo ta sameki duka zata kara Miki, kitashi muje saiki zauna a gonar yaya bello ni kuma na ɗebo ruwan "to zoki rikeni natashi, matsowa hiyana tayi ta kama kafaɗarata, ta tai maka mata tamike har tangal tangal take kamar zata faɗi da kyar ta tsaya a kan kafafunta aruɗe hiyana tace "diyana yanaga jini a jikin zanin ki wai ma ina ki kaje jiya
"a tsorache diyana tafara magana hiyana bansan ya akayi naga jininba nima, daga gabana ya fito
shiru hiyana ta ɗanyi kafin tace to chanza kaya muje, zamuyi magana a hanya dan in muka tsaya magana a nan inna zatazo ta same mu, da sauri ta ɗauko wa diyana wani tsunmar zanin atampa yasha ruwa duk ya koɗe ta ɗaura mata, tariko hannun ta
da kyar diyana ke ɗaga kafa da kyar take ɗin gisa kafar tana tafiya suka fito tsakar gida, suka samu su amrat kowache takama aikin ta, amma kallo ɗaya zaka musu kasan suna chikin tashin hankali ga yinwa duk sun galabaita, girgiza kai kawai hiyana tayi, ta duƙa ta ɗauki cups ɗin data ajiye suka nufi waje

Suna futa hiyana tafara tambayar diyana "ina kikaje jiya diyana "jiya na kwantane awajen da kika barni sai barchi ya ɗauke ni ina chikin barchi kawai sainaji a'na kokarin chiremin zani, nabuɗe idona a razane sainaga bubane, da nayi kokarin guduwa shine yakamani ya wanka min mari, kuma yasa kafa ya takamin wuya ya chiremin zani, inata rokansa da ya kyaleni amma yaki da kyar na samu na laluɓi wani karfe nabuga masa a kafa, shine yachire kafarsa a wuyata yafaɗi kasa ni kuma natashi da kyar zan gudu kawai naji ya bugamin wani abu a kai daga nan kuma ban sake sanin komai ba saida inna ta zuba mana ruwa ɗazun ta kare maganar chikin shesshekar kuka "to ae na ki kasamu jinin jikin kin nan kuma "nifa hiyana nache miki ban'saniba kawai ganinsa nayi " jinjina kai hiyana tayi tana faɗin yazama wajibi muneman wa kammu mafita wlh " to yanzu ya zamuyi ke nan tayi maganar dai dai lokachin dasuka isa bakin rafin"hiyana tace ki bari inmun samu lokachi iri idan inna bata nan sai muje muyi magana da bappa, yanzu dai ki ɗebo ruwa ki wanke jinin jikin ki nan, san nan muyi al'wala kinsan jiyama bamuyi sallar azhar laasar mangariba da kuma issha ba, gashi yan zu kuma ana sallar asuba sai muhaɗa dukka,muje kasar itachen chan mubiya bashin sallolin kafin mufara ɗiban ruwa "to kawai diyana tace san nan tanufi bakin rafin ta ɗebo ruwa ta koma gefe ta wanke jikinta tas san nan sukayi al'wala suka nufi kar'kashi bishiyar mangoron suka shinfiɗa ɗan kwalin su suka ta da sallah,
sai da suka biyan bashin sallar da akebin su, najiya san nan sukayi sallah asuba

addua hiyana tai sosai" ya allah kayafewasu amra ba laifin su bane innache kehanasu yin sallah Allah mun'tuba haɗa sallah da muke Allah kayafe mana
diyana kuwa adduar Allah yakawo musu mafita take hakadai suka gama adduar san nan su kamike " hiyana tanufi bakin rafi tana faɗin diyana kishiga gonar yaya bello ki zauna ki huta, ruwa ta ɗeba a cups ɗin ta kama hanyar gd, ta kuma diyana tashiga chikin gonar yaya bello ta zauna da yake gonar a bakin rafin yake daga chikin gonar kana iya kallan chikin rafin

har karfe 8 na safe diyana na zaune a chikin gonar bello, hiyana kuwa saifaman jidan ruwa take ammafa da cups yan zuma taɗebo ruwan takama hanyar gida tanajan kafarta da kyar da kyar har takai kusa da gida zata shiga ke nan, buba ya tare mata gaba ɗaure fuska hiyana tayi sosai" babu kabani hanya
hannu buba yasa ya buge cups ɗin dake hannunta yafaɗi kasa ruwan yazube, hiyana kamar zatayi kuka ta duka kasa ta ɗauki cups din har kwallah yafara zuba a idan ta batachewa buba ko kalaba takama hanya tajuya tanufi hanyar komawa rafin, tana tafiya wasu siraran hawayene masu dumin gaske ke zuba mata a'kan kunchin ta.

haka takoma rafin tasake debo ruwan tajuyo ta zata tafi ke nan taga diyana a tsaya a bayan ta "hiyana kawo in karɓa miki kekuma kije ki huta tunda tun asuba kike deban ruwan nan "aa diyana kingafa ke baki da lfy dan haka kije ki zauna kibari zanyi "diyana tace aa to kawo nayi ko sahu 10 ne sai ki karba " sahu 10 yayi yawa diyana ki daiyi 3 "to bani cups din, mikama ta cups ɗin hiyana tayi, tawuche tanufi chikin gonar yaya bello
diyana kuma tanufi hanyar gida kodataje itama zata shiga gida buba tagani tsaye a bakin kofar gidan su batache masa ko sannuba tazo taraba gefen'sa zata wuche, buba ba tsoran Allah yasa hannun sa yasake buge cups din ruwan da diyana take da shi suka faɗi kasa ruwan ya zuɓe "a fusache diyana ta ɗago zatayi magana kome ta tuna kuma sai tafasa ta duƙa ta ɗauki cups din tajuya takama hanyar komawa rafin, buba kuwa yana ganin ta tafi yayi murmushi mugun ta cheke da izza da iya shege yafara magana,"ai kunshiga uku dani wlh bazan taba bari ku zauna lfy ba, narinka kuntata muku san nan kuma in na Auri hiyana in maida ta baiwar kowa na kauyen nan,dariya yayi sosai san nan ya chigaba da chewa kai amma goggo habiba ma yar aljanna che wlh ta iya horaku ɗeban ruwa da kofi ai shine maganin ku, a hakanma nikuma ba barin ku zanyiba, narinƙa addaban rayuwar ku kenan ina kifar da ruwan, yau sai kafarku ta daina takawa yasake kwashe wa da dariya kamar mahaukachi

diyana kuwa juyawa tai komawa rafin ta taɗebo wani ruwan tanufo gida, ko datazo kofar gida ba'tasami buba'ba ba'karamin daɗi tajiba alhllh ta furta san nan tanufi gidan zata shiga, kamar daga sama taji an buge cups ɗin hannunta sun faɗi kasa ruwan yazube
a fusache ta ɗago ganin bubane a gabanta hakan yasa tarufe ido ta zabga masa mari a kumatu
diyana daman bata da hakurin jure wulakanchi

buba kuwa bai'yi wata wata ba ya kwashe kafafunta tafaɗi kasa kanta ya bugu da jikin wani dutse dake bakin kofar gidan, wani ihu azaba ta sake, buba kuwa bai tau saya mata ba ya hau bugunta kamar ai aikoshi
diyana sai ihu take ganin zai mata illa babu wanda yakawo mata agaji yasa tamike da kyar tana kokarin guduwa
damkoh hijabinta yayi tabaya ya shake mata wuya ya bugata da kasa wani azaba taji gashi yaki sakin hijabin nata ga wuyan'ta a shake da gyar take numfashi ,tagama sad'dakkarwa mutuwa zatayi sae kuma taji buba yayi ihu kuma ya saketa "da kyar ta iya buɗe ido ta sauke su a kan yaya bello dake tsaye rike da sandar kiwo,sai huchi yake kamar wani zaki, ga buba kuma sume a kasa
hannu yaya bello yasa ya ɗauke ta chak ya saɓata a kafaɗarsa yanufi hanyar rafin da ita, nan sukabar buba kwanche, bello irin mazan nanne masu karfi gashi dogo sosai kakkarfa

kai tsaye gonarsa yanufa da ita hiyana na zaune taga yaya bello ɗauke da diyana a kafadarsa
da sauri tamike tanufi'sa tana faɗin hande miboni yaya bello me kuma yasame'ta

Please Login or Register in order to submit comment