Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ki kwanta ko da safe da kaina zan kai ki wajen yaya Aryan kuma ki daina tunanin ko bai da lfy, lafiyan sa kalau sharrin sheɗan ne yasa kike ganin kamar bai da lfy, kije kiyi addu'a ki kwanta kinji, to kawai diyana tace san nan ta nufi ɗakin ta,

Hannun Aunty farida dady'n junior ya kama suka nufi stair ɗin suka koma ɗaki,
"My farida wai meke faruwane?, ko dai Aryan shine mijin da Abba yayi wa diyana
"Dady'n junior wlh nima abun yafara ɗauremin kai, nan dai Aunty farida ta shiga bashi lbr duk wani abun da ta sani dan gane da yaya Aryan da diyana, ta karisa maganar dai dai lokachin da suƙe hawa kan gadon su,

"Kinsan me my farida, batare daya jira amsar taba ya chigaba da chewe "Abba yana da gaskiya domin kinga dukkan kannen namu basu taɓa soyayya ba hasalima basu ɗauki mace da daraja ba, ganin ta suke kamar abun banza, wlh a irin wan nan yanayin da suke chiki idan aka ɗauki mace aka basu to ta shiga uku domin basusan darajar taba zasu wahalar da ita sosai, yanzu dai ki dubi yadda Aryan ke masifar son yarinyar nan batare da yasan Son nata yake ba amma duk dahaka daga ɗan magana dasu Umar sukayi, ya fusata har yaje ya samu Ammi ido da ido yace bayason ganin diyana kinga a nan ma rashin sanin darajar mace ya bayyana karara, a tare dashi, wlh gwara da Abba ya masa hakan, kuma ku barshi sai ya gasu sosai sai yasan mace fa halittace mai daraja wadda kowani ɗa namiji ke son kasan chewa da ita, ku kyalesa sai ya furata da bakin sa chewar yana Son ta, in ba hakaba ko an musu aure ran da su Umar suka sake mai maita abun da sukayi shima sake mai maita abun da yayi zai yi. da katawa yayi da maganar yana mai da numfashi,

"Kana da gaskiya dady'n junior wlh rashin sanin darajar macece har yasa Aryan ya iya tinkarar Ammi ya faɗa mata hakan, to amma abun tausayin a nan shine ita diyana yanzu dai da kunnen ka kaji halin da take chiki, tana son Aryan sosai Amma itama batasan chewa Son nashi takeba, saboda kaga ita yarinya che kuma gashi ba wani ilimin ke gareta ba ita ko kallon film batayi sai dai buga game kawai, ta iya

"Hakane my farida dolene diyana ta zama abun tausayi amma ke zaki jata a jiki domin ki rinƙa rage mata, kewar nashi kada ki bari ta rinƙa zama ita kaɗan, gobe idan Allah ya kaimu zan saya mata sabuwar waya mai kyau sai kisa Sim naki a chiki, ki mata download game's dayawa, idan kin gama ki chire Sim ɗin, san nan kema kiyi taka tsantsan da wayar ki dan kinsan gaba ɗaya kannen ki basa iya yin wuni ɗaya batare da sun kira ki ba, kada ki kuskura ki sakawa diyana Sim card a wayar ta, domin a yadda kika bani lbr na fahimci yariyar akoi kwakwalwa sosai, dan haka sai kinyi taka tsantsan da ita sosai

"To shike nan dady'n junior zanyi duk yadda kace Saboda nima ina kaunar diyana sosai kamar yadda nake kaunar Aryan, bazan so taje gidan mijin da bai san darajar ta ba, zanyi iya bakin kokarina wajen ganin, na bata kulawa na chanza mata abubuwa da dama

"Good my farida hakan yayi to yanzu dai mu kwanta muyi barchi kinga dare yayi ma karisa maganar gobe idan Allah ya kaimu,

atare suka kwanta ta shige chikin kirjin sa ta lafe shi kuma yana shafa bayan ta har barchi ya ɗauke su.

Kano

Tun misalin karfe 6 su hiyana suka gama shirin zuwa school, yaya Khalid kawai suke jira yazo ya ɗauke su.

sai misalin karfe 7:30 yaya Khalid yazo ya tasa su a gaba suka fito harabar gidan suka nufi parking space, yau da kanshi ya tuƙa su a family car,

Gudu yake shararawa da motar sosai akan shin fiɗaɗɗiyar hanyar school nasun, chikin kan kanin lokaci suka isa makarantar,kai tsaye parking space na ya nufa yana kashe motar, ya fito a gurguje ya yana faɗin "kufito ku tafi class dan kun kusa makara, yana gama faɗin hakan ya nufi office na HM na makarantar, domin naje ya biya musu kuɗin makaranra.

Abangaren su hiyana kuwa yaya Khalid na tafiya suma ko wace ta kama hanyar class nasu, amma kallo ɗaya zaka yiwa hiyana kasan tana cikin matsanan chiyar damuwa ga blue eyes natan nan duk sun kunbura da alama tasha kuka, dan dai ita ba mai yawan kallon mutane bane kullun kanta na kasa shiyasa mutun ba zai gane kunburin da idon nata sukayiba, tazo dai dai zata shiga class nasu, taji daga bayan ta an che "ke zonan chikin tsiwa, da sauri ta juyo, ganin....✍️✍️

More comments an share
[6/15, 8:07 PM] Princess Teema Yola: *💫STAR LADY💫*30

💖The Talent Troupe Writer's 💖


*DUK ƘARFIN IZZATA*

💖Story And Written💖
⬇️
*Star lady*


Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai



*Episode 3️⃣0️⃣*


Gudu take kamar zata tashi sama har tsallake stari uku take ta tana na huɗu batare da ta sani ba, a dai dai tsakiyar palon kasa tayi karo da Aryan baya baya tayi zata faɗi, yayi sauri rikota yana faɗin "ai daman na san za'ayi hakan shiyasa na biyo bayan ki me ke faruwa? Bai gama rufe baki ha yaga Bgs na saukowa a guje sai wani huchi yake, a sukwane ya saki diyana yace "ki kudu sister kar ki tsaya ko ina sai bayan Abba, ai diyana bata jira taji me Aryan zai cheba dan yana sakin ta ta kwasa a ɗari tayi waje.

Azuchiye Bgs ya sauko ya nufi hanyar fita da sauri Aryan yasha gaban sa yana faɗin haba bro lfy? Hannu yasa ya hankaɗe Aryan gefe ya nufi kofar fita, A zafafe Aryan ya saƙe tare masa gaba, chikin tsawa Bgs yace "Aryan ka bani hanya tun ban illataka ba "haba Bgs pls kayi hakuri mu koma chiki, wani naushi Bgs ya kai wa, Aryan a fiska, da sauri Aryan ya tare yana faɗin "aa bro ba dai yanzu ba gaskiya, a zuchiye Bgs yasa ɗayan hannu sa ya damki wuyar Aryan ya ɗa gashi sama yayi wurgi dashi gefe guda, ya juya ya nufi hanyar fita da gudu Haidar da Umar daƙe tsaye a bakin kofar palon wadda kusan tare daman suka shigo da Aryan, suka juya suka bar part ɗin gaba ɗaya.
Tattaro dukka sauran karfin sa Aryan yayi ya miƙe ya saƙe tarewa Bgs gaba, "Aryan zan illata wlh idan baka barni na bugi yarinyar nan ba "haka na keso daman kafara illatani kafin ka illata ta, dun kule hannu Bgs yayi ya sake kai wa Aryan bugu a firji wadda sai da yasa Aryan tan gal tan gal kamar zai faɗi, amma abun ku da soja, chikin zafin nama ya kame jikinsa chikin bachin rai ya kaiwa Bgs duka a wuya da karfi, a fusache Bgs ya ɗaga sama yayi wurgi dashi a tsakiyar palon chikin zafin nama ya nufi hanyar fita..

...har ya kai bakin kofar palon zai fita sai kuma ya ja birki da sauri ya juyo, gani ko motsi Aryan ba yayine yasa Bgs kariso wa wajen daya ke kwanche da sauri,
Duƙawa yayi yasa hannun sa a dai dai sai tin kofar hanchin Aryan yana faɗin "my blood kar kamin hakan, hannu Aryan yasa ya chapko hannun Bgs tare da waro ash eyes nashi kan face ɗin Bgs ɗin, dogon tsaki Bgs yana kafin yace "me hakan ɗin? " To ai bani da wani zaɓi na da katar da kai ne sai hakan ɗin, miƙewa Bgs yayi san man ya ɗuƙa ya ɗauki Aryan chak ya saɓasa a kafaɗar sa yanufi stair ɗin dashi
"Amma Aryan baka kyau ta min ba "me kuma na maka? " Da ka hanani bugun yarinyar nan mana "au to kai daman so kake na barka kayita bugun yaya mutane, kuma kasan idan kache zaka bugi yarinyar nan a yadda kake chikin fushin nan, tofa zaka iya kasheta "to ta mutu mana menene amfanin ta daman? ai inaga wlh watara na idan ban kashe enamiece nawa ba kai zaka mutu a shiga faɗar da ba ruwan ka, tsaki Aryan yaza dai dai lokachin Bgs ke kwatar dashi kan katafaren gadon sa

"Wlh Bgs baka da kirki ko kaɗan yanzu gashi ga bugi yar sarki Zaria tana asibiti, jiya naje hospital ɗin dan naga ya jikin nata saboda baban ta ya ɗau zafi dayawa, kar yaga ko ɗaya daga chikin mu bai jeba ya duba taba, Allah ya rinyar nan ko motsi batayi kamar ba rai a jikinta amma a hakan kuma yau kake so na barka kasake bugun wata ko?

"au wai dan babanta har wani zafi ya ɗauka ke nan to ya baku sanar dani ba dan shima na hukuntashi, waro ido waje Aryan yayi kafin yace "zaka iya zuwa ai yanzu ma sai ka hukun tashi, ni dalla ka bani ruwa nasha hai, Aryan ya karisa maganar chikin ɓachin rai

"Wlh Aryan ba dan ina kaunar ka ba Allah da yau inaga sai dai a kwashi gawarka ya kai karshen maganar tare da miƙewa ya nufi freij, " zaka iya ajiye kaunar a gefe ai sai ka kashe nin Aryan ya faɗa chikin fushi, Bgs ba tare daya sake chewa komai ba ya ɗauko ruwa kawai ya dawo kan gado ya ɓalle bakin robar ya ɗago kan Aryan ya kafa masa robar a baki, sosai Aryan ya sha ruwan har sai da ya kusa shanyewa, sannan Bgs ya chire roban daga bakin shi yana faɗin "ya isa haka shan ruwan, Aryan yace "to ba kai ka min wani wawan naushi a kirji ba ai dole nasha ruwa "kaɗan ma kagani ai wlh ka chigaba da shiga faɗan da ba ruwan ka watarana sai dai a kwasheka zuwa hospital.

murmushi kaɗan Aryan yayi san nan ya yunkura ya miƙe zaune, a hankali y zuro kafarsa kasa ya miƙe tsaye "ina zakaje bro? Bgs ya tambaya yana kallon face ɗin sa, "fada zanje wajen Abba mana, "why ba zaka tsaya a nan ba "no akoi maganar da zamuyi ne mai mahimmanci "ok let's go together, ya kai karshen maganar tare da miƙewa, atare suka fito

Dai dai wajen part na Ammi sukachi karo da su Zahra sun fito daga palon Abba.
Ganin Bgs da yaya Aryan yasa diyana ta fasa ihu ta watsa a guje ta shige ɓangaren Ammi, da gudu hiyana tabi bayan ta, su Zahra ma ba'a barsu abaya ba da gudu suka wache suka bi bayan su hiyana.

"Bgs gaskiya baka kyauta wa yanzu dan Allah dubi yadda yaran nan suke ihu da suka ganka kamar sunga dodo, wani dogon tsaki Bgs yaja kafin yace "bana son haka Aryan ka daina kawomin maganan yaran nan, "ai gaskiya na faɗa maka bro menene anfanin kasa su suna jin tsoronka, shiru Bgs yayi bai sake magana ba har suka karisa chikin fada

Misalin karfe 11 :20 Aryan ya fito daga fada ya nufi part nashi dan ya je yayi wanka yazo dai dai part na Ummi sai yaji haidar da Umar suna hira tsayuwa yayi da kyau ya kasa kunne yana jin su,

"Umar ai wlh ko baka faɗaba kowa yasan Son yarinyar nan yaya Aryan yake, bakaga yadda yake kallonta ba idan mun haɗu wajen chin abinchi,

"kai haidar kai kallo kawai ka gani ka dubafa yau saboda ita yaya Aryan yayi faɗa da yaya prince, ai mugu mugun Son ta yake, wani dariya Umar yayi kafin yace "tab aiko zamuga ya, yaya prince zai yi idan yaji lbr yaya Aryan ya faɗa soyayya dariya suka kwashe a tare har da riƙe chiki,

A fusache Aryan ya juya ya fasa shiga part nashi ya nufi part ɗin Ammi sai wani huchi yake, chikin ransa yana faɗin soyayya ni wai aa never wlh har abada.

da sallama yashiga palon bb kowa kai tsaye betroom ɗi ta ya nufa, a bakin kofa ya tsaya yayi sallama, Ammi na daga chiki ta amsa masa tare da bashi izinin shigowa, shiga yayi ya zauna saman manya manya throw pillow dake tsakiyar ɗakin
"Aryan lfy kuwa naga ranka a ɓache haka, "Ammi so nake yarinyar nan ta bar gidan nan "wace yarinyar kuma? "Wan nan yarinya dake kawomin coffee "au diyana? "eh ita ban son sake ganin ta gaskiya, yana kaiwa nan ya miƙe ya fita rai a ɓace, miƙewa Ammi tayi itama ta ɗauki alkyabban ta ta sanya ta fito ta nufi fada

Da sallama ta shiga ta karisa wajen Abba ta zauna saman kujera tana masa sannu da hutawa "Aisha lfy naga kamar ranki a ɓache? Abba ya tambaya yana kallon face nata, Ammi bata ɓata lokachi ba wajen sanar da Abba abun da Aryan ya faɗi

a tunanin ta Abba zai ɓata rai sai kuma taga yana murmushi ya ɗauko wayar sa dake gefensa yafara kiran layin Aunty farida,
Bugu ɗaya Aunty farida ta ɗaga tare da faɗi "hello Abba na "my daughter ki zo fada yanzun nan ki sameni, yana gama faɗin hakan ya katse kiran,

baifi minti 5 sai ga Aunty farida ta shigo da Sallama har kasa ta duƙa chikin girmamawa ta gaida Abba da Ammi, da fara'a dukkansu suka amsa, "zauna my daughter muyi magana chewar Abba
Miƙewa Aunty farida tayi ta kowa saman kujera ta zauna ta zubawa Abba ido tana sauraron taji mai zai che "so nake yanzu ba sai anjima ba ki ɗauki diyana ku koma Maiduguri da ita, kuma karki kuskura ki sanar da wani tana wajen ki koda Aryan ne ko zai miki tambaya dubu idan ki ka kuskura ki ka sanar da shi to ban yafeba. Sai da Abba ya daka ta da magana sannan Ammi ta fara magana

Ranka yadaɗe me yasa zaka che hakan? "Aa Aisha ku kyaleni tun da har Aryan bai ji kunyar idon ki ba yazo yace baya son ganin yar ɗan uwanki to wlh sai nayi maganin sa, "tayaya zakayi maganain sa to? Ai naga shi yace bai son ganin ta to kaga idan ta tafi ai sai yafi kowa murna da hakan "Aisha ke nan yanzu kina nufin bakisan chewa Aryan na Son diyana ba, to idan ma baki sani ba yau kin sani, kuma So bana wasa yake mata ba "amma yana Son ta kuma yace baya son ganin ta a gidan nan?

"Kedai ba ruwanki kuyi abun da nache muku wlh duk wadda tasake ta faɗi inda diyana take to sai na ɓata muku, kutashi kuje, my daughter yanzun nan ku tafi kuma karki bari kowa yaga kin fita da diyana, "to kawai Aunty farida tace sannan ta miƙe tanan murna sosai dan ambata diyana atare suka fito fada da Ammi

Yola

Ihu take tana faɗin nashiga uku na ku kawo min agaji zan mutu, da gudu yaya bello ya fito daga chikin gonar sa ya nufi gonar bappan su dan daga nan yake jiyo ihun,

"Subhanallah innar buba lfy? Chikin ihu da kuka innar bubu tace "Bello mutuwa zanyi na shiga uku kumurchin machijine ya sareni a kafa, chikin sauri bello ya kai kallonsa kan kafar nata, gaba ɗaya kafar ta kunbura sundum, girgiza kai Bello yayi yana faɗin "shike nan dafin yagama shiga jikin ki wlh ko kinsha magani yanzu ba lallai ki chigaba da takawa da kafar ki ba, dan dafin ta riga ta illata namar kafar taki

"Bello ka taimake ni mutuwa zanyi wayyo Allah, da gudu yaya bello ya juya ya koma chikin gonarsa ya tsinko wasu ganye ya nufi rafi ya wanke su tas, san nan ya ɗauko wani ɗan kwarya, ya dawo wajen innar buba, murje ganyen bello ya shigayi chikin kwaryar sai da ta fitar da ruwa san san nan ya bawa innar buba, ruwan akan tasha ganyen kuma ya manna mata awajen chizon machijin.

Tana shan maganin ta fara amai, amai sosai ta amayar da dafin machijin, amma kafar ta kuma har yanzu a kunbure yake gashi yayi wani green dashi, ɗaukan kwaryar yaya Bello yayi ya koma rafin ya ɗebo mata ruwa ya dawo ya bata tasha, san nan ya ɗauke ta chak ya saɓata a kafaɗar sa ya nufi hanyar gida

Da sallama ya shiga gidan hasana na tuƙa tuwo ganin yaya Bello ɗauke da innar buba a kafaɗar sane yasa hasana miƙewa da sauri ta ɗauko ta barma mai kyau daga ɗakin ta ta shin fiɗa a tsakar gidan.

A hankali yaya Bello ya kwantar da innar buba a kan ta burman, san nan ya dubi hasana yace "kiyi sauri ki kammala abinchin ki zuba mata, to kawai hasa tace Sannan ta miƙe ta koma wajen girkin nata, innar buba kuwa sai hawaye take saboda azabar da kafarta ke mata,


Masu karatu na muku wan nan ɗan takaitaccen page ɗin ne saboda nasan kuna chikin zullumin ya diyana da Bgs zasu kare, shayasa na muku amma gobe ba update sai Monday shiyasa ma ban tsaya awajen da zaku shiga tunani ba 😸😻


💖NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER'💖

*LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
👇👇👇👇

*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
by(Star Lady)

*2,GIDAN AUNTY*
by(mss lee)

*3,SARKI SAMEER*
by(xeemat....love)

*4, JINI DAYA*
by(mrs bbk)





More comments an like pls
[6/15, 8:07 PM] Princess Teema Yola: *💫STAR LADY💫*32

💖The Talent Troupe Writer's 💖


*DUK ƘARFIN IZZATA*

💖Story And Written💖
⬇️
*Star lady*


Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai



*Episode 3️⃣2️⃣*

Da sauri ta juyo ganin jabir ne yasa ta ƙara ɗaure fuska sosai, ta sunkuyar da kanta kasa, "my hiyana me ya same ki kikayi kuka? Chewar jabir Ya yi maganar yana matsowa kusa da ita, ɗan ja da baya kaɗan tayi kasa kasa tace "ina kwana, batare da ya amsa gaisuwar nata ba ya sake mai mai ta mata tambayar daya mata da farko "me yasa meki ki kayi kuka? waya taɓamin ke?

Chikin sanyin murya tace "ni ba wanda ya taɓani kawai nayi kuka ne saboda an mai da kanwata garinmu,
"Eyya to sorry kinji kije class idan an tashi break kizo muyi hira dan ina missing naki sosai, ko dai ke baki missing na ne? Ya karisa maganar yana ɗan dukar da kai yana leka fuskan ta dayake ta sunkuyar da kan kasa, shiru tayi bata sake che masa komai ba, ganin bata da niyar magana ne yasa yace "to kije class ɗin idan antashi sai kizo na kawo miki tsaraba
Bata jira ya karisa maganar shiba ta shige class nasu da sauri, binta yayi da kallo har ta shige sannan ya juya ya nufi nasu class ɗin

Sosai Bgs yake sauri kamar zai tashi sama taku yake irin na sadaukin yaki, yazo dai dai zai shiga ɓangaren Aryan, yajiyo muryan Abba daga bayan sa yana faɗin "jirani mushiga tare, batare da ya juyoba ya tsaya har Abba ya kariso, wajen a tare suka jera zuwa chikin part ɗin,

"Menene ya hana Aryan zuwa sallar asuba Abba ya tambaya yayi maganar dai dai lokachin da zasu haura stair case ɗin chikin palon Aryan,

"Abba wlh nima ban saniba abun da nazo tambayar sa kenan, shiru Abba yayi bai sake chewa komai ba, har suka karisa betroom ɗin, da sallama suka shiga a tare

Kwanche yake saman katafaren gadon sa,yana sharara barchin, da mamaki Abba ya juyo ya kalli Bgs wadda shima Abba yake kallo..

....Karisawa bakin gadon sukayi a tare zama Abba yayi a gefen gadon shi kuma Bgs ya haye saman gadon ya ɗan jayye bargon da Aryan ya lulluɓu, zuba masa ido Bgs yayi sosai kamar mai karantar wani abu a kan face nashi

"Abba da alama ɗan uwana bai yi barchi jiya da daddare ba koda kuma yayi to kaɗan ne, ka duba time fa yanzu Almost 8:5am amma yana barchi ko sallar asuba bai yiba, anya Aryan yana da lfy kuwa? Dogon numfashi Abba yaja kafin yace "kila akoi abun da ya tsare sa ya hana shi barchi da wurine.

Guntun tsaki Bgs yaja sannan yasa hannu yana ɗan bubbuga hannun Aryan,
"Aa Safras ka barshi mana yayi barchin sa chewar Abba "aa Abba ya tashi dai kofa sallar asuba bai yiba ya tashi idan yayi Sallah sai ya koma barchin, shiru Abba yayi bai sake Magana ba, bubbuga Aryan Bgs yake yana kiran sunan sa "my blood, my blood

Da kyar Aryan ya iya waro ash eyes nashi nan, sun chanza sunyi jaa saboda barchi chikin muryan barchi yace "Bgs lfy? Ɗaure fuska Bgs yayi kafin yace "zaka tashi kaje kayi sallar asuba ne ko dai sai na maka 1bloo 7 die,

Wani sallar asuban kuma? I Already nayi sallar ton asuba ɗin, yayi maganar yana kokarin miƙewa zaune, da kyar ya iya miƙewa zaune, da sauri yasa hannu ya dafe kansa dan ji yake kamar kan nashi zata faɗi kasa ga wani azaban chiwo da take masa, sai sara masa kan keyi kamar zai fashe,

Ganin Aryan ya dafe kai ne yasa Bgs saurin kai hannunsa saman goshin Aryan ɗin yana faɗin "my blood lfy? Menne? Kai ɗinne ke maka chiwo? Karisa hayewa gadon Abba ma yayi ya sa hannun'sa ya riko kan Aryan yana faɗin

"Aryan meke damun kane? ɗago jajayen idon sa yayi yana binsu da kallo ganin yadda suka ruɗene yasa ya ɗan kakalo murmushi gefen fuska, da kyar ya iya motsa lallausan red lips nashi ya furta "bb komai, a tare Bgs da Abba suka chire hannun su daga saman goshin nasa,

Aryan me yasa baka je masallaci da asuba ba? Chewar Abba yayi maganar yana sauƙa daga gadon, "Abba makara nayi wlh, lokachin da natashi already an gama Sallah "me yasamu wayar ka? na kiraka da asuba ai a kashe, Bgs ya tambaya yana kallon face nashi,
"Eh Ni na kashe wayar jiya da daddare, to akan idan nazo barchi zan kunna sai na manta

Shiru Bgs ya ɗan yi kafin ya chiro wayar sa daga aljihu wandon sa, ya kunna hasken screen ɗin ya chire password ya shiga contact nashi, layin Fahad ya fara kira ringing ɗaya Fahad ya ɗaga

"Hello big bro, ina kwana, "lfy Fahad, baki buɗe Abba da yaya Aryan ke kallon Bgs tunani Abba yake wai daman Bgs ya iya amsa gaisuwa tab lallai Fahad yarone mai Sa'a ya chire tuta a gidan nan, kaiii

Yaya Aryan ma tunani yake anya na taɓajin Bgs yana amsa gaisuwar wani ko wata kuwa? Yayi iya tunanin sa duk bai tunano in da Bgs ya taɓa ansa gaisuwa ba kwata kwata, ko awajen Aiki yaran mu zasu gaishe sa sai dai ya ɗaga musu

Please Login or Register in order to submit comment