Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ayanda aka mata fyaden nan zai san bada amincewarta aka yi ba, dafe saitin zuciyarsa yayi yayinda wani matsanin kaunarta ke ratsa bango da tsokar jikinsa.... har ya fara taka benen domin zuwa side dinsa sai kuma ya tsaya cak hadi da dafa kansa
"opphs, mummy na manta ina tareda patient (mara lafiya) dana hadu da ita ahanyar dawowa na"

"salati mummy tasaki tace "yanzu son kana tareda patient amma kuma baka bata taimakon gaggawa ba, tukunna ma meyasa baka kaita hospital ba?"

"mum" yafada amarairace kana yace"saboda dare yayi shiyasa ban koma asibiti ba"...

"so where is she now?" mummy ta tambayeshi.
"tana cikin motana" ya bata amsa ataikace.
"muje toh, kada wani abu yasamu yar mutane"
cikin tafiyarsa dake nuna lafiyayye namiji ne shi ya mara mata baya, tana kwance kamar yanda ya ajiyeta, sake daukarta yayi ya dora ta akirjinsa yayinda mummy na biye dasu, duk da tazo ganin fuskarta amma gashinta ya rufe domin babban mainson dinsu awadace yake da fitilu kamar rana...

ganin yana kokarin kwantar da ita akan kujeran falon yasa mummy saurin cewa "son ka kaita dakinka mana, ina tunanin kayan aikin na dakinka, yakamata ka hanzarta tunda tana bukatar taimakon gaggawa, nidai Allah ya tsaremu yasa mutum ce, domin duniya tazama abun tsoro yanzu" mummy ta fada tana daga idanunta sama alamun roko ga rabbu sammawati.

kalaman mummy na karshe yaso sashi dariya matuka, saidai shi ba mai yawan dariya bane, "babu komai in sha Allah mum, just relax"
yafada domin kwantar mata da hankali,
"hmmm ameen son" mummy tasaki ajiyar zuciya.

tamkar babu komai rugunme a hannunsa ya shiga taka benen cikin sauri, bayan shigarsa dakin ya kwantar da ita akan gadonsa yayinda ya shiga bata taimakon gaggawa... bayan ya gama yi mata abunda yadace, ya koma kan sofa ya zauna yana jin sa atakure domin ya saba rayuwa shi kadai a dakin, wanka yayi a bathroom dinsa hadi da sanja kayan jikinsa zuciya jallabiyan maza maroon color duk a toilet yasanya kana ya fito ya kwanta kan sofa ya dan samu bacci kafin akira asuba...

ana kiran sallah farko ya bude idanunsa dake ciki da gajiya, ya sauke su kan abrar dake kwance kamar yadda ya barta, yayinda har yanzu fuskarta ke a rufe da gashinta, banda kirjinta daya ga yana bugu da sauri sauri dazai ce mataciyya ce saboda yanda take kwance ko yatsarta bata motsawa...

ahankali ya sauke kyakyawan kafafunsa kasa ya nufi toilet yayi wanka hadi da daura alwala ya fito, nafiloli yayi kana ya nufi massalaci. Sai karfe shida da rabi ya bar masallaci dake cikin mainson din nasu ya nufo cikin aihinin gidan...

workers ya gani to ko ina suna ta aikinsu, yayinda suke ga gaishe shi cikin girmamawa, part dinsa ya koma still kan sofan ya koma ya kwanta, "ka...ka taimakeni kada ya sake samun galaba akaina, domin idan hakan ya faru zan mutu!!!" ya tuno kalaman abrar, ko waye yake biyayarta? ya aiyana aransa yana sake kallonta, dan tabe bakinsa yayi kana ya lumshe idanunsa bacci yayi awan gaba dashi...

takwas dot yafarka ya bude wardrobe dinsa yana bata rai, shi ala dole yana ataruke komai yanzu a toilet zai dinga yi, kananun kaya masu kyau da tsada ya dauka, ya dau mintuna 30 kana ya fito tsaf dashi, direct part din mummy ya nufa gaba daya suna zaune kan dining table mummy, amal, hanan, tundaga nesa su duka ke kallonsa domin kaunar dasuke matukar yi masa saboda ya kasance tamkar sanyin idaniyansu ne, bayan ya ja kujera ya zauna yace "mum good morning"
"morning dan albarka mummy tace tana shafa sumar kanshi.
"ya aaban ina kwana"amal da hanan suka hada baki wurin fadin hakan, jinjina kai yayi alamun amsawa, sanin halinsa dasukayi yasa basu damu ba.
"son mezaka ci" mummy ta tambayesa.
"mum only black tea" ya amsa
"no son kahada da wani mana, ni har mamaki nake yanda baka jin abunci kuma baka ko ramewa" hanan da amal suka yi dariya kasa kasa, domin kada ya juyosu.
Dafe kansa yayi kana yace " da soyayyen kawai" girgiza kai mummy tayi ta zuba masa hadi dire masa gabansa.
"au son na manta ina patient dinka ta tashi kuwa"?
"noo mummy amma zata iya farkawa a kowani lokaci"... jinjina kai tayi alamun gamsuwa, yayinda amal da hanan suka kalli juna alamun tambaya, yana gama breakfast yayi sallamawa dasu ya nufi hospital...

suna ganin fitarsa amal tace"mummy wacce patient kike magana akai?"
ataikace mummy tayi musu bayani, har hanan tace zata je taganta mummy ta hanata hadi da cewa "kinsan yayanku bayason shishigi ko?"
"toh" tace kana ta fara kokarin kiran wayar ammi domin yau tayiwa abrar alkawarin zuwa, sai dai duk kiran datake yi ba'a dauka, jitayi ba dadi, gashi so take ta kara tambayan address din domin ta manta, fatan ta Allah yasa abrar na lafiya....

"AMMI"
kokarin riketa, domin matukar ya bari takai kasa komai ze iya faru da ita, sai lokaci ammi tafara dawowa nutsuwarta, idanunta kuri kan alhaji shettima tana masa kallon tsoro, kallon matsanincin mamaki, still hawaye na zuba idanunta, ashe abunda tilon yarta mafi soyuwa aduniyarta take fada gaskiya ne? ashe alhaji ke cutar da diyarta duk tsayin shekarun nan bata sani? ashe da gasken ne shi ya ketta mata haddi, yayi mata fyade bata sani ba? ita kuwa wacce irin uwa ce data kasa gane halin da diyarta take ciki? akan namiji, namijin ma mugu azzulumi ta banzantar da yarta, akan namijin karon farko arayuwa ta dau hannu ta mari yarta. me duniya zasu ce akanta? ya akayi takasa gano hakan sai a kurarren lokaci, take duk abubuwan da abrar ke gayamata hadi da canjin data dinga gani atare da ita ya shiga dawowa kwakwalwarta, haba shiyasa tun ganin farko da diyarta abrar tayi masa ta tsaneshi ashe shine silan rugujewar rayuwarta, take wani kuka ne ya kufce mata, kana tayi masa wani mugun hankada ta shiga dukanshi to ko ina tana cewa "mugu azzalumi sai na maka ka akotu, kotu ce zata raba mu da kai dan kaga bamu da kowa akasar nan shiyasa ka cutar da yata hankalin ka kwance, to kasani Allah ne gatanmu zaka ga yanda zaka wulakanta aduniya, natsaneka, tsana mafi muni, kuma basai gobe ba yanzu nakeson ka rubuta min takardan saki domin zama dakai gwara zama da bunsuru, alhaji shettima daya ji azaban duka ya riko hannunta duka biyun ya fara kokarin janta domin kaita dakinta, sai kokarin kwace hannunta take amma takasa domin karfin ba daya bane, gabadaya ya cike da gumi kamar wanda ruwan sama yayiwa duka, ko maganar ma ya kasa bai taba tunanin akwai abunda zai daga masa hankali haka ba, bai yi tunanin cewa haka komai zai gwabe masa har haka ba, dakin ya yi saurin cillata kana ya rufo dakin har da sa key ya rufe, bubbuga kofar ammi take tana cewa "ka bude mun mara imani inje in nemi yata " haka ta cigaba da cewa tana bubbuga kofar da dukkanin karfinta...
fita alhaji shettima yayi haraban gidan gate yagani arufe, hakan yasa shi sanin cewa bata nan ta fita ba, domin be taba kawowa aransa cewa zata iya taka lada ta dira ta kasa ba, ma'aikatan gidan ya tasa gaba daya yace a bazama nemo masa abrar ....


atayani share dan Allah da mazonsa🙏

comment and vote ✔


insha Allah zan fara turo muku littafina mai suna RAYUWAR FAHEEEMAH domin ba kowa yasanshi ba, kasancewar sai dana document dinsa sannan nayi sharing

noor Eemaan loves you all💖


https://chat.whatsapp.com/FEfWeTiufpk96my8yNBeaM

✨MIJIN AMMINA NE SILA✨

written by noor Eemaan
wattpad:NoorEemaan

page27-28

cikin sauri ma'aikatan suna shiga duba ko wani lungu da tsakon gidan, shima alhaji shettima ba'a barshi abaya ba har da shi ake neman nata, bayan sun duba ko ina basu ganta ba suka sanar da alhaji cewa bafa ta cikin gidan, cikin wani tashin hankali yafara tunanin ina taje? can sai ya kalli mai gadi babu alamun wasa yace
"kodai ka bude mata gate ne?
murya na rawa mai gadi yace "wallahi tallahi alhaji ban bude mata gate ba" domin shi kam be shirya rasa aikinsa ba...
"Toh acikin ku waye yaji fitar ta?"
shiru duk sukayi sai daya daga ciki yace

"ni dai alhaji ina kwance adaki naji an diro kasa, amma ban leka ba"

Cikin takaici alhaji shettima yace kwada masa mari yace"shashashan banzan da wofi meyasa baka lekan ba?" domin alhaji shettima ya fahimci cewa lada ta hau ta dira kasa, tunda me gadi be bude mata ba domin babu wata hanyar agidan, adaran nan yasa dukkansu banda megadi baza nemanta, shima mota ya hau ya bar gidan...

Duk inda suke tunanin zasu ganta sun duba amma ko alamarta babu, har karfen bakwai din safe suke nemanta, dasuka gaji kawai ya kira su kwaro yace duk inda suka ga abrar su kawo masa ita tunda sun santa ya kuma yimusu alkwarin basu kyauta me tsako, domin shi be shirya asirinsa ya tonu ba, domin ana ganin mutuncinsa agarin na abuja sosai, da wanda ya nufi gida...

Bangaren ammi kuwa gaba daya ta fita a hayyacinta kuka take sosai, kukan nadama akurarren lokaci, "wani hali abrar take yanzu?" shine tambayar dake kai kawo aranta, gashi tana rufe balle tasamu ta fita ko Allah ze sa tayi dacen ganin yarta, tana cikin wanna tunanin taji an dan bude kofar hadi da tura mata plate din abinci kafin ta taso an rufe kofar...

"Waye nan? wanene dan Allah abude min inje neman yata"...

dariyar alhaji shettima taji yace "hajiyata ki kwantar da hankali, ana kan nema miki yarki, sai dai kisani idan an ganta wani gidan daban zan kaita in cigaba da lasar zumanta domin bazan iya barinta ba, za kuma ki cigaba da zama anan dakin har a ga abrar, karki damu zan dinga turo miki abinci kullum"...

cikin kuka ammi tace "Allah ya isa tsakanina da kai, sai ka wulakanta aduniya, idan ka isa ka sake ni na bar maka gidan ka, domin gidanan tamkar kuzurmin daji haka nake ganinta"

"hhhh hajiyata kenan ina raga miki ne saboda son hadi da sha'awar da nake wa abrar daba haka ba... sai ya ja kwafa hadi da barin wurin.

da misalin karfe hudun yamma zaune suke a babban falon gidansu su duka ukun yayinda mummy ta kalli hanan dake faman danna waya rai abace tace "ke kam hanan me damuwarki ne"
"tambayeta mummy ta damu mutane da tsaki" amal ta fada tana harararta.
turo baki tayi tace "mummy ki raba ni da anty amal"
"ke ni ba wanna na tambayeki ba, meke damunki?"
"number amminsu abrar nake ta kira baya shiga, gashi inason zuwa gidan".

mummy na shirin bata amsa suka ji wani razananan ihu da sautin sa ya karade duk ila'irin mainson din nasu, kallon kallo aka shiga yi tsakanin mummy, hanan, amal, yayinda suka mike atare suka nufi bangaren aaban domin tabass ta nan wanna ihun ke tashi, suna kokarin hawa matattakala sai suka ji dariyarta na tashi sosai can kuma sai kuka gaba daya suka rugo aguje suka dawo falon har da mummy kuwa😅 kukan ne ya shi gaba da tashi yayinda suka zauna jugum cikin rashin sanin abunyi, dadinta daya yau aaban da wuri ze dawo, take ciwon abrar ya fadowa hanan, domin irin ciwon abrar ne wanna patient din ya aaban keyi amma nata be kai wanna ba, sun kai awa daya awanna halin kana suka ji tsayuwar motar aaban ajiyar zuciya suka sauke, yana sallama yabi su da kallon mamaki se dai be tambaya ba, be kuma nuna afuska ba, "yawwa son welcome home, ga patient dinka can tana kuka hadi da dariya kaje ka duba awani hali take ciki"..

jinjina kai yayi alamun "toh" duk da yayi mamakin abunda tace toh kenan meye matsalarta? ya aiyana aransa yana nufan side din nashi, sai duk suka bara masa baya, suna zuwa kofar dakin suka tsaya domin har yanzu dariyar hadi da kukan na tashi.

ko dar be jiba ya shige dakin, hannu yasa ya rike kugunsa, ganin yanda gaba daya ta sanja masa kamanin daki, tamkar dakin mahaukata, kallonta yayi yaga gaba daya gashinta ya kara hargitsewa ya dawo gaban fuskarta duka wanda hakan yasake rufe face dinta.

cikin tafiyar sa ta burgewa yakarasa wajenta hadi da karbe wani kwalben turarensa data fasa, g jini ahannunta da alama ta caka wa kanta, tana jin ya karbe ta fasa wani ihu hadi da bubbuga hanunsa sai ta dau pillow ta shiga dukkansa dashi, hannunta ya damko kana cikin husky voice dinsa yace "will keep the hell out shout"
kamar kuwa taji tayi shiru din, sai kuma ta fara kyakyale dariya har da kifewa kan gadonsa, wasu allurori ya hada mata yayimata babu jimawa kuwa bacci yadauketa, take ya fahimci matsalarta, duk da shi karatunsa ba bangaren kwakwalwa yayi taba, zai yiwa abokinsa musaddiq magana ya zo duba aihinin matsalan domin ya tabattar...

kallonsu mummy yayi yayinda ya hango tausayinta a idanunsu, domin kwantar musu da hankali yace "kada ku damu mum nayimata allura xata dau lokaci bata farka ba"
"toh son, bazaka ci abincin ba?"
"no mum sai dare"
"ok ka kula da kanka please, ko hanan ta gyara maka dakin, tunda bakason masu aiki suyi maka"
"noo mum, i will do it my self tnx" yafadi haka yana bata peck (sumbata) a kumatu.
murmushi tayi kana suka bar wajen

bayan ya cire rigar suit dinsa, ta cikin data kasance fari ya tattare hannun, nan ya shiga aiki, komai data hargitse ya mayar da ita muhallinsa yayinda wadanda suka fashe ya zubar a waste bin( kwandon shara) kana ya share dakin ya goge take dakin ya dawo hayyacinsa, wanka ya shiga bayan ya gama yasa kananun kaya marasa nauyi ya dawo kan sofa, sai kuma ya mike ya bude wardrobe dinsa ya ciro rigar abrar dinnan data yayyage, ya kwanta kan sofa ya bar rigar kan fuskarshi yayinda yake shakan natural body scent dinta dake sa masa nutsuwa, tunaninta yake as usually yayinda kaunar ta ke karuwa aransa, kiran sallah magriba ne ya katse masa tunaninsa...

washegari yana off hakan yasa shi kiran doctor musaddiq abokinsa, wanda ya masa alkawarin zuwa da rana tunda yana half day ne, kamar yadda ya alkawaranta sai gashi da rana da kayan dazai mata gwaji domin daman aaban yayi masa bayanin yanayin ciwon nata, bayan ya gama duba ta, suka dawo falon kasa, nan ya shiga yi musu bayanin ciwonta tamkar dai yanda likitan nan a cyprus yayiwa hanan sai dai bambamcinsu shine, wanna karon ciwon ya sake ninka na baya... sun yi matukar tausaya mata, ga hanan datake wani tunanin na daban, domin irin ciwon patient din ya aaban shi abrar ke fama dashi
"ya Allah kasa abrar na cikin kwaciyar hankali" tafada cikin kaunar kawarta...

"bayan sati daya"
alhaji abdur-rauf ya diro kasar nigeria domin yayi hutun daya dauka tsayin wata biyu da iyalansa domin ba karamin kewarsu yayi ba. gaba daya gidan ya kacame da murna daga masu gidan har yan aiki, domin daddy shi kowa nasa ne, har dare baki na zuwa yimasa sannu da zuwa, hakan yasa be zauna sun tattauna da iyalansa ba,...

sai washe gari daya kasance sunday suna zaune dukkansu suna hira, abun birgewa daddy ya zauna cikin iyalansa suna ta raha da nishadi, wanda su mummy sunyi missing wanna kyakyawan halin nasa, hajiya mummy baki yaki rufuwa daddy ya dawo lolz😜
"mummynsu jiya kin fara min magana akan abokina, (aaban, domin da haka yake kiranshi tun yarinta) tukunna ma yana ina? wai har yanzu baya shiga jama'a? anya bake ya yayo ba kuwa?" yafada cikin zolaya yana kallon mum, dariya sukayi kana mummy tace "ai daddy wanna abokin naka Allah kadai yasan inda yasamo wanna halin nashi, sanna zan so yana nan sai mu hadu muyi maganar gaba daya alright bari na kira shi" daddy ya fada.

bangaren aaban kuwa yana zaune idanunsa a lumshe yana tunanin decent one dinshi, jin motsi yasa shi ware idanunsa abrar ya gani zaune tana kokarin tashi, kara rufe idanunsa yayi yana tunanin kai ta asibitin kwakwalwa domin aduba ta duk da besan ya kalar fuskarta yake har yanzu ba, amma yaji yana da niyyar taimaka mata.

sake ware idanunsa yayi adalilin ringing din da wayarsa keyi, karawa yayi akunne bayan ya daga yaji ance "abokina kazo falo muna jiran ka yanzu"
"ok dad" ya amsa ataikace

yana zuwa ya zauna akusa da daddy yayi shiru idanunsa alumse, murmushi mai sauti daddy yayi kana yace
"mummynsu ina jinki?"
"daddy daman akan maganar auren aaban ne, yasamu matar aure, shine nakeso anema masa auranta, yarinyar dai kawar hanan ce, duk da bamu gama sanin address din su ba, amma na na yaba da hankalinta kwarai... hanan na shirin tambayar wacce kawar tata, suka ji dariya hadi da kuka na tunkarosu yayinda cikin sauri take taka benen domin saukowa gaba daya suka juyo suna kallonta banda aaban da idanunsa ke alumshe, daddy da fuskarsa ya nuna mamaki domin besan da zamanta cikin gidan ba,,, "wacece wannan" daddy ya tambaya.
nan mummy ta shiga bashi labarin komai da komai... cikin tausayawa yace "Allah ya bata lafiya, sai ya kalli abaan yace abokina da an kaita asibiti ayi aikin ko za'a dace ko?"
"eh dad abinda nake shirin yi kenan"
"toh masha Allah" daddy ya fada.
daddy yace "wacce unguwa suke, indai an san unguwar, toh sanin gidan da sauki ai, mummy zata yi magana suka ga abrar da ta yi zaman yan bori akasa ta mike hadi da daura hannunta kan gwiwowinta kamar dai ruku'u, sai tasake dago kanta wanda hakan yasa gashinta mai uban yawa yin baya take fuskarta ya nuna, nan ta shiga bin ko wannesu da kallo sai kuma tafara zallan kuka mai ban tausayi, sai lokacin aaban ya bude idanunsa yasauke su kan beautiful face dinta kara murza idanunsa yayi domin tabbatarwa, cikin sauri ya mike kana ya tunkareta hadi da cewa
"decent one" yayinda hanan tace " bestie abrar kallon mamaki hanan da aaban suka yiwa juna, yayinda suka jefa su mummy cikin duhu...

share pls✔
comment✔
vote✔
edit❌

gaskiya comment dinku yana kadan, idan baku kara ba zan rage typing, domin baku bani karfin guiwan typing, tunda bazai yu in dinga typing domin faranta muku ace kuma kalillan ne zasu na comment ba

noor Eemaan✍
l

https://chat.whatsapp.com/FEfWeTiufpk96my8yNBeaM

✨MIJIN AMMINA NE SILA✨
(A heart touching story)

written by Noor Eemaan

page29-30

cikin madaukakin mamaki mummy tace "Aabaan Hanan kun san tane?" amma sam hankalinsu baya tare da ita musamman Aabaan daya ke jinshi cikin farinciki mara iyaka adalilin ganin Abrar, tabass baya ko tantama decent ce tsaya agabansa, agabansa ma cikin gidansu, duk da ta kara girma akan da, amma ko yana magagin bacci baze taba manta fuskartaba, dama all this while itace? amma ya kasa gane ta...

kusan lokaci daya suka karasa gabanta shi da Hanan, beyi tunanin abunda ze faru ba, beyi tunanin cewa akan be dace ba, shi dai burinsa kawai yasa ta a kirjinsa ko ze ji saukin ciwon sonta hadi da radadin rasata dayayi abaya...

cikin zafin nama ya manna ta a kirjinsa, yayinda ya lumshe ido yana jin saukin radaddin sonta a kirjinsa, cikin muryansa dake son bayyana rauninsa yace

"where have you been decent one? i so much miss you please stay with me ok?"

Abrar kuwa shiru tayi ta lafe akirjinsa sai faman raba idanu kawai take, kukan Hanan ne yadawo dashi nutsuwarsa, tace

"bestie Abrar daman kece? meyasamiki, yasake taba ki ne? dan Allah ki gayamin Abrar"... Abrar kara shigar da kanta jikin Aaban take hadi da boye fuskarta, kukan hanan ne ya karu domin ta fahimci ciwon Abrar yafi na da tunda har ta kasa ganeta...

cikin mamaki su mummy ke bin Aaban da kallon domin basu taba tunanin cewa ze iya wanna rudewar akan mace ba, macen ma mara cikakken lafiya, cikin wani sabon rudewan mummy tace "ba magana nake muku ba, nace kun santa ne!!!" mum ta kara fada a tsawace

sai lokacin Hanan tace "mummy Abrar ce fa, Abrar kawata damuka hadu a cyprus"

cikin sake daure kai mummy tace "ban gane ba, daman tana da tabin hankali ne?"

kuka Hanan tasa tace "mummy ba tabin hankali bane, my bestie is not insane matsananci damuwa hadi da firgici ne ya haddasa mata wanna halin datake ciki yanzu haka"...

mummy zata sake magana daddy yace "mummynsu duk ku zauna mu tattauna wanna maganar a nutse domin nima kaina ya daure, saboda ina mata kallon sani, kallon Aaban dake rugunme da Abrar har yanzu idanunsa alumshe daddy yayi, murmushi yayi dashi kadai yasan ma'anar yasa kana yace abokina zo ku zauna muyi magana"

sai lokacin yabude idanunsa dasuka sanja launin, yayinda yake jin zafin ciwonta, meyasa duk haduwarsu baya taba ganinta cikin yanayi mai kyau, yakuma fahimci wasu abubuwan daga maganganun Hanan, a hankali ya rabata da kirjinsa ya riko hannunta, saurin sake shigewa jikinsa tayi, be hanata ba, ya tafi da ita ahaka tana gefen kirjinsa kan kujera suka zauna yayinda ta shiga boye fuskarta tamkar me jin tsoron kada akamata.

Hanan kasa hakuri tayi tace "yanzu bestie na baki gane ni ba, nice fa Hanan"

Aaban kallon Hanan yayi yana cike da mamakin yanda har Hanan ta santa har haka, Abrar kuwa tsura mata ido tayi kana ta fashe da dariya hadi da dukan Aabaan tana masa alaman ya kalli Hanan, cikin rashin jin dadi halin datake ciki ya kama hannun datake dukansa dashi ya matse cikin nasa hannun kana ya dora hannunsa kan lips dinsa alamun tayi shiru, kallonshi tayi sai kuma tayi shiru kamar wacce ta fahimci maganarsa...

gyaran murya daddy yayi yace " Mummynsu idan na fahimce ki, wanna Abrar itace kikeso Abokina ya aura ko? shin baki taba haduwa da ita bane?"

cikin mamakin da be gama sakin mummy ba tace "daddynsu haka maganar take, domin Aaban ya shiga mayuwanci hali abaya akan son wata patient daya ce ya hadu da ita, saide yace mun ya ganta ahalin na mara kyau domin an mata fyade ya sinceta, nikuma nace masa da raina dai bazan bari wacce bata tare da mutuncinta ta shigo cikin zuri'a ta ba, na kuma ce masa kawar Hanan Abrar ze aura, domin na yaba da nutsuwarta duk da cewa ban taba haduwa da ita azahiri ba... Ajiyar zuciya ta saki kana ta cigaba da cewa; sai dai yanzu na kasa gane komai, domin naji Hanan tace kawarta ce Abrar, ga Aaban daya nuna shima yasanta, gashi naji kaima kace kana mata kallon sani, daddynsu am totally confused na kasa gane komai"...

jinjina kai daddy yayi yace "abokina zaka iya mana bayanin inda kasanta?"

kallon Abrar yayi hadi da cewa "itace wacce na gaya wa mum inaso... nan ya sake bada labarin abunda ya faru adaren daya fara haduwa da Abrar din

"ikon Allah" daddy yace yana girmama girman al'amarin, "idan na fahimce ku, wanna yarinyar kawar Hanan ce, wacce kikeso Abokina ya aura, wanda baki san cewa itace dai shi abokin nawa ke baki labarin cewa ita yakeso ba,,,, nima kuma nasanta domin aranar dana je taron yaye dalibai dinsu a cyprus na hadu da ita, domin Hanan ta gabatar min da ita amatsayin kawarta, sedai ranar lafiya lau na ganta tsabanin yau, ko hanan zaki iya bamu labarin yadda akayi take wanna halin yanzu...

hawaye hanan tashare zata yi magana kenan mummy tayi saurin cewa "daddynsu wacce bayani zata yi kuma ? bayan ga abu afili, yarinya kawai taje ta zubar da mutuncin ta atiti za'a raina mana hankali, nafada zan sake maimaitawa bazan hada jini da mara kamun kai ba, sannan zata bar gidan domin bazan iya zama da ita ba, domin ada nazata mai nutsuwa ce, shiyasa na ce ita Aabaan ze aura idan kuma bata bar gidanan, toh ban yarda ko Hanan tace zata kula da ita ba, wanda yadauko ta ya cigaba da dawainiyya da ita domin idan tafara haukan ba iyawa zamuyi da ita ba"

"kai mummy bafa mahaukaciya bace, sannan Abrar kamilalliya ce kaddara ce ta fada mata...

"ke dalla can rufemin baki, sakarya kawai" mummy na gama fadin haka ta bar wajen fuuuu, yayinda amal da itama sai yanzu ta gane kan zancen tabi bayan mummy.

Abrar kuwa abun tausayi ta shige jikin Aabaan saboda fadan da mummy keyi, Aaban idanunsa na lumshe duk be ji dadin yanda mummy ta aibata decent one din shi ba, amma ba yanda ya iya uwa ce dolensa yayi hakuri.

daddy daya bi mummy

Please Login or Register in order to submit comment