Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

samu kariba to gwaranima, mardiya ko ɗayan bata samuba dan haka muna bukatar ƴaƴa agidan nan, yanzu haka Fahad shekarun sa inban mantaba zasukai 25 ga Haidar da Umar suma sun kai 23 ga Zahra Auta an zama yan mata yanzu haka Zahra nada 16 years to mekuke bukata dayawuche aure Allah ya hore muku komai,to yazama dole kuyi aure yan zu kam takarisa maganar da alamar ɓachin rai a face ɗinta, Ummi dai ido ta zuba musu tana kallon su dan ita ba mai yawan magana ba che " laaa ni Aunty farida kin tunamin ma inasan muyi wata magana, chewar khalid ɗin "ok to inzo muje waje ke nan, Khalid ya ɗan sachi kallan inda Zahra da Ummi suke san nan yace eh to muje palan Abba zai fi tunda nasan yanzu baya nan yana fada "to muje amma kafin nan bari nayi waya da yan uwan kan nan dan inasan gabaɗayan mu muhadu a palan Abba bayan sallar issha "to kawai Khalid yace tare da mikewa yanufi hanyar fita "Ummi tache adawo lfy Baba tunda abun sirri ne "murmushi yayi yana shafa kansa batare da yache komai ba yafiche daga palon

To

(Garin yola ✈️🛬

kyakkyawar yarinya che fara tas ga dogon hanchi har baka doguwa che amma ba sosai ba bata da kiba duk da tana sanye chikin hijabi, hakan bai hana gashin dake kwanche a gaban goshin ta fito waba dark black ne gashin very smooth gata da manya manyan blue eyes, laɓɓan'ta ɗan karami pink colour bazata wuche 14 years ba sanye take chiki wata ko ɗadɗiyar atamfa ta koɗe tayi fari ga wata je mam miyar hijabi baki ne amma saboda koɗewa sai da ya dawo ash colour tsaye take tana riƙe da bokiti irin na penti almost 5mnt tana tsaye chikin fushi tafara magana da harchen fullanchi "hiyana idan bazaki fitoba wlh tafiyata zanyi na barki, tayi maganar tana kallan kofar wani gida
Gida ne ɗan ma dai dai chi kofar gidan ansa masa buhu an rufe a matsayin labule,irin gidan fulanin nanne masu kiwon shanu ke waye gidan yake da zana, daga chikin gidan hiyana ta da wata murya mai daɗin gaske tana faɗin adin kai diyana ina zuwa ina dubawa amrat hijabi ne "to wai waya chemaki amrat zata bi mu ne, zamuɗebo har da rabonta dan haka ta zauna a gida taƙarisa maganar tana yamutsa fuska " yaye labulen buhun hiyana tai tafito, subhanallah sarki ya tabbata ga ubangiji da yayi wan nan halittar hiyana tafi diyana kyau sosai ta ɗan fita fita tsawo, kuma da alama zata ɗan fita shekaru dan hiyana zata kai 16 years farache sosai tafi diyana haske idon tama yafi na diyana girma da shiga colour idon ta yayi blue sosai kyakkyawa che ajin farko, rike take da hannun wata yarinya wadda bazata wuche 11 years ba yarinyar tana kama da diyana sosai sai dai ita idon ta baki ne manya manya, karaso'wa wajen da diyana ke tsaye su kayi hiyana na faɗin kiyi hakuri diyana kinji "haba hiyana ke che babba amma keche ke ja'mana duka kullun "to shike nan diyana kiyi hakuri zan gyara kinji muje to "aa bazamu tafi da amrat bafa ki mai data gida "diyana kibari mutafi da ita mana babu kowa fa a gidan bappa kuma yayi barchi kin sani bansan mu barta a gd ita kaɗai "nikuma Allah hiyana bansan amrat tabi'mu rafin nan akoi wahala Allah "to yanzu kam tun da mun fito muje kawai mu daina ɓata lokachi, juyawa diyana tana tura ɗan karamin bakin tan nan suka jera su kasa amrat a tsakiya

Wani dan siririn hanya suka nufa mai chike da dogayen chi yayi tsakiyar chi yayin suka kutsa tafiya sukayi mai nisan sosai kafin su isa wani rafi mai girma gefe gefen rafin chike yake da gona'ki da shuke shuke, ruwa suka ɗiba a buket ɗin dasuka riƙe hiyana ta ɗora'wa diyana nata buket ɗin chike da ruwa san nan da kyar itama ta ɗora nata ta kamo hannun amrat suka fito daga rafin suka kama hanyar gd, tafiya suke ba wan da yace da ɗan uwan sa ko kala, a dai dai wata katuwar bishiyar mangoro wani saurayin da bazai wuchi 24 years wani ɗan dotti dashi pusu pusu kamar an kwato shi daga bakin Kura ba yasha gaban hiyana birki suka ja suka tsaya suna kallan sa, ɗaure fuska diyana tayi tana faɗin "buba me haka dan Allah kabamu hanya mu wuche, wani kallan uku 10 buba ya watsawa diyana kafin yace "ke ba take nake ba tukun nan kibari nagama da hiyana zan dawo kanki "chikin sanyin murya hiyana tafara Magana buba kayi hakuri kaji kabar mu,mutafi wlh ruwan nan akoi nauyi kabari in muka dawo ɗiban na biyu sai mu tsaya muji me zakache "ke ni sa'ankine dazaki che na jira ku to baku isa ba yanzu nake san yin maganata idan ruwan yamuku nauyi,sai ku sauke kasa ku ajiye idan nagama maganan da zanyi sai ku ɗauki ruwan kutafi, diyana sarkin rashin hakuri a kule ta juye'wa buba ruwan dake kanta ajikin sa tun daga kansa har kafa yamike shar'kaf ta watsa a guje tanufi hanyar gida, dafe kai hiyana tayi tana faɗin "kayi hakuri buba..bata kai karshen maganar ba buba ya buge ruwan dake kanta ya faɗi kasa ya zube ɗaukar boket ɗin buba yayi yafara bugawa da katsa yana kokarin fasawa, hiyana kuwa ganin hankalin buba ya koma kan yana san fasa musu boket ne yasa ta kama hannun Amrat suka kwasa aguje sukayi hanyar gd, sai buba ya gama fashe musu bo'kitan gaba ɗaya san nan yabi bayan su a guje

Da gudu diyana ta faɗa gd wani ɗakin buk'ka tashiga,sai haki take tana numfashi da kyar, wani bawan Allah dake zaune chikin ɗakin, a kan gadon chiyawa, daka gan shi kaga ka mannin hiyana duk da tsufa da wahala dake tattare dashi ba zai hana ka gane kyan sa ba "diyana lfy kika shigo kina haki haka meyasaki gudu wani kika tso kana ko "bappa wlh buba ne shine zai bugeni na gudu kuma ba abun dana masa, bappa zaiyi magana sai ga hiyana tashigo rike da amrat dukkan su sai haki suke suna numfashi sama saman "hiyana har dake yau kuma bappa ya tambaya yana kallan hiyana, chikin sar'kewar murya hiyana tace "aa bappa laifin diyana che ta shafe ni, "ya Allah ya kawo muku mafita ƴa'ƴana, har suna haɗa baki wajen chewa ameen bappa, basu gama rufe baki ba aka ba paɗo ɗakin babu ko sallama wata mata che baka mai ƙaton hanchi, damkoh wuyar hiyana ta jata zuwa tsakar gd ta hau bugu matar nan tsaka nin ta da Allah take bugun hiyana, ta ko ina ihu hiyana keyi tana faɗin "dan Allah inna kiyi hakuri, "au kinsan da hakuri ke nan koh har buba zaku jiƙa da ruwa kuma ku zage'shi koh to wlh yau sai kun yabawa aya zakin ta, komawa ɗakin tayi ta damkoh diyana da gudu Amrat tayi bayan bappa ta buye, inna kuwa jan diyana tayi har tsakar gd ta ɗaukoh wani itache ta hau bugun hiyana da diyana dashi bugun su take sosai duk inda ta samu take sauke musu itachen, tun kukan su na iya fita har sautin kukan ya daina fita,duka sosai inna tamusu sai da ta faffashe musu jiki, san nan ta kyalesu takoma gefe kan wani dutse ta zauna tana mai da numfashi, su kuma suka dun kule waje ɗaya suna kuka, sai da inna ta gama hutawa san nan ta ɗago ta dube su tafara magana, "ke hiyana ko kina so ko baki so buba zaki aura dan kin samu ma zai rufa miki asiri, kuma kutashi tun da kun fusata buba ya fasa buket ɗin ɗiban ruwan to da kofi zaku koma ɗiban, wlh kutashi ku ɗauki kofi kutafi kufara ɗiba min ruwa yanzun nan, ku chika komai na gd san nan ku chika durum na dabbobin nan,kutashi tun ban zo na karai'raya kuba ta karisa maganar chikin tsawa, da kyar suka miƙe har suna tangal tangal suka sufi wani ɗan ki chin suka ɗaukoh kofi kowache ta ɗauki cup 1 suka fito suna kuka suka nufi waje

Bappa na zaune chikin ɗaki yana hawaye Amrat ta fito daga buyan datayi a bayan sa tafara goge masa hawayen tana faɗin bappa ka daina kuka kaji, rungume ta bappa yayi yachigaba ga kwalla

Su hiyana kuwa han yan rafin suka nufa suna rike da kofin suna kuka, "chikin kuka hiyana tace yanzu diyana bakin ga irin abun danake faɗamiki ba, kullun ina faɗamiki komai buba zai mana muyi hakuri dan in mu kache zamu biye masa wlh mu zamu sha wahala komai kan mu zai dawo amma ke bakiji,bansan wani irin kai ne dake ba "share kwallan fiskar ta diyana tayi tana faɗin yanzu hiyana haka zamu chigaba da rayuwa ni gaskiya bazan iya jure wa ba, yazamuyi mu ɗebo ruwa da kofi kuma a che mu chika abuba dake gida da ruwa har dana dabbobi nidai bazan iyaba "to duk bake kika jaba da zaki che bazaki iyaba kin nafa sane da kyar bappa yasamu yaje chikin birni ya sawo mana buket ɗin nan, yanzu gashi kinsa buba ya fasa bappa kuma ba takawa yake ba yanzu bare ya sawo mana wani ai dole ma mu ɗebo ruwa da kofin tun da dai kin san inna in tayi magana ba wan da ya isa yasa ta chanza, shiru diyana tayi bata sake chewa komai ba harsuka kai bakin rafin suka ɗebo ruwa a kofin suka juyo suka kama hanyar gd

More comments an share
[7/3, 5:45 AM] Al~Quyraemey: *DUK ƘARFIN IZZATA*

_💖Story And Written💖_
⬇️
*Mrs BMB*

💫New team 💫
⬇️
💖The talent troupe writer's 💖

Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

*Episode 3*


Kwan che DON yake chikin ɗan karamin pool nashi dake wajen sha'katawar sa na chikin ɗaki kwan che yake chikin ruwan gaba ɗaya jikin sa na chiki iya kansa kawai yabari a waje idon sa a lunshe kamar mai barchi, Aryan dake zaune saman ɗaya daga chikin kujerun wajen, yace "DON da alama fa maganar Yusuf zai zama gaskiya, batare daya buɗe ido ba yace "haba Aryan kayi magana da Yusuf ɗin ne "aa bamuyi ba amma dai da alama zan chen nashi zai iya zama gaskiya "hmm da kuwa sun gama dani sun kashe idan haka ne "to yanzu wani mataki zaka dauka Aryan ya tambaya yana kallan face ɗin shi, sai lokachin ya buɗe green eyes nashi ya sauke su akan Aryan, yayi da Aryan ɗin ma shi yake kallo " Slowly ya furta banyi tunani a kai ba amma anjima zanyi magana da aunty farida Jinjina kai Aryan yayi yana faɗin "why baza kayiwa, Ammi maganar ba "hmmmm kai ma dai Aryan da wani magana kake,kafasan halin Ammi ni ko kallo ma ban ishetaba bare tasa baki a lamari na, shiru Aryan ya ɗanyi kafin yace "bari nizan gwada, yimata magana, guntun tsaki DON yaja yana faɗin "dama ka kyaleta dan ba sauraran mu zatayi ba nasani "eh to hakane kam amma dai yakamata tasa baki, mikewa yayi yana kokarin fita daga chikin pool ɗin,wayarsa dake ɗaki tafara kara, daukan towel dake jere awajen yayi yana goge jikin sa, yana faɗin "nifa inaganin kai tsaye zan yiwa Abba magana dan gaskiya a yadda nakeji yanzun nan bazan iyaba "to kana ganin hakan shine mafita " kwarai kuwa, yayi maganar yana kokarin shiga ɗaki "

Katafaren gadon sa yanufa yasa hannu ya ɗauki wayar, dake kan gadon kafin ya ɗauki wayar kiran ta katse,dubawa yayi dan yaga waya kirasa ganin Khalid ne,yasa yabi kira ringing ɗaya Khalid yayi picking, sa wayar a H-free DON yayi ya ajiye saman mirrow, yana gyara lallausan haɗaɗɗen gashin kansa sai kyalli gashin ke yi kwanche har bayan sa,

daga ɗayan ɓangaren Khalid yace 'wai yanzu DON da gaske bakuyi kewar mu ba ko?,ko neme mu bakuyi ba, guntun tsaki DON yaja yana faɗin abun da ka ƙira ka tambaya ke nan, "kwarai kuwa shi nakira na tambaya "DON zai sake magana, Aryan yasa hannu ya ɗauki wayar yana faɗin " dan Allah ku zauna a naija pls kar ku dawo dan da kuka tafi rayuwar tafi daɗi ma,dariya Khalid yayi kafin yache hakan ya tabbatar min da kunyi kewar mu ke nan, tun da kache mu zauna a naija hakan na nufin muyi sauri mudawo ke nan tsaki Aryan yaja kana ya jefar da wayar a kan gado ya juya yanufi hanyar fita ɗakin yana faɗin in kagama shiri kakirani awaya san nan ya fiche daga dakin, DON kuwa yana jin Khalid nata magana achikin wayar amma yayi banza, har yagama gyara gashin sa yatara ya ɗaure a baya san nan ya shafa mai mai kamshi da tsada ya fesa Dubai perfume mai kamshi sosai yanufi dressing room almost 30mnt san nan yafito, sanye chikin black jeans da blue t-shirt kayan sun kara bayyanar da Asalin kyan sa chi'kakkiyar surar sa irin na jaruman maza yakara bayyana, faffaɗar kirjin san nan a tsaye dam dam ga dam'tsen hannun sannan kamar zasu fashe a chike suke sosai laɓɓansan yayi ret sosai kamar yasa jan baki, sake fisa turare yayi a jikin sa yasa booth baki akafara sa sai wata dan ƙareriyar agogon daimon mai matikar kyau da tsada ya daura a hannun sa ba karamin kyau yayiba tamkar shiyayi kansa, a hankali ya tako kamar bai san taka kasan yanufi gaban, katafaren gadon sa hannu yasa ya ɗauki wayar sa yana bin screen ɗin da kallo a hankali ya buɗe baki kamar bayasan magana yace Khalid wai har yanzu baka gama surutun naka bane "a fusache Khalid yace gaskiya DON kai dan rai'nin hankaline "oh baka gama surutun ba kenan to pls in kagama ka katse kiran dan zan fitane,rai a ɓache khalid yake faɗin "zaka sanine wlh zamu haɗune, DON dai bai sake chewa komai ba, Khalid dayaji shiru sai ya katse kiran girgiza kai DON yayi yana faɗin na sani bani da masoya kamar ku nima kuma ina kaunar ku
dau kan wayar sa yayi a nitse yanufi waje yana ko karin kiran layin Aryan kirayayi har takatase Aryan bai ɗagaba, waje gaba ɗaya yanufa, a dai dai baƙin kofar babban palo sukayi karo da Aiman da Ahmad, ko kallan inda suke bai yiba yabi gefen su zai wuche "wato DON bakayi murna da dawowar mu bakoh? chewar Ahmad

Aiman kuwa wuche warsa yayi shima ko kallan DON ɗin bai yiba ya haura stair ɗin tsakiya yanufi ɗakin'sa DON kuwa chigaba yayi da tafiyarsa batare daya tankawa Ahmad ba, sai daya kai tsakar gidan batare daya juyoba yafara magana to daman wayache kudawo "rai a bache Ahmad yace ae daman badan kai muka dawoba dan kuwa inda dan kai nema wlh ko kallan kasar nan bazamuyi ba, DON dai bai sake chewa komaiba hasalima tsayuwa yaje yayi a bakin katafaren pool nasu na tsakar gidan, tsayuwa yayi ya juyawa chikin gd baya ya zura hannu a aljihu

Rai a ɓache Ahmad ya juya ya nufi chikin gida a tsakiyar babban palo yachikaro da Aryan shima yana sanye da black jeans da white t-shirt yana daure da agogon daimon irin na DON, ya tara gashin kansa waje ɗaya ya ɗaure yazuba jelar abaya kamar wata mace ga gashin da tsawo, har bayan sa yayi kyau sosai kamar shiyayi kansa, ko kallon in da Ahmad yake bai yiba ya wuce yanufi waje, a kule Ahmad yafara magana "kudai bakuji daɗin halinkuba mutane ne kamar wasu aljannu yanzu haka kafin mu iso sai danayi tayiwa Aiman faɗa amma ko kallona bai yiba haba dan Allah yakamata ku chanza hali, Aryan dai wuchewar'sa waje yayi batare da yace komai ba, haurawa san benen Ahmad yayi yana surutai

Waje Aryan ya nufa kai tsaye inda DON ke tsaye yanufa irin tsayuwar da DON yayi shima yayi ya zura hannu a aljihu suna fiskantar babban gate ɗin gd, gaba ɗayan su fiska kaman an aiko musu da sakon mutuwa, Almost 30mnt suna tsaye a haka babu wanda yache da ɗan uwan sa kala kuma ko motsi basuyiba a tsayuwar tasu
jim kaɗan saiga Aiman yafito shima ya shirya chikin blue jeans da t-shirt ash yayi kyau sosai kuwa duk kansu agogon hannun su iri daya ne, gefen Aryan yazo ya tsaya
juyawa DON yayi yafara tafiya ta ɓan garen dama, ganin DON yajuya yafa tafi yasa Aryan juyawa shima yabi bangaren hagu,Aiman kuma ya miƙi hanyar tsakiya yanufi bakin gate

wani gate dake chikin gidan ta ban garen daman DON yashiga, wasu haɗadɗun motochi ne masu tsadar gaske awajen da alama nanne parking space na gd zubawa motochin ido yayi na ɗan wasu mnt, wasu jibga jibgan sojoji ne suka nufo inda yake tsayen a kalla zasu kai 10, kusa dashi suka ja suka tsaya hannu suka ɗaga suna sara masa, jinjina kai kawai yayi,batare dayayi magana ba kana yasa hannu ya musu nuni da motar da zai hau wata dan karekiyar motache kirar Marcedes Benz, black colour, wani matashin sojane mai jini jiki kato mai ji da karfi fari tas yanufi motar da DON yanuna ya shiga yawa motar key har,inda DON ke tsaye ya jawo mota, wani bakin soja kato dashi kak karfan gaske yazo da sauri ya buɗe wa DON kofar motar
takawa yake sannu a hankali yashiga motar ya zauna, sara masa sojan yayi san nan ya rufe kofar motar, sojan yaja motar da ma tsakai chin gudu suka fita ta ɗayan gate ɗin

A gaban Aryan da Aiman motar DON tayi parking, sauƙe glass din motar DON yayi, yasa hannu ya karbi bindigar da Aryan ke mika masa juyawa Aryan yayi yanufi nashi motar
Aiman kuwa yana tsaye,suma kuma suna tsaye basu tada motochin nasu ba Almost 5 mnt suna tsaye shiru a nitse DON ya ɗago green eyes nashi yana kallan Aiman calmly yafara magana "kai inbazaka shiga bane muyi tafiyar mu, tsaki Aiman yaja yana faɗin "au ashe dai bazaku iya tafiya ku barni ba, na zachi nima wulakanchi zakumin DON dai bai sake magana ba sai ma mai da glass ɗin motar yayi ya rufe Aiman kuwa sai da ya sake tsai dasu for Almost 5mnt tukun nan yabude motar DON yashiga, ko kallan in dayake DON bai yiba yayiwa Abdol umarnin akan suwuche a nitse Abdol ya taɗa motar da matsakai chin gudu suka nufi gate, tun basu karisa security suka wangale musu katafaren gate ɗin a jere suka dan na hanchin motochin nasu waje, motar DON ne a gaba sai na Aryan ke bi masa sai wasu motochi 3 chike da sojoji, shinfi ɗadɗiyar titi suka miƙa

kira ne yashigo wayar DON saida wayar takusa katsewa yachirota daga aljihu, Yusuf shine sunan daya bayyana a kan screen ɗin wayar, picking call ɗin yayi ya kara a kunnensa yana faɗin hello daga ɗayan ɓangaren Yusuf yace "bro ykk "a hankali ya furta normal kai fa "Yusuf yace nima normal, inaganin gobe zan shigo abun dayasa ban shigo yau ba kaga Abba yana da zama damu, Aiman da Ahmad sun gudu sunki jiran meeting ɗin , SO kaga bai kamata nima naki tsayawa ba jinjina kai DON yayi yana faɗin "eh hakane amma kayi amfani da lokachin ka dan lokachi bata jira sai dai ajirata "kai DON tun munayara kake yawan faɗa mana haka inshaa allah zamuyi amfani da lokachin mu, " good kawai yace san nan ya katse wayar
Aiman dake zaune Age'fensane yace akoi matsala fa DON " batare da ya kalla inda Aiman yakeba yafara magana matsala batada wajen zama a family Abubakar saraki, tsaki Aiman yaja kafin yace "ta kanka kuwa zatama fara "koh? DON ya tambaya yana kokarin mai da wayar sa aljihu Aiman dan haushi bai ma sake maganaba

Yola Nigeria

Da kyar da kyar suke tafiya suna rike da kofi a hannun su kamar bazasu kai lbr ba tun safe yaran nan suke debo ruwa da cups amma har yanzu karfe 6 na yamma basu gama ba subhanallah

da kyar diyana ta bude baki tafara magana hiyana bazan iya chigaba da ɗeban ruwan nan ba wlh yinwa nakeji numfashi na zai iya ɗaukewa "ki kara hakuri diyana Allah natare kinji, kiyi addua kawai adun halin dakika tsinchi kanki kuma ki kasan che mai godewa Allah sai Allah yakawo miki sauki "alhamdulillah alhamdulillah alhamdulillah Allah ngd, Allah mai kyauta mai kari ya ubangiji kadube mu da idon Rahma Allah ka kawo mana sauki "
ameen ameen diyana haka zaki rinkayi a kowanihali kika tsinchi kanki, diyana batare da ta sake magana ba tanemi waje kasan wata bishiya ta zauna, a'razane hiyana ke faɗin "aa diyana kitashi dan Allah mutafi inbahakaba kinfasan inna "wlh hiyana sai dai yau inna takashe ni, haba da wani kafa kikesan intafi nagaji nagaji yinwa nakeji ko ran dunan dake chikin gidan nan fa bamugama chikawaba barema har musa na dabbobi ta karisa maganar kamar zatayi kuka, hiyana zatayi magana sai sukaji magana ta bayan su da sauri suka juya gaba ɗayan su har suna haɗa baki wajen chewa "inawuni yaya bello "lfy me kukeyi anan da man'gariban nan " ruwa muke ɗiba wa inna diyana tabashi amsa, "to ya kamata kutashi kutafi gida tunda kunga man'gariba ta kawo kai ga dajin nan da machizai, ina ruwan naku in taya ku ɗauka zuwa chikin gari, hiyana ta nuna masa kofin dake hannun ta tache gashi nan "to yau kuma da kofi kuka koma debo ruwan ne ina boket na ɗiban ruwan naku, da sauri diyana tace buba ne ya fasa mana boket, inna kuma tache mukoma debowa da kofi, girgiza kai bello yayi yana faɗin kuchigaba da hakuri kuna addua inshaa Allah, Allah zai kawo muku mafita amma dai yanzu kutashi kutafi gida
"da kyar diyana tamike daga zaman datayi yaya bello yayi gaba su kabi bayan sa tafiya suke kamar babu jini ajikin s,Juyowa bello yayi yana faɗin "ga gyada ku karba kuchi yanzu na chiro a gona yayi maganar yana mika musu ledar gyaɗan dake hannun sa chikin ladabi hiyana ta ansan musu gyadar tana faɗin mun gode murmushi kawai bello yamata batare daya amsaba ya juya ya chigaba da tafiya,suma suka chigaba da tafiya da kyar da kyar har suka fito chikin gari, bello ya nufi gidan sukuma suka tsaya a kasar bishiya mangoron kofar gidan nasu, suka fara chin gyaɗar da yaya bello yabasu

kinsan me hiyana naso ache gyadar nan dafaffache "au yanzu diyana hakanma baki godewa Allah ba karki manta fa tun safe fa ba abun da mukachi, kuma babu wanda ya tausaya mana yabamu wani abu dan kin'samu yanzu yaya bello yabamu gyada shine zaki waniche da dafaffache koh, to kije kidafaɗin, in bazaki iyachi hakaba sai kibari dan bawanda yamiki dole "aa hiyana abun ae bafaɗa bane kawai daga faɗin ra'ayi na "wan nan ba ra'ayi bane diyana rashin godiyar Allah ne kawai, kuma kullun ina faɗa miki kirinka godewa Allah a duk yadda kika samu kanki "to kiyi hakuri hiyana nayi kuskure alhadulillah Allah nagodema dakaba mu abun da za mu sa abakin mu "to kokefa yanzu naji magana "la hiyana kingafa kamar lamrat che ke zuwa diyana tafaɗa tana ɗan murmushi " da sauri hiyana ta juyo tana kallan inda diyana ke nunawa "itache wlh mujirata ta karaso sai mushiga

Please Login or Register in order to submit comment