Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mutumin ya bayyana wanna zeyi shekaru 38, cikin son daidaita yanayinta tace

"nagode bawan Allah"

"a'a babu komai ranki ya dade, dama sako ya aiko ni dauka yace ya manta ta adakinsa".


"ok toh je ka daukan masa"

tana ganin fitarsa ta zari hijab kana ta lallaba ta fito, tana fitowa haraban gidan ta daidaita nutsuwarta kana ta nufi bakin get, masu tsoron gidan na nan, duk da atsorace take domin bata sani ba ko alhajin yasanar dasu kada a barta ta fita? tana daf da isa bakin gate taji maganar daya daga cikinsu, cak ta tsaya jitayi yace
" hajiya bari a kaiki amota"
ajiyar zuciya ta sauke a boye kana tace "a'a barshi kawai, inason mika kafata ba nisa zanyi ba"... jinjina kai yayi alamun gamsuwa kana ya koma bakin aikinsa.

cikin gudu gudu sauri sauri ammi ke tafiya yayinda take fatan kada ta hadu da alhaji, sosai take sauri har tayi nesa da unguwar maraba ta fada unguwar masaka batareda ta sani ba, horn take taji abayanta gaba daya ta rude tama kasa motsi har motar ta bugeta... cikin sauri mutanen motar suka fito da sallati abakinsa macen ce tadago kanta tana fadin sannu! cikin zaro ido hadi mugun mamaki tace "Rahilat!"
"nadeem kanwata ce rahilat, kataimaka min kana ta mutu....


(ku cigaba da bina dan jin yadda zata kaya, shine, Abrar harma da ammi zasu kubuta ahannun alhaji Shettima? kuma su kwaro na samun nasaran gano abrar? shin wani yanayi ammi zata kasance idan taga yayarta? ya alhaji shettima zeyi idan ya fahimci ammi bata gidansa, sannan wani mutum ne ya taimaki ammi meye kuma alakarsa da alhaji shettima? shin mummy na amincewa da auran Aaban da Abrar? amsarku na nan duk cikin littafin mijin ammina, just be patient zan warware muku zare da abawa).😉👌



SHARE✔
COMMENT✔
VOTE✔
EDIT❌

Noor Eemaan✍☺

zaku ji ni gobe in sha Allah, son so my people😘
✨MIJIN AMMINA NE SILA✨
(A heart touching story)

ELEGANT ONLINE WRITER'S📚✍

✍written by noorEemaan

page 35-36

cikin madaukakin mamaki shima Nadeem ya kai kallonsa zuwa gareta, tabass wanna rahilat ce, duk da ta kara shekaru akan d'a sai de tayi rama, ta wani bangare kuwa yaji dadi da Allah ya kaddara saduwarsu, domin matarsa bata da damuwa kullum sai na tilon kanwarta da yarta, cikin sauri suka saka ta a back seat kana ya bawa motar wuta...

cikin motar ya kalli matarsa dake kuka yace "kiyi hakuri, in sha Allah zata farfado ba wani bugewa mai yawa tayi ba, dan haka zamu kaita gida mu kira doctor ya bata taimakon gaggawa" jinjina kai tayi yayinda hawaye ya cigaba da zuba a idanunta...

bayan sun isa gidan, direct part dinsu suka yi da ita, yayinda Nadeem ya kira family doctor dinsu, cikin mintuna kalilan ya iso, taimakon gaggawa ya bata kana ya daura mata trip hadi da basu tabbacin normal zata farka in sha Allah, godiya mai yawa suka yi masa kana ya fice...


da misalin karfe shida'n yamma ammi ta farka, a hankali ta fara bude idanunta, ganinta a wani hada'ddan bedroom ya dan tsorata ta ahankali komai ya shiga dawo mata har hatsaren data yi, hawayen tausayin kansu ne ya zubo mata, ita yanzu ko wani hannu ta fada kuma?... tana cikin wanna tunanin ta ji ance "sannu Rahilat, kin tashi ya jikin?" ware ido ammi tayi cikin sauri, jin muryan da bazata taba mantawa da ita ba, murza idanunta tayi domin tabattar da abinda ta ji kuma ta gani "yaya Raheenat! kice nake gani ko gizo idanuna ke min"
ammi ta fada cikin muryan mamaki, murna, hadi da kuka...

"nice Rahilat kanwata, nice nan a gabanki, ga yaya Nadeem nan ma" yaya Raheenat ta fada tana nuna Nadeem dake gefe yana kallonsu, yayinda kwalla ta cika idanunsa.

"yaya nadeem!"
ammi ta kira shi, sai kuma ta fashe da kuka tana rungume yayarta, ita ma yaya raheenat kukan take, kukan murnan ganin tilon yar'uwarta.

son dau tsahon lokaci suna kukan, kana Nadeem ya rarrashesu suka yi shiru, yaya raheenat na shirin yin magana suka ga an turo kofar, wani magidanci mutum ne me kama da yaya nadeem da wata mata agefensa da alama matar wanna magidancin ne, sai wani kyakyawan saurayi black beauty daga bayansu, sallama dauke a bakinsu bayan su ammi sun amsa, wanana magidanci yace

"Munji shigowarku tun da dadewa Nadeem, sai kuma bamu kara jin motsinku ba shiyasa muka leko muga ko lafiya?".

"hmmm yaya alkasim yau dai Allah ya hada ni da kanwata Rahilat" yaya raheenat tace cikin murna.

"babban magana matar magidancin nan ta fada ke ce mu zauna maganar babba ce"
ta fada tana kallon ammi.

"ai kuwa dai" yaya raheenat ta fada.

bayan sun zauna, da gaisuwa daya wakana a tsakaninsu yaya Nadeem yayi gyaran murya hadi da cewa "da farko zamu so sanin meye ya kawo ki garin abuja, ina kuma sajeed da Abrar? amma kafin nan bari na gayamiki silan namu zuwan abuja...

"TUNA BAYA"
Wanna sunan shi yaya alkasim yayana ne wanna kuma matarsa ce anty ni'imah wanna yaronsu ne sunanshi Adam, yayana ya kasance babban kasuwa anan garin abuja, tun a cameroon ya sha zuwa akan na dawo nigeria amma naki, acewa na, nafison zaman kasata bayan wasu shekaru ya sake dawowa akan na dawo nigeria domin girma ya fara kama shi ga kuma company's dinsa na bukatar wani daze tsaya a madadinsa, ga kuma dansa adam na yin nashi aikin so baya da lokacin kula dana mahaifinsa, da taimakon yayarki dai na amince zan dawo, anayi gobe zamu tashi muka fara sauka niger domin yimiki sallama, sai de muna shigowa gate din gidan muka hadu da mahaifiyar sajeed wato surikarki, take tafara zagi hadi da ci mana mutunci, bamu yi zuciya ba muka bata hakuri akan sallama muka zo yi miki, amma matar nan taki barinmu shiga ita bata son dangin matsiyata suna shigowa gidanta, kema kina daf da barin danta da dai sauran maganganu marasa dadi haka, ganin haka yasa muka bata number akan ta baki idan kin kira mu zamuyi miki bayyanin komai, tadai warci takarda bamu dai sani ba ko ta baki? cikin kuka ammi tace "wallahi bata bani ba"... jinjina kai yayi kana ya cigaba, haka dai muka nufo nigeria cikin rashin jin dadin ganinki da bamuyi ba, nan muka cigaba da rayuwarmu yayinda nake taimakawa yayana akan business dinsa, amma kullum yayarki bata da damuwa sai taki, bayan wasu shekaru muka sake komawa nijer a tunanin mu zuwa wanna lokacin ta sauko sai dai abun mamaki muna zuwa taki bari a budemana gate hadi dacewa ai baku gidan, bata san inda kuke ba, dan haka mu daina zuwa muna takura mata da tsiyarmu, hakika munyi matukar jin ba dadi, haka muka dawo muka cigaba da fawallawa Allah komai muna fatan wata rana mu hadu, gashi kuma Allah ya hada mu, alokacin da bamuyi zato ba wanna shine takaitacen abunda ya faru bayan rabuwarmu, dan haka munajinki yaya Nadeem ya karasa yana sakin ajiyar zuciya...

kuka dayayi matukar taba dukkanin zuciyoyinsu ammi ta fashe dashi yayinda ta ce "ni na rasa ta yanda zan fara bada labari bayan rabuwarmu, domin babu komai a ciki sai tarin, nadama, son zuciya irin tawa, a taikace basan tayaya zaku dauki labarin ba" ammi ta fada tana jan majina.

"haba Rahilat yaya zaki ce haka idan baki gaya mana ba tayaya hankalinmu ze kwanta, domin kafin motarmu ta bige ki bakya cikin nutsuwarki ki sani cewa babu dan adam daya wuce kuskure a rayuwa, dan haka gaya mana kin ji kanwata" ta karasa cikin lallama.

wani majinan ammi ta kara ja yayinda ta fara basu labari tun daga mutuwar sajeed har izuwa korar da mahaifiyar sajeed ta musu, da zuwansu cameroon, da zuwansu nigeria haduwarta da alhaji Shettima har ma da aurensu, kukan ta ne ya karu tuno ranar da abrar ke sanar da ita cewa alhaji Shettima ya keta mata haddi amma taki amincewa, ajiyar zuciya ta sauke kana ta shiga basu labarin komai da komai babu abinda ta boye musu har izuwa yau din data kubuta a hannun alhaji shettima....

sallati suka sanya adakin gaba daya, yayinda yaya Raheenat ta shiga yiwa ammi fada sosai kamar zata kai mata bugu, kuka ammi take domin tasan ta cancanci fiye da haka, yaya Alkasim ne yace "yi shiru haka raheenat fada baya gyara komai, a gaskiya kin tafka kuskure babba na rashin sauraran yarki, alokuta da dama yaya'yanmu kan zo mana da magana me muhimmanci, maimakon mu nutsu mu sauraresu da idon basira mu kuma yi bincike, sai muyi tsabanin hakan, yanzu ba lokacin mayar da magana bane lokacine daya kamata mu san hanyar da za mu bi domin sanin halin da yarmu take ciki... bayan mu samo yarmu zamu maka shettima a kotu domin ya sakeki, domin ba mijin aure bane, kuma koton ta bi wa Abrar hakkinta, mu zamu tafi sai gobe in Allah ya kaimu dan haka ki huta, ki samu bacci tunda bakya jin dadin jikinki" yaya Alkasim ya fada yana mikewa yayinda matarsa ta mara masa baya, shima saurayin nan mai suna Adam ya mike ya bi iyayensa cikin tausayawa halin da ammi take ciki...


"kai fa manu ka samu matsala, ina wanna yarinyar da oga ke nema ina wanna? sam basa kama kawai kaga mutum da matarsa kace ita ce, da alama dai yau ka sha da yawa" inji kwaro

kai dallah karka raina min hankali akwai wanda ya kai ka shan giya, ni yau kwalba daya kawai na kwankwada kuma karka manta wanna yarinyar nine na saceta daga dakin datake asibiti sosai na kalleta domin baby'n tayi min dan dai kawai kayan oga ce shi yasa na yi a'yane ka gane ai na daga mata kafa"

cikin fada shima kwaro yace "toh wallahi in dai mun karasa wajen ba ita muka gani ba sai na karta maka akuyanci"....

wani kallo manu ya aika masa kana yace 'eh naji muje idan kuma itace wallahi ni oga ze bawa tsoka mai yawa cikin share dinmu" balle murfin motar suka yi suka fito sai de sam ba alamun motar Aaban awajen....
"ka gani ko? kawai ka jaza mana asara da tuni mun huta da bulayin nemanta"
nan suka shiga zage -zagen junansu...

a hankali ya riko hannunta bayan ya daidai ta sayuwar motarsa a parking lot, ganin tana dingishi yasashi jin ba dadi har zuciyarsa, dole kafar tayi zugi ace kafar tagama tsami aka sake fama ta ai dole, a akan ma ya ga juriyarta, ahankali yake bi da ita har suka karasa cikin main falon ta dukkaninsu na zaune a palour, daddy na kallon news a tv yayinda Amal da Hanan ke danne-danne a tsadaddiyar wayarsu, mummy kuwa shiru tayi cikin tunanin sallamarsa ce ta katse musu abunda sukayi, amsawa duk sukayi, yayinda Abrar ta buyo abayansa, "abokina ina kuka je da safe haka"
k'ura mata ido yayi kana ya sauke ajiyar zuciya hadi da cewa "dad ashe tayi tardage da dadewa ban lura ba, har kafan tayi tsami shine na kaita wurin me gyara"
"ayya sannu Allah ya kara sauki"
ameen dad.
sanina cewa bata yarda da kowa yasa Hanan kin tashi daga zaunen tace cikin tausayawa
"sannu bestie Abrar Allah ya baki lafiya"

mikewa mummy tayi ta nufo su yayinda duk suka bita da kallon mamaki, abrar kuwa cikin tsoro ta kara shigewa jikin Aabaan....


Share and comment pls...✔✔
Edit❌❌

NoorEemaan ce

in sha Allah kafin magrib gobe zan sake muku sabon post.

✨ MIJIN AMMINA NE SILA✨
(A heart touching story)

ELEGANT ONLINE WRITER'S✍📚

written by Noor Eemaan✍😊

Page 37-38

Mummy bata damu da yanda taga Abrar na gudun ta ba, ta kamo hannun Aaban tace "son na yarje mana auren ta, amma akan dalili daya tak, matukar ta dawo hayyacinta yanayin nutsuwarta be mun ba toh dolenka ka kara aura, kasani cewa babu wata uwa a duniya komai lalacewarta dazata so dan cikinta ya auri macen da bata tare da mutuncinta, amma na yarda da kaddara ina muku fatan Alkhairi" tana fadin haka ta sa hannu ta share kwallar daya zubo mata...

Murmushin da har jerarrun fararen hakoransa suka bayyana yayi kana ya bawa mummy wani Sumba mai tsayi a goshinta kana cikin muryansa dake bayyana halin zallan farincikin dayake yace

"thank you so much mum na yarda da sharadin ki"

tsalle hadi da ihun murna Hannan ta daka ta rungumi mummy cikin farinciki, mummy ma rungumeta tayi batare da tace komai "mummy ina me tabattar miki sai kin yabi halin Abrar da bakin ki is just a matter of time, but mummy please ki bani dama na fada muku dalilin daya sa Abrar shiga wanna halin"...

"Zanso jin hakan ko hankalina ze kwanta da wanna auran, amma ba ke nakeson ki gayamin ba, ita Abrar din nakeson jin komai daga bakinta"...

"but Mummy... bazata iya yin wani bayani ba, domin bata a cikin hankalinta yanzu" Hanan tace cikin damuwa.

"Nasani, zan jira ta samu lafiya, kuma matukar naji dalilinta be gamsheni ba, ko kuma da amincewarta hakan ya faru toh dole dana ya rabu da ita, domin yanmmata na irin haka da amincewarsu za'a keta musu mutuncinsu daga baya su fake da cewa fyade aka musu ko kuma kaddara ce ta fada musu".... Mummy na gama fadin haka ta bar wajen cikin yanayin da suka kasa ganewa, Amal dake cike da jin haushin amincewar da mummy tayi da aura ta bar wajen...

Daddy murmushi yasaki, murmushin so hadi da alfahari da matarsa domin yasan fadan da yayi mata ya yi matuk'ar shigar ta...

Yayinda su Aaban suka bi Mummy da kallon suna kuma saka ran zata sauko gaba daya musamman idan ta fahimci wacece asalin Abrar...

Daf da kunne daddy Aaban yace "dad please ka aura min ita da wuri, domin in kula da ita, gashi inason fitar da ita India a sati nan" yana gama fadin haka ya ja hannun Abrar suka bar wajen fuskar nan ba alamun wasa kai baka ce shi yayi wanna maganar ba"...

Dariya daddy yayi kana girgiza kai, tabbas soyaayya ko yace mace kan sanja namiji, be taba tunanin cewa Aaban ze iya wanna rudewar kan mace ba, amma adalilin ta har magana me dan tsayi take yi sabanin da, ze fara sanar da yan'uwansa duk da abun yazo a kurarren lokaci, amma zesa abuga kati tunda yau talata sai su sa ranar daurin auran ya kasance ranar asabar da Wanda tunanin ya mike domin yana da appointment da wani abokin kasuwancin sa nan abujan....

Sai lokaci Hanan tace "daddy me ya Aaban ke rada maka akunne dazu"

"Je ki tambayeshi mana, ya baki amsa" Daddy yace yana mata hararan wasa...

Zaro ido tayi tace "ni Daddy! ya Aaban ya balla ni"

Dariya daddy yayi sai yace "wato ni kika raina ko?"

"A'a Daddy kayi haku'ri " ta fada itama cikin dariya...

Daddy na fita ta haura saman Aaban domin so take ta taya shi murna sosai...

Zaunen yake a gabanta ya k'ura mata idanunsa kamar ko yaushe, yayinda fuskar'sa ke fitar da wani murmushi da shin kanshi be San yana murmushin ba, imaging kawai yake gata ta samu lafiya suna shimfuda soyayyarsu, a yau jinsa yake a farinciki mara mitsaltuwa, burinsa ya cika mummy ta amince yanzu fatansa daya Allah ya bata lafiya ya nuna mata zazzafan kaunar dayake mata...
Abrar kuwa sai wasa take da wayarsa ta juya ta nan ta juya ta can bata ma San yanayi ba...

Kallonsu Hanan ke yi kallon so hadi da murna, taji dadi da Abrar ta samu me sonta tsakani da Allah ba dan wani Abu daya gani a jikinta ba, ya kuma kasance yayan'ta ne ke mata wanna tsananin son, domin tasan halinsa kaf, tabbas Abrar na bukatar farinciki domin irin wandan'da suka fama da irin wanna kaddarar na bukatan abokin rayuwarsu ya kasance mai son su fisabilillah ba dan wani abu nasu ba, saboda kaucewa wulakanci, amma idan ba haka kullum suna cikin damuwa kadai'ci Wanda ze cigaba da hargitsa kwakwalwarsu, za kuma su dinga ji ajikinsu tamkar sun bambanta da sauran al'ummah duniya... Ajiyar zuciya me tafe da k'walla Hanan ta saki kana ta karasa wajansu.

"Ya Aaban"... ta kira sunanshi

"Yes little" ya fada yana dan waiwayo wa domin Sam be ji shigowarta ba.

"yaa Aaban am so happy for you, can't wait in ga ka auri bestiena"...

Murmushi ya sakar mata hadi da cewa
"soon little, soon in sha Allah"

"Murmushi farinciki itama ta sakar masa, hannun Abrar ya kamo yace " little kin tuna wanna zoben?"

Dan waro ido tayi tace "yes! ya Aaban wanda ka siyomin ne, be mun daidai ba, amma how comes ya zo hannu bestie?"...

"Good" yace kana ya sauke ajiyar zuciya ya cigaba "da ring dinnan hadi rigar jikinta kinsani ke na siyo wa, amma ina yawan manta rigar a asibiti, nina sanya mata, wanda bansan dalilina na yin hakan ba, ashe matsananci sonta ne ya kama ni..."

Dariyar murna hanan keyi, ba shakka Abrar ko tace soyaayar Abrar na neman sanja ya Aaban, yau ya Aaban ke bata labari, ta fahimci duk rashin son maganarsa amma idan Abu ya shafi Abrar ya kan daure yayi magana.

"Amma ya Aaban nayi mamaki sosai ace duk shekarun nan muna tare da Abrar amma ban taba lura da ring din hannunta ba? Ikon Allah" tace tana jinjina kai sai kuma ta motsa wajen Abrar sosai kana cikin wasan tsakona ta kamo hannunta hadi da cewa "gaskiya bestie ciro min kayana da ring dinnan ai kin mora ya isa haka"...

Abrar ihu tasa ta shiga dukan hannun Hanan hadi da turo dan tsut din bakinta kai kace Hanan din yankar ta tayi, idanunsa alumshe yace " I swear Hanan kika bari hawayen decent one ya zuba ko kadan ne sai kinyi kukan kema"...

Dariya hadi da rufe baki Hanan tayi tana barin dakin, dama tsokanarsa tayi so take taji abunda ze ce.

"Haba Mummy dan Allah ya zaki yi haka? ya zaki amince da auran wanna mad girl din, bayan bakya sonta da ya Aaban, ni wallahi banason zamanta a gidanan mummy so kike muji kunya dan Allah?"... Amal ta fada cikin zuga mummy.

'Hmmm Amal ya zanyi? Duk sun kasa fahimtata, ga Aaban na shiga damuwa duk adalilinta da dalilin kin amincewata ina lura da shi sarai, you no inason farincikin dana banason damuwarsa, ga daddy'nku is angry at me, idan ba haka nayi ba, kina tunanin hankalina ze kwanta ne Amal?"....

Turo baki Amal tayi cikin jin haushi, tana kuma fatan Allah yasa Abrar ta kasa cika sharadin mummy'n ayi waje da ita...


Bangaren alhaji shettima kuwa, yana zaune yana jiran aiken daya yiwa PA dinsa, yana zaune a office din sa yana aiki kai kace mutumin kwarai ne, kwankwasa kofar aka yi, ya bada izinin shigowa ganin tahir ne PA jikinsa yasa shi cewa
" yawwa tahir ka gani ko?"
"Yes yallabai ai baya boyayyen wuri kan gado na ganshi" tahir ya fada yana Mika masa cikin girmamawa...

Har tahir ya juya ze fita sai ya juyo cikin sauri domin so yake ya sanar da alhajin Shettima'n kila yayi masa kyautar ban girma.

"Yallabai ashe ka kulle madam a daki ka manta, dana je wallahi naji bugun kofa na bude mata" ya karasa cikin washe 32 teeth's (hakoran) dinsa...

Alhaji Shettima jiyayi tamkar an buga masa guduma, kana ya tsaya cak! Daga bude file din, take idanunsa suka yi jajawur, mikewa yayi ya zagayo daidai saitin inda Tahir ke tsaye cikin wata murya dake nuni da matsanancin fushi yace "Tahir ka bude mata kace?" Ya fada yana cakuman kwallar rigar Tahir din, cikin zaro ido tahir ya ce "eh na bude mata tace kai ka rufe.... Ai Tahir be kai aya ba alhaji ya bashi wani kyakyawan naushi kana ya shiga sauke duk wani fushinsa akan tahir din, sai dan kanshi ya sake sa hadi da cewa " wallahi yau zaka bar kamfanina, tunda aikin da ba'a saka ba kake yi, ka fita na sallame ka, zan turo maka kudinka na aikin rabin watan dakayi" yana fadin haka ya dau wayarsa yana kokarin kira....

"Yallabai ka taimaka min dan Allah ka rufamin asiri, ina da iyali da ya'ya ya zanyi ga rayuwa tayi tsada, ga samun aiki da wahala, bazan kara ba ka taimakeni dan Allah!!!" Tahir yace cikin kuka me ban tausayi tamkar dan karamin yaro

Dago jajayen idanunsa yayi yana ya sauke su akan Tahir ko kad'an ya ki jin tausayin sa, duk da shi din abin tausayi ne, cikin wata murya dake nuni da yana daf da aikata komai yace "ka fita a office dina idan ba haka zan kasheka, zanyi iya kasheka TAhir, kasan asarar daka ja min kuwa? Toh kasani bazan taba iya dawo da kai ba, kai ko matsayin masu goge-goge bazaka samu a company'n SHETTIMA ba!" Ya fad'a muryansa har wani amsa amo take yayinda bakinsa ke kumfan bala'i ...

Sum sum Tahir ya juya ya fita ganin alhaji ya burkice tamkar wani sabon kamu, shi yanzu yazasu rayu da iyalansa shine damuwarsa da wanna tunanin ya bar company din....

"Hello kwaro kana jina inaso ku zagaya abuja da kewanta ku nemo.... Ai kafin ya karasa manu ya warce wayar yana cewa " alhaji da matsala fa, mun ga yarinyar nan, amma kwaro yaki amincewa ita ce da shegan mutsu bala'in sa, daga baya dai muka fito domin ganin ko ita ce mu kwamusheta, sai muka ga wayam motarsu babu alamarsu...

Cikin fushi hadi da fitar hayyaci alhaji Shettima ya buga wayarsa da bango, rigar jikinsa ya cire ya shiga fiffita da ita, duk da Ac daya cika office din amma jiyayi iska hadi da sanyi dayake shaka tayi masa kadan! Ya sani ammi ta gudu, sai kuma ya saurin cewa "a'a nasan bazata gudu ba, Rahilat na sona sosai" yar karamar wayarsa ya dauka ya kira security akan kada su bar ammi ta fita, take security ya sanar da shi "ai ta fice tun dazu alhaji"... Ihu yasa ya shiga wulli da takardun dake kan table, komai yazo ya kwabe masa alokaci daya shi yanzu ta ina ze fara neman uwar da yar.....


SHARE✔
COMMENTS✔
VOTE✔
EDIT❌


Tnx all da soyaayyar da kuke nunawa books dina, noorEemaan loves you all.💞

✨MIJIN AMMINA NE SILA✨

Written by NoorEemaan✍

ELEGANT ONLINE WRITER'S📚✍

Page 39-40

.......... Gaba daya jiyayi zaman office din ya ishe shi, company ya bari ya nufi gida kamar wani zautacce shi kadai sai surutu yake a mota, ai ranar gaba daya ma'aikatan gidan suma sun san oga baya cikin hayyacinsa, domin ya fita da mota yafi sau a kirga duk cikin neman su ammi daga baya ya dawo cikin gidan ya zauna cikin rashin sanin madafa, shi yanzu burinsa ya gansu domin daga uwar har yar yana bukatarsu domin suna da amfani agareshi ba kuma yaso asirinsa ya tonu a gari....


A yau asabar dubban jama'a suka shaida daurin auren AABAN ABDUR-RAUF MAI FATA TARE DA KYAKYYAWAR MATARSA ABRAR SAJEED. Aaban dake sanye cikin tsadadiyyar gezna fari da aka yi masa dikin babban riga, tsadadiyyar zaran dinki ya kasance golden, hula da talkaminsa sau ciki suma kalan shigarsa ne, hannunsa kuwa rolex watch ne me tsada gaske.... yana jin an shafa fatiha wani sanyin dadin ya shiga ratsa jini da sokan jikinsa, kana kallon sa zaka hango wani shirtattacen murmushi shimfu'de kan kyakyyawan fuskarsa,... Bayan jama'a sun fara watsewa ya nufi wurin daddy dake ta gaisawa da jama'a, a bazata daddy yaji Aaban ya rungumesa hadi da furta
"nagode dad Allah ya kara girma"
Bubbuga bayansa daddy yayi hadi da cewa "godewa Allah son, Allah ya baku zaman lafiya"
"Alhamdulillah, ameen ya Rabb dad" ya fada cikin muryan dakeson bayyana yanayin farincikin dayake ciki...

Daga wurin daurin auren reception aka wuje direct a wani hada'dden hall, wanda kuma ya kasance zallan maza ne a wurin, Aaban Allah-Allah yake a tashi ya je ya ga decent one dinshi, domin arufe take adakin wanda hakan ya kasance umarnin mummy ne wanda shi be san dalilinta nayin hakan ba.... (Mummy kuwa tayi haka ne domin kada ta fito mutanen biki su ganta ta, ta rasa amsar basu)

Da misalin 12 na rana aka watse daga taron babu bata lokaci ya nufi gida, domin burinsa kawai ya jita a kirjinsa, yaji wannan feelings din na kasancewarta halalinsa, musaddiq ne ya tuko su a tsadaddiyar motar Aaban di'n da yau ya fara hawanta, shi musaddiq din dariya hadi da mamakin abokinsa yake domin be taba tunanin cewa ze so wata ya mace aduniya haka ba, domin baro-baro ya karanci zumudi

Please Login or Register in order to submit comment