Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wlh nikam a barni gara namutu wlh da amin allura " ajiye kofin tea ɗin Ammi tayi a kan drawer san nan tadubi don tace rikemasa ita yamata alluran nan dan nalura bazata tsayaba " hiyana jin anfaɗin hakan tafasa kara ta zura a guje zatayi waje " taku ɗaya don yayi ya damkohta yaɗagata sama sai kan gadan sai faman wurga kafa da hannu take sama taki tsayawa " aguje diyana ma tayi kan gadan itama suka sake rungumar juna " mamakine yaka don da Aryan yara kaman wasu chingam "
Ammi dai chewa tayi barina natafi ai dankuna kallonane inbaku ganniba kila kuji tsoron yayyunnaku tadubi don tamasa magana chikin harshen turanchi, karkamusu tsawa sosai kaga bata da lfy kabisu a hankali, dayake su diyana basa jin turanchi, bayan Ammi taga fadawa don hakan tajuya, tace to gaku ga yayanku inbaki tsayaba ya bugeki baruwana ,natafi tana gama faɗin haka tafiche,

Aryan yaɗago yana kallan don irin kallan me abunyi yanzu " kan kadan don yanufa yana zuwa yasa hannu yakamo hiyana yakuma dakawa diyana tsawa ke sauka, jiki na bari ta saukoh tana kuka " haɗe hannun hiyana don yayi ya matse san nan yache da Aryan kayimata allurarmana kana kallona " murmushi kaɗan Aryan yayi kana yace haka akerike wadda za'awa allura ka gyaramin ita da kyau pls " harara don ya wurgawa Aryan san nan yajawota jikinsa ya rungumeta sosai ya dauke fuska daga kallon Aryan yakara ɓata rai " Aryan kam abunma dariya taso bashi amma ya matse dan kar don yache bazai riketaba kuma inbasu mata alluraba Ammi bazataji daɗin ba " kawo hannunki chewar Aryan " hiyana kamar bataji me yache ba taki bada hannu " kallan don yayi san nan yache mikomin hannunta " a'fusache ya damki hannunnata ya mikawa Aryan " rike hannun Aryan yayi sosai dan sai mutsu mutsu take taki tsayawa
Aryan natsira mata allurar ta pasa kara ta kankame don tana faɗin wayyo allah Ammi kasheni zasuyi " da gudu diyana ta dawo kan kadan ta zauna kusa da hiyana " Aryan na zare allurar " don yana sakinta yamike da sauri yabar ɗakin,
Shima Aryan ɗin daukan box nashi yayi yabi bayan don " hiyana kuwa kuka take sosai sai rarrashinta diyana take " Zahra na ganin su Aryan sun fita tashigo ɗakin da gudu

Don nafita daga bangaren Ammi kai tsaye part nashi yanufa " Aryan ma yana fitowa yabi bayansa kusan tarema suka shiga part ɗin don ɗin suna shiga betroom ɗin " Aryan ya ajiye box ɗin hannunsa akan mirrow yajuyo zaiyi magana don yarigasa dachewa " maganar me kakesan muyi kuma " Aryan yace kai akoi alamar tambaya akankufa don " alamar tambaya kuma to akanmu nidawa don ya tambaya yana jiran amsa " kai da yarinyar nan mana Aryan yabashi amsa a takaiche " wache yarinya kuma chewar don " wanda karike yanzu nawa allura " dogon tsaki don yaja kana yace banasan haka Aryan danna riketa kawai kasanifa farinchikin Ammi nema kawai yasa nazo ɗakin ba wai wani abuba " tabbas akoi aya tambaya akanku bagashiba period natanma daya fara zuwa kai yafarayiwa sallama " waro green eyes nashi waje yayi yace what mekake nufi banganeba " Aryan yace kalli jikinka mana kagani " da sauri don yadukar da kansa yanabin jikinsa da kallo jini yagani a dai dai saitin a' sukwane yachire jallabiyar yayi wurgi da ita gefe " Aryan baisan sanda ya kwashe da dariyar da baitabayiba dariya yake harda rike chiki yana faɗin tab aiko " akoi babbar a'yar tambaya makuwa abun harda short " da sauri don yadubi short ɗin jikinsa aiko jinin yagani a dai dai saitin a'sukwa yanufi toilet " chikin dariya Aryan kefaɗin kai amma jininma ya iya zaɓen wajen da zai zuba wlh, ai nazachi short ɗinma chireminshi zakayi a nan yasake kwashewa da dariya harda faduwa kan gado

Ammi che tashigo ɗakin da sallama tasamesu akan gado hiyana da diyana anchi kuka ankoshi " hiyana ki dauki tea din nan kisha kitashi kije kiyi wanka ki gyara jikinki chewar Ammi " to kawai hiyana ta amsawa Ammi dashi tamike kenan taga jini a inda tatashi da mamaki take kallan wajen zatayi magana sukaji maganar yusuf yana shigowa yana waya da sauri hiyana tanufi toilet " Ammi ta kalli Zahra tache kitashi ki gyara wajen ki dauko mata always da pant tana kaiwa nan tajuya zata fita ke nan dan tayi sauri ta tare yusuf awaje sai gashi yashigo " yabakuyi shirin zuwa school ba karfe 7:35 yanzu " aa yusuf yau nache su ajiye zuwa school ɗin sai gobe chewar Ammi " kallon Ammi yusuf keyi kamar akoi abun da ke damunta dan yaga alamun hakan a chikin idonta, amma sai yache to shike nan, daman nazo daukarsune, tun da bazasu jeba barinaje nadubo don da Aryan " to kawai Ammi tace " yusuf yajuya yafita yana fita Ammi ma tafiche daga ɗakin

Misalin karfe 3 na rana

Aunty amarya che zaune a palonta ita da Aryan da kuma Aiman " rai aɓache Aunty amarya tasoma magana "me sakaninka da yarinyar nan da sauri suka ɗago kai kaba ɗayansu suna kallanta kara ɗaure fuska tayi tace wai ba tambayar ka nake ba Aryan " a sanyaye yache kai Aunty amarya meyasa kikemim irin wan nan tambayar ni meruwana da ita mekuma zanyi da ita kawai ta iya haɗa coffee sosai ne shiyasa nache tarinka haɗamin, " to banaso banasan tarinka kusantar'ka banso kanemi wata mai haɗa maka coffee ɗin amma ba yaran nan ba " shiru yayi bai sake tan kawaba saima wayarsa daya ɗauka yayi waje ...✍️✍️

Masu karatu amin afuwa sai munhaɗu gobe idan mai dukka ya kaimu

💖The Talent Troupe Writer's 💖

1 Duk Karfin Izzata
2 Gidan Aunty
3 Jini Ɗaya
4 Sarki Sameer
5 Kafita Zakka

Kar kubari abaku lbr love Story's

More comments an share pls 🙏
[7/3, 5:47 AM] Al~Quyraemey: *💫STAR LADY💫*

*DUK ƘARFIN IZZATA*

💖Story And Written💖
⬇️
*Star Lady*

Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

*Episode 11*


Mai martabane zaune a fada shida Aryan, Ahmad Khalid da'kuma Yusuf a nitse mai martaba yafara magana " Aryan meyasa zaka mari diyana kanajin faɗan danayiwa safras fa ranan akan marin dayayiwa hiyana shine kaikuma kasake marin diyana koh wai bakuda tausayine nikam eh " calmly Aryan yasoma magana kayi hakuri Abba wlh tabatamin raine sosai shiyasa " nasani Aryan nasan halin diyana itakuma haka allah yayita hakuri zakurinkayi da ita ban hanaku kumusu faɗaba amma kurinka ragewa kuma bai'kamata kuɗora hannunku a jikinsuba bakuganin yanayin'sune, yanzu kaje kadubi fuskar diyana da kyau kagani shattin yatsunkane kwanche akai to na'menene hakan gaskiya bansan hakan karna karaji kuma karna kara gani " inshaa allah Abba zan kiyaye chewar Aryan " Khalid yace Abba yabatun zakkan nanfa " eh kuna barwa ai kukula da komai " Ahmad yamike yana faɗin aa Abba su yaya Khalid dai nikamma bari naje na dubo Aiman " harara Yusuf ya watsawa Ahmad yana faɗin zakasani ne ai dakai da Aiman ɗin gaba daya wlh munkusayin maganinku a gidan nan " Ahmad dai bai sake maganaba yafiche abunsa

Aryan yace Abba yabatun komawarmu England ne " aikuda komawa kam to banacheba kabari ayi naɗin sarauta tukun nan sai inyi tunani akai chewar Abba " mikewa Aryan yayi yana faɗin to shike nan Abba allah ya kaimu san nan yafiche daga fadan " Khalid da Yusuf ma mikewa sukayi suka fito sunayiwa Abba sai anjima

Gabaɗaya family sun haɗu a palo dan chin abinchin dare amma banda don, dakuma yan matan Ammi subasu zoba , " mai marbata yace waishin ina yan'matana'ne mesukeyi basu fitoba, ko dai daga buɗa baki shike nan bazasuchi abinchin dareba" Ammi zatayi magana sai sukajiyo sallamar'su nanfa kallo yadawo kansu banda Aryan da fahad kowa na palon kallansu yake, "

diyana na sanye chikin dogon wando baki da rigansa zuwa guiwa pink colour still dai ba ɗan kwali a kanta ta zuba gashin nan har baya sai kwalli gashin yake nakinkirin dashi har tsakiyar bayanta, dan karamin bakin nan nata yasha janbaki pink ga blue eyes yasha kwalli ta gyara sagenta ga zarazaran gashim idanta, tasa high heel pink kalar rigarta

" hiyana ma dogon wando baki tasa sai riga sky blue zuwa guiwa ta ɗaure gashin Kanta, tayishi kamar donut ta yafa gyalen kayan akanta paki kalan wando dan bakin nan nata yasha ret janbaki tayi kyau sosai kamar kasacheta ga blue eyes yasha kwalli sai'yaƙara kyau sosai yana kyalli sajenta kwanche a gefen kumatun'ta gashin geranta kamar tayi caving tasa flat shoe sky blue kalar rigar

Zahra ma dogon wando baki tasa sai riga yellow tayafa gyalen kayan akanta shima bakine ɗan karamin bakin tan nan tasanya masa janbaki pink colour tayi kyau sosai itama daman zahra kama take da don sosai wan nan dalilinsaya suka zama kamar tagwaye da hiyana sai dai banbanchin kwayar ido dan zahra idanta bakine kamar nawa

Lamrat kuwa dogon riga baki tasa mai shegen kyau,
Tasa flat shoe fari, tayi rolling ɗin karamin farin gyale a kanta Zahra tamata make up sosai kamar wata balarabiya tazama

Amrat kuwa dogon wanto fari dasa sai yar farar t-shirt navy blue itama batasa ɗan kwaliba amma zahra tamata pakin na gashin a tsakiyar kanta tazuba jelar gashin a' baya har tsakiyar bayanta booth navy blue tasa a kafarta

Yusuf ne yache wow my baby zo " gaba ɗaya kallo yadawo kan Yusuf, a' sukane Aryan yaɗago yana kallan Yusuf ɗin shi ko ajikinsa kallan su diyana ma yake baisanma jama'a na kallansaba " bin inda Yusuf ɗin ke kallo Aryan yayi " "Aryan kasa kawar da kannasa yayi daga kallanta ?

Karisawa wajen table ɗin sukayi sukayi kowa tasamu waje ta zauna lamrat zata zauna kusa da Ammi " yusuf yache zo nan kizauna kusa dani my baby " bamusu lamrat takoma kusa dashi ta zauna " haidar da umar sai gulma suke kasa kasa " Ammi da Ummi kam ko ajikinsu abinchinsu kawai sukechi " Aunty amarya kuwa sai chika take tanata harararsu " ɗaukoh fura ki damamin hiyana chewar mai marbata " da sauri hiyana tamike tanufi kichin, kwarya ta ɗaukoh san nan ta daukoh fura, tanufi freig ta ɗauki ruba ɗaya na nono tajuya takoma palan mai martaba, da sallama tashigo palan ta dawo wajen zamanta ta zauna tafara dama furar

Sai'hira suke jefi jefi mai marbata yache banso a che muntafi umrah nan mun barkuba amma makaranta basu baku hutuba " Ammi ne tache sai suje hajji kawai kokuma subari sai wata shekarar " mai martaba zaiyi magana " Ummi tace Fahad tashi ka kaiwa yayanku abinchi " da sauri Fahad yamike yana faɗin ina abinchin " yana kichin Ummi tabashi amsa , " fichewa yayi daga palan

Bayan hiyana tagama dama furan tamikawa mai marbata " karɓa yayi yana murmushi kana yace duk gidan nan hiyanata tafi kowa iya dama fura " turo baki diyana tayi tana faɗin wlh nafita abun dama nina ko.... bata karisa maganaba sakamakon wani mugun kallan da Aryan yake wurga mata " shiru tayi

Mai martabane kuwa sai kallansu yake yana murmushi yana farinchikin burinsa yafara chika aishi haka yakeso kodama hararanne Aryan kewa diyana daɗi zaiji dan daga harara sai kallan mutunchi " Ammi che ta katse masa tunani dache ranka ya daɗe sai da safe " hararar wasa mai marbata ya wuga mata kana yace inada magana dake " to kawai Ammi tache " jin mai marbata yace. yana da magana da Ammi yasa kowa yatashi suka fiche

Mai martaba yadubi Ammi yafara magana jiya Yusuf yasame damaganar akan Khalid da zahra, Khalid yafaɗawa Yusuf yanasan Zahra tun tana karama ina faɗamiki hakanne bawai dan kifaɗa mataba sai hakkinki a matsayin uwa da'kuma kisamata ido karkibari tawa Khalid kishiya, danni tun da Yusuf yafaɗamin nariga nabawa Khalid auren ta, kokina da wani abun faɗe " ajiyar zuchiya Ammi tayi san nan tace, nikaina inakaunar Khalid nina renesa a hannuna yagirma babu halinsa da bansaniba bawani abun da zanche saidai inmusu fatan alkhairi kawai " to masha allah Amma fa kinsan yau a ɗakin'ki nake amma kikechemin sai da safe koh " murmushi Ammi tayi tana tace tubanake wlh nagajine a'zumin yau ɗin nan ya wahalar dani " haryanzu dai lallanchinki bai raguba Aisha, to muje chiki namiki tausar koh " mikewa Ammi tayi tana faɗin mujedai ninamaka " dariya mai martaba yayi san nan yamike yabi bayanta sukayi chikin betroom

Karfe 10 na dare

Rike take da cup ɗin coffee tanufi bangaren Aryan jikinta sanye da kayan barchi riga da dogon wando pink colour still dai kanta babu ɗan kwali tafiya take tana kunkuni" ni wlh barchi nakeji nagaji saikayitaba mutun wahala dan mugunta " da sallam tashigo palan baya palo kai tsaye ta wuche betroom ɗin " kwanche yake akan makekiyar gadansa yana latsawaya jin shigowarta yasa ya ɗago kai yana kallanta " sai turo baki take tana magana kasa kasa " from head to toe ya karemata kallo san nan ya ɗauke kansa da sauri " karisa shigowa chikin ɗakin tayi tazo gaban gadan ta duka san nan tace. Ina wuni yaya Aryan " shiru yayi bai amsaba kuma bai motsaba " itama shiru ta zauna har kusan 15 mnt, san nan tache yaya Aryan dan allah ka karɓi coffee ɗin mana wlh nagaji " banzah Aryan yayi da ita kamar baiji metake faɗe ba shiru shiru baiyi maganaba ganin bai daniyar magana yasata tamike, tanufi indayake wai dan taga yayi barchine
Aji cup ɗin coffee ɗin tayi akan dan karamin table ɗin dake tsakiyar ɗakin san nan tanufi kan gado hawa gadan tayi taga idansa a lunshe , ta turo baki tana faɗin shine dan mugunta kabarni ina duke kan guiwowina har kafata namin zafi kaikuma kayi barchinka koh, to banyafe... Bata karisa maganarba taga ya waro manya manya ash eyes ɗin nan nashi akan fuskarta " a'sukwane ta juya tana kokarin sauka gadan wani damka yayiwa gashin kanta wandayasa tadawo baya tafaɗa kan kirjinsa " kware baki tayi zatayi ihu yasa hannu yarufe mata baki " kasa kasa yace kina buɗemin baki ina harbinki da bindiga meya hauwar dake gadona yayi maganar tare da chire hannunsa daga bakinta " murya na rawa tace dan allah yaya aryan kayi hakuri kasakemin gashina wlh zafi yakemin " banche karna sake ganinki ba ɗankwali ba eh " kayi hakuri zanrinka sawa chewar diyana tayi maganar chikin muryar kuka " harchikin ransa yaji voice nata na karshe kayi hakuri zanrinka sawa a hankali yazame hannunsa daga kannata, yana faɗin to tashinmin ajiki " da sauri tamike tana faɗin to ga coffee ɗin " mikewa yayi shima kana yace bazanshaba ki mayar kije kisa ɗankwali saiki kawomin " a shagwabe tace ayya dan allah kayi hakuri kasha allah gobe zan daura dan kwalin kafin nakawoma wlh yanzu nagaji kuma barchi nakeji " kallanta yayi from head to toe san nan yache nikam, kekam kinada hankali kuwa kinsan chiwon kanki kuwa " turo baki diyana tayi tana faɗin mekuma nasakeyi " wlh azim idan kikasake fitowa a haka batare da hijabi ko kayan arziki ajikinkiba allah zakiyabawa aya zakinta " binjikinta tayi da kallo achikin zuchiyarta tana tunanin to me laifin kayan nan tayi nisa chikin tunani taji ya daka mata tsawa " wai badake nake magana bane nache kifitamin a ɗaki koh, da sauri tajuya tabar ɗakin binta yayi da kallo har tafita
san nan yamike yanufi inda ta ajiye coffee ɗin ya ɗauko cup ɗin yadawo gefen gadansa ya zauna yafara sha,

Bangaren diyana kuwa tana fita bangaren Aryan kai tsaye part nasu tanufa da sallama tashigo palan, da sauri taja burki tana faɗin ya yaya Yusuf kaima bakayi barchiba " murmushi yusuf yayi yana faɗin eh ina hira da baby's nawane suna koyamin fillanchi " karisawa indasuke diyana tayi tana faɗin kema amrat hardake yau bakiyi barchiba sai kije school kiyita barchi a class koh " lamrat tace ainikam ma yanzu zanje na kwanta " zama diyana tayi kusa da Yusuf zatayi magana " Yusuf yace kuje ku kwanta dare yayi kunsan akoi tashin asuba ga zuwa school yayi maganar yana mikewa yanufi hanyar fita " suma mikewa sukayi suka wuche ɗaki

Karfe 4 dai dai na asuba gaba ɗayansu sun haɗu a palon mai martaba danyin sahur amma banda don abinchi sukechi chikin kwanchiyar hankali " Ammi tache hiyana da Zahra kuchi abinchin nan dawuri ku'ɗauki na yayanku ku kaimasa zahra najin Ammi tache sukaiwa don abinchi tafasa kara sai da kowa na palan yaɗago yana kallanta " lfy auta ta chewar Abba " Zahra dai taki magana sai kukanta kawai take " hiyana kam datariga da tasan me Zahra takewa kuka ko kallanta batayiba, su Ammi sunyi tambayar duniyar nan amma Zahra taki magana sai kuka take " Aryan ne ya daka mata tsawa zakimana shirune kosaina babballaki a nan " tsit tayi kamar ruwa yachita "
Aunty amarya ne tamike tana faɗin kai umar kaje ka dauki abinchin yayan naku ka kaimasa kuma daga yau kai zaka rinƙa kai masa abinchi tana kaiwa nan tafiche tana tunanin aranta ai bazan taɓa barin yaran nan surinƙa kusantar samarin gidan nanba daga yau har ranar da gagarabadau zai musu aiki ido zan samusu sosai da sosai ɗakinta tawuche ta haye gado babu ko sallah takama barchi

Bangaren"su hiyana kuwa sunajin Aunty amarya tace umar yakai abinchin yayansu nantake suka fara murna sukamike a tare suna faɗin barimuje muyi sallah " Ammi ta kalli hiyana chikin harchen fillanchi tace wani sallah kuma badai kina period ɗin kike sallah ba " shiru hiyana tayi dan ita batama san idan a na period baa sallah ba " ganin tayi shiru yasa Ammi ta dubi zahra tace kije ki koyamata abun daya dace tayi " to kawai zahra ta amsa dashi san nan suka fiche

Mikewa Yusuf yayi yana faɗin gaskiya lokachi yayi dazan koyi fullanchi nima haba yanagama faɗin haka yayi waje " Khalid ma yace tab aiko nima dole naje Zahra ta koyamin irin wan nan wariya daake nunamana kana yamike shima yayi waje " dogon tsaki aiman yaja san nan yamike yafiche " shidai Aryan zaune yake ahiru yana latsawaya har saida yafarajin kiraye kirayen sallah yamike yanufi bangarensa " Ammi da Ummi ma suka fiche sukayi nasu bangaren danyin sallah " palan yarage fahad haidar da Abba " Abba yace wai kunyi arwala'ne kunfasan su safras sunafitowa zamuwuche masallahchi " mikewa haidar yayi yana faɗin aa baridai naje nayi " fahad ko chewa yayi nikam nayi Abba" ok kawai mai martaba ya amsa dashi
Shiru suka zauna har sauran matasan suka fito sukajera zuwa masallachi

Aɓan garen inna kuwa da sallama tashiga gidan su buba zaune tasameshi a tsakar gida " buba na ganin inna yafara murmushi yana faɗin inna jamɓandu( inna ina wuni) " lfy buba ya kafar taka " da sauki inna" inna tache to allah yakara lfy ina innarka take " tana garke tanabawa shanu ruwa da abinchi buba yabata amsa " to barina dubota bata jira amsar buba tayi gaba abunta " a garken shanun ta iskoh innar buba da sauri inna ta karisa wajenta tana faɗin albishir rinki yar uwa rabinjiki " ɗago kai innar buba tayi tafara murmushi tana faɗin goro " to kifito muje yau kuɗin sunchika dubu goma dai dai chewar inna " da sauri innar buba ta ajiye sandar hannunta datake juyawa shanu ruwan gishiri tafito daga garken tana murmushi jerawa sukayi suka koma chikin gida innar buba ta ɗaukoh mayafi suka fiche

Wani ƙungurmin daji suka shiga tafiya suke har suka isawajen wani dutse ga hayaki nafitowa daga chikin kogon dutsen chikin kogon sukashiga " wani kasurgumin bakin bokane awajen ga idon san nan jajawur duk yabi ya huhhuda hanchi yasa wasu karafuna gawani katan karfe mai raun dayasa a kunnensa bashida kyan gani ko kaɗan
Zama su inna sukayi kusa dashi " zasu fara magana ke nan yayi wani mahaukachin dariya ha, ha, ha, da murya masa daɗin Ji yace aikin ku bazaiyuwu a chikin azumiba saboda duk an ɗaure mana mutanenmu amma kuje sai bayan sallah kudawo ha ha ha yana gama faɗan haka ya ɓache ɓat " da sauri su inna suka mike suka fito inna tace to yanzu barinaje na ajiye kuɗin sai bayan sallah mudawo da haka suka kuche gida.

Kamar kullum yauma zaune suke a wajen chin abinchinsu na makaranta karatu boko hiyana take yaukam tun da bata da tsarki " zahra da diyana da faria kuwa hirar wani film suke waishi love story English movie
Lamrat da amrat suna rubutu a takardunsu "
Kamar daga sama sukajiyo muryan jabir yana faɗin ke hiyana zo mutafi " ɗogo kai hiyana tayi a nitse tafara magana kayi hakuri jabir wlh yau banida lfy ne chikina namin chiwo " to yakikesan nayi ke nan ga abokaina chan kowa budurwarsa tazo ni bandani ke nan ba zaiyiwuba i don't care koma meke damunki, nidai kitashi mutafi " kamar hiyana zatayi kuka haka tamike tanufeshi tana faɗin muje " kallan uku 10 diyana tawa jabir kasa kasa tache mugu wlh sainayi maganinka " kallanta zahra tayi san nan taja guntun tsaki " jabir tunda yakira hiyana suka tafi basu dawoba har saida a katashi nanma saida diyana da zahra sukaje wajen dayake zama da abokan nasa sukache hiyana tazo sutafi mai ɗaukansu yazo " jabir dayaji haka sai yache to taje zasu haɗu gobe " jerawa sukayi suka nufi wajen da suke tsayuwa sujira motochin dake ɗaukansu "

suna tsaye awajen sukaji magana daga bayansu " gaba ɗayansu suka juya " hiyana tace uncle Omar ina wuni " da faraa a fuskanshi ya amsa san nan su Zahra suka gaidashi zaisake magana saiyaga motochin ɗaukansu yazo nanfa yamusu sallama yawuche " sukuma suka shiga mota kamar yadda sukasaba hiyana Zahra diyana motarau ɗaya " amrat da lamrat suma motarau ɗaya " da gudun gaske motochin sukabar bakarantar" gudu suke sosai suna kan hanyane" zahra tace kinsanme hiyana " girgiza'kai hiyana tai alamar aa " uncle Omar fa wai san diyana yake chewar zahra " kan uban chan niyakeso lallai kuwa yana ruwa wlh dannikam inba sojaba bazanyi aureba " baki buɗe hiyana ke kallan diyana " Zahra kuwa chewa tayi meyasa kikesan soja sojojifa mugayene " eh ae a chikin sojanma mugun nakeso wanda zaiyimin maganin yaya Aryan kuma wanda yake da bindiga shima " zahra tace to me yaya Aryan ɗin yayimaki haka dakike neman mugun soja yayi maki maganinsa " to bashine kullun inna masa laifi saiyache zai ɗaukoh bindiga ya harbeni namutu kowa yahutaba " aikuwa hiyana bata san sanda takwashe da dariyaba tana faɗin kai amma kuwa da yaya Aryan ya kyauta wlh " Zahra kuwa chewa tayi dalla rabu da hiyana kinji faɗamin muguntar me yake miki " bayan harbeni dayake chewa zaiyi saikuma jamin gashi da takuramin nasa ɗakwali dakuma kawo coffee kullun tayi maganar dai dai lokachin da motochinsu ke parking a parking space na chikin gida
Fitowa sukayi suka nufi chikin gida rike da hannun juna

Misalin karfe 4 na yamma gaba ɗaya yanmatan zaune suke a palon Ammi suna kallo hiyana kuma tana karawa lamrat karatun qur'ani gaba ɗayansu shiga iri ɗaya sukayi duguwar riga abaya dukkansu colour ɗaya baki " Ammi ma nazaune a gefe tana gyarawa amrat jigidarta da Aunty farida ta saya musu to ya matseta sosai " da sallama Khalid da yusuf suka shigo palan " da gudu Zahra ta mike ta nufi Khalid,faɗawa kan kirjinsa tayi ta rungumesa sosai tana faɗin oyoyo yaya Khalid " Yusuf ne yace my baby kema kizo kimin oyoyo mana

Please Login or Register in order to submit comment