Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gadon tana tunani

Yau yakama Monday tun karfe 6 nasafe Khalid yazo bangaren Ammi, dan ya ɗauki su hiyana suje a musu registration a school ɗin su zahra, zama yayi a palan Ammi yana jiransu " da'sallama sukashigo palan hiyana na sanye chikin riga da sket na kanti mai kyau ash colour rigar mai dogon hannu yaɗan kamata sai sket din daga sama ya ɗan kamata kasan kuma yabude sosai kayansu iri ɗaya da diyana, sai dai na diyana light green ne, sunsaka hijab da bazata wuchi guiwaba ,amrat da lamrat kuwa riga da wando sukasa rigar zuwa goiwa wandan koma dogo har kasa sky blue sun yafa karamin gyale "
"Zahra kuma nasanye chikin uniform nasu, riga da wando da dan karamin hijab rigar fara tas zuwa goiwa sai dogon wando navy da ɗan karamin hijabin da baiwuche kirjiba "
"Wow chewar Khalid gaskiyane my sister's kunyi kyau sosai abunku to kuzo mutafi"
"Ina kwana yaya inji hiyana" lfy lau yabata amsa"
Ganin hiyana ta gaidashi yasa suma su diyana suka gaidashi ya amsa fuska a sake, san nan yache kuzo muje karmuyi latti kunga har 7:4 tayi " gaba yayi sukabi bayansa" suna fitowa harabar gidan suka samu yusuf tsaye jikin mota, yana sanye da white jeans da ash T-shirt bakaramin kyau yayiba sai kanshi ke tashi daga jikinsa kamar anyi barin turare ha gashin kan nan yasa har kam kafaɗarsa ya sha gyara sai kyalli yake daman gashin bakine sosai "
Gaidashi suka farayi " yana amsawa fuska a sake " inazakaje yusuf Khalid yajefo masa tambaya " rakaku zanyimana " dariya Khalid yayi sosai kafin yache to yau kuma wasa kakejiyimin kenan " daure fuska yusuf yayi yana faɗin wasa kuma to daman muna wasane, inzakazo mutafi kazo muta inkuma bazuwa zakaiba ni sai na daukesu muje namusu registration din " da mamaki khalid ke kallansa kamar bazai tankasaba saikuma yache to muje " mota 3 sukayi zahra hiyana diyana mota ɗaya suka shiga" Khalid lamrat amrat suka shiga mota ɗaya yusuf kuwa nashi motar yashiga " sai wasu motochi 3 kuma dake binsu a'baya dauke da sojojin yusuf guda 9 kowani mota sojoji uku " dagudu gaske motochi suka miki hanya harzuwa bakin gate nan take security suka gangalemusu katafaren gate ɗin suka dauki hanya gudu sosai suke shararawa chikin kankanin lokachi suka isa school ɗin " sunayin parking sukafito kai tsaye office din principal suka nufa, nan danan batare da ɓata lokachiba suka gama komai kuma suka roki alfarman da akai diyana da hiyana primary 6 tun da sunyi girma amrat da lamrat kuma a kaisu primary 4 da kyar principal ya aminche nanfa suka mika masa amanar'su diyana san nan Khalid da yusuf suka fito sukabar su hiyana sukaje suka shiga moto chinsu suka juyo sai gida"

"Kwanche tashi babu wuya awajen allah yau su diyana sunchika 1 month da dawowa kano sunchanza sosai kamar basuba sunyi kyau ga kiba dasukayi sunyi fresh dasu kamar yayan larabawa sunfara wayewa da gogewa " bangaren karatu kuwa baa magana dan sun dage sosai " sai dai a wan nan bangaren sunsamu banbanchi dan kuwa ita hiyana tafi maida hankali kan karatun islamiya musamman karatun qur'ani " itakuma diyana tafi dagewa a pannin boko" amrat da lamrat kuwa dukka bangare biyun suna dagewa "

yauma kamar kullum sun dawo daga school misalin karfe 4 na yamma suna kwanche a ɗakinsu gaba ɗayansu suna hira " diyana tamike tana faɗin natafi palo nayi kallo " saikin dawo inji zahra " fichewa diyana tai jikinta sanye da doguwar riga fari tas mai kyau amma jikin'rigar bawani kwalliya plen'ne kanta kuwa babu dan kwali ta zuba gashin nan har gadan baya sai sheki da kyalli yake kawar wata yar india " zama tayi a palan abinta ta kunna kallo ta kamo tashar discovering tana kallan daji da abun dake chikinta " daman diyana sarkin san kallone " "tayi nisa chikin kallan datake batama ji shigowar mutunba " sai dai kawai taji yana faɗin ke jeki kawomin coffee " da sauri ta ɗago tana kallansa" murya na rawa tache ina wuni yaya Aryan " bai amsaba kuma bai sake dagowaba" mikewa tayi jikinta har rawa yake ta saukoh kasa tanufi kichin " coffee ta hada masa yadda taga bintu mai aiki kehadawa ta dora a kan plate san nan ta dauka takoma sama" yadda tabarsa haka tasamesa gabansa tazo ta duka tamika masa cup ɗin batare datayi maganaba " shiru bai ansaba kuma shima baiyi maganaba har kusan 10 mnt tukun nan a shagwabe take magana ayya yaya nagaji wlh hannuna zafi yake kakarɓa mana pls " da sauri yaɗago yana kallanta yadda take maganar hankalinta kwanche,sai daya ƙare mata kallo from head to toe , tukun nan yasa hannu a nitse ya karbi cup ɗin yana faɗin karnasake ganinki babu ɗan kwali " "shiru tayi tana tunanin daman yana kallan mutanene basai mutun yazo yawuchesa sau darima bai ɗaga kai ya kallesaba tayi nitsa chikin tunani " yadaka mata tsawar da sai'dayasa tamike, badake nakeba" murya narawa take maganar eh eh naji yanzu zanjema,na daukoh " batare daya kalli,indatakeba to jiki daukoh kizo " da sauri ta juya tanufi ɗakinsu

A hankali ya kai cup ɗin coffee ɗin saitin bakinsa ya kurba da sauri yasauko da cup ɗin yadawo dashi saitin idansa yana kallan coffee ɗin,mamakine ya bayyana karara a kan fuskarsa sake kai cup ɗin bakinsa yayi yasake kurba ya lumshe ido,kana yabuɗe sosai yake shan coffee ɗin har takare batare daya saniba,shiru yayi yana tunanin wai bayache yarinyar nan tasa ɗan kwali yazoba,meyasa bata dawoba,ganin tunani babu abunda zaimasa,yasa yachiro wayarsa,yafara neman layin yusuf ringing wayar take amma ba'a ɗagaba har saida kiran takusa katsewa Yusuf,yaɗauki kiran a nitse yake magana yusuf kana da num ɗin zahra ne " eh inadashi lfy faɗin yusuf " eh lfy turomin yanzu " ok inji yusuf " katse kiran yayi ya ajiye wayar a gefensa saikuma wani tunani tafara shiga zuchiyar wai meya haɗani da itama to dazan'nemeta, wani bangare na zuchiyarsa ke bashi amsar dachewa saboda coffee mana,afili yake faɗin yes saboda coffee,wayar'sane tayi kara alamar shigowar sako yana dubaka,saiyaga num ɗin zahra yusuf ya tura masa

kiran layin yafarayi ringing ɗaya zahra ta ɗaga " chikin isa take magana wai wayene naga sabuwar number" "kamar daga sama taji muryan Aryan yana faɗin kichewa yarinyar nan tazo palo tasameni, " saura kaɗan zahra tayi fitsari a wando saboda tsoro in ina tasomayi,ina ina inawuni yaya " baijira yaji wata maganaba yakatse kiran " aruɗe zahra ta dubi diyana,tache diyana ke kaɗai che kikafita ɗakin nan mekikaje kika aikata to kiyi sauri yaya Aryan na palo na jiranki " murguɗa baki diyana tayi san nan tafara magana,mekuma zanyi niga iya coffee kawai yache nakawo mar kuma nakaimasa, sai ɗan kwali dayache na saka kuma basawa zanyiba ato irin zafin nan dake damuna, wlh ni gashinma yankesa zanyi da almakashi dan zafi yakesa naji " Zahra dai a tsorache take, tafara magana kai dagaji muryar tama kasan a tsorache take kitashi to kije dawuri yana palo yana jiranki " batare da'tasake maganaba tamike tayi waje tana murguɗa baki, yadda ta barshi haka ta dawo tasameshi da sallama a bakinta tashigo palan," bai amsaba kuma bai ɗagoba " gabansa tazo ta duka a sanyaye tayi magan gani nan " bai tankataba kuma bai ɗagoba kusan 8 mnt " dan allah yaya kayi magana mana wlh nagaji da dukawan nan kafofina sunnamin zafi chewar diyana " kamar baiji me tafaɗaba yachigaba da daddanna wayarsa saida yakara kusan 10 mnt " tukun nan, ya ajiye wayar a gefe bata re daya kalletaba yafara magana ina dan kwalin danache kisa " shiru tayi batayi maganaba kana ta zuba masa ido tana kallansa " dago manya manyan idan'sa yayi ya saukesu a kanta, saida ta tsorata ganin shikuma kalar idon nasa ash ne, ita tunda takema bata taba kallon idansuba dan basa dago kai " tsawa yamata badake nake maganaba " nantake tafara hawaye tana faɗin dan allah yaya kayi hakuri wlh akoi zufane idan mutun yasa ɗan kwali kuma.. " Bata kai karshen maganarba yaɗaga mata hannu yana faɗin it's ok waya haɗa miki coffee ɗazun " nine dakaina na haɗa tabashi amsa " ke da kanki yayi tambayat yana kawar da idonsa daga kallanta " eh nina haɗa " to tashi kije kiyi nill down a chan " toni menamaka, a shagwabe tayi maganar " mamakine yakamashi, ya mai mai ta maganar nata toni menamaka, nan take ya daure fukar nan kamar baitaba dariyaba, wani mugun kallo ya wurga mata wadda tasata mikewa ba shiri takoma tsakiyar palan tayi nill down,"
Jingina kansa yayi a jikin sofar ya lumshe ido makar mai barchi, kusan 15mnt ya ɗauka a hakan kamar daga sama kuma yajiyo voice na Aiman yana faɗin wai daman nan kazo inata nemanka " batare daya buɗe idoba yake faɗin, to mezaka bani " yusuf dake tsaye a gefe guda ne yache mekuma diyana tamaka " "sai'lokachi yaɗago kai azuchiyarsa yana mai mai ta sunan diyana kallon inda take yayi sai faman haɗa zufa take, ɗauke kansa yayi yamaida,kan su yusuf dake tsaye kusa dashi zaiyi magana " yusuf yarigashi dachewa diyana tashi kitafi ɗaki " ai tun Yusuf bai karisa maganaba tamike da gudu tana hawaye tayi ɗaki " harara Aryan ya wurgawa yusuf kana yache me ruwanka da ita kai kabata punishment ne dazakache ta tashi " "harara yusuf ma ya watsa masa kana yanufi sofar yana kokarinzama yanafaɗin kudai bakuji daɗin zuchiyarkuba wlh ko tausayin yaran nan bakuji kunafa sane da irin rayuwar dasukayi amma baku kyautawa wlh " " kallan banza Aiman yayiwa yusuf san nan yafara magana to kai tunda kanajin tausayinsu ba shike nanba, inaruwanka da zakache musai mungi tausayin nasu, to bamuji kuma bazamujiba " kallan banza shima yusuf ke bin Aiman dashi kawai batare dayayi maganaba " mikewa Aryan yayi yanufi hanyar fata daga palan batare dayayi maganaba " kallo Aiman yabishi dashi har yafiche tukun nan ya dawo da kallansa kan yusuf yafara magana " kamar wani abu nadamun tager fa ko yakagani " eh naga alamar hakan achiwar yusuf " to bari nabi bayansa dan naji me matsalar chewar Aiman " adawo lfy inji yusuf " Aiman bai amsaba yafito kaitsaye bangaren Aryan yanufa.

Zaune take a gefen gadanta tana fuskantar hajj sadiya wasu abubuwa hajj sadiya tafitar daga jakanta guda uku tamika mata tana faɗin angama da batun sarauta, sauran batun wayan nan yaran da Aisha takawo, gagarabadau yachemin infaɗamiki aiki akansu bakaramin aiki bane sai munbashi lokachi dan da alama yaran akoi tsari ajikinsu saiyafara warware tsarin jikinsu,tukun nan zai iya yimasu wani aiki," Aunty amarya ne tasoma magana to wayan nan yarakuma inasukaga wani tsari ajiki saboda allah dai " hannu hajj sadiya tasa tarufewa Aunty amarya baki,tana faɗin ke wlh gagarabadau baya karya kuma kiyi a hankali dan daga nan zai iya jiyo mekike faɗi, batun yara kuma dakike magana duk fulanin nan dakike gani suna zaune a dajin nan chemiki akayi a banza haka kawai suke zaunene ai tun randa suka haifi ƴaƴansu, aranar suke farajijjikasu da magunguna " "chere hannun hajj sadiya Aunty amarya tayi daga bakinta kana tache to shike nan yanzu wayan nan kayan dakika banifa ya za'ayi amfani dasu kuma nan da kwana nawa gagarabadau ɗin yache zaiyi aiki akansu " eh munyi dashi akan zandawo nan da wata 2 chewar hajj sadiya " zaro ido aunty amarya tayi tana faɗin wata biyu kuma zata sake magana komai tatuna sai tache to shike nan ba damuwa,yanzu dai waɗan nan abubuwa yazanyi dasu " tona rami zakiyi ki binnesu da hannunki chewar hajj sadiya " to shike nan gobe zanje ta bayan gidan nan na binnesu,sai maganar Safras da zulaihat chewar aunty amarya " eh shima sai bayan sallah dan yache aikin nada matukar wahala kuma gashi sallah yakawo kai jamaa sunmasa yawa sosai kowache tana kawo kukanta asa mijinta tafito da ita sallan nan ta haɗu sosai, " mikewa Aunty amarya tayi tana faɗin bari nakawomiki kuɗin motakoh tanufi wajen Waldrop din kayan'sawarta

Misalin karfe 8 na dare gaba ɗaya family sun haɗu a palo suna chin abinchi kamar yadda suka saba " shiru kakeji bakajin karar komai sai karar spoon, bayan sungama chin abinchin ne " mai martaba yayi gyaran murya yasoma magana yau azumi saura kwana 33 yakamata kufara fitto da kayan abinchi kuna rabawa al umma san nan kuma gaba ɗayan mu zamuje umrah, saiku shirya, akoi mai magana " shiru palan yayi " diyana che tache Abba inasan da'sallah inje kauye ingano yaya bello " wani kallan banza yusuf ya wurga mata akule yafara magana au yanzu duk azabar dakukasha sake tunanin kauyenma kuke ke nan " mai martaba yayi murmushi yana faɗin to kai ina ruwanka kasan tsakaninsu da bello'ne to barikaji zasuje kuma kuzaku kaisu kukulamin dasu har sudawo " afusache don yamike zaibar palan " sai ina chewar Ammi " shiru yayi baiyi maganaba kuma bai dawo ya zaunaba " mai martaba yayi murmushi yache to ki kyalesamana jeka abinka ammafa kashirya dan dakai zaku kaisu diyana kauye " batare dayache koh uppan ba yayi waje " kallan Ammi mai martaba yayi chikin harchen fillanchi yake faɗin ki kyalesu inamusu hakane ko zansamu zuchiyar nan tasu taragu inba hakaba akoi matsala " jinjina kai Ammi tayi tana faɗin eh hakanma yana da kyau ai gara murinka koyamusu sanyi kobayawane " mikewa Aryan yayi yanufi waje har yakai bakin kofa saikuma yajuyo yana kallan diyana a nitse da sexy voice nashi nan yafara magana kisameni a ɗaki inzakizo kikawomin coffee yana kaiwa nan yawuche " gaba ɗaya palan mamakine yakamasu baranma yusuf suda sukasan hali, "nan take zahra jikinta yafara rawa ta kalli diyana tafara magana kasa kasa chikin harchen fillanchi wayache kiche zakije kauye to wlh yau babu ruwana dan zaki karɓi hukunchi " murguɗa baki diyana tai tamike tayi waje " baki sake zahra ke kallanta azuchiyarta take tunanin lallai diyana inaga darabon zakisha bugu kilama harda karaya,"
Da ɗai ɗai suka bar palan gaba ɗayansu kowa yanufi bangarensa

Zaune take a gaban murhun wuta tana kokarin hurawa innar buba tashigo gidan da sallama inna ta amsa mata sallamar,tamata iso zama innar buba tazo tayi kusa da inna suka gaisa " innar buba tafara tambayat inna wai har yanzu habiba baki samu kuɗin bane nifa wlh nafara karaya " aa karkikaraya dan kuwa nasamu natara dubu 5 yanzu kuma anjima zansake zuwa tallah kinga da kuɗin sun kai dubu 10 sai muje koh kiɗan kara hakuri kinji chewar inna " to badamuwa allah yakaimu nibari nazo nakoma gida dan mai dubawa buba kafarsa zaizo anjima chewar innan buba " inna habiba tache yajikin nashi " innar buba ta amsa da sauki sosai wlh dankuwa kafar tafara komawa dai dai " mashaa allah chewar inna " to habiba sai kinshigo tafaɗi hakan tana kokarin mikewa, har kofar gida inna habiba ta rakata san nan ta dawo

Pls more comments and share
[7/3, 5:47 AM] Al~Quyraemey: *💫STAR LADY💫*

*DUK ƘARFIN IZZATA*

💖Story And Written💖
⬇️
*Star Lady*

Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

*Episode 9*


Rike take da cup ɗin coffee datahaɗa masa tafiya take, itakanta batasan ina tanufaba dan bata san part nashiba tazo dai dai,zata fita bangaren Ammi tachi karo da Fahad " baya taɗan koma kaɗan kana tache ina wuni yaya Fahad " bai amsaba kuma bai ko kalletaba yazo yawucheta " da sauri ta tache yaya Fahad dan allah inane bangaren yaya Aryan " banza yayi da ita yayi wuchewarsa chiki yabarta tsaye " tayi kwafa tana faɗin wlh dani kake zanyi maganin kane tajuya tachigaba da tafiya, sai sauri take kamar tasan inda zata

kai tsaye palan mai martaba tanufa da sallam tashiga babu kowa awajen dan haka tanufi betroom kai tsaye sallama tayi a bakin kofar betroom ɗin tunba'a amsa sallamar kuma ba'abata izinin shigowaba tashige abunta " zaune tasamu Mai martaba da Ummi a kan gado suna hira " mamakine yakama Ummi " Mai martaba kam bai damuba dan yasan halin diyana sosai " Ummi che tache diyana lfy kika shigowa mutane ɗaki babu sallama " turo baki diyana tayi tana faɗin dakin yaya Aryan nake nema, natambayi yaya Fahad yaki faɗamin " Ummi zatayi magana, mai martaba yarigata dachewa " idan kika fita nan kibi pangaren hannun damanki a nan part nasa yake " to ai kofa biyu'ne awajen wanene nashi chewar diyana " na biyun shine mashi mai martaba yabata amsa " to kawai tache san nan tafiche abunta " dawo da kallansa mai martaba yayi kan Ummi data sake baki take kallan ikon god " ya akayine mai martaba yatambayeta " hmmm su diyana manya mamakin tabani ne itakam ko ajikinta kawai tafaɗowa, mutane daki chewar Ummi " murmushi kawai mai martaba yayi kana ya girgiza kai

Tura kofar part ɗin tayi tashiga tana tafiya tana wakarta chikin harchen fullachi " (fullo daru midarata fullo daru midarata) " har tashiga palan babu kowa, dan haka sai tanufi kofar datagani a chikin palo kai tsaye tashiga babu ko sallama " jin mutun yashigo yasashi ɗago kai yana kallanta tachikin mirrow, daure,yake da towel a kugunsa da alama wanka yafito, gawani gashi mai tsantsi bakinkirin a kwanche akan faffadar kirjin'sa, damtsen hannunsan nan kamar zai fashe saboda karfi,tamkar wani zaki, ga gashin kansan nan kuwa ajike, yake da'alama ya wanke kanne, gashin kwanche yake har kafaɗarsa, zuba mata wan nan ash eyes ɗin nashi yayi " sai waige waige take da alama bata magansaba " shiru ta tsaya kamar mai sauraron wani abu" "zuba mata ido yayi sosai yana kallanta " sanye take chikin doguwar riga abaya still dai kanta babu ɗan kwali," "juyawa tayi zata fita karaf idanta ya sauka chikin nashi ta chikin mirrow, tsabar tsorata, wani kara tayi kana tayi wurgi da cup ɗin coffee dake hannunta ta watsa aguje zata nufi waje amma ina, taku biyu yayi ya tamki kugunta " saboda tsabar tsoro nunfashinta ɗaukewa yayi " sai dai kawai yaji tasake jiki zata faɗi da sauri yariketa da kyau,

Kallan fuskarta yayi yaga alamar kamar suma tayi, yasa hannu ɗaya ya ɗauke ta Chak sai kan makeken gadansa ya kwantar da ita " san nan yakoma gaban miro yachigaba da abun dayake, bayan yagamane
yanufi dressing run nashi, saida ya dauki kusan 10 mnt kafin yafito sanye da kayan barchi a jikinsa doguwar wando da riga mai dogon hannu masu laushi farare tas " kai tsaye freij yanufa ya daukoh ruwa, yazo ya zauna a gefen gadan yabuɗe bakin rubar ruwar ya tarfa a hannunsa, ya shafa mata a' fuska " wani nauyayyar ajiyar zuchiya ta sauke haɗe da jan dogon numfashi,
batare da tabuɗe idoba tafara sambatu " don Allah kayi hakuri wlh bansan bakaya ajikinka bane nashigo kuma kaikache nazo dan allah karka bugeni " ke kimin shiru chewar Aryan " da sauri ta buɗe ido tana kallan inda take, mikewa tayi da sauri ta saukoh daga gadan tanufi hanyar fita " kamar daga sama taji yana faɗin " inazakije konache kitafine? " Da sauri ta juyo tana in ina a'a " to zo nan ki zauna yayi maganar yana nuna mata kasan carpet ɗin " da sauri takoma ta zauna " wayache kizubarmin da coffee " ɗago kai tayi tana kallansa taga bama ita yake kalloba wayarsa yake latsawa " kayi hakuri zankawo maka wani tabashi amsa " kinsan meyasa nakiraki " aa bansaniba " wlh wan nan shine last worming na karshe da zanmiki idan kikasake yimana maganar wan nan shegen kauyen a gidan nan saina babballaki kinajina " murya na rawa diyana tache eh naji "

kuma inasan kibuɗe kunne ki saurareni idan kika bari nasake ganinki babu ɗan kwali saina aske gashin nan gaba ɗaya " da sauri diyana tache yauwa yaya dan allah ka askemin inka iya wlh banaso daman " mamakine yakama Aryan tunani yashigayi idanfa yabiyewa yarinyar nan to tabbas zaiya babballata " dan haka sai yache ke yanzu kitashi kije kikawomin wani cofee ɗin san nan kuma kullum dasafe karfe 7 dai dai kikawomin coffee haka da daddarema karfe 9 dai dai shima inabutar coffee idan kika kuskura kika wuche time dana baki,sai jikinki yafaɗa miki kuma banche wani yahaɗa , coffee ɗin ba kezaki rinƙa hadawa kinaji, tashi kije kikawomin wani yanzun nan yayi maganar a kausashe " da sauri tamike tanufi kofar fita har takai bakin kofa kuma saita juyo tana faɗin yaya Aryan to yabatun askin zaka askemin gashin " wani mugun kallo ya wurga mata waddayasata fita a' aguje "

gyara konchiyarsa yayi a kan gadan yana kokarin ɗaukar wayarsa saiyaji kira tashigo, saida wayar takusa katsewa tukun nan yayi picking call ɗin " hello akache daga ɗayan bangaren " ykk hisham chewar Aryan " lfy y gd, wai meyasa innakiraku Aryan baku san daukar call na chewar hisham " Aryan yache au kakirane ka tambaya, to ra'ayi yanzuma kayi sa'a ne dan inachikin farinchiki badan hakaba bazan daukaba " haka zakachemin koh Aryan to waima menamukune " kara daure fuska Aryan yayi kamar hisham na kallansa yache kaga hisham mufa duk wanda yahaɗa hanya da mace to bamatare, dashi dan yazama mai rauni, mukuma bamasan mai rauni kusa damu " wani mahaukachin dariya hisham ya kwashe dashi yana faɗin inshaa allah Aryan kaine mutun na farkoh a chikinku dazai fara faɗawa soyayya kuma inshaa allah yadda kuka wahalar da soyayya itama saita wahalar,daku, wahalarma ba.. "Aryan baijira hisham yakare jawabansaba yakatse kiran yayi wurgi dawayar gefe " dai dai lokachin diyana ta dawo hannunta ɗauke da cup ɗin coffee bakinta dauke da sallama " wani mugun kallo ya wurga mata a kausashe yache get out " da sauri tajuya dan yadda taga fuskarsan nan kamar wani zaki " kichin tanufa ta ajiye coffee ɗin a kan table san nan tafito kai tsaye sashen Ammi tanufa abunta ,

Tana shiga tayi ɗakinsu tasamu su zahra har sunyi barchi hayewa saman gadan itama tayi ta kwanta abunta bajimawa barchi ya dauketa

Washe gari misalin karfe 7 sungama shirinsu chikin uniform naso sunyi kyau sosai abunsu
Diyana sarkin aiki dachikawa bata daure gashin gantaba tasa hijabi, wutsiyar gashin yalekoh sosai saboda gashin,yafi hijabin,tsawo

Kai tsaye palan mai martaba suka nufa dan yin breakfast da sallama suka shiga " kowa nagidan yana zaune kan table suna breakfast " mai martaba dakansa ya amsa musu sallamar yana faɗin wow yan matana kunyi kyau gaskiya " Ummi da Ammi ma sai murmushi suke suna yaba kyansu auntu amarya ko sai harararsu take " yusuf kuwa chewa yayi kai sweet sis yanzunema asalin kamanninki da don kekara bayyana " asukane don ya ɗago kai yana kallan yusuf " yusuf baimasan yanayiba saima karachewa yayi ammafa kinfi don kyau gaskiya, domin kuwa blue eyes yafi green eyes kyau "

a,fusache don yamike yayi yana faɗin zama danake inachin abinchi,dakuma yafara kawo raini, kana yadawo da kallansa kan Ummi yana faɗin daga yau arinka kaimin, abinchi na bangarena, dagahaka yayi waje " murmushi kawai Mai martaba keyi yana girgiza'kai kana yadubi su diyana dake tsaye, to tsayuwar me kuke kuzo kuzauna kuchi abinchi kutafi karkuyi latti " wuchewa sukayi suka zauna kan kujerun table din " bintu sufara sarving nasu, nantake sukafara chin abinchin "

ke banache karfe 7 dai dai kirinka kawomin coffee ba yayi maganar kansa na duke yana danna waya kamar bashike maganarba " chikin sanyayyiyar murya diyana, tafara magana, kayi hakuri yaya Aryan wlh nayi tunanin kafasane dan naga jiya kache nafita maka a ɗaki " mai martaba

Please Login or Register in order to submit comment